Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saboda ta gama tsorata da fusatar Aymanul Faris.
Aymanul Faris ya daka mata wani irin harara wanda yasa hantar cikinta ta kaɗa, ta ji tamkar zatayi fitsari a wando. Ya matso daf da ita ya ce, "Wannan shi ne sakamakon abinda kika sa a yiwa mahaifiyata a kurkuku ko? Tabbas yanzu na gasgata maganar da masu iya magana ke cewa, BAREWA BATA GUDU, ƊANTA YAYI RARRAFE. Kamar yadda mahaifinki yake azzalumi kema haka kika kasance azzaluma, ba kya son a kashe mahaifiyata ba tare da anyi mata azaba ba, shiyasa kika ce a kaita kurkuku ko?" Koda jin wannan tambaya sai zuciyar gimbiya Jaanu ta buga da ƙarfi ta ce, "Ba haka bane, bansan cewa wannan kurkuku za'a kaita ba da ban bari ba..." Bata ƙarasa rufe bakinta Aymanul Faris ya sa hannunsa guda ya doki gefen wuyanta, ta sulale ƙasa sumammiya. Nan take ya ɗauko wata murtuƙeƙiyar igiya ya ɗaɗɗaure hannayenta ta baya, sannan ya ɗagata ya zaunar da ita kan wata kujera. Ya juyo ya dubi aljani Ranganu ya ce, "Shin ya dace na rama abinda suka yiwa mahaifiyata akan wannan ƙaramar yarinƴa?" Aljani Ranganu yayi murmushin jin daɗi da nunan jinjina ga abinda Aymanul Faris yayi ya ce, "Ba akan wannan yarinƴa zaka ɗauki fansa ba, saboda ko kaɗan bata da wani laifi. Sarki Kuffuru, sarki Ratanam da sarki Ayubul Zairiy su ne manƴan abokan gabarka. Musamman ma sarki Kuffuru domin shi ne mai gidan waɗannan sarakuna da na lissafa maka, komai kaga sun yi da umarninsa suke. Fiye da shekaru ashirin da suka shuɗe sarki Kuffuru kashe ƴaƴan Samudul Ansari yake, da zarar ya kama su. Shin kuwa dalilin da yasa sarkin yake kashe ƴaƴan Samudul Ansari?" Aymanul Faris da Jaruma Riya suka kalli junansu cikin tsananin mamaki. Mai gida Barban ya yi farat ya ce, "Ya shugabana ai babu wanda bai san amsar wannan tambaya ba, tsakanin zuri'ar sarki Kuffuru da zuri'ar Hasanul Jalwar gaba ake yi mai tsanani tun zamanin sarki Al-Khamis shiyasa sarki Kuffuru keta kashe jinin sarki Samudul Ansari domin ɗaukar fansar abinda suka yiwa kakanninsa." Aljani Ranganu yayi murmushin jin daɗin wannan amsa ta mai gida Barban. Ya dube su ɗaya bayan ɗaya ya ce, "Tun da zamanin sarki Samudul Ansari ya shuɗe ba'a taɓa samun jinin zuri'arsa da ya taso rago ko mara ƙarfi ba, a kullum jinin zuri'arsa sadaukai ne kuma jarumai na gaban kwatance. Bari na faɗa muku wani sirri, tabbas Samudul Ansaru ya mutu amma ruhinsa na nan a raye. Ruhin na ajiye a cikin wata ƙwalba da aka ajiye a kogon Madarul Ansari, wannan kogo shi ne taskar Samudul Ansari anan ya ajiye dukkanin kayan yaƙinsa da kayan sihirinsa. Duk wanda ya sami nasarar mallakar wannan ruhi na Samudul Ansari sai ya gagara anan duniya, saboda tsananin ƙarfi da iya yaƙin da zai samu a cikin ruhin. Babu mai iya mallakar wannan ruhi sai wanda ya kasance jinin Samudul Ansari, saboda haka ne yasa sarki Kuffuru yayi bincike a halwar tsafinsa domin gano yadda zai mallaki wannan ruhi dukda kasancewarsa ba jinin Samudul Ansari ba. Ya gama iya bincikensa amma bai samu wata hanƴa wacce zai iya mallakar ruhin ba, sai wata hanƴa guda ɗaya jal, itama babu tabbas. Dukda haka sarki Kuffuru ƙoƙarin jarraba hanƴar yake.
"Wannan hanƴa ba komai ba ce face ya sami ƙatuwar ƙwalba ta sihiri ha ɗinga ɗura jinin zuri'ar Samudul Ansari cikinta har sai ta cika. Tun kafin sarki Kuffuru ya zamo sarki, yake kashe ƴaƴan Samudul Ansari yana ɗura jininsu cikin wannan ƙatuwar ƙwalba amma ta ƙi cika. A halin yanzu ƙwalbar tafi rabi, kuma indai ta cika akwai yiwuwar sarki Kuffuru ya sami ƙarfin da zai iya zuwa kogon Madarul Ansari ya ɗauko ruhin sarki Samudul Ansari. Babu wanda ya san wannan sirri na sarki Kuffuru daga ni sai ku ɗinnan, saboda bai taɓa furtawa wani wannan sirri ba daga shi sai zuciyarsa. Kunsan dalilin da yasa ya yarda aka taho da mahaifiyar Aymanul Faris domin ayi musanƴa a karɓo gimbiya Jaanu?" Dukkansu suka jinjina kai alamun basu sani ba. Aljani Ranganu ya ci gaba da bayani, "Wannan jarumi da kuke kallo sunansa Marganu ɗa ne a wajen sarki Ratanam. Wannan jarumi yana matuƙar son gimbiya Jaanu so bana wasa ba, a dalilinta ne ya sadaukar da rayuwarsa yaje birnin Kufa wajen sarki Kuffuru domin yayi masa izini ya ɗauko Hajriya ya kawota nan. Sarki Kuffuru bai amince da wannan buƙata ta yarima Marganu ba sai akan yarjejeniyar zai kamo masa Aymanul Faris da jaruma Riya a raye ko a mace, ko kuma ya kamo masa Kilawud Barban a raye. Haƙiƙa wannan jarumi yayi kuskure soyayya ta rufe masa idanu, amma daga baya zaiyi dana sani da zarar ya shiga dajin Marsas zai fuskanci hakan." Lokacin da aljani Ranganu yazo nan a labarinsa sai su Aymanul Faris suka cika da tsananin mamaki, Aymanul Faris ya tabbatar da cewa lallai akwai jan aiki a gabansa. Jaruma Riya ta dubi aljani Ranganu ta ce, "Ya shugabana tashon wane lokaci wannan jarumi zai ɗauka kafun ya ƙaraso wannan daji na Marsas?" Aljani Ranganu ya ce, "Sai ya yi tafiyar kwanaki goma sha tara sannan zai isa dajin, amma inda zai fuskanci matsala shi ne, akwai muggan dazuzzuka akan hanƴar da kuma wani ƙaton gari na arnan daji dake bisa wani tsauni." Nan take ya sanar sharrukan dake cikin dajin Djinn da dajin Shiwazu da kuma tsaunin Barzasa. Koda gama jin wannan labari sai Aymanul Faris ya daɗa birkicewa ya ce, "Yanzu akwai yiwuwar wannan jarumi zai iya shallake waɗannan muggan dazuzzuka da ransa harma ya kare rayuwar mahaifiyata?" Aljani Ranganu ya ce, "Babu tabbas, sai dai mu jira muga abinda zai faru." Aymanul Faris yayi ajiyar zuciya ya ce, "Kana nufin ba zan iya zuwa na ƙarbo mahaifiyata daga hannunsa ba, kafin ya iso nan ɗin?" Aljani Ranganu ya ce, "Kwarai kuwa, ka daina ɗaga hankalinka. Marganu gawurtaccen jarumi ne kuma yasan sirrin dazuzzukan matuƙa akwai alamun zai iya giftawa ta cikinsu."
