Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sarki Fairaz da fadawansa sun yiwo kansa, ga dukkan alamu mubaya'a suke so suyi masa. In ba mubaya'a ba meye zai sa sarki da kansa har da fadawansa suzo tarɓarsa?
Fairaz da fadawansa suka zo gaban sarki Kuffuru suka zube bisa gwiwowinsu, suka sunkuyar da kawunansu alamun sun yi mubaya'a.
"Daga yau munyi mubaya'a ga babban sarki, sarki Kuffuru magajin Gauhan Ansari." Inji sarki Fairaz da dukkanin fadawansa cikin haɗa murya.
Koda sarki Kuffuru yaji sun kira sunan 'Gauhan Ansari' sai tsikar jikinsa ta mimmiƙe. A duk faɗin duniya in banda sarki Kuffuru da mahaifiyarsa babu wanda ya san Gauhan Ansari.
"Mu je cikin fada," inji sarki Kuffuru. "Maganata da ku mai tsaho ce." Sarki Fairaz ya sallami dukkanin waɗannan fadawa nasa, sannan ya yiwa sarki Kuffuru jagora cikin wata hamshaƙiyar turaka mai tsananin kayan alatu da abubuwan more rayuwa.
Akan wani lumtsemen gado aka zaunar da sarki Kuffuru aka kawo masa abinci mai rai da lafiya gami da ruwan sha kala dabam-dabam, sarki Fairaz ya zauna a gefensa har ya gama cin wannan abinci.
"Na kasance a cikin tsananin farin-ciki," inji sarki Fairaz. "Da babban sarki kamar kai ɗinnan ya kawo min ziyarar-bazata. Shin ya shugabana zan iya sanin dalilin da yasa ka taso da ƙafafuwanka kazo har ƙasata?"
Sarki Kuffuru ya ɗauki wani ƙofin-shayi ya kurɓa sannan ya fara jawabi, "Daga ganin yanayin yadda nazo ƙasarka, ka san bada son raina nazo ba. Idan da ace baka san da zuwana ba meyasa zaku yi min mubaya'a kai da fadawanka bayan kunji sunana?"
Sarki Fairaz ya yi murmushi ya ce, "Labari ne mai tsaho. Shin ka san waye ne gagarumin ɓarawo wanda ya gallabi sarakunan duniya da sata?" Sarki Kuffuru ya sake kurɓar wannan shayi ya ce, "Ko kaɗan amma ina da labarinsa. Kai na taɓa kallonsa a cikin madubin tsafi na ma, amma meyasa ka kawo labarin wannan ɓarawo?"
Sarki Fairaz ya risina cikin biyayya ya ce, "Ina ɗaya daga cikin sarakunan da wannan ɓarawo ya yiwa sata. Kimanin shekaru huɗu da suka wuce yazo wannan birni nawa ya sace min sarƙoƙin-zinari na matata wanda na bata a matsayin sadaki, tunda ya sace waɗannan sarƙoƙi na rabu da matata, domin ban isa na kusanceta ba dole sai tana tare da waɗannan sarƙoƙi na zinari. Na shafe fiye da shekaru uku ina kai ziyara wajen gawurtattun bokaye a ɓangarori dabam-dabam na duniya ana yi min bincike akan wannan ɓarawo amma har yau ban sami wani abun kamawa ba saboda ƙarfin sihirinsa ya wuce duk inda nake tunani. Har na haƙura na daina zuwa wajen bokaye, watanni uku da suka wuce ɗinnan ne wani baƙon boka yazo wucewa ta cikin wannan birni nawa ana kiransa da suna Balwaz. Haƙiƙa na tsinke da al'amarin boka Balwaz saboda abubuwan al'ajabi da ya ɗinga nunawa a birnin nan, saboda haka ne na keɓe da boka Balwaz na bayyana masa buƙatata.
"Boka Balwaz ya ce min, a duniya kaine kawai wanda yake da ikon kama wannan ɓarawo. Balwaz ya ce min nan gaba kaɗan zaka zo wannan birni to nayi maka mubaya'a kuma na baka yardata ɗari bisa ɗari tabbas kaine wanda zai iya yin sanadin da za'a kamo wannan ɓarawo.
"Ya kai wannan sarki kayi sani cewa, gaba ɗaya sarakuna tamanin da uku da wannan ɓarawo ya yiwa sata, mun sami zama dasu mun tattauna. Waɗannan sarakuna sun ɗorani a matsayin shugaba wanda zai jagoranci kamo wannan ɓarawo. Kayi sani cewa wannan ɓarawo baya satar dukiya sai abubuwa masu shegen-tsada da amfani, kamar dai yadda ya rabani da matata bayan sace sarƙoƙin-zinari.
"Waɗannan sarakuna guda tamanin da uku sun amince da cewa duk wanda yayi sanadi aka kamo wannan ɓarawo zasu yi masa biyayya kamar bayinsa, saboda muhimmancin abinda wannan ɓarawo ya sace musu yafi gaban tunani. Muna so da zarar ka koma birninka ka fara tunanin yadda zaka kamo mana wannan ɓarawo."
Koda sarki Kuffuru ya gama jin jawabin sarki Fairaz sai ya bushe da dariyar farin ciki, har yana buga sawunsa a ƙasa. Daga bisani ya dubi Fairaz ya ce, "Ku sa a ranku an kamo wannan ɓarawo. Tayaya kake ganin masarautu har guda tamanin da uku zasu dawo yi min biyayya, idan na kamo wannan ɓarawo sannan ace na gagara kamo shi? Daga nan zuwa watanni uku da yardar abin dogarona wannan ɓarawo yana cikin sabuwar kurkukuna an gama. Sai dai ina da sharaɗi guda ɗaya... Duk wanda a cikin wannan sarakuna ya bijirewa umarnina tabbas zan hallaka birninsa gaba ɗaya. Da fatan zaka isar musu da wannan saƙo?"
Sarki Fairaz ya risina ya ce, "An gama mai duniya. Tabbas idan ka sami nasarar kamo wannan ɓarawo, ka ɗauke mu a matsayin bayinka kawai. Eh mana, yadda nake tsananin ƙaunar matata Jamriyya ace wani ya rabani da ita ai akwai matsala." Sarki Kuffuru ya bushe da dariya sannan ya tafa hannayensa sau uku wani ɓarkeken aljani ya bayyana, Kuffuru ya haye bayan wannan aljani ya zauna.
"Bayan wata guda da mako biyu kazo birnin Kufa ka sameni, domin ka ji yadda aikin yake tafiya." Inji sarki Kuffuru a lokacin da wannan ɓarkeken aljani keta kaɗa fuka-fukinsa zai tashi sama. Sarki Fairaz ya zube ƙasa bisa sawunsa cikin biyayya.
Wannan aljani ya lulluka da sarki Kuffuru cikin gajimare suka ɓace ɓat! Sarki Fairaz ya bisu da kallo kawai har ya daina hango su.
***
Maimakon sarki Kuffuru ya wuce kai tsaye izuwa birnin Kufa sai ya umarci wannan aljani da ya kaishi kogon Hubbaz inda boka Hubbazu yake. Bayan kamar daƙiƙa ɗari takwas da tamanin suna tafiya sai wannan aljani ya dira a bakin wannan kogo, sarki Kuffuru ya sallami aljanin ya tafi.
Kuffuru ya buɗe ƙofar wannan kogo kamar yadda ya saba sannan ya shige cikin kogon, ya nufi karagar boka Hubbazu. A wannan lokaci ma Hubbazu da kansa ya taso ya tari sarki Kuffuru suka koma kan wannan karaga suka zauna tare, har Hubbazu ya tafa hannaye domin teburin abinci ya bayyana amma sai Kuffuru ya ce masa ya ƙoshi. Don haka sai ya dakata.
