Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hasanul Jalwar na gama faɗin haka ya wuce kai tsaye izuwa cikin wannan ɗaki wanda ƙofar shiga gidan ƙarƙashin ƙasa take, ya buɗe ƙofar sannan ya kunna kai izuwa cikin gidan. Yana shiga ya wuce bakin wannan ƙaton rami ya tsaya, wuta tayi feshi gangar jikin aljani Nara ta bayyana.
"A cikin falalolin takobin Saiful-Shiradu baka kalli kaso ashirin a cikin ɗari ba." inji aljani Nara.
Hasanul Jalwar ya yi murmushi ya ce, "Haka ne, amma wanne aljani ne ya ceci Kuffuru? Kuma meyasa takobin Saiful-Shiradu bata yi tasiri akan sa ba?" Nara ya yi dariya ya ce, "Maigidan sarki Kuffuru mana, wannan aljanin wanda nace maka shine ya turo shi wannan ƙauyen."
"Eh, haka ka ce min amma ai baka min bayanin aljanin ba." Hasanul Jalwar ya ce. Aljani Nara ya yi ajiyar zuciya ya ce, "A zamanin sarki Samudul Ansari, anyi wata babbar ƙabila ta aljanu da ake kira Buƙal. Waɗannan aljanu mugayen gaske ne, a nahiyar da suka bayyana akwai wata babbar ƙasa mai tarin al'umma amma kafun wata guda sai da suka baje wannan ƙasa. Wannan labari ba shi da tushe shiyasa zakaji bazai baka ma'ana ba. Amma ance sarki Samudul Ansari ne ya yaƙe su kuma ya fatattake su, a garin ne ya kamo wannan aljani wanda ake kira Shiyyu Djinn ya ajiye shi a cikin dajin Djinn domin ya yayi tsaron hanƴa. Ance shi wannan Shiyyu Djinn ɗin ya gaji da wannan aiki da sarki Samud ya saka shi, amma bai isa ya bari ba sakamakon wani asiri da Samud yayi masa. Babu mai karya wannan asiri face Samud ko kuma wanda ruhinsa ya shiga jikinsa. Wannan shi ne dalilin da yasa Shiyyu Djinn ya haɗa kai da sarki Kuffuru saboda a tunaninsa sarki Kuffuru zai iya mallakar wannan ruhi. Abinda yasa kaga wannan takobi batayi tasiri a kansa ba shi ne yana daga cikin hadiman sarki Samudul Ansari waɗanda ya barwa aiki kafun yayi ƙaura don haka akwai ƴar amana tsakanin kayan yaƙin Samudul Ansari da hadimansa."
Hasanul Jalwar ya kyaɗa kai cikin fahimta ya ce, "Yanzu meye abin yi don indai haka ne, sarki Kuffuru na da hatsari a gare mu."
******RUHIN JARUMATAKA!
*
Babi na 37: *Ƙarfi yazo daya*
*
*
UMAR SANGARU
*
Kafun sarki Kuffuru ya karasa cikin ɗakin da matarsa Anisa ke kwance yaji an kwarara wata uban tsawa tamkar tsakiyar damuna, wannan tsawa akwai abinda take yi masa nuni dashi, a duk lokacin da yaji irin wannan tsawa aljani Bukalshiyu Djinn ne keyi masa gargaɗi da wani mummunan abu dake shirin faruwa da shi.
Don haka tsayawa yayi yana ta tunani ya gagara ƙarasawa cikin wannan ɗaki wanda matar tasa take kwance a ciki, tsahon ɗan lokaci yana ta tunani shi bai ƙarasa ba kuma bai juya ba.
Har saida aka sake kwararo wannan tsawa a karo na biyu sannan ya yanke shawarar amsa wannan kira da Bukalshiyyu Djinn ke yi masa. Sarki Kuffuru ya buɗe jakar tsafinsa ya fiddo wata jar darduma ya warwareta sannan ya zauna a kanta, ya rufe idanunsa.
Nan take wannan darduma ta tashi dashi sama cikin iska suka fara gudu a cikin gajimare, suka nufi wani katon daji wanda yake jiwo wannan tsawa daga cikinsa.
Cikin yan daƙiƙu suka karasa cikin wannan daji, wanda ake kira HUSUM. Sarki Kuffuru ya nannaɗe dardumarsa ya mayar da ita cikin wannan jakar tsafi sannan ya kama dube-dube.
Wani katon tsauni daga cikin tsaunikan wannan dajin yayi girgiza ya dawo siffar aljani Buƙalshiyu Djinn. Kuffuru ya waigo ya dube shi cikin tsananin mamaki ya ce.
"Lafiya kayi min irin wannan kira cikin gaggawa haka?"
"Hasanul Jalwar da aljaninsa na nan tafe, nan da cikar rabin sa'a zasu iso wannan daji. Idan har bamu zo ni da kai mun tare su ba, tabbas idan suka ritsa mu abin ba zaiyi kyau ba. Wannan shi ne dalilin da yasa na kiraka cikin gaggawa." Djinn ya amsa.
Sarki Kuffuru ya murtuƙe fuska yayi kwafa ya ce, "Tabbas sun zo a lokacin da ya dace domin na ɗauki fansar abinda Hasanul Jalwar yayi min a watannin baya."
Rabin sa'a na cika wani irin ɗumi wanda shi kadai ya isa ya gasa nama, ya fara fesowa daga can sararin samaniya. Kwatsam! Sai ga bayyanar aljani Nara ɗauke da Hasanul Jalwar a gadon bayansa.
Sarki Kuffuru da aljani Shiyyu Djinn suka ɗaga kansu sama suka bisu da kallo kawai har suka saƙƙo. Jikin sarki Kuffuru na karkarwa sakamakon tuno baƙaƙen maganganun da Hasanul Jalwar ya faɗa masa.
Su Hasanul Jalwar suna dira aka fara kallon-kallo cikin tsananin fusata da mugun nufi.
Hasanul Jalwar ya sauƙo daga kan aljani Nara ya matso kusa da sarki Kuffuru ya dube shi, ya ce, "Matsoraci! Kana tunanin don wancan karon an kuɓutar da kai, zan ƙyaleka ne? Ai tunda ka kashe min mutane babu abinda zai hana ni sare kanka."
Koda sarki Kuffuru yaji wannan batu daga bakin Hasanul Jalwar sai ya kwarara uban ihu irin wanda ke razana kananun jarumai a filin daga, ya dakawa Hasanul Jalwar tsawa.
"Wai me kake ɗaukar kanka ne? Kada kayi tunanin don kayi nasara akaina wancan karon, yanzu ma zaka yi. Tabbas a yanzu ni murucin kan dutse ne ban fito ba sai da na shirya, amma a yanzu bazaka fuskanci hakan ba, har sai mun fara fafatawa."
Hasanul Jalwar yai dariya sannan ya zaro takobin Saiful-Shiradu daga cikin kufenta.
Nan take yanayin wannan wuri ya sauya, wani zafi mai kama da an buɗe tsohuwar rijiya ya fara fesowa. Sararin samaniya ta fara kaɗawa waɗansu jajayen gajimare masu kama da guma-guman wuta suka fara bayyana a cikinta. Ƙananun bishiyoyi dake ƙasa suka fara yonƙonewa girmansu na raguwa sakamakon zafin wannan wuta.
Fuskar Hasanul Jalwar ta sauya matuƙa, ƙwayar idanunsa ta fara ci da wuta. Gashin kansa ya fara hayaƙi ammafa ja. Wannan baƙar doguwar riga ta jikinsa ta koma jajawur kalar wuta. Waɗansu aljanu guda uku na wuta suka bayyana a bayansa suna fesar da wuta daga bakinsu suna yiwa takobin Saiful Shiradu kirari.
Sarki Kuffuru ya ƙyalƙyale da dariya shima ya zaro wannan takobi dake ɗaure a gadon bayansa wacce ake kira Siwod-del-bulod.
Nan take wani kambun sarauta ya bayyana akansa. An ƙera kambun ne da sinadarin jini sannan yana da zanen hatimai guda uku a kansa.
Hatimi na farko hoton bil'adama ne, na biyu kuma hoton sadaukin aljani ne, cikon na ukun kuma hoton zaki ne.
Hatimin dake ɗauke da hoton bil'adama ya kawo haske, take gangunan jikin bil'adama sadaukai guda goma suka bayyana amma a matsayin haske.
Hatimin dake ɗauke da hoton aljani shima ya kawo haske, take waɗansu aljanun-haske guda goma suka bayyana kowannensu zare da zabgegiyar takobi.
Hatimin dake ɗauke da hoton wannan murgujejen zakin ma yayi haske, nan take waɗansu murguza-murguzan zakuna na haske guda goma suka bayyana.
Idanun sarki Kuffuru suka kaɗa suka yi jawur, ga kambun sarauta mai ɗauke da haske guda uku a saman kansa. Ga sadaukan bil'adama masu jiki na haske guda goma tsaitsaye a bayansa, ga aljanun-haske guda goma a sama sunyi masa inuwa, ga kosassun zakuna guda goma suna kewaye dashi.
Hasanul Jalwar yayi murmushi ya ce, "Shiri mai kyau. Tabbas yanzu ne nasan na haɗu da cikakken namiji mai kyakkyawan shiri!" Yana gama faɗin haka ya kaɗa wannan takobi ta Saiful-Shiradu.
Faruwar hakan keda wuya wadannan aljanun wuta guda uku dake bayansa, suka rikide suka zamo manya-manyan mutum-mutumi guda uku. Ɗaya an halicci gangar jikinsa da zallar wuta, ɗaya kuma da zallar tafashashshiyar dalma aka yi shi, na karshen kuma da zallar baƙin ƙarfe aka yi shi. Dukkaninsu su ukun sai wani irin mugun tiriri suke bayarwa tamkar na tsohon kabari.
"Kamar yadda aka ƙirƙiri takobinka daga sinadarai guda uku." inji sarki Kuffuru a lokacin da yake nunawa Hasanul Jalwar takobin Siwod-del-bulod.
"Wannan takobi tawa ma, sinadarai guda uku gareta." yace. "Ga su nan tsaye a gabanka." ya ƙara da cewa.
"Hmm. Zan yi maganin wannan tarkacen naka," inji Hasanul Jalwar.
"GAZMUL-NARA ka tunkari waɗannan zakunan,"
"DAZMUL-NARA ka farfasa min waɗannan aljanun,"
"Kai kuma AZMUL-NARA ka fatattaka min waɗannan shashashun bil'adaman."
Hasanul Jalwar ya baiwa waɗannan mutum-mutumi guda uku nasa umarni.
Nan take waɗannan mutum-mutumi guda uku suka kwarara uban ihu suka nufi kan wannan karamar tawaga ta sarki Kuffuru. Mutum-mutumin wuta ya tunkari waɗannan zakunan, mutum-mutumin dalma kuma ya tunkari aljanu, shi ko na bakin-karfe saiya tunkari bil'adama.
Sarki Kuffuru yai dariya ya dubi waɗannan zakuna guda goma yayi musu magana da yaren tsafi, sannan ya dubi wadannan aljanu dake saman kansa ya ce, bana so wannan mutum-mutumi ya kwana a duniya. Ya juya ya dubi waɗannan sadaukan-bil'adama guda goma masu baƙaƙen kaya ya ce.
"JININ INFIRO DA ZARAR KUN GAMA DA WANNAN SHASHASHAN MUTUM-MUTUMI, INA SO KU SARO MIN KAN HASANUL JALWAR." ya basu umarni.
A ganin sarki Kuffuru ƙarfin sadaukai jinin Infiro kaɗai ya isa ya tarwatsa ƙauyen Gazwar gaba ɗayansa ba ma Hasanul Jalwar ba. Su goma mahaifinsu ya haifa kuma dukkaninsu sadaukai ne, amma da aka zo haɗa takobin Siwod-del-bulod duk kashesu akayi aka ɗauki jininsu.
Zakuna guda goma suka yi gurnani suka ruga da gudu kan mutum-mutumi GAZMUL-NARA, aljanun-haske guda goma suka afkawa DAZMUL-NARA, shi kuma AZMUL-NARA sadaukan bil'adaman ne suka kewaye shi a tsakiya, kowannensu riƙe da zabgegiyar takobi.
Sarki Kuffuru, Hasanul Jalwar, aljani Nara da Shiyyu Djinn dukkaninsu kawai idanu suka zubawa waɗannan mutum-mutumi guda uku da hadiman Siwod-del-bulod.
GAZMUL-NARA na haɗuwa da waɗannan zakuna, suka fara daka tsalle suna kawo masa wawura. Maimakon ya ɗinga kaucewa tsayawa kawai yayi a waje guda, ya daina motsawa. Zakuna guda biyu suka daka tsalle suka kawo masa haɗiya da bakunansu, yana nan kyam bai motsa ba. Bakunan suka dira akan kafaɗunsa take wuta ta kona su, irin wuta ta musamman wacce tasa suka yi bindiga suka tarwatse.
