Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya shafi kambun tsafin dake hannunsa take su Hubbus Dawan suka bayyana. Ya basu umarnin kaisu bakin kogin Ril.
Nan take aljanun suka yi sama dasu suka dire su a bakin wani ƙaton kogi mai ban al'ajabi. Ruwan wannan garai-garai ne yana ta gudu, saboda tsananin haskensa da tsaftarsa har kifayen da ke yawo a ciki mutum zai na hangowa.
"Mai gida?" inji Aymanul Faris. "Ina da tambaya, wai shin su Hubbus Dawan baza su iya tsallakar da mu wannan kogi bane?"
Barban ya yi dariya ya ce, "Ka manta abinda na ce maka ne? Ai dole sai mun sare kan wannan macijiya mun kaiwa Tameer indai muna so ya amince da wannan buƙata tamu?" Ayman ya ce, "Kwarai haka ne fa."
Barban ya yi murmushi ya samar da wata ƴar ƙaramar kwale-kwale ta itace mai wajen zaman mutum biyu, sannan akwai mawani a tsakiyarta wadda mutum zaina wainawa domin ƙara mata gudu ko kuma ragewa.
Ba tare da ɓata lokacin komai ba, ya shiga cikin wannan kwale-kwale, Aymanul Faris ma ya shiga ya zauna a gefensa. Barban ya fiddo wata ƙatuwar riga a cikin jakar-tsafinsa ya baiwa ita Aymanul Faris.
"Da zarar mun iso tsakiyar wannan kogin ka saka wannan ƙatuwar riga sannan ka faɗa cikin wannan ƙaton kogin domin fafatawa da wannan macijiya. In dai wannan ƙatuwar riga tana jikinka bazaka taɓa nutsewa a cikin kogi ba. Kaga wannan zai baka dama ka gwabza yaƙi da wannan macijiya harma ka kasheta." inji Barban.
Yana gama faɗin haka ya waina wannan mawani dake tsakiyar kwale-kwalen nan take ta fara tafiya a cikin wannan kogi, da farko a hankali ta fara tafiya amma a hankali ta ɗinga ƙara gudu ta tunkari tsakiyar wannan kogi. Tsakanin Aymanul Faris da Barban babu wanda ya ce uffan har suka iso tsakiyar wannan kogi, sannan Barban ya gyaɗawa Aymanul Faris kai.
Nan take ya ɗakko wannan ƙatuwar riga ya sanƴa sannan ya daka tsalle ya faɗa cikin wannan kogi, ai kuwa bisa mamaki saiya ga wannan riga ta baje a saman ruwa ta ƙi nutse shima kuma bai nutse ba.
Barban ya ƙara gudun wannan kwale-kwale kafun Aymanul Faris ya ankara tuni jirgin ya yi gaba da gudu, cikin ƴan daƙiƙu ya ɓace a cikin duhun hazon kogin.
Aymanul Faris na bisa wannan kogin yana ta wutsil-wutsil, tsahon ƴan daƙiƙu yana ta dube-dube da kalle-kalle yana so yaga ta ina wannan macijiya zata fara kawo masa hari. Har rabin sa'a ta shuɗe babu alamun wannan macijiya. Lamarin da yasa Aymanul Faris ya fara kwakwanton anƴa wannan macijiya zata bayyana kuwa?
Kwatsam! Ba zato ba tsammani yaji wani abu daga ƙarƙashin wannan kogi ya jawo sawayensa izuwa ƙarƙashin wannan ruwa tamkar ya faɗa cikin rijiya haka ya faɗa cikin wannan abu. Ashe ba wani abu bane illa wannan macijiya kuma ita ce ta haɗiye shi.
Wani irin mugun hajijiya ya ɗebi Aymanul Faris kansa yayi duhu, ya daina ganin komai. Daga nan ya sulale ƙasa sumamme.
Lokacin da ya farfaɗo daga wannan suma da yayi saiya tsinci kansa a cikin wani ƙaton ɗaki mai girma da faɗin gaske. Wata ƙawanƴar wuta mai ci daga ƙarƙashin ƙasa ta kewaye shi. Koda yayi niyyar motsa hannayensa sai yaji su a ɗaure tamau, ya duba haka yaga waɗansu sarƙoƙi da aka kafa kafarsu daga ƙarƙashin ƙasa su ne suka ɗaure shi.
