Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da addinin da kowa ke yi.
Da shigarsu cikin birnin sai Aymanul Faris ya dubi Barban ya ce, "Maigida? Ya ya akayi ka san amsar waɗannan tambayoyi akan addinin Dayyarish? Wannan tsoho da na kalli kana kuka sakamakon jin muryarsa, waye shi?"
Maigida Barban ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Amsar waɗannan tambayoyi aljani Ranganu ne yake faɗa min su, batare da kowa ya gan shi ba. Wannan tsoho da kake kallo ba wani bane illa mahaifina. Abinda yasa kaga ina kuka shi ne, dubi halin da ya shiga. Ba shi da komai kuma ba shi da kowa, ya dawo mabaracin kan titi. A da ya wulaƙanta mu ni da mahaifiyata ga shi yanzu na sami ɗaukaka a lokacin da shi kuma duniya ta guje shi. Tabbas wannan rayuwa ta duniya a cike take da darasi, amma sai mai hankali ke ganewa. MAHAIFINA, MAHAIFINA ne ko me zaiyi min bazan guje shi ba, tabbas da zarar mun sami nasarar wannan aiki zansa aljanuna su ɗauke shi su kaishi birnin Istanbul, na bashi kuɗi mai yawa da kuma gina masa gida, don ya ƙarar da rayuwarsa cikin jin daɗi." Maigida Barban na zuwa nan a zancensa hawaye ya zubo masa amma yayi maza ya share hawayen.
Ya saka hannunsa a cikin aljihun rigarsa ya fiddo taswirar birnin Askandariyya ya nunawa Aymanul Faris dai-dai inda suke tsaye. "Daga wannan wuri zuwa masarautar Darwazu tafiya ce ta sa'a ɗaya kacal. Yanzu haka jama'a nata shiga cikin gidan sarautar suna zuwa gaban wannan gunki suna sujjada. Don haka yi maza kazo mu tafi don mu saje da mutanen." Inji maigida Barban.
Ba tare da ɓata lokaci ba shi da Aymanul Faris suka kama hanƴa suka nufi gidan sarautar birnin, wacce suka hangowa daga can nesa. Suna daɗa tunkarar ginin gidan sarautar dakaru da jama'a na ƙaruwa, kai da gani ka san akwai abinda ke faruwa a can. Sannu-a-hankali dai har suka fara hango ƙofar shiga gida sarautar wacce aka ƙera da zallar ƙarfen deman mai sheƙi. Dakaru kimanin guda hamsin na tsaitsaye a bakin ƙofar don tabbatar da tsaro. Babu wanda ake cajewa a wannan wuri saboda yawan jama'a amma da buƙatar a tabbatar babu makami a jikin mutum.
Tun daga nesa waɗannan dakaru suka ƙurawa maigida Barban da Aymanul Faris idanu, kai da ganin kallon da ake yi musu kasan ba'a yarda dasu ba. Duk da taurin zuciya da rashin tsoro irin na Aymanul Faris sai da ƙirjinsa ya buga da ƙarfi saboda ganin yadda dakaru suke ta kai-kawo a wannan wuri, ya tabbatar da cewa ko yaya asirinsu ya tonu to akwai matsala.
Lokacin da suka iso bakin ƙofar shiga cikin gidan sarautar, sai shugaban dakarun dake tsaro a wurin ya sha gabansu ya tare musu hanƴa. Cikin kallon rashin yarda ya dubi Barban ya ce, "Shehu? Ya ya akayi muka ganka kai ɗaya alhalin ance shaihunai basa rabuwa? Me kuka zo yi a gidan sarautar sarki, ko kaima zakaje ka yiwa gunki Sairamas sujjada ne, maigirma Haiƙàn ya ƙoneka?" Koda Barban yaji waɗannan tambayoyi sai gabansa ya faɗi ya tabbatar da cewa lallai sunyi kuskure domin kuwa amfanin kayan dake jikinsu ya ƙare tun shigowarsu cikin birnin. Barban ya gagara baiwa wannan badakare amsar tambayoyin da yayi masa.