Sauran zakunan guda takwas suka tsaya cirko-cirko suna kallon-kallo da GAZMUL.
A ɗaya ɓangaren kuma tuni DAZMUL ya gama hallaka waɗannan aljanu guda goma, domin kuwa suna haɗuwa dalma tayi bindiga duk ta narka su. Faruwar hakan keda wuya hasken dake jikin hatimin aljani ya ɓace daga kambun sarki Kuffuru.
Shima AZMUL tuni ya ci karfin sadaukai jinin Infiro domin kuwa ya hallaka biyar daga cikinsu.
Haka dai aka ci gaba da fafatawa tsakanin hadiman takobin Siwod-del-bulod da kuma mutum-mutumin Hasanul Jalwar, amma abin mamaki a duk lokacin da waɗannan mutum-mutumi suka hallaka waɗannan zakuna ko aljanu ko kuma bil'adama, sai sarki Kuffuru yayi dariya ya sake gyara zaman wannan kambu akan kansa, take hatiman guda uku zasu sake kawo haske.
Aljanu guda goma su sake bayyana, hakama zakuna da sauran bil'adaman. Ga dukkan alamu dai ƙarfin wannan takobi ta Saiful-Shiradu da kuma Siwod-del-bulod yazo ɗaya.
To, amma idan mutum yana matsawa kusa da sarki Kuffuru zai fuskanci cewa hasken dake jikin wannan kambu, a duk lokacin da ya ɓace, idan yazo sake bayyana baya kai na farkon haske. Ma'ana dai yana disashewa amma a hankali, haka kuma ƙarfin waɗannan halittu guda talatin shima yana raguwa.
Hasanul Jalwar da aljani Nara basu fuskanci haka ba, amma aljani Shiyyu Djinn da sarki Kuffuru sun san abinda ke faruwa kuma tuni hankalinsu ya ɗugunzuma domin za'a kai munzalin da waɗannan haske guda sun daina kawowa idan kuwa suka daina kawowa, to tabbas waɗannan halittu guda talatin daina bayyana zasu yi. Idan suka daina bayyana tamkar sarki Kuffuru yaje ƙasa ne, saboda su ne masu kare shi daga sharrin takobin Hasanul Jalwar.
Tuni aljani Shiyyu Djinn ya baiwa sarki Kuffuru umarnin abinda ya kamata yayi.
Sarki Kuffuru yai tsalle ya dira a gaban Hasanul Jalwar hannunsa riƙe da takobin Siwod-del-bulod ya ce, "Ga dukkan alamu ƙarfin aljanunmu yazo ɗaya, meye zai hana mu fafata ni da kai gaba-da-gaba?"
Hasanul Jalwar ya dubi sarki Kuffuru da kaifafan idanunsa ya ce, "Ƙarfin aljanun mu baizo ɗaya ba, ni nasan komai daren-dadewa aljani na shine zaiyi nasara akan naka. Idan kana shakkar wannan magana tawa zaka iya jira ka gani nanda ɗan lokaci ƙanƙani. Idan kuma baza ka iya jira ba, to kazo mu gwabza domin a bambance tsakanin aya-da-tsakuwa."
Sarki Kuffuru ya riƙe takobinsa da hannu-biyu ya ce, "Kazo mu gwabza domin a bambance waye mai-ƙarfi."
Hasanul Jalwar yayi murmushi ya ɗaga takobinsa sama, hasken-rana ya haskata nanfa ta fara sheki tana kashe idanu. Sarki Kuffuru ya sake dako tsalle ya kawowa Hasanul Jalwar sara a wuya, cikin kwanciyar hankali Hasanul Jalwar ya sunkuya ƙasa, takobin sarki Kuffuru ta wuce ta sari iska. Kafun Kuffuru ya juyo tuni Hasanul Jalwar yasa takobi ya sare shi a kaurin-sawunsa. Nan take wajen ya kone, kamar an gasa shi. Sarki Kuffuru ya kwarara uban ihu sakamakon mugun zogin da shige shi.
