Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

barci. Ba tare da ɓata lokaci ba, suka
firfito suka wanke idanunsu sannan suka zo suka fara ɗibar gara.
Bayan kowa ya ci ya ƙoshi, sai maigida Barban ya dubi Aymanul Faris da jaruma Riya ya
ce, "Saura rabin sa'a kacal, mahaifiyarka ta iso cikin wannan daji don haka kuzo muje
mu tari Marganu domin yin musanƴa." Yana gama faɗin haka ya tashi ya fice daga cikin
kogon, Aymanul Faris, jaruma Riya da gimbiya Jaanu suka take masa baya. Gimbiya
Jaanu tana tafiya tana kallon Aymanul Faris zuciyarta nata kukan rabuwa da shi, tabbas
a daren jiya ya burgeta matuƙa kuma ta ji daɗin sumbatar da ta yi masa.
Haka dai suka ci gaba da tafiya har suka iso wani ƙaton fili, mai yawan dogayen
bishiyoyi. A saman bishiyoyin ne suka yi arba da waɗansu dakarun aljanu kimanin su
dubu uku, kowannensu ya ɗame kyauro bisa baka yana shirin harbi. Aljani Ranganu ya
bayyana a gabansu ya ce, "Duk wanda a cikinku yayi wani yunƙuri na yaƙar yarima
Marganu take waɗannan dakaru zasu harbe shi, ya mutu don haka ku kiyaye." Yana
gama faɗin haka ya ɓace ɓat.
***
Lokacin da yarima Marganu ya shigo cikin dajin Marsas sai yaji wani irin kasala ya rufe
shi, baisan meyasa ba amma sam yaji bashi da wani kuzari kuma yaji tamkar an cire
masa dukkan ƙarfin damtsensa. Suna ƙara dannawa cikin dajin yana jin wani irin abu a
ransa mai kama da karayar zuciya da kuma rashin ƙwarin gwiwa. Suna shafe tafiyar
rabin sa'a kacal suka iso wani wuri mai yawan dogayen itatuwa, yarima Marganu yayi
arba da dakarun aljanu bisa waɗannan bishiyoyi sun saita tsakiyar filin da kwari da
baka.
Kafun su yarima Marganu su shiga cikin wannan filin, wani ƙaton aljani ya bayyana a
gabansu. Aljani ne dogo mai manƴan fuka-fuki guda biyu a gadon bayansa, inda a ce
maigida Barban na wannan da tuni zai gane wannan aljani domin shi ne mai gidansa a
harkar sata. "Ni ne aljani Ranganu, nazo gareka ya kai wannan ɗan sarki domin nayi
maka kashedi akan kada ka kuskura kace zaka yaƙi su Aymanul Faris domin kana yin
hakan, waɗannan dakaru nawa zasu harbeka!" Inji aljani Ranganu yana kallon Hajriya
dake kwance a gefen Marganu idanuwanta a rufe. Yarima Marganu ya ƙarewa aljani
Ranganu kallo ya ce, "Meyasa tun da na shigo cikin wannan daji, nake jin sauyin yanayi a
jikina? Fatan dai ba yaudarata kuke so kuyi ba domin ku haɗamu ni da gimbiya kuyi
garkuwa da mu?" Aljani Ranganu ya ɓata rai ya ce, "Kai yaro! Shin kana tunanin akwai
abinda zamu buƙata a wajen iyayenka ne? Idan taƙamarku dukiya ce, to nan gidanta
kazo! Idan mulki ne kuma ni ɗinnan da kake kallo ƙasashen aljanu bakwai ne a
ƙarƙashin ikona. Ka shiga taitayinka!!" Aljani Ranganu na gama faɗin haka ya ɓace ɓat.
Aljani Gulzab ya waiwayo da kansa ya dubi yarima Marganu ya ce, "Ya kai wannan ɗan
sarki, meyasa baka da tsoro ne? Meyasa kake yiwa manƴa maganganu marasa daɗi?
