Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ambata, amma sai naga jin
tarihinsu a wannan lokaci ba shi da wani amfani. Yana da kyau ace sai ka gama cika ka
zamo namijin duniya sannan ka ji haɗarurrukan waɗannan sarakuna ga rayuwarka da
yadda zaka tarwatsa su."
Aymanul Faris ya cika da tsananin mamaki, shin wanne irin haɗari waɗannan sarakuna
suke da a fannin rayuwarsa? Amsar da ya rasa kenan.
*******************Ruhin Jarumtaka!
*
Babi na 15: *Marganu da Jaanu*
*
*
Umar Sangaru
*
Aljani Gulzab ne a cikin giza-gizai keta faman sharara uban gudu, kai kace tauraruwa ce
mai wutsiya. Yarima Marganu da gimbiya Jaanu na zaune bisa gadon bayansa. Tun da
suka fara tafiyar, gimbiya Jaanu ta haɗe fuska, ba ta sake kallon inda yarima Marganu
ke zaune ba. Shi kuma yarima Marganu zuciyarsa ce keta tafarfasa kamar zata ƙone,
idanuwansa sun kaɗa sunyi jawur, zaka ka iya cewa yarima Marganu bai taɓa fusata a
rayuwarsa irinta wannan lokaci ba. "Yanzu ace duk wahalar da na sha akan hanƴar
zuwa dajin Marsas ta tashi a banza? Mene ne na yiwa wannar yarinƴa harda zata tsane
ni haka? Na sayar da rayuwata na shigo cikin dazuzzuka masu haɗari na sha baƙar
wahala amma a ƙarshe ace na tashi da tutar babu? Shin mene ne abinda ke tsakaninta
da Aymanul Faris?" Haka dai Marganu yayi ta yiwa kansa tambayoyi ba tare da ya sami
amsarsu ba, har suka shafe tafiyar sa'a huɗu cur.
Koda yarima Marganu ya fuskanci cewa gimbiya Jaanu ba zata bashi fuska ba, sai ya
matsa kusa da ita ya yi murmushin ƙarfin hali ya ce, "Ya ke wannan gimbiya, ina son
muyi magana ta nutsuwa da fahimta..." Kafin ya rufe bakinsa gimbiya Jaanu ta juyo ta
kalle shi, fuskarta babu yabo ba fallasa. Marganu ya sake yin murmushi gami da gyaran
murya ya ci gaba, "Shin akwai laifin da na taɓa yi miki ne? Kiyi sani cewa tun ina yaro
ɗan shekaru tara, bokan garinmu yake nuna min hotunanki a madubin tsafi, tun daga
lokacin na kamu da tsananin ƙaunarki. Yadda nake ƙaunarki gani nake babu abinda ba
zan iya yi ba, idan na rasa ki. Meyasa ko sau ɗaya ba ki taɓa nuna min soyayya ba?
Mahaifina da mahaifinki abokai ne waɗanda suka taso tun daga yarinta, kuma
dukkanninsu suna so su haɗa aure a tsakaninmu? Me yasa ba zaki ƙaunace ni kamar
yadda nake ƙaunarki ba?" Koda gimbiya Jaanu taji bayanan yarima Marganu sai ta
turɓune fuska ta ce, "Ya kai yarima, ina so sanar da kai cewa shi SO gamon jini ne. SO
babu ruwansa da kyau, matsayi, shekaru ko wanin waɗannan. Kayi haƙuri Allah bai saka
min sonka a cikin zuciyata ba, ni kaina tausayinka nake ji, saboda yadda kake wahala
akan neman soyayyata. Shin babu waɗanda suka fini kyawu ne da matsayi a birninku?
Kayi sani cewa tuni wani ya gama mallakar zuciyata, kayi haƙuri ka daina sona, domin
ba zaka taɓa mallakata ba."
Yarima Marganu ya ji tamkar an soka masa kibiya mai dafi a tsakiyar zuciyarsa, fuskarsa
ta fara gatsinewa, hawaye mai zafi ya fara ƙwaranyowa daga cikin idanunsa saboda
tsananin fusata, baƙin ciki da takaicin maganganun da gimbiya Jaanu ta faɗa masa. Ya
ɗago kansa ya daka mata wani wawan harara irin wanda ke firgita ƙaramin jarumi ya
gudu daga filin daga, jikin gimbiya Jaanu ya fara ƙyarmar razana. Marganu ya ɗaga
hannunsa da niyyar ya shara mata mari, koda hannunsa ya kusa taɓa kuncinta sai ya
kasa marinta ya fara kakkarwa, idanunsa suka ci gaba da zubar da hawaye. Gimbiya
Jaanu ta haɗe fuska, domin babu abinda ta tsana a rayuwarta kamar mutum ya zabga
mata mari a fuska, a baya munga lokacin da jaruma Riya ta shara mata sai da tayi
haɓo. Wurin zamanta kawai ta koma ta zauna, fuskarta a murtuƙe kamar bata taɓa
dariya ba.
Yarima Marganu ya zaro takobinsa yazo gabanta ya tsaya, cikin rashin tsoro da tsantsar
kafiya gimbiya Jaanu ta ɗago kanta ta dube shi. Marganu ya durƙusa a gabanta bisa
gwiwowinsa ya ce, "Gimbiya! Ki faɗa min gaskiya, kina sona ko kuma ba kya sona?"
Gimbiya Jaanu ta kalle shi cikin rashin tsoro ta ce, "Akan wanne dalili zan ƙi ka? Kaifa
tamkar ɗan uwa kake a wajena." Maimakon zuciyar Marganu tayi fari, wani baƙin ciki ne
ya sake lulluɓe shi. "Ki amsa min tambayata, kai tsaye mana. Kina sona ko a'a?" Inji
yarima Marganu. Shuru kawai gimbiya Jaanu tayi har tsahon ɗan lokaci, Marganu ya gaji
da jira ya shafa kaifin takobinsa ya ce, "Idan kina sona kin tsira! Idan kuma ba ki aureni
ba, take zan kashe kaina a wannan wuri sannan kema na kasheki!!!" Cikin tsawa.
Hantar cikin gimbiya Jaanu ta kaɗa don ta tabbatar da cewa yarima Marganu da gaske
yake, ko kaɗan babu alamun wasa a cikin maganganunsa. Gimbiya Jaanu ta dube shi a
fusace tana shirin cewa bata sonsa, kwatsam sai tunanin Aymanul Faris ya faɗo mata a
rai. Gimbiya ta ji babu abinda take so a duniya kamar sake kallon fuskar Aymanul Faris.
Marganu ya fara ƙyarma yana shirin fille kanta, ya ji ta fashe da kuka. Al'amarin da ya yi
matuƙar bashi mamaki kenan.
"Tabbas na fuskanci ba ƙaunata kake ba! Ya za'ayi ka kashe wanda kake so sannan ka
kashe kanka? Wannan wacce irin soyayya ce? Ka taɓa ganin an kamu da son mutum
farat ɗaya? Kayi haƙuri sai mun koma birninmu zan faɗa maka hukuncin da na yanke
akan soyayyarka!" Inji gimbiya Jaanu hawaye na zuba bisa kyawawan kumatunta. Wata
irin kunƴa ta rufe yarima Marganu ya sunkuyar da kansa ƙasa, ya ce, "Kiyi haƙuri ya
masoyiyata. Tabbas soyayya ce ta rufe min idanu. Da ace na rasa ki gwanda ace na
mutu don hakan shine zai fiye min sauƙi. Tabbas nayi alƙawari daga yau ba zan sake
kawo miki batun soyayya ba, har mu isa birninku domin naji amsar da zaki bani wacce
nake fatan ta kasance mai kyau." Gimbiya Jaanu ta share hawayen idanunta, ta yiwa
Marganu mai taushi a karon farko. Wani irin farin ciki ya lulluɓe Marganu yaji tamkar
kansa zai fashe.
Haka dai suka ci gaba da tafiya har tsahon kwanaki goma sha takwas, a cikin
waɗannan kwanaki yarima Marganu ya zamo abokin gimbiya Jaanu na kusa. Sukan
shafe yini guda suna hira, yarima Marganu yaji hankalinsa ya kwanta sosai domin gani
yake tamkar gimbiya ta amince dashi ne, an gama.
