Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙoƙarin raba ka da ARYA. Kayi haƙuri lokacin banyi wani bincike mai zurfi akan ta ba shiyasa." inji Ranganu.
"ARYA?" Aymanul Faris ya tambayi kansa. "Wace ce kuma ARYA?"
Aljani Ranganu ya yi ajiyar numfashi ya ce, "Idan ka amince ka yafe min wannan kuskure da nayi ƙoƙarin aikatawa, to, zan faɗa maka wace ce ARYA."
"Na yafe maka, dan Allah kayi min bayani na gane..." inji Aymanul Faris.
Aljani Ranganu yayi murmushin jin daɗi ya ce, "Lokacin da nazo cikin wannan kogo na Razman nayi maka gargaɗi akan soyayyar Gimbiya Jaanu, na nuna maka illoli da rashin fa'idar soyayyar taku. Bayan tafiyata ban tsaya a ko'ina ba face cikin halwar tsafina, na gudanar da bincike akan wannan yarinya har tsahon wata guda ban leƙo koda waje ba.
"Binciken da nayi ya tabbatar min da cewa wannan yarinƴa ita ce ARYA ko kuma nace magajiyar sarauniya ARYA wadda tayi zamani da babban sarki Samudul Ansari.
"Tun kafun a haife ku, an riga da an rubuta labarin soyayyarku don haka ka ci gaba da ƙaunarta gami da kula da ita, ni da Barban zamu tabbatar da cewa abinda ake nema ya samu.
"TABBAS DOLE NE TAURIN YA AURI ARYA IDAN YANA SON ZAMA CIKAKKEN TAURIYEN."
Cikin tsananin mamaki Aymanul Faris ya dube shi ya ce, "Waye ne TAURIYEN? Tunda nake a rayuwata ban taɓa jin wannan sunan ba."
Aljani Ranganu ya yi dariya ya ce, "Tambaya guda ɗaya nake da ikon amsa maka a yanzu, kuma har na amsa maka. Sannan kuma na isar maka da saƙo; ka ci gaba da soyayya da gimbiya Jaanu." Aljanin na gama faɗin haka ya tashi ya fice daga cikin ɗakin.
Cikin mamaki da kaɗuwa Aymanul Faris ya bi bayansa, a wannan rana kansa ya gama kullewa.
Idan gimbiya Jaanu itace ARYA, to waye TAURIN kada dai ace shi ne?
Daga wannan rana aljani Ranganu ya samar da gida na ƙarƙashin ƙasa da ƙarfin sihirin tsafinsa, aka yiwa gidan ƙofofin shiga guda uku. Ƙofa ta farko tana amfani da madubi mai haska fuska, ƙofa ta biyu tana amfani zanen yatsu, ƙofa ta uku kuma da ƙarfin zuciyar mutum. A taƙaice sun samar da gida na ƙarƙashin ƙasa kamar wanda sarki Kuffuru yayi amfani dashi ya ɓoye Saiful Shiradu.
Tsahon kwanaki bakwai aka ɗauka ana baiwa Aymanul Faris da Barban horo akan yadda zasu iya ketare waɗannan ƙofofi masu irin wannan mugun tsaro, musamman aljani Ranganu ya ɗauko dakarun-aljanu dake tsaron babban birninsa ya basu wannan aiki na horar da su Barban.
Ranar sha-takwas ga watan Satumba, Barban ya shafi kambun tsafin dake hannunsa, su aljani Hubbus Dawan suka bayyana.
"Ku ɗauke mu, ku kaimu tsakiyar lambun gimbiya Jaanu. Kuyi amfani da salon tsafi mai mataki na bakwai, domin kada a san da zuwanmu." inji Barban.
*****RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 42: *Abubuwan da ake buƙata, wajen kamo Barban/Hodon*
*
*
✍️✍️✍️UMAR SANGARU✍️✍️✍️
*
A bakin ƙofar shiga fadar birnin Kufa wannan doki mai fuka-fuki ya dire sarki Kuffuru, yana sauƙa ya shafi wuyan dokin da hannunsa na hagu. Nan take dokin ya tashi sama cikin iska ya nufi gabas har ya ɓace a cikin gajimare.