Boka Hubbazu ya dubi Kuffuru ya ce, "Watanni biyun da na ɗebar ma har sun wuce baka zo ba, ina ka shiga?" Sarki Kuffuru ya ce, "Wallahi mantawa nayi. Ya ake ciki? Ka gano yadda zan samu nasarar kamo sarkin ɓarayin-duniya da Aymanul Faris?" Boka Hubbazu ya bushe da mahaukaciyar dariya sannan ya ce, "Nayi bincike akan yadda za'a kamo sarkin ɓarayin-duniya kuma an dace..." Sarki Kuffuru ya gyara zama yana sauraro.
"Sarkin ɓarayin-duniya a duniya ba shi da kowa in banda mahaifinsa, wanda wannan mahaifi nasa dashi gwamma babu. Saboda ko kaɗan bai damu da sarkin ɓarayin-duniya ba kuma bai damu da mahaifiyarsa ba. Jiya-jiyan nan bincike yazo mini a hallarar tsafi cewa mahaifin sarkin ɓarayin-duniya na nan cikin birnin Askandariyya yana bara domin neman abinda zai ci. Ya kai wannan sarki kayi sani cewa abubuwa guda uku kacal muke da buƙata wajen gano maɓoyar sarkin ɓarayin-duniya.
"Abu na farko shi ne, ainihin sunan wannan ɓarawo da ainihin kamanninsa. Waɗannan abubuwa zasu taimaka mana sosai wajen zana taswirarsa, idan muka sami taswirarsa zamu iya ganin inda duk yake a faɗin duniya.
"Abu na biyu shi ne sunan mahaifiyarsa da ranar da ta haife shi, domin na saka hadiman aljanuna suyi mini bincike akan jariran da aka haifa a wannan rana da inda aka binne cibiyoyinsu.
"Abu na ƙarshe shi ne zanen-yatsun wannan ɓarawo, wanda nake da tabbacin za'a same shi a jikin baban nasa.
"Idan ka samo amsoshin waɗannan tambayoyi kuma ka kawo min wannan mahaifi nasa tabbas tamkar mun kama wannan ɓarawo ne."
Koda sarki Kuffuru ya ƙare jin kalaman boka Hubbazu sai ya cika da tsananin mamaki ya ce, "Tayaya zamu iya samo wannan mutumi a cikin dubbannin mutane dake bara a birnin Askandariyya?" Boka Hubbazu ya sake bushewa da dariya ya ce, "Wannan mutumi ɗan ƙabilar Nuyes ne. Gashin kansa ruwan ɗorawa ne, na tabbata duk faɗin birnin Askandariyya babu ɗan-ƙabilar Nuyes idan ba shi ba." Sarki Kuffuru ya jinjina kai ya ce, "Na fuskance ka, amma da kaina zanje birnin Askandariyya ko kuma na tura manzanni?"
"Tayaya zaka tura manzanni kuma?" Inji boka Hubbazu. "Da kanka zaka je mana, idan ka tura manzanni aka samu matsala fa?"
Sarki Kuffuru ya yi ajiyar zuciya sannan ya tashi ya nufi ƙofar fita daga kogon, har yaje bakin ƙofa yaji muryar boka Hubbazu a kunnensa.
"Meyasa zaka zo har ka tafi ba tare da ka bani labarin matsafiya Rauhanul-Ziyya ba? Shin ka manta ne ko kuma da saninka kayi hakan?" Inji boka Hubbazu.
A gigice sarki Kuffuru ya dawo wajen boka Hubbazu ya sake zama, ya dubi bokan ya ce, "Meye ka sani akanta?" Boka Hubbazu ya bushe da dariya ya ce, "Idan ka samo mahaifin sarkin ɓarayin-duniya kenan, kaje ka kamo wannan mutumi saboda yanzu haka farautarsa ake don an fara gano cewa shine mahaifin sarkin ɓarayin-duniya, kuma ka san farautarsa za'a yi." Sarki Kuffuru ya haɗe gira sannan ya fice daga cikin kogon domin ya fuskanci cewa boka Hubbazu baya so yayi masa bayani akan RAUHANUL-ZIYYA!