****
Tafe suke a cikin wani faffaɗan daji mai yawan dogayen duwatsu da tsaunika, shurun dajin kaɗai ya isa ya firgita mutum bare kuma mutum ya jiyo ruri da gurnanin manƴan dabbobin daji da aljanu dake rayuwa bisa tsaunikan. Amma abun mamaki waɗannan mutane guda biyu tafiya suke cikin kwanciyar hankali tamkar a cikin gidansu. Idan ka kalli wanda ke tsaye a gefen dama, zaka kalli namiji ne dogo mai ƙira ta sadaukantaka, fuskarsa na bayar da kanshin sarauta da cikakken iko. A wannan lokaci sanƴe yake cikin kayan yaƙi waɗanda aka ƙera da zunzurutun ƙarfen deman zalla, idan ka ƙarewa fuskarsa kallo zaka ga ba wani bane illa sarki Kuffuru na birnin Kufa. Idan kuwa wannan mutumi ya kasance sarki Kuffuru ne to babu tambaya na gefensa ba wata bace illa gimbiya Firziyya. Budurwa ce kyakkyawa ta gaban kwatance, ta sanƴa baƙaƙen kaya waɗanda suka ƙara fiddo hasken fatarta.
"Ya kai abbana, kana da tabbacin cewa boka Hubbazu zai yi mana cikakken bayani akan burin da ke gabanmu?" Inji gimbiya Firziyya. Ba tare da ya kalleta ba ya ce, "Ɗari bisa ɗari ma kuwa, saboda wannan boka na yarda shu'umancinsa da ƙarfin sihirinsa. Kiyi sani cewa zama a cikin wannan baƙin daji sai bokan da ya amsa sunansa domin haɗarin dake cikin wannan daji yafi gaban tunanin mutum." Yana gama rufe bakinsa suka iso bakin wani ƙaton kogon dutse wanda aka rufe ƙofarsa da wata ƙatuwar ƙofa ta baƙin ƙarfe. A jikin wannan ƙofa akwai waɗansu jajayen rubutu dake bayar da wani haske tamkar wuta na ruri a cikinsu, anyi rubutun ne da wani tsohon yare na tsafi.
Kai tsaye sarki Kuffuru yaje bakin wannan ƙofa ya soka ɗan yatsansa a cikin wannan rubutu, sannan ya fara waɗansu surutai da ƙarfi cikin wata ƙatuwar murya wacce ta ninka asalin muryarsa a kauri da amsa kuwwa. Sai da ya shafe daƙiƙu ɗari da tamanin a cikin wannan yanayi sannan wata irin iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa a cikin dajin, sararin samaniya ta fara juyawa tamkar hadari zai taso. Wata ƙara mai cika dodon kunne ta cika dajin gaba ɗaya, al'amarin da yasa gimbiya Firziyya durƙushewa bisa gwiwowinta kenan ta toshe kunnuwanta. Wannan ƙatuwar ƙofa ta wannan kogo ta fara buɗewa a hankali, a yayin da wannan ƙara ta ci gaba da ƙaruwa tamkar zata doɗe dodon kunnen mai sauraro. Amma abin mamaki har wannan ƙofa ta gama buɗewa sarki Kuffuru na nan tsaye daram ko gezau baiyi ba, ƙofar na gama buɗewa yanayin dajin ya dawo daidai. Sararin samaniya ta tsaya cak, wannan iska dake kaɗawa ta tsaya itama, wannan ƙara mai cika dodon kunne ma ta ɗauke. Sarki Kuffuru ya kamo hannun gimbiya Firziyya ya tasheta suka shige cikin wannan ƙaton kogon dutse. Suna shiga suka tsinci kansu a cikin wata makekiyar fada wadda aka ƙawata ainun da kayan more rayuwa. Gaba ɗaya fadar a haskake take da wani irin haske wanda mutum bai isa ya gane ta ina yake samuwa ba, ko'ina ka duba kuyangi ne keta kaiwa da komowa suna ta ayyuka iri-iri a cikin fadar. Ita kanta iskar da su sarki Kuffuru ke shaƙa sai suka ji tayi dabam da wadda suka baro wajen kogon, iska mai bayar da ni'ima da ƙanshi. Wannan fada dole ne a kirata da aljannar duniya, domin babu abinda mutum zai nema ya rasa a wannan fada. Sarki Kuffuru ya daɗa ƙanƙame hannun gimbiya Firziyya suka kunna kai izuwa cikin wannan ƙasaitacciyar fada, suka yi ta ratsawa ta tsakiyar kuyangin nan ba tare da sunyi musu magana ba. Yayin da suka yi tafiya mai nisa a cikin wannan fada sai suka hango karagar mulki a can ƙarshen fadar, bisa wani tudu wanda aka yiwa matattakalar bene guda hamsin da biyar.
Zaune bisa wannar karaga ta mulki wani mutum ne, fari fat. Yana da lafa-lafan kunnuwa da suka kalli sama, fuskarsa na bayar da razana da nuna isa a fannin tsafi. Gashin girarsa yana da kauri sosai, kuma fari ne sol. Yana da gemu da gashin baki wanda ya kewaye bakinsa shima duk furfura ta lullube shi. A wannan rana yayi shiga ta baƙaƙen kaya irin na manƴan bokaye, kana haɗa ido dashi zaka ji kwarjini da razana na ratsaka.
Koda wannan boka yayi arba da su sarki Kuffuru sai ya taso da kansa, yana tafiya yana dogara sanda yazo ya tarɓe su. Suka ƙarisa kan wannan karagar mulki suka zauna gaba dayansu akanta, wannan boka yayi tsafi abinci da abin sha ya bayyana akan wani teburi, sannan ya yiwa sarki Kuffuru da gimbiya Firziyya umarnin fara cin abincin. Ba tare da shakkar komai ba suka ci mai isar su sannan suka wanke hannu.
Koda wannan boka yaga sun sami nutsuwa sai ya fara yi musu bayani da cewa, "Barkanku da zuwa kogon Hubbaz, na san abinda ke tafe daku kuma na san yadda za ku iya magance matsalarku." Yana gama faɗin haka ya dubi sarki Kuffuru sannan ya ci gaba da cewa, "Ya kai wannan sarki, ba komai bane ya kawoka wannan fada tawa ba sai domin nayi maka bincike akan yadda zaka mallaki ruhin sarki Samudul Ansari da wuri, hakane?" Sarki Kuffuru ya dubi boka Hubbazu cikin tsananin mamakin yadda aka yi yasan wannan sirri nasa. Boka Hubbazu yayi murmushi ya ce, "Kada kayi mamakina, domin a halin yanzu duk faɗin duniya mutum biyu ne rak suka fini ƙarfin sihiri. Waɗannan mutane biyu ba wasu bane face, ruhin Samudul Ansari da kuma wani aljani wanda har yau ban gane wane ne shi ba. Idan kana so ka cika burinka na mallakar ruhin Samudul Ansari dole sai ka cika ƙwalbar tsafi da jinin ƴaƴan Samudul Ansari, godiya dubu, dama ka fara wannan aiki. A halin yanzu naga har kafi rabin ƙwalbar ma wato ta kusa cika, abinda nake so na sanar da kai shi ne, koda zaka tattaro dukkanin ragowar ƴaƴan Samudul Ansari da suka yi saura a duniya ka yanka su ka saka jininsu a cikin wannan ƙwalba bazata cika ba." Sarki Kuffuru ya zazzaro idanu cikin mamaki ya ce, "Kamar ya kenan? Nifa ban gane inda ka dosa ba?" Boka Hubbazu ya sake yin murmushi ya ci gaba da cewa, "Ka nutsu ka ji bayanaina mana. Ruhin Samudul Ansari yana da hankali da tunani nasa na kansa, tunda Samudul Ansari ya mutu wannan ruhi ke ajiye a cikin wata ƙwalba a kogon tsafinsa. A halin yanzu wannan ruhi ya zaɓi jarumin da zai shiga jikinsa, kuma idan aka yi kuskure wannan jarumi ya gaji wannan ruhi to tabbas sai ya mulki wannan nahiya tamu gaba ɗayanta. Bisa bayanan da suka zo mini daga aljanun dake yankin birnin Sin sun shaida min cewa, wannan jarumi yana tare da sarkin ɓarayi na duniya a cikin wani daji waishi Marsas suna ɓoye cikin wani kogon dutse da ake kira Razman. Ya kai wannan sarki wancan jarumi shi ne babbar barazanarka a yanzu domin shi ne zai hanaka mallakar ruhin Samudul Ansari. Mu dawo kan batun da na fara, wannan ƙatuwar ƙwalba ba zata taɓa cika ba face ka samo jinin wannan jarumi wanda ruhin Samudul Ansari ya zaɓa a matsayin magajinsa ka sanƴa a cikin wannan ƙwalba sannan zata cika. Idan ka cika wannan ƙwalba da zallar jinin ƴaƴan Samudul Ansari to tabbas zaka sami isasshen ƙarfi wanda zai iya ɗaukar ruhin Samudul Ansari ba tare da ka mutu ba."
Lokacin da sarki Kuffuru ya gama jin wannan jawabi na boka Hubbazu sai ya bushe da dariyar farin ciki, ya dubi bokan ya ce, "Ai indai wannan ne anyi mai sauƙi da kaina zanje har dajin Marsas, na kashe wannan jarumi na ɗebo jininsa na zuba a cikin wannan ƙwalba." Boka Hubbazu ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Idan baka manta ba, na ce maka a cikin mutum biyun da suka fini ƙarfin sihiri ɗaya daga cikinsu aljani ne wanda bansan wane ne shi ba. To a binciken da nayi na gano cewa wannan aljani yana tare da su Aymanul Faris a cikin kogon Razman. Kayi sani cewa wannan daji na Marsas mallakin mahaifin wannan aljani ne, babu yadda za'ayi kaje cikin dajin kayi nasara akansu. Dole ne ka sake bani dama ta tsahon watanni biyu domin nayi bincike na gano yadda zamu iya kashe wannan jarumi wanda ya kira kansa da suna Aymanul Faris sannan mu kama mai gidansa wato sarkin ɓarayin duniya, shin kuwa ka san cewa sarakuna tamanin da uku ne ke farautar wannan gagarumin ɓarawo?" Koda jin haka sai sarki Kuffuru da gimbiya suka cika da tsananin mamaki. Kuffuru ya dubi boka Hubbazu ya ce, "Ya kai wannan boka, wai shin wane ne wannan gagarumin ɓarawo wanda ake ta labarinsa ko'ina a duniya?" Boka Hubbazu ya ce, "Har yau har gobe babu wanda yasan taƙamamman sunan wannan ɓarawo, babu wanda ya san fuskarsa. Amma bisa binciken da tarihi ya tabbatar ana zargin cewa shima jinin Samudul Ansari ne." Sarki Kuffuru yayi ƙwafa ya ce, "Tsinannen jini kenan. Duk wata rigima a wannan nahiya mafarinta wannan tsinannen jinin ne, tabbas babu abinda ke tsakaninmu da waɗannan mutane face kisa."