Sarki Kuffuru ya mayar da takobinsa cikin kufe sannan ya saka dungulmin kayin sarki Ratanam a cikin jakar tsafinsa, yana shirin shiga cikin wannan fada kenan, yaga gimbiya Firziyya ta dawo bisa ingarman doki itama zata shiga cikin gidan sarautar. Ga dukkan alamu wani waje dabam taje.
"Daga ina kike?!" Sarki Kuffuru ya tambayeta cikin tsawa.
"Naje rangadi ne zuwa lambunka," inji gimbiya Firziyya.
Sarki Kuffuru ya yi mata wani kallo cikin rashin yarda, ya ce, "Je ki shirya kizo mu koma wajen boka Hubbazu don yau ne ranar da aljani Sheezuwa zai dawo da bayanan hanƴoƴin da za'a bi wajen kamo Barban." Yana gama faɗin hakan, ya shige cikin wannan gidan sarauta, gimbiya ta bi bayansa.
Ba tare da sun ɓata wani lokaci mai tsaho ba, suka kimtsa. Sarki Kuffuru ya kirawo babban hadimin aljaninsa ya ɗauke su ya kaisu har bakin kogon Hubbaz inda boka Hubbazu yake rayuwa. Aljanin yayi sallama da sarki Kuffuru ya ɓace ɓat!
Kuffuru ya buɗe ƙofar shiga wannan kogo kamar yadda ya saba, ya kama hannun gimbiya Jaanu suka shige cikin kogon.
A wannan rana ko hadimin aljani guda ɗaya basu tarar a wannan fada ba, babu kowa a cikin fadar daga boka Hubbazu sai kayan tsafinsa. Hakan ne yasa fadar tayi tsit, tamkar mutuwa ta gifta.
Boka Hubbazu ya taso da kansa yazo ya taryi sarki Kuffuru da gimbiya Firziyya ya kaisu har kan karagar mulkinsa ya zaunar da su. Suna zama abinci da abinsha suka bayyana bisa teburi. Ba gardamar komai sarki Kuffuru da ƴarsa suka ɗan taɓa wannan abinci.
Boka Hubbazu ya yi murmushi ya ce, "Tun safe nake ta duba hanyarku amma ban ga kunzo ba, tuni aljani Sheezuwa ya gama samo hanƴoƴin da za'a bi wajen kamo Barban. Yanzu haka kirana kawai yake jira..." Yana zuwa nan a zancensa ya kwalawa aljani Sheezuwa kira sau uku, nan take wannan shuɗin hayaƙi dake ci a cikin wannan kaskon ya dunƙule a waje guda ya bayar da siffar aljani Sheezuwa.
Aljanin ya risina ya gaishe da boka Hubbazu da sarki Kuffuru sannan shima ya samu kujera ya zauna, ya yi tsafi wani teburi madaidaici ya bayyana a tsakiyar su.
Aljanin ya zira hannu a cikin jakar-tsafinsa ya fiddo taswirar Barban ya shimfiɗeta akan wannan teburi. Kamar yadda aka sani wannan taswira tana ɗauke da zanen dukkanin ƙasashen duniya, sannan kuma mutum zai iya saka yatsunsa guda biyu yana zuƙo taswirar, tana ƙara girma tana nuna duk inda mutum ke buƙatar kallo.
"Kamar yadda kuka sani anyi amfani da sunan Hodon, sunan mahaifiyarsa, shekarar da aka haife shi, asalin cibiyarsa da zanen yatsunsa wajen samar da wannan taswira. Tabbas wannan aiki da nayi yayi kyau matuƙa, tunda an samu biyan buƙata wannan taswira ta samu kuma tana nuna mana duk inda wannan mutum yake a faɗin duniya.
"Inda ace gama-garin mutum zamu kamo da yanzun nan zamu duba wannan taswira muga inda yake a cikin abinda bai wuce rabin sa'a ba, mu kamo shi. Amma wannan mutum da muke so muyi amfani da wannan taswira wajen kamo shi, yafi kowa ƙarfin sihiri a duniya, yafi kowa hikima, basira da wayo a duniya. Karon farko lokacin da na kawo wannan taswira a yadda ta nuna yana cikin garin Jildaz, saboda wannan dalili yasa naje garin Jildaz domin nayi arba da wannan mutumi. Amma, kafun na isa garin tuni ya samu saƙo har ya bar garin.
"Ina so kuyi sani cewa wannan ɓarawo ya san da cewa an samar da taswirarsa, kuma ya shirya tsaf domin tunkarar duk wanda ke son kama shi. Kai, a yadda nake samun labari a wajen ɓoyayyun aljanu cewa suke, wannan ɓarawo da saninsa ya barni naje na tone ƙasar inda aka binne cibiyarsa kuma yana kallona naje kan dutsen Shayis na ƙauyensu na ɗakko zanen yatsunsa.
"Kun ga kenan, duk wanda zai bari a samo sirrukansa irin haka. Ba ƙaramin shiryayye bane. Na so ace kun bar sarki Kuffuru da wannan taswira ya tafi neman Barban, wallahi, da kamar yadda aka yi garkuwa da gimbiya Jaanu a watannin baya, haka shima Barban zai kama shi.
"Kai Kuffuru! Ka so kayi gaggawa da abinda ba'a son ayi masa gaggawa. Kana tunanin inda Barban zai kamu cikin sauƙi a yadda ka ɗauka, zai kai wannan lokaci bai shiga hannu ba?
"Barban cikakken matsafi ne wanda yake da cikakken shiri. Tsahon kwanaki ukun da nayi bana nan bincike naje na gudanar akan waɗansu mutane guda uku.
"Kuyi sani cewa hanƴoƴin da za'a bi wajen kamo Barban guda uku ne; hanƴa ta farko dole ne a samo SADAUKAI UKU masu baiwa ta musamman. Hanƴa ta biyu ita ce dole sai an ginawa Barban gidan kurkuku mai zaman kanta, wadda komai ƙarfin sihirin tsafi ba zai karyata ba, komai ƙarfin damtse ba zai ɓalla ta ba. Sannan kuma komai hikimar mutum da basirarsa bai isa ya gano fasalin yadda wannan kurkuku take ba. Hanƴa ta uku dole ne a kawar da aljanin da yake taimakawa Barban, idan kuwa ba haka ba shi wannan aljani shi ne kaɗai zai iya kuɓutar da Barban daga wannan kurkuku da za'a gina masa shi kaɗai.
"SADAUKAI UKU ƴan baiwa su ne; SARKI KUFFURU, SARKI DARWAZU da SARAUNIYA RAUZIYYA. Waɗannan sadaukai guda uku su ne kaɗai zasu iya haɗa ƙarfi-da-ƙarfe su kamo Barban ta hanƴar amfani da wannan taswira." Aljani Sheezuwa ya ƙare wannan dogon bayani.
"Akwai mai tambaya a cikinku kafun na ci gaba da jawabi?" Ya tambaye su.
Caraf sarki Kuffuru ya amsa, "Sadaukai guda uku da zasu iya kamo wannan ɓarawo, shin zaka iya mana bayani akan kowanne ɗaya daga cikin mu da kuma amfaninsa? Meyasa Barban ya bari aka samar da taswirarsa, shin a wannan lokaci ya shirya miƙa kansa ne ga sarakunan da ya yiwa sata? Sannan kurkukun da za'a ginawa Barban da wanne irin tubali za'a yi amfani wanda tsafi ba zai ci shi ba, ƙarfin damtse ba zai fasa shi ba, sannan hikimar mutum bazata iya gane fasalinsa ba. Wanne irin tubali ne?"
Aljani Sheezuwa ya yi murmushi ya ce, "Amsar waɗannan tambayoyi naka, su ne jawabina na gaba.
"Kai Kuffuru kana daga cikin sadaukai uku ƴan baiwa da zasu iya kamo Barban; Baiwar ka ita ce baka da tsoro, kana da tsananin kwarjini. Amfaninka a wannan aiki shi ne, duk duniya kaine kaɗai kake da takobi wacce take daidai da takobin Saiful Shiradu. Wannan takobi taka tana iya samar da halittu guda talatin, ciki har da sadaukai jinin Infiro. Kayi sani cewa ƙarfin sadaukai jinin Infiro kaɗai daidai yake da ƙarfin sadaukan bil'adama dubu goma. Amma, a wannan aiki ba'a buƙatar ƙarfin waɗannan sadaukai, abinda kawai ake buƙata shi ne su ɗauki siffarka. Zaka rarraba su kaso daban-daban, idan aka ganka anan, aka ganka acan. To, tabbas za'a razana da shirinka. Aikin da zaka yi a wannan tafiya da zakuyi ba shi da wani yawa, shiyasa zakaji aikin kamar kame-kame. Sauran abokan aikin naka guda biyu sun fika amfani, don haka bari nayi maka bayanin amfanin da zasuyi maka dalla-dalla.