Sarki Kuffuru na fitowa daga cikin wannan kogo ya tafa hannayensa wannan aljani ya sake bayyana, Kuffuru ya umarci aljanin da ya kaishi kurkukun-mutuwa. Aljanin ya buɗe fuka-fukinsa ya lulluka cikin gajimare, bayan ɗan-lokaci ya dira a tsakiyar wani wuri mai rusasshen gine-gine. Babu komai kuma babu kowa a wannan wuri face wani mutum guda ɗaya jal, wanda ke cikin wani ƙaton daki na gilashi.
Sarki Kuffuru ya murtuƙe fuska zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata ƙone saboda tsananin fusata domin ya gano cewa lallai sarauniya Rauziyya ce ta ruguje wannan kurkuku nasa gaba ɗayanta.
Sarki Kuffuru ya ƙwarara uban ihu ya ɗaga muryarsa ya ce, "NA RANTSE DA ƘOLOLUWAR ABIN DOGARONA, KOMAI DAREN DAƊEWA SAI NA KAMO WANNAN SARAUNIYA NA WULAƘANTATA KUMA NA KASHE TA. WANNAN ALƘAWARI NE."
Sarki Kuffuru ya ƙarasa inda yarima Marganu ke kulle a cikin wannan ɗaki ta gilashi, ya karanta waɗansu ɗalasimai wannan ɗaki ya buɗe. Sarki Kuffuru ya finciko yarima Marganu da ƙarfi daga cikin ɗakin, ya ɗaga shi sama ya doka da ƙasa ya take wuyansa ya ce, "Faɗa min abinda ya faru, bayan wannan sarauniya tayi jifa dani ko kuma in kashe ka?" Tun da yarima Marganu yake bai taɓa ganin fusataccen mutum kamar sarki Kuffuru ba, kuma gani yake idan bai faɗawa sarkin abinda ya faru ba, zai iya rasa rayuwarsa gaba ɗaya.
Cikin kakari yarima Marganu ya ce, "Bayan ɓacewarka wannan sarauniya ta rushe gidan kurkukun nan gaba ɗaya, sannan tazo har gaban wannan ɗaki da ka ɓoyeni domin ta hallaka ni amma ta kasa buɗe ƙofar ɗakin, koda ta ci gaba da ƙoƙarin buɗe ƙofar sai aka ɗagata sama akayi jifa da ita, bansan me yayi jifa da ita ba. Wannan shi ne abinda ya faru anan!"
Sarki Kuffuru ya taƙarƙare ya bushe da mahaukaciyar dariya ya ce, "Zancen banza kenan... Ashe ba wani ƙarfin sihiri ne da ita ba kawai tayi sa'a akaina ne. Kai, faɗa min mene ne a tsakaninku har da zata haɗo gagarumar runduna haka tazo farautarka?"
Yarima Marganu ya taso zaune ya ce, "Lokacin da zanje karɓo gimbiya Jaanu ne, na ratsa ta tsaunin Barzasa to, ita ce mai mulki a birnin dake saman wannan tsauni. Bayan na yiwa dakarunta mummunar ɓarna shi ne naje har gidan bautarsu na sare kan gunkin da suke bautawa..." Sarki Kuffuru ya dakatar da yarima Marganu da hannu ya ce, "Tabbas ka ɗebo ruwan dafa kanka a dalilin soyayya. Na farko ban gama yi maka hukunci ba, na biyu ga wannan ga baƙar-matsafiya dake neman rayuwarka ruwa-a-jallo. Tabbas ko yanzu soyayya ta kaika ta baro..." Kuffuru ya ƙare maganarsa yana mai dariyar Marganu.
Idanun yarima Marganu suka kaɗa sukayi jawur, zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata ƙone ya ce a ransa, "Duk abinda ya sameni a dalilinki ne, gimbiya Jaanu. Ina matsayin yarima ɗan-sarki na dawo fursuna a gidan yari. Ki karɓi soyayyata ko kuma na kasheki na kashe kaina, mu rayu a barzaƙ."
Sarki Kuffuru ya kaikaici idanun yarima Marganu ya mangare shi, Marganu ya sulale ƙasa sumamme. Kuffuru ya dubi wannan aljani dake tsaye a bayansa ya ce, "Ka ɗauki Marganu ka kaishi gidan kurkukun AZABA-UKU. Ku saka shi a ɗakin-gilashi domin rayuwarsa zata iya fuskantar barazana daga kowanne lokaci." Yana gama faɗin haka ya ɓace ɓat. Wannan aljani ya suri Marganu yai sama dashi tamkar ya ɗauki ɗan-tsako ya ɓace a cikin gajimare.
*******
******RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 24: *Durƙusawar Sarki Fairaz*
*
*
✍️✍️✍️ Umar Sangaru ✍️✍️✍️
*
Sarkin ɓarayin-duniya Barban ne zaune a cikin wani tangamemen ɗaki yayi shuru gami da faɗawa kogin tunani. "Ya aka yi kwata-kwata ban fita da sa'a a wannan karon ba? Meyasa wannan akwatin sihiri ta kamani, dukda cewa nayi iyakar bakin-ƙoƙari na wajen kauce mata? Yanzu inda ace an kama ni da yaya kenan?" Haka dai Barban ya yi ta yiwa kansa tambayoyi ba tare da ya sami amsar su ba. Yana cikin wannan hali ne aljani Ranganu ya bayyana a gabansa sanƴe cikin fararen tufafi.
"Barban, sakamakon taɓa wannan akwati da kayi," inji aljani Ranganu. "Bayananka sun bayyana a wurin boka Balwaz. Ya san sunanka... Ya gano mahaifinka. Tabbas yanzu rayuwarka tana cikin haɗari, kuma lallai za'a iya ganoka cikin sauƙi. Indai muna so mu sake ɓoyeka da bayananka dole sai mun yi abu guda..." Aljani Ranganu ya yi shuru lokacin da yazo nan.
Cikin kaɗuwa da razana Barban ya dube shi, ya ce, "Meye zamu yi kenan?" Maimakon Ranganu ya faɗa amsar wannan tambaya baki-da-baki kawai sai yayi masa raɗa a kunne. Murmushi ne kawai ya gilma ta gefen bakin Barban. Aljani Ranganu ya ɓace ɓat, shima Barban sai ya shafi wannan kambu dake ɗaure a damtsen hannunsa ya ɓace ɓat. Bayan ɗan-lokaci ya sake bayyana a cikin wannan ɗaki, sannan ya tunkari ƙofar ficewa daga ɗakin.
Yana fitowa ya nufi ɗakin da aka kwantar da Aymanul Faris, da zuwa bakin ƙofar ɗakin, ya buɗe ya shige ciki. Aymanul Faris na kwance bisa wannan gado, daga shi sai gajeran-wando sakamakon yawan raunikan dake kan tumbinsa. Barban ya tako yazo har inda yake ya tsaya akan wannan gado, yana nazarin raunikan Aymanul Faris.
"Ya jikin?" Inji Barban.
"Ah.. Jiki ya fara samun sauƙi," inji jaruma Riya. "Jikin nasa mai kyau ne. Don naga har raunikan sun soma haɗewa, kuma ina ganin nan da cikar kwanaki goma zai gama warwarewa."
"Kwanaki goma?" Barban ya yamutse fuska. "Meye amfanin Laziyya kenan? Tabbas na san koda sau ɗaya idan ta bashi magani, zai warke." Yana gama faɗin haka ya rintse idanunsa ya kwalawa Laziyya kira sau uku. Ai kuwa take ta bayyana a cikin wannan ɗaki.
"Uwar-likitoci wannan saurayin nake so ki duba min..." Laziyya ta risina sannan ta fiddo kayayyakin aikinta ta fara dudduba Aymanul Faris.
Tsahon rabin sa'a ta ɗauka tana gyagygyara masa raunikan sannan ta ɗago. "Nan da bayan-gobe warhaka, zai gama warwarewa." Inji aljana Laziyya.
Barban ya yi murmushi ya ce, "Da kyau. Aikin ki na kyau. Uwar-likitoci. Je ki na sallameki sai wani lokacin." Aljana Laziyya ta yi musu sallama ta ɓace ɓat daga cikin ɗakin.
Fitar ta keda wuya maigida Barban ya dubi inda Hajriya ke kwance yaga ta gama warkewa sumul, har fatar jikinta ta fara yin kyau. Ga dukkan alamu lokacin da Aymanul Faris zai farfaɗo itama zata farka, murmushi kawai Barban yayi ya dubi jaruma Riya ya ce.
"Ya ke ƴar-uwar Aymanul Faris, zamanku a cikin wannan gida yazo ƙarshe. Daga yau zan ɗauke ku na mayar da ku birnin Darul Barban, a can za ki ci gaba da jiyyar mahaifiyar Aymanul Faris domin can ya faɗi tsaro."
Jaruma Riya ta cika da tsananin mamaki ta dubi Barban ta ce, "Mene ne ya kawo wannan sauyin yanayi? Ko dai an fara gano maɓoyar tamu ne?" Barban ya kaɗa kai ya ce, "Ko kaɗan. Kawai dai naga kwanan nan ni da Aymanul Faris baza mu na zama sosai a gida ba, saboda muhimman ayyukan dake gaban mu. Kuma idan jama'arku suna ganinku a birnin Darul Barban hankalinsu zaifi kwanciya kuma mahaifiyar Aymanul Faris zata fi samun nutsuwa acan ɗin fiye da nan."
Koda jaruma Riya taji waɗannan kalamai na Barban sai nan take taji ta aminta da abinda yake cewa, ta dubi inda Hajriya da Aymanul Faris ke kwance ta ce, "Tabbas wannan shawara ce mai kyau amma Aymanul Faris ya sani kuwa?" Barban ya yi murmushi ya ce, "Aymanul Faris nan da cikar kwanaki biyu zai farka, kuma tabbas zaiyi farin-ciki kamar yadda kika yi."
Barban na gama faɗin haka ya dafa kafaɗar Riya suka ɓace tare, bayan ɗan-lokaci ya bayyana a cikin wannan ɗaki. Ya yi wani tsafi wani gadon sihiri ya bayyana ya ɗora Hajriya akan wannan gado, jikinta na gama hawa kan wannan gado ta ɓace ɓat! Da wannan Barban ya mayar da su Riya birnin Darul Barban saboda a ganinsa can zaifi dacewa dasu tunda Ranganu yace a kowanne lokaci za'a iya gano inda yake.
***
Kamar yadda aljana Laziyya ta faɗa haka abin ya kasance, bayan kwanaki biyu jikin Aymanul Faris ya gama warwarewa sarai, inda aka sossoka masa waɗannan wuƙaƙe duk ya haɗe. Ya samu sauƙi sosai don har miƙewa tsaye yana iya yi, tafiya ce dai yake iya yi kaɗan-kaɗan.
Koda Barban ya ga haka sai ya cika da tsananin farin-ciki domin samun lafiyar Aymanul Faris na nufin ci gaba da ayyukansa da ya shafe tsahon shekaru yana yiwa tanadi, tun da ya mayar da su Riya birnin Darul Barban ya dawo mai jiyyar Aymanul Faris dare da rana.
Don haka a kullum suna tare, a wannan rana ma suna tare cikin wannan ɗaki.
"Ina mahaifiyata da jaruma Riya suke?" Inji Aymanul Faris cikin wata murya mai ban al'ajabi.
