Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Ka san waye ce Hushriba?" inji Fairaz. "Inda ace ka san waye ce da ba zaka min wannan kashedin ba. Kuma da ba zaka ga laifina ba akan na kawowa Barban duka ba."
Barban ya ajiye kofin shayin dake hannunsa ya ce, "Har ka gano sunana da sauri haka?" Sarki Fairaz yayi murmushi ya ce, "Babu yadda za'ayi mutum ya san Hushriba baisan yayanta Barban ba. Amma abinda na kasa fahimta shi ne ya akai na manta da ainihin sunanka, tabbas ainihin sunanka ba Barban bane, meyasa kake ɓoye ainihin sunanka?"
Barban ya yi murmushi ya ce, "Ka taɓa ganin inda mutum kamata ke bayyana bayanansa da kansa? Indai ka kasance ɗan asalin birnin Shàha-Deher ka san me Barban yake nufi. Ba wani abu bane mai amfani. Kashedi nazo yi maka a matsayina na wanda ya sanka sosai amma kai baka sanni ba sunana kawai kake ji. Kashedi na farko shi ne ka ajiye muƙamin da aka baka na shugaban sarakuna tamanin da uku ko ince da huɗu masu farauta ta. Kashedi na biyu shi ne daga yau baza ka sake kawo min maganar sarƙoƙin-zinarinka ba domin ba mallakinku bane. Kashedi na uku shi ne kada ka kuskura kace zaka sake yiwa sarki Kuffuru mubaya'a idan ya dawo birninka. Karya ɗaya daga cikin waɗannan kashedi nawa, daidai yake da rasa komai naka, ka dawo talaka fitik wanda bashi da ko rigar da zai sanƴa. Idan kunne yaji..." Barban na gama faɗin haka ya miƙe tsaye da nufin fita daga cikin gidan sarautar Fairul-Faizara. Aymanul Faris ya zare waɗannan gajerun adduna guda biyu nasa, ya nuna sarki Fairaz dasu ya ce, "Ko ya ya kayi wani yunƙuri na kawo mana farmaki ta baya, tabbas taka ta ƙare."
Barban ya kama wannan igiya yayi sama, Aymanul Faris ma ya kama tasa suka tashi sama kamar yadda suka shigo cikin wanna wuri haka suka fice salin'alin. Sarki Fairaz dai da kallo kawai ya bisu cikin tsananin mamakin irin wannan baiwa tasu.
Suna fitowa daga cikin gidan sarautar suka nufi cikin waɗannan duhuwowi, nan ma suka sake amfani da waɗannan dogayen igiyoyi suka sake hawa kan wannan dogon tsauni. Barban ya mayar da igiyoyin cikin jakar tsafinsa, sannan ya murza kambun dake ɗaure a hannunsa, waɗannan aljanu guda uku suka bayyana a gabansa, suna masu risinawa.
"Waɗannan aljanu naka," inji Aymanul Faris. "Basu da suna ne? Kullum sai dai ka kirasu kawai amma ko magana basa yi?" Barban yai dariya ya ce, "Sunan wannan..." Ya nuna wanda ke tsaye a ɓangaren dama wanda yafi sauran tsaho da kauri ya ce, "Hankub Dawan." Wannan kuma, "Garkub Dawan." Na ƙarshensu kuma, "Hubbus Dawan." Wato gaba ɗaya ƴan-ƙabila ɗaya ce kenan, ƙabilar Dawan.
"Ku ɗauke mu, ku kaimu birnin Darul Barban. Aymanul Faris na buƙatar ganin jama'arsa." Barban na rufe bakinsa waɗannan aljanu guda uku sukai sama dasu, suka lulluka cikin gajimare suka ɓace ɓat.
Duk wannan abinda ya faru akan idanun sarki Fairaz ya faru yaga abinda sukayi amma baiji abinda suka tattauna ba. Tabbas ganin su aljani Hubbus Dawan ba ƙaramin ci gaba zai kawo wajen kamo Barban ba.
