Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna tunanin yadda zasu afko daga saman wannan dogon gini ba tare da sunji raunin komai ba. Koda suka leƙo ƙasan ginin sai suka hango sarki Fairaz a cikin wannan tafkin wanka tare da ƴan-mata guda biyu suna wanka. Kewaye da wannan tafki kuwa, waɗansu irin samudawan ƙarti ne kimanin su arba'in keta kai-kawo suna tsaron lafiyar sarki.
Nan fa Aymanul Faris da Barban suka kalli juna suna ƙoƙarin yanke shawarar yadda zasu yi su dira daga wannan gini sannan kuma su kawar da waɗannan samudawan ƙarti a lokaci guda.
"Ayman, alhakin sumar da waɗannan dakaru," inji Barban. "Yana wuyanka. Dole ne ka sumar dasu, bana so kashe su. Saboda kashedi muka zo yiwa sarki Fairaz ba sata ba."
"Tayaya zamu saƙƙo daga saman wannan gini?" Inji Aymanul Faris.
Barban ya yi murmushi ya sake fiddo irin waɗannan murtuƙa-murtuƙan igiyoyi masu ƙugiya ya baiwa Aymanul Faris ɗaya, ya ce, "Dole ne mu san yadda zamu yi waɗannan igiyoyi su ratayo wuyan dakaru guda biyu daga cikin waɗancan dakaru indai muna so mu sauƙa cikin ƙoshin lafiya."
Barban na gama faɗin haka ya fara wulwula igiyar dake hannunsa yana saita wuyan wani badakare, shima Aymanul Faris sai yayi koyi da shi.
Sarki Fairaz na tsakar wanka shi da waɗannan ƴan-mata guda biyu cikin kwanciyar hankali da samun nishaɗi, dakarunsa nata kai-kawo amma basu isa su kalli abinda yake aikatawa da waɗannan ƴan-mata ba.
Kwatsam! Ba zato sai suka ga biyu daga cikinsu sun kwarara ihu, waɗansu igiyoyi guda biyu sun kanannaɗe wuyansu an janƴe su sama. Dakarun biyu na gama yin sama aka ga waɗansu mutane guda biyu sanƴe cikin baƙaƙen tufafi sun diro bakin wannan tafki.
Koda sarki Fairaz yayi arba da kalar waɗannan kaya guda biyu, sai gabansa ya faɗi ƙirjinsa ya buga da ƙarfi domin ya gano mai irin waɗannan kaya. Jikin sarki Fairaz ya fara kyarmar fusata, fuskarsa tana gatsinewa saboda tsananin jin haushi da tuno abinda ya faru a baya.
Nan take waɗannan dakaru suka kewaye Aymanul Faris da Barban a tsakiya suna masu ritsa su da makamai, Barban ya yi murmushi zai ratsa ta cikinsu ya wuce, ɗaya daga cikinsu yai tsalle ya kawo masa duka a ƙafada da dunƙulallen hannunsa. Kafun badakaren ya sami nasarar aiwatar da abinda yayi niyya tuni Aymanul Faris ya gabza masa naushi a wuya, take ya sulale ƙasa sumamme. Kai dukan nan da Aymanul Faris ya yiwa wannan badakare da ban al'ajabi yake, domin cikin zafin nama da kwanciyar hankali ya gabza masa dukan.
Koda sauran ƴan-uwan wannan badakre suka ga abinda ya faru sai suka afkowa su Aymanul Faris gaba ɗayansu suka ƴanƴame su. Barban dai na tsaye a inda yake, Aymanul Faris ne ya wanzu yana ta yawo a tsakiyar waɗannan dakaru yana ta hanɓare su suna zubewa ƙasa sumammu. Saboda tsananin zafin namarsa, cikin abinda bai wuce daƙiƙa ɗari huɗu da goma ba ya zubar da dukkanin waɗannan dakaru hamsin ɗin a wannan wuri, dukkaninsu sumammu.
Saboda tsananin mamaki da kaɗuwa sarki Fairaz gagara fitowa yayi daga cikin wannan tafki yayi. Na farko ga kwarjinin Barban wanda ke dukansa don ganin aljani yake yiwa Barban saboda yadda akayi Barban ya sace waɗannan sarƙoƙi na matarsa, dole ne yayi matuƙar mamaki. Na biyu kuma ga wannan baƙon-jarumi wanda Barban ya taho dashi wanda ƙarfin-damtsensa da iya yaƙinsa ya wuce tunaninsa.
Wurin wata kujera ta alfarma Barban ya ƙarisa wacce aka ajiye a bakin wannan tafki, sannan aka ajiye ƙaramin teburi wanda aka cika da kofunan shaye-shaye. Barban ya zauna akan wannan kujera sannan ya zuba shayi a cikin wani kofi ya fara sha.
"Ka gane ni?" Inji Barban.
Sarki Fairaz ya tunkuɗe ƴan-mata dake rakuɓe a jikinsa cikin tsoro, ya fito daga cikin wannan tafki yazo inda Barban ke zaune ya durƙusa bisa gwiwowinsa ya ce, "Ya kai wannan ɓarawo, dan Allah ka faɗa min abinda nayi maka har da zaka sace min sarƙoƙin da na baiwa matata a matsayin sadaki? Ka faɗa min duk abinda kake so na dukiya, na rantse zan baka idan har zaka dawo min da waɗannan sarƙoƙi. Kayi sani cewa ina kewar matata. Dan Allah." Sarki Fairaz ya ƙare maganarsa kamar zaiyi kuka.
"Kashedi nazo nayi maka," inji Barban. "Kana tsammanin zaku iya kamani ne?" Ya kurɓi wannan shayi. "Ku gwada ku gani." Barban ya ci gaba da kora wannan shayi. Har a wannan lokaci sarki Fairaz a durƙushe yake bisa gwiwowinsa.
"Kana ta shan shayi," inji sarki Fairaz. "Idan akwai guba fa?"
"Guba?!" Inji Barban fuska a yamutse.
Fairaz ya sake durƙusawa ya ce, "Ina roƙonka don girman iyayenka ka faɗa min, laifin da nai ma har ka sace min abinda yafi komai muhimmanci a rayuwata?"
"Ka san waye ce Hushriba?" Inji Barban.
Koda jin wannan suna sai Fairaz ya ja da baya a razane, daga bisani kuma ya dako wawan tsalle ya kawowa Barban duka a tsakar kai da dunƙulallun hannayensa.
*****RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 25: *Saihar al-Aswàd*
*
*
✍️✍️✍️ Umar Sangaru ✍️✍️✍️
*
Sarki Kuffuru bai bayyana a ko'ina ba, sai a tsakiyar fadar birninsa. Yana bayyana ya tura wani hadimi ya kirawo masa gimbiya Firziyya. Sannan ya wuce kai tsaye izuwa cikin turakarsa ya zauna yana tunanin tafiya zuwa birnin Askandariyya domin kamo wannan tsohon mutumi.
Yana cikin wannan tunani ne aka turo ƙofar wannan turaka, gimbiya Firziyya ce ta shigo sanƴe cikin baƙaƙen tufafi marasa nauyi sosai. Tazo har kan gadon sarki Kuffuru ta zauna, sannan ta dube shi ta ce, "Da fatan dai, kana lafiya? Ina wannan shegiyar matsafiya ta aika ka?"
Sarki Kuffuru ya yi murmushi ya ce, "Ai wannan jifa dani da wannan sarauniya tayi naji daɗinsa ba kaɗan ba..." Bai ƙarasa rufe bakinsa ba, gimbiya Firziyya ta tari numfashinsa ta ce, "Ya kai abbana, haƙiƙa baka fuskance ni ba. Ina nufin cewa wannan sarauniya tafi ƙarfinmu tunda har ta sami nasarar yin wurgi da kai, uwa-duniya. Wai shin ina ta wurga ka ne, har da kake cewa kaji daɗin wannan jifa da tayi da kai?" Sarki Kuffuru ya sake yin murmushi ya ce.
"Wannan ita ce tambayar da nake son kiyi min. Sanadiyar jifar da sarauniya Rauziyya tayi dani, na haɗu da sarkin birnin Fairul-Faizar, sarki Fairaz. Wannan sarki jagora ne na waɗansu sarakuna guda tamanin da uku da sarkin ɓarayin-duniya ya yiwa sata. Wannan sarki ya shaida min cewa bokayensa sun tabbatar da cewa ni ne kaɗai, wanda zai iya sanadiyar kamo wannan gagarumin ɓarawo. Ɗazu-ɗazun nan naje wajen boka Hubbazu kuma ya tabbatar min da cewa akwai wani dattijon mutum wanda yake da nasaba sosai da ɓarawo a cikin birnin Askandariyya yana bara, dole ne naje birnin Askandariyya na kamo wannan mutumi kuma na kaiwa shi boka Hubbazu domin yayi min bayanin yadda za'a iya kamo wannan ɓarawo. Je ki gama shiri kizo mu tafi izuwa birnin Askandariyya kamo wannan mutumi."
Gimbiya Firziyya na jin wannan batu ta miƙe tsaye da sauri ta nufi ƙofar ficewa daga turakar, har tazo bakin wannan ƙofa ta ficewa daga wannan turaka ta tsaya ta juyo ta dubi Kuffuru ta ce, "Ina yarima Marganu?!" Cikin wata irin murya mai nuna tausayawa da kulawa.
Sarki Kuffuru ya haɗe fuska ya ce, "Marganu? Me haɗinki da shi?" Gimbiya Firziyya ta ce, "Babu komai." Ta fice da sauri daga cikin turakar. Sarki Kuffuru ya bi bayanta da kallo cikin tsananin mamaki, mene ne ke tsakanin ƴata da yarima Marganu? Wataƙila tsantsar tausayinsa take ji, tun da dama can abokai ne kasancewar akwai dangantaka tsakanina da sarki Ratanam. Da wannan sarki Kuffuru ya kwantar da hankalinsa baiyi wani tunani mai kyau ba akan abinda ke tsakanin Marganu da ƴarsa Firziyya.
Yana cikin wannan hali ne gimbiya Firziyya ta dawo cikin turakar, sanƴe da jajayen tufafi samfurin birnin Misra wato doguwar riga da wando. Haƙiƙa waɗannan kaya ba ƙaramin kyawu suka yi mata ba. Sarki Kuffuru ya yi murmushi ya ce, "Da kyau ƴata, kamar kinsan cewa irin shigar da ya kamata muyi kenan wajen zuwa wannan birni." Yana faɗin haka ya miƙe tsaye ya ɗakko wata alkyabba ya sanƴa. Sannan ya tafa hannayensa wannan ƙaton aljani ya bayyana, kuma ya ranƙwafa.
Sarki Kuffuru da gimbiya Firziyya suka haye bayansa, shi kuma ya buɗe fuka-fukinsa ya tashi sama ya lulluka cikin gajimare ya ɓace ɓat! Bayan shuɗewar ƴan sa'o'i ya dira a farkon dajin Ras, sannan yai sallama da Kuffuru ya ɓace ɓat. Kuffuru da ƴarsa Firziyya suka tasarwa ƙofar shiga birnin Askandariyya kai tsaye. Sarki Kuffuru yai amfani da rawani ya rufe fuskarsa don kada a shaida shi.
"Ya kai abbana," inji gimbiya Firziyya. "Da wacce alama zaka iya gane wannan mutumi a cikin dubbannin mutane masu bara a cikin birnin Askandariyya?"
Sarki Kuffuru ya yi murmushi ya ce, "Wannan mutumi sunansa SAIHAR AL-ASWÀD. Ɗan wata ƙabila ce da ake kira Nùyes. Mutanen wannan ƙabila gashin kansu ruwan-ɗorawa ne, boka Hubbazu ya tabbatar min da cewa duk faɗin birnin Askandariyya babu ɗan-ƙabilar Nùyes idan ba wannan mutum ba. Kin ga kenan gano shi zaiyi mana sauƙi sosai, idan muka yi la'akari da bayanan boka Hubbazu." Sarki Kuffuru na rufe bakinsa suka iso bakin ƙofar shiga birnin Askandariyya, inda suka yi arba da mutane a jere layi guda, suna zuwa da ɗaiɗaya ana cajesu kamar dai yadda su Barban suka gani.
Babu musu sarki Kuffuru da ƴarsa Firziyya suka saje cikin mutane wato suka shiga cikin wannan layi na mutane, layi ya ci gaba da tafiya har aka zo kansu.
"Kai! Mene ne dalilin da yasa zaka rufe fuskarka, alhalin ka san cewa doka ce mai ƙarfi ba'a zuwa wannan wuri da rufaffiyar fuska?" Inji badakare Kuffan mai tsaron ƙofa.
Maimakon sarki Kuffuru ya bashi amsar wannan tambaya da yai masa, kawai sai ya ɗaga idanuwansa ya dakawa badakare Kuffan wani irin harara mai razana ƙaramin jarumi ya gudu. Wani irin iko na tsafi ya doki Kuffan take yaji tsikar jikinsa ta mimmiƙe, zufa ta fara keto masa. Tunda yake aiki a wannan wuri bai taɓa yin arba da mutum mai ƙarfin sihirin tsafi, kamar wannan mutumi mai rufaffiyar fuska ba.
Cikin razana Kuffan ya dubi bayi masu buɗe ƙofa ya ce a buɗewa wannan mutumi. Abin mamaki ba haka yaso a ransa ba, a ransa so yake kawai ya kama sarki Kuffuru ya kaishi wajen sarki Darwazu ayi masa hukunci amma bisa mamaki sai zuciyarsa taƙi bin wannan umarni, umarni ɗaya kawai ta sani shi ne yin abinda sarki Kuffuru keso. Lallai al'amarin sarki Kuffuru a ɓangaren tsafi ya girmama.
Ana gama buɗe wannan ƙofa Kuffuru ya kama hannun Firziyya suka shige cikin birnin, cikin kwanciyar hankali da nutsuwa. Kai kace ɗakin barcinsu zasu shiga a haka.
Wani abin mamaki da ya sake afkuwa shi ne kwata-kwata badakare Kuffan ya manta da su sarki Kuffuru, ya ɗinga ganin abun kamar mafarki ko almara wanda ba shi da tushe. Wannan shi ake kira TSAFI GASKIYAR MAI SHI.
Kuffuru na shiga cikin wannan birni ya fiddo madubin tsafinsa ya tsaya a gindin wata bishiya ya fara bincike. Madubin tsafin yai haske sannan ya fara nuna abinda ke faruwa tsakanin sarki Darwazu da wani dattijon mutum mai yawan gashi, ruwan-ɗorawa. Ga dukkan alamu tattaunawa ce ke gudana, don haka sai sarki Kuffuru da Firziyya suka kasa kunne.
"Ya sunanka?" Inji sarki Darwazu.
"Suna na SAIHARUL-WADI AL-ASWÀD, wannan shi ne cikakken sunana." Inji wannan dattijon mutum.
"Barka Saihar. Waɗansu ƴan tambayoyi nake so nayi maka, wanda idan ka bani amsarsu daidai, ina tabbatar maka da cewa kai da talauci kam, sai dai ka gani a wurin wasu. Amma hatta tattaɓa-kunnenka baza su san wannan kalma ta talauci ba." Sarki Darwazu ya faɗa.
Saihar ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ka faɗi tambayoyinka, naji. Amma dukiyarka sam bazata ta dameni ba."
Sarki Darwazu yai murmushi ya ce, "Tambayoyina su ne: WAYE NE BARBAN? MEYE ASALIN SUNANSA? WANNE ABU DA WANNE ABU YAKE SO? MEYE YAFI TSANA A RAYUWARSA? A WACCE SHEKARA AKA HAIFI BARBAN? Idan ka amsa min waɗannan tambayoyi dai-dai zan karrama ka sosai, zanyi maka goma-ta-arziki amma idan ka ƙi kuma, ba zan faɗa maka meye zanyi maka ba amma ka sani cewa wanda ke kwance cikin kabari sai yafi ka jin daɗi."
"BARBAN?" Saihar ya yamutse fuska. "Waye shi, ni bansan shi ba." Zuciyar sarki Darwazu ta fara tafarfasa ya ce, "Kada ka raina min hankali mana. Wannan mutumi kana da nasaba sosai dashi, ka isa kace min baka san shi ba?"
"Hmmm" Saihar yaja dogon numfashi. "Ya kai wannan sarki, kada kayi tunanin amfani da ƙarfinka zaisa na baka haɗin-kai. Kayi sani cewa babu irin jin-daɗin da ban samu a duniya ba, kada kayi tunanin azaba kaɗan zata sa na saduda. Ka fayyace min komai, idan kayi sa'a na baka haɗin-kai." Saihar ya faɗa cikin rashin tsoro da dakewar zuciya. Kai da ka ji muryar wannan dattijo zaka san ko kaɗan babu tsoro a cikinta.
Sarki Darwazu ya yi dariya ya ce, "BARBAN ɗanka ne na cikinka. Kuma a halin yanzu shi ne gagarumin ɓarawo da duniya take nema ido a rufe, kwanakin baya yazo har cikin wannan gidan sarauta tawa ya sace min farin lu'u-lu'una. Ya kai wannan tsoho, ka bani haɗin-kai ɗari bisa ɗari domin na samu nasarar kamo wannan ɓarawo, idan kuwa ka ƙi na rantse da karagar mulkina kulleka zanyi a kurkuku."
Tsoho Saihar ya zaro idanu cikin tsananin mamaki ya ce, "ƊANA? Kana nufin ɗana yana nan a raye?" Sarki Darwazu ya murtuƙe fuska ya ce, "Ka amsa min tambayoyina mana?!"
"Amma baka da hankali kuma baka da lissafi, ya za'ayi uba ya bayar da bayanan ɗansa. Aje a kamo shi ayi ta gana masa azaba? Ko bani da hankali kana ganin zan yarda na amsa maka waɗannan tambayoyi. ƊANA, ƊANA ne tabbas lokacin da yake yaro na wulaƙantashi da..." Saihar bai gama rufe bakinsa ba, sarki Darwazu ya zabga masa wawan mari wanda yasa ya tuntsire ƙasa, bakinsa ya fashe ya fara aman jini.
"Ƙarya kake... Dole sai ka amsa min waɗannan tambayoyi... Na bika ta ruwan-sanƴi ka ƙi, bari mu koma ta tsiya-tsiya..." inji sarki Darwazu. Ya juya ya dubi waɗansu dakaru guda huɗu ya ce, "Ku ɗauki wannan shashashan tsohon, ku kaishi gidan kurkukun THAIRAM. Wajen sadauki Zairamu ya yi ta gana masa azaba har sai yai bayani. Nima kuma ina zuwa da kaina don naga dattijon ɗan-rainin hankali ne."
Yana gama faɗin haka ya miƙe tsaye ya shige cikin gidan sarautarsa. Waɗannan dakaru guda huɗu suka rugo wajen da Saihar ke kwance suka ɗaɗɗaure shi da igiya sannan suka ɗauke shi suka fice dashi daga cikin wannan gida na sarauta.
A daidai lokacin ne sarki Kuffuru ya shafi madubin tsafin da hannunsa hoton komai ya ɗauke. Ya dubi gimbiya Firziyya ya ce, "Mun sami babbar dama ta ƙwace Saihar al-Aswàd. Zo muyi maza muje mu yiwa waɗannan dakaru kwantan-ɓauna a bayan gari." Yana gama faɗin haka ya dafa kafaɗar gimbiya Firziyya suka ɓace ɓat! Daga wannan waje.
Dakarun nan guda huɗu suka fito da Saihar a ɗaɗɗaure suka nufi wata siririyar hanƴa da ta nufi wani ƙaton tsauni wanda aka gina wata makekiyar kurkuku a samansa. Kasancewar a cikin birninsu suke tafiya, hankalinsu a kwance yake kuma suna da yaƙinin cewa babu abinda zai same su. Suna tafiya cikin nishaɗi suna ta yiwa Saihar tambayoyin izgilanci suna ƙyaƙyata dariya.
A tsakiyar wannan siririyar hanƴa akwai wata doguwar bishiya mai yawan duhuwa a gefen hanƴar. Kafun su iso gindin wannan bishiya ɗaya daga cikinsu ya raɓe, ga dukkan alamu wata buƙata zai kawar. Sauran basu tsaya jiransa ba suka ci gaba da tafiya, har suka iso gindin wannan bishiya suka wuceta, sai dai kuma basu yi nisa ba suka ji sauƙar kibbau guda biyu a lokaci guda, suka soke mutum biyu suka zube ƙasa matattu. Ɗayan da ya rage ya razana ya falfala da gudu cikin daji, yana ihu da neman taimako. Baiyi nisa ba yai arba da wata tsaleliyar budurwa tsaye a gabansa, cikin shiga ta jajayen tufafi masu ɗaukar-hankali.
Wataƙila wannan budurwa ma neman taimako take, domin kuwa ko kaɗan ba tai kama da jarumai masu yin yaƙi ba. Wannan badakare ya ruga kanta yana mai zare takobinsa gami da daka mata tsawa. "Wace ce ke?!" Inji shi. Murmushi ne kawai ya gilma ta gefen bakin wannan budurwa. Ganin haka ran wannan badakare ya ɓaci yai tsalle sama ya kai mata wawan sara a kafaɗa domin ya rabata gida biyu.
