Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce, "Ya kai wannan aljani wane ne kai?!"
Djinn ya fusata ya yiwa wannan sarki duka tsakiyar kai, take naman wannan sarki ya rududduge yayi fata-fata tamkar an daka a turmi. Koda ganin haka sai jama'a suka daɗa ruɗewa suka ci gaba da karkarwa.
"Daga yau ga sarkinku!" inji Djinn ya nuna Kuffuru. "Duk wanda ya yi masa biyayya ya tsira, wanda duk ya bijirewa umarninsa ya hallaka kamar yadda na hallaka wannan sarki naku haka shima zan hallaka shi."
Daga wannan rana Kuffuru ya zamo sarkin birnin Kufa kuma daga wannan rana suka ƙulla yarjejeniya da aljani Buƙalshiyu Djinn akan cewa zai taimaka masa ya mallaki ruhin Samudul Ansari, shi kuma zai kwance ƙullin da aka yiwa aljanin a dajin Djinn.
Tsahon shekaru uku cir, sarki Kuffuru na mulki a birnin Kufa. Mulki ya ratsa shi ya zamo babban sarki mai cikakken iko, jama'ar birnin na tsananin tsoronsa saboda ƙarfinsa da jarumtakarsa. Ko kaɗan Kuffuru ba shi da tausayi, hawansa kan karagar mulkin ya sauya duk tsare-tsaren hukunci na ƙasar. Laifi kaɗan mutum zaiyi masa ya yanke masa hukuncin kisa.
A ranar da ya cika shekaru uku akan karagar mulkin ne da yammaci, ya fita rangadi bayan gari tare da dakaru guda ɗari kacal. Suna tafiya har suka iso cikin wani daji mai yawan manƴa-manƴan tsaunika da duwatsu, dama ana baiwa sarki Kuffuru labarin wannan daji don haka ya taso da kansa domin ganin waɗannan manƴa-manƴan duwatsu masu ban al'ajabi.
Shigowarsu cikin wannan daji keda wuya, duwatsu suka fara ɓuɓɓugowa daga ƙarƙashin ƙasa suna tashi sama suna yawo a cikin iska. Dakarun dake tare da sarki Kuffuru suka goge idanunsu da kyau don tabbatar da abinda suke gani, domin suna tsammanin mafarki ne ko kuma almara kawai. Dutse ace ya fito tun daga ainihin tushensa?
Sarki Kuffuru ya san abinda ke shirin faruwa, don haka ya dubi waɗannan dakaru ya ce su koma da baya da gudu. Ai kuwa basuyi gardama suka ja da baya suka ruga da gudu suka nufi ƙarshen dajin. Tafiyarsu keda wuya waɗannan duwatsu suka narke suka haɗe a waje guda, suka bayar da siffar aljani Buƙalshiyu Djinn.
"Ya rayuwarka ta sarki take?" inji aljanin. "Da fatan kana jin daɗin zama a birnin Kufa?"
Kuffuru ya ce, "Kwarai kuwa. Ina jin daɗin zama a wannan birni. Dama kwanan nan nake tunanin kai maka ziyara kuma na tambayeka akan yaushe ne zan fara farautar ƴan ƙabilar Kuyúru?"
Djinn ya bushe da dariya ya ce, "An riga an buɗe ƙwalbar tsafi kowanne lokaci zaka iya fara farautar waɗannan mutane, abinda ake buƙata shi ne ko kai ko mahaifiyarka ku kashesu da hannunku ko kuma da hannun da kuka umarta."
Sarki Kuffuru ya ce, "Ta ya ya zan iya gane waɗannan mutane a duk inda nayi arba dasu? Ban taɓa kallon ko mutum ɗaya daga cikinsu ba." Djinn ya fiddo wani madubin tsafi daga cikin jakar tsafinsa ya nunawa sarki Kuffuru siffar ƴan ƙabilar Kuyuru, kuma ya shaida masa cewa a tsibirin Gazwar kawai zai na samun irinsu.
"Kana nufin ka ce basa yawo dole sai dai naje da kaina har wancan tsibiri ina kamo su?" inji sarki Kuffuru.
