Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na wannan gida. Kada ka damu suna nan lafiya kuma tabbas suna cikin aminci."
Hankalin Aymanul Faris ya kwanta ya bi bayan hadimin suka fice.
******
A can birnin Damashkar kuwa, sarki Ayubul Zairiy ne zaune bisa karagar mulkinsa ya
murtuke fuska tamkar bai taba dariya ba. Wata mace ce wacce ke daure da ankwa
durƙushe akan mumbari na fadar, kanta a sunkuye yake kai da gani kasan hukunci take
jira. Wannan mace tana tsananin kama da Aymanul Faris, kai inda ace yana wannan
wuri to da tabbas ya gane waye ce, domin kuwa ba wata bace illa mahaifiyarsa. Ko ya
ya aka yi sarki Ayubul Zairiy ya samu nasarar kamo mahaifiyar Aymanul Faris?
"Na yankewa wannar matar hukuncin kisa, yanzu take za'a fille kanta. Bata yi laifin
komai ba amma jinin sarki Samudul Ansari ce, kowa yasan haɗarin masu irin wannan
jini. Masana suna ganin cewa indai za'a dinga barin jinin Samudul Ansari a doron kasa
to kuwa tabbas masifu da bala'i baza su daina saukowa ba. Saboda haka zamu kasheta
yanzu don tsarkake birninmu." Inji sarki Ayubul Zairiy.
Wani ƙaton mutum ya fito yazo ya tsaya bayan wannan mata, riƙe da wata zabgegiyar
adda ƙirar birnin Sin. Sarki Ayubul Zairiy ya ɗaga hannunsa sama da nufin yana sauƙe
hannun, hauni zai sare kan wannan mata.
"A yi mata afuwa mai martaba?" Inji wata kyakkyawar yarinya dake zaune a bayan
sarkin.
Ayubul Zairiy ya cewa hauni ya tsaya. Sannan ya juyo ya dubi yarinyar, ya ce, "Haba
'yata. Shin kuwa kinsan su waye waɗannan mutane? Su ne fa sanadiyar mutuwar
kakanki Yurbaru da ɗan uwansa Asasinu. Kin kuwa san darajar baba Yurbar? Balle kuwa
ta dan uwansa Asasinu?" Idanun yarinyar suka ciko da kwalla ta ce, "Ni dai abba. Kada a
kashe wannan mata amma a kaita kurkuku. Bana son ganin jinin mata na ta zuba a ƙasa,
idan za'a ɗauki fansa a dauka akan mazaje. Ba'a kan mata masu rauni ba, ko kaɗan
basu da laifi. Kashe mata rauni ne a gurin jaruman kwarai." Sarki na jin haka jikinsa yayi
sanƴi yasa aka dauki wannan mata aka nufi gidan kurkuku da ita, "Kinyi sa'a." Inji sarkin.
Wannan yarinya ita ake kira da suna gimbiya *Jaanu* ta kasance kyakkyawa ta gaban
kwatance. Tana da dara-daran idanu da dogon gashi mayalwaci, gashin gimbiya Jaanu
na da ban al'ajabi domin kuwa ba baƙi bane. Jajawur ne amma ba har can ba, irin
wanda Turawa. Fatar jikinta fara ce mai haske da sheki. Ba ta da baiwa ta jarumta ko
kaɗan, a ganinta zubar da jini ba shi da wani amfani a duniya. Shiyasa indai tana wuri to
fa sarki bai isa ya yanke hukuncin kisa ba. Saboda son zaman lafiyanta da sassaucin da
take nemawa jama'a a wajen sarki, yasa jama'ar birnin Damashkar ke tsananin
ƙaunarta.
Tun gimbiya Jaanu tana 'yar shekaru goma 'ya'yan manyan sarakunan duniya suka
sakata a gaba, kowanne ɗan sarki ba shi da burin da yafi ya aureta, saboda tsananin
kyawunta. Hakan ne yasa sarakuna da kansu suka dinga zuwa wajen sarki Ayubul Zairiy
domin yiwa 'ya'yansu kamu amma gimbiya Jaanu ta ƙi amincewa da ko ɗaya daga
cikinsu.
Gaba sauran 'ya'yan sarakunan sun hakura amma akwai wani guda ɗaya wanda ya ƙi
hakura. Wannan ɗan sarki ana kiransa da suna *Marganu*.
Yarima Marganu ɗan wani hamshaƙin sarki ne dake birnin Hirtoliya wai shi Ratanam.
Marganu ya birkice akan auren Jaanu, ya ɗagawa sarki Ratanam hankali har ya rasa ya
zaiyi. Sau bakwai yarima Marganu yana yunƙurin kashe kansa akan an hana shi auren
gimbiya Jaanu amma sai sarki Ratanam ya kwantar masa da hankali yace komai daren
daɗewa zai aura masa ita.
Idan aka samu wanda ya kawo labarin gimbiya Jaanu birnin Hirtoliya, kyautar da ake
masa har sai ya riƙe baki saboda tsananin mamaki. A taƙaice dai yarima Marganu ya
kamu da mahaukacin son gimbiya Jaanu, amma a ɓangarenta kam, a duk cikin 'ya'yan
waɗannan sarakuna babu wanda ta tsana kamar Marganu saboda ya kasance azzalumi,
mara tausayi.
Bayan an kai mahaifiyar Aymanul Faris kurkuku sai sarki Ayubul Zairiy ya sallami kowa
dake fadar, sannan ya tura hadimi yaje ya kirawo masa boka Ruguzan. Gimbiya Jaanu
tayi sallama da sarki sannan ta tashi ta koma cikin gidan sarautar, tafiyar ta keda wuya
boka Ruguzan ya bayyana.
Bayan sun gama gaisawa da sarki sai ya fiddo tarkacen kayan tsafinsa ya fara bincike.
Sarki Ayubul Zairiy ya kwashe duk abinda ya faru a yayin wannan gumurzu ya zayyanewa
boka Ruguzan. "Tabbas cetonsu aka yi." Inji boka Ruguzan. "To amma waye? Na gama
bincike na na gagara gano ko waye ne. Duk yadda akayi wani kasurgumin bokan ne
daga wata kasa dabam yake taimakonsu." Sarki Ayubul Zairiy ya yi ajiyar zuciya ya ce,
"Nifa jarumtakar waɗannan yara guda biyu tafi daukar hankalina. Tabbas wadannan
yara idan suka girma akwai aiki don sai sun gallabi dukkan abokan gabarsu." Boka
Ruguzan ya sake kallon madubin tsafinsa ya ce, "Sunan yarinyar Riya 'yar wani sadauki
ne da ake kira Jarata. Wannan sadauki jinin sarkin yaki Makau ne na birnin Shaha-
Deher."
"Ya kai wannan sarki, ka san kuwa da ace ka kashe wannan mata da ba karamin
kuskure kayi ba. Saboda me? Ita ce makaminmu a yanzu. Duk inda Aymanul Faris da
jaruma Riya suke baza su daina shirye-shiryen daukar fansar abinda muka yi musu ba,
amma idan suka tabbatar da cewa wannan mata tana hannunmu to tabbas zasu ji
tsoron mu. Shiyasa nake jin dadin zaman 'yarka a fada domin kuwa ta fika lissafi." Sarki
Ayubul Zairiy yayi shuru sannan yayi murmushi ya ce hakane.
****
A wancan boyayyiyar fada kuwa, kashe gari tun da sassafe jarumi Ayman ya farka.
Kuyangi suka kawo masa abincin kalaci ya ci sannan yayi wanka aka rako shi fada, da
zuwansa fada ya zauna akan kujerar da ya zauna jiya. Yana jiran fitowar shugaban
ɓarayin duniya.
Sai da Ayman ya gaji da jira har ransa ya fara baci, sannan saurayin ya fito.
"Kayi hakuri na ajiye ka anan kana jira, ko?" Inji saurayin. Ayman ya haɗe gira bai ce
komai ba. Saurayin ya kama hannun Aymanul Faris suka bar cikin fadar suka nufi wani
ɓangare dabam na gidan sarautar.
Kai tsaye suka je cikin wani katon ɗaki wanda girmansa ya kai na wata unguwa guda,
babu komai a cikin wannan ɗaki face waɗansu manya-manyan rijiyoyi, rufaffu. Waɗansu
sadaukan aljanu guda bakwai Aymanul Faris ya gani suna gadin waɗannan rijiyoyi, da
ganin saurayin sai suka risina. Saurayin ya ce su bude rijiyoyin.
Nan take suka cika umarni, suka bubbuɗe waɗannan rijiyoyin, babu komai a cikin
rijiyoyin face kayan dukiya kala dabam-dabam babu kalar da babu. Kama daga dinare,
zinari, yaƙutu, zubar daji, lu'u-lu'u da waɗansun waɗannan. Tun Aymanul Faris yana
kirga yawan rijiyoyin har ya gaji ya daina, amma aƙalla yasan sun kusa dubu.
"Har yanzu baka faɗa min sunanka ba?" Inji Aymanul Faris.
"SUNANA KILÁWUD BARBÀN amma da BARBÀN ake kirana. Ba don komai nake son
nuna maka dukiyata ba, sai domin ka tabbatar da cewa dukiya bata gabana, ɗaukar
fansa nake. Wannan ita ce taskata ta farko akwai kalarta guda goma a bangarori
dabam-dabam na duniya.
"Babu wanda ya san inda maɓoyata take a duk faɗin duniya, fiye da shekaru goma ina
sata amma ko sau ɗaya ban taba haduwa da ɓacin rana ba. Ina da yara a kowacce
ƙasa dake faɗin duniyar nan, fiye da mutum dubu arba'in ke aiki a karkashina amma
babu wanda ya taba kallon fuskata. Hasalima ko alamuna basu taɓa kallo ba, fiye da
mutum dubu talatin da biyar suna birnina da na sakawa suna DARUL BARBAN. A
wannan birni kowanne ɗan ƙasa yana da albashi, babu mugu babu ɓarawo, mutanen
kirki ne kawai. Mafi yawa daga cikinsu marayu ne waɗanda suka rasa iyayensu a
lokacin yaƙe-yaƙe. A ƙa'idar sata ta bana yiwa talaka ko attajiri sata, sarakuna kawai.
Sarakunan ma azzalumai." Inji Barban.
Aymanul Faris bai san sa'adda ya gigice ba sakamakon jin wannan suna. "Dama kaine
kasurgumin ɓarawo, Barban?"
Barban ya ce, "A duniya da mutum uku kawai na yarda. Na farko mahaifiyata. Na biyu
kaine. Na uku kuma ba zan bayyana maka shi ba tukunna. Wannan siffar da kake kallo
ba ainihin siffata ba ce, wannan ta bogi ce. Da sannu zaka ga ainihin siffata." Yana
gama fadin haka ya sake kama hannun Aymanul Faris suka rankaya izuwa fadar.
Duk da cewa mutanen dake ƙauyen Gazwar basa yawo amma sun san labarin barawo
Barban sarai, saboda shi ne ɓarawon da ya yiwa sarkin birnin Sin sata wacce ta talauta
shi.
Aymanul Faris kawai mamaki yake, kuma gani yake tamkar mafarki yake. Suna isowa
fada sarkin ɓarayi Barban ya sallami dukkanin hadiman dake fadar, ya rage saura shi da
Aymanul Faris kawai. Sarkin ɓarayi Barban ya nuna allon tsafin dake fadar da hannunsa
guda take hoton birnin Damashkar ya bayyana inda ake yankewa mahaifiyar Aymanul
Faris hukunci.
"Idan kana yiwa Allah ka fitar dani daga cikin wannan gidan domin naje na ƙwato
mahaifiyata. Na rasa abbana bana son sake rasa mahaifiyata, na roƙe ka." Aymanul
Faris ya durƙusa a gaban sarkin ɓarayi Barban.
Sarkin ɓarayi ya ce, "Ba zasu kasheta ba domin kuwa gimbiya Jaanu zata hana. Zan tura
sauran mutanenka zuwa birnin Darul Barban daga baya zamu yi tunanin ƙwato
mahaifiyarka daga hannunsu amma bayan kayi min alƙawari guda daya." Aymanul Faris
ya ce, "Fadi abinda kake so na yi maka ko mene na rantse zanyi, ni dai kada su cutar da
mahaifiyata." Sarkin barayi Barban ya ce, "Zauna muyi magana, babu abinda zai samu
babarka matukar Jaanu tana raye a birnin Damashkar." A sannan ne hankalin Aymanul
Faris ya fara kwanciya.
"Meye burinka a rayuwa? Me kake so ka cimma?" Inji Barban.
Aymanul Faris ya yi shuru ya faɗa kogin tunani mai zurfi har tsahon dakiku dari da
tamanin. Sannan ya numfasa.
"Burina shi ne naga an daina zalunci a ban kasa. A daina zubar da jini. Burina na biyu shi
ne cika wasiyyar da abbana ya bar min, ta kare lafiyar mahaifiyata da kuma ɗaukar
fansa akan manyan sarakuna guda uku wato sarki Ayubul Zairiy da sarki Ratanam da
sarki Kuffuru. Ban san meye suka yiwa abbana ba amma dole ne na sare kan kowanne
daga cikinsu." Inji Aymanul Faris cikin kololuwar yadda. Shi kansa bai san meyasa ba
amma yaji ya yarda da Barban tamkar wani ɗan uwansa.
"Burinmu iri daya ne da kai" inji Barban. "Abubuwan harinmu duk ɗaya ne, wadannan
sarakuna guda uku. Bari nayi maka taƙaitaccen tarihi akan kowanne daga cikinsu da
abinda yasa zan dauki fansa akansu. Kafun nayi maka tarihin wadannan sarakuna bari
na fara baka tarihin rayuwata da birninmu."
Sarkin barayi Barban ya gyara murya shikuma Aymanul Faris sai ya gyara zama, bisa
mamaki sai Aymanul Faris yaga sarkin barayi Barban ya tashi yaje bakin ƙofa ya budeta.
Jaruma Riya ta shigo cikin fadar. "Ni na tura a taho da ita saboda tana da muhimmanci
sosai a ayyukanmu, kuma tana da riƙon amana." Inji Barban a lokacin da suka zo suka
zauna kusa da Aymanul Faris. Bayan Aymanul Faris sun gama gaisawa da jaruma Riya
sai sarkin ɓarayi Barban ya fara bayani.
"Kimanin shekaru tamanin da biyar baya, a arewa-maso-yammacin duniya anyi wani
ƙaton birni mai suna Shàha. Wannan birni da girma yake domin ya tara tarin al'umma
da manƴan attajirai. Birnin ya kunshi ƙabilu kala dabam-dabam har guda goma, ƙabilar
da tafi kowacce fice a kasar ana kiranta banu Kuyuru. Dama tun asali ma su ne suka
kafa birnin Shàha, don haka gaba ɗaya muƙaman iko suna hannun mutanen wannan
ƙabila ta banu Kuyuru.
"Sarkin da ke mulkin wannan birni a wancan ya kasance sadauki kuma jarumi ana
kiransa da suna Al-Khamis. Sarki Al-Khamis na da 'ya'ya guda biyu sadaukai, Deher da
Meher. Uwarsu daya ubansu daya.
"Ƙabilar da ke bin bayan banu Kuyuru a wancan zamani wata kabila ce da ake kira banu
Huturu. Sun kasance masu tsananin kishi da zalunci suna ganin kamar an zaluncesu ne
tunda babu nasu a cikin majalisar kasar, saboda haka suka fara yiwa sarki Al-Khamis
maƙirci domin su samu su kawar da shi su haye karagarsa. Lokacin da sarki Al-Khamis
ya fara tsufa sai farin ciki ya lullube 'yan ƙabilar babu Huturu da ƙabilar Jenher, suna
ganin kawai idan sarki ya mutu zasu karɓi mulki.
"Kwatsam! Kuma sai 'ya'yan sarki Al-Khamis suka taso wato Deher da Meher, suka
zamo zakwakuran mayaƙa, zaratan sadaukai da ba'a taba kamar su ba a birnin Shàha.
Komai zasuyi kansu a haɗe suke yi, basa zalunci. Lokacin da sarki Al-Khamis ya kamu
da cutar ajali wacce ta hana shi fitowa fada, sai 'ya'yan sa suka fara zuwa suna zartar
da hukunci. Da yake birnin Shàha katoto ne sai aka raba 'ya'yan sarkin biyu, Deher ya
tsaya a bangaren arewa. Meher kuma aka tura shi yankin kudu.
"Nan take al'amuran mulki suka ci gaba da gudana kamar sarki yana nan, mutane suna
tsananin jin dadin mulkin Deher da Meher saboda sun gado mahaifinsu a fagen adalci.
"Bayan wata bakwai, sarki Al-Khamis ya mutu. Aka binne shi sannan aka dawo rikici
akan waye zai gaji sarki? Bayan zubar da jini da yaƙe-yaƙe majalisar ta amince a raba
birnin Shàha gida biyu - birnin Shàha-Deher da birnin Shàha-Meher. Kowa ya amince da
wannan tsari har da su kansu ƙabilar banu Huturu da Jenher kuwa.
"Ashe wadannan ƙabilu a fuska ne kawai suka nuna sun amince amma a baɗini haushi
suke ji, saboda an kashe musu mayaka da yawa sakamakon yakin da aka gwabza.
Shugaban ƙabilar banu Huturu ya tara dukkanin manƴan kabilar a gidansa domin suyi
shawara akan yadda zasu ga bayan 'ya'yan sarki. Da farko ɗakin yayi tsit, amma daga
baya sai wani dattijon mutum mai yawan dogon gemu ya ce, "Idan muna son muga
bayan waɗannan 'ya'yan sarki, tofa lallai sai dai mu ɓullo da salon yaudara tunda karfin
soja an nuna mana an fimu." Kowa ya nutsu yana sauraron jawabin dattijon.
"Dattijon ya ci gaba da cewa, "Mazajen duniya da suka yi zamani suka shuɗe, suna da
rauni. Wannan rauni shi ne soyayya. Misali kamar sadauki Hantaru mai saiful lujara
soyayya ce taga bayansa. Kamar haka ne, indai muna son kashe waɗannan 'ya'yan
sarkin zamu saka su faɗa soyayya da 'ya'yanmu mu kuma sai muyi amfani da wannan
dama mu gama da su." Dattijon yaja dogon gemunsa yana kallon sauran mutanen dake
ɗakin yana sauraron ko akwai mai wata shawara. "Macen da tafi kowacce kyau a
kabilar banu Huturu, ita ce Samra 'yar sadauki Jamnas. Dole ne Jamnas ya amince
mana mu aurawa sarki Deher wannan 'ya tasa don cika burinmu." Sadauki Jamnas ya
gyada kai alamun amincewa. "Akan kabilata zan iya sadaukar da komai." Inji shi.
Dattijon ya yi murmushi, ya ci gaba. "Ruhin Huturu ya albarkaceka. Wacce take bin
bayan Samra a fagen kyau kuwa ba wata bace illa gimbiya Amra 'yar shugaba Fahalu na
kabilar Jenher. Gobe zamu shirya kowacce daga cikin 'ya'yan nan namu mu turawa
kowanne sarki, mu ce idan bai aureta toh har abada baza mu taɓa mara masa baya ba."
"Gaba daya mutanen dake dakin suka kyada kai alamun amincewa sannnan suka
jinjinawa wannan dattijo bisa shawarar da ya kawo. Kashe gari aka tura waɗannan 'yan
mata guda biyu gurin kowanne sarki, tare da wasika da sa hannun kowacce ƙabila.
"Koda Meher yayi arba da Amra sai ya ɗimauce saboda tsananin kyawunta, take ya
amince da bukatar ta. Aka daura musu aure a take a fadar, ba tare an gayyaci kowa ba.
"A bangaren sarki Deher kuwa, cewa yayi sam wannan ba abu ne mai yiwuwa ba,
saboda ya yiwa mahaifiyarsa alkawari; 'yar kabilar banu Kuyuru kawai zai aura. Saboda
haka ya baiwa Samra haƙuri, ya hada ta da dukiya mai yawa ta koma inda ta fito.
"Koda su sadauki Jamnas suka ga ɗaya ya amince dayan kuma bai amince ba sai suka
sake zama. Dattijon nan ya yi murmushi ya ce, "Hakanmu ya cimma ruwa." Wani daga
manyan ƙabilar Jenher ya dube shi ya ce, "Haba baba Amjas. Kamar ya ya?" Dattijon da
aka kira baba Amjas ya ce, "Zamu yi amfani da dutse daya mu jefo tsuntsaye biyu.
Amra zata canjawa Meher ra'ayi akan ya juyawa ɗan uwansa baya kuma ya yaƙe shi,
hakan zai janyo 'ya'yan sarkin suyi ta yakar juna har suyi mutuwar ragas." Kowa a dakin
ya bushe da dariya.
"Lokacin da sarki Deher ya samu labarin cewa ɗan uwansa Meher ya auri Amra 'yar
kabilar Jenher sai hankalinsa ya dugunzuma domin ya tabbatar da makiricin da ake ƙulla
musu. Saboda haka ya rubuta wasiƙa da kansa kuma ya buga hatiminsa ya aikawa ɗan
uwansa.
"Wani abin mamaki shi ne Allah ya jarrabi Meher da tsananin kaunar Amra tun sa'adda
ya aureta tayi amfani da surƙulle ta tsafe shi. Ya dawo tamkar bawanta duk abinda take
so shi yake yi, ko kara ta ajiye bai isa ya tsallaka ba. Manzon sarki Deher ya isa birnin
Shàha-Meher lafiya to amma koda aka karanta wasiƙar da ya kawo take Amra tasa
sarki yasa aka sare kan manzon sannan aka maidawa sarki Deher raddi mai zafi.
"Ran sarki Deher yayi mugun ɓaci ya ce, yanzu ɗan uwana ne zai min haka. Na rantse da
sadaukantakar babanmu sai na sato wannan mata tasa na sare kanta kamar yadda suka
yiwa manzona Razzan.
"A sirrance sarki Deher ya tura a nemo masa ɓarawon da yafi kowa iya sata a duniya."
Sarkin barayi Barban ya yi murmushi sa'adda yazo nan a labarinsa, sannan ya ci gaba.
"Asalin sunana shi ne Aswàd. Ina rayuwa a wani ɗan ƙaramin ƙauye dake tsakanin birnin
Shàha-Deher da birnin Shàha-Meher ana ce masa Shahil. Babana ya kasance mashayin
giya, mutumin banza, mai son holewa da bin mata sosai. Mahaifiyata ta kasance abar
wulanƙatarwa da muzantawa a gare shi, a gaban idanunta yake shigowa da karuwansa
har ɗakinsu na aure suyi ta fasikancinsu.
"Saboda ka sa jurar ganin wannan abu yasa mahaifiyata ta ɗaukeni muka bar masa
gidan, muka koma kwana a rumfar kasuwa. Da safe sai muyi tabi rumfa-rumfa muna
bara domin samun abinda zamu ci, wataran a ji tausayinmu a bamu wataran kuma a
hanamu. Wani abin takaici shi ne mahaifina yasan halin da muke ci amma bai taɓa kula
mu ba, kullum cikin sharholiyarsa yake.
"Watarana sai mahaifiyata ta kamu cuta mai tsanani. Hankalina yayi mugun tashi na
ɗauketa na kaita gurin wani mutumi mai magani. Koda ya gwadata sai ya dubeni ya ce,
"Cutar òlsa ne ya kamata sakamakon yadda take yawan zama da yunwa. Abun har yayi
yawa dole sai an kashe mata makudan kudade kafun ta samu lafiya." Na durkusa na
cewa mai maganin dan Allah ya yi mata aikin, ko nawa ne zan kawo. "Kudin ba kaɗan
bane saurayi. Dinare dubu arba'in fa. A ina zaka same su?" Na ce shi dai yayi mata aikin
da yamma zan kawo masa. Don gudun kada yace bazai yi ba, na ruga da gudu na
shiga kasuwa. Ina shiga kasuwa na nemi gindin wata bishiya na zauna, ina ta nazari
akan ina zan sami dinare dubu arba'in?
"Ina cikin wannan hali na hango mahaifina tare da wata zabgegiyar budurwa sun nufi
gidanmu, cikin hanzari na bi bayansu. Mahaifina na daure da wata lalita a kunkuminsa
wacce ya ajiye kudinsa a ciki, sai da na bari sun shiga cikin cunkuson jama'a na zaro
wata ƴar karamar wuƙa na yanke lalitar na gudu. Na nemi wata bishiya na sake zama na
irga abinda ke cikin lalitar na samu dinare dubu tamanin. Saboda tsananin farin ciki
bansan sa'adda na bushe da dariya ba. Na koma wurin mai magani na biya shi kuɗin
aikinsa dubu arba'in. Naga yana yi min wani kallo-kallo kamar bai yadda dani.
"Abokin babana ne attajiri Zairan ya bani kuɗin" na fadawa mai maganin. Bayan kwana
goma ya sallame mu, dama kafun mahaifiyata ta fito tuni na saya mana ƙaton gida da
sauran kudin da na sato a lalitar babana.
"Mahaifina ya yi juyin duniyan Allah ya rasa a ina kudinsa suka ɓata, sai da ya kusa
haukacewa saboda tsabar son kudin da yake. Dubu tamanin ba wani abu bane a
wajensa amma dukda haka sai da ya rude. Koda yaji labarin mun sayi gida sai ya
tabbatar da cewa lallai ni ne na saci kuɗinsa, da farko ƙarata ya kai gurin sarki. Sarki ya
kore shi.
"Ban san hawa ba, ban san sauƙa ba watarana na dawo daga cikin kasuwa nazo na
sami mahaifiyata kwance a cikin jini tana numfarfashi. An caka wata wuƙa mai tsananin
kaifi a cikinta ta dube ni ta ce, "Kada ka zamo talaka! Har ka mutu a rayuwarka ka ci
gaba da neman kudi kawai ta kowanne hali......." Nan take numfashinta ya ɗauke, jikinta
ya sandare. Ta mutu akan hannayena. Nayi kuka har na gaji bayan an binneta.
"Daga wannan lokaci na gallabi mahaifina da sata don na tabbatar shi ne ya kasheta.
Babu irin tarkon da mahaifina bai kafa min ba amma na haye, daga karshe guduwa yayi
ya shiga duniya ya barni a wannan ƙauye. Sai dai kafun ya tafi ya bawa wani abokinsa
labarin baiwata akan sata.
"Daga lokacin da mahaifina yayi hijira na daina sata, na dawo ina neman abinci da
ƙarfina. Babban abinda yake bani matsala shi ne ko kaɗan bani da jarumta, aikin karfi
yana wahalar dani sosai. Nan fa yunwa ta fara kamani saboda ragontaka ta wanda
ubangiji ya ɗaura min, na rasa ina zan saka kaina domin na ciyar da kaina. Idan ina
neman taimako korata ake."
"Kwatsam! Watarana sai naji labarin sarki Deher yana neman ɓarawon da zai sato masa
gimbiya Amra akan kudi dinare milyan guda. Koda naji wannan labari sai farin ciki ya
lullube ni, na dauko rigata guda ɗaya na saka na nufi fada.
"Fada ce kasaitacciya a wannan fada babu kowa daga sarki sai masu tsaronsa. Ina
shigowa sarki Deher ya bini da kallo kawai har nazo na kwashi gaisuwa a gabansa, sarki
ya sallami duk na cikin fadar suka fice. "Dama kai nake jira domin ka sato min Amra, na
san kai kaɗai ne zaka iya wannan aiki a duk faɗin duniya." Inji sarki Deher. Idanuna suka
zazzaro na cika da tsananin mamaki yadda akayi wannan sarki ya gane ni.
"Sarkin ya ci gaba da cewa, "A halin yanzu ɗan uwana ya samu labarin ina son sace
matarsa, ya karfafa tsaron birnin Shàha-Meher. Dole sai kayi da gaske, a nan ne
hikimarka zata yi aiki." Bayan sarki ya gama min jawabi akan birnin Shaha-Meher sai
nayi masa sallama na tafi. Ko sanda ban dauka a matsayin makami ba balle ayi tunanin
wani abu daga ni sai rigata da wandona.
"Daga birnin Shàha-Deher zuwa birnin Shàha-Meher tafiya ce ta sa'a biyar kacal,
saboda haka da yammaci na isa kofar birnin wacce aka yi ta zallar mulmulallen karfe
mai kaurin gaske. Tun daga dazuzzuka da ƙauyukan dana ratso lissafi kawai nake
tayaya zan iya wucewa da gimbiya idan na satota?
"Kofar birnin Shàha-Meher a kulle take, a saman kofar an rubuta 'ba'a shiga wannan
birni sai zuwa wani kayadadden lokaci.' Dukda cewa na karanta waɗannan rubutu
amma sai naje bakin kofar na kwankwasa. Wata mitsitsiyar taga ta buɗe aka harare ni,
"Kai mara kunya, ba kaga abinda aka rubuta a saman kofar nan bane?" Na ce na gani.
Aka ce me ya kawoka? Na ce, "Ni dan aike daga ƙabilar Bulaizu." Mai gadin ya ce,
"Maƙaryacin banza a yankin kasashen nan namu babu ƙabilar Bulaizu." Bisa mamaki sai
mai gadin nan yaji shuru, ya daka tsawa yaji ban amsa ba. Kawai sai naga ya turo ƙofa
zai bude don ya leƙo yaga ina nayi. Nikuma ɓuya nayi a saman dutse dake bakin ƙofar,
mai gadin na fitowa ya shaki wani abu mai kama da banju ya bingire ƙasa ya kama
bacci, ba wani bane ya watso masa banju ba sai ni ɗinnan. Na toshe hancina da
tsumma don kada nima banjun yayi aiki akaina, na sauƙo daga kan dutsen naja wannan
sadauki cikin jeji na cire kayan jikinsa na saka. Sannan kai tsaye naje na shiga cikin
birnin, sa'ar da nayi ita ce a dai-dai lokacin rana ta fadi ba'a shaida masu gadin sosai.
"Dakyar na samu na mayar da wannan kofa na rufeta don tsananin nauyi, dare nayi aka
sallamemu daga wurin aiki wadansu dakaru dabam suka zo suka karɓa mana. Na shiga
kasuwar garin na sayi bakaken kaya na ajiye, na kuma sayi farare. A wannan dare banyi
wani yunƙuri na shiga gidan sarautar sarki ba, amma a anguwar da 'yan kabilar Jenher
suka fi yawa na kwana, na yi ta yi musu tambayoyi akan Amra.
"Washe gari kasuwar garin ke ci, don haka tun da safe na tafi kasuwa sanƴe da fararen
tufafi, na tara jama'a ina ta nuna musu siddabaru da rufa ido. Gimbiya Amra tana
matukar son ganin irin wannan wasa, kamar yadda na samu bayani daga baƙin mutanen
garin. Koda jama'a suka ga abubuwan al'ajabin da nake a kasuwa sun fara yawa sai
aka fara yaɗa labarina a cikin gari, wannan ya faɗawa wancan wancan ya faɗawa
wannan. Har sai da naga waɗansu kuyangin gidan sarautar sunzo sannan na fara wani
wasa.
"Takobi nake sakawa na fille kan wani saurayi sannan daga baya na dauki kan na sake
ɗaura masa, bisa mamaki sai aga kan saurayin ya sake jonewa kamar ba'a sare shi ba.
Na sake dubawa inda waɗannan kuyangi suke tsaye naga sai shewa suke, suna ta
mamaki. Kawai sai na saka baƙaƙen kayan nan dana saya, na fara zane-zane akan kasa.
Dokin wasa na zana amma bisa mamaki sai aka ga dokin itace ya ratso ya fito.
"Wannan saurayi wanda muke wasan nan dashi, ya haye kan dokin. Take dokin ya tashi
sama yana ta lilo akan iska yana kewaya jama'a, 'yan kallo. "Kai ammafa wannan
saurayin ya iya wasan tsafi. Inda ace sarauniya zata ganshi na rantse da sai taji dadi."
Inji daya daga cikin kuyangin nan. Kawai sai naga sun rankaya sun nufi unguwar da
gidan sarauta yake. Saurayin nan ya ci gaba da lilo akan iska kafun ya sakko.
"Haka dai muka

Please Login or Register in order to submit comment