Babu yadda za'ayi ya iya motsa hannayensa saboda a ɗaure suke sannan kuma ga ƙawanƴar wuta wacce ta kewaye shi, zafinta yana damunsa.
Wannan abu yayi matuƙar baiwa Aymanul Faris mamaki ya za'a yi shi da ya faɗa kogi, zai tsinci kansa a cikin gida na ƙarƙashin ƙasa?
Kafun ya samu amsar wannan tambaya ne, yaga wannan ƙawanƴar wuta wacce ta kewaye shi ta fara ɗaukewa, tana shigewa cikin ƙarƙashin ƙasa.
Mutum zai iya cewa Aymanul Faris zai iya yin farin ciki tunda wannan wuta wacce zafinta yake damunsa ta ɓace, amma a zahiri ba haka bane. Shi kansa ya san cewa lallai wani mugun abun zai iya faruwa bayan ɗaukewar wannan wuta.
Ai kuwa wannan wuta na gama shigewa ƙarƙashin ƙasa, wata ƙatuwar ƙofa daga ƙarƙashin ƙasa ta buɗe. Wata irin zabgegiyar macijiya ta fara fitowa daga cikin wannan ƙofa, ta shiga ta tsakankanin sawayen Aymanul Faris tana wucewa.
Al'amarin da yayi matuƙar ɗugunzuma hankalin Aymanul Faris kenan, domin baisan ta yadda zai yaƙi wannan macijiya ba. Na farko ga hannayensa guda biyu dake ɗaure a jikin wannan kafa da aka dasa a ƙarƙashin ƙasa, sannan ga babu makamai a jikinsa.
Wannan macijiya na gama fitowa daga wannan rami da ya buɗe, ta miƙe tsaye ta kawo kanta daidai fuskar Aymanul Faris ta ƙura masa idanu.
Gaba ɗaya jikin wannan macijiya baƙi ne mai ratsi-ratsin ja, idanuwanta kuma ruwan-ɗorawa ne, da wani baƙin ɗan-ido a cikinsu baƙi sidik. Bakinta na da faɗin gaske sannan tana fesar da wani irin ruwan dafi.
Aymanul Faris na ganin cikin idanun wannan macijiya yaji wani irin kwarjini da iko ya rufe shi, bai san sa'adda ya kawar kansa ga barin ganin idanunta ba.
Wannan macijiya na gama ƙarewa Aymanul Faris kallo, tayi girgiza girman jikinta ya ragu ainun. Jikin ya dawo tamkar na ainihin maciji wanda aka saba kallo yau-da-kullum.
Ai kuwa tana dawowa haka, ta fara kanannaɗe jikin Aymanul Faris daga sawayensa tana yin sama. Duk gaɓar jikinsa da ta wuce sai yaji tamkar da ƙarafu aka ɗaure gaɓar, tana ƙoƙarin ɓaɓɓallewa.
Aymanul Faris ya tabbatar da cewa duk kuskuren da yasa ya bari wannan macijiya ta gama kanannaɗe jikinsa, to, matse shi zatayi a waje guda, ƙasusuwan jikinsa su kakkarye ya mutu.
Babban tashin hankalinsa a yanzu shi ne tayaya zai iya tsitstsinka waɗannan sarƙoƙi da suka ɗaɗɗaure shi, har ya kwaci kansa daga sharrin wannan macijiya?
Aymanul Faris ya tuna da cewa sai an gwada ake sanin na ƙwarai. To, me zai hana ya gwada tsitstsinka waɗannan sarƙoƙi.
Koda ayyana hakan a ransa, saiya tattaro ƙarfinsa gaba ɗaya ya fara jan waɗannan sarƙoƙi da ƙarfi yana so ya tsinko tun daga tushensu na ƙarƙashin ƙasa.
Nan fa jijiyoyin jikinsa suka kukkumburo suka yi burɗin-burɗin, damatsan hannunsa da kafaɗunsa suka kumbura. Wani irin azababben zogi ya shige shi, bai san sa'adda ya fasa ƙoƙarin tsitstsinka waɗannan sarƙoƙi ba.
A daidai lokacin kuma wannan macijiya har ta iso ƙugunsa, nan fa yaji daga ƙugun nasa zuwa sawayensa tamkar an kakkarya ƙasusuwan wurin. Ya kwarara wani irin uban ihu mai razanarwa.