Djinn ya ce, "Kwarai ma kuwa amma bada niyyar yaƙi za ka na zuwa ba, a matsayin bafatake mai sayan amfanin-gona zaka na zuwa. Kaga kenan ta ƙarƙashin ƙasa zakana yaƙarsu."
Kuffuru ya ce, "Mene dalilin da yasa kace haka, ni fa sarki ne zan iya zuwa da rundunar dakaru na murƙushe su gaba ɗaya." Djinn yayi murmushi ya ce, "Ka manta abinda na faɗa maka ne? Hasanul Jalwar shi ne wanda wannan ruhi ya zaɓa a matsayin magajinsa yanzu, kuma na ce maka ba zaka taɓa yin nasara akan Hasanul Jalwar ba face ka rabashi da takobin SAIFUL SHIRADU, ka manta ne?"
Sarki Kuffuru ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Kash, ai sai yanzu na tuno. Amma zanyi yadda kace ɗin wato zan na zuwa a matsayin bafatake."
Ba tare da ɓata lokaci ba suka yi sallama da aljani Buƙalshiyu Djinn ya ɓace, Kuffuru ya juya dokinsa ya koma cikin birnin Kufa.
Daga wannan rana sarki Kuffuru ya fara zuwa tsibirin Gazwar a matsayin bafatake yana sayan amfanin gona da kuma amfanin-gona, amma bai bayyana musu asalinsa ba ya ce sunansa... AURAN ZIYAS.))
Koda Aymanul Faris yazo nan a karatun wannan littafi sai ya mayar dashi ya rufe, yana tsananin mamaki wai ashe ZIYAS shi ne Kuffuru? Idan kuwa haka ne to lallai yasan komai na tsibirin Gazwar kuma babu mamaki idan akace shi ne yayi sanadiyar mutuwar Hasanul Jalwar saboda akwai dangantaka mai kyau a tsakaninsu. Abinda ya sake baiwa Aymanul Faris mamaki shi ne ace duk faɗin tsibirin Gazwar babu wanda ya gano munafuki Kuffuru?
***
*****RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 29: *Hodon*
*
*
✍️✍️✍️ Umar Sangaru ✍️✍️✍️
*
Kwance yake akan wani farin gado na haske, gaba ɗaya jikinsa yayi sanƴi ko kaɗan baya motsi, kai kace ya mutu. Idan mutum ya lura sosai zai ga akwai waɗansu irin fararen igiyoyi na tsafi a sossoke a jikin wannan tsohon mutumi. Abin mamaki mutane guda uku ne kewaye da wannan gado, dukkansu sun ƙurawa wannan dattijo dake kwance akan gadon idanu. Mutum na farko ya kasance tsoho mai yawan gashin gira da dogon gemu, yana sanƴe da baƙaƙen kaya irin na gawurtattun matsafa. Mutum na biyu kuma ya kasance dogo mai murɗaɗɗen jiki kuma lokaci-lokaci ƙamshin sarauta na tashi a jikinsa. Ta ukun nasu kuma mace ce ƴar kimanin shekaru ashirin da haihuwa. Idan mutum ya ƙarewa waɗannan mutane guda uku kallo zai fuskanci cewa ba wasu bane illa boka Hubbazu, sarki Kuffuru da ƴarsa gimbiya Firziyya.
"Ƙoƙarin karanta abinda ke cikin ƙwaƙwalwarsa nake," inji boka Hubbazu. "Tun da kun ce ya ƙi ya yiwa sarki Darwazu bayani, ni nasan yadda zanyi nasa yayi bayani ko yana so ko baya so!" Yana faɗin haka ya fiddo waɗansu igiyoyin haske guda biyu ya soka a cikin gashin kan Saihar al-Aswàd. Yin haka keda wuya wani allon tsafi dake jikin gini a gefe guda yayi haske, ya fara nuna rayuwar Saihar tun daga kuruciyarsa har zuwa sa'adda yayi arba da mahaifiyar Barban ya aureta. Har ta sami juna biyu ta haifi Barban.