A daidai lokacin ne kuma wadansu ɗigo-ɗigon jini guda talatin da ɗaya suka bayyana akan iska daidai wuyan Hasanul Jalwar inda sarki Kuffuru ya kai masa sara a ɗazu, nan take waɗannan ɗigo-ɗigon suka soma haɗewa a waje guda suna bayar da siffar igiya kafun Hasanul Jalwar ya gama ankarewa tuni wata siririyar igiya ta bayyana a daidai wuyansa kuma ta ɗaure wuyan nasa.
Kan kace me tuni ta fara shaƙe shi, Hasanul Jalwar ya saka hannayensa biyu yana ƙoƙarin tsinka wannan igiya amma sai yaji wayam babu wannan igiya. Shi kansa yasan ba haka bane, tabbas wannan igiya tana nan. Cikin biyu za'ayi ɗaya ko dai wannan igiya ɓacewa take, ko kuma wani sirri ne a jikinta wanda yasa hannun Hasanul Jalwar baya iya kamata.
Nan fa jijiyoyin jikin Hasanul Jalwar suka fara kukkumburowa suna burɗin-burɗin, idanuwansa suka kaɗa suka yi jawur, kuma suka fito ɓulu-ɓulu kamar zasu faɗo. Kamar yadda Hasanul Jalwar ya tsinci kansa a cikin wannan mawuyacin hali, haka shima sarki Kuffuru ya sami kansa.
Wannan kafa tasa wacce Hasanul Jalwar ya sara ta kumbura suntum, waɗansu ƙananun tsagu sun bayyana da yawa akanta suna ta zubar da ruwa. Sarki Kuffuru ya tsaya ƙyam a waje guda ya gagara motsi, saboda bai isa ya ɗaga wannan ƙafa a haka ba. Kai saboda tsananin zogin da yake ji, sai yaji kamar ma a sare wannan kafa zai fiye masa sauƙi.
Tuni Hasanul Jalwar ya durƙushe kan gwiwowinsa yana ta aman wata farar-kumfa, tabbas idan baiyi wani abu ba nan da cikar daƙiƙu ashirin mutuwa zaiyi.
To, a daidai wannan lokaci ne haske guda uku dake jikin kambun sarki Kuffuru suka bace ɓat gaba ɗayansu, take waɗannan halittu guda talatin dake fafatawa da mutum-mutumi suka ɓace ɓat! Waɗannan mutum-mutumi ma suka yi haske suka ɓace ɓat, kai kace dama can ba halittu bane iska ce.
A wannan lokaci tuni Hasanul Jalwar ya kwanta ƙasa yana ta karkarwa ransa na gab da fita, shi kuma sarki Kuffuru tuni wannan kafa tasa ta gama kumbura tamkar zatayi bindiga, ruwa da jini nata zubowa daga jikinta. In banda ihun azaba babu abinda sarki Kuffuru keyi, kuma tuni ya fita a hayyacinsa baima san halin da Hasanul Jalwar ya tsinci kansa a ciki ba.
Abin mamaki a gefe guda ma, aljani Bukalshiyyu Djinn da aljani Nara ne durƙushe akan gwiwowinsu suna ta amai. Kai da gani ka san cewa sun sha wahala sosai sakamakon amfani da ƙarfinsu da akayi.
Kwatsam! Hasanul Jalwar na karkarwa kawai sai yaga bayyanar haske guda uku sun kama wannan igiya data shaƙe shi sun tsitstsinkata, faruwar hakan keda wuya yaji numfashinsa ya dawo kuma wuyansa ya daina yi masa ciwo. Amma dukda haka bai iya miƙewa koda zaune ba.
A bangaren sarki Kuffuru ma tuni wannan kafa tasa ta daina yi masa zogi amma bai iya motsata, sakamakon wannan mugun kumburi da tayi. A takaice dai sun kuɓuta daga wannan mugun-hari da kowanne ya yiwa ɗan-uwansa amma ƙarfinsu ya ƙare, a wannan lokaci baza su iya komai ba, hakama aljanunsu.
Da ƙyar da siɗin-goshi aljani Buƙalshiyyu Djinn ya samu ya ɗauke sarki Kuffuru ya tashi dashi sama suka lulluƙa cikin gajimare, shima aljani Nara ya ɗauke Hasanul Jalwar suka tashi sama suka nufi ƙauyen Gazwar.