"Mutanen da ke rayuwa a saman tsaunin Barzasa, ƴan wata ƙabila ce da ake kira Edwan. Kamar yadda yazo a littatafan tarihi da dama, wannan ƙabila ta Edwan tana da kusanci sosai da baƙaƙen aljanun dake rayuwa a saman tsaunikan nasu. Saboda tsananin kusancin dake tsakaninsu ance kowanne ɗan ƙabilar Edwan yana da aljani nasa na kansa, ance a lokuta da dama aljanun su kan arawa waɗannan mutane dake da mallakinsu ƙarfinsu su yaƙi abokin gaba da shi. Ya kai Kuffuru idan baka manta ba, lokacin da sarauniya Rauziyya tazo kurkukun mutuwa, bayan kun yi baƙin gumurzu ta kirawo waɗansu ɗalasimai na tsafi waɗanda suka sa gunki Barzasa bayyana a cikin wannan kurkuku, har dai tayi jifa da kai can yankin ƙasar Fairul-Faizar. To, ka sani cewa da ƙarfin aljani gunki Barzas tayi amfani wajen cin galaba akan ka.
"Aljani Barzas wani irin shu'umin aljani ne, yana iya samar da taswirar kowanne irin mutum a duniya. Matuƙar dai aka ce ya san sunan wannan mutumi. Shi ne ya samar da taswirar yarima Marganu wacce suka yi amfani da ita suka kawowa kurkukun mutuwa farmaki. Aljani Barzas baya buƙatar zanen hannu ko kuma sunan mahaifiya, abinda kawai yake buƙata wajen samar da taswira shi ne ainihin sunan mutum.
"Eh, mun samar da taswirar Barban amma ku sani cewa a kowanne lokaci wannan taswira zata iya daina aiki, kuma idan muka ga inda Barban yake kafun ma muje wajen labari zai riske shi. Yayi saurin ƙaura daga wajen.
"Idan muna so wannan taswira ta dawo aiki din-din-din, dole ne a kaiwa ita sarauniya Rauziyya tayi mana gyare-gyare sosai a kanta. Sannan kuma waɗansu lunguna da saƙo na wannan taswira babu wanda zai gano a ina suke da inda za'a tarar dasu face Rauziyya.
"A duk lokacin da gumurzu yayi gumurzu ko bala'i yayi bala'i, sarauniya Rauziyya zata iya kiran aljani Barzas ya kawo ɗauki.
"Don haka ina so na jaddada muku cewa, TAFIYA DA RAUZIYYA WAJEN KAMO BARBAN YA ZAMO DOLE."
Sarki Kuffuru ya tari numfashin aljani Sheezuwa ya ce, "Kana nufin ka ce sai mun haɗa kai da wannan shaiɗaniya? Wadda tuni na riga nayi rantsuwa akan sai na wulaƙanta ta?"
Aljani Sheezuwa yayi dariya ya ce, "Wannan kuma tsakaninku, ni umarnin da shugabana ya bani nake cikawa.
"Sarki Darwazu, ɗan ƙabilar Adbéncan ne. Mutanen wannan ƙabila da gashi ruwan-toka ake haihuwarsu. Sirrin dake jikin wannan gashi nasu yana da yawan gaske. Abu na farko shi ne su matsafan gaske ne, duk tsafin da aka ce ma ɗan ƙabilar Adbéncan ne yayi shi, to yana aiki sosai. Sannan kuma, tsafi baya tasiri akan su sosai. Komai ƙarfin sihirin tsafin waje suna iya ratsawa su wuce lafiya. Bincike ya tabbatar da cewa dukkan wajajen da Barban yake ɓuya, wajaje ne masu mugun sihirin tsafi. Babu wanda ya isa ya gano wajajen balle harma yayi tunanin zuwa, kai koda mutum yaje bai isa ya iya shiga cikin wurin ba, saboda ƙarfin tsafin wajen. Sannan kuma, duk duniya ƴan ƙabilar Adbéncan ne kaɗai ke iya sarrafa ƴan ƙabilar Edwan saboda tsafi baya tasiri akansu yasa waɗannan aljanu ke tsananin shakkar ƴan ƙabilar Adbéncan.