Ba shiri ya sake tattaro ƙarfinsa waje guda ya fara ƙoƙarin tsitstsinka waɗannan sarƙoƙi, a wannan karon ma jijiyoyin jikinsa sake kumburowa suka yi, idanuwansa suka kaɗa suka yi jawur.
Damatsan hannunsa da ƙaurin hannunsa na amsawa tamkar zasu ɓalle gida biyu saboda tsabaragen zogi, amma a haka ya jure, idanuwansa na gudun hawayen wahala. Idan kaga yadda jijiyoyi da ƙwanji suka cika jikisa sai ka cika da tsananin mamaki, kuma dole ka jinjinawa tsananin jarumtakarsa da ƙarfin damtsensa.
Da ƙyar da siɗin goshi Aymanul Faris ya samu ya finciko asalin ƙarafunan waɗannan sarƙoƙi waɗanda aka binne a jikin wannan kafa, nan take hancinsa da bakinsa suka fashe saboda tsananin wahalar da yasha kafun ya finciko ƙarafun.
A wannan lokaci tuni wannan macijiya ta iso kan ƙirjinsa tana ƙara sama tana matse shi, saboda tsabar wahalar da ya sha sai da ya ɗan huta na ƴan daƙiƙu kafun yasa hannayensa ya kamo bakin wannan macijiya.
Hannu guda ya riƙe leɓen ƙasa na macijiyar, hannu guda kuma ya riƙe na sama. Aymanul Faris ya sake tattaro ƙarfinsa a karo na uku, ya ja wannan baki nata da ƙarfi. Ai kuwa nan take leɓen ƙasa da na sama ya rabe gida biyu, jini yayi feshi daga jikin macijiyar ta zube ƙasa matacciya.
Aymanul Faris ya warware wannan ɗauri da tayi masa ya jefar da gawarta gefe guda, ya nemi waje a cikin ɗakin ya zauna domin hutawa daga wannan baƙar wahala da yasha.
Zamansa keda wuya bangon wannan ɗaki ya tsage gida biyu, irin wannan siffa ta wannan ƙatuwar macijiya da ta fara fitowa daga ƙarƙashin ƙasa ta bayyana daga cikin bangon.
Macijiyar ta nannaɗe jikinta a waje guda ta fasa kai tana shirin kaiwa Aymanul Faris sara, da yake a wannan lokaci Aymanul Faris ba'a ɗaure yake ba, ko kaɗan babu damuwa a fuskarsa.
A hannun Aymanul Faris babu kowanne irin makami face waɗannan sarƙoƙi waɗanda ya tsitstsinka ɗazu. Shima take ya gyara tsayuwarsa yana jira yaga ta ina wannan macijiya zata fara kawo masa hari.
Tsahon ƴan daƙiƙu suna ta kallon-kallo, kafun wannan macijiya ta wangame bakinta cikin shammace ta watsa masa wani irin ruwan-dafi mai mugun zafi tamkar an tafasa dalma.
Cikin baƙin zafin nama Aymanul Faris yayi wani wawan tsalle wanda shi kansa sai da yayi mamakin yadda akayi yayi tsallen, ya dira a gefe guda. Wannan ruwan-dafi ya dira a jikin bangon wannan ɗaki. Kamar an narka roba a wuta haka wannan bango ya narke, abinda ke bayan bangon ya bayyana.
Aymanul Faris ya hango gangar ruwan wannan kogi wanda Barban yake ta gudu a cikinta bisa wannan kwale-kwale. Hakan ne ya tabbatar masa da cewa lallai wannan ɗaki a bisa tsibiri aka gina shi sannan yana daf da bakin gaɓa domin yana hango hazo-hazon gidaje.
Aymanul Faris ya wulwula waɗannan sarƙoƙi dake hannunsa ya daka tsalle sama, ya saka waɗannan sarƙoƙi ya shaƙo wuyan wannan macijiya sannan ya zagayo ta bayanta, ya ɗane kan wuyanta sannan ya shaƙe wuyan nata.
Nan take wannan macijiya ta fara wutsil-wutsil tana ta kaiwa Aymanul Faris duka da jelarta domin ta samu ta jeho shi ƙasa, amma ina, tuni ya riga ya riƙe wuyan nata da ƙarfi kuma ya shaƙe da kyau.
Kafun ka ce me wannan, tuni wannan macijiya ta hargitsa wannan ɗaki duk abinda ta kaiwa duka da wannan jela nata indai ta same shi, sai dai kaga ya dagargaje ya rushe.
Aymanul Faris ya ci gaba da shaƙe wannan wuya nata da ƙarfi, nan fa waɗannan sarƙoƙi suka yi ta matse wuyan suna danna maƙwagoronta ciki, lamarin da yasa wata farar kumfa ta fara tsiyayowa daga bakin wannan macijiya kenan.
Ta ci gaba da wutsil-wutsil domin ta jefar da Aymanul Faris amma ya riƙe gagam ya ƙi sakinta, hakan ne yasa jijiyoyin jikinsa suka sake kumbura.
Haka dai suka ci gaba da kokawa da wannan macijiya har tsahon rabin sa'a sannan jikinta yayi sanƴi ta sulale ƙasa matacciya.
Aymanul Faris ya sauƙa daga kanta, ya zauna a gefe guda ya huta sosai.
Daga nan ya tashi yaje wajen wannan rusasshen gini ya ɗauko wani gungumemen dutse mai tsini, yazo daidai wuyan wannan macijiya ya ɗaga dutsen sama ya caka shi akan wuyan, nan take kan macijiyar ya guntule.
Aymanul Faris ya sunkuya ya ɗauki kan macijiyar ya ɗaura akan kafadarsa sannan ya fice daga cikin wannan ɗaki ta wannan bango wanda ya rushe. Yana zuwa bakin gaɓar wannan kogi ya tsaya, yana tunanin tayaya zai bi bayan Barban ɗauke da wannan ƙaton kayi na wannan macijiya.
Kamar daga sama sai ya jiwo ƙarar tahowar wannan jirgi na Barban, wani irin farin ciki ya lulluɓe Aymanul Faris ya sauƙe kan wannan macijiya ƙasa.
Jim kaɗan sai ga Barban ya ƙaraso wannan wuri, koda yaga kan wannan macijiya saiya cika da tsananin farin ciki, yazo yayi ta yiwa Aymanul Faris bisa wannan namijin ƙoƙarin da yayi wajen saro kan wannan macijiya.
Aymanul Faris ya kwashe labarin duk yadda abun ya auku ya faɗawa Barban, shima Barban sai da ya cika da tsananin mamakin yadda aka yi Ayman ya tsinci kansa a cikin wannan ɗaki dake bisa wannan tsibiri.
Bayan gama ƴar tattaunawa Barban ya dafa kafaɗar Aymanul Faris suka ɓace daga wannan wuri, har da wannan kai na wannan macijiya.
Basu bayyana a ko'ina ba sai a tsakiyar garin Rildaz. Barban a matsayin tsohon mutum mai yawan ƙasumba, shi kuma Aymanul Faris ya bayyana a matsayin saurayi mai dogon gemu da gashin-baki. Babu yadda za'ayi ka kalle su a haka, ka iya shaida su.
Barban ya wuce gaba goye da wani buhu a gadon bayansa, Aymanul Faris kuma ya take masa suka nufi cikin wannan gari na Rildaz.
Garin Rildaz a tsare yake; babu cunkuson gidaje ko kuma shagunan kasuwa. Komai a jere yake layi-layi, mutanen garin kuma, irin shigar dasu Barban suka yi irinta ce dasu, wato kusan kowa a garin zaka kalle shi da dogon gemu ko kuma ƙasumba.
Barban ya tare wani mutum mai sanƴe da ƴar-shara da yazo wucewa ta gefensu. "Barka malam. Dan Allah, tambaya muke?" ya faɗawa mutumin.
"To, Allah yasa na sani?" inji mutumin. Barban ya ce, "Gidan mai-zane Tameer muke nema?"
Mutumin ya riƙe baki ya ce, "Gidan Tameer kuke nema? Idan kuka miƙe hanƴar nan kuka yi tafiya kamar ta rabin sa'a, zaku iso wata maƙera inda aka sarrafa zinari, kuna zuwa daidai wannan maƙera ku sha kwana ku nufi gabas, za ku hango wani gidan-sama wanda aka yiwa ado da zane-zane. To, nan ne gidan Tameer. Da fatan da alheri ku kazo?"
Barban ya ce, "Mun gode sosai da wannan kwatance naka. Daga ganinmu ai ka san bamuyi kama da mugaye ba, mun zo ne domin a zana mana taswirar wani jeji." Yana gama faɗin haka ya wuce gaba Aymanul Faris ya take masa baya.
Kamar yadda wannan mutumi yayi musu kwatance, haka suka bi, har suka iso ƙofar wannan gida mai bene wanda aka yiwa ado da zane-zane.
Gidan ƙaton gaske ne, anyi masa irin samfurin ginin mutanen Misra. Ƙofar a garƙame take da ƙaton-kwaɗo, zaka yi tsammanin babu kowa a cikin gidan.
Aymanul Faris ya ƙarasa ƙofar gidan ya kwankwasa, "Tameer yana nan?" ya faɗa da ƙarfi. Saida yayi hakan har sau uku, sannan yaji anyi gyaran-murya daga cikin gidan.
Yana jin haka ya dawo gefen Barban ya tsaya, suna jiran a buɗe ƙofa Tameer ya fito. Jim kaɗan ƙofar gidan ta buɗe, wani dogon mutum fari mai dogon gemu jajawur ya fito daga cikin gidan.
Ya yiwa su Barban kallon nutsuwa ya ce, "Suna na Tameer, ku ne kuke sallama?" Muryarsa na bayar da nutsuwa da kamala.
Barban da Aymanul Faris suka matso kusa da Tameer, Barban ya ce, "Suna na Kilawu, wannan kuma sunansa Ayman. Daga birnin Tomori muke, mun kawo maka wani aiki ne na zanen taswirar fuskar wani mutum."
Tameer ya riƙe baki cikin tsananin mamaki ya ce, "Daga birnin Tomori kuke? Wai ku na nufin sunana har yaje wajajen can?"
Barban ya gyaɗa masa kai alamun hakane. "Ah lallai kun sha hanƴa kuzo muje ciki na baku masauƙi ku huta, kafun mu tattauna akan aikin da ya kawo ku." inji Tameer.
Yana gama faɗin haka ya juya ya shige cikin wannan gida, Barban da Aymanul Faris suka take masa baya. Suna shigowa aka baiwa Aymanul Faris da Barban ɗaki guda mai kyau, aka kawo ƴaƴan itatuwa suka kimtsa cikinsu, sannan aka kawo musu nono a cikin ƙoƙo suka karɓa suka sha, sannan suka buɗe shafin hira.
"Maigida, wai tayaya wannan mutumin zai iya zana mana taswirar fuskar Kuffuru, tunda ga dukkan alamu bai taɓa kallon Kuffuru ba?" Aymanul Faris ya tambayi Barban.
"Nima ban sani ba, wallahi. Amma dole akwai yadda yake yi wajen zana fuskokin mutane, tunda hatta kansa maigirma Ranganu bai faɗa mana ga abinda zamu ce ba, ya ce kawai muje mu sami Tameer." inji Barban.
Aymanul Faris ya jinjina kai ya ce, "Wai shin kamar yadda shiga wannan gari yake da haɗari haka shiga garin Sulken ma yake?"
Barban yayi murmushi ya ce, "Bari mu gama da wannan babin tukunna, zan yi maka bayanin garin Sulken."
Haka dai suka ci gaba da hira har dare ya soma rabawa sannan barci ya sace su gaba ɗaya. Washe gari suna farkawa suka samu an kawo musu abincin kalaci mai kyau, nan take suka kimtsa cikinsu.
Suna gama cin abincin aka buɗe ƙofar wannan masauƙi nasu. Tameer ya shigo cikin ɗakin, riƙe da farar takarda da alƙalami da kuma waɗansu fararen kwalabe.
"Da fatan kun tashi lafiya?" ya tambaye su, a lokacin da yake zama a gabansu.
"Lafiya ƙalau." inji Barban.
Tameer ya ajiye waɗannan abubuwa dake hannunsa ya fuskanci su Barban. "Ina fatan dai, tun kafun kuzo wannan gari namu kuna da labarinsa, sannan nima kuna da labarina da kuma sharuɗɗa na?
"A wannan gari namu kowa attajiri ne, amma dukiyar da muka tara duk ta banza ce, tunda babu abinda zamu saya da ita. Duk wanda ya san garin Rildaz tabbas yana da labarin macijiya Ril, wacce take hana shiga ko fita wannan gari.
"Sannan aiki da ni yana da matuƙar tsada, tun da kun san kowa a wannan gari namu attajiri ne, da me zaku iya biyana ladan aikin da zan yi muku. Taswirar waye kuke so a zana muku?" ya ce.
Barban ya yi murmushi ya ce, "Kamar yadda muka sami labari wannan macijiya da ta addabi wannan birni naku, an gagara hallaka ta, kuma duk wanda ya hallakata zai sami babban matsayi a wannan gari, haka ne?"
Tameer ya zaro da idanu cikin tsananin mamaki yana ƙarewa su Aymanul Faris kallo, kamar ya fara fuskantar ina suka dosa. Koda yaga irin murɗewar jikin Aymanul Faris da ƴan ƙananun raunikan dake jikinsa, sai ya sha jinin jikinsa.
"Haka ne, ba ma batun samun babban matsayi ba. Anyi alƙawari a majalisar garin nan duk wanda ya kawo kan macijiya Ril shi za'a naɗa sarki." ya ce.
Barban ya yi murmushi ya ce, "Fuskar sarki Kuffuru na birnin Kufa muke so a zana mana, nawa ne ladan mu?"
Tameer ya miƙe tsaye ya ce, "Sarki Kuffuru? Ai idan ba mulkin wannan gari za'a bani ba, babu gangancin da zai sa na zana taswirar wannan mutumi."
Barban ya sake yin murmushi ya jawo wannan buhu dake gefe guda, ya buɗe buhun ya fiddo kan macijiya Ril ya miƙawa Tameer.
Cikin mamaki da kaɗuwa Tameer ya karɓi kan wannan macijiya, ya ƙura masa idanu, kamar yana shakkun anƴa shi ne kuwa?
"Shin wannan ladan ya isa yasa a zana mana taswirar fuskar sarki Kuffuru zamu ƙaro wani abu?" inji Barban cikin izza da yarda da abinda yake cewa.
"Ehem. Wannan lada yayi, amma na gode sosai da kuka kawo min kan macijiya Ril, kamar kun san burin dake raina kenan, mulkin garin Rildaz. Dan ALLAH wataran ku sake kawo min ziyara kun ji?"
Barban ya yi murmushi ya gyaɗa masa kai. "A fara wannan aiki."
Tameer ya yi murmushi ya ɗauko farar kwalba guda ya ajiye a gabansa ya ce, "Mene ne ainihin sunansa da sunan mahaifiyarsa da inda aka haife shi?"
"SUNANSA KUFFURU, SUNAN MAHAIFIYAR KABSHIYA, A DAJIN DJINN dake yankin birnin Hadriyan aka haife shi." inji Aymanul Faris.
Kamar wannan kwalba tana jin abinda yake cewa, take launinta ya koma kore.
Tameer ya sake ɗauko ɗaya kwalba farar ya ajiye a gabansa ya ce, "Shin a cikin ku akwai wanda ya taɓa ido-da-ido da shi?"
Caraf Barban ya ce, "Na taɓa ganawa dashi a lokacin gasar-jarumtaka da aka gudanar a birninsa har takobin Saiful Shiradu ta zamo mallakinsa."
Nan take wannan farar kwalba tayi wani farin haske mai kashe idanu, Tameer ya ɗauki kwalbar ya saita hasken da idanun Barban. Take hotunan fuskar sarki Kuffuru suka bayyana da yawa a cikin wannan kwalba kamar dai yadda Barban ya kalle shi.
Tameer ya ɗauki kwalaben biyu ya jijjiga su, take abubuwan dake cikinsu ya juye izuwa ruwa. Tameer ya juye ruwan akan wannan farar takarda, kamar tsafi fuskar Kuffuru ta bayyana. Dukda haka sai da Tameer ya ɗauki wannan alƙalami nasa ya yiwa fuskar gyare-gyare.
Idan ka ganta zaka rantse da Allah kace Kuffuru ne.
Tameer ya ɗauki takardar ya baiwa su Barban, su kuma, suka damƙa masa kan macijiya Ril. Nan take suka yi sallama da juna, Barban ya jefa takardar a cikin jakar tsafinsa suka yi sallama da Tameer suka tafi.
