Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kim Sam ya ɗan yi gajeren murmushi ya ce, "Waɗannan abubuwa a ina kake tunanin zamu same su, alhalin ko sunan wannan mutumi bamu sani ba?"
"Wannan shi ne dalilin da yasa na taho da wannan bokan, yanzu abinda nake buƙata daga gareka ka sa a ɗakko mana wannan hatimi da wannan ɓarawo ya ajiye sa'adda yayi maka wannan sata, sannan ka kaimu wajen boka Biu Lin." inji sarki Ayubu.
Kim Sam ya sake yin shuru yana tunanin yadda akayi wannan hatimi ya salwanta. "Wa ya faɗa muku har yanzu wannan hatimi yana nan? Ai sa'adda nayi ido huɗu dashi, da na kai hannuna zan ɗauke shi, sai na ga ya narke ya zama ruwa. Wannan shi ne yadda akayi wannan hatimi ya salwanta."
Sarki Ayubu ya ciji leɓe cikin tsananin takaici, ya dafa hannunsa guda akan goshinsa ya fara tunani. Tsahon ɗan lokaci kamar ba zai sake cewa komai ba, ya ce, "A jikin wannan hatimi irin rubutun wannan ƙasa taka ce, shin zaka iya tuno abinda aka rubuta?"
"Tabbas irin rubutun wannan ƙasa tawa ce, amma ba zan iya tuno abinda aka rubuta ba saboda shekarun da yawa fa, kuma a wancan lokaci a gigice nake." inji sarki Kim Sam.
"Yanzu mene ne abinyi kenan?" Ayubu ya tambaya.
A karon farko boka Ruguzan yasa bakinsa a cikin wannan tattaunawa ta su. "Mu bokaye mun san abubuwa da yawa, waɗanda ku ba ku sani ba. Me zai hana a kaimu wajen wannan babban boka, mu haɗa ƙarfi da ƙarfe dashi domin gano mafita?"
Bayan kai-komo sarki Kim Sam da sarki Ayubu suka amince da wannan magana ta boka Ruguzan. Sarkin yasa aka kawo keken doki guda biyu, ya shiga cikin guda sannan ya baiwa su Ayubu guda.
Waɗannan kekunan doki guda biyu suka nufi bayan gari, inda aka gina wani ƙaton gida a bakin kogi. Suna isowa ƙofar wannan gida, aka tsayar da kekunan dokin sannan sarki Kim Sam, Ayubu da boka Ruguzan suka fito suka tsaya a ƙofar wannan gida.
Jim kaɗan, wani dattijon mutum sanƴe da hular Fulani ya fito daga cikin wannan gida, yayi musu barka da zuwa.
Ya buɗe ƙofar wannan gida sannan ya yi musu jagora izuwa cikin gidan. A cikin wani ƙasaitaccen falo suka zauna wanda aka yiwa ado da kayayyakin bokaye.
"Kada ku wahalar da kanku a banza wajen samar da wannan taswira domin kuwa an riga da an samar da ita." inji boka Biu Lin.
Wannan magana tasa sai da ta girgiza sarki Ayubu da boka Ruguzan kuma suka tsinke da ƙarfin sihirin tsafinsa. Shi kuma sarki Kim Sam murmushi kawai yayi saboda yasan komai akan hatsabibancin wannan boka.
Boka Biu Lin bai jira suka ba shi amsa ba, ya samar da wani madubin tsafi a cikin iska mai fuska huɗu. Ba wai bayyanar madubin tsafin bane, ya baiwa su boka Ruguzan mamaki ba, a'a, abinda madubin tsafin ke nunawa shi ne ya girgiza su.
Ko shakka babu, tattaunawa ce ta musamman ke gudana tsakanin mutane guda huɗu da aljani guda ɗaya. Mutanen sun kewaye wata taswira da aka shimfiɗe akan teburi. Dukkansu sun zubawa wata sarauniya idanu wacce take ta zane-zanen ɗalasimai akan wannan taswira.
Waɗannan mutane ba wasu bane illa sarki Kuffuru, sarki Darwazu, boka Hubbazu da sarauniya Rauziyya. Aljanin dake gefen su kuma ba wani bane illa aljani Sheezuwa.
Sarauniya Rauziyya ita ce ta duƙufa akan wannan taswira tana ta gyare-gyare. Tun sa'adda aka samar da wannan taswira da ta nuna Barban yana cikin garin Jildaz, da ta ɗauke daga wannan lokaci bata sake kawowa ba.
Tsahon sa'a biyu cur, sarauniya Rauziyya tana ta aiki akan wannan taswira sannan ta samu ta kammala ta. Tana gamawa zane-zanen dake jikin wannan taswira suka ɗauke gaba ɗaya, kafun daga bisani suka sake bayyana amma dara-dara.
Maimakon wannan taswira ta farko dake ɗauke da koren-haske guda ɗaya na Barban, wannan taswira korayen-hasken guda biyu ne a jikinta. Ɗaya a tsakiyar teku, ɗayan kuma a tsakiyar wata wuta.
"Me hakan yake nufi? Barban guda biyu ne kenan?" sarki Kuffuru ya tambaya.
Sai dai babu wanda ya isa ya amsa wannan tambaya, saboda babu wanda ya sani. Ana cikin wannan wasu-wasi ne koren-hasken dake tsakiyar wannan teku ya ɓace.
"R. Ziyya. Mene ne ma'anar hakan? Mutum biyu ne kenan?" Aljani Sheezuwa ya tambaye ta.
Sarauniya Rauziyya ta cika da tsananin mamakin wannan abu, amma ita kanta bata san me hakan yake nufi ba, sannan bata san wanne bayani zata yiwa waɗannan mutane ba.
"Mutum ɗaya ne, kawai dai taswirar ce sai yanzu ta gama saituwa." ta faɗa musu haka.
Tana gama faɗin haka ta saka yatsunta guda biyu ta fara ƙara girman wannan taswira, sannu-a-hankali garin Jiminis ya bayyana. Abin mamaki a wannan gari yaƙi aka gama fafatawa, kuma har an ƙone garin, a tsakiyar garin zaune bisa wata karaga suka kalli Barban. Lokacin da wannan taswira ta gama ƙure girmanta.
Wannan Barban ɗin da suka kalla saurayi ne, mai yawan dogon gashi.
"Ga nan Hodon, ku zo muyi gaggawar zuwa mu kamo shi, ko a ina wannan gari na Jiminis yake?" inji sarki Kuffuru.
Sarauniya Rauziyya ta yi murmushi ta ce, "Yankin ƙasashen Jerawa ne."
***
@#@#@#@#@#@@
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment