Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jaririnta, ta nufo wajen da gudu tana ta gurnani. Gimbiya Kabshiya ta jiwo wani irin gurnani mai ban tsoro ya nufo su, sai ta ɗauki jaririnta dukda cewa tana jin mugun zogi da raɗaɗi a jikinta sakamakon lokacin da ta ɓarnatar tana nakuda kafin ta haife shi. Ta falfala da gudu izuwa cikin wannan daji, tayi ta gudu iya ƙarfi har tsahon rabin sa'a sannan ta fara gajiya.
A daidai lokacin ne ta waigo ai kuwa sai ta hango wannan ƙatuwar kura nata gudu har ta kusa ta cimmata. Gimbiya Kabshiya ta rungume jaririnta ta rufe idanu cikin saduda da yarda da cewa ƙarshen ta yazo.
Wannan ƙatuwar kura ta dako wannan tsalle sama da nufin ta turmushe Kabshiya da jaririnta ta cinƴesu a lokaci guda, bisa rashin sa'a tana dako wannan tsalle wata murgujejiyar bishiya dake gefe guda ta faɗo tsakaninta da su Kabshiya. Kurar bata ankara ba, ta soka bakinta a jikin wani reshe na wannan bishiya, nan take tayi wani ruri mai ban tsoro ta mutu a wannan waje.
Ita dai Kabshiya ƙamewa kawai tayi cikin tsananin mamaki, tabbas ko tambaya babu, ta san cewa akwai wanda ke taimaka musu a ɓoye.
Kai tsaye ta nufi cikin wani ƙaramin kogon dutse ta zauna, ta fiddo mamanta ta fara baiwa wannan jariri. Koda yasha ya ƙoshi sai ya fara barci. Kabshiya ta kwantar da shi a cikin ƙwari na dutse sannan ta ɗebo ganƴaƴe ta lulluɓe shi dasu, ta fita daga cikin wannan kogo domin samo abinda zata ci itama.
Bata yi nisa da barin wannan kogo ba, tayi arba da wata ƙatuwar zakanƴa nan ma juyawa ta falfala da azababben gudu ta nufi hanƴar komawa wannan kogo. Zakanƴar ta saki barewar da ta kamo a bakinta ta bi Kabshiya da gudu suka kasa tsere, ko daƙiƙa ɗari masu kyau ba'a yi ba wannan zakanƴa ta cimma gimbiya Kabshiya. Tayi tsalle sama ta sa ƙirjinta ta bangaje Kabshiya, Kabshiya ta faɗi a wannan wuri a galabaice.
Zakanƴar nan tazo ta tsaya akanta tayi gurnani tayi haniniya, sannan tasa faratan hannunta ta yage kayan jikin Kabshiya gaba ɗayansu. Nan fa Kabshiya ta bayyana tsirara, haihuwar uwarta. Zakanƴar na shirin kafa haƙoranta a wuyan Kabshiya ne, wata zungureriyar kibiya ta fito daga saman wata bishiya ta cake bakinta ta ɓullo ta gadon bayanta. Zakanƴar tayi haniniya mai ƙarfi sannan ta zube ƙasa matacciya.
Har a wannan lokaci gimbiya Kabshiya bata dawo hayyacinta ba, sakamakon ganin mutuwa a fili muraran.
Wani mutum sanƴe cikin kayan farauta ya sakko daga wannan bishiya, rataye da kwari da baka. Ya nufo inda Kabshiya ke kwance. Yana zuwa yai arba da tsananin kyawun gimbiya Kabshiya, nan fa ya ruɗe kuma ya kiɗime. Yayi sauri ya fiddo wata alkyabba daga cikin jakar guzurinsa ya lulluɓawa ita Kabshiya, don kada zuciyarsa tafi ƙarfinsa. Sannan ya yayyafa mata ruwa ta farfaɗo.
Kabshiya tana buɗe idanunta ta tsinci kanta a cikin alkyabbar wannan mafarauci wannan abu yayi matuƙar bata mamaki, ta yiwa abun mummunar fahimta. Ko kaɗan bata yi tunanin zakanƴa ce ta yayyage mata sutura ba, sai tayi tsammanin wannan mafaraucin ne. Koda ta dube shi taga duk inda ake neman namiji yakai, ba za ta iya ɗaukar fansa a gare shi gaba da gaba ba, sai ta bar abun a ranta.
"Ya ke wannan kyakkyawar budurwa, wace ce ke?" Inji wannan mafarauci.
"Sunana Laila ƴar sarki Dulmuru na birnin Failas, harin bazato aka kawo mana aka ruguje birninmu daƙyar na samu na tsira da rayuwata na shigo wannan daji, har ma na haihu a cikinsa. Amma kai kuma waye kai?" Kabshiya ta ɓoyewa wannan mafarauci asalinta.
"Sunana Wusam Kuyuru, ni ɗan asalin birnin Sháha ne, tun babban sarki Al-Khamis yana raye na dawo cikin wannan daji naci gaba da sana'ata watau farauta. Ina wannan jariri da kika ce kin haifa?" Inji shi.
Koda Kabshiya taji sunan wannan mafarauci sai ta murtuƙe fuska, zuciyarta tayi baƙi amma bata nuna masa ba. Ba don komai ba sai domin ta tsani ƴan wannan ƙabila ta Kuyuru, saboda su ne sanadiyyar ɓarkewar yaƙi tsakanin birnin Shàha-Deher da Shàha-Meher. Kuma a sanadiyar wannan yaƙi ne ta rasa mahaifinta, yayanta da kuma mijinta sarki Meher don haka dole ne ta tsani duk wani jini na wannan ƙabila (Kuyuru).
Kabshiya ta shige gaba tana nunawa mafarauci Wusam hanƴa, har suka iso bakin wannan ɗan ƙaramin kogo inda ta ajiye jaririnta. Suka shige ciki suka zauna, Wusam ya fiddo abinci daga cikin jakar guzurinsa ya bawa Kabshiya ta ci ta ƙoshi. Sannan yai sallama da ita zai tafi kuma ya shaida mata cewa zai na zuwa wannan wuri kullum da safe domin duba lafiyarta da na jaririnta kuma zai na taho musu da duk abinda suke buƙata.
Kabshiya tayi masa godiya sannan ta rakashi bakin ƙofar kogon ya fita ya tafi. Sannan ita kuma ta koma ta zauna tana tunanin irin matakin da ya kamata ta ɗauka akan wannan mafarauci domin ɗaukar-fansar abinda yayi mata. Na farko tana tunanin ya keta mata haddi, tun da har ya cire mata kayan jikinta wato ta yiwa wannan abu da zakanƴa tayi mata mummunan fahimta. Na biyu kuma shi ne kasancewarsa ɗan-ƙabilar Kuyuru, ƙabilar da tayi sanadiyar mutuwar ƴan-uwanta da mijinta.
Tsahon rabin-sa'a Kabshiya tana zaune tana tunani, kwatsam! Ba zato ta ji yanayin wannan kogo ya sauya. Wani irin sanƴi mai kama da sanƴin-hunturu ya kama busowa izuwa cikin kogon wanda yasa nan take ta fara karkarwa. Bisa dole ta tuɓe wannan alkyabba ta fata ta lulluɓawa wannan jariri nata domin kada sanƴin ya illata shi.
Wani haske ya bayyana a tsakiyar kogon wanda ya kashewa Kabshiya idanu, bisa dole ta kawar da kanta. Wata sura ta wani baƙin-aljani ta fara bayyana a cikin hasken a hankali, har ta gama bayyana sannan wannan haske ya disashe. Kabshiya ta buɗe idanun cikin tsoro-tsoro, abinda tayi arba da shi shine yayi matuƙar ɗugunzuma mata hankali, jikinta ya karkarwar razana. Ba wani abu tayi arba dashi ba illa ganin jaririnta a hannun wannan basamuden ƙaton aljani wanda ya cika wannan kogon dutse gaba ɗaya saboda girman jikinsa, aljanin na riƙe da jaririn yana ta karanto waɗansu ɗalasiman tsafi yana tofa masa a ƙirji. Ita dai Kabshiya tsoro ne ya hanata ƙarasawa wajen wannan aljani, balle tayi tunanin ƙwato jaririnta har wannan aljani ya gama abinda zaiyi. Ya juyo ya dubi Kabshiya ya ƙyalƙyale da wata irin dariya tamkar ana zubo ƙwaranƙwatsa daga sama, daga bisani ya tsuke bakinsa ya ce.
"Barka dai, ummul-gauhan. Suna na HASAMUL-SAWAZ ni ne babban hadimin sarki Gauhan tun zamanin sarki Samudul Ansari. Ya ke wannan kyakkyawar mata kiyi sani cewa, wannan jariri naki sai ya gawurta a wannan nahiya tamu, kuma lallai kafun ya mutu sai yayi wani abun al'ajabi wanda zai yi matuƙar baiwa mutane mamaki. Tun kafun a haifi wannan jariri sarki Gauhan ya bani labarinsa, Gauhan ya ce min sunan wannan jariri naki shine 'KUFFURU'. Ya ke Kabshiya kiyi sani cewa akwai wani buri wanda sarki Gauhan ya mutu dashi, wannan buri bana komai bane face zama akan karagar birnin Sháha. Wannan buri nasa bai cika ba domin sarki Samudul Ansari yayi wani ɓakin-tsafi wanda zai hana duk wani wanda ya zauna kan wannan karaga kwanciyar hankali da samun nutsuwa. Babu mai zama akan wannan karaga ya samu jin daɗi face wanda ya mallaki RUHIN SARKI SAMUDUL ANSARI, dake ajiye a cikin ƙwalba a taskar tsafinsa.
"Ya ke Kabshiya kiyi sani cewa nayi bincike akan wannan jariri naki, naga cewa lallai jikinsa zai iya ɗaukar ruhin sarki Samudul Ansari dukda kasancewarsa ba jinin Samudul Ansarin ba. Amma dole sai yasha baƙar wahala kafun ya samu nasarar wannan aiki. Akwai wata ƙwalba ta tsafi da sarki Gauhan ya bari a cikin kogon tsafinsa dake ƙarƙashin ƙasa a birnin Sin, dole ne Kuffuru ya cika wannan ƙwalba da jinin ƴaƴan Samudul Ansari. Idan dai yai haka tamkar ya mallaki ruhin ne.
"Ya ke Kabshiya daga yau zan fara taimaka miki wajen ganin wannan ɗa naki ya zamto magajin ruhin Samudul Ansari. Yanzu abinda nake so dake shine ki taho tare dani domin na nuna miki wannan kogo na ƙarƙashin ƙasa da ƙwalbar da ake so Kuffuru ya cikata da jinin ƴaƴan Samudul Ansari."
Aljani Hasamul-Sawaz na zuwa nan a zancensa ya durƙusa, ita kuma gimbiya Kabshiya ta haye bisa gadon bayansa. Ya lulluka cikin gajimare ya nufi ɓangaren Gabas. Bai sauƙa a ko'ina ba sai a cikin wani ƙaton kogo na dutse mai girma da faɗin gaske, babu komai a cikin wannan kogo face kayayyakin tsafi da na yaƙi sai kuma wata ƙatuwar ƙwalba guda ɗaya jal, wacce ta tokare da saman kogon saboda tsananin tsahonta.
Babu komai a cikin wannan ƙwalba face wata farar takobi guda ɗaya jal, idan ka hango takobin daga nesa zakayi tsammanin itacen wuta saboda tsananin haskenta.
Aljani Hasamul-Sawaz ya nunawa Kabshiya wannan ƙwalba ya ce, "Wannan ita ce ƙwalbar da akeso Kuffuru ya cika da jinin Samudul Ansari. Da zarar wannan ƙwalba ta cika hasken dake jikin wannan takobi zai sauya launi ya koma jajawur da zarar ta koma haka Kuffuru zai iya ɗaukarta yayi amfani da ita wajen ratsawa ta cikin dazuzzukan da za'a bi domin riskar wannan ruhi. Yanzu zo mu koma cikin wannan kogo naku, ki fara ganin misali daga Wusam Kuyuru."
Aljani Hasamul-Sawaz yana zuwa nan a zancensa ya ɗauki Kabshiya suka koma cikin wannan ɗan ƙaramin kogo, kafun yayi sallama da ita sai ya fiddo wata siririyar wuƙa ta sihiri ya bata ya ce, ta san yadda zatayi ta cakawa Wusam wannan wuƙa. Yana bata wuƙar ya ɓace.
Washe gari da sassafe mafarauci Wusam ya yiwo farautar barewa ya fyaɗeta sannan ya gasa namanta, ya kawowa su Kabshiya. Kabshiya ta karɓi wannan nama tayi godiya sosai, sannan ta fara ci. Wusam bai tafi ba sai da ya tabbatar ta ci wannan nama ta ƙoshi sannan yayi sallama da ita ya juya zai tafi, dama abinda Kabshiya take jira kenan.
Ta fiddo wannan siririyar wuƙa ta cakawa ita Wusam a gadon bayansa ta ɓullo ta ƙirjinsa, Wusam ya kwarara uban ihu sakamakon mugun zogi da raɗaɗi da ya shige shi. Sannan ya durƙushe bisa gwiwowinsa yana cewa, "Yake wannan kyakkyawar mata, faɗa min wace ce ke meye asalinki? Me nai miki da har za ki kashe ni?"
Maimakon Kabshiya ta bashi amsar waɗannan tambayoyi sai ta sake caka masa wannan wuƙa a cikinsa, take Wusam yai aman jini sannan ya ce ga garinku. Nan take ya mutu bisa gwiwowinsa wato yayi mutuwa irinta manƴan mazaje.
Ai kuwa da mutuwar Wusam ba'a ɗau lokaci ba aljani Hasamul-Sawaz ya bayyana a cikin wannan kogo yana jinjinawa Kabshiya bisa ƙoƙarinta wajen wannan aiki. Hasamul-Sawaz ya sake durƙusawa ta haye bayansa suka sake tafiya cikin wannan ƙaton kogo na ƙarƙashin ƙasa, inda wannan ƙatuwar ƙwalba take.
Bisa mamaki sai gimbiya Kabshiya tayi arba da jini ɗan kaɗan a cikin wannan ƙwalba, kuma abin mamaki shi ne babu ta inda za'a iya zuba wannan jini. Ƙwalbar daga sama har ƙasa a sumulmule take, babu ko alamun ƙofa wacce za'ai amfani da ita wajen saka wani abu a cikin wannan ƙwalba.
"Daga yau an buɗe wannan ƙwalba kenan, na rubuta sunanki da sunan Kuffuru a matsayin waɗanda zasuna zuba jini a cikin wannan ƙwalba. Daga yau duk wani jinin Samudul Ansari dake ko Kuffuru ya kashe nan jininsu zai na zuwa yana taruwa, har wannan ƙwalba ta gama. Ki koma cikin wannan kogo kici gaba da renon Kuffuru har ya girma sannan ki koya masa yaƙi sosai, daga yau nikam zanyi bankwana dake. Bazan sake bayyana ba sai Kuffuru ya girma. Ku ci gaba da kashe ƴaƴan Samudul Ansari iyakar iyawarku. Lallai akwai alamun zaku iya cika burin mai girma Gauhan." inji Hasamul-Sawaz.
*****RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 28: *Bayyanar Djinn*
*
*
✍️✍️✍️ Umar Sangaru ✍️✍️✍️
*
Hasamul-Sawaz na gama faɗin haka, ya sake durƙusawa. Kabshiya ta haye bayansa ya lulluka cikin gajimare. Bai sauƙa a ko'ina ba, sai a cikin wannan ɗan ƙaramin kogo. Yana dira ya yi tsafi, kayayyakin abinci da na buƙatar yau-da-kullum suka bayyana a cikin wannan kogo, har da kuyangin aljanu guda biyu da zasu ɗinga yiwa Kabshiya da jaririnta hidima. Yana gama hakan ya ɓace ɓat.
Daga wannan rana Kabshiya ta ci gaba da rainon Kuffuru a cikin wannan daji, babu inda suke zuwa kuma babu wanda yake zuwa wajensu har tsahon shekaru goma sha-bakwai. Nan ne fa Kuffuru ya girma ya zamo kyakkyawar saurayi na gaban kwatance kuma jarumi sadauki.
Tun yana ɗan shekara bakwai Kabshiya take koya masa dabarun yaƙi da kuma bashi horo mai tsananin wahala, hakan ne yasa ya taso jarumi kuma mara tsoro. Kuffuru na da baiwar jiki mai kyau, domin dogo ne sosai kuma yana da ƙira ta ƙarfi.
Lokacin da ya cika shekaru goma sha-bakwai sai ya fara shiga cikin wannan daji na Djinn yana yiwo farauta da kansa, ba tare da taimakon kowa ba. Wataran a ga ya dawo da gawar damisa, wataran kuma a ga ya dawo da zaki bisa kafaɗarsa. Tun abin na baiwa Kabshiya tsoro har ta daina tsorata kuma ta tsinke da al'amarin wannan ɗa nata.
Wata rana Kuffuru ya fita farauta da sassafe, a wannan rana a dajin Djinn da wani irin yanayi aka tashi mai tsananin hazo. Saboda kaurin wannan hazo mutum ba zai na hango abinda ke nesa sosai ba, dukda haka Kuffuru bai karaya ba ƙara danna kai kawai yake cikin dajin.
Har rana ta fara takewa Kuffuru baiyi arba da ko dabbar daji guda ɗaya ba, al'amarin da yayi matuƙar girgiza shi kenan kuma ya bashi mamaki. Tun tasowarsa a cikin wannan daji na Djinn fiye da shekaru goma sha bai taɓa ganin irin wannan yanayi na hazo ba, kuma bai taɓa fitowa farauta ya kai wannan lokaci baiyi arangama da muggan dabbobi kamar guda goma ba. Nan take ya tabbatar da cewa lallai akwai abinda ke faruwa a cikin wannan daji.
Saboda haka ƙara dannawa kawai yake yi, cikin dajin hannunsa na riƙe da takobinsa. Har azahar ta kusa Kuffuru bai ga komai ba kuma baiji motsin komai ba, lamarin da yasa ya haƙura da farautar kenan ya juya da baya domin komawa cikin kogon da suke rayuwa.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani. Ya ji wata irin iska mai tsananin ƙarfi ta fara kaɗawa a cikin dajin, kai kace guguwa ce saboda tsananin ƙarfin gudunta da kuma kaurinta. Iska ta taso daga gabashin dajin ta yiwo yamma gadan-gadan, tana tafe tana turmuza ƙasa ƙura na tashi. Nan fa hankalin bishiyoyi da duwatsun wannan daji ya tashi, ganƴaƴe suka rinka zubowa tamkar takardu. Duwatsu suka kama girgiza kamar zasu tashi sama. Kuffuru ya tsaya ƙyam yana ganin ikon Allah, kuma yana jira yaga wanne abu ne wanda ya haddasa wannan gagarumar guguwa mai ban tsoro.
Yana tsaye wannan guguwa ta ƙaraso inda yake, yaji tamkar za'a ɗauke shi ayi jifa dashi saboda ƙarfin iskar. Kuffuru ya dake yaƙi motsawa har wannan guguwa ta wuce shi, ta sake afkawa cikin wannan daji.
Wucewar wannan guguwa keda wuya, duwatsun wannan daji suka fara tashi suna lulluƙawa cikin gajimare. Kuffuru ya goge idanunsa da kyau don ya tabbatar da cewa abinda yake gani ba mafarki bane, ya za'ayi ace dutse ya ɓuɓɓugo tun daga ƙarƙashin ƙasa ya tashi sama yana yawo a cikin iska, ai wannan babban al'amari ne. Aƙalla sai da duwatsu guda arba'in manƴa-manƴa suka haɗu a sama suka yiwa wannan daji inuwa, sannan wata irin farar wuta tayi feshi daga ƙarƙashin ƙasa ta doki waɗannan duwatsu, nan take suka fara narkewa suna motsewa a waje guda. Kai kace auduga ce aka jefa a cikin wuta.
Kusan rabin sa'a waɗannan duwatsu suka ɗauka suna narkewa a sama, ba tare da sun zubo kan Kuffuru ba. Sannan suka soma haɗewa a waje guda, suna bayar da wata siffa ta wata halitta mai ban al'ajabi. Ruwan duwatsun na gama haɗuwa aka kwararo wata tsawa mai ban tsoro, wacce tasa Kuffuru durƙushewa bisa gwiwowinsa gami da rufe idanunsa da kunnuwansa.
Bayan ƴan daƙiƙu ya bude idanun nasa, inda yai arba da wata irin jibgegiyar halitta tsaye a gabansa ta ƙura masa idanu.
Gaba ɗaya jikin wannan halitta dutse ne tamkar da duwatsu aka halicci jikinta. Surar tafi kama da jikin namijin-aljani mai tsananin ban tsoro.