A ranar da kwana na goma sha-takwas ta cika ne, aljani Gulzab ya dira a bakin ƙofar
birnin Damashkar. A bakin ƙofar garin su yarima Marganu suka yi arba da sarki Ayubul
Zairiy da sarki Ratanam, a wannan lokaci ne yarima Marganu ya ƙarewa sarki Ayubul
Zairiy. Ayubul Zairiy dogo ne, kakkaura mai murɗaɗɗen jiki. Murmushi kawai yarima
Marganu yayi domin yaga jikin maza, sarki Kuffuru. Suna sauƙowa gimbiya Jaanu ta
ruga da gudu wajen mahaifinta ta rungume shi, ya ƙanƙameta a ƙirjinsa yana rintse
idanunsa hawayen farin ciki na zuba. "Lale marhaban da dawowar ƴata, da fatan dai
basu yi miki wani abun ba?" Inji sarki Ayubul Zairiy. Gimbiya Jaanu ta janƴe jikinta daga
nasa ta ce, "Ba abinda suka yi min, wata ƙasaitacciyar fada ma suka kaini." Ayubul Zairiy
ya cika da tsananin mamakin wannan abu. Maimakon yarima Marganu ya ƙarasa inda
mahaifinsa ke tsaye, a inda yake tsaye anan ya tsaya kikam kamar gunki, yana kallon
gimbiya Jaanu domin yaji amsar da zata bashi amma shuru.
Sarki Ratanam ya tako da ƙafafunsa yazo inda yarima Marganu yake suka rungume juna,
yana mai nuna tsananin farin cikinsa bisa dawowar yarima Marganu. "Ɗana haƙiƙa ka
cika sadauki kuma jarumi abin ƙwatance domin kayi abinda manƴan jarumai ma daƙyar
suyi. Ina so ka bani labarin tafiyarka tun daga sa'adda muka rabu da kai." Marganu yayi
ajiyar zuciya ya dubi inda gimbiya Jaanu ke tsaye sannan ya sake duban mahafinsa ya
fara bashi labarin tafiyarsa tun daga farko har ƙarshe.
Alamun tsoro da razana suka bayyana ƙarara akan fuskar sarki Ratanam ya ce, "Baka da
hankali ne? Meyasa ka yarda da sharaɗin sarki Kuffuru na kamo su Aymanul Faris da
sarkin ɓarayi? Shin ka samu nasarar kamo nasarar kamo koda ɗaya daga cikinsu? Ka
aikata babban kuskure da ka sare kan gunki Barzasa, na rantse da karagar mulkina
wannan sarauniya bazata daina farautarka a duniya ba. Tabbas kana buƙatar tsari, don
haka yi maza kazo mu koma birninmu domin muje wurin boka Hubbazu ya baka
maganin tsari da sharrin maƙiya." Sarki Ratanam na gama faɗin haka ya fizgi hannun
yarima Marganu domin ya ja shi su tafi, amma Marganu ya turje yaƙi tafiya yana kallon
gimbiya. Sarki Ratanam yayi-yayi amma ina, Marganu ya ƙi tafiya.
Sarki Ayubul Zairiy yazo inda suke tsaye ya dubi yarima Marganu ya ce, "Gaisheka
babban jarumi haƙiƙa kayi mini babban aiki, wanda bansan da me zan saka maka ba..."
Yarima Marganu ya haɗe gira ya ce, "Ban gane baka san dame zaka saka min ba? Don
me nayi wannar tafiyar?" Sarki Ayubul Zairiy ya yi murmushi ya ce, "Zan yi magana da
gimbiya kuma zan shawo kanta, zata amince kada ka damu." Yarima Marganu ya ce,
"Ai amincewa kam, ta zama dole. Idan ba haka kuwa ba zan faɗi me zanyi ba..." Yana
gama faɗin haka ya nufi inda sarki Ratanam ke tsaye suka rankaya bisa dawakai, suka
fice daga birnin.
Sarki Ayubul Zairiy ya ja gimbiya Jaanu izuwa gidan sarautarsa, yana tayi mata
tambayoyi akan abubuwan da suka faru a yayin da take hannun su Aymanul Faris.
Gimbiya Jaanu tayi ta ɓoye masa, bata bayyana haƙikanin abinda ya faru ba. Hankalin
sarki Ayubul Zairiy ya kwanta, ya saki ransa. Daga wannan rana gimbiya Jaanu ta nemi
kafintan da yafi kowa iya sassaƙa a birnin Damashkar ta bayyana siffofin Aymanul Faris,
ya sassaƙa gunki mai irin kamannin Aymanul Faris kai kace Aymanul Faris ɗinne. Da
zallar ɗanyen dutsen yaƙutu mai tsada akayi amfani wajen ƙera wannan gunki. A
sirrance gimbiya Jaanu ta sa aka rubuta mata sunan Aymanul Faris a ƙwarin gadon
bayanta, da dara-daran rubutu. Anyi rubutun ne da baƙar tawada kuma wanda yayi
gwani sosai, ba ƙaramin kyau suka yi ba a gadon bayan nata.
A duk lokacin da sarki Ayubul Zairiy ya kawowa gimbiya Jaanu batun yarima Marganu
sai yaga ranta ya ɓaci, ta tashi ta fice daga inda yake batare da tayi masa sallama ba.
Hakan ne ya ɗugunzuma hankalin sarkin domin ya tabbatar da cewa indai bai aurawa
yarima Marganu gimbiya ba a wannan karon, alaƙar dake tsakaninsa da sarki Ratanam
zata rushe. Bisa wannan dalili ne ya fara tunanin me ya kamata yayi?
***
Lokacin da sarki Ratanam tare da ɗansa yarima Marganu suka fito daga cikin birnin
Damashkar sai suka yanki daji suka yi ta gudu kamar zasu tashi sama, kowa ka kalla a
cikinsu zaka ga fuskarsa a murtuƙe. Shi dai sarki Ratanam abinda yasa ya murtuƙe
fuskarsa shi ne, meyasa yarima Marganu zai amince da sharuɗɗan sarki Kuffuru, ba tare
da yayi tunani mai kyau ba. Shi kuma yarima Marganu haushi kawai yake ji akan
gimbiya Jaanu ta ƙi ta bashi amsar matsayinsa a cikin zuciyarta. Har suka shafe tafiya
mai tsahon gaske ba tare da ɗayansu yace uffan ba.
Bayan shuɗewar waɗansu sa'o'i suka fara hango wani tafkeken daji mai yawan dogayen
duwatsu, idan ba'a manta ba a wannan daji ne muka ga sarki Kuffuru tare da ƴarsa a
kwanakin baya. Sarki Ratanam da ɗansa yarima Marganu suna zuwa suka afka cikin
dajin, ba tare da shakkar komai ba. Bayan shafe doguwar tafiya suka iso bakin wannan
ƙaton kogon dutse wanda aka rufe da ƙatuwar ƙofa ta sihiri, sarki Ratanam yaje ya soka
ɗan yatsansa a cikin waɗannan jajayen rubutu dake jikin wannan ƙofa. Sararin samaniya
ta fara kaɗawa, ƙara mai cika dodon kunne ta cika dajin, iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa
tana saka ganƴaƴen bishiyoyi suna rangaji. Sarki Ratanam da ɗansa yarima Marganu ko
gezau basuyi ba har komai ya lafa, wannan ƙatuwar ƙofa ta buɗe.
Ratanam da ɗansa yarima Marganu suka shige cikin kogon, inda su ma suka tsinci
kansu a cikin wannan makekiyar fada. Ko'ina ka duba kuyangi ne keta ayyuka, suka
ratsa ta tsakiyar kuyangin suka nufi karagar boka Hubbazu. A wannan karon boka
Hubbazu bai taso ba domin taryarsu, jira yayi har suka ƙarasa inda yake. Maimakon ya
zaunar dasu kan karagarsa sai ya nuna musu wasu kujeru guda uku dake gefen karagar
suka zazzauna.
Boka Hubbazu ya yi gyaran murya ya ce, "Lale marhaban da zuwanku! Na san abinda ke
tafe da ku kuma nasan maganin matsalarku. Ya ku waɗannan baƙi nawa kunzo ne
domin na yi muku maganin tsari akan abokan gabar yarima, hakane?" Sarki Ratanam ya
gyaɗa kai. Boka Hubbazu ya sake cewa, "Haƙiƙa kai Marganu, ka tsokano tsuliyar dodo.
Sarauniya Rauziyya gagarumar matsafiya ce, zan iya cewa in banda ni da waɗansu
mutane guda biyu babu wanda ya fita ƙarfin sihiri a duniya. Gunki Barzasa ba gunki
bane, wani taƙadarin shaiɗanin aljani ne. Lokacin da ka fille kan gunkin wannan aljani
bayanan, domin baya zuwa wannan birni face lokacin bauta yayi. A yanzu haka, yaje
wannan birni yaga dukkanin ɓarnar da kayi kuma yayi baƙin ciki matuƙa musamman ma
kashe sadauki Jautaru da kayi, domin shi wannan Jautarun shi ne mai yiwo farautar
mutanen da za'a yankawa gunki Barzasa. Kai shi ne ma yake fille kan mutane a cikin
ƙoƙon wannan gunki. Ina so kuyi duba izuwa cikin wannan madubin tsafi nawa domin
ganin tattaunawar da su sarauniya Rauziyya suka yi akan yarima Marganu." Boka
Hubbazu ya nuna wani allon tsafi dake rataye a jikin bangon fadar da hannunsa na hagu,
take allon yayi fari ya fara nuna abinda ya faru.
****
Ɗakin taro ne mai faɗin gaske. A tsakiyar ɗakin an ajiye wani ƙaton teburi wanda aka
kewaye da kujeru. Zaune akan waɗannan kujeru waɗansu mutane guda uku da aljani
guda ɗaya. Kallon farko yarima Marganu ya yiwa macen dake zaune a tsakiya ya gane
wace ce, ba wata bace illa sarauniya Rauziyya.
Cikin kakkausar murya wannan aljani ya fara jawabi da cewa, "Wannan yaro sunansa
Marganu ɗan sarki Ratanam ne dake birnin Hirtoliya. Wannan yaro yana da tsananin
sa'a akan wannan tafiya da yayi shiyasa har ma ya ratso ta cikin wannan gari namu har
yayi nasara. Zanyi tsafi na baku taswirarsa wacce a duk inda yake a faɗin duniya, zata
nuna. Umarnina shi ne a kamo mana wannan yaro domin mu kaishi kurkukun dake
saman wannan tsauni namu." Sarauniya Rauziyya ta cije harshe ta ce, "Ya maigirma, mai
iko ka bamu umarnin fille kansa mana kawai..." Aljanin ya bushe da dariya ya ce, "Ni na
san abinda ku baku sani ba..." Yana gama faɗin haka yayi tsafi waɗansu fararen takardu
suka bayyana, sannu-a-hankali zane-zanen taswira ta fara bayyana akan kowacce daga
cikin waɗannan takardu.
Wani irin farin haske mai kashe idanu ya bayyana akan taswirar daidai inda birnin
Damashkar take. Aljanin ya sake bushewa da dariya ya dube su ya ce, "Kun wannan
farin hasken? Shi ne inda yarima Marganu yake. Babu inda zai shiga a duniya bamu
laluɓo shi ba, tabbas ina son a kamo mana shi a raye domin ya fuskanci hukunci..."
Sarauniya Rauziyya ta yi murmushin mugunta ta ce, "Ya shugabana. Wannan aiki da ka
bamu shan ruwa yafi shi wahala a wajenmu, ka bamu sati guda rak, da izininka zamu
kamo shi."
****
Boka Hubbazu ya sake nuna allon tsafin da hannunsa take hoton komai ya ɗauke. Ya
dubi su sarki Ratanam ya ce, "To kun ga irin shirin da suke yi akanku. Babu yadda za'ayi
yarima Marganu ya iya ɓacewa daga cikin wannan taswira. A duk inda yake a faɗin
duniya waɗannan arnan daji, ba za su daina farautarsa ba." Boka Hubbazu ya yi shuru
yana kallon yarima Marganu. A firgice sarki Ratanam ya ce, "Ya kai wannan boka shin
babu wani maganin tsari da zaka bashi wanda zai kare shi daga sharrin waɗannan
arnan daji?" Boka Hubbazu ya yi murmushi ya ce, "Akwai mana. Wata laya ce zan bashi
ya ɗaura a wuyansa, in dai yana tare da ita babu wani tsautsayi da zai same shi. Haka
kuma ba zai taɓa haduwa da waɗannan arnan daji ba, a kullum sun ɗinga saɓani
kenan." Boka Hubbazu na zuwa nan a zancensa ya fiddo wata laya daga cikin jakar
tsafinsa ya miƙawa ita yarima Marganu, Marganu ya karɓa sannan ya ɗaurata a
wuyansa. Nan dai suka yi sallama da boka Hubbazu suka fito daga cikin wannan kogon
dutse, suka kama hanƴar tafiya izuwa birnin su - birnin Hirtoliya.
*****RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 16: *Dakarun-masifa*
*
*
Umar Sangaru
*
A can birnin Kufa kuwa, duk abinda ya faru tsakanin yarima Marganu da su sarkin ɓarayi
Barban sarki Kuffuru na gani a cikin madubin tsafinsa. Wani abin mamaki shi ne baya
ganin siffofin Barban da aljani Ranganu sosai, yana ganinsu ne dishi-dishi. Tuni ya cika
da tsananin baƙin ciki bisa ganin cewa yarima Marganu baiyi wani yunƙuri na kama su
Aymanul Faris da Barban ba, zuciyarsa ta kama tafarfasa, babu abinda sarki Kuffuru ya
tsana a sha'anin mulkinsa kamar ya bada umurni a ƙi bi. Cikin tsananin fusata ya fice
daga cikin gidan sarautarsa, ya tafa hannayensa wannan basamuden aljani ya sake
bayyana. Aljanin ya ɗauke shi ya kaishi izuwa kurkukun mutuwa.
Suna dira sarki Kuffuru ya wuce kai tsaye izuwa bakin kurkukun, waɗannan dakaru guda
bakwai suka tare shi suka yi masa barka da zuwa. Zaka iya cewa waɗannan dakaru
guda bakwai su ne shuwagabannin wannan kurkuku, babu mai shiga ko fita ba tare da
saninsu ba. Gefe guda sarki Kuffuru ya ja su, ya ce, "Akwai fursunan da nake so a kamo
min, kuma bana so a tura masa ƙananun dakaru. Dakarun-masifa nake so a tura su
kamo shi. Haka kuma idan aka kamo shi, kai tsaye nakeso a kaishi ɗakin duhu domin
Bandaru ya koya masa hankali, munyi yarjejeniya da shi amma ya kasa cika yarjejeniyar.
Wannan fursuna ba wani bane illa yarima Marganu wanda muka zo dashi wannan
kurkuku a kwanakin baya sa'adda muka ɗauki wannar ƴar ƙabilar Banu Kuyuru. Ya zo ya
cika min baki akan zai iya kamo su Aymanul Faris amma ba abinda yayi, ya dawo hannu
rabbana. Maimakon ma yazo ya bani haƙuri baizo ba, don haka yanzu-yanzu nake so a
tura masa dakarun-masifa su kamo shi..." Sarki Kuffuru na gama faɗin haka ya juya inda
wannan aljani nasa ke jiransa, ya hau sannan aljanin ya lulluka da shi cikin gajimare suka
koma.
Kai tsaye waɗannan dakaru guda bakwai suka wuce cikin gidan kurkukun, suka nufi
wani ɓangare dabam. Bayan tafiya ta kimanin rabin sa'a, suka iso wani ƙaton ɗaki da
aka garƙame da makulli. Ɗaya daga cikinsu ya zaro mabuɗi daga cikin aljihunsa ya
buɗe ƙofar ɗakin, suka shige ciki gaba ɗayansu.
Waɗansu irin samudawan ƙarti ne guda arba'in da huɗu ke zazzaune a cikin wannan
ɗaki, idan mutum ya lura zaiga an ɗaure musu hannaye da ankwa. Dukkansu babu
wanda ke sanƴe da riga a jikinsa, hakan ne ya bayyana murɗaɗɗen jikinsu wanda zaiyi
kunnen-doki da na sarki Kuffuru. Idanuwan waɗannan dakaru jajazur ne, kai da gani ka
san babu imani koda na kwayar zarra. Jikinsu kuma a mummurɗe yake, sun tara ƙwanji
kamar bishiyar kuka. Kai a tsaya bayyana siffofin waɗannan dakaru sai a ɓata lokaci,
amma kana ganinsu kaga sadaukai, jarumai fusatattu.
Ɗaya daga cikin dakaru guda bakwai ɗinnan ya fara jawabi da cewa, "Barka da wannan
lokaci, dakarun-masifa. Kuyi sani cewa kun shafe tsahon lokaci kuna jiran akawo muku
aiki amma aikin bai samu ba, shiyasa ma muka ɗaɗɗaure ku da ankwa don kada ku
fusata ku afka cikin kurkukun nan. A wannan karon ina tabbatar muku cewa an samu
fursunan da za'a kamo, ba wani bane face Marganu ɗan sarki Ratanam. Muna so ku
kamo mana shi a raye, nan da cikar kwanaki uku. Saboda haka yanzu zamu
kwakkwance ku domin yin wannan aiki." Badakaren na gama faɗin haka, wani ƙato daga
cikin dakarun-masifa ya bushe da mahaukaciyar dariya ya ce, "Har kwanaki uku?
Tabbas sun yi yawa. A yau ɗinnan idan muka isa birnin Hirtoliya zamu kamo wannan
ƙaramin jarumi."
Nan take waɗannan dakaru guda bakwai suka kwakkwance ankwar da aka ɗaɗɗaure
dakarun-masifa, suka fito daga cikin wannan ɗaki. Waɗannan dakaru suka ɗauko
kulaken duka suka rarrabawa dakarun, sannan aka kawo musu dawakai domin yin
wannan tafiya zuwa birnin Hirtoliya. Dakarun-masifa suka yi sallama da waɗannan
dakaru guda bakwai sannan suka kama hanƴar tafiya zuwa birnin Hirtoliya.
Idan ka kalle su daga nesa zaka ga dakaru guda arba'in da huɗu, sanye cikin baƙaƙen
tufafi bisa ingarmun dawaki. Gaba ɗayansu fuskokinsu a rurrufe suke da wani jan ƙyalle,
idanuwansu kaɗai ake kallo.
****
Tun sa'adda yarima Marganu da mahaifinsa suka koma birnin Hirtoliya, sai barci ya
ƙauracewa idanunsa, abinci ya gagara shiga bakinsa har tsahon kwana biyu. Nan take
ya fara ramewa sakamakon yadda yake yini da ƴunwa da kuma yadda yake raba dare
yana kuka bisa rashin samun gimbiya Jaanu, sarki Ratanam bai lura da wannan sauyin
yanayi ba sai a ranar kwana ta biyun. Bisa wannan dalili suka keɓe shi da yarima
Marganu a cikin wani mani'imcin lambu dake bayan gari.
Sarki Ratanam ya dube shi ya ce, "Ya kai ɗana, mene ne abinda yake damunka cikin
kwana biyun nan naga duk ka sauya?" Yarima Marganu yayi ajiyar zuciya ya ce, "Haba
baba, meyasa zaka yi min tambayar da ka san amsarta? Ka sani cewa fa akan gimbiya
na sayar da rayuwata na shiga haɗarurruka waɗanda bansan ƙarshensu ba, amma daga
baya tazo tana ƙoƙarin watsa min ƙasa a ido. Mun yi magana da ita akan zata bani
amsar matsayina a cikin zuciyarta, da zarar mun iso birnin Damashkar amma bata faɗa
min ba. Don haka gobe-goben nan zanyi shiri na tafi izuwa birnin Damashkar domin jin
amsar tambayata, idan ta ƙaunace ni shikenan, idan kuwa taƙi na rantse da Nurutu sai
na kasheta..." Hankalin sarki Ratanam ya ɗugunzuma ya ce, "Yi haƙuri ɗana, tabbas a
wannan karon jikina yana bani cewar zata amince... Na haneka da zuwa birnin
Damashkar a gobe ka jira, na tabbata abokina zai turomin halin da ake ciki." Yarima
Marganu ya ce, "Ba zan iya jira ba baba, kayi haƙuri amma nikam tabbas sai naje birnin
Damashkar kuma sai na aiwatar da abinda nayi niyya." Sarki Ratanam ya tashi ya fice
daga cikin lambun a fusace, saboda ganin cewa yau ɗan da ya haifa yaƙi bin
umarninsa.
Marganu yayi murmushi ya ce a ransa, "Nidai ba abinda zai hanani zuwa birnin
Damashkar domin jin shawarar da gimbiya Jaanu ta yanke akan soyayyata." Yana gama
faɗin haka shima ya tashi ya fice daga cikin lambun. Har dare ya raba yarima Marganu
bai sake zuwa inda sarki Ratanam yake ba, domin gani yake a kowanne lokaci sarkin zai
iya hana shi wannan tafiya.
Kashe gari tunda duƙu-duƙun safiya yarima Marganu ya kimtsa. Ya sanƴa kayan yaƙinsa
sannan ya ratayo jakar guzurinsa, dama ya saka wani bawa nasa ya kimtsa masa doki.
