Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗinne da yammaci, suna tsakar tafiya. Aymanul Faris dake zaune a gaban kwale-kwalen yana ganin hanƴa, ya soma hango hazo-hazon waɗansu gidaje a can nesa kaɗan bisa wani tsibiri.
Bambancin waɗannan gidaje da na garin Rildaz kawai shi ne, sun fi na garin Rildaz girma da tsaho da kuma fenti mai kyau. In banda wannan, zaka iya cewa su Aymanul Faris garin Rildaz kawai suka sake dawowa.
"Wannan kogi," inji Barban. "Shi ne abinda ya raba garin Rildaz da garin Sulken amma duk a waje ɗaya suke." inji Barban lokacin da wannan kwale-kwale nasu ta ƙarasa bakin gaɓar wannan kogi.
Barban ya tsayar da kwale-kwalen sannan ya fito daga cikinta Aymanul Faris ya biyo bayansa, suka nufi wannan gari na Sulken.
Garin Sulken ba wani babban gari bane, amma shima kamar yadda aka tsara garin Rildaz haka aka tsatstsara shi. Amma, mutanen wannan gari sun bambanta sosai da mutanen garin Rildaz.
A ƙofar shiga wannan gari babu ko mai gadi guda ɗaya, amma a saman ƙofar akwai alaman ƙoƙon kan mutum.
"Garin mayu kenan. Sai mun yi hankali da su." inji Barban.
Suka wuce kai tsaye izuwa cikin wannan gari, suka yi ta danna kai izuwa cikin garin ba tare da sun cewa kowa ƙala ba.
Mutanen garin ma kawai kowa harkar gabansa yake, babu wanda ya kalle su balle ya ce dasu ku ci kanku.
Inda ace waɗansu ƙananun mutane ne suka zo, da cikin hanzari waɗannan matsafa zasu dasa musu wawa. Amma, da yake su Barban gogaggu ne a harkar sihiri sai suka gagara yi musu komai.
Mutanen wannan gari babu buƙatar su kaiwa mutum hari gaba-da-gaba, su kawai ruhin mutum suke farmaka. Idan suka kama ruhin mutum tamkar sun kama shi mutumin kansa ne. Mayu kenan.
Tsahon rabin sa'a su Aymanul Faris suna ta tafiya a cikin wannan gari, ba tare da sun yiwa kowa magana ba. Har suka iso wani babban gida wanda yafi dukkanin gidajen wannan gari girma da ƙawatuwa. An yiwa gidan fenti ruwan jini, ga dukkan alamu wannan gida shi ne gidan sarkin mayu Jadukar.
A ƙofar shiga wannan gida akwai waɗansu dakaru guda huɗu, tsaitsaye riƙe da zabga-zabgan takubba. Koda suka ga su Barban sun durfafo wannan gida sai kowannensu ya ɗora hannunsa akan takobinsa ya fara shafa ta.
Aymanul Faris yana shirin zaro takobinsa kenan, Barban ya yi masa magana. "Bar su kawai, babu abinda suka isa suyi mana." Ayman ya fasa zaro wannan takobi.
Suna zuwa ƙofar shiga wannan gida, dakarun nan guda huɗu suka zaro takubbansu suka kewaye su. "Ku faɗa mana su waye ku? Ya ya akayi kuka iso wannan wuri?" Ɗaya daga cikinsu ya tambayi Barban.
Maimakon Barban ya basu amsar wannan tambaya da suka yi musu, kawai saiya ɗaga kansa ya kalle su ɗaya bayan ɗaya duk su huɗun. Nan take waɗannan dakaru suka zube a wannan wuri suka fara barci.
Barban da Aymanul Faris suka wuce kai tsaye cikin wannan gida, suna shigowa gidan suka nufi fadar sarkin mayu.
Tun daga nesa suka hango wani shirgegen ƙato zaune akan wata karaga ta mulki, ya saka nama a cikin faranti yana ci. Ko riga babu a jikin mutumin, ya tara tumbi kamar tarun wanki.
Sau ɗaya kawai ya ɗago kai ya kalli su Barban daga nan kawai ya ci gaba da cin namansa, har suka iso inda yake zaune suka zazzauna bisa wasu kujeru a gefensa.