"Duk duniya in banda Darwazu babu wanda ya isa, yayi gaba da gaba da sarauniya Rauziyya kuma ta saurare shi. Don haka kafun kuje birnin Barzas dole sai kun samu haɗin kan Darwazu ɗari bisa ɗari. Sauran amsar tambayoyinka guda biyu kuma sai gaba zan sanar da ku."
Aljani Sheezuwa na rufe bakinsa sarki Kuffuru ya sake tambayarsa, "Tayaya zan iya shawo kan sarki Darwazu, bayan a halin yanzu ya gano cewa ni ne wanda yaje har ƙasarsa ya sato tsoho Saihar? Sannan tayaya zan iya shawo kan sarauniya Rauziyya, bayan na hanata ɗaukar yarima Marganu a cikin kurkukuna?"
Aljani Sheezuwa ya ƙyalƙyale da dariya ya ce, "Dangane da batun sarki Darwazu kada ka ɗagawa kanka hankali, shi da kansa zaizo har birninka ya nemi haɗin kanka bisa wannan buƙata saboda haka bokansa ya faɗa masa.
"Sannan maganar sarauniya Rauziyya ai ka bawa kanka amsa. Meyasa sarauniya Rauziyya ta haɗo gagarumar runduna ta kawowa kurkukun mutuwa hari?" Sarki Kuffuru ya ce, "Saboda ta kwaci yarima Marganu taje su ɗauki fansar abinda yayi musu."
Aljani Sheezuwa ya ce, "To me zai hana ka ɗauki Marganu, ka kai mata har kan wannan tsauni nata ka bata shi kyauta, sannan ka nemi haɗin kanta akan wannan aiki. Na tabbata indai kayi hakan sarauniya Rauziyya zata amince. Saboda idan bata yarda an haɗa kai da ita an kamo Barban ba, akwai yiwuwar nan gaba ya sato wani abu daga gareta."
Sarki Kuffuru ya cika da tsananin farin ciki ya ce, "Gaisheka shugaban masu hikima na duniya, tabbas kayi hange mai kyau. Indai na kaiwa sarauniya Rauziyya yarima Marganu, babu abinda zai hanata haɗa kai da ni!"
To, a gefe guda kuma gimbiya Firziyya ce tayi shuru, tana ta kukan-zuci. Tuni gimbiya Firziyya ta kamu da tsananin ƙaunar Marganu, kamar yadda take ƙaunar ranta. Babu irin ƙoƙarin da bata yi ba wajen kuɓutar da Marganu daga kurkukun azaba-uku ba amma abu ya gagara, saboda an rasa sadaukan da zasuyi gangancin sayar da rayukansu su tunkari wannan kurkuku.
A yanzu da taji sarki Kuffuru da aljani Sheezuwa suna maganar bayar da Marganu ga sarauniya Rauziyya domin a yankawa gunki Barzasa jininsa, sai hankalinta dubu yayi mummunan tashi. Tabbas ta kowanne hali sai ta hana faruwar wannan al'amari koda kuwa hakan zai zamo silar rugujewar alaƙar dake tsakaninta da mahaifinta. Wannan shi ne alwashin da gimbiya Firziyya ta ɗauka a ranta, ta zaɓi tayi rayuwar farin-ciki da Marganu akan ta zauna tare da sarki Kuffuru.
"Kaje ka gama haɗo kan sarki Darwazu da sarauniya Rauziyya, idan kuka haɗu ku uku sai kuzo nayi muku bayanin yadda za'a fara neman Barban." inji aljani Sheezuwa.
Da wannan sarki Kuffuru yayi sallama da boka Hubbazu da aljani Sheezuwa ya kama hannun gimbiya Firziyya suka fito daga cikin wannan kogo, suna fitowa wannan aljani ya ɗauke su ya mayar dasu birnin Kufa.