Shin kuwa ka san waye ne aljani Ranganul Husubul Ansari?" Yarima Marganu ya fusata
ya ce, "Koma waye shi bai dame ni ba, yi maza ka ƙarasa da mu izuwa tsakiyar wancan
wurin..." Ya nunawa aljani Gulzab cikin wannan dogayen itatuwa. Take aljani Gulzab ya
buɗe fuka-fukinsa ya dira a tsakiyar wurin, inda yarima Marganu yayi arba da mutane
huɗu a tsaitsaye. Wanda yafi ɗaukar hankalin yarima Marganu a cikin mutane huɗun
shine Aymanul Faris, saboda shima saurayi ne mai irin shekarun yarima Marganu amma
jikinsa yafi na Marganu murɗewa nesa ba kusa ba.
Marganu ya sauƙo daga kan aljani Gulzab sannan ya goya mahaifiyar Aymanul Faris
akan kafaɗunsa suka fuskanci juna. Dukda cewa gimbiya Jaanu na tsaye a wannan wuri
amma idanun yarima Marganu akan Aymanul Faris tuni ya cika da tsananin mamaki,
ashe za'a samu saurayi mai irin shekarunsa wanda ya fishi murɗewa da kafiya?
Tambayar da ya yiwa kansa kenan amma bai samu amsarta ba.
Kilawud Barban ya tako sawayensa ya taho inda yarima Marganu ke tsaye yana
kallonsa, har ya iso inda yake tsaye. Aka yi kallon kallo sannan Barban ya fara jawabi da
cewa, "Lale marhaban da zuwan jarumi uban jarumai. Muna so ka ajiye wannan mata
bisa wancan dutsen domin mu ga lafiyarta, mu tabbatar da cewa babu wani sihiri da
kuka yi mata..." Ya nunawa yarima Marganu wani faffaɗan dutse dake ajiye gefe guda,
yarima Marganu ya harare shi sannan yaje ya ɗaura Hajriya bisa wannan dutse. Barban
yaje ya tsaya akanta ko daƙiƙu sittin masu kyau bai shafe ba ya dawo, ya tabbatarwa da
yarima Marganu tana lafiya. "To ai sai ku bani gimbiya na tafi koh?" Inji yarima Marganu
yana hararar Barban.
Barban ya yi murmushi yazo daf da yarima Marganu har suna shaƙar numfashin juna
sannan ya ce, "Baka san waye ne a tsaye a gabanka ba, shiyasa kake min izgilanci. Shin
ba zaka bi umarnin da aka baka bane? Ka kama ni mana idan ka isa? Ni ne Kilawud
Barban ɓarawon da ya gallabi duniya da azzaluman cikinta da sata, ga ni tsaye a
gabanka idan ka isa ko ɗan yatsa ka ɗaga min!" Koda yarima Marganu yaji furucin
Barban sai yaja baya a tsorace, domin bai taɓa tsammanin wannan mutumin shi ne
ɓarawon da ya addabi sarakunan duniya da sata ba. Yarima Marganu ya ƙare masa
kallo yaga ko kaɗan ba shi da wata sura ta jarumta, jikinsa a sake yake tamkar na mata.
Wani murmushin nuna isa ya gilma ta bakin maigida Barban kawai ya juya ya nufi inda
su Aymanul Faris ke tsaye.
****RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 14: *Aikinmu na Farko*
*
*
Umar Sangaru
*
Yana zuwa daidai inda suke ya tabbatar musu da cewa, Hajriya tana lafiya. Aymanul
Faris ya kama hannun gimbiya Jaanu suka nufi inda yarima Marganu ke tsaye. Babu
yadda za'ayi mutum ya kalli gimbiya Jaanu da Aymanul Faris yace babu soyayya a
tsakaninsu, saboda irin kwanciyar hankalin dake kan fuskar gimbiya Jaanu tamkar a
hannun ɗan uwanta take, shi kuma Aymanul Faris sam babu alamun damuwa a tattare
da fuskarsa, tafiya suke a hankali tamkar baza su isa inda yarima Marganu yake ba.
Koda suka iso kusa da inda yarima Marganu ke tsaye sai suka yiwa juna bankwana irinta
masoyan asali. Gimbiya Jaanu ce ta fara magana, "Ya kai masoyina kayi sani cewa, da
zarar na koma gida zan nemi wanda yafi kowa iya sassaƙa a birninmu domin ya sassaƙa
min gunkinka, sannan zan sa a rubuta min sunanka a gadon bayana saboda kada
kewarka ta illata ni." Aymanul Faris ya yi murmushi ya ce, "A sauƙa lafiya... Gimbiyata."