Bayan tafiyar ƴan sa'o'i Barban da Aymanul Faris suka dira a tsakiyar birnin Darul Barban, kafun su iso tuni Barban ya sauya fuska izuwa fuskar wannan mutumi mai yawan ƙasumba da gemu. Jama'a suka kewaye su suna ta yiwa Barban jinjina gami da yi masa kirari, cikin tsananin ƙauna da kulawa kamar yadda suka saba.
Basu tsaya a ko'ina ba, sai unguwar BARBANUL KUYUR inda aka sauƙe gaba ɗayan jama'ar ƙauyen Gazwar. Suna shigowa cikin wannan ƙauye jama'a suka fara zubewa a gaban Aymanul Faris suna kwasar gaisuwa kamar yadda suka saba yiwa Hasanul Jalwar, mahaifinsa. Nan take tunanin abinda ya faru a baya ya fara faɗowa Aymanul Faris a rai, ya yi ta zubar da hawaye. Musamman idan ya tuno irin kisan gillan da aka yiwa jama'arsu akan gaɓar teku.
Aymanul Faris ya yi ta kwantarwa da jama'arsa hankali yana nuna musu cewa komai daren daɗewa zasu sake haɗuwa a ƙarƙashin birni guda daya mai cikakken ƴanci. Wannan shi ne alwashin da Aymanul Faris ya ɗauka a ransa, wato sake kafa babban birnin Sháha mai zaman kansa.
Suna tafe har suka iso bakin ƙofar wani ƙerarren gida wanda duk faɗin wannan unguwa babu mai kyawunsa, Aymanul Faris yayi ta mamakin ko waye aka ajiye a cikin wannan gida? Suna zuwa bakin ƙofar gidan yai arba da masu gadi mutum huɗu sun sha sulke riƙe da makamai. Ana ganinsa tare da Barban masu tsaron suka zube ƙasa suka kwashi gaisuwa, sannan suka buɗe ƙofa. Aymanul Faris da Barban suka kunna kai izuwa cikin wannan gida, duk inda suka wuce sai suga an ƙawatashi sosai fiye da hasashen mutum. Wani irin ƙanshi na musamman ne ke tashi a cikin wannan gida mai sanƴaƴa zuciya.
Tsakiyar wani falo suka iso, inda sukai arba da mata guda biyu a zaune suna ta hira. Ɗaya daga cikinsu babba ce don zata kai shekaru arba'in da haihuwa, ɗayar kuma budurwa da bazata wuce shekarun gimbiya Jaanu ba. Koda waɗannan mata guda suka ga su Aymanul Faris sai suka miƙe tsaye cikin farin-ciki suka rungume Aymanul Faris su biyu a tare. Wannan budurwa ta janƴe jikinta daga nasu, ta bar masoyan guda biyu ƙanƙame da junansu. Wannan haɗuwa ce ta farko a tsakaninsu tun kafin sarki Ayubul Zairiy ya yiwa ƙabilarsu mummunar bazato.
Idan ka ƙarewa wannan mata kallo daga sama har ƙasa, zaka ga tana tsananin kama sak, da Aymanul Faris. Kai kace kara aka tsaga saboda tsananin yadda suke kama. Ko tambaya babu ka san mahaifiyarsa ce.
Hajriya ta kasance mace doguwa, mai yawan baƙin-gashi wanda ya zubo har kan gadon bayanta. Idanuwanta kalar shuɗi ne dasu maimakon baƙi irin na Aymanul Faris. Fatar jikinta tana da tsananin haske mai ban mamaki, kai kace rana ce abar haskawa. Indai kyawu ne anyi ittafaƙi cewa duk ƙabilar banu Kuyuru babu kamarta a lokacin da take budurwa. Don haka Aymanul Faris gadon kyawu yai.
"Ɗana? Ashe zan sake yin arba da kai?" inji Hajriya cikin sanƴin murya. Kai daga jin muryar ka san tausayin halin da suka tsinci kansu take.
Aymanul Faris ya janƴe jikinsa daga nata ya ce, "Kiyi haƙuri yake ummina akan abinda ya faru dake a kurkukun mutuwa. Tabbas ban san cewa zasu yi miki azaba haka ba, amma ki ƙyaleni dasu zan ɗaukar miki fansa."