Sarki Kuffuru na dira a ƙofar fadarsa, wani badakare ya rugo da gudu ya ce, "Ya shugabana, tunda sassafe kayi wani baƙo basarake, yana can bayan gari yana jiran iso daga gareka."
"Basarake?" inji sarki Kuffuru. "Wanne sarki ne?"
Wannan badakare ya ce, "Naji ƴan uwana dakaru, suna maganar wai sarkin birnin Askandariyya ne yazo."
"A je a taho da shi!" Sarki Kuffuru ya bayar da umarni.
Wannan badakare ya ruga da gudu ya tafi, sarki Kuffuru ya kama hannun Firziyya suka je cikin wannan fada tasa suka zauna suna jiran zuwan sarki Darwazu.
Tsahon rabin sa'a suna zaune suna tattaunawa, kwatsam, sai suka jiwo bugun tambura da tashin algaitu. Sarki Darwazu ya iso.
Sarki Kuffuru ya miƙe tsaye, sarki Darwazu na shigowa ya bishi da kallo kamar baisan abinda ke tafe da sarkin ba.
Sarki Darwazu ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa ya ce, "Meyasa wancan lokacin da kaje birnina baka ce min kaine Kuffuru ba? Shin ka san yadda muke nemanka sosai ni da boka Balwaz kuwa?"
Cikin jin daɗi sarki Kuffuru ya kamo kafaɗun sarki Darwazu ya tashe shi tsaye, ya miƙa masa hannu suka gaisa.
"Sarki baya taɓa durƙusawa sarki. Daga yau ka zamo babban abokina, zamu haɗa kai, mu yaƙi abokan gaba tare, zamu haɗa kai wajen kamo Barban!" inji sarki Kuffuru.
"Na amince ɗari bisa ɗari, kuma nayi godiya sosai." inji Darwazu.
Nan dai sarki Kuffuru yasa aka kawowa sarki Darwazu abinci mai rai da lafiya, sannan aka haɗa shi da hadimi wanda zai kai shi masauƙinsa ya huta. Idan ya gama hutawa sai su tsara yadda zasuje tsaunin Barzasa wajen sarauniya Rauziyya.
Sarki Darwazu na kwanciya a cikin masauƙinsa barci mai nauyin gaske, yayi gaba da shi.
Tsahon kwanaki biyu ya ɗauka yana hutawa sannan suka sake keɓewa shi da sarki Kuffuru a cikin wata rumfa.
"Ka bar min alhakin kula da arnan dajin tsaunin Barzasa, kuma ka barmin alhakin yiwa sarauniya Rauziyya magana. Abinda kawai nake buƙata a wajenka shi ne ya zamanto kaine wanda zai damƙa mata Marganu hannu da hannu." inji sarki Darwazu.
Sarki Kuffuru ya yi murmushi ya ce, "Ka ɗauke aiki mai wahalan, yanzu muje na ɗakko kan sarki Ratanam muje kurkukun azaba-uku na nunawa Marganu shi, sannan mu ɗauke shi daga nan mu wuce zuwa tsaunin Barzasa mu damƙawa sarauniya Rauziyya ɗan banza."
Sarki Darwazu ya yi dariya ya ce, "Tabbas idan Marganu yayi arba da kan mahaifinsa a hannunka zuciyarsa zata yanke yayi ta kuka, kuma na tabbata ba zai daina jimami ba, har sarauniya Rauziyya ta yanka shi."
Sarki Kuffuru ya yi dariya sannan ya miƙe tsaye ya nufi cikin gidan sarautarsa, Darwazu na biye dashi.
"A lokacin da ka rasa wani abokin, ubangiji zai kawo maka wani. Ga shi na rasa tsinanne Ratanam, ubangiji ya kawo min kai." inji sarki Kuffuru.
"Haka ne, kuma idan ka rasa wata masoyiyar Allah zai kawo ma wata." inji sarki Darwazu.
Kuffuru yayi dariya yace, "Idan aka kawo maganar soyayya babu wanda nake tunowa kamar Marganu, shin ka san cewa duk masifan da Marganu ya shiga ba kowa bane ya janyo masa ba face soyayya? Yanzu ga shi zata sa mu kaishi inda za'a yanka shi?"
Cikin mamaki sarki Darwazu ya riƙe baki ya ce, "Amma waye ce matar tasa wadda ya sadaukar da rayuwarsa domin ta?"
"Mata?" Sarki Kuffuru ya yi dariya. "Ai yarinyar da yake ta haukan nan akanta, ko kaɗan bata ƙaunarshi. Yanzu haka halin nan da yake ciki ko tausaya masa sau ɗaya bata yi ba."
"Ah wannan mahaukaci ne," inji sarki Darwazu.
A daidai lokacin suka iso cikin ɗakin ajiyar sarki Kuffuru, Kuffuru ya ɗauko wannan jaka wacce ya sanya kan sarki Ratanam a cikinta. Ya fiddo kan, sannan ya kira aljaninsa. Ya cewa aljanin ya kaisu kurkukun azaba-uku, aljanin ya rankwafa suka haye bayansa, bai sauƙa a ko'ina ba sai a saman tsaunin Duksum.
Koda dakaru suka ga sarki Kuffuru sai duk suka zuzzube ƙasa bisa gwiwowinsu suka kwashi gaisuwa, sarki Kuffuru da Darwazu suka wuce kai tsaye izuwa cikin wannan kurkuku.
Aljani Duksum na ganin sarki Kuffuru ya faɗi ya yi masa sujjada.
"Gurin wa kake so a kaika?" inji ɗaya daga cikin kawunan wannan aljani. Ɗaya kayin nasa kuma yana hararar sarki Darwazu, ɗayan kuma yana kallon dungulmin kan Ratanam.
"Wajen yarima Marganu!!!"
Duksum yayi dariya da dukkanin waɗannan kayuka nasa guda uku sannan ya juya ya nufi wata hanya wacce zata sada shi da waɗansu ɗakuna guda uku. Sarki Kuffuru da sarki Darwazu suka take masa baya.
****RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 43: *Soyayya ta koma Ƙiyayya*
*
*
✍️✍️✍️UMAR SANGARU✍️✍️✍️
*
~Ɓangaren yarima Marganu.
*
Zaune yake a cikin wani ƙaramin ɗaki wanda mutum bai isa ya kwanta ko kuma ya miƙe sawayensa a ciki ba. Marganu ya kifa kansa akan gwiwowinsa yana ta kuka gami da begen mahaifinsa da kuma gimbiya Jaanu.
Wani abun al'ajabi shi ne duk wannan abu da ya faru dashi, soyayyar gimbiya Jaanu na nan a cikin zuciyarsa. Idan ma yaji ya tsaneta, baya wuce na ƴan daƙiƙu ko sa'o'i soyayyarta zata sake dawowa ransa.
Wannan ɗaki da yake ciki, shi ne ɗaki na uku a cikin jerin ɗakuna guda uku da ake baiwa dukkan wani fursuna da aka kawo wannan kurkuku.
Maganar azabobin da ya sha a wannan kurkuku kuma, ba'a magana. Domin aljani Duksum bai taɓa jin ya tsani wani, kamar Marganu ba. Hakan ne yasa azabobin da ya yiwa Marganu suka fito dabam, bai taɓa tsammanin Marganu zai iya jure azabobin ɗaki na farko ba balle ɗaki na biyu, amma ga shi yanzu Marganu na cikin ɗaki na uku wanda yana kammala shi, sarki Kuffuru zai iya sallamarsa daga kurkukun gaba ɗaya.
Dukda cewa Marganu ya sha baƙar wahala a wannan kurkuku, jikinsa na sadaukai na nan a yadda yake, sannan kyakkyawar fuskarsa ma na nan a yadda take. Sai dai ƴan tabo ɗaya-biyu da ba za'a rasa ba.
Ranar da sarki Kuffuru ya sare kan sarki Ratanam, a wannan rana kwata-kwata Marganu rasa sukuni yayi, ya gagara zaune ko tsaye. Dukda cewa bai san me yake faruwa ba, amma jikinsa yana bashi wani mummunan abu na faruwa a wani waje dabam.
Shin gimbiya Jaanu ce aka sake sacewa?
Shin wani abu ne ya faru da mahaifinsa?
Waɗannan su ne tambayoyin da suka fara

Please Login or Register in order to submit comment