Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ɗago kai ya ƙurawa sarki Ayubul Zairiy idanu.
"Wannan ita ce ladar tarɓa da kuka yi min," inji sarki Ayubu. "Idan aikin mu da ku ya kammala akwai kyauta ninkin wannan sau huɗu."
Ɗan-fashi Kauzur ya bushe da mahaukaciyar da dariya, ya miƙe tsaye ya doki ƙirjinsa da hannaye biyu ya ce, "Faɗi duk aikin da kake so a yi maka. Na rantse da wannan tsohuwar sana'a tawa zamuyi shi. Dama zaman me muke yi a cikin baƙin-dajin nan? Dukiya muke son tarawa, na tabbata idan muka mallaki wannan dukiya da ka ambata mun gama zama gawurtattun attajirai."
Ba tare da ɓata lokacin komai ba, sarki Ayubu ya zayyanewa ɗan-fashi Kauzur wannan shiri nasa wanda suka gama tattaunawa da shi da aljani Jizid.
Ɗan-fashi Kauzur ya ƙyalƙyale da dariya ya ce, "Ban taɓa tunanin wannan shiri naka zaizo da sauki haka ba. Shi kenan, je ka abinka kawai ka zuba idanu tabbas zamu gama wannan aiki kamar yadda kake bukata."
Wannan shi ne usulin yadda aka yi sarki Ayubul Zairiy ya haɗawa sarki Ratanam tuggu, wanda ga dukkan alamu bai isa ya tsallake ba.
****
KURKUKUN AZABA-UKU.
****
Kamar yadda muka ji tattaunawa ɗazu a bakin sarki Ratanam da sadauki Ashram akan bayanan kurkukun azaba-uku zamu fuskanci cewa wannan kurkuku ce mai tsananin tsaro. To, bari muyi duba izuwa ga wannan kurkuku.
Ƙaton tsauni ne mai samfurin ƙasa ruwan-toka. A jikin wannan tsauni akwai ƙananun bishiyoyi wanda suka ɗan sauya masa launi izuwa kore-kore. A ƙiyasi tsahon wannan tsauni zai iya kai kamu metan sau uku, wato dai wanda ke can saman wannan tsauni zai na hango abinda ke ƙasa mini-mini.
A jikin tsaunin kuma an gina wata matattakala ta bene wadda tayi sama daga ƙasa, sannan kuma akan wannan matattakala sojoji ne a tsaitsaye layi-layi riƙe da zabga-zabgan takubba.
A can saman tsaunin kuwa, wani ƙaramin gini ne wanda aka yiwa samfurin da'ira. Dakarun tsaro dake wannan wuri kuma, yadda ka san tururuwa haka suke saboda tsananin yawansu.
Kwatsam! Kamar daga sama sai waɗannan tarin dakaru suka hango wata runduna ta waɗansu sadaukai daga can yammacin wannan daji. Amma na saman wannan tsauni ne suka hango rundunar, su na ƙasa basu hangota ba saboda nisan tazarar dake tsakaninsu.
Nan take ɗaya daga cikin dakaru na saman wannan tsauni, ya haye kan wani tudu ya zaro dogon ƙaho daga cikin wandonsa ya kafa a bakinsa sannan ya ɗaga sama ya fara busawa da ƙarfi. Kan kace me tuni ƙarar wannan ƙaho ta cika wannan daji gaba ɗaya.
Dakarun dake ƙasa na jin ƙarar wannan ƙaho, suka fara jeruwa sahu-sahu suna fiddo makaman yaƙinsu. Su kuma waɗanda suke sama sai suka fara saƙƙowa daga saman tsaunin su ma suna fiddo makaman yaƙin su.
Kafun ka ce kobo, tuni waɗannan dakaru dake tsaron wannan kurkuku sun gama haɗuwa a waje guda sun bayar da gagarumar runduna ta gawurtattun sadaukai.
Shugaban waɗannan dakaru ya kafa hannu a saman idanunsa ya hanga, ya murtuƙe fuska ya juyo ya dubi dakarun dake tsaitsaye a bayansa ya ce, "Ga dukkan alamu waɗancan mutane da muke hangowa daga birnin Hirtoliya suke, don naga kalar suturar sojojin Hirtoliya ne a jikinsu. Sannan kuma naga kamar akan giwaye suke, ko shakka babu wannan yaron suka zo kuɓutarwa amma sarki Ratanam yayi ganganci."
Shugaban dakarun na gama faɗin haka ya fiddo takarda da alƙalami ya rubuta wasiƙa ya baiwa wani badakare yace ya kaiwa sarki Kuffuru.
A daidai lokacin ne kuma wannan runduna ta ƙaraso ƙofar wannan kurkuku. Sadaukai ne aƙalla guda dubu goma, sanye cikin shudin-sulke mai hatimin birnin Hirtoliya a ƙirjinsa. Gaba ɗaya sadaukan fuskokinsu a rurrufe suke da baƙaƙen rawani, iya idanuwansu kaɗai ake kallo.