Aljanin ya kasance mai tsananin tsawo da kauri, domin Kuffuru baya ganin fuskarsa face ya ɗaga kansa sama. Idanuwansa kuma hasken wuta ne keci a cikinsu, sunyi jajawur. Kai a taƙaice dai yadda za'a iya gane siffar wannan aljani ita ce; gaba ɗaya jikinsa da dutse aka halicce shi, sannan kuma idanuwansa wuta ce keci a cikinsu.
"Suna na Djinn!" inji wannan aljani cikin wata murya wacce sauraron ƙarar-aradu yafi ta sauƙi. "Wannan daji nawa ne, duk abinda zai shigo ko kuma ya fita daga cikinsa sai da sanina. Ya kai wannan saurayi kayi sani ni ne wanda ya baku muhalli kuka zauna a cikin wannan daji har tsahon wannan lokaci. Ba don na amince muku da tuni aljanu sun jima da shanƴe jininku, duk farautar da kaga kake yi wannan daji, muna kallonka. Ka san meyasa muka yi muku wannan sutura ta wannan tsahon lokaci?" Djinn ya tambayi Kuffuru.
Kuffuru ya girgiza masa kai alamun bai sani ba.
Djinn ya tuntsire da mahauciyar dariya ya ce, "Asalin suna na shine BUƘALSHIYU DJINN, asalina ni ɗan daular Irashnur kafun sarki Samudul Ansari ya yaƙe mu. Tun da sarki Samudul Ansari ya ci ƙasarmu da yaƙi ya kamoni ya kawoni wannan daji, ban san dalilin da yasa ya kawoni wannan daji ba, sai bayan mutuwarsa. Amfanina shi ne hana mutane wucewa izuwa inda kogon tsafinsa yake, nafi shekaru arba'in ina tsaron wannan hanƴa. Tsahon wannan lokaci na kashe jarumai da bokaye aƙalla guda dubu ashirin. Ya kai wannan saurayi kayi sani cewa na gaji da bautar banza wacce bata da amfani, babu yadda za'ayi na kuɓuta daga wannan aiki da sarki Samudul Ansari ya sakani face shi da kansa ya kwance ni. A halin yanzu ya riga ya mutu amma ruhinsa na nan a raye, duk wanda ya mallaki wannan ruhi na Samudul Ansari zai iya kwance ni daga wannan bauta.
"Ya kai wannan saurayi nayi bincike a halwar tsafi kuma naga cewa bayan ƴaƴan Samudul Ansari akwai alamun kaima zaka iya gadan wannan ruhi, hakan ne yasa na baka mafaka a cikin wannan daji, kayi ta rayuwa har tsahon shekaru goma sha-bakwai. Shin ka san wanda yake ceton rayuwar mahaifiyarka, lokacin da kura da zakanƴa suka kawo mata hari? Ni ne!"
Kuffuru ya dubi Buƙalshiyu Djinn cikin tsananin mamaki ya ce, "Waye ne SAMUDUL ANSARI? Tsahon zamana a cikin wannan daji, ban taɓa jin sunansa ba. Mahaifiyata bata taɓa kawo min labari irin wannan ba."
Aljani Buƙalshiyu Djinn ya sake bushewa da dariya ya ce, "Ba za ka san wayene sarki Samudul Ansari ba face an baka hikayarsa gaba ɗaya, hatta mahaifiyarka bata san wane ne shi ba. Mutum ɗaya ne yake da cikakkiyar hikayar, kuma ba wani bane face tsoho Samazan dake rayuwa a birnin Hindu cikin kogon dutse. Ya kai wannan saurayi, ina so mu ƙulla yarjejeniya da kai, zan taimaka maka ka mallaki ruhin Samudul Ansari kai kuma zaka taimaka min ka kwance ƙullin da yai min na tsaro a wannan daji. Shin ka amince da wannan yarjejeniya?"
Kuffuru ya sake duban Buƙalshiyu Djinn ya ce, "Wanne irin ƙulli ne wanda aka yi maka a wannan daji? Idan na amince da yarjejeniyar, mene ne sakamakona?"
Djinn ya yi ajiyar numfashi yace, "Wani sashe daga cikin jinin zuciyata aka ɗauka aka ƙulla wani sihiri dashi sannan aka binne sihirin a cikin RIJIYAR ZARSHÉN. Wannan rijiya ta Zarshén a cikin wannan daji take, cikin wani ƙaton kogo dake ƙarƙashin ƙasa babu mai sanin inda wannan kogo yake face wanda ruhin Samudul Ansari ya shiga jikinsa. Sakamakon da zaka samu bayan ka kuɓutar dani shi ne, zan baka kyautar bayi masu irin halittata guda ɗari hudu da arba'in. Ya kai wannan saurayi kayi sani cewa jikina da zallar dutse aka yi shi, babu kaifi ko tsini da zaiyi tasiri akaina. A tarihin ƙabilata ba'a taɓa jiwa ɗan-uwanmu rauni ba, jinin mu bai taɓa zuba ƙasa ba. Indai kaga anyi nasara akanmu wato an kashe mu, to sai dai ayi amfani da ƙarfin sihirin tsafi. Sunan wannan ƙabila tamu shi ne Buƙal."
Kuffuru ya cika da tsananin mamaki ya ce, "Waɗanne matakai zan bi wajen ganin na mallaki ruhin Samudul Ansari?"
Djinn ya yi murmushi ya ce, "Matakan guda uku ne; na farko dole sai ka cika ƙwalbar da sarki Gauhan ya bari da zallar jinin ƴaƴan Samudul Ansari. Babu yadda za'ayi ka iya wannan aiki face ka zamo babban sarki mai mulkin babbar ƙasa, yadda zakana amfani da ƙarfin ikonka wajen sawa ana kama waɗannan mutane kuma ana kashe su. Mataki na biyu shi ne dole ne ka kashe mutumin da ruhin Samudul Ansari ya zaɓa a matsayin magajinsa, a halin yanzu ina tunanin Hasanul Jalwar shi ne wanda wannan ruhi ya zaɓa. Mataki na uku dole ne ka mallaki takobin SAIFUL SHIRADU ta sarki Samudul Ansari. Wannan takobi ma a halin yanzu tana hannun Hasanul Jalwar, babu yadda za'ayi kayi nasara a kansa face ka mallaki wannan takobi."
Kuffuru ya dubi Djinn cikin mamaki da ruɗewa ya ce, "Ta ya ya kake tunanin zan zamo sarki, alhalin bani da kowa bani da komai face mahaifiyata? Rayuwata gaba ɗaya a cikin wannan daji ta ƙare, ya ya za'ayi rana ɗaya a ce na zamo sarki? Wane ne Hasanul Jalwar kuma a ina yake? Ta ya zan iya gane shi balle har na kashe shi?"
Buƙalshiyu Djinn ya yi dariya ya ce, "Waɗannan duk abubuwa ne masu sauƙi, kayi sani cewa shan ruwa yafi wannan aiki wahala a wajena. Ni ne fa Shiyu Djinn abin alfahari a daular Irashnur. Ka zaɓa tsakanin birnin Kufa, Ƙisra, Sin, Rum da Hadriyan wanne birni kake so ka mulka?"
Kuffuru ya haɗe fuska ya ce, "Duk cikin waɗannan birane ina na sani? Ka zaɓa min da kanka dai, kuma a inda kake ganin za'afi samun ƴaƴan Samudul Ansari da yawa." Djinn ya yi murmushin jin daɗi ya ce, "Birnin Kufa shi ne inda yafi dacewa. Domin a ƙarƙashin birnin akwai manƴan biranai har guda uku, kuma akwai ƙauyuka babu adadi. Ƴaƴan Samudul Ansaru babu abinda suka sani a rayuwarsu in banda noma da kiwo, a yankin birnin Kufa akwai albarkar ƙasa sosai kuma tunda aka gama wannan yaƙi nake jin labarin ana ganin ire-irensu a can."
Kuffuru ya ce, "Shi kenan, na amince. Amma bari naje na faɗawa mahaifiyata halin da ake ciki." Djinn ya yi dariya ya ce, "Mahaifiyarka ta san komai domin tana jin duk abinda muke tattaunawa, kada ka manta wannan daji nawa ne!"
Daga wannan lokaci aljani Buƙalshiyu Djinn ya ɗauki Kuffuru da mahaifiyarsa Kabshiya suka je birnin Kufa suka sami sarkin garin na zaune bisa karagarsa ya harɗe.
Aljani Buƙalshiyu Djinn na bayyana dukkan jama'ar dake fadar suka zube ƙasa suna ta karkarwa, wasu suka fara fitsari a wando saboda tsananin razana da firgita saboda kallon halittar sa. Sarkin garin yayi ta maza ya

Please Login or Register in order to submit comment