Yarima Marganu ya haye kan wannan doki, ya sanƴa hular ƙarfe ya rufe fuskarsa sannan
ya kaɗa linzamin dokin ya nufi ƙofar ficewa daga gidan sarautar. Har yazo bakin ƙofar
fita sannan yayi arba da sarki Ratanam tsaye cikin tsananin damuwa, ya dube shi ya ce,
"Kana nufin ba zaka bi umarnin da na baka ba kenan?" Yarima Marganu ya yi murmushi
ya ce, "Ba haka bane baba, kawai dai idan na zauna a nan ɗinne baƙin ciki zai iya kashe
ni shiyasa." Batare da ya tsaya jiran amsa daga bakin baban nasa ba, ya fita daga cikin
gidan sarautar ya nufi hanƴar da zata fitar da shi daga gari.
Yarima Marganu na fitowa daga cikin birnin Hirtoliya ya fara tsala azababben gudu a
cikin daji ya tasarwa birnin Damashkar, gudu yake tamkar zai tashi sama. Duk wata
ƙatuwar dabbar daji ko aljanin da yayi arba da shi sai kaga ya canja hanƴa saboda
tsananin kwarjinin yarima Marganu, a haka dai har ya shafe sa'a huɗu cur yana wannan
gudu. A hankali dokinsa ya fara rage sauri, har ya dawo sassarfa, bisa dole yarima
Marganu ya yada zango a cikin wani ƙaton daji a bakin wata ƙorama. Dokin nan yaje
cikin ciyawi dake bakin ƙoramar ya fara kiwo, shikuma yarima Marganu a gindin bishiya
ya zauna, ya fiddo abinci a cikin jakar guzurinsa ya fara ci.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani yarima Marganu ya fara jiwo sukuwar dawakai daga
can nesa, cikin tsananin fusata ya miƙe tsaye ya ƙurawa inda yake jiwo sukuwar
dawakan. Daga nesa ya fara hango mahaya bisa dawakai sanƴe da baƙaƙen tufafi, ba
wai ƙarar sukuwar bace ta ba shi tsoro ba, dakarun da ya hango zazzaune bisa
dawakan sune suka razana shi. Dukda cewa tsakaninsu akwai tazara mai yawan gaske
amma yarima Marganu na ganin girman kowanne daga cikinsu, idan zai iya tunowa a
wuri ɗaya ya taɓa kallon kalar waɗannan dakaru, ba'a ko'ina bane face gidan kurkukun
mutuwa. Yarima Marganu ya zare takobinsa ya tsaya kikam a inda yake, har waɗannan
dakaru suka ƙariso.
Dakaru ne guda arba'in da huɗu, gabza-gabza ne tamkar ragowar mutanen farko. Koda
suka tabbatar da cewa wanda ke tsaye a gabansu shi ne yarima Marganu sai suka
zazzaro kulaken dukansu, suka kewaye shi a tsakiya. Yarima Marganu ya daɗa riƙe
takobinsa ya turje a inda yake tsaye, ya dakawa dakarun nan tsawa ya ce, "Kuyi min
bayanin kanku, kafin na sassare muku kawuna! Idan kun kasance ƴan fashi to ku ajiye
makaman yaƙinku ku miƙa wuya domin nayi muku hukunci. Idan kuwa kun kasance
dakarun sumame to ku kashe kanku gaba ɗaya a gabana domin hakan zai fiye muku
sauƙi." Wataƙila waɗannan dakaru basu da kunne domin tamkar basu ji abinda yarima
Marganu ya faɗa ba.
Ɗaya daga cikinsu ya sauƙo daga kan dokinsa yazo daf da yarima Marganu ya fiddo
wata takarda daga cikin aljihunsa ya fara karanta ta a fili kamar haka:
"Takarda daga shugaban kurkukun mutuwa, sadauki Zayyadu. Ni sadauki Zayyadu na
baiwa waɗannan dakaru nawa umarnin kamo mutum mai bayanai kamar haka: suna:
Marganu. Ƙasar haihuwa: Birnin Hirtoliya. Shekarun haihuwa: goma sha-takwas. Akan
laifi: Karya yarjejeniyar da

Please Login or Register in order to submit comment