Badakaren ya ƙyalƙyale da dariya ya ce, "Ban yarda daku ba, saboda haka zan sa a caje min ku. Bayan an cajeku sai ku hanzarta barin ƙofar gidan sarautar nan kafun fushina ya tabbata a kanku." Yana gama faɗin haka ya ce, "A caje su." Nan take waɗansu dakaru guda biyu suka fara caje Aymanul Faris wanda ke tsaye a gaba, aka gama caje shi babu komai a jikinsa face waɗannan tulin littatafa. Aka dawo kan Barban aka fara caje shi, badakaren na sa hannunsa a cikin aljihun rigar Barban yaji alamun takarda don haka sai ya fiddota, ya warware. Take yayi arba da taswirar birnin Askandariyya. Cikin hanzari ya nunawa shugabansu, shugaban nasu na gani ya ce a kama su Barban, lallai duk yadda aka yi ɓarayi ne ko kuma ƴan leƙen asiri.
A karon farko a tarihin satar ɓarawo Barban tsoro ya bayyana ƙarara a fuskarsa ya tabbatar da cewa lallai idan ya bari aka kamasu asirinsa sai ya tonu a duniya, an gano ko shi waye. Yana shirin shafar damtsen hannunsa domin waɗannan aljanu guda uku su bayyana, ashe akwai wani badakare tsaye a bayansa yana ganin abinda ke faruwa. Cikin hanzari ya sa ƙotar takobinsa ya doki Barban a gefen wuya da ƙarfi, ai kuwa take Barban ya sulale ƙasa sumamme.
Lokacin da Barban ya farfaɗo sai ya tsinci kansa a tsakiyar yanki na farko na gidan sarautar Darwazu a gaban gunki Sairamas, Aymanul Faris na zaune a gefensa lafiyarsa ƙalau babu abinda ya same shi. Al'amarin da yayi matuƙar baiwa Barban mamaki kenan, ya tambayi kansa a cikin ransa. "Shin ina waɗannan dakaru dake shirin kama mu sukai? Aymanul Faris ne kenan ya ceci rayuwata? Shin asirinmu ya tonu ko kuwa har yanzu muna kan shiri?" Amsoshin da ya gagara baiwa kansa kenan.
"Har yanzu shirinmu na tafiya dai-dai. Zo muyi maza mu shige cikin yanki na biyu," inji Aymanul Faris. "Kada ka ce zaka tambayeni akan yadda akayi muka kuɓuta domin labari ne mai tsaho, ka bari sai mun koma gida." Aymanul Faris na gama faɗin haka ya miƙe tsaye da nufin ci gaba da tafiya. Maigida Barban ya miƙe shima suka nufi yanki na biyu inda doguwar husumiya take. Har a wannan lokaci malun-malun ce a jikin Barban, wato dai basu sauya tufafi ba.
"Da zarar mun shiga yanki na biyu..." Inji Barban. "Waɗannan baƙaƙen kaya zasu bayyana a jikinka, kuma daga sannan ne za'a farga damu." Aymanul Faris ya juyo ya ce, "Ina takobina take?" Barban ya ce, "Tana jikin waɗannan kayan mana, suna bayyana zaka ganta." Yana rufe bakinsa suka shigo cikin wani wuri mai yawan jar-ƙasa, wanda takata kaɗan zai haifar da ƙura. Tun daga nesa suka fara hango waɗansu girɗa-girɗan dakaru waɗanda suka fi dakarun dake tsaron kurkukun mutuwa girma da kauri, suna ta kai-kawo a wannan wuri. A bayan waɗannan dakaru akwai wata doguwar gini wato husumiya.
Wannan husumiya da zallar dutsen Heshèir aka ginata - dutsen Heshèir wani irin dutse ne mai taurin gaske a wannan zamani wanda ake samowa a tsakiyar wata teku. Tana da tsahon kamu ɗari biyu da ɗoriya, babu ko alamun ƙofar shiga a jikin wannan husumiya. Tana da launin kore mai ɗaukar idanu kai kace koriyar wuta ce abar ruruwa.
"Ƙofar shiga wannan husumiya," inji Barban. "Tana can sama ne ta ɓangaren arewa. Babu yadda za'ayi muje wannan wuri ba tare da mun kawar da waɗannan dakaru dake tsaron wannan wuri ba. Daga wannan lokaci amfaninka a wannan tafiya zai fara, ka kashe waɗannan dakaru, ka kare rayuwarka da tawa. Yanzu kayan dake jikinka zasu bayyana ka tabbatar da cewa ka ƙarar da waɗannan dakaru gaba ɗayansu domin na samu damar da zan gano mana ainihin inda wannan ƙofa take." Barban na gama faɗin haka ya doki ƙasa da sahunsa guda, lamarin da yasa ƙura mai yawan gaske ta turnuƙe wajen kenan. Babu abinda mutum zai kalla idan ba wannan ƙura ba, al'amarin da ya jawo hankalin dakarun dake tsaron wurin kenan suka rugo da gudu suka kewaye ƙurar, a yayin da ta fara lafawa.
Wani saurayi suka gani ya bayyana ya a cikin ƙurar sanƴe da baƙaƙen tufafi, ba'a kallon komai a jikinsa face idanuwansa kaɗai. Wataƙila wannan saurayi ba daga cikin wannan ƙura ya bayyana ba, domin kuwa ko ɗison ƙura babu a jikinsa. Baƙaken kayan dake jikinsa har sheƙi suke.
Ko cacar baki basu yi ba, wannan saurayi ya zaro zabgegiyar takobin dake ɗaure a gadon bayansa, ya ja layi a tsakiyar waɗannan dakaru. Su kansu waɗannan dakaru saboda ganin shigar da wannan saurayi yayi suka tabbatarwa da kansu cewa lallai ɓarawo ne. Don haka zare makaman yaƙinsu kawai suka yi suka afka masa, aka garƙame da azababben yaƙi. Ba kowa bane wannan saurayi illa AYMANUL FARIS.
Aymanul Faris ya ɗaga zabgegiyar takobinsa sama, ya yi kururuwa ya afkawa waɗannan dakaru da sara da suka cikin bakin zafin nama, juriya da bajinta. Duk girman waɗannan dakaru da yawansu sai ya zamo na banza. Aymanul Faris yayi ta ratsawa ta tsakiyarsu yana saransu da sukarsu an rasa mutum ɗaya da zai samu nasarar koda lakutar jikinsa. Koda waɗannan dakaru suka fuskanci baza suyi nasara akan Aymanul Faris ta wannan salo ba, sai suka sauya salon yaƙin. Rabi daga cikinsu suka tsaya a bayan Aymanul Faris, rabi kuma suka tsaya a gabansa. Nan take suka afka masa gaba ɗayansu da sara da suka ta gaba da ta baya.
A wannan lokaci ne fa hankalin Aymanul Faris ya rabu gida biyu domin ta ko'ina sara da suka ne ke zuwa. Sai dai kaga waɗannan dakaru sun falfalo da gudu ta gaba da ta baya suna kawo masa farmaki. Aymanul Faris ya fara tsalle-tsalle kamar tsuntsu yana tsallake su, kuma a saman ya ɗinga fille musu kai. Kafun a jima jini ya fara tsartuwa yana malala a ƙas... Dakaru na ta zubewa ƙasa matattu. Koda waɗannan dakaru suka sake fuskantar wannan salo ma bashi da wani amfani don sun kasa riskar Aymanul Faris sai suka sake sauya salon yaƙin.
Ƙafafuwansu suka ɗinga bugawa a cikin jar-ƙasar dake wurin lamarin da yasa ƙura ta fara tashi kenan, tana hana gani sosai. To, su waɗannan dakaru sun saba da irin wannan jar-ƙasa shikuma Aymanul Faris wannan shi ne ganinta na farko a rayuwarsa. Nan fa ya fara ganin waɗannan dakaru dishi-dishi da yake dama kalar suturar dake jikinsu irin wannan jar-ƙasa ce.