Cikin ƙwarewa da kwanciyar hankali wannan budurwa ta kauce, takobin badakaren ta sari iska. Kafun ya juyo tuni wannan budurwa ta doki tsakiyar wuyansa da tafin hannunta guda, take wannan badakare yai aman jini gami da durƙushewa bisa gwiwowinsa. Tabbas dole ne mutum ya cika da tsananin mamaki idan yaga ɗan-dukan da wannan budurwa tayi wa wannan badakare, kai kace shafarsa kawai tayi ammafa tayi masa illa ta ciki. Wannan badakare ya yi ta aman jini har sai da yayi amai mai yawan gaske, sannan ya sulale ƙasa ya fara karkarwa kafun daga bisani ya afka lahira.
Murmushi kawai gimbiya Firziyya tayi ta nufi gindin wannan doguwar bishiya. Tana zuwa gindin bishiyar ta tafa hannayenta sau biyu, yin hakan keda wuya wani dogon mutum ya diro daga saman wannan bishiya riƙe da zabgegiyar kwari da baka. Wannan mutumi ba kowa bane face KUFFURU.
Kuffuru da Firziyya suka nufi inda tsoho Saihar ke kwance, cikin tsananin jin daɗi da farin-cikin samun nasarar abinda ya kawo su birnin Askandariyya cikin sauƙi. Har a wannan lokaci tsoho Saihar a sume yake, bai ma san abinda ke faruwa.
Kuffuru na zuwa daidai kan tsoho Saihar ya miƙa hannu da nufin ya ɗauke shi domin su tafi. Ba zato ba tsammani! Da shi da gimbiya Firziyya suka ji an doki ƙirjinsu da ƙarfi. Sukai tsalle baya suka faɗo kan gadon bayansu. Cikin razana da tsananin mamaki sarki Kuffuru da gimbiya Firziyya suka ɗago kansu domin ganin wanda yayi musu wannan ɗanƴen-aiki.
Wani mutum suka gani ya bayyana. Dogo ne kuma kakkaura na kwatance. Yana da murɗaɗɗen jiki da tarin ƙwanji kamar shi yayi kanshi. Gashin kansa ruwan-toka ne mai sheƙi. Yana rataye da zabgegiyar takobi a cinƴarsa ta dama. Idanuwansa na bayar da tsoro da tsantsar kafiya irinta sarakunan farko.
Sarki Kuffuru ya miƙe tsaye ya cire alkyabbar dake jikinsa ya bayyana a cikin waɗansu irin kayan yaƙi masu ban tsoro da kwarjini irin na sarakuna. Har a wannan lokaci fuskarsa a rufe take da wannan mayafi, don haka sarki Darwazu baiyi arba da fuskarsa ba.
"Ya kai wannan ɗan-tawaye," inji sarki Darwazu. "Wane ne kai? Meyasa zaka hallaka min dakaru har guda uku, ba don ɗayansu ya kai min rahoto ba da tuni ka wargaza min shiri, ka cuce ni. Meyasa kake son sace SAIHAR AL-ASWÀD. Ka bani amsar waɗannan tambayoyi kafun na kaika kurkukuna ka sha azaba dubu a hannun Zairamu."
Sarki Kuffuru ya ƙyalƙyale da dariya mai nuna isa da kai, har yana bubbuga ƙafa a ƙasa. Daga bisani ya ce, "Daga jin muryarka kaine sarki DARWAZU na wannan birni. Nikuma baza ka san ko ni wane ne ba. Ya kai wannan sarki ina mai shawartarka da ka bani wannan dattijo na tafi, domin shi ne ya kawoni wannan birni naka. Idan kuwa ka ƙi tabbas zakayi nadama, wannan haka yake."
Sarki Darwazu ya murtuƙe fuska, zuciyarsa ta kama tafarfasa. Idanuwansa suka kaɗa sukai jawur. Yana matsayin sarki mai cikakken iko a cikin wannan birni amma har a samu wasu baƙi daga waje da zasu zo suna yi masa barazana a cikin birninsa.
"KOMAI NA DUNIYA NA MAI ƘARFI NE. GA NI GA KU GA TSOHO SAIHAR. Wanda duk yafi kowa ƙarfi a cikinmu sai ya ɗauke shi ya tafi." inji sarki Darwazu a lokacin da yake zaro zabgegiyar takobinsa.
Sarki Kuffuru ya yiwa gimbiya Firziyya magana cikin raɗa wanda su kaɗai suka ji. Yana gama faɗin hakan, ya zaro takobinsa ya dako tsalle ya dira a gaban sarki Darwazu suka fara kallon-kallo.
"Gashin kanka ruwan-toka ne meye sirrinsa kai ɗan wacce ƙabila ce?" inji sarki Kuffuru.
"Kana nufin ka ce baka san ƴan-ƙabilar Adbéncan ba?" sarki Darwazu ya amsa masa.
"Ya ya za'a yi na sansu alhalin bana rayuwa tare da su."
Sarki Darwazu yai tsalle ya kawowa Kuffuru sara a wuya, cikin kwanciyar hankali Kuffuru ya kauce. "Ƴan ƙabilar Adbéncan, su ne ƴaƴan sarki Dariyya na farko. Kowanne ɗan wannan ƙabila da gashi ruwan-toka ake haihuwarsa." inji sarki Darwazu.
Sarki Kuffuru yai tsalle shima ya kawowa Darwazu a ƙirji, cikin zafin nama Darwazu ya ja da baya. Takobin sarki Kuffuru ta sari iska. "Amma ƴan ƙabilar Adbéncan suna zuwa lahira da wuri koh?"
Sarki Darwazu ya zaro wata siririyar wuƙa ya jefi sarki Kuffuru da ita, Kuffuru yai tsalle gefe guda wuƙar ta caki wannan ƙatuwar bishiya.
"Me ka gani? Har kake tambayar ƴan ƙabilar Adbéncan suna zuwa lahira da wuri?" inji sarki Darwazu.
Haka dai sarki Kuffuru da sarki Darwazu suka ci gaba da gwabza yaƙi kuma suna hira a lokaci guda, har tsahon sa'a guda. A lokacin ne sarki Darwazu ya lura da cewa ai tuni gimbiya Firziyya ta daɗe da barin wannan wuri domin kuwa bata bayan sarki Kuffuru. Sarki Darwazu ya juya baya inda Saihar al-Aswàd ke kwance, amma sai yaga wayam Saihar baya nan. Babu shi babu alamunsa.
Nan take sarki Darwazu ya gano cewa lallai sarki Kuffuru da saninsa yayi ta jansa da hira domin ƴarsa ta samu damar sace Saihar cikin sauƙi, kuma lallai abinda ya raɗa mata kenan.
Sarki Darwazu ya taƙarƙare ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa. Ya nuna sarki Kuffuru da tsinin takobinsa ya ce, "Tabbas ka shammace ni, yaushe kuka sace wannan tsoho?"
Sarki Kuffuru yai dariya ya ce, "Wannan shi ake kira YAUDARA a filin daga. Tabbas na san cewa babu yadda za'ayi na sace tsoho Saihar a gaban idanunka, kuma ka bari. Shiyasa nayi ta janka da surutu muna yaƙi. Tabbas na san yanzu tuni tsoho Saihar ya isa inda nake so akaishi. Nima zamana a wannan birni naka ya ƙare, kayi ta bincike har ka gano ko ni waye. KAFUN NAN NA GAMA YIN ABINDA ZANYI DA TSOHO SAIHAR." Kuffuru na zuwa nan a zancensa, jikinsa ya bi iska ya ɓace ɓat!
****
RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 26: *Abun Hari Na Uku*
*
*
✍️✍️✍️ Umar Sangaru ✍️✍️✍️
*
Saura ƙiris hannayen sarki Fairaz su dira akan fuskar maigida Barban, ba zato yaji an kamo ƙafafunsa ta baya. Nan ya fara reto akan iska, a hakan ne ya samu ya juyo da fuskarsa yai arba da wanda ya kama shi. Ba wani bane illa AYMANUL FARIS. Sarki Fairaz ya cika da tsananin mamakin ƙarfin-damtsen Aymanul Faris, ya za'a yi a ce duk nauyinsa wannan jarumin zai kama shi ya riƙe a cikin iska yana reto, kamar wanda ya riƙe majaujawa?
Aymanul Faris ya ɗaga shi sama ya fyaɗa da ƙasa sannan ya take hannayensa a ƙasa, ya zauna kan ruwan-cikinsa. Ya tallafo kansa ya ce, "Ka shiga taitayinka, duk tsautsayin da yasa ka sake yunƙurin dukan maigida, hannayenka zasu bar gangar jikin ka. Ka kula!" Aymanul Faris ya tashi daga kan sarki Fairaz. Shikuma Fairaz ya miƙe zaune.


Please Login or Register in order to submit comment