Allon tsafin ya ci gaba da nuna inda aka je aka binne cibiyar Barban, yadda Barban ya taso da yadda Saihar ke wulaƙanta su shi da mahaifiyarsa. A taƙaice dai duk abinda ya faru tun daga haihuwar Barban har izuwa girmansa babu abinda su sarki Kuffuru basu gani ba, abinda ya basu mamaki shi ne Barban na girma siffar jikinsa na sauyawa izuwa dishi-dishi wato basa iya shaida shi. Saboda haka basu isa su ce ga yadda kamanninsa suke ba, abinda kawai suka sani shi ne kammaninsa na yarinta.
"Wannan mutumin gogaggen matsafi ne, ajin-ƙarshe. Koda mutum ya sami damar kallon tarihin rayuwarsa bai isa ya iya shaida kamanninsa ba, babu yadda za'ayi mu iya gano shi da ainihin kamanninsa face wannan dattijon yayi mana bayani." inji boka Hubbazu.
Ya sake fiddo wata igiya mai tsananin haske ya dannata a ƙirjin tsoho Saihar, lamarin da yasa yayi ƙara kenan. Hubbazu yayi dariya ya ce, "Wannar igiya da kake ji a jikinka, da numfashin mutum take amfani. Ko kayi abinda muka ce ko kuma numfashinka yayi ta ɗaukewa har ka mutu." Yana gama faɗin haka ya danna wannan igiya a ƙirjin Saihar da ƙarfi. Take numfashin Saihar ya ɗauke, jikinsa ya sandare, idanuwansa suka kafe suka kalli sama.
Sarki Kuffuru ya ce, "Baka da hankali ne? Meyasa zaka kashe babban makaminmu a yanzu?" Ya dakawa boka Hubbazu tsawa.
Zata iya yiwuwa Hubbazu baiji abinda sarki Kuffuru ya ce ba domin ko motsawa baiyi ba balle ya bashi amsa, har tsahon daƙiƙu ɗari uku da talatin sannan ya zaro wannan igiya daga ƙirjin tsoho Saihar.
Saihar ya ja dogon numfashi sannan idanunsa suka buɗe a hankali ya kalli su boka Hubbazu akansa a tsaye, suna yi masa kallon rashin imani.
"Barka da dawowa daga mutuwa, yanzu sai ka amsa mana waɗannan tambayoyi idan baso kake ka mutu ba," inji boka Hubbazu yana ƙyaƙyata dariya. "MENE NE AINIHIN SUNAN ƊANKA? MENE SUNAN MAHAIFIYARSA? A WACCE SHEKARA AKA HAIFE SHI? A INA ZAMU SAMU ZANEN ƳAN-YATSUNSA? Idan ka amsa waɗannan tambayoyi daidai ka tsira, idan kuma baka amsa su ba zaka ɗanɗana azabobi kala ɗari akan wannan gado na haske." Hubbazu na zuwa nan a zancensa ya fiddo wata irin igiya mai baƙin-haske ya dannata a ƙirjin Saihar.
Nan take tsohon ya fara karkarwa zufa ta fara zubowa ta ko'ina daga cikin ƙofofin gashinsa, lamarin da yasa wannan gado ya fara jiƙewa kenan. Wani irin tari ya turnuƙe tsohon ya yi tayi kamar ransa zai fita.
Sarki Kuffuru ya dubi boka Hubbazu a fusace ya ce, "Wai so kake ka kashe wannan tsohon ne da waɗannan banzan azabobi naka? Kayi masa tambayoyin mana idan ya ƙi baka amsa in yaso sai ka azabtar dashi." Boka Hubbazu yayi dariya ya ce, "Na tabbata yanzu zaiyi bayani don ya tabbata azabobina ba irin na sarki Darwazu bane. Kai tsoho bamu amsoshin mu?"
Boka Hubbazu ya zare wannan baƙar igiya daga ƙirjin Saihar, take ya daina karkarwa kuma zufa ta daina keto masa. Bayan ƴan daƙiƙu ya dawo hayyacinsa.
"ASALIN SUNAN ƊANA SHI NE *HODON AL-ASWÀD* sunan mahaifiyarsa kuma Shamsul-Sauwaba ƴar sarki Kamrakamu na birnin Zuwedes. A shekarar 1642 aka haifi Hódón. A wuri ɗaya nake tunanin za'a iya samun zanen ƴan-yatsunsa. Ba wani wuri bane illa dutsen dake tsakiyar ƙauyenmu na Shahil, Hódón ya kan zuwa kan wannan dutse yana wasa lokacin da yake yaro, na tabbata a nan ne kaɗai za'a iya samun zanen ƴan-yatsunsa." Saihar na ƙare bayani ya sume akan wannan gado.
Boka Hubbazu ya miƙe tsaye ya nufi wani ƙaton kasko dake ƙarshen wannan ɗaki, an cika kaskon da itatuwan sihiri. Wani irin shuɗin hayaƙi yana tashi daga cikinsa. Yana zuwa gindin wannan ƙaton kasko ya fara karanto waɗansu ɗalasiman tsafi yana haɗawa da ambaton ainihin sunan Barban 'Hódón' tsahon ɗan lokaci kafun wannan shuɗin hayaƙi ya fara juyewa izuwa siffar wani guntun aljani mai faɗin fuska.
Boka Hubbazu ya dubi wannan aljani yayi masa magana a cikin yaren tsafi, aljanin ya kaɗa kai ya ɓace. Hubbazu ya koma wajen su sarki Kuffuru ya tsaya. Yasa hannunsa biyu ya dafa wannan gado wanda Saihar ke kwance akansa, take kuwa gadon ya rikiɗe ya juye izuwa siffar gado mai laushin gaske. Tsoho Saihar ya bayyana akan gadon yana ta sharara barci.
Boka Hubbazu ya dubi su sarki Kuffuru ya fara musu bayani, "Aikinmu ya kammala. Amsoshin da wannan tsoho ya bamu daidai ne. Wannan aljani da kuka ga na kirawo zaije ƙauyen Shahil ne ya ɗakko zanen yatsun Hódón ya haɗa da ƙasar inda aka binne cibiyarsa. Sannan ya sana'anta mana wata taswira wacce zata nuna duk inda Barban yake a faɗin duniya, wannan aljani kuma shi ne wanda zai faɗa mana hanƴoƴin da za'a bi wajen kamo wannan ɓarawo. Don haka ku zo muje mu kwanta mu huta, zuwa kwanaki uku kafin ya dawo."
Koda sarki Kuffuru da ƴarsa Firziyya suka ji batun boka Hubbazu sai hankalinsu ya kwanta, suka kalli juna suka yi murmushi.
Shi dai sarki Kuffuru tun sa'adda yayi arba da sarki Fairaz yaji bayanansa sai yaji duk duniya babu abinda yake so kuma yake buri kamar kama ɓarawo Barban domin waɗannan sarakuna guda tamanin da uku su dawo ƙarƙashin mulkinsa, kuma da yaji labarin Aymanul Faris na tare da Barban sai yaji abun ya sake tunzura shi. Idan zai iya tunawa boka Hubbazu ya taɓa ce masa indai ya kashe Aymanul Faris ya saka jininsa a cikin wannan ƙwalba, ƙwalbar zata cika domin jinin Aymanul Faris kaɗai yafi ƙarfin rabin ƙwalbar kasancewarsa jinin Hasanul Jalwar.
Ba tare da ɓata lokaci ba, boka Hubbazu da su sarki Kuffuru suka koma cikin fada suka zauna suka ci gaba da tattaunawa akan yadda zasu iya kamo Barban.
***
A can wani ɓangare na wata ɓoyayyiyar duniya kuwa, Barban ne tare da aljani Ranganu zaune cikin wata ƙasaitacciyar fada sun ƙurawa wani madubin tsafi idanu. Abin mamaki shi ne duk abinda ke faruwa tsakanin boka Hubbazu da tsoho Saihar shi wannan madubin tsafi ke nunawa. Don haka sun ga duk abinda su boka Hubbazu suka aikata.
"Na fuskanci har yanzu bokayen duniya basu gama fuskantar ƙarfinka ba," inji aljani Ranganu. "Wannan shi ne dalilin da yasa na sauya aikin sarki Kuffuru daga na ƙarshe izuwa na uku, tunda yana ganin shi ne mai farautarka. Ya kamata ka nuna masa cewa bai isa ba, idan muka je cikin birninsa mukayi sata tabbas nasan zai saduda ya tabbatar da cewa kama Kilawu ba ƙaramin aiki bane."
Barban ya yi murmushi ya ce, "Tabbas duk abinda ka faɗa hakane, maigirma. Naga alama wannan sarki ma yana buƙatar ayi masa ladabi. Amma idan aljani Sheezuwa ya gama aikin da suka saka shi, wannan taswira zata nuna inda nake?"
Da jin wannan tambaya Ranganu ya yi dariya ya ce, "Shakka babu, zata nuna inda kake kuma zasu iya zuwa duk inda kake ɗin amma sai sunzo zamu nuna musu, me ake kira da BAMBANCI TSAKANIN ƘARFIN SIHIRI DA GUNDARIN TSAFI! Don haka ka kwantar da hankalinka, bari muga iya gudun ruwansu."
*****
Bayan kwanaki uku da tafiyar aljani Sheezuwa izuwa aikin da boka Hubbazu ya saka shi, ya dawo cikin wannan ƙaton kogo na tsafi ɗauke da wata jar akwati mai jan haske.
A wannan rana boka Hubbazu, sarki Kuffuru da gimbiya Firziyya na zaune bisa kujeru sunci sun ƙoshi, suna dakon dawowar Sheezuwa.
Yana dira a fadar ya faɗi gaban boka Hubbazu yayi gaisuwa, kamar yadda ya saba.
"Aljani Zuwa an dace ne?!" Boka Hubbazu ya tambaye shi.
Aljani Sheezuwa ya sake risinawa ya ce, "Aikin da ka sakani ya kammala, nayi nasarar haɗa wannan taswira wacce zata bi diddigin inda wannan mutum yake. Amma ba zata fara aiki ba face an salwantar da rayuwar makusancinsa na jini wanda suke da kyakkyawar alaƙa. Wannan taswira tana buƙatar ta zuƙi jinin wannan mutumi wanda za'a salwantar, domin tayi amfani da jinin ta bi diddigin wannan mutumi."
"Jinin Saiharul-wadi al-Aswàd Núyes zai wadatar da wannan aiki?" Boka Hubbazu ya tambayi Sheezuwa.
Aljani Sheezuwa ya ce, "Ina shi wannan Saihar ɗin yake, na gwada jininsa?"
Boka Hubbazu ya tafa hannayensa wannan gado na haske ya bayyana, Saihar ya bayyana kwance akan gadon. Hubbazu ya nuna Sheezuwa da tafin hannunsa take wannan gado ya tafi izuwa inda yake tsaye.
Aljani Sheezuwa yasa farcen hannunsa mai kama da tsinin takobi ya yanki tafin hannun Saihar, jini ya zubo ƙasa. Amma kafun wannan jini ya isa ƙasa wata iska mai ƙarfi ta zuƙe shi, ya ɓace ɓat, ba'a ga inda yayi ba.
Sheezuwa ya fiddo wata takarda mai kaurin gaske daga cikin jakar tsafinsa ya ƙura mata idanu, yana ta nazarin waɗansu abubuwa.
Sarki Kuffuru da gimbiya Firziyya kawai da kallo suka bi aljanin don basu taɓa ganin halitta mai sarrafa ɓakin-tsafi kamar wannan aljani ba.
"Jininsa zai yi!" Inji Sheezuwa.
Gimbiya Firziyya da sarki Kuffuru suka yi tsallen farin ciki.
Aljani Sheezuwa yasa farcen hannunsa kamar takobi akan wuyan Saihar, ya ɗaga kansa sama ya fara karanto waɗansu ɗalasimai. Kai kace karatun yanka yake.
Yana gama karanto ɗalasiman ya datsa wuyan Saihar da kaifin wannan farce, kai kace rago aka yanka. Gimbiya Firziyya ta kawar da kanta gefe, saboda ganin tsananin rashin imani da rashin tausayi.
Abin mamaki shi ne jinin Saihar ko ɗiso bai zubo ƙasa ba, duk wannan iska mai ƙarfin ce ta zuƙe shi. A wannan wuri Saiharul-wadi al-Aswàd Núyes ya rigamu gidan gaskiya.
Aljani Sheezuwa ya miƙawa boka Hubbazu wannan taswira ya ce, "Na gama aikina!" Hubbazu ya karɓeta ya ce, "Gaishe ka babban hadimi, tabbas ina alfahari da kai." Sheezuwa yayi murmushi ya ɓace ɓat daga cikin kogon.
Boka Hubbazu, sarki Kuffuru da gimbiya Firziyya suka koma kan waɗannan kujeru suka zazzuna. Hubbazu ya shimfiɗe wannan taswira akan wani teburi, dukkansu suka ƙura mata idanu.
Taswirar tana ɗauke da zanen gaba ɗaya ƙasashen duniya, baya ga haka kuma mutum zai iya amfani hannunsa yana zuƙo duk inda yake so hakan zaisa taswirar tana nuna duk wani lungu da saƙo na faɗin duniya. Akwai wani koren haske a jikin taswirar wanda ke nuni da wajen da Barban yake, babu wani lungu ko loƙo da Barban zai shiga a wannan duniya wannan taswira bata nuna ba.
"Bari mu koma na fara shirin tafiya kamo Hódón!" Sarki Kuffuru ya faɗa yana dariya kuma yana faman nannaɗe wannan taswira.
"Baka da hankali ne?!" Boka Hubbazu ya daka masa tsawa. "Kana tunanin mallakar wannan taswira zai sa ka iya kamo Hódón ne? Ka manta abinda na taɓa faɗa maka ne? Hódón na tare da aljanin da yafi kowa ƙarfin sihiri a duniya, koda munsan inda yake bamu isa mu iya kama shi ba, muddin yana tare da wannan aljani."
Sarki Kuffuru ya haɗe fuska ya ce, "Wai me kake ɗaukata ne? Kana tunanin ni ba sadauki bane? Idan taƙamarsa aljani ne nima fa inda aljani Buƙalshiyu a bayana ko yau na faɗa masa damuwata zai magance min ita!" Boka Hubbazu ya ce, "To ai sai kace masa yaje ya kawo maka ruhin Samudul Ansari ko?"
"Kun ga faɗa da musu ba naku bane," inji Firziyya. "Mene ne abin yi ya kai babban boka?"
Boka Hubbazu ya yi murmushi ya ce, "Dole ne mu sake saurarawa tsahon kwanaki uku, domin Sheezuwa yaje ya sake yin bincike akan yadda zamu kamo wannan ɓarawo."
"Ba zai yiwu ba!" inji sarki Kuffuru.
******
Zaune take ta sakawa bishiyoyin filawan dake cikin lambun idanu, idanunta nata zubar da hawaye. Ga dukkan alamu wannan kuka da ta keyi ba na ƙa'ida bane, irin kuka ne wanda ake zubarwa a yayin tunanin abin bege.
Budurwa ce kyakkyawa ta kwatance, gashin kanta ja mai haske da sheƙi. Idan mutum ya san gimbiya Jaanu to zaiga ita ce a wannan lambu ba wata ba.
A wannan lokaci ita kaɗai ce ke zaune a cikin wannan lambu na gidanta, tana kallon bishiyoyi. Babu abinda take tunowa kuma yake faɗo mata a rai kamar lokacin da suke wasa ita da Aymanul Faris a wannan waje.
Tun dawowar gimbiya Jaanu daga hannun su Aymanul Faris a kullum, bata da aiki banda zama ita kaɗai tana kuka da tuno Aymanul Faris. Soyayyarsa ta shiga zuciyarta har babu iyaka, bata san inda yake ba kuma bata san a ina zata iya samunsa ba balle taje ta riske shi.
Kusan kullum sai sarki Ayubul Zairiy ya sameta da batun auren Marganu, amma har kullum bata taɓa amincewa ba. Kai sai da ta yiwa sarki Ayubul Zairiy gargaɗin kada ya sake kawo mata batun yarima Marganu saboda ta tsane shi kamar yadda ta tsani mutuwarta.
Gimbiya Jaanu na zaune cikin wannan hali wata amintacciyar kuyangarta ta shigo cikin lambun, tazo gaban gimbiya ta zube ta ƙwashi gaisuwa.
"Sarki ne ya ce yana son ganinki?" inji Kuyangar.
Gimbiya Jaanu ta cika da tsananin mamaki. "Lafiya sarki ke son ganina a yanzu?"
****
*****RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 30: *Tattaunawa*
**
*
*
✍️✍️✍️ Umar Sangaru ✍️✍️✍️
*
A daidai wannan lokaci da gimbiya Jaanu ke ƙoƙarin sanin dalilin da yasa sarki ke son ganinta, a cikin fadar sarkin kuwa wata tattaunawa ce ta musamman ke gudana. Sarki Ayubul Zairiy, sarki Ratanam, boka Ruguzan da waɗansu mayaƙa guda uku ne a zazzaune bisa kujeru sun kewaye wani teburi.
"Rayuwar yarima Marganu tana cikin mugun haɗari. Arnan-dajin dake bautar baƙin-aljani Barzas sune suke farautar rayuwarsa ruwa-a-jallo," inji boka Ruguzan. "Kwanakin baya ma sa'ar da yayi ita ce, sarki Kuffuru yasa an kulle shi a cikin ɗakin ƙarƙashin ƙasa wanda aka gina da zallar gilashi mai taurin gaske. Ba don haka ba da tuni waɗannan arnan-daji sun ɗauke shi sun tafi dashi. Ance babu irin ƙoƙarin da wannan sarauniya ba tai ba wajen fasa wannan gilashi amma batayi nasara ba, kuma ance matsawa da tayi sai ta fasa wannan gilashin ne yasa waɗannan kayan tsafi nata suka yi jifa da ita, kamar yadda ta jefar da sarki Kuffuru."
Sarakunan biyu suka yi ajiyar zuciya a tare gami da gyaɗa kai. Sarki Ayubul Zairiy ya ce, "Amma meyasa sarki Kuffuru zai yiwa Marganu wannan ɗanƴen-hukunci? Don kawai ya gagara kamo su Aymanul Faris?"
Sarki Ratanam ya tari numfashin Ayubul Zairiy ya ce, "Tabbas ko ni ne wannan hukunci zanyi masa, in banda hauka da shirmen yaro. Ina shi, ina iya kamo ɓarawon da yafi ƙarfin sarakuna tamanin da uku? In banda yarinta da rashin sanin me yake yi, waye zai ɗaukarwa sarki Kuffuru alƙawari alhalin bashi da tabbacin cika alkawarin?" Daga jin kalaman sarki Ratanam kasan ransa a ɓace yake, kuma tabbas yana fushi da abinda Marganu ya aikata. Idan zamu iya tunawa kafun Marganu ya fito daga birnin Hirtoliya domin zuwa birnin Damashkar sai da sarki Ratanam ya hana shi amma ya ƙi bin umarnin mahaifin nasa, inda yana fitowa kuma yai kiciɓus da dakarun-masifa suka masa dukan kawo-wuƙa suka kama shi. Saboda haka don sarkin yayi fushi da shi abin mamaki bane.
"Yanzu Marganu yana ina? Kuma tayaya zamu iya kuɓutar dashi? Wannan shi ne dalilin da yasa aka kirawo mu wannar tattaunawa." inji ɗaya daga cikin sadaukan nan guda uku dake zaune.
Boka Ruguzan ya dubi sadaukin ya ce, "Ashram? Ka san gidan kurkukun da tafi kowacce tsaro a wannan nahiya tamu, banda kurkukun mutuwa?" Ashram ya ce, "Kwarai ma kuwa. Kurkukun dake saman tsaunin Duksum tafi kowacce haɗari. Don ance duk ƙarfin mutum da iya yaƙinsa indai aka shigar dashi wannan kurkukun ya shiga kenan, sai yadda aka yi dashi. Kar dai kace can sarki Kuffuru ya tura Marganu don wulaƙanci?"
Boka Ruguzan yayi murmushi ya ce, "Ko shakka babu can aka tafi da Marganu. Saboda sarki Kuffuru ya fuskanci cewa rayuwar yarima Marganu tana cikin haɗari don a kullum da koda yaushe sarauniya Rauziyya ba zata daina farautarsa ba. Amma shigarsa cikin wancan kurkukun babban bala'i ne a gare shi don sai ya gwammace da ma kashe shi akayi, saboda tsananin azabobin da ake ganawa a cikin wannan kurkuku."
Sarki Ayubul Zairiy ya dubi boka Ruguzan ya ce, "Ta ya akayi wannan sarauniya ta san inda yarima Marganu yake?"


Please Login or Register in order to submit comment