Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Koda Aymanul Faris yazo nan a tunaninsa sai ransa ya ɓaci, zuciyarsa ta kufulo, jijiyoyin jikinsa suka kukkumbura suka yi burɗin-burɗin. Ya ɗaga takobinsa sama ya afkawa waɗannan aljanu suka ruguntsume da azababben yaƙi mai razanarwa.
A wannan karon waɗannan aljanu da takubban hannunsu suke aiki wajen kawo masa hari, da yake wannan karon Aymanul Faris a fusace yake sai yaƙin ya fara daɗin kallo. Ba zaka ji sautin komai a cikin wannan husumiya ba, sai haɗuwar ƙarafa gami da kururuwar jaruman.
Tsahon sa'a guda aka ɗauka ana wannan gumurzu ba tare an sami wani canji ba; Aymanul Faris na ta ƙoƙarin kare kansa gami da mayar da martani. Su kuma waɗannan aljanu kawai sauƙe masa ruwan sara da suka suke, ko kaɗan basa ƙokarin kansu. Kuma koda takobin Aymanul Faris ta dira a jikinsu, ba ta yi musu illa kai kace duwatsu ma yake sara.
Koda sa'a guda ta shuɗe sai Aymanul Faris ya fara haki, alamun ya fara gajiya amma waɗannan aljanu guda shida ko alamun gajiya babu a jikinsu. Kai kace a sannan ma suka fara wannan gumurzu.
Ana cikin wannan hali ne ɗaya daga cikin aljanun ya sami nasarar kaftawa Aymanul Faris sara a gefen ƙirjinsa, takobin aljanin ta tsaga wannan baƙar riga ta Aymanul Faris sannan ta yanki ƙirjinsa, jini ya tsatstsafo. Aymanul Faris ya yi ƙara gami da dafe wannan rauni na ƙirjinsa a lokacin waɗansu guda huɗu suka kawo masa suka da tsinin takubbansu guda huɗu a tare, biyu ta baya, biyu ta gaba. Cikin zafin nama da ƙwarewa Aymanul Faris ya kaucewa guda uku daga cikinsu, ɗaya takobin kuma ta soke shi a cikinsa ta baya. Nan fa Aymanul Faris ya taƙarƙare ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa sakamakon mugun zogin da yaji.
Cikin tsananin ƙarfin hali da juriya Aymanul Faris ya yi dungure ƙasa ya suri takobin ɗan uwansu wanda ya kashe ɗinnan, ya yi amfani da wannan takobi ya fille kan wanda ya soka masa wuƙa ta baya. Take kan aljanin ya tashi sama sannan ya faɗo ƙasa cikin husumiyar.
Nan fa waɗannan aljanu guda biyar da suka rage suka sake fusata suka afkawa Aymanul Faris da sabon gumurzu, suka yi ta ɗauki ba daɗi har tsahon sa'a uku da rabi, sannan Aymanul Faris ya kashe su gaba ɗayansu a lokacin suka sossoka masa takobi har sau uku.
Iya rayuwar Aymanul Faris bai taɓa shan baƙar wahala irin ta wannan rana ba, yana gama kashe dakarun ya yanki jiki ya faɗi ƙasa sumamme.
Bayan kamar rabin sa'a da faruwar wannan al'amari sai ga Barban ya shigo cikin wannan husumiya, da wannan doguwar igiya da Aymanul Faris ya yi amfani da ita ya shigo. Koda Barban yaga Aymanul Faris kwance face-face cikin jikin jini, sai hankalinsa ya ɗugunzuma don ya tabbatar da cewa akwai matsala. Aymanul Faris ne kaɗai wanda zai iya fitar dasu daga cikin wannan husumiya, ace ya mutu ko ya suma ai kawai matsala.
Barban ya tako a hankali ya nufi inda Aymanul Faris ke kwance, don ya tabbatar da cewa yana raye ko ya mutu. Bisa rashin sa'a yazo wucewa ta kusa da wannan tudu wanda aka ajiye wannan farar akwati, ya taka gawar ɗaya daga cikin aljanun nan da Aymanul Faris ya kashe ya zame, ya faɗi kan akwatin. Take hasken jikin akwatin ya ɗauke, wata ƙararrawa mai tsananin sauti ta fara kaɗawa a cikin wannan birni.
Nan fa alamun tsoro da razana suka bayyana ƙarara akan fuskar Barban. Ya ruga kan Aymanul Faris yana girgiza shi, "Ka tashi Ayman. Ka tashi. Idan baka tashi ba, yau ƙaryarmu ta ƙare." Yayi ta girgiza Aymanul Faris. Amma ina, kamar wanda ya mutu Aymanul Faris ko motsi baiyi ba. A duk bayan daƙiƙa sautin wannan ƙararrawa ƙaruwa yake maimakon raguwa.
Kwatsam! Barban yaga an zuro igiyoyi masu yawan gaske daga can saman husumiyar, da alamu dai sojoji ne zasu fara shigowa. Koda ya ɗaga kansa sai yayi arba da waɗansu samudawan ƙarti kimanin su talatin suna shigowa cikin husumiyar, kowannensu rataye da zabgegiyar takobi.
Koda maigida Barban yaga babu hanƴar tsira sai ya shafi kambun dake ɗaure a hannunsa, don waɗannan aljanu guda uku su bayyana domin su ɗauke su. Amma har tsahon daƙiƙa ɗari shuru basu bayyana ba. Al'amarin da ya sake razana maigida Barban kenan, a daidai lokacin kuma waɗannan murza-murzan dakaru suka fara sakkowa ƙasan husumiyar, suka kewaye maigida Barban da Aymanul Faris wanda ke kwance a ƙasa kamar gawa.
Dakarun suka zazzare takubbansu suka ritsa maigida Barban suka ce, ya miƙa wuya ko su hallaka shi. Maigida Barban ya ɗaga hannayensa sama alamun ya miƙa wuya. Ɗaya daga cikin dakarun yazo ta bayansa ya doke shi, Barban ya faɗi ƙasa rub da ciki. Badakaren ya saka ankwa ya ɗaure hannayen Barban ta baya. Ɗaya daga cikinsu ya nufi inda Aymanul Faris yake kwance zai daure shi.
Ba zato! Suka ga Aymanul Faris ya miƙe zaune zumbur, koda yaji ƙarar wannan ƙararrawa kuma yaga waɗannan dakaru, ya kuma kalli Barban ɗaure da ankwa a gefe guda sai ya fuskanci abinda ke faruwa. A lokacin ne yaji raunikan dake jikinsa sun fara masa sabon zogi da raɗaɗi, yaji da wuya ya iya miƙewa koda tsaye.
Aymanul Faris ya fuskanci cewa gazawarsa a wannan lokaci tana nufin an kama shi da laifin sata, an kama maigida Barban a matsayin shugaban ɓarayin duniya. Hakan kuma yana nufin ya rasa gimbiya Jaanu, ya rasa mahaifiyarsa, ya kuma rasa sauran abokansa da ƴan uwansa dake birnin Darul Barban.
Koda Aymanul Faris ya gama fuskantar haka sai ya miƙe tsaye cikin tsananin juriya da dakewa irinta mazan kwarai. Ya ɗaga takobinsa sama ya ruga kan waɗannan dakaru suka garƙame da sabon gumurzu. Ko daƙiƙa ɗari biyar masu kyau ba'a yi ba Aymanul Faris ya fara cin lagon waɗanan dakaru, saboda a matuƙar fusace yake kuma faɗa yake ko a mutu ko ayi rai.
Koda aka shafe sa'a biyu da rabi ana wannan gumurzu sai Aymanul Faris ya kashe waɗannan dakaru gaba ɗayansu, a lokacin ne kuma wasu dakarun kimanin guda ɗari suka sake kamo waɗannan dogin igiyoyi suka tsirgo cikin husumiyar, lamarin da ya ɗugunzuma hankalin Aymanul Faris kenan. Ya sake ɗaukar takobinsa ya afka musu, bayan ya sake shan baƙar wahala ya kashe mutum hamsin da ɗaya daga cikinsu, sauran kuma suka razana suka ja da baya. Aymanul Faris ya nuna su da takobinsa ya ce, "Duk wanda keso uwarsa ta haifi wani... Ya shigo?!" Dakarun suka tsaya zuru-zuru suna kallon juna.
Aymanul Faris ya sunkuya ya buɗe wannar farar akwati ya ɗauko lu'u-lu'u wacce ta ƙara haska wurin, ya ƙara haske fiye da ko yaushe. Ya cilla lu'u-lu'un cikin jakar guzurinsa, ya daka tsalle ya fillewa mutum biyar daga cikin dakarun nan kai, suka zube ƙasa matattu.
"Nafi ƙarfinku. Duk wanda yayi gangancin tunkarata kansa sai ya tsinke ya bar gangar jikinsa." Inji Aymanul Faris. Ya ruga inda maigida Barban ke kwance ya sare ankwar da aka ɗaure shi da ita. Aymanul Faris ya goya Barban a gadon bayansa, ya juyo ya yiwa dakarun nan wani kallo, sannan ya daka tsalle ya kama ɗaya daga cikin igiyoyin nan yayi sama, yana tafiya yana sassare sauran igiyoyin da aka zuro don kada waɗannan dakaru su biyo shi.
Maimakon tafiyar rabin sa'a sai da Aymanul Faris yai ta sa'a guda sannan ya fice daga cikin wannan husumiya gaba ɗaya. Kamar cewa ake fito jiranka ake. Yana fitowa yayi arba da gungun dakaru kimanin dubu arba'in tsaitsaye wasu bisa dawakai, wasu akan sawayensu.
Koda Aymanul Faris ya yi arba da waɗannan dakaru sai jikinsa yayi sanƴi, zuciyarsa ta karaya ya tabbatar da cewa lallai ko shi ne sa'a bai isa ya tserewa waɗannan dakaru ba. Maimakon Aymanul Faris ya sake tako wannan matattakala don ya sauƙo gurin waɗannan dakaru masu yawa ayi abinda za'ayi. Kawai sai ya juya da baya ya falfala da azababben gudu akan wannan baranda, ya nufi inda yake hango ƙarshenta ta ɗaya bangaren.
Ai kuwa cikin azababben gudu waɗannan dakaru ma suka rugo suka fara hawa kan wannan matattakala don su bi bayansa, kafun su zo tuni na gaba yayi gaba... Aymanul Faris na cikin gudu ya iso ƙarshen wannan baranda inda yayi arba da wani ƙaton rami wanda ruwa keta gudu a cikinsa kuma a haɗe yake da babban ƙoramar garin.
Ba tare da shawara ko shakkun komai ba, Aymanul Faris ya daka wawan tsalle daga saman wannan baranda ya afka cikin wannan ƙatuwar ƙorama mai tsananin gudun ruwa. Sai da yayi tafiya ta aƙalla daƙiƙa ɗari bakwai da hamsin a sama sannan ya faɗo cikin ruwan ƙoramar ya nutse. A daidai lokacin ne waɗannan dakaru suka ƙaraso wurin, suka tsaya cirko-cirko suna kallon cikin wannan ƙorama ko zasu ga su Aymanul Faris sun taso amma shuru babu su, babu labarinsu.
Waɗannan dakaru suka tsaya suka rasa meye zasuyi, inda ace su Aymanul Faris basu saci farin lu'u-lu'u ba, da babu ruwansu da su amma sun saci abinda yafi komai daraja a birnin Askandariyya. Suna tsaitsaye wani mutum ya bayyana a gabansu cikin iska.
Mutumin ya kasance zabgegen ƙato, kakkaura mai tsaho da murɗewa. Gashin kansa ruwan toka ne, idanunsa na nuna kafiya da razana. Babu komai a jikinsa face bante na fatar damisa, kana ganinsa zaka ga fankacecen ƙirji kamar na zaki.
"Aikinku yayi kyau. Ku koma cikin gari. Ku barni da waɗannan ɓarayin, tabbas zan sa aljanun-ruwa su kamo min su a cikin wannan ƙorama." Inji wannan mutumi cikin wata murya kamar hura tsohon ziga-zigi a maƙera. Mutumin na gama faɗin haka ya ɓace ɓat. Sauran dakarun kuma suka jujjuya suka nufi ƙasan barandar.
****RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 20: *Sadauki Zayyadu*
*
*
✍️✍️✍️ Umar Sangaru ✍️✍️✍️
*
Sai bayan tafiyar wuni guda cur, dakarun-masifa suka iso cikin kurkukun mutuwa. Kai tsaye suka wuce da yarima Marganu izuwa cikin wani ƙaton ɗaki mai tsananin duhu dake tsakiyar gidan kurkukun, wannan ɗaki yafi wanda aka kai Hajriya duhu da ban tsoro don mutum ba zai na kallon abubuwan cikin ɗakin sosai ba. Kan wata kujera aka je aka zaunar da yarima Marganu sannan aka ɗaɗɗaure hannayensa ta baya a jikin kujerar, waɗannan dakaru na gama haka suka fice daga cikin ɗakin suka bar shi, shi ɗaya jal.
Tsahon sa'a biyu da rabi yarima Marganu ya ɗauka a cikin wannan ɗaki sannan ya dawo hayyacinsa, koda ya ganshi a cikin ɗaki mai duhu kuma a ɗaɗɗaure cikin sarƙoƙi sai ransa ya ɓaci zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata ƙone. Nan take yaji ya tsani sarki Kuffuru kamar yadda ya tsani mutuwarsa, domin ya gano cewa duk wannan wulaƙanci da aka yi masa, sarki Kuffuru ne ya saka. Marganu yayi-yayi ya tsitstsinka waɗannan sarƙoƙi da suka ɗaure shi amma ya kasa, al'amarin da ya ɗugunzuma masa hankali kenan, ya tabbatar da cewa rayuwarsa na cikin matsala indai ya kuskura aka zo akayi masa azaba.
Marganu ya tuno cewa duk wannan wahala da yasha daga farkon tafiyarsa izuwa dajin Marsas zuwa wannan wulaƙanci da ake niyyar yi masa a kurkuku duk a dalilin soyayyar gimbiya Jaanu ce, nan take ransa ya ɓaci zuciyarsa ta kufulo yaji ya tsani gimbiya Jaanu. "Na rantse da darajar uwata, idan na fita daga wannan kurkuku naje wajen gimbiya Jaanu taƙi amincewa da buƙatata, wallahi hallakata zanyi." Ya faɗa a cikin ransa gami da cije haƙora.
Bayan kamar shuɗewar daƙiƙa ɗari biyu da arba'in Marganu ya fara jiwo takun sawaye na tunkaro wannan ɗaki da yake ciki, taku ne mai nauyi da ɗaukar hankali. Kai kace giwa ko kuma wata ƙatuwar dabba ke tafiya a wannan wuri. Marganu ya murtuƙe fuska kuma ya ci gaba da ƙoƙarin tsinka waɗannan sarƙoƙi amma ya kasa, har wani ƙatoton mutum ya shigo cikin ɗakin.
Mutumin ya kasance dogo kuma kakkaura. Idanuwansa jajaye ne tamkar gauta. Jikinsa a mummurɗe yake kamar wanda aka jerawa duwatsu. Kansa yasha aski ƙwal-kobo, amma yana da gemu da ƙasumba. Saboda tsananin tsawonsa tamkar zai taɓo rufin ɗakin, faɗin ƙirjinsa kuma ya kai kamu huɗu. Kai a taƙaice dai kana ganinsa kaga ragowar samudawa.
Wata ƙatuwar kujera wannan mutumi ya jawo ya zauna a gaban Marganu suka fuskanci juna. Koda Marganu ya haɗa idanu dashi, sai ya ji razana da firgici duk a lokaci guda suna ratsa shi. Saboda tsananin kwarjini da kamalar wannan mutumi, kuma ko kaɗan baiyi kalar masu imani ba.
"Suna na ZAYYADU ɗan GUNDAS, ni ne shugaban dakarun dake tsaron kurkukun mutuwa ta sarki Kuffuru. Ni ne wanda ya tura dakarun-masifa su kamoka saboda bin umarnin mai gidana Kuffuru. Ya kai wannan jarumi zan baka zaɓi guda biyu, na salon azabar da za'ai ma. Shin waye kake so yayi maka azaba, ni ko mataimakina Bandaru?" Inji sadauki Zayyadu.
Yarima Marganu ya sake turɓune fuskarsa, cikin shammace ya tofawa sadauki Zayyadu yawu a fuska ya ce, "Ƙarya kake, ƙasƙantaccen jarumi. Nafi ƙarfin ka wulaƙanta ni, na rantse da darajar uwata kayi sa'a a ɗaure nake, da sai..." Bai ƙarasa rufe bakinsa ba, sadauki Zayyadu ya sa lafcecen hannunsa ya zabga masa mari. Saboda ƙarfin wannan mari sai da yarima Marganu ya dungura ƙasa tare da kujerar da yake zaune.
"Ƙaryarka ta sha ƙarya," inji sadauki Zayyadu a lokacin da yake tuɓe rigar jikinsa. "Tabbas yau ka ɓata min rai matuƙa, har ni zaka tofawa yawu? Ka raina ni, amma yau zan koya maka hankali. Daga yau ba zaka sake raina wani ba." Zayyadu na gama faɗin haka ya gama tuɓe rigar jikinsa, nan fa jikin maza ya bayyana. A hankali ya ƙarasa inda yarima Marganu ke ɗaure yasa hannayensa biyu ya tsitstsinka sarƙoƙin da ƙarfin tsiya.
Ya ɗauki yarima Marganu kamar wanda ya ɗauki shara, ya fyaɗa shi a jikin bangon wannan ɗaki. Yana cewa, "Na kwanceka, taso mu gwada ƴar ƙwanji, yaro!" Yarima Marganu ya daddake ya miƙe tsaye, ya juyo inda sadauki Zayyadu ke tsaye. Nan fa yayi arba da narkeken ƙato wanda ko a labari bai taɓa jin mutum kamar sa ba.
Koda sadauki Zayyadu yaga yarima Marganu ya miƙe tsaye sai ya dako wannan tsalle cikin baƙin zafin nama, ya doki ƙirjin yarima Marganu da ƙafafunsa guda biyu. Marganu ya tashi kamar wanda aka harba yaje ya haɗu da bangon wannan ɗaki, ya baje ƙasa a galabaice. Zayyadu yazo ya haye kan ruwan cikin Marganu ya yi ta gabza masa naushi kamar ba gobe, fuskar Marganu tayi ta daujewa jini yana ta zuba amma ko kaɗan Marganu bai raga masa ba.
Kai duk wanda ya san yarima Marganu, yasan jarumtakarsa idan yaga yadda ya gagara taɓuka komai a hannun sadauki Zayyadu sai ya cika da tsananin mamaki, kuma dole mutum ya jinjinawa sadauki Zayyadu bisa ganin yadda yake wasa da yarima Marganu kamar wanda ya sami ɗansa.
"Kaɗan ma ka gani," inji sadauki Zayyadu. "Daga yau baza ka sake tofawa wani yawu ba." A wannan lokaci fuskar yarima Marganu tayi kaca-kaca ta sauya matuƙa. Ko motsin kirki ba yayi, wataƙila ya mutu, wataƙila kuma suma yai. Sadauki Zayyadu ya tashi daga kansa, ya nufi inda aka ajiye wata akwati ta ƙarfe ya jawota. Ya buɗe wannan akwati inda kayayyakin kaifi suka bayyana irinsu almakashi mai kaifi, adduna masu faɗi da kaifin bala'i da sauran kayayyakin azaba irin na gidan kurkukun mutuwa.
Zayyadu ya ɗauki wasu wuƙaƙe masu tsananin kaifi guda biyu, ya nufi inda Marganu ke kwance. Yana zuwa kansa yasa waɗannan wuƙaƙe guda biyu ya fara zane akan ƙirjin yarima Marganu, nan fa jini ya fara tsatstsafowa daga cikin inda yake yankan. Lamarin da yasa Marganu ya fara mutsu-mutsu yana kwarara ihu kenan, sadauki Zayyadu yayi murmushi ya ce, "Ashe kana raye?" Maimakon ya daina yankan ƙirjin Marganu, kawai sai ya ci gaba yana ƙyalƙyala dariyar mugunta. A haka dai har jikin Marganu gaba ɗaya yayi fata-fata da jini. Kai babu yadda za'ayi ka kalli Marganu a wannan hali kace yana da sauran rai, saboda ɗan-karen dukan da yasha da kuma azabar da aka gana masa.
Sadauki Zayyadu ya sunkuya ya ɗauki Marganu akan kafaɗarsa ya juya ya nufi ƙofar ficewa daga cikin wannan ɗaki na duhu, yana fitowa daga cikin wannan ɗaki dakaru guda biyar suka rugo da gudu suka karɓi Marganu daga hannunsa. Zayyadu ya dube su ya ce, "Ku kaishi wurin sadauki Bandaru ya ci gaba da gana masa azaba har sai sarki Kuffuru ya neme shi." Dakarun suka ruga da gudu suka nufi ɗakin duhu na sadauki Bandaru.
Har a wannan lokaci Marganu bai ma san inda hankalinsa yake ba, komai rashin tausayin mutum idan yaga halin da Marganu ya shiga sai ya tausaya masa. Amma idan mutum ya tuno cewa duk wannan wahala da Marganu ke sha a sanadiyar soyayyar gimbiya Jaanu ce, sai ya ce tabbas Marganu ya cika mahaukaci wanda baida hankali sai kace gimbiya Jaanu ce kaɗai a duniya?
Ana shiga cikin ɗakin duhu na sadauki Bandaru aka zaunar da yarima Marganu akan wannan kujera wacce aka zaunar da Hajriya akai, Bandaru ya dube su ya ce, "Meyasa zaka kawo min nakasasshe wanda ya kusa mutuwa?" Ɗaya daga cikin dakarun nan yayi gyaran murya ya ce, "Hannun shugaba Zayyadu ya shiga shiyasa ka gan shi haka." Sadauki Bandaru ya ƙyalƙyale da dariya ya ce, "Tab... Duk yadda akayi ya yiwa shugaba rashin kunƴa. Me shugaba ya ce za'ayi masa?" Badakaren nan ya ce, "Shugaba ya ce, ka ci gaba da gana masa azaba har zuwa lokacin da sarki Kuffuru zai neme shi." Bandaru ya sake ƙyalƙyalewa da dariya ya ce, "Da kyau. Yaushe rabona da samun fursuna?"
Tun daga wannan rana aka ci gaba da ganawa yarima Marganu azabobi a cikin kurkukun mutuwa, babu dare babu rana kullum cikin azabtar da shi ake. Marganu baya samun isasshen abinci, baya samun isasshen barci lamarin da yasa ya fara ramewa kenan, idan ba farin sani mutum yayi masa ba bazai gane shi ba. Har tsahon kwana talatin sarki Kuffuru bai neme shi ba, kuma bai ce a daina yi masa azaba ba. Marganu dai ya riga ya sallama rayuwar duniya, don ya tabbatar da cewa shi da jin daɗi kam sun raba gari, indai ba barin wannan kurkuku yayi ba. Marganu ya ƙudurce a ransa cewa, soyayyar gimbiya Jaanu ce ta jawo masa wannan ƙasƙanci kuma tabbas sai ya ɗauki FANSA akanta. Babu abinda zai yiwa gimbiya Jaanu ya huce wannan takaici da aka ƙunsa masa face yayi mata fyaɗe kuma ya kasheta, wannan shi ne alwashin da yarima Marganu ya ɗauka a cikin ransa.
A ranar da kwana na talatin ta cika ɗinne da yamma, yarima Marganu na zaune a cikin wannan ɗakin duhu. Sadauki Bandaru ya gama jibgarsa kamar yadda ya saba, an kawo masa wani irin abinci mai wari da rashin ɗanɗano. Babu yadda ya iya dole ne yaci wannan abinci, idan bai ci ba ƴunwa zata kashe shi. Bayan ya gama cin abincin, ya sunkuyar da kansa ƙasa yana kukan takaici. Ba zato yaji ana buɗe ƙofar wannan kurkuku, yarima Marganu ya ɗago kansa yana jira yaga waye za'a shigo dashi cikin wannan kurkuku.
Sadauki Zayyadu ya gani ya shigo cikin wannan ɗaki da yake ciki, Zayyadu ya dube shi ya bushe da dariyar mugunta ya ce, "Wannan shi ake kira da kurkuku. Ba ma ɗagawa uban kowa ƙafa. Tabbas ko yanzu mun koya maka hankali... Ta shi mu tafi sarki Kuffuru ke son ganinka." Koda yarima Marganu yaji abinda Zayyadu ya ce sai ya murtuƙe fuska, ya miƙe tsaye ya nufi ƙofar ficewa daga ɗakin. Idan ka gan shi zakaga yana tafiya a hankali, kamar zai faɗi sakamakon yadda ƴunwa tayi daga-daga da shi.
Sadauki Zayyadu ya bishi a baya suka nufi wani yanki na gidan kurkukun wanda aka ƙawata matuƙa, bayan tafiyar rabin sa'a, yarima Marganu ya hango sarki Kuffuru da gimbiya Firziyya zazzaune bisa waɗansu kujeru sun ƙura masa idanu daga nesa. Inda yarima Marganu zai matso yaga halin da gimbiya Firziyya ke ciki da sai ya gane akwai wani abu a ƙasa, don ko kaɗan fuskarta babu walwala sosai. Wataƙila tausayawa Marganu take, wataƙila kuma tsantsar ƙaunarsa ce ta kamata. Shi ko sarki Kuffuru murmushin mugunta kawai yake yiwa Marganu, ko kaɗan bai lura da halin da gimbiya Firziyya ke ciki ba.
Bayan ɗan lokaci ƙanƙani sadauki Zayyadu da yarima Marganu suka iso inda sarki Kuffuru ke zaune, Zayyadu ya gurfanar da Marganu a gaban kujerar da sarki Kuffuru ke zaune a kai. Sannan ya tsaya a bayan Marganu hannunsa guda bisa takobinsa yana shafata.
"Ya mu kayi da kai?," Inji sarki Kuffuru. "Kada ka zargeni akan abinda nayi ma kaine wanda ya jawowa kanka. Kace zaka kamo sarkin ɓarayi na duniya, ka kamo shi? Ka ce zaka kamo Aymanul Faris da jaruma Riya, ka kamo su? Na ce ka kama ko ɗaya daga cikin waɗannan mutane? Kuma don ka raina min hankali shi ne ko kazo ka bani haƙuri akan laifin da kayi min?" Sarki Kuffuru ya ƙare maganarsa yana kwantar da fushin zuciyarsa.
Marganu ya ɗago kansa a fusace ya dubi sarki Kuffuru cikin rashin tsoro ya ce, "Tabbas kayi min wulaƙanci son ranka amma ka jira kaga abinda zan yi ma. Na rantse da darajar uwata sai kayi kuka da idanunka..." Sarki Kuffuru ya ɗaga masa hannu alamun yayi shuru, sannan ya ce, "Kai yaro! Ka san waye Kuffuru kuwa? Ni ne fa maigidan mahaifinka da sarki Ayubul Zairiy dukkansu tamkar yarana haka suke, sai abinda na ce suyi. Mahaifinka babu irin roƙona da baiyi ba akan na sakeka daga wannan kurkuku amma na ƙi, saboda ka ɓata min rai wallahi. Yanzu zan baka zaɓi guda uku, idan har kana so na sakeka daga kurkukuna..." Marganu yayi caraf ya tari numfashin sarki Kuffuru ya ce, "Ka riƙe zaɓinka guda uku, bana buƙatar jinsu don ba zanyi ba. Kuma na rantse maka zamana a cikin wannan kurkuku ya kusa zuwa ƙarshe."
Koda sarki Kuffuru yaji alwashin da yarima Marganu yayi sai ya bushe da dariya yana cikin dariyar ne ya shammaci Marganu ya zabga masa mari a fuska, saboda ƙarfin marin sai da Marganu ya sulale ƙasa a gaban gimbiya Firziyya. Lamarin da yasa ya kalleta kenan, ai kuwa ba zato yaga hawaye na zubowa daga idanunta. Al'amarin da ya bashi mamaki kenan, saboda irin waɗannan hawaye ba kasafai suke zubowa ba, kuma irin hawayen da ake zubarwa ne lokacin da masoyi ke wulaƙanta. Nan take Marganu ya tuno lokacin da suke kan hanƴar zuwa kurkukun mutuwa tare da sarki Kuffuru, lokacin da gimbiya Firziyya ke satar kallonsa, take ya gane cewa lallai wannan gimbiya ta kamu da ƙaunarsa.
"Zan ga wanda zai ceceka a cikin wannan kurkuku, kuma tunda kayi min rashin kunƴa ka shigo kenan. A nan zaka ƙare sauran rayuwarka, har ka mutu. Zan rubuta takarda gobe-goben nan na aikawa sarki Ratanam cewa, ka ɓata min rai na hallaka ka. Tabbas anan za'a rufe shafinka kai kam." Inji sarki Kuffuru.
Ba zato, ba tsammani! Sai

Please Login or Register in order to submit comment