"Mahaifiyarka? Ina da tabbacin cewa yau ɗinnan itama ta sami lafiya kamar yadda kaima ka sami lafiya. Ni ne na mayar dasu izuwa birnin Darul Barban domin zamansu a can zai fiye mana alkhairi saboda ayyukan dake gabanmu ba wasa bane. Kuma idan suna ganin irin wannan mugayen halaye da muke shiga tabbas zasu na samun karayar zuciya gami da shiga damuwa mai tsanani." inji Barban.
Aymanul Faris yayi shuru gami da faɗawa cikin tunani. Tabbas abinda Barban ya faɗa hakane, yanzu waye zai so yaga ɗan-uwansa yana cikin mummunan hali mai kama da rai ko mutuwa?
"Waye abin harinmu na biyu?!" Inji Aymanul Faris.
"Sarki Fairaz na birnin Fairul-Faizara shi ne abin harinmu na biyu. Kimanin shekaru huɗu da suka wuce na taɓa zuwa na yiwa wannan sarki sata, ba komai na sato ba face waɗansu sarƙoƙin-zinari masu tsadar gaske. Sanadiyar sato waɗannan sarƙoƙi na zinari na raba aurensa da matarsa. Ni ba azzalumi bane, kayi sani cewa asalin waɗannan sarƙoƙi na Hushriba ne. Hushriba ƴar-uwata ce, babana da babanta wa-da-ƙani suke. Sarki Fairaz yasa aka sato masa waɗannan sarƙoƙi nata a lokacin da ta shigo yankin ƙasarsa domin gudanar da gasar-kyawu ta duk shekara.
"A halin yanzu babu abinda zamu sato a wajen sarki Fairaz face yi masa gargaɗi kawai, da ina da niyyar sato rigar-zinarin sa wacce ya ƙwata a wajen mijin Hushriba amma sai na fasa. Yiwa sarki Fairaz kashedi kaɗai ya wadatar da mu a aiki na biyu."
****
Bayan kamar kwanaki biyu da wannan tattaunawa tsakanin Aymanul Faris da Barban sai jikin Aymanul Faris ya gama warkewa sumul, kai kace bai taɓa jin wani rauni ba. A wannan rana aljani Ranganu ya kawowa Barban taswirar birnin Fairul-Faizara, suka zauna shi da Aymanul Faris suka gama bayanan tsare-tsaren yadda zasu afkawa sarki Fairaz cikin ruwan sanƴi. Suka ajiye ranar huɗu ga watan Maris a matsayin ranar da zasuje birnin Fairul-Faizara domin yiwa sarki Fairaz kashedi.
Ai kuwa wannan rana tana zuwa tunda duƙu-duƙun safiya Barban ya kirawo waɗannan aljanu nasa guda uku suka ɗauke suka kaisu gindin wannan tsauni wanda mutum yana kewaya shi zai riski birnin Fairul-Faizara.
A wannan rana dai, Barban bai ɓoye fuskarsa ba amma kayan da suke jikinsa irin waɗannan baƙaƙen kaya ne masu sheƙi da ɗaukar idanu. Shi kuma Aymanul Faris daga sama har ƙasa jikinsa a rufe da irin waɗannan baƙaƙen kaya, idanuwansa kaɗai ake kallo.
Ana ajiye su a gindin wannan tsauni, Barban ya fiddo madubin tsafinsa ya shefe shi da hannu guda, take cikin gidan sarautar sarki Fairaz ta bayyana. Aka nuno sarki Fairaz cikin wani tafkin wanka tare da wasu tsala-tsalan ƴan mata guda biyu suna wanka. Barban ya yi dariya ya ce, "Daidai ɗin zuwa kenan, muje mu ritsa ɗan-iska." Yana gama faɗin haka ya ruga da gudu kan wannan ƙaton tsauni.
Aymanul Faris na ganin haka ya take masa baya da gudu dama ya riga ya gama yiwa Aymanul Faris bayanin yadda zasu afka cikin wannan birni ta saman wannan ƙaton tsauni, ba tare da sun fuskanci matsalar komai daga dakarun ƙasar ba.
Suna gama hawa kan ƙololuwar wannan tsauni, Barban ya fiddo waɗansu murtuƙa-murtuƙan igiyoyi masu tsananin tsaho da kauri ya baiwa Aymanul Faris ɗaya, shi ma ya riƙe ɗaya. Yin hakan keda wuya suka hau saman waɗansu manƴa-manƴan bishiyoyi masu tsahon gaske akan wannan tsauni, suka saita waɗansu duhuwowin bishiyoyi dake can ƙasa cikin birnin Fairul-Faizara da waɗannan igiyoyi sannan suka cilla igiyoyin cikin wannan duhuwowi. Abin mamaki sai waɗannan igiyoyi suka tafi da gudu tamkar waɗanda aka harba daga cikin baka. Suna zuwa daidai waɗannan duhuwowi waɗansu irin ƙugiyoyi suka bayyana a saman kowacce igiya suka cake a jikin waɗannan duhuwowi.
Barban da Aymanul Faris suka ɗaure jikinsu a jikin waɗannan igiyoyi sannan suka daka tsalle suka afka cikin birnin Fairul-Faizara suna masu maƙalewa a jikin waɗannan igiyoyi, nan fa suka tafi da gudu suka yi ƙasa daga saman wannan tsauni. Idan ka hango su daga ƙasa zakaga mutane biyu sanƴe cikin baƙaƙen tufafi suna sauƙowa daga saman tsauni a jikin igiyoyi tamkar ƴan aiken-mutuwa. Tsahon rabin sa'a suna sauƙowa daga wannan tsauni sannan suka dira a tsakiyar waɗannan duhuwowi.
Suna dira Barban ya fiddo wannan taswira wadda aljani Ranganu ya bashi ya buɗeta ya nunawa Aymanul Faris daidai inda waɗannan duhuwowi suke ya ce, "Mun yi nasarar sauƙa cikin birnin Fairul-Faizara lafiya, kuma mun sauƙa a inda ya kamata a ce mun sauƙa. Daga wannan wuri zuwa fadar wannan sarki tafiya ce kaɗan, kuma kamar yadda kake gani a jikin wannan taswira babu dakarun tsaro ta wannan wuri domin tanan bayan gidan sarautar yake." Barban na gama faɗin haka, Aymanul Faris ya jinjina masa kai alamun ganewa.
Da ganin haka sai Barban ya ratso ta cikin wannan duhuwa ya fito, Aymanul Faris na take masa baya suka kama hanya suka yi ta tafiya bisa sawayensu ba tare da sun hau komai ba. Tsahon sa'a guda sai ga su sun bayyana a bayan wani dogon gini na sarauta. A wannan wuri babu ko badakare guda, saboda tsananin tsayin ginin wanda da wuya a samu mahaluƙin da zai iya tsallakawa koda kuwa yana tare da aljani ne.
Barban ya fiddo wani irin ruwa mai danƙo daga cikin jakar tsafinsa, ya shafa a hannunsa sannan ya shashshafawa Aymanul Faris ma. Koda yin hakan sai suka da gudu suka fara kan wannan bango da gudu tamkar ƙadangaru. Kuma abin mamaki albarkacin wannan ruwa mai danƙo da suka shashshafa a hannunsu basu faɗo ƙasa ba, har sai da suka yi tafiya mai nisa akan wannan gini sannan ruwan danƙon ya soma ƙarewa. Barban ya yiwa Aymanul Faris inkiyar su ci gaba da tafiya kawai wannan ruwan danƙo zai ƙarasar da su.
Ai kuwa haka aka yi sai da suka je can saman wannan gini sannan wannan ruwan danƙo ya ƙare. Nan fa suka tsaya zuru-zuru

Please Login or Register in order to submit comment