Idanun Hajriya suka ciko da ƙwalla ta ce, "Tabbas duk wanda yayi sanadiyyar kaini wannan kurkuku ya cuce ni, dubi fa ka gani na rasa babban ɗan-yatsa na. Tabbas ya kai ɗana komai daren-daɗewa ina so ka yanko min kan sadauki Bandaru, sarki Ayubul Zairiy da duk wani wanda keda sa hannu a cikin wannan wulaƙanci da akai min! Wannan shi ne abinda nake buƙata daga wajenka." Aymanul Faris ya ce, "NA ƊAUKAR MIKI ALƘAWARI UMMINA, TABBAS SAI NA YANKO KAWUNAN WAƊANNAN MUTANE NAZO NA NUNA MIKI."
Hajriya tayi murmushi ta ce, "Ina alfahari da kai, ɗana. Kuma na san zaka iya." Ta nuna Barban dake tsaye a gefe guda ta ce, "Wannan kuma waye? Ba kayi min bayaninsa ba."
"Wannan da kike kallo, shi ne wanda ya ceci rayuwata da rayuwar jaruma Riya da rayuwar dukkanin sauran jama'armu daga sharrin sarki Ayubul Zairiy. Ba don wannan mutumi ba da tuni na daɗe da mutuwa, da tuni dukkanin al'ummarmu da suka yi saura sunje ƙasa. Shima da kike kallo asalinsa ɗan birnin Shàha-Deher ne, wato ɗan-uwanmu ne. Wannan birni da kike kallo shi ne wanda ya ginasa, shi ne wanda yake ɗebo marayu daga sassa daban-daban na duniya yana basu mafaka. Tunda nake a rayuwata ban taɓa ganin mutum mai kamala, karamci, tausayi da sanin darajar mutane kamar Kilawud Barban ba." inji Aymanul Faris.
Hajriya tayi murmushi ta dubi Barban ta ce, "Gaisheka gwarzon namiji. Namiji guda ɗaya wanda yafi mazaje dubu ɗari amfani. Tabbas jin bayananka daga bakin ɗana yasa naji hankalina ya kwanta da kai, tabbas kaine irin wanda ake turowa a kowanne zamani domin ya share hawayen al'umma."
Barban yai murmushi ya ce, "Ki daina zugani haka. Ni ba kowa bane face mutum mai taimako kawai. Da fatan dai mun same ku lafiya, domin akan hanƴa muke, nan bada daɗewa ba zamu koma."
Tun da su Aymanul Faris suka shigo cikin wannan ɗaki, jaruma Riya ta ƙura masa idanu kawai ko ƙiftawa batayi. Aymanul Faris ya ƙara haske, fuskarsa ta ƙara cika. Gashin kansa ya ƙara kwanciya kuma ya ƙara baƙi sosai. Tabbas ya ninka kyawunsa na da sau uku a wannan lokaci, kuma babu wadda zatai arba da shi a haka bata kamu da mahaukacin ƙaunarsa ba. Wannan shi ne dalilin da yasa jaruma Riya tayi shuru ta gagara cewa komai, ta ƙura masa idanu kawai soyayyarsa tana kwarara a cikin zuciyarta.
"Akan hanƴa kuke? Habawa! Ai sai kunyi mako guda a wannan birni domin na samu damar ganawa da ɗana sosai." inji Hajriya. Tabbas Barban bashi da damar cewa a'a akan wannan batu na Hajriya don haka sai ya amince nan take. Amma sai ya nemi su Hajriya su bashi dama ya gana da Aymanul Faris na tsahon rabin sa'a kacal.
"Meye zaku tattauna?" Inji Hajriya.
"Magana ce da ta shafeni ni da shi kawai. Kuyi haƙuri dan Allah." inji Barban. Ya kama hannun Aymanul Faris suka fice daga cikin ɗakin.
"Riyalatu? Meyasa ki kayi shuru kika gagara magana a gaban Ayman, shin tsoronsa kike ji ne?" Hajriya ta tambayi jaruma Riya.
"Hmm. Ummu-Ayman baki ga yadda ɗan naki ya dawo bane. Ya ƙara kyawu sosai fa. Ga murɗaɗɗen jiki ga kyawun fuska, tabbas wannan ɗa naki abin burgewa ne. Kuma dole ne kowacce budurwa tai mafarkin samunsa a matsayin abokin rayuwa." inji Riya.
Hajriya tai dariya ta ce, "Idan na fuskance ki sosai, wani abu ne ke shirin shiga tsakaninki da ɗana, hakane?" Jaruma Riya ta cije baki cikin tsokana ta ce, "Wani abu kuma? Shi ne yake ƙaunata ba ni nake ƙaunarsa ba." Kai daga jin muryar jaruma Riya ka san kawai kalaman a iya baki suka tsaya basu kai zuci ba.
"Zamu gani ai waye ne a cikinku zai fara bayyanawa ɗan-uwansa abinda ke ransa." inji Hajriya.
A daidai wannan lokaci da Hajriya ke ƙoƙarin gano jaruma Riya na ƙaunar Aymanul Faris, a wannan lokaci a farfajiyar wannan gida, Barban ne da Aymanul Faris zaune bisa waɗansu kujeru masu fuskantar juna, amma an saka wani teburi a tsakaninsu.
Barban ya ɗauki lemo mai sanƴi a cikin wata kwalba ya kurɓa ya ce, "Ga dukkan alamu zamu shafe sati guda a cikin wannan birni. Domin bana so ja... da umarnin mahaifiyarka mai karamci. Sannan kuma aljani Ranganu ya kawo min bayanai akan ABUN HARI NA UKU, wanda sarkin da zamuje mu yiwa sata a aikinmu na uku da kai. Ga wannan littafin kaje kayi ta karantawa, bayanai ne akan wannan sarki da zamuje mu yiwa sata. Ka tabbatar ka karance wannan littafi a cikin sati guda ka ji ko?" Aymanul Faris ya gyaɗa kai alamun amincewa. Fuskarsa na ɗauke da alamun damuwa.
"Ayman, mene ne abinda ke damunka?" Barban ya tambaye shi.
"Maigida! Yau ku san watanni huɗu ban kalli madubin zuciyata ba. Tun abin baya damuna har ya fara damuna sosai. A yanzu kallon jaruma Riya da nayi, ya tuno min da masoyiyata gimbiya Jaanu. Maigida nayi ƙoƙarin cire tunanin gimbiya Jaanu a raina amma na kasa. Soyayyarta ta riga ta gama ginuwa a cikin zuciyata babu yadda za'ayi naji daɗin rayuwa idan bana tare da ita."
Maigida Barban ya yi shuru yana kallon Aymanul Faris har ya gama. "Ayman? Me kake so kace?"
Aymanul Faris ya kalli gefe ya ce, "So nake kwanan nan na kalli fuskar gimbiya Jaanu, kuma kunnuwana su ji zazzaƙar muryarta."
"Hmm. Wannan ai abu ne mai sauƙi ka bari sai mun zo komawa gida, zansa akaimu birninsu kayi arba da ita. Shikenan?" Inji Barban.
Aymanul Faris ya zube ƙasa yana godiya, cikin jin daɗi da farin-ciki.
"Abun harinmu na uku, sarki Kuffuru ne. Ba sai nayi maka bayani akan zalunci da rashin imanin sarki Kuffuru ba. Ka san komai. Meye zamu sato a birnin Kufa?
"Kimanin shekaru goma sha-bakwai baya, ana gudanar da gasar-jarumtaka a wannan nahiya tamu. Wannan gasa ta jarumtaka sarakuna guda huɗu ne suka ƙirƙirota, a wannan gasa ana asarar rayukan manƴan jarumai. Duk wanda yai nasara a wannan gasa ana bashi kyautar kuɗi har dinare miliyan saba'in. Shekaru huɗu da suka wuce naje kallon wannan gasa nayi arba da wata takobi ta daraja a hannun wani jarumi baƙo da ba'a san ko shi waye ba. A wannan shekara a birnin Kufa aka gudanar da wannan gasa.
"Wannan baƙon-jarumi ya gallabi jaruman-gasar wannan shekara albarkacin wannan takobi dake hannunsa. Sai da wannan jarumi ya hallaka manƴan sadaukai guda goma a wannan gasa, yazo wasan-ƙarshe inda yai gumurzu da wani jarumi mai suna Shar.
"A zahiri da tabbatarwa wannan baƙon jarumi yafi sadauki Shar a komai, amma ana fara wannan gasa wani daga cikin ƴan kallo yayi amfani da ƙarfin sihirin tsafi ya baiwa sadauki Shar sa'a ya fille kan wannan jarumi baƙo da yazo. Ƙa'idar wannan gasa shi ne duk jarumin da aka kashe a wannan gasa, kayayyakinsa da dukiyarsa sun zama mallakin wannan sarki da ake gudanar da wannan gasa a birninsa. Saboda haka sarki Kuffuru ya gaji wannan rantsatstsiyar takobi ta wannan baƙon jarumi.
"Bayan an ɗauke gawar wannan jarumi an tafi da ita daji, an binneta. Sai naje na haƙe kabarin na ɗauko kansa, na tafi dashi. Fiye da shekaru biyu na ɓata ina ta bincike akan na gano waye ainihin wannan jarumi domin ni dai ina ji a jikina na sanshi. Da ƙyar da siɗin-goshi na gano cewa wannan jarumi ɗan birnin Shàha-Deher ne, sunansa JILLAS KUYURU. Ya kasance tamkar ƙani a wajen mahaifinka domin ɗan-ƙanin mahaifinka ne. Bayan gano hakan sai na gano cewa ai wannan takobi dake hannunsa ba wata bace illa SAIFUL SHIRADU mallakin sarki Samudu na farko, mutumin da ya fara kafa ƙabilar banu Kuyuru a ƙauyen Salwaza. Wannan takobi ita kaɗai ce abinda yayi saura daga kayayyakin sarki Samudu duk sauran suna tsare a kogon tsafinsa. Babu mai mallakarsu face magajin RUHINsa.
"Sarki Kuffuru ya ɓoye wannan takobi a cikin wani gida na musamman dake ƙarƙashin ƙasa, wanda duk duniya babu wanda ya isa ya shiga cikin wannan gida sai shi kaɗai. Ban san meye zaiyi da wannan takobi ba, amma har yau bai fiddota ba. Ya kai Ayman, wannan takobi tana da matuƙar amfani a garemu. Da ita ce kaɗai zamu iya sato abu na huɗu daga cikin jerin abubuwan da zamu sato.
"Don haka ɗakko wannan takobi ya zamo wajibi a garemu. Idan muka koma gida zan sanar da kai yadda zamu yi komai daki-daki kamar yadda nai ma bayani a yayin zuwa birnin Askandariyya." Barban ya ƙare bayaninsa gami da kurɓar wannan lemo. Har Aymanul Faris ya buɗi baki zaiyi magana amma sai Barban ya dakatar dashi.
"Yin tambayoyi a yanzu ba shi da wani amfani. Ka je ka karanta wannan littafi. Zaka fahimci komai da komai akan wannan takobi ta SAIFUL SHIRADU kuma zaka fahimci ainihin waye ne sarki Kuffuru da tarihinsa." Barban na gama faɗin haka ya yiwa Aymanul Faris bankwana ya ɓace daga wannan wuri.
Aymanul Faris ya saka wannan littafi a cikin aljihun wandonsa ya miƙe tsaye ya nufi wannan ƙaton falo da ya bar mahaifiyarsa da jaruma Riya a ciki. Yana shiga cikin ɗakin yayi arba da ƙaton teburi cike da abinci da abinsha irin nasu na ƙabilar Kuyuru wanda suka saba ci.
Aymanul Faris ya zauna akan kujera ya saka wannan abinci a gaba da nufin ya fara ci. Mahaifiyarsa Hajriya na ganin haka ta miƙe tsaye ta fita daga cikin falon, ta ƙyale shi daga shi sai jaruma Riya. Aymanul Faris ya yanko tsokar nama guda ya sa a bakinsa ya fara ci, jaruma Riya ta matso kusa dashi bisa wata kujera tana satar kallonsa, da zarar ya ɗago kai zasu haɗa idanu sai ta kawar da kai.
Tuni ya gama gano shirin jaruma Riya wato tana so ta bayyana masa abinda ke cikin ranta, shiyasa mahaifiyarsa ta fita ta basu wuri. Koda Aymanul Faris yaga sai noƙe-noƙe take tana tsoron yin magana, sai yai murmushi ya ci gaba da cin abincinsa har sai da ya ƙoshi yasha ruwa.
"Ƴar-uwa da alamu akwai magana a bakin ki, kuma tun da na shigo cikin wannan ɗaki naga kina ta faman kallona. Wani abu ne?" Ya tambayeta.
"Ehh.. mana.. gaba ɗaya ka sauya min na gani." Ta faɗa muryarta na rawa.
"Hmmm. Na sauya kamar ya? Aymanul Faris ɗin ki ne da kika sani!!!"
Jaruma Riya ta sake yin shuru gami da sunkuyar da kanta ƙas tana wasa da ƴan-yatsunta. Ta gagara ce masa komai.
Tuni Aymanul Faris ya cika da tsananin mamaki duk irin surutun jaruma Riya da ya sani ace yau tayi shuru kamar bata nan tabbas ko tambaya babu, akwai abinda ke tafiya.
"Ki faɗi abinda zaki faɗa nifa tafiya zanyi domin a gajiye nake..." Ya faɗa mata yana ƙoƙarin tashi daga kan wannan kujera. Amma sai yaji ta kamo hannunsa, ta ɗago kanta idanunta nata zubar da hawaye ta ce.
"ƊAN-UWANA AYMAN KANA SONA?"
****RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 27: *Tarihin sarki Kuffuru*
*
*
✍️✍️✍️ Umar Sangaru ✍️✍️✍️
*
Aymanul Faris ya sa hannunsa ya share hawayen dake zuba daga idanun jaruma Riya, bisa mamaki yaji waɗannan hawaye sanƴi ne dasu tamkar ruwan-ƙanƙara. Ya dubeta ya ce, "Yanzu idan aka faɗa miki bana sonki zaki yarda? Kiyi sani cewa tun tasowar mu babu wacce na sani sosai kuma na saba da ita kamar ke ɗinnan. Ya za'ayi a ce kina yi min irin waɗannan tambayoyi, waɗanda kin riga kin san amsoshinsu. Ina sonki mana."
Jaruma Riya tayi murmushi ta ce, "Nagode. Bisa jin waɗannan kalamai daga bakinka. Idan babu damuwa daga yau zan kasance mai ɗebe maka kewa gami da nishaɗantar da kai." Aymanul Faris ya yi murmushi ya ce, "Kiyi zamanki sai zuwa nan da wani ɗan lokaci. Tabbas yanzu akwai muhimman ayyuka a gabana, kuma bani da tabbacin gama su lafiya. Kiyi haƙuri sai nan gaba komai zai daidaita." Yana gama faɗin haka ya tashi ya fice daga ɗakin. Jaruma Riya tayi tsalle cikin murna tana cewa, "Ya karɓi soyayyata. Wannan ita ce ranar da na daɗe ina jira, tabbas wannan rana ta musamman ce a gareni. Aymanul Faris nawa ne, ni kaɗai."
Kai tsaye Aymanul Faris ya wuce izuwa cikin ɗakin da aka tanadar masa domin ya kwanta ya huta kuma yai barci, yana tafe yana ta tunanin maganganun da jaruma Riya ta faɗa masa. Babban abinda yafi ɗugunzuma masa hankali shi ne, yasan ba zai iya rabuwa gimbiya Jaanu saboda jaruma Riya ba. Kuma haɗa soyayyar ƴan-mata guda biyu a lokaci guda abu ne mai wuyar sha'ani musamman a irin wannan hali da ya tsinci kansa a ciki. Yana shigewa cikin ɗakin ya kwanta akan wani ƙaton gado mai laushin gaske, ya ci gaba da tunanin meye ya kamata yayi?
Shin tsakanin jaruma Riya da gimbiya Jaanu wacce tafi dacewa da shi a wannan lokaci? Amsar da ya gagara baiwa kansa kenan.
Indai batun kyawu ake, za'a iya cewa sunyi kunnen-doki amma mutum zai iya cewa gimbiya Jaanu tafi kyau saboda kalar gashin kanta mai tsananin kyawu.
Aymanul Faris na cikin wannan tunane-tunane yaji alamun littafi a cikin aljihun wandonsa, ba shiri ya fiddo littafin, ya fara duba shi. A jikin bangon littafin an rubuta:
*TARIHIN SARKI KUFFURU DA BAYANAI AKAN TAKOBIN SAIFUL SHIRADU*
Aymanul Faris ya ce a ransa, ina ta jin labarin sarki Kuffuru yau kam bari na karanta cikakken tarihinsa na gani. Yana gama faɗar haka ya buɗe shafin farko na wannan inda yai arba da zuben rubutu kamar haka:-
((Bayan kammala yaƙi tsakanin sarki Deher da sarki Meher, gimbiya Kabshiya ta gudu daga birnin Shàha-Meher ta cikin wata ɓarauniyar hanƴa da babu wanda ya san da ita face sarki Meher kaɗai, kuma shi ne wanda ya nuna mata wannan hanƴa. Ba don komai ba, sai don ita ce kaɗai a cikin matansa ta samu juna biyu dashi don haka yafi ƙaunarta akan komai.
Gimbiya Kabshiya na cikin gudu a tsakiyar dokar daji nakuda ta kamata, gashi inda take daji ne zalla babu gida gaba ko baya. Ko alamun mutum babu a wannan waje. Wannan abu ya ɗugunzuma hankalinta sosai domin wannan shi ne haihuwarta na farko ace babu masu taimaka mata ai da akwai matsala.
A daidai wannan lokaci ne hadari baƙi-ƙirin ya gangamo daga gabashin wannan daji, nan fa aka fara kwararo tsawa da walƙiya. Wata iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa tamkar zata ɗauki Kabshiya tayi jifa da ita. Kuma a wannan lokaci Kabshiya tana tsaka da nakuda babu yadda za'ayi ta iya miƙewa koda zaune balle taje ta shige cikin wani kogo ko kuma gindin wata bishiya ta tsirawa wannan ruwa dake shirin sakkowa.
Tsahon sa'a biyu da rabi tana ta nakuda amma bata haihu ba, kuma ba'a tsuge da wannan ruwa ba. Amma hadari ya gama haɗuwa iya haɗuwa yayi baƙi-ƙirin ya tokare da sararin samaniya.
Sa'a biyu da rabin na cika gimbiya Kabshiya ta haifo wani irin santelelen jariri mai tsananin kyawu da ban al'ajabi. Ai kuwa yana sauƙowa duniya aka tsuge da ruwan sama kamar da bakin-ƙwarya, aka yi ta ruwa har tsahon sa'a huɗu ba tare da an tsagaita ba. Wani abin al'ajabi da gimbiya Kabshiya ta gani shi ne ko kaɗan wannan ruwan sama baya zuwa inda suke sosai, bata san me yasa ba amma ruwan baya zuwa.
Wannan jariri nata na da ban al'ajabi domin ko irin kukan nan da jarirai keyi shi baiyi ba, murmushi ne kawai a fuskarsa. Albarkacin ruwan da aka zabga a wannan daji, duk jinin dake jikin wannan jariri ya wanke, kuma inda zata lura da zata ga an yanke masa cibiya kuma an gama jara shi. Duk irin abinda jariri ke buƙata an yiwa wannan jariri, wannan abu ya baiwa Kabshiya mamaki domin bata san wanda yai hakan ba.
Tana cikin wannan hali ne wata murgujejiyar kura ta fito daga cikin ƙaton kogon dutse ta biyo ƙanshinsu ita da

Please Login or Register in order to submit comment