Tameer ya ce, dan Allah wataran su dawo su kalli yanayin mulkinsa. Suka amsa da to. Suka fice daga gidan.
***RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 46: *Firziyya ta zo ceto*
*
*
UMAR SANGARU
*
Tun sa'adda sarauniya Rauziyya ta watsawa yarima Marganu wannan walƙiya daga wannan lokaci, jikinsa ya mutu. Tsahon waɗannan kwanaki guda uku da yayi a cikin wannan keji wanda ta jefa shi a ciki kafun ranar da za'a yanka shi tazo, babu wanda ya sake kula shi. In banda wani irin abinci mara daɗi da ake kawo masa babu wanda yake zuwa kusa da kejin, amma a nesa da kejin akwai dakarun tsaro birjik sun zuba masa idanu.
Saboda tsananin galabaita yarima Marganu ko iya miƙewa zaune baya iya yi, kullum yana kwance a cikin wannan keji. Dama kafun a kawo shi wannan waje, sai da ya sha baƙar wahala a kurkukun azaba-uku sannan ga ƙarin wannan azaba da arnan-daji keyi masa.
Tuni Marganu ya gama sallamawa da rayuwar duniya saboda ya gama tabbatar da cewa, lallai waɗannan arnan daji yanka shi zasuyi. A ce a garinsu, kowa ba shi da burin da yafi ace gunkinsu ya sha jininsa, tayaya zai iya kuɓutar da kansa?
A cikin waɗannan kwanaki uku tunani da zulumi ya addabi Marganu. Komai ƙarfin damtsenka da jarumtakarka idan aka ce ka san ranar da za'a yi maka yankan-rago sai ka razana. Musamman ma ace anyi maka tsafi ƙarfin damtsen naka da jarumtakar taka sun tafi.
Cikin Marganu ya faɗa ciki, ƙasusuwan ƙirjinsa suka fara bayyana saboda tsabar ramewa da rashin samun abinci. Kai, komai rashin tausayin mutum idan yaga Marganu a wannan hali, dole ne ya tausaya masa.
A zuciyar Marganu ba wai baƙin cikin za'a kashe shi yake yi ba. Baƙin cikin da ya addabi zuciyarsa shi ne zai mutu ba tare da ya yiwa gimbiya Jaanu fyaɗe kuma ya kasheta ba, sannan zai mutu ba tare da ya ɗauki fansar jinin mahaifinsa da aka zubar ba. Waɗannan abubuwa guda biyu su ne suka sa nan take hawaye ya fara zubowa Marganu saboda baƙin cikin gagara cika su.
Ranar Laraba, tun da asuba yarima Marganu yaji wannan gari na arnan-daji ya ruɗe da buge-bugen ganguna da kaɗe-kaɗe. Ai kuwa nan take jikinsa ya fara tsuma, hawayen baƙin ciki suka fara zubowa daga idanunsa.
A wannan lokaci ne wani baƙin ciki ya rufe Marganu, a ce duk tsananin sadaukantakarsa da jarumtakarsa ace wai yau shi za'a yiwa yankan rago? Kuma wai ma ba'a ƙoƙarin kare ƙasarsa ko mahaifinsa wannan abu ya faru dashi ba, sai akan wata mace wacce ta wulaƙanta shi ta zubar da mutuncin birninsu.
Cikin tsananin juriya da jarumtaka Marganu ya dake ya miƙe tsaye, wani irin mugun jiri ya ɗebe shi sakamakon ƴunwar dake damunsa, bisa dole ya dafa ƙarafunan wannan keji da aka kulle shi a ciki.
Jim kaɗan ya hango waɗannan arnan-daji sun rugo wannan waje da gudu, waɗansu zaratan sadaukai guda goma aka saka su fiddo shi, nan take suka buɗe ƙofar wannan keji. Suka finciko Marganu da ƙarfi daga cikin wannan keji, sannan suka watsa masa wata hodar-sihiri take jikinsa ya sake mutuwa ya sulale ƙasa, tamkar sumamme amma ba suma yayi ba.
Ba tare da ɓata wani lokaci ba suka yayyage kayan jikinsa, suka kawo waɗansu baƙaƙen kaya

Please Login or Register in order to submit comment