Aymanul Faris ya riƙe takobinsa da hannu biyu gyam, ya tsaya yana nazarin kowanne irin motsi. Waɗannan dakaru basu yi wani yunƙuri na kai masa hari ba, sai da suka bari jar-ƙasar ta gama gauraye wurin gaba ɗaya, ta yadda baka iya ganin dakarun kansu albarkacin kalar kayan dake jikinsu. Mutum goma daga cikinsu suka daka wawan tsalle sama, suna saita kan Aymanul Faris da takubban hannunsu don su tsarge shi gida biyu. Wasu mutum goma suka kawo masa hari ta ƙasa don su giddidiba shi. Waɗansu mutum goma suka sake jeho masa masu don su tsire shi a ƙirji. Duk waɗannan hare-hare Aymanul Faris bai san da su ba, balle yayi ƙoƙarin kaucewa.
Amma shi kansa ya tabbatar da cewa lallai mugun abu na tunkaro shi, don haka tsalle yai ya bar wurin. Dakaru goman nan suka sari iska, waɗanda suka taho ta sama suka sari ƴan uwansu a kafaɗa. Kafun su ankara su ma masu guda goma sun nutse a cikin jikinsu, nan take dakaru guda ashirin suka afka lahira. Sauran ƴan uwansu basu san abinda ke faruwa ba, shi kansa Aymanul Faris bai san mutum ashirin sun mutu a ƙoƙarin kashe shi ba.
Yana tsaye cikin wasu-wasi yaji mashi yazo ya caki rigar dake jikinsa dai-dai ƙirjinsa amma bisa mamaki rigar bata huje ba, mashin ne ma ya ɓalle gida biyu ya faɗi ƙasa. Aymanul Faris ya cika da tsananin mamaki, kafun kace me masu guda arba'in sun dira a jikinsa amma wannan riga ta hanasu huda shi.
Koda waɗannan dakaru suka ga makaman yaƙinsu basa aiki akan Aymanul Faris sai suka zaro waɗansu irin manƴa-manƴan kulake na baƙin ƙarfe suka kewaye shi, a lokacin ne wannan ƙura ta gama lafawa. Koda suka ga yadda ƴan uwansu har mutum ashirin suka mutu, sai suka fusata suka afkawa Aymanul Faris da duka kamar zasu cinƴe shi.
Aymanul Faris ya fusata ya mayar da takobinsa cikin kufe, ya zaro wasu gajerun adduna guda biyu ya fara kaiwa waɗannan dakaru sara dasu. Su kuma suka wanzu suna kawo masa duka da kulaken dake hannunsu. Nan fa suka sake buɗe sabon shafin gumurzu, Aymanul Faris ya gagara samun nasarar kashe su, su kuma sun gagara samun kawar da shi har tsahon sa'a ɗaya.
Kwatsam! Aymanul Faris baiyi zato ba, yaji an rarume shi ta baya an ɗaga shi sama an danfara da ƙasa. Wanda ya doka shi da ƙasan ya hau kan ruwan cikinsa sannan yasa ƙafafunsa guda biyu ya take hannayen Aymanul Faris. Ashe shugaban waɗannan dakaru ne ya fusata ya yiwa Aymanul Faris ɗiban amarya.
Cikin baƙin zafin nama badakaren ya ɗaga kulkinsa ya gabzawa Aymanul Faris duka a gefen fuskarsa, saboda ƙarfin dukan sai da fuskar Aymanul Faris ta kalli gefe jini yayi feshi da cikin bakinsa. Badakaren ya sake ɗaga kulkinsa ya doki fuskar Aymanul Faris ta ɗaya gefen, lamarin da yasa jini ya fara zubowa kenan daga bakin Aymanul Faris. Badakaren ya bushe da dariya ya sake ɗaga kulkinsa da nufin ya rotsawa Aymanul Faris a tsakar kai, yadda yana rotsa masa kansa zai fashe ƙwaƙwalwa tayi fata-fata.
Ba zato! Aymanul Faris ya riƙe kulkin sannan ya ƙwace shi, ya rotsawa badakaren duka a wuya iyakacin ƙarfinsa. Take wuyan badakaren ya karye ya taho ƙasa luu... zai faɗon kan Aymanul Faris.