Tamkar basu zo wannan wuri ba, ko kallonsu bai sake yi ba, har ya gama cin wannan nama, su ma kuwa basu yi masa magana ba. Naman na gama ƙarewa ya ɗauki wani ƙaton kofi cike da wani abinsha ja ya sha, yana gama sha ya juyo ya dubi Barban.
"Yau babban baƙo nake da a garina kenan?" inji sarkin mayu Jadukar. "Hodon, meke tafe da kai?"
Barban ya yi murmushi ya ce, "Zan yi mamaki idan aka ce sarkin-mayu kamar ka, bai gano waye ni ba. Sannan zanyi baƙin ciki idan ya gagara hakan saboda aikin da nazo dashi mai muhimmanci ne."
Jadukar ya yi murmushi ya kalli Aymanul Faris sannan ya sake duban Barban ya ce, "Mutanena sun aiko da saƙo tun kafin ku iso wannan fada tawa, akan cewa sun ga baƙin mutane guda biyu, waɗanda suka ɓoye kurwowinsu ba'a gani. Sannan sun ce min idan suka tunkari kurwar ɗaya mutumin ji suke kamar zasu ƙone. A yanzu da naga idanun wannan yaron, tabbas nasan cewa shi ne wanda suke magana a kai. Ko a ina ka samo mutum mai tsarkakakken jini haka?"
Aymanul Faris ya cika da tsananin mamakin yadda Barban da Jadukar suke magana tamkar dama can sun san juna. Koda yake ba komai ya sani akan Barban ba, wataƙila abokinsa ne.
"TAU'RIN ne!" inji Barban.
Jadukar ya zaro idanu cikin tsananin mamaki. "Ko zan iya sanin me kuka zo nema a wajena, kai da Tau'rin?" ya tambaya.
"Kurwar wani mutum." inji Barban.
"Kurwa kuma?" Jadukar ya yamutse fuska. "Ka san kowacce da farashinta fa, kuma bamu cika baiwa waɗanda ba ƴan-uwanmu (mayu) kurwa ba. Faɗa min kurwar wa kake so?"
Barban ya yi murmushi ya ce, "Ba wai dukkanin gangar jikin muke buƙata ba, kawai zanen yatsunsa da samfurin jininsa ya wadatar."
Jadukar ya ɗan haɗe fuska ya ce, "Eh naji, faɗa min waye ne?"
"SARKI KUFFURU na birnin Kufa." inji Barban.
Jadukar ya murtuƙe fuska tamkar tunda yazo duniya bai taɓa dariya ba. Ya dubi Barban ya ce, "Ba don da Tau'rin kazo wurina ba, da ba zan amince ba. Amma faɗa min yanzu mene ne sakamako na?"
Aymanul Faris yayi shuru a wannan wuri yana ta sauraron abinda suke ta cewa. 'Taurin' kalmar nan tana ta yawo a ransa, ya rasa gane me suke nufi.
"Idan na baka kyautar taska ta dake birnin Zallash zaka amince?" Barban ya tambaye shi.
Jadukar ya sake murtuƙe fuska ya ce, "Taska guda ɗaya kacal? Mene ne a cikin wannan taska?"
"Zinari da tagulla ne irin wanda ake samowa a tsibirin Kabrish." Barban ya ce.
"Da gaske?" inji Jadukar. "To, na amince!"
Yana gama faɗin haka ya miƙe tsaye, ya nufi cikin wani ƙaton ɗaki yana mai yafito su Aymanul Faris da hannunsa guda. Nan take suka miƙe suka bi bayansa, suna shigowa ɗakin suka iske Jadukar tsaye a gaban wata ƴar ƙaramar ƙofa, ya dafa tafin-hannunsa akan ƙofar.
Ƙaramar ƙofar ta ɗauki zanen hannunsa, ai kuwa take ta buɗe suka shige cikin ɗakin.
Babu komai a cikin wannan ɗaki face manya-manyan tebura waɗanda aka ɗaɗɗaurawa kwalabe kala daban-daban, wasu manya, wasu ƙanana. Sannan launinsu ma ya bambanta, babu irin launin da babu.
Kai tsaye Jadukar ya wuce kan wani ƙaton teburi dake can ƙarshen wannan ɗaki. Abin mamaki dukkanin kwalaben dake bisa wannan teburi jajaye ne tamkar wuta. Sannan kurwowin dake cikinsu, maimakon halitta guda ɗaya dake cikin kowacce kwalba, su a cikin su halittu guda bibbiyu ne.
"Waɗannan kwalabe da kuke gani, su ne kurwowin gawurtattun mutane masu sarrafa ifritun Aljani. Jiya-jiyan nan naga wani sabon yaro ya ƙaddamar da aljanin-haske a matsayin aljanin sa." Jadukar na zuwa nan a zancensa ya nuna musu wata kwalba wacce ke ɗauke da kurwar Marganu.
Ayman da Barban suka kalli kwalbar amma kwata-kwata basu lura da Marganu bane, Aymanul Faris ya ɗan ƙarewa siffar jarumin kallo amma daga bisani ya kawar da kai.
Ba tare da ɓata lokacin komai ba, Jadukar ya ɗakko wata zabgegiyar kwalba, wacce tafi dukkanin waɗannan kwalabe dake bisa wannan teburi ja. Ya saka hannu ya finciko kurwar dake cikin kwalbar, abin mamaki ba kurwar bane a cikin wannan kwalba face ruhin sarki Kuffuru.
Wani abun al'ajabi shi ne, ga shi dai ruhin yana hannun sarkin-mayu Jadukar amma bai isa ya yiwa ruhin komai ba. Abubuwan da yake da ikon sarrafawa kawai su ne; hannayen sarki Kuffuru da kuma gashin kansa.
"Wannan shi ne tsarin da kowanne ma'aboci ifritu yake samu, babu yadda mayu suka iya da ruhinsa. Amma, a matsayina na shugaban mayu akwai hanƴoƴin da nake bi wajen amfani ruhin nasu." inji Jadukar.
Yana gama faɗin haka, ya dafa kafaɗar wannan kurwa. Nan take wannan kurwa ta ƙara girma sosai, ta dawo tamkar girman sarki Kuffuru.
Jadukar ya yi tsafi waɗansu fararen ƙyalle guda biyu suka bayyana a hannunsa, ya shafa su a tafukan hannayen wannan kurwa ta sarki Kuffuru.
Yana gama yin hakan ya juyo ya dubi Barban ya ce, "Na gama nawa, saura ka bani mabuɗin taska. Ni kuma na baka waɗannan fararen ƙyallaye."
Barban ya yi murmushi mai nuna jin daɗi, ya saka hannu a cikin jakar tsafinsa ya ɗakko wata farar takarda mai ɗauke da zanen taswira da kuma wani makulli na zinari ya miƙawa Jadukar.
Cikin tsananin jin daɗi da fara'a Jadukar ya karɓi wannan makulli sannan ya baiwa Barban waɗannan ƙyallaye guda biyu. Nan take ya miƙawa Barban hannu suka yi musabaha kamar wasu abokan kasuwanci.
Jadukar ya janƴe hannunsa daga cikin na Barban sannan ya miƙawa Aymanul Faris. Ba tare da musun komai ba, Aymanul Faris ma ya miƙa masa. Hannayensu na haɗuwa a waje ɗaya, Aymanul Faris yaji wani abu a cikin ransa.
"Ka zage damtse babban jarumi. Tabbas nan gaba ruhinka zai iya kai wani babban matsayi wanda duk duniya babu wanda ya taɓa kaiwa. Tunda nake wannan sana'a ta maita ban taɓa ganin ruhi mai ƙarfi kamar naka ba." Jadukar yana gama faɗin haka ya juya ya fita daga wannan ɗaki, su Barban suka take masa baya.
Ba tare da ɓata wani lokaci ba, suka yi sallama da juna. Barban da Aymanul Faris suka fice daga wannan gida na sarkin-mayu. Basu tsaya a ko'ina ba, sai a bakin gaɓar wannan kogi.
Aymanul Faris yana zama a cikin wannan kwale-kwale wani irin mugun jiri ya ɗebe shi, ya zube ƙasa sumamme a cikin wannan kwale-kwale. Daga wannan lokaci baisan abinda ya sake faruwa ba.
Lokacin da ya buɗe idanunsa saiya tsinci kansa a cikin wannan fada ta aljani Ranganu. Barban na zaune akan wannan kujera dake gefen karagar aljani Ranganu.
Ranganu yana ganin ya farka ya nuna kujera ɗaya dake gefe guda ya ce shima ya zauna. Babu musu Aymanul Faris ya zauna akan wannan kujera.
Ranganu ya samar musu da abinci da abinsha mai rai da lafiya, suka cika cikin su.
Yana ganin sun sami nutsuwa ya tafa hannaƴensa sau uku, nan take wannan mutum-mutumi mai siffar jikin sarki KUffuru ya bayyana.
Ranganu ya karɓi zanen wannan fuska da Tameer ya yiwa su Barban, ya yi mata tofi da ɗalasiman tsafi masu ƙarfi. Sannan ya tashi ya nufi inda wannan mutum-mutumi yake, yana zuwa ya ɗaura wannan takarda a daidai fuskar mutum-mutumin.
Takardar na haɗuwa da jikin wannan mutum-mutumi ta narke, iyakacin zanen ne kawai ya rage. Ai kuwa, tana gama narkewa waɗannan zane-zane suka haɗe da fuskar wannan mutum-mutumi.
Nan take tsarin idanu irin na sarki Kuffuru ya bayyana, yanayin tsayuwar hancinsa ya taso, da duk wani abu da ya shafi fuskar sa.
Idan kaga fuskar wannan mutum-mutumi zaka rantse da Allah sarki Kuffuru ne tsaye a wannan wuri, saboda tsananin yadda suke kama.
Ranganu ya sake karɓar waɗannan fararen ƙyallaye guda biyu, su ma yayi tofi kamar yadda ya yiwa wannan zane. Yana gama yi musu tofin, jini ɗan kaɗan ya bayyana akan kowacce daga cikin ƙyallayen.
Ranganu na ganin haka ya ɗaura ƙyallayen akan tafukan hannayen wannan mutum-mutumi. Nan take suka zuƙe jinin dake jikin waɗannan ƙyallaye. Zanen ƴatsu da alamun jini ya bayyana a jikin hannayen wannan mutum-mutumi.
"Aikin da mukayi ya kammala. Ku je birnin Kufa, ku ɗauko takobin Saiful Shiradu, kuzo da ita wannan fada tawa. Akwai buƙatar mu sake kaiwa aljani Nara ziyara domin ya baiwa Aymanul Faris maganin tsari wanda zai kare shi daga sharrin masu sharri." Inji Ranganu.
Yana gama faɗin haka wani irin jiri ya ɗebi Aymanul Faris ya sulale ƙasa sumamme.
****
@###@@######RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 49: *Takobin mu, abin alfaharin mu*
*

*
UMAR SANGARU
*
Aymanul Faris yana buɗe idanunsa ya tsinci kansa a tsakiyar wani babban birni mai dogayen gine-gine waɗanda saboda tsananin tsahon su, har cikin gajimare suka shige. Yana waigawa bayansa ya kalli Barban tsaye da wani mutum mai rufaffiyar fuska. Aymanul Faris bai san wane ne wannan mutumi ba, amma ba shi da ikon yiwa Barban tambaya saboda yasan duk abinda Barban yake yi, yana yin sa ne akan tsari da kuma lissafi.
"Yauwa, barka da zuwa birnin Kufa," inji Barban. "Ku zo muje fadar sarki Kuffuru inda gidan ƙarƙashin ƙasa yake domin ɗauko wannan takobi." Yana gama faɗin haka ya wuce gaba, Aymanul Faris da wannan mutumi suka take masa baya.
A wannan karon basu sauya suturar dake jikinsu ba, wato basu sanƴa waɗannan baƙaƙen kaya da suka saba sakawa a duk sa'adda suka je aiki ba.
Amma, kayan da suke jikinsu irin na mutanen birnin Kufa ne, hakan ne yasa basu ja hankalin jama'a sosai ba.
Barban yana ainihin siffarsa; kyakkyawan saurayi mai dogon gashi. Aymanul Faris kuma, kyakkyawan saurayi mai baƙin gashi da murɗaɗɗen jiki. Wannan mutum mai rufaffiyar fuska kuma, bamu san ma wane ne shi ba.
Haka dai suka ci gaba da tafiya a cikin wannan birni suka tasarwa gidan sarautar Kuffuru gadan-gadan.
Tun daga nesa suka soma hango wani dogon gini wanda saboda tsananin tsahonsa har ba'a hango ƙarshen sa. "Gine-ginen sarki Kuffuru kenan, duk duniya babu mai irin su. Ko aljani bai isa ya tsallake waɗancan katangun ba, shiyasa har yau har gobe ba'a taɓa yiwa sarki Kuffuru sata ba." inji Barban.