Saida kowannensu yayi jiyya ta tsahon watanni bakwai sannan suka warke sumul, ai kuwa suna warkewa Hasanul Jalwar ya baiwa aljani Nara umarnin sake kaiwa sarki Kuffuru hari. A wannan rana ma a cikin wannan katon daji suka hadu aka sake gwabzawa, abinda ya faru a faro dai shi ne ya sake faruwa wato ragas aka yi.
Suka sake komawa suka yi jiyya ta tsahon watanni bakwai sannan suka sake dawowa suka kuma gwabzawa amma a wannan karon ma ragas aka sake yi.
Haka dai Hasanul Jalwar da sarki Kuffuru suka yi ta gwabza yaƙi lokaci-lokaci amma babu wanda ya taɓa samun nasara akan ɗan-uwansa a kullum ragas suke yi. Sai da suka gwabza yaƙi sau ashirin da shida sannan suka haƙura, saboda sun san cewa baza su taɓa samun nasara akan juna ba.))
A daidai wannan wuri ne Aymanul Faris yazo ƙarshen wannan littafi wanda Barban ya ce ya karanta a cikin sati guda. Aymanul Faris ya rintse idanunsa yana ta tunani, tabbas karatun wannan littafi yayi masa amfani sosai ba kaɗan ba. Ya gano mece ce takobin Saiful Shiradu kuma yaji tarihin sarki Kuffuru da irin muguntar da yayi a ƙauyen Gazwar sannan kuma uwa-uba yaji dalilin da yasa mahaifinsa ya ce, ya tabbatar da cewa ya sare kan sarki Kuffuru. A wannan lokaci tuni dare ya gama rabawa, don haka kawai saiya rufe littafin sannan ya fara barci. Saboda washe garin-gobe ne maigida Barban zai dawo ya ɗauke shi.
*****RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 38: *Kurkukun Azaba-uku*

*
UMAR SANGARU
*
Lokacin da sarki Ratanam tare da sadauki Ashram suka fito daga cikin birnin Damashkar, bayan sun gama tattaunawa da su sarki Ayubul Zairiy wacce ƙarshenta baiyi musu dadi ba, sai suka yanki daji suka ci gaba da tafiya a cikin keken dokinsu suka tasarwa birninsu - birnin Hirtoliya.
Sarki Ratanam na zaune a cikin keken dokin, ya sunkuyar da kansa ƙasa hawaye masu zafi nata zuba akan kumatunsa musamman idan ya tuno irin halin da yarima Marganu ya shiga a yayin karɓo gimbiya Jaanu da kuma halin da yake ciki a yanzu a kurkukun azaba-uku sai ransa ya ɓaci zuciyarsa ta ci gaba da tafarfasa.
Sadauki Ashram ya dafa kafaɗarsa, Ratanam ya ɗago kai suka haɗa idanu. Sadaukin ya ce, "Ya shugabana, kuka ba naka bane. Tozartawa dai, an riga an tozarta mu, tunda aka wulaƙanta mana yarima. Yanzu abinyi shi ne muyi magana akan abinda ya kamata mu fara tunkara? Shin gidan kurkukun azaba-uku zamuje mu kuɓutar da Marganu? Ko kuma shirin-yaki zamuje muyi da sarki Ayubul Zairiy tunda ya bamu kunƴa a idon-duniya?"
Sarki Ratanam na jin waɗannan kalamai na sadauki Ashram ya goge hawayen idanunsa sannan ya sake sunkuyar da kai ya faɗa kogin tunanin abinda ya kamata yayi. Tabbas maganar da sadauki Ashram yazo da ita abar dubawa ce, cikin biyu dole ayi daya; ko dai su kubutar da rayuwar Marganu ko kuma su yiwo shirin yaƙi su ruguje birnin sarki Ayubul Zairiy.
Tsahon ɗan lokaci sarki Ratanam na ta tunani kamar ba zai ce komai ba, daga can sai ya ɗago kai ya ce, "Ni na san waye ne sarki Ayubu, tabbas tunkararsa da yaƙi a yanzu ba shi ne mafita ba. Haka kuma tabbas kuɓutar da ɗana Marganu daga kurkukun azaba-uku ba zai haifar mana da komai ba face tashin-hankali da fushin sarki Kuffuru wanda a ƙarshe zai iya janƴo sanadiyar rasa rayuwata, rayuwar ɗana da kuma ƙasata da al'umata baki ɗaya. Wannan al'amari ne wanda ba zan iya yanke hukunci a yanzu ba, tabbas ina buƙatar lokaci na yanke hukuncin abinda ya kamata mu yi."