*****RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 10: *Shiga Dajin Djinn (2)
*
*
Umar Sangaru
*
Sai da aljani Gulzab ya shafe tafiyar kwana goma sha biyar cir, sannan ya dira a bakin
wani gabjejen daji. Ya dira ya dubi yarima Marganu dake zaune a bayansa ya ce, "Ya
shugabana, anan zamuyi sallama, sai ka shiga cikin dajin Djinn domin kawar da fararen
aljanu masu shan jini." Yarima Marganu yayi murmushi sannan ya daka tsalle ya dira a
gefen aljani Gulzab ya juyo ya dube shi, "Ya kai abokin tafiya, ka ajiye min wannar matar
kaci gaba da kula da ita lallai ina shaida maka cewa nan da cikar sa'a goma zan fito
daga cikin wannan daji, mu ƙarasa dajin Shiwazu." Marganu na gama faɗin haka ya
falfala da gudu izuwa cikin dajin Djinn ba tare da shakkar komai ba.
Dajin Djinn ƙaton daji ne mai yawan dogayen itatuwa da manƴan kwazazzabai, bishiyu
da duwatsun dajin siffofin aljanu ne dasu. Sai dai kaga inuwar aljani a cikin kwazazzabo
tana ta iyo, ko kuma kaga inuwan aljanu nata shawaƙi amma ba zaka aljanun ba. Haƙiƙa
wannan daji ya ci sunansa Djinn, domin duk wanda ya tsinci kansa a cikin dajin dole ne
ya firgita saboda ruri da kururuwar aljanu. Yarima Marganu ya daɗa ƙanƙame takobinsa
da kyau, sannan ya kunna kai izuwa cikin dajin. Sai da yayi tafiya ta tsahon taku ɗari uku
da goma sannan ya iso wannan mararrabar hanƴa wacce sarki Kuffuru ya bashi labari,
a farkon kowacce hanƴa an kafe allo mai ɗauke da rubutu. Marganu ya ƙarasa kusa da
allo na farko na ɓangaren Arewa, ya fara karanta abinda aka rubuta akan allon, kamar
haka:
“Ya kai baƙon wannan daji, kayi sani cewa rayuwarka tana cikin masifa da bala'i wanda
bashi da iyaka, idan ka bi wannar hanya zata sada ka da farkon dajin Shiwazu, bayan ka
gwabza yaƙi da masu tsaron hanya ahalin aljani Sharuza. Muna yi maka fatan samun
nasara akan abinda ya kawo ka.”
Yarima Marganu na gama karanta wannan rubutu ya falfala da gudu ya kama wannan
hanƴa ta arewa, in banda takobinsa da yake riƙe hannu biyu babu wani makami a
jikinsa. Yana fara tafiya akan wannan hanƴa ya tsinci kansa a cikin wani siririn lungu
wanda manƴa-manƴan bishiyoyi suka saka a tsakiya, duk yadda ya ɗaga kai akan ya
hango ƙarshen bishiyoyin amma bai ga ƙarshensu ba. Marganu ya sha jinin jikinsa ya
tabbatar da cewa lallai yazo wuri mafi haɗari a cikin wannan daji. Sai da ya ɓata daƙiƙu
sittin yana tunani sannan ya ci gaba da tafiya, yana kallon gabas da yamma, kudu da
arewa yana jiran yaga ta ina waɗannan aljanu zasu fara ɓullo masa. Amma bisa mamaki
sai da ya shafe tafiyar sa'a biyu da rabi ba tare da ya yi karo da ɗaya daga cikin aljanun
nan ba, har ya iso tsakiyar.
Kwatsam! Sai ya ga ganƴen manƴa-manƴan bishiyoyin nan sun fara kaɗawa da ƙarfi,
wata iska wadda tafi guguwa ƙarfi ta dira a gefen Marganu ta kama kewaya shi tana
murza ƙasar dake gefensa lamarin da yasa ƙura mai kauri ta turnuƙe wajen gaba ɗaya.
Yarima Marganu ya daina ganin komai dake gabansa, al'amarin da ya ɗugunzuma
hankalinsa kenan. Amma sai ya sake nutsuwa ya kasa kunne yana jin kowanne irin sauti
komai ƙanƙantarsa. Kwatsam! Sai yaji tahowar naushi daga cikin guguwar nan, yarima
Marganu yayi amfani da dukkanin zafin namarsa ya daka tsalle gefe guda, wani irin
faren haske yaga ya wuce mai siffar dunƙulallen hannun bil'adama yaje ya doki ɗaya
daga cikin bishiyoyin dajin, take bishiyar tumɓuko daga cikin tare da jijiyoyinta.
Al'amarin da ya ɗugunzuma hankalin yarima Marganu kenan, ya tabbatar da cewa ya ya
gamu da gamonsa. Cikin tsananin gudu wani hannun ya sake fitowa daga cikin
guguwar nan yaje ya doki ƙirjin yarima Marganu da ƙarfi dukda cewa yayi ƙoƙarin
kaucewa. Saboda ƙarfin dukan sai da yarima Marganu ya tashi sama yaje ya maku a
jikin wata ƙatuwar bishiya, ya faɗo ƙasa a lokacin da yaji tamkar ƙasusuwan gadon
bayansa sun kakkarye gaba ɗaya. Nan fa ya gagara miƙewa zaune, koda ya yunƙura sai
yaji tamkar ƙasusuwan bayansa zasu ɓaɓɓalle.
Marganu ya ɗago kansa da ƙyar yaga wannan guguwa ta tarwatse ta bi iska, waɗansu
irin gungun fararen aljanu ya gani sun bayyana akan iska kimanin su ɗari uku da ɗoriya.
Aljanun basu da girman jiki sosai, domin ba za su fi ƙaramin zaki ba. Wani irin
zungureren baki yarima Marganu ya gani a jikin kowannensu, nan take batun sarki
Kuffuru ya faɗo masa a rai, akan kada ya kuskura ya bari wannan zungureren baki ya
huda jikinsa. Waɗannan aljanu suka buɗe fuka-fukinsu suka nufo inda yarima Marganu
ke kwance magashiyan, suka fara shawaƙi akansa tamkar shahon da ke son ɗaukar ɗan
tsako.
A daidai wannan lokaci ne yarima Marganu ya saduda ya tabbatar da cewa lallai a
wannan wuri ajalinsa zai riske shi, ya yi nadamar barowarsa gida domin cika wannan
buri. Yana cikin wannan hali ne yaga ɗaya daga cikin aljanun nan ya taho da gudu, yana
mai saita zungureren bakinsa a daidai ƙirjinsa, Marganu ya rufe ido alamun jiran
mutuwarsa. Ba zato sai yayi arba da fuskar gimbiya Jaanu, nan take wani sabon ƙarfi ya
shige shi. Saura ƙiris bakin wannan aljani ya tsire shi a ƙirji, cikin zafin nama ya mirgina
gefe guda, bakin aljanin ya huda ƙasa ya nutse a cikinta. Yarima Marganu ya ɗaga
takobinsa ya sari wuyan wannan aljani da ƙarfi, take wuyan ya tsinke jini yayi feshi,
aljanin ya bingire ƙasa matacce.
Koda sauran ƴan uwansa suka ga abinda ya faru sai suka afkowa yarima Marganu gaba
ɗayansu aka garƙame da azababben yaƙi, ya zamana cewa waɗannan aljanu suna
kawowa Marganu suka da zungureren bakinsu shi kuma yana karewa da takobinsa
gami da mayar da martani. Nan fa ihu da kururuwar waɗannan fararen aljanu ya cika
dajin gaba ɗaya, da zarar zungureren bakinsu ya haɗu da takobin yarima Marganu sai
ƙara ta tashi tamkar haɗuwar ƙarfe da ƙarfe. Tunda yarima Marganu yake bai taɓa
haɗuwa da halittu masu zafin nama da naci kamar waɗannan aljanu ba, in ba don ya
kasance mai tsananin zafin nama ba da tuni aljanun zasu yi masa farat ɗaya. Da zarar
aljani ya kawowa Marganu sai ya kaga ya goce ya kaiwa aljanin sara a wuya amma kafin
takobin ta isa wuyan sai kaga wasu sun sake ƴanƴame Marganu, nan suka hana shi
sakat. Ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya sare musu kai amma sai abu ya gagara.
Koda aka shafe sa'a ɗaya da rabi ana wannan gumurzu sai hankalin yarima Marganu ya
ɗugunzuma domin kuwa ya fara gajiya, amma waɗannan aljanu tamkar ma a sannan
zasu fara yaƙin. Ɗaya daga cikinsu wanda yafi sauran zafin nama ya kawowa yarima
Marganu suka da bakinsa, Marganu ya goce gefe guda cikin baƙin zafin nama, shi
kansa sai da yayi mamakin yadda aka yi wannan aljani bai sami nasarar huda shi ba.
Kafin ya juyo wani daga cikinsu ya sake kawo masa suka ta ɗaya gefen, nan ma ya goce
cikin zafin nama. Kafin a jima dai suka sake rikita Marganu, har wannan mai shegen
zafin naman ya samu nasarar kartar gefen cikin Marganu da zungureren bakinsa.
Yarima Marganu ya takarkare ya kwarara wani uban ihu mai tsananin firgitarwa a
lokacin da yaji wani irin mugun zogi ya shiga jikinsa, cikin tsananin jarumtaka da
dakewa yarima Marganu ya yage rigar jikinsa ya ɗaure wannan rauni na gefen cikin nasa
domin tsayar da jini. Wannan ihu da Marganu yayi ya sa waɗannan aljanu dakatawa
daga kai masa hari suka tsaitsaya a sararin samaniya suna kallonsa.
Su kansu waɗannan aljanu sun cika da tsananin mamakin jarumtakar yarima Marganu
domin shi ne mahaluƙin da suka gagara hallakawa a cikin daƙiƙu tamanin kacal, a iya
tsahon wanzuwarsu a cikin wannan daji. Yarima Marganu ya ɗaga kai ya kallesu a
lokacin da hawayen wahala ta cika masa idanu, sakamakon mugun raɗaɗin da yake ji
akan raunin nan. Marganu ya doki ƙirjinsa da hannu biyu ya kwarara uban ihu, ya
sunkuya ya ɗauki takobinsa. Ya buɗe hannayensa biyu alamun ya shirya.
Waɗannan aljanu suka cure a waje ɗaya gaba ɗayansu suka taho da gudu kamar ƙudan
zuma, yarima Marganu ya sake damƙe takobinsa da kyau. Suna zuwa daidai kansa ya yi
katantanwa da takobinsa ya fillewa biyar daga cikinsu kai, jini yayi feshi suka zubo ƙasa
matattu. Al'amarin da ya sake fusata aljanun kenan, suka sake ƴanƴame Marganu aka
sake ruguntsume da sabon gumurzu. A iya rayuwar Marganu bai taɓa shan baƙar
wahala kamar ta wannan rana ba, sai da ya zamana aljanun nan sun karci jikinsa sau
uku a lokacin da suke daf da tsire shi amma sai ya kauce su karci gefen wurin. Dukda
cewa kashe aljanun yake amma sun ƙi ƙarewa a wannan lokaci ya gaji ainun, ga mugun
zogi dake ratsa shi, ga wani irin jiri dake ɗibarsa yana neman kifewa a ƙasa.
Yarima Marganu ya tuno cewa shi fa sadauki ne kuma jarumi wanda ke neman suna, ya
tuna cewa indai baiyi nasara akan aljanun nan ba tamkar ya rasa gimbiya Jaanu ne. Ya
sake tunowa waɗannan aljanu fa su ne matakin farko na wannan tafiya tasa, ai kuwa sai
ransa ya ɓaci zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata ƙone, idanuwansa suka kaɗa
suka yi jawur. Ya kurma uban ihu, ya dake a inda yake tsaye. Waɗannan aljanu suka
sake yi masa ƙawanya, yarima Marganu ya daka tsalle sama ya fita daga tsakiyarsu,
kafin su juyo ya hau su da sara da suka. Nan

Please Login or Register in order to submit comment