Aymanul Faris ya hankaɗe shi ya faɗi gefe guda sannan ya miƙe tsaye, yana tofar jinin dake zuba daga cikin bakinsa. Cikin baƙin rai da fusata Aymanul Faris ya afkawa waɗannan dakaru da duka. Sai dai kaga ya doki wuyan badakare da wannan kulki take ya faɗi ƙasa matacce. To, da yake Aymanul Faris ya riga ya kashe shugaban waɗannan dakaru sai jikinsu yayi sanƴi yayi ta dukansu a wuya ko a ka, suna ta faɗuwa ƙasa matattu. Kafun sa'a biyu da rabi ta cika tuni ya bazar dasu gaba ɗaya a wurin wasu sun mace, wasu kuma sun suma. Yana gama kashe dakarun maigida Barban ya bayyana.
"Na gano ƙofar shiga wannan husumiya, kamar yadda nayi hasashe ta sama take kuma ta ɓangaren Arewa. Biyoni da gudu muje mu shige cikin wannan husumiya domin ɗaukar farar lu'u-lu'u." Inji maigida Barban. Ya ruga da gudu.
Aymanul Faris ya bishi a baya da gudu sanƴe da waɗannan baƙaken kaya waɗanda har a wannan lokaci sheƙi suke, tamkar ba da su ya fafata ba.
****RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 19: *AHALIN RAÚ'AN*

*
✍️✍️✍️ UMAR SANGARU ✍️✍️✍️
*
Gudu suka yi na tsahon daƙiƙa ɗari biyu kacal suka iso bakin wata doguwar matattakala wacce tayi sama izuwa saman rufin wani dogon ɗaki, saboda tsahon wannan matattakala mutum ba zai iya hango ƙarshenta ba. Ba tare da shakkun komai Barban ya fara hawa kan wannan matattakala Aymanul Faris ya take masa baya da gudu.
Sai da suka yi kusan rabin sa'a suna gudu kuma suna hawa kan wannan matattakala sannan suka iso ƙarshenta, inda suka tsinci kansu a saman wata baranda. Daga can ƙarshen barandar kuma jikin wannan husumiya wanda tayi sama, da alamu dai ko rabinta bai kai ba. Amma a jikin bangon husumiyar akwai ƴar ƙaramar ƙofa, rufaffiya. A jikin ƙofar akwai rubuce-rubuce cikin yaren tsafi mai wahalar karantawa.
"Duk duniya ni ne kaɗai wanda zai iya karanta waɗancan rubutun idan ka cire sarki Darwazu." Inji maigida Barban. "Da zarar mun shiga cikin wannan husumiya zamu yi arba da aljanu ahalin RAÚ'AN, kamar yadda na faɗa maka indai muna so mu sami nasara to tabbas sai mun kashe su gaba ɗaya, su bakwai ne. Idan muka kashe su zamu wanke akwatin sihiri da jininsu, in dai mukayi haka mun kuɓuta daga sharrin wannan akwati."
Yana gama faɗin haka ya nufi inda wannan ƴar ƙaramar ƙofa take, Aymanul Faris dai tsayawa kawai yayi yana kallon abinda maigida Barban zaiyi.
Barban na zuwa daidai bakin ƙofar ya fiddo wani ƙyalle mai ɗauke da hatimin aljani Ranganu ya nuna wannan rubutu dashi, wani baƙin haske ya fita daga cikin hatimin ya doki waɗannan rubutu dake jikin ƙofar. Hasken na dukarsu suka fito dara-dara, maigida Barban ya fara karanta su da ƙarfi cikin wani irin yare wanda komai sauraronka ba zaka fahimci kalma guda ɗaya ba.
Tsahon rabin sa'a ya ɗauka yana wannan surutai sannan ƴar ƙaramar ƙofar ta buɗe a hankali. Maigida Barban ya yafito Aymanul Faris yana masa nuni da yazo ya shiga, ba tare da tsoro ko shakkun komai ba Aymanul Faris ya rugo da gudu yazo bakin ƙofar, ya sa kansa ya leƙa izuwa can ƙasa. Babu abinda ya kalla idan ba duhu ba saboda tsananin nisan dake tsakanin wurin da kuma ƙasan husumiyar, juyowa ya yi ya kalli Barban ya ce, "Yanzu tayaya zamu shiga wannan wuri?"
Maigida Barban ya yi murmushi ya saka hannunsa acikin jakar tsafinsa ya fiddo wata murtuƙeƙiyar igiya doguwa, ya miƙowa Aymanul Faris. "Babban jarumi, kai zaka fara shiga cikin wannan husumiya," inji Barban. "Da zarar ka kawar da waɗannan halittu ahalin RAÚ'AN, zan shigo domin satar wannan lu'u-lu'u. Hikimata anan ita ce, idan muka shiga mu biyu, hankalinka zai iya rabuwa gida biyu - kana so ka kare kanka, nima kuma ka kareni. Kaga kenan baza ka zage ka yaƙi ahalin RAÚ'AN yadda ya kamata ba. Don haka zo ka shige ciki, domin fafatawa dasu."
Barban na gama faɗin haka ya ɗaure igiyar nan a jikin wani turken itace, sannan ya zira igiyar a hankali izuwa cikin wannan husumiya. Aymanul Faris ya gyara ɗaure makaman yaƙinsa, yazo ya kama wannar igiya ya shige ta cikin ƴar ƙaramar ƙofar nan, ya daka tsalle ya afko ƙasan husumiyar.
Tafiyar rabin sa'a cur yayi akan wannan igiya sannan ya dira a tsakiyar wannan husumiya. A nan yayi arba da wata farar akwati mai haske da sheƙi a ajiye bisa wani tudu.
Waɗansu irin halittu guda bakwai ya gani sun bayyana tsulum, sun kewaye shi. Kamar yadda Barban ya faɗa haka abin yake, rabin jikin halittun na zaki ne, rabi kuma na mutum. Jikin mutum ɗin ya kasance murɗaɗɗe sosai, ga tarin ƙwanji da jijiyoyi kamar me. Dukkaninsu suna riƙe da zabga-zabgan takubba masu tsananin kaifi, tsini da kuma nauyi.
Aymanul Faris ya zaro waɗannan gajerun adduna guda biyu gami da gyara tsayuwa a tsakiyar waɗannan aljanu. Nan fa aka fara kallon kallo tsakaninsu da Aymanul Faris shi bai afka musu, su ma basu afka masa ba har tsahon daƙiƙa ɗari da tamanin.
"Aka ce ku ne ahalin RAÚ'AN? Shin waye ne wannan RAÚ'AN ɗin?" Inji Aymanul Faris fuska a murtuƙe.
Maimakon waɗannan aljanu su bashi amsar tambayar da yayi musu sai yaga sun ja gaba ɗayansu, irin yadda zaki keyi idan zai daka tsalle. Dukkaninsu sai lashe baki suke kai da gani ka san tsohuwar maita ce ta motsa.
Ƙaramin cikinsu ya dako wawan tsalle sama, yana mai ware hannayensa gami da kawo wangama da bakinsa da nufin ya turmushe Aymanul Faris kuma ya cinye shi. Koda Aymanul Faris ya fuskanci haka sai ya tale sawayensa yayi ƙasa kamar yadda jaruma Riya ta koya masa. Saura ƙiris aljanin ya diro kan Aymanul Faris take yasa addunansa guda biyu ya sari tumbin aljanin da ƙarfi.
Ai kuwa tumbin ya farke kayan aljanin suka zubo ƙasa, ya faɗi gefe guda matacce. Jini yayi feshi ya ɓata Aymanul Faris da kayan jikinsa.
Tsahon daƙiƙa ɗari biyu da arba'in wannan ɗaki ya ɗauka cikin shuru, kai kace babu mai rai a cikinsa. Su dai waɗanna aljanu guda shida da suka rage ƙamewa suka yi a tsaye tamkar gumaka cikin tsananin mamaki, shima Aymanul Faris mamakin yadda akayi ya hallaka ɗaya daga cikinsu cikin sauƙi haka yake.