Aymanul Faris ya riƙe baki cikin mamaki. "Abin mamaki, ko tayaya zamu iya shiga cikin wannan masarauta kuma mu kammala abin da ya kawo mu, dukda cewa sarki Kuffuru yana cikinta?"
Barban ya yi murmushi ya ce, "Sarki Kuffuru baya nan, ka manta nace maka suna can suna farauta ta."
"Ai indai da wancan taswira suke amfani, ya kamata a ce sun kalli zuwan mu wannan birni, kuma har su zo su farmake mu!" Aymanul Faaris ya ce.
"Hmm, idan zan kamu cikin sauƙi haka, da ban shafe shekaru goma ina wannan sana'a ba. TABBAS ZAN GIRGIZA SU SARKI KUFFURU." inji Barban.
Aymanul Faris ya cika da tsananin mamaki amma sai yaja baki yayi shuru bai sake cewa komai ba, har suka iso bakin ƙofar shiga wannan masarauta ta sarki Kuffuru. Inda suka yi arba da dakarun tsaro kimanin mutum dubu ɗaya da ɗoriya tsaitsaye riƙe da makaman yaƙi sunyi cirko-cirko kamar zasu ci babu.
Koda suka ga mutane guda uku. Samari guda biyu da ɗaya mai rufaffiyar fuska sai suka taso musu, cikin rashin yarda suka kewaye su.
"Kai, amma kun raina mana hankali. Haka kawai ku sako wannan fada a gaba zaku shiga, kamar ɗakin uwarku!"
"Ni tunda nake ban taɓa ganin waɗannan fuskokin a cikin birnin nan ba."
"Ni wannan mai rufaffiyar fuskar ma yafi bani tsoro, kuma duk yadda akayi baida gaskiya."
Haka dai maganganu irin waɗannan suka ɗinga tashi a tsakanin dakarun nan da suka kewaye su Barban.
Aymanul Faris na tsaye zuru-zuru yana faman zare takobinsa, kawai sai wannan mutum mai rufaffiyar fuska ya ɗan buɗe fuskarsa kaɗan, ya harari waɗannan dakaru.
Suna ganin fuskarsa jikinsu ya fara karkarwar razana, suka zube ƙasa suka kwashi gaisuwa, sannan suka buɗe musu ƙofar shiga wannan fada.
Barban, Aymanul Faris da wannan mutumi suka shige cikin masarautar, waɗannan dakaru kuma suka jawo ƙofa suka sake rufewa.
"Sarki ne fa ya dawo."
"Eh mana, amma zuwan bazata yayi, wataƙila yana so ya gano wani abu ne da ake yi a ɓoye idan baya nan..." su Barban suka ɗan jiwo gulmar da waɗannan dakaru suke yi.
Kai tsaye Barban ya nuna musu wata ɓarauniyar hanƴa, suka fara tafiya akanta. Duk badakaren da suka haɗu dashi, da zarar wannan mutumi mai rufaffiyar fuska ya nuna musu fuskarsa sai kaga an basu hanƴa.
Tsahon rabin sa'a suna ta tafiya sannan suka hango wani ɗan fili, wanda aka yiwa ado da tagulla zalla kamar kilishi.
A harabar wannan wuri akwai waɗansu gabza-gabzan dakaru guda huɗu dake gadi. Girman jikinsu da tarin ƙwanjinsu kamar na sadauki Zayyadu dake kurkukun mutuwa da aka ruguje.
Waɗannan dakaru suna ganin su Barban suka zaro kwari da bakansu, suka ɗame kibiyoyi suka saita su Barban. Amma, wannan mutum mai rufaffiyar fuska na buɗe fuskarsa duk waɗannan dakaru suka sauƙe makaman hannunsu, sannan suka zube ƙasa suka kwashi gaisuwa.
Ko kallon su mutumin baiyi ba, ya ƙarasa bakin ƙofar wannan gida na ƙarƙashin ƙasa. Ya zana waɗansu ɗalasimai a jikin ƙofar, lamarin da yasa ta buɗe kenan. Wata matattakalar bene zururu ta bayyana da tayi ƙarƙashin ƙasa.
Wannan mutumi da su Barban suka tattaka benen suka yi ƙasa a cikin wannan gida. Wani abun al'ajabi shi ne, maimakon a samu duhu a cikin wannan gida kamar yadda kowa zaiyi tsammani, amma haske ne fayau a cikin gidan, yadda ko allura ce ta faɗi mutum zai ganta.
Su Aymanul Faris basu yi nisa da fara tafiya a cikin wannan gida ba, suka iso bakin ƙofa ta farko wacce aka yi ta da farin-gilashi mai haske. A jikin wannan ƙofa akwai wani madubi ƙarami daidai tsahon fuskar mutum.
Wannan mutum-mutumi ya cire rawanin da ya rufe masa fuska ya jefar dashi, sannan ya ƙarasa daidai wannan madubi ya saita fuskarsa.
Madubin ya kawo farin haske wanda ya rarrabu gida uku. Haske na farko dake sama, ya haska idanun wannan mutum-mutumi. Tsahon daƙiƙu biyar, farin hasken dake saman ya zamo kore.
Haske na biyu dake tsakiya ya haska hancin wannan mutum-mutumi, shima tsahon daƙiƙu biyar ya zamo kore. Haske na uku ma ya haska bakin wannan mutumi da kumatunsa, tsahon daƙiƙa biyar ya zamo kore.
Wannan madubi na gama zamowa kore, wannan ƙofa ta farko ta bude a hankali. Barban da Aymanul Faris da wannan mutum-mutumi suka shige ta cikinta suka tunkari ƙofa ta biyu wacce suke hangowa daga nesa
"Ba don wannan fuska ta wannan mutum-mutumi ba, da yanzu ba wannan labarin ake ba!" inji Barban.
Wannan ƙofa ta biyu baƙa ce sidik, kamar baƙin dutse. A tsakiyarta an zana tafin hannun mutum da farin fenti mai kawo haske.
Kai tsaye wannan mutum-mutumi ya wuce bakin wannan ƙofa ya ɗora hannunsa akan wannan farin fenti. Hasken dake jikin alamar ya ƙara haske ainun, sannan ya ɗinga gaba yana dawowa baya.
"Wannan ƙofa tana gama buɗewa wannan mutum-mutumi zai narke ya bi iska. Don haka kaine wanda zai buɗe ƙofa ta uku, sannan ka shiga ka ɗakko takobin mahaifinka." Barban ya faɗawa Aymanul Faris.
Tsahon daƙiƙa talatin wannan haske yana ta kewaya hannun wannan mutum-mutumi kafun daga bisa ya zamo koren-haske. Ai kuwa yana zamowa wannan koren-haske wannan ƙofa ta rabe gida biyu hanƴa ta samu a tsakiyarta.
Faruwar hakan keda wuya wannan mutum-mutumi ya juyo ya kalli su Barban sannan ya yi musu murmushin ƙarshe. Jikinsa ya fara karkarwa daga bisani ya tarwatse ya zamo hoda, iska ta ɗauki hodar tayi awon gaba da ita.
Aymanul Faris da Barban suka ratsa ta cikin wannan ƙofa ta biyu suka wuce suka tunkari ƙofa ta uku, saura taku arba'in su iso bakin ƙofar Barban ya ja gefe ya tsaya.
"Wannan ƙofa da ƙarfin zuciya take amfani, kamar yadda na faɗa ma. Ka sa a ranka zata buɗe, ka cire kwakwanton komai a ranka." Barban ya baiwa Aymanul Faris umarni.
Aymanul Faris ya gyaɗa kai cikin fahimta sannan ya tunkari wannan ƙofa, cikin kwanciyar hankali tamkar wanda ya tunkari ƙofar shiga ɗakinsa.
Kafun ya iso wani irin farin haske mai tsananin ƙarfi ya haska ƙirjinsa, tsahon daƙiƙu arba'in kafun daga bisani wannan farin haske ya koma kore shima.
Hasken na dawowa kore wannan ƙofa ta uku, ta shige cikin ƙarƙashin ƙasa. Aymanul Faris ya ƙarasa bakin wannan ƙofa cikin kwanciyar hankali da farin cikin yau zai kalli takobin mahaifinsa, wacce ƴan ƙabilarsa suka dogara kacokan akanta.
Yana shigewa ta cikin wannan ƙofa ta uku ya tsinci kansa a tsakiyar wani ƙaton ɗaki, wanda aka gina da zallan gilashi.
Babu komai a cikin wannan ɗaki face wata zabgegiyar takobi guda ɗaya wacce aka ajiye a saman wani teburin gilashi, anyi mata kufe da koren-gilashi mai haske.
Wannan takobi tana nan kamar yadda muka santa, tana da tsaho da kauri. Sannan tana da tsananin tsini da kaifin bala'i. Idan baka santa ba, zaka yi tsammanin gama-garin takobi ce, amma ga wanda ya santa ya san cewa a cikin rantsatstsun takubban ma ita babba ce.
Aymanul Faris ya karasa inda wannan teburi yake, ya saka hannunsa ya ɗauko wannan takobi.
Hannunsa na taɓa mariƙin Saiful Shiradu, yaji wani aminci da kamala a cikin ransa. Babu buƙatar a ce masa ita ce ko ba ita bace. A cikin jininsa yake jin ta.
Aymanul Faris yana shirin ɗaura wannan takobi a gadon bayansa, wannan koren kufe nata ya tarwatse ya zube. Ya dai cika da tsananin mamaki amma baiyi wata-wata ba ya ɗaura takobin a kafaɗarsa sannan ya juya fice daga cikin ɗakin.
Tun daga nesa da Barban ya hango Aymanul Faris ɗauke da wannan takobi, sai yaji farin ciki a cikin ransa.
Duk duniya in banda Hasanul Jalwar da mutanen da suka rayu a zamanin da aka kashe mutane ɗari da hamsin ɗinnan, babu wanda ya kai Barban sanin sirrin wannan takobi ta Saiful Shiradu.
Idan ba mu manta ba dai, Barban a ido mutum zaiyi masa kallon saurayi, amma idan aka lissafa shekarunsa yafi shekara tamanin a duniya. Kawai dai sirrin rashin tsufa ne.
Aymanul Faris na ƙarasowa Barban ya tarɓe shi, yayi masa jinjina gami da taya shi murnar samun wannan babbar takobi ta kakansa na farko.
"Barkan mu da samun wannan takobi. Yanzu aikin da ya rage mana shi ne fita daga cikin wannan gidan sarauta. Ka san cewa ba ma tare da wannan mutum-mutumi amma muna tare da rantsatstsiyar takobin da hatta shi kansa sarki Kuffuru bai isa ya tunkareta, koda yana nan."
Barban na zuwa nan a zancensa ya fiddo hatimin da yake nuna alamarsa ya ajiye shi akan wani tudu, sannan ya juya suka fice shi da Aymanul Faris.
Suna fitowa daga cikin wannan gida na ƙarƙashin ƙasa suka yi arba da waɗannan dakaru guda huɗu masu irin siffar sadauki Zayyadu.
Koda waɗannan dakaru suka ga babu sarki Kuffuru a tare da su Barban, kuma suka ga takobin Saiful-Shiradu rataye a kafaɗar Aymanul Faris sai suka zare takubbansu suka kewaye su.
Barban ya yi murmushi sannan ya ɗaga hannunsa guda ɗaya, ya yiwa Aymanul Faris inkiya da yatsa guda ɗaya. Yana nuna masa alamar hari ɗaya kawai ake buƙata wajen kawar da waɗannan dakaru guda huɗu.
Aymanul Faris ya zaro wannan takobi ta Saiful-Shiradu daga cikin asalin kufenta. Nan take yanayin wannan wuri ya sauya, wani zafi mai kama da an buɗe tsohuwar rijiya ya fara fesowa. Sararin samaniya ta fara kaɗawa waɗansu jajayen gajimare masu kama da guma-guman wuta suka fara bayyana a cikinta.
Duk mahaluƙin dake cikin birnin Kufa a wannan rana saida ya razana saboda ganin bala'i na shirin afkowa cikin garin.
Idanun Aymanul Faris suka fara ci da wuta, kayan jikinsa suka ɗauki kalar wuta. Waɗansu hatimai na fuskokin aljanu guda goma suka bayyana a jikin ƙarfen wannan takobi.
Huɗu daga cikin su suka kawo haske. Nan take aljanun-wuta guda huɗu suka bayyana a bayan Aymanul Faris cikin gajimare suna kaɗa fuka-fukinsu.
Ita takobin Saiful-Shiradu ta dabam ce, da zarar

Please Login or Register in order to submit comment