Duk wannan maganganu da suka yi yarima Marganu yana ji, kuma sun san yana ji ɗin
amma basu damu ba, ga dukkan alamu suna yi domin yaji haushi.
"Ƙarya ne," Inji yarima Marganu. "Ba ki isa kiyi soyayya da babban maƙiyinmu ba.
Tabbas na san kina yin hakan ne domin kawai naji haushi amma ba soyayya kuke ba."
Gimbiya Jaanu ta dube shi, cikin wani irin kallo wanda ke nuni da cewa ina ruwanka da
abinda nake? Ran yarima Marganu ya ɓaci kawai ya koma kan aljani Gulzab ya zauna.
Aymanul Faris yaje gurin wannan faffaɗan dutse ya ɗauki mahaifiyarsa bisa kafaɗarsa,
ya juyo ya dubi inda yarima Marganu ke zaune ya ce, "Nagode fa, bisa ɗawainiyar da
kayi kafin ka kawo min babata." Yarima Marganu ya harare shi, ya ɗora hannunsa kan
kufen takobinsa ya fara shafata amma koda ya ɗaga kansa yaga yadda aljanun nan suka
kewaye filin kuma ya tuno da gargaɗin aljani Ranganu sai ya fasa.
Gimbiya Jaanu taje ta hau kan aljani Gulzab ta zauna, tana kallon Aymanul Faris tana
murmushi. Aymanul Faris ya juya ya nufi inda su Barban ke tsaye ya bar wurin da sauri.
Yarima Marganu ya yiwa aljani Gulzab umarnin tashi take kuwa ya buɗe fuka-fukinsa ya
tashi ya lulluka cikin gajimare.
Aymanul Faris na zuwa inda su Barban ke tsaye, aljani Ranganu ya bayyana ya dube su
ya ce, "Zamanku a dajin Marsas ya ƙare, kuyi maza ku tafi izuwa ɓoyayyiyar fadar
Barban domin jiƴƴar wannar mara lafiya." Yana gama faɗin haka ya ɓace ɓat. Barban ya
shafi damtsen hannunsa waɗannan aljanu guda uku suka bayyana suka ɗaukesu suka
tafi izuwa wannan ɓoyayyiyar fadar wadda babu wanda yasan haƙiƙanin inda take.
Suna dira a fadar, Barban ya sa kuyangi suka kawo musu abinci da abinsha kala dabam-
dabam, take suka ci suka ƙoshi. Har a wannan lokaci idanun Hajriya a rufe suke, kai
kace suma tayi amma a zahiri ba haka bane. Barban ya tafa hannayensa sau uku take
wata farar aljana ta bayyana tana sanƴe da fararen kaya masu haske ta zube a gabansa.
Barban ya ce, ta duba wannan mara lafiyan. Aljanar ta kwantar da Hajriya akan wani
gado sannan ta ɗauko kayayyakin aikinta ta fara gwaje-gwaje.
Bayan kamar rabin sa'a tana wannan aiki, likitar ta ɗago kai ta dubi su Aymanul Faris ta
ce, "Wannan mara lafiya tasha duka sosai a sassan jikinta da ma cikinta, a halin yanzu
akwai raunika da yawa a cikin cikinta sakamakon dukan da ta sha, zan baku wani
magani wanda za'a ɗinga bata kullum kafin rana ta fito har tsahon wata guda, indai ta
gama shanƴe wannan magani akwai tabbacin zata sami cikakkiyar lafiya. Haka kuma
wannan rauni da aka yi mata na guntule babbar ɗan yatsanta anyi amfani da baƙin ƙarfe
mai kaifi wajen aiwatarwa, shima zan gyara shi yanzu." Tana gama faɗin haka ta fiddo
wata ƙwalba mai ɗauke da wani farin ruwa mai sanyi ta baiwa Aymanul Faris ta ce shi
za'a na baiwa mara lafiyar kullum kafin rana ta fito, sannan ta fiddo wata farar auduga
daga cikin jakar, ta gyara wannan rauni dake kan babbar ɗan yatsan. Tana gama gyara
raunin ta fiddo wani irin magani wanda su Aymanul Faris basu taɓa ganin kalarsa ba, ta
shashshafa a duk inda ya kumbura a jikin Hajriya take kuwa duk kumburin ya saɓe.
Haka dai wannan likita ta ci gaba da gyagygyara raunikan dake jikin Hajriya har ta
tsahon sa'a uku sannan ta kammala, ta juyo ta dubi sarkin ɓarayi Barban ta ce, "Ya
shugabana na kammala aikin da ka sakani, yanzu abinda ya rage shi ne kulawa da
wannar mara lafiyar har tsahon wata guda." Maigida Barban ya yi murmushi ya ce,
"Gaisheka ki, Laziyya. Tabbas kinyi aiki mai kyau." Yana gama faɗin haka aljana Laziyya
tayi masa sallama ta ɓace ɓat.
Aymanul Faris ya ƙarasa inda mahaifiyarsa ke kwance ya zauna kusa da ita sannan ya
ɗora hannunsa akan kafaɗarta yana kallon fuskarta, hawaye ne masu zafi suka zubo
daga cikin idanunsa a lokacin da ya tuno da wasiyyar mahaifinsa. "Anƴa na cika
wannan aiki kuwa, na kare lafiyar mahaifiyata?" Ya tambayi kansa a cikin ransa. Jaruma
Riya tazo ta zauna daf da shi, ta dube shi ta dubi Hajriya sannan ta ce, "Ya kai ɗan
uwana, farin cikinka farin cikina ne. Baƙin cikinka nawa ne. Duk abinda zai sameka ina
so ya same mu tare. Kayi sani cewa maigida Barban ba ƙaramin taimako yayi mana ba,
wajen ganin an ƙwato mahaifiyarka daga kurkuku mafi tsaro a wannan nahiya tamu don
haka nakeso ka amince masa a duk irin ayyukan da zaku yi saboda dalilai guda uku. Na
farko ya taimaka wajen ganin an ƙwato mahaifiyarka, na biyu ya bata kula irin wacce da
wuya mu iya bata, na ƙarshe ya baiwa sauran al'ummarmu maɓoya a birnin Darul
Barban dukda cewa banje wannan birni ba amma jikina yana bani mutanenmu suna nan
cikin ƙoshin lafiya."
Aymanul Faris yaji wata nutsuwa ta lulluɓe shi saboda jin bayanan jaruma Riya, shiyasa
take matuƙar burge shi saboda hangen nesanta da iya magana. "Idan muka fara aiki da
Barban waye zai kula da babata," inji Aymanul Faris. "Shin kin manta da kalaman aljana
Laziyya ne?" Jaruma Riya ta yi murmushi ta ce, "Shiyasa na ce farin cikinka farin cikina
ne, baƙin cikinka ma nawa. Ina so ka bar mahaifiyarka a hannuna zan kula da ita tamkar
yadda zan kula da mahaifiyata, nayi maka alkawarin wannan." Aymanul Faris ya yi
murmushi mai taushi ga jaruma Riya sannan ya fara gode mata. Barban dake tsaye a
gefe guda ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Ya kai babban jarumi, zo muje wani ɓangare na
wannan gidan sarauta tawa domin na fara maka bayanin aikin da zamuyi na farko."
Yana gama faɗin haka ya juya ya fice daga cikin ɗakin Aymanul Faris ya yiwa jaruma
Riya bankwana sannan ya bi bayan maigida Barban.
Wani ɓangare dabam na gidan sarautar Barban yaja Aymanul Faris inda aka ajiye kujeru
guda biyu kacal, sannan waɗansu tafka-tafkan bishiyoyi masu fala-falan ganƴe suka
kewaye idan mutum ba shiga wurin yayi ba, ba zaiyi tsammanin akwai inda mutane
zasu zauna ba. Ga dukkan alamu dai a wannan wuri maigida Barban ke ganawar sirri
da baƙinsa. Aymanul Faris na shigowa wannan wuri yaji wani iko ya buge shi, ya
tabbatar da cewa in cutar dashi za'ayi a wannan wuri bai isa ya kare kansa ba saboda
tsananin sihirin wajen. Barban ya ja hannunsa suka zauna akan waɗannan kujeru guda
biyu.
Barban ya zuba shayi a cikin wani kofi ya kurɓa sannan ya fara bayani, "Wannan waje
shine wurin ganawa ta sirri da aljani Ranganu. Aikin da zamu yi da kai na farko shi ne
zuwa birnin Askandariyya domin sato farin lu'u-lu'u. Kayi sani cewa wannan lu'u-lu'u
darajarsa ta kai dinari milyan ɗari bakwai da sittin. Meyasa zamu sato wannan farin lu'u-
lu'u? Ka san cewa ni ɓarawo ne amma bana zalunci hasalima ban taɓa yiwa talaka ko
attajirin kirki sata ba, satata tana da ƙa'idoji kamar haka: Bana yiwa talakawa sata, idan
naje yin sata bana yin kisa, kafin nayi sata sai na gama kasafin abubuwan da zanyi da
kuɗin, bana sata a wurin adilan sarakuna, bana shiri da azzalumi, na ƙarshe a duk
sa'adda nayi sata sai na bar alamar da aljani Ranganu ya bani domin ita ce shaidata.
"Dangane da ƙa'idojin da na faɗa maka yanzu, sarki Darwazu ya karya ɗaya daga
cikinsu. Wannan abu da sarki Darwazu ya karya shi ne, ya yiwa wani mutum zalunci ya
ƙwace dukiyarsa saboda tsananin baƙin ciki wannan mutumi ya rataye kansa ya mutu,
ya bar ƴaƴa guda biyu, mace da namiji. A halin yanzu suna can cikin birnin
Askandariyya suna bara saboda yara ne ƙanana. Ba komai sarki Darwazu ya ƙwace a
hannun wannan mutumi ba face wata farar lu'u-lu'u mai tsadar gaske wacce na baka
labari.
"Asalin wannan lu'u-lu'u mallakin wata gagarumar attajira ce a birnin Askandariyya, ana
kiranta da suna Zarshiyya. Wannan mace tana da dukiya har na gaban misali, kwatsam
watarana tayi arba da wannan mutumi ta ɗauke shi a cikin fataken dake yi mata fatauci.
Koda taga kyawawan halayensa, da kuma riƙo da amanarsa sai ta aure shi. Bayan sun
haifi yara guda biyu Zarshiyya ta mutu sakamakon cutar ajali, wannan mutumi ya ci gaba
da juya dukiyarta. Watarana sarki Darwazu na bincike a madubin tsafinsa sai yayi arba
da wannan mutumi, tsafin Darwazu ya tabbatar masa da cewa wannan mutumi ya fishi
dukiya saboda wannan dalili ne sarkin ya tura dakaru suka ƙwato farin lu'u-lu'u suka
kaiwa sarkin. Wannan farin lu'u-lu'u shi ne kaso saba'in da biyar cikin ɗari na dukiyar
Zarshiyya, saboda yadda ake wahalar samun farin lu'u-lu'u. Ba'a jima da yiwa wannan
mutumi fashi ba, talauci ya yi masa yawa ga yara guda biyu da matarsa ta bar masa.
Dukkanin ma'aikatan dake aiki a gidansu suka watse, ya rasa wanda zai kula da
waɗannan yara bisa wannan dalili ne ya kashe kansa don ya huta da baƙin ciki. Aljani
Ranganu ne ya bani wannan labari.
"Wannan farin lu'u-lu'u da sarki Darwazu ya ƙwace ya ajiye shi a cikin wani dogon gini
dake tsakiyar gidan sarautarsa. Gini ne dogo mai samfurin husumiya. Akwai dakaru
kimanin mutum dubu goma suna kai-kawo a wannan wuri, baya ga haka wannan farin
lu'u-lu'u a cikin wata akwati aka kulleta. Akwati ne na sihiri wanda ko ya ya mutum ya
taɓa shi, wata ƙararrawa mai sautin gaske zata fara kaɗawa ta cika birnin gaba ɗaya.
Da zarar anji ƙarar wannan ƙararrawa kowa ƙamewa yake a inda yake saboda dakaru
su ji daɗin kama ɓarawon dake ƙoƙarin guduwa cikin ruwan sanƴi. Me yasa sarki
Darwazu ya baiwa wannan farin lu'u-lu'u gagarumin tsaro haka? Saboda yana so ya sayi
wani katafaren gida ne dake birnin Kisra. Idan baka manta ba wannan gida shi ne
wanda na ce maka sarki Kim Sam na birnin Sin yake burin saya a baya kafun na
tarwatsa shi. Yanzu sai ka kasa kunnuwa da kyau kuma ka bani hankalinka ɗari bisa ɗari
domin ka ji yadda zamuyi wannan sata, ba tare da wannan akwati ta tona mana asiri
ba.