Tun da aljani RAÚ'AN yayi zamani ya shuɗe, kimanin shekaru ɗari da arba'in baya. Ya bar ƴaƴa guda dubu talatin da uku a duniya, tun daga wannan lokaci kawo i yanzu ko zazzaɓi ɗayansu bai taɓa yi ba. Saboda tsananin cikar lafiyarsu da kamalarsu. Amma ace yau an kashe ɗaya daga cikinsu a karon banza, ai da akwai magana.
"Kafin mu kasheka mu sha jininka, ina so naji tarihinka da tarihin waɗannan adduna dake hannunka?" Inji ɗaya daga cikin aljanun.
Aymanul Faris ya yi murmushi ya ce, "Tarihina? Duk wanda ya san tarihina a ƙiyama yake kwana. Shin kana buƙatar ji, ka tafi lahira?"
Koda waɗannan aljanu suka ji kalaman izgilanci daga bakin Aymanul Faris sai ransu ya ɓaci, suka fusata. Suka ɗaga murya cikin haɗin baki suka kira wani ɗalasimin tsafi. Take takubbansu suka fara haske suna sheƙi, kafin daga bisani suka fara fitar da hayaƙi tamkar an kunnawa ɗanƴen itace wuta. Waɗannan aljanu guda shida suka sake kewaye Aymanul Faris suna lashe baki.
Aymanul Faris na shaƙar wannan hayaƙi tari ya rufe shi, tamkar zai amayar da kayan cikinsa. Hawayen wuya ya fara zubowa daga cikin idanunsa, suka kaɗa yi jawur.
Ɗaya daga cikin aljanun ya sake dako wawan tsalle yana mai kawowa Aymanul Faris hadiya da bakinsa. Aymanul Faris ya daka wawan tsalle gefe guda wannan zaki ya dira a ƙasa, kafun Aymanul Faris ya sake ankarewa guda biyu sun sake dako tsalle, ɗaya ya kawo masa haɗiya, ɗayan kuma ya kawo masa bangaza da ƙirjinsa.
Aymanul Faris damar kaucewa hari ɗaya kawai yake da a cikin waɗannan guda biyu. Yaga idan ya bari aka haɗiye kansa mutuwa zaiyi, don haka sai ya kaucewa aljanin da ya kawo haɗiyar, ya fuskanci wanda ya kawo bangaza. Ƙirjin wannan zaki na haɗuwa da jikin Aymanul Faris, aka yi jifa dashi tamkar anyi jifa da hoge, haka Aymanul Faris yaje ya haɗu da bangon wannan husumiya. Ya faɗo ƙasa a galabaice, bakinsa da hancinsa ya fashe.
Daƙyar Aymanul Faris ya miƙe tsaye a lokacin da waɗannan aljanu guda shida suka kewaye shi, kowannensu na ɗaga takobinsa sama. Ko tambaya babu ka san afka masa zasuyi da gaske.
Koda Aymanul Faris ya fuskanci haka sai ya shima ya gyara riƙe takobinsa, yana ganinsu dishi-dishi. Waɗannan aljanu kururuwa suka sake yi a tare suka afkawa Aymanul Faris aka garƙame da masifaffen yaƙi.
Aymanul Faris ya wanzu a tsakiyar su yana mai kare hare-harensu amma ko sau ɗaya bai samu damar mayar da martani ba, saboda tsananin zafin naman aljanun, juriyar su gami da iya yaƙinsu. Ko daƙika ɗari uku masu kyau ba'a shafe ba Aymanul Faris ya san cewa lallai ya gamu da gamonsa, abu ne mawuyaci ya kuɓuta daga sharrin waɗannan aljanu.
Abinda Aymanul Faris ya fara tunowa na farko shi ne mahaifiyarsa, shin wanne hali zata tsinci kanta idan taji labarin ya mutu a lokacin kyautatawa mutumin da ya taimaka sosai aka ƙwato ta daga hannun azzalumai su Kuffuru. Shin maigida Barban zaiyi alfahari dashi idan ya bari wannan shiri wanda Barban yafi shekaru goma yana yi ya tafi a banza? Tabbas mutuwarsa a wannan wuri tana nufin cewa ya rasa gimbiya Jaanu har abada.


Please Login or Register in order to submit comment