Koda sadauki Ashram yaji haka saiya murtuƙe fuska ya ce, "Haba ya shugabana, wulaƙancin yayi mana yawa. Na farko mun ɓata wajen shekaru goma muna zuwa birnin Damashkar neman auren gimbiya Jaanu amma a ƙarshe an wulakanta mu. Na biyu an kama yarima mai jiran gado na birninmu an kaishi gidan kurkuku waɗansu ƙasƙantattun sadaukai sun wulakatan shi. Na uku sarki Ayubu wanda ya kamata ya haɗa kai damu ya taimaka mana wajen ganin anyi abinda ya dace wajen kwato Marganu daga kurkuku, amma ya haɗa kai shi da ƴarsa ta nuna mana bata ƙaunar Marganu domin kada mu sake zuwa birninsu. Kaga kenan, kamar sunyi amfani da Marganu ne sun cimma burinsu sannan sun watsa mana ƙasa-a-ido."
Waɗannan kalamai na sadauki Ashram suka ratsa sarki Ratanam sosai, ya sake sunkuyar da kansa yana tunani. Tabbas duk abinda Ashram ya faɗa gaskiya ne, wato sarki Ayubul Zairiy kamar yayi amfani da Marganu ya cimma burinsa yanzu kuma yana ƙoƙarin zare kansa don kada sarki Kuffuru ya zargi wani abu. Saboda wannan hangen-nesa da hikima ta sadauki Ashram shiyasa sarki Ratanam ke zuwa da shi duk inda zaije.
"Ina tunanin fara karya mulkin sarki Ayubul Zairiy zai fiye mana sauƙi akan kuɓutar da rayuwar Marganu," inji Ratanam. "Saboda a yanzu idan muka yi wani yunƙuri na kuɓutar da Marganu, idan fa bamuyi nasara ba sarki Kuffuru da sarki Ayubu haɗa kai zasuyi su yaƙe mu gaba daya. Amma idan aka ce mun karya mulkin sarki Ayubu ƙasarsa da sojojin yaƙinsa duk zasu dawo ƙarƙashin mulkina kaga kenan a cikin ruwan-sanƴi zamu kuɓutar da rayuwar Marganu."
Sadauki Ashram ya jinjina kai alamun ganewa ya ce, "Wannan hukunci da ka yanke yayi daidai ya shugabana, amma ina ganin kamar munyi gaggawa a yanzu bamu san cikin wanne hali yarima Marganu yake ba. Kamata yayi a ce mun fara dubo halin da Marganu ke ciki sannan sai mu yanke hukunci."
Cikin mamaki da jinjina sarki Ratanam ya dubi sadauki Ashram ya ce, "Tabbas ka kawo shawara mai kyau kuma abar dubawa, amma idan na fuskance da kyau so kake kace muje kurkukun azaba-uku dubo Marganu, haka ne?" Sadauki Ashram ya gyaɗa kai ya ce, "Kwarai ma kuwa, kuma daga nan nake so mu wuce zuwa kurkukun."
Sarki Ratanam yayi murmushin takaici ya ce, "Tabbas na fuskanci cewa baka san ina ne kurkukun azaba-uku ba shiyasa kake ganin zamu iya zuwa a kowanne lokaci kuma cikin sauƙi. Bari nayi ma bayani kaɗan daga cikin bayanan kurkukun azaba-uku, wai shin ma kasan meyasa ake ce mata azaba-uku?
"Sunan tsaunin da aka gina kurkukun azaba-uku a samansa Duksum, Duksum sunan wani ƙaton aljani ne mai gangar jiki guda uku. Jikin wannan aljani yana da gangar jiki guda uku, kuma kowanne gangar jiki yana da kai, hannaye da fuka-fuki. A taƙaice dai wannan aljani halittu guda uku ne a haɗe a waje guda.
"An gina wannan kurkuku da zallar dutsen-wuta irin wanda aka gina kurkukun-mutuwa dashi, sannan an gina katanga mai tsahon kamu metan. Ko aljani bai isa ya tsallaka wannan katanga ba, idan ba shi da fuka-fuki.


Please Login or Register in order to submit comment