"Ta ya ya zamu shiga birnin Askandariyya? Ta ya ya zamu shiga gidan sarautar sarki
Darwazu kai tsaye? Ta ya ya zamu isa inda wannan doguwar husumiya take? Ta ya ya
zamu shiga cikin husumiyar ba tare da dakaru sun kama mu ko kuma sun hallaka mu
ba? Ta ya ya zamu saci farin lu'u-lu'u ba tare da akwatin sihiri ta tona mana asiri ba?
Idan muka sami amsar waɗannan tambayoyi tamkar mun sami nasara a wannan sata
ne." Maigida Barban ya saisaita maƙwagoronsa ya sake kurɓar wannan shayi, yana
kallon Aymanul Faris wanda ke cike da tsananin mamaki.
"Kamar yadda bayanai suka zo mini daga bakin mai girma Ranganu, birnin Askandariyya
na da ƙofofin shiga guda biyu kacal, ɗaya a kudu ɗayar kuma a arewa. A bakin
kowacce daga cikin waɗannan ƙofofi akwai dakarun tsaro aƙalla dubu ashirin, babu mai
shiga birnin Askandariyya face waɗannan dakaru sun caje shi kuma sunyi masa
tambayoyi akan inda ya fito. Shiga birnin ba zai bamu matsala ba saboda babu wanda
ya sanmu balle ya san abinda ke cikin ranmu. Za muyi shiga irinta malami da kuma
ɗalibinsa masu neman karatu a addinin Darayyish, wani addini ne da mutanen birnin
Askandariyya ke bautawa ruwa. Tabbas idan aka ganmu da wannan shiga za'a barmu
mu wuce. Kaga mun gama da matsala ta farko wato shiga birnin Askandariyya.
"Gidan sarautar sarki Darwazu tana da muggan tsaro, mai girma Ranganu ya ce min, ba
mutane ne ke tsaron lafiyar sarki Darwazu ba waɗansu irin halittu ne masu siffa biyu,
rabin jikinsu na zaki rabi kuma na mutum. Daga cibiyarsu yayi ƙasa shi ne na zakin, daga
sama kuma jikin mutum. Waɗannan halittu Ranganu ya ce suna da tsananin ƙarfin
damtse har na Allah ya isa. Zaka iya cewa mu da ba sarki Darwazu zamu kaiwa hari ba
meye zai haɗamu faɗa da waɗannan halittu? Hakane, akwai irin waɗannan halittu guda
bakwai dake cikin wannan husumiya suna kewaya farin lu'u-lu'u babu dare babu rana,
kullum a cikin aiki suke. Matsalar waɗannan halittu shi ne ƙarfin sihirin tsafi baya tasiri
akansu sai tsagwaron jarumtaka da iya yaƙi. Ba zamu fuskanci matsalar komai ba a
shiga cikin gidan sarautar amma ko ya ya muka yi gangancin zuwa inda wannan
husumiya take zamu ga fushin dakarun gidan sarautar.
"Kaga kenan da zarar mun shiga gidan sarautar zamu san hanƴar da zamu bi mu shiga
cikin wannan doguwar husumiya, inda matsalar take muna shiga zamu yi arba da
waɗannan dakaru masu siffa biyu.
"Wannan akwati ta sihiri asalinta boka Balwaz ne ya ƙirƙireta, amfaninta kawai shine
tona asirin ɓarawo idan yazo satan abinda ke cikinta. Ya kai babban jarumi kayi sani
cewa waɗannan dakaru masu siffa biyu da na baka labari, wannan akwati bata aiki
akansu. Bansan meyasa ba amma haka mai girma Ranganu ya faɗa min, don haka ta
kowanne hali sai mun kashe waɗannan dakaru guda bakwai dake cikin husumiyar mu
wanke wannan akwati da jininsu indai mukai haka, ko mun taɓa akwatin ba zata haifar
da ƙara ba.
"Waɗannan su ne amsoshin waɗannan tambayoyi da na zayyane maka ɗazu. Yanzu sai
ka sake saurarawa da kyau domin ka ji amfanina da amfaninka a cikin wannan aiki.
"Amfanina a cikin wannan tafiya shi ne zanyi amfani da hikimata wajen amsa
tambayoyin da masu gadi zasu yi akan addinin Darayyish, sannan zanyi amfani da
hikimata wajen gano hanƴar da zamu bi mu shiga cikin wannan husumiya, sannan zanyi
amfani da hikimata wajen ɓoye farin lu'u-lu'u ba tare da an kalleshi a hannunmu ba. Kai
kuma amfaninka a wannan tafiya shi ne zaka yi amfani da dukkanin ƙarfin damtsenka
yaƙar waɗannan halittu guda bakwai, idan baka manta ba sihirin tsafi baya tasiri
akansu. Zaka yi amfani da ƙarfin damtsenka wajen shigar damu cikin wannan husumiya
domin ina tunanin ta sama zamu shigo. Zaka yi amfani da ƙarfin damtsenka wajen kare
lafiyarka da tawa da kuma abinda zamu sato wato farin lu'u-lu'u. Wannan shi ne
taƙaitaccen bayani akan aikin da zamuyi na farko. Shin kana da tambaya ko kuma
neman ƙarin bayani?"
Aymanul Faris ya yi shuru gami da shiga kogin tunani, yana ta jinjina maganganun
maigida Barban a cikin ransa yana tunanin ta ina ya kamata yayi tambaya. "Yaushe
zamu je wannan birni na Askandariyya domin wannan gagarumar sata? Ka ce
waɗannan dakaru masu siffa biyu ƙarfin sihiri baya tasiri akansu, shin sara da suka zaiyi
tasiri akansu kuwa? Idan muka je yin wannan sata za'a ga fuskokinmu ko kuma rufe su
zamuyi? Sannan ina so kayi min ƙarin bayani akan sarki Darwazu da zaluncinsa.
Waɗannan su ne tambayoyina ya shugabana." Inji Aymanul Faris.
Maigida Barban ya gyara zama sannan ya sake kurɓar shayi ya ce, "Yau talatin ga watan
Nuwamba. Ranar sha-tara ga watan Disamba zamu je wannan gagarumin aiki. Bani da
tabbacin cewa sara da suka yana tasiri akan waɗannan dakaru amma kafin nu tafi zan
tambayi mai girma Ranganu. Ban taɓa zuwa nayi sata fuskata a buɗe ba, yana daga
cikin ƙa'idar sana'ar sata, koda ba'a san ɓarawo ba yana da kyau ya rufe fuskarsa
saboda tsaro. Don haka fuskokinmu a rufe zamuje muyi wannan sata, akwai wata hula
da aka dinka a birnin Shuzzus wacce aljani Ranganu ya bani, da irinta zamuyi amfani.
"Sarki Darwazu ɓarkeken ƙato ne, sadauki ne kuma jarumi. Asalinsa ɗan ƙabilar Dajjan
ne, bayani akan zaluncinsa ba zai wassafu ba face abubuwan da idanu suka gani
kawai. Amma kayi sani cewa sarki Darwazu ya taɓa ƙwaƙule idanun yara goma a cikin
kogon tsafinsa domin aiwatar da wani sihiri, Darwazu ya taɓa fyaɗe mace mai juna biyu
ya fiddo ɗan-tayin dake cikin cikinta yayi tsafi dashi. Ka sani cewa waɗannan dakaru
masu siffa biyu dake tsaron lafiyar Darwazu asalinsu waɗansu mayun aljanu ne dake
rayuwa akan wani tsauni, basu da abinci da ya wuce naman bil'adama, ruwan shansu
kuma shi ne jini. Sarki Darwazu yasan da haka amma ya amince, kullum ci da shan
waɗannan dakaru yana wuyan sarki Darwazu. Sun fi shekaru goma suna tsaron lafiyar
wannan sarki, kayi kintacen adadin naman da suka ci da kuma jinin da suka zuƙa?"
Koda Aymanul Faris yaji wannan batu sai ya cika da tsananin mamakin rashin imanin
sarki Darwazu. Ya dubi maigida Barban ya ce, "Tabbas a duniyar nan akwai abubuwan
shaiɗanci da zalunci da yawa. Wani abun idan mutum yaji sai yaji kamar ya kashe kansa
saboda takaici, mutum da hankalinsa da tunaninsa zai fyaɗe mace mai ciki ya ɗauki
ɗan cikinta yayi me da shi? Tabbas dolene mu hukunta wannan sarki." Maigida Barban
ya yi murmushi ya ce, "Wannan kaɗan kenan, zakaji sauran sarakuna guda tara da suke
cikin littafin harinmu. Su ma zakaji tsantsar rashin imaninsu." Aymanul Faris ya yi ajiyar
zuciya ya ce, "Kuma a duk cikin waɗannan ayyuka guda tara, nima ina da amfani?"
Barban ya ce, "Kwarai ma kuwa. Kayi sani cewa wahalar da zaka sha a waɗannan
ayyuka namu zasu zamo tamkar horo wajen ratsa dajin Djinn domin riskar ruhin
kakanka." Aymanul Faris ya ce, "Yaushe zamu kaiwa dattijo Samazan ziyara domin jin
hikayar SAMUDUL ANSARI?" Barban ya ce, "Sai bayan munyi aiki na biyar, zamu je
wajen wannan dattijo. Saboda idan muka yi aiki na biyar zamu huta sosai wajen shekaru
biyar kafin mu ci gaba." Aymanul Faris ya cika da tsananin mamaki. "Kana nufin zamu
shafe fiye da shekaru goma a wajenka?" Barban ya ce, "Kwarai ma kuwa. Shin akwai
abinda baka jin daɗinsa anan ne?" Aymanul Faris ya kaɗa kai alamun a'a.
Maigida Barban ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Ya kai babban jarumi, ina so nayi maka
waɗansu tambayoyi? Mene ne a tsakaninka da gimbiya Jaanu? Waɗanne maganganu
kuka tattauna lokacin da Marganu yazo ɗaukarta? Shin kana ƙaunar jaruma Riya a cikin
ranka?" Koda Aymanul Faris yaji waɗannan tambayoyi sai idanunsa suka zazzaro ya
dubi Barban cikin tsananin mamaki, kamar yana mamakin meyasa Barban zaiyi masa
waɗannan tambayoyi.
"Gimbiya Jaanu? Masoyiyata ce, tana ƙaunata nima kuma ina ƙaunarta. Ba zan ɓoye
maka komai ba, saboda kallon ubangida nake ma. Tabbas ina ƙaunar Jaanu fiye da
yadda kake tsammani, amma gani nake kamar soyayyar tamu ba zata yiwu ba. Tun da
ta bar wannan wuri namu bansan a ina zan sake kallonta ba. Mahaifiyanta ba zai taɓa
aminta dani na zama sirikinsa ba, kuma idan na fille kansa gimbiya Jaanu ba zata
manta dani ba, saboda baƙin cikin da zan ƙunsa mata. Waye zai ƙaunaci mutumin da ya
kashe masa mahaifi?
"Maganganun da muka tattauna, bankwana ce kawai irinta masoya, bayan wannan
bamu tattauna komai ba. Jaruma Riya? Ƴar uwata ce kuma abokiyata. Idan nace maka
bana ƙaunar Riya kasan ƙarya nake, ina sonta sosai amma bata kai matsayin gimbiya
Jaanu a cikin zuciyata ba." Inji Aymanul Faris.
Maigida Barban ya cika da tsananin mamakin kalaman Aymanul Faris, "Waya ce baza
ka iya auran gimbiya Jaanu ba? Soyayya ƙarya ce aka ce ma? Tabbas zaka iya auranta
amma bayan ka jure wahala da wulaƙanci." Aymanul Faris ya yi murmushi. "Wahala
kuma? Kamar wanne kenan?" Barban ya ce, "Ba zaka taɓa samun nasarar kashe sarki
Ayubul Zairiy, sarki Ratanam da sarki Kuffuru ba face ka mallaki ruhin jarumta. A farkon
haɗuwarmu sa'adda na baka tarihin rayuwata da rayuwar birnin Shaha naso na baka
tarihin waɗannan sarakuna guda uku kamar yadda na

Please Login or Register in order to submit comment