Shugaban dakarun dake tsaron wannan kurkuku ya dakawa wannan runduna tsawa. "Kai! In banda rashin basira irin taku, don kun rufe fuskokin ku zamu gagara gano ku ɗin su wane ne? Kuna tunanin wannan ƙaramar runduna taku zata sa mu saki Marganu ne?"
Koda yazo nan a zancensa sai ya matsa gaba kaɗan, kusa da shugaban waɗannan dakaru masu rufaffiyar fuska. "Ga dukkan alamu kaine sarki Ratanam. Kayi gaggawar barin wannan wuri sannan kaje fadar sarki Kuffuru ka bashi hakuri. Wataƙila idan kayi hakan zai fasa sare kanka..."
Kafun shugaban waɗannan dakaru ya gama rufe bakinsa tuni wannan sadauki dake tsaye a gaban yan-fashin ya zaro wani gajeren mashi daga kunkuminsa ya jefi shugaban waɗannan dakaru da shi. Nan take mashin ya soke shi a goshinsa ya ɓullo ta ƙeyarsa, take ya zube ƙasa matacce ko shurawa baiyi ba.
Koda waɗannan dakaru suka ga an kashe shugabansu sai suka afkawa waɗannan ƴan fashi aka fara gwabza gumurzun yaƙi. Tsahon sa'a goma aka ɗauka ana gwabza wannan mummunan yaƙi sannan yazo ƙarshe.
A cikin waɗannan dakaru dubu tamanin dake tsaron wannan kurkukun daƙyar mutum dubu ashirin suka tsira da ransu. Su kuma waɗannan ƴan-fashi guda dubu goma bai wuce mutum ɗari biyar kacal suka yi saura ba. Ana cikin gumurzun sadauki Kauzur ya zaro ƙaho ya busa, take shi da waɗanda suka rage suka ruga da gudu bisa giwayensu suka ɓace a cikin ƙungurmin daji.
Idan ka dubi wannan wuri babu abinda zaka gani face gawarwakin dakaru a kwakkwance a ƙasa fululu, jini kuma yadda ka san ruwa haka yake ta gudu.
****
A can birnin Damashkar kuwa, sarki Ayubul Zairiy ne ya bushe da dariyar farin-ciki. Ya shafi madubin tsafinsa da hannun hagu hoton komai ya ɗauke.
"Wasa yazo ƙarshe," ya ce. "Ratanam ka gaishe da na lahira irin su kakanmu Asasinu."
Yana gama faɗin haka ya fice daga cikin ɗakin-tsafin sa ya nufi fadar birninsa.
Abin mamaki a wannan rana, fadar a cike take maƙil da tarin al'umma. A tsakiyar fadar kuwa bisa wani tudu wata makekiyar karaga ce ta mulki aka ajiye, a gefen karagar kuma ƙananun kujeru ne amma na alfarma.
A ɓangaren dama ga gimbiya Jaanu a zaune akan wata kujera ta zinari, ta sanƴa baƙaƙen tufafi masu ado da zinari. Gashin kanta jajawur na ta haske da sheƙi musamman idan rana ta haska shi. A ɓangaren hagu kuma boka Ruguzan ne da sauran fadawan sarki.
Ana zaune cikin wannan hali ne sarki Ayubu ya shigo cikin wannan fada, fuskarsa cike da annuri. Gaba ɗaya jama'a suka miƙe tsaye cikin girmamawa har sarki yaje ya zauna akan karagar mulki sannan aka zazzauna aka yi tsit, kai kace mutuwa ce ta gifta.
Sarki Ayubul Zairiy ya yi murmushi ya fara jawabi da cewa.
"Ya ku jama'ata, kuyi sani cewa ba don komai na taraku ba sai domin na sanar da ku cewa, a yau-yau ɗinnan zan tafi birnin Sin. Zanje wajen sarki Kim Sam na kai masa ziyara. Daga yau na bar ƙasata a hannun ƴata JAANU, duk wanda yayi mata biyayya ya tsira, wanda duk ya saɓawa umarninta ya halaka. Koda ba ma nan akwai hadiman aljanu da zasu na saka idanu akan komai."
Sarki Ayubu na gama faɗin haka ya miƙe tsaye ya kamo hannun gimbiya Jaanu, ya fidda kambun-sarautar dake kansa ya ɗaura mata akanta. Mutanen birnin Damashkar na ganin haka, suka sunkuyar da kansu cikin biyayya da mubaya'a ga gimbiya Jaanu.
Boka Ruguzan ya gyara wuyan rigarsa ya ɓace ɓat. Sarki Ayubu ma na ganin haka ya yi girgiza ya ɓace ɓat.
******RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 40: *Faɗuwar sarki Ratanam*
*
*
UMAR SANGARU
*
~Kogon Hubbaz.
~Birnin Hadriyan.
*
Boka Hubbazu ya yi murmushi ya ce, "Dole ne mu sake saurarawa tsahon kwanaki uku, domin Sheezuwa yaje ya sake yin bincike akan yadda zamu kamo wannan ɓarawo."
"Ba zai yiwu ba!" inji sarki Kuffuru.
Boka Hubbazu ya sake yin murmushi ya warware wannan taswira ya saka hannunsa guda, ya fara zuƙota tana ƙara girma. Kuma daidai inda yake zuƙowa ɗin, a nan wannan koren-haske yake.
Sannu-a-hankali garin Jildaz ya bayyana, amma bisa mamaki sai hoton garin ya fara komawa hazo-hazo ta yadda basa iya shaida a wacce unguwa Hodon yake, kuma sai wannan koren haske ya ɗauke gaba ɗaya tamkar baya garin.
Boka Hubbazu ya bushe da dariya ya ce, "Kana tunanin idan ka tafi da wannan taswira a haka zaka iya kamo Hodon ne? Inda ace Hodon zai ganu cikin sauƙi haka da tuni an jima da kama shi a cikin shekaru goma. Babban matsafi ne. Mutum ne mai tsananin hikima da basira."
Sarki Kuffuru ya yi ajiyar numfashi ya ce, "Yadda duk nake tunanin Hodon ya wuce nan, tabbas ban isa na iya kamo wannan mutumi ni kaɗai ba. Yanzu mene ne abin yi?"
"Nagode da ka fahimce ni. Yanzu ka koma birninka sai bayan kwanaki uku ka dawo, domin mu ji amsar da aljani Zuwa zai bamu akan hanƴoƴin da za'a bi wajen kamo Barban." boka Hubbazu ya amsa masa.
Sarki Kuffuru ya miƙa hannu zai karɓi wannan taswira amma sai ya haɗa idanu da ƴarsa, take tayi masa alamar kada ya ce zai karɓi taswirar.
Nan dai suka yi sallama da boka Hubbazu akan sai bayan kwanaki guda uku zasu dawo domin jin amsar aljani Sheezuwa. Sarki Kuffuru ya kama hannun gimbiya Firziyya suka fice daga cikin wannan kogo.
Wannan shi ne yadda aka yi muka kalli sarki Kuffuru a fadar birninsa lokacin da wannan manzo ya kai wasiƙa.
***
~Birnin Kufa
***
Tuni gagarumar runduna ta sadaukai ta fara haɗuwa domin cika umarnin sarki Kuffuru na zuwa birnin Hirtoliya domin saro kan sarki Ratanam.
A wannan rana da yammaci, sarki Kuffuru da ƴarsa gimbiya Firziyya suna zaune a cikin fada suna tattaunawa akan yadda wannan yaƙi zai kasance. Kamar daga sama sai suka jiwo sukuwar doki da gudu, a fusace sarki Kuffuru ya kallo bakin ƙofa domin ganin mai shigowa.
Nan take wannan sadaukin ya shigo wanda shugaban kurkukun azaba-uku ya aiko da wasiƙa. Sarki Kuffuru na ganin wannan sadauki ya murtuƙe fuska kuma ya miƙe tsaye, sadaukin na ƙarasowa ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa kuma ya fiddo wannan wasiƙa da aka bashi ya miƙawa sarki Kuffuru.
Sarki Kuffuru na gama karanta wannan wasiƙa, ya fice daga cikin fadar da sauri. Gimbiya Firziyya ta kamo wannan sadauki dake durƙushe a ƙasa ta ce, "Mene a cikin wannan wasiƙa?" Sadaukin ya amsa, "Ni kaina ban san mene ne a cikin wannan wasiƙa ba, amma dai shugabana ne ya bani ita a lokacin da dakarun sarki Ratanam suka kawo mana hari a kurkuku"
Gimbiya Firziyya tayi jifa da sadaukin gefe guda sannan ta bi bayan sarki Kuffuru da sauri, tana zuwa ta iske shi acan saman wani dogon mumbari ya tara dukkanin waɗannan dakaru nasa.
"Shirin wannan yaƙi ya sauya, a yau-yau ɗinnan zamu tafi birnin Hirtoliya amma dakaru guda dubu ɗari kacal nake buƙata. Sauran dakaru kuma nagode bisa amsa kirana da kuka yi." Wannan shi ne abinda Firziyya ta fara ji daga bakin mahaifinta, Kuffuru.
Sarki Kuffuru na gama faɗin haka ya saƙƙo daga saman wannan mumbari, ya kirawo sarkin-yaƙinsa ya ce, a zaba masa dakaru guda dubu ɗari zaƙwaƙurai. Sadaukin ya zube ƙasa cikin biyayya sannan ya juya ya nufi inda waɗannan dakaru suke.
Gimbiya Firziyya ta ƙaraso gaban sarki Kuffuru ta ce, "Haba ya abbana, yanzu yamma ta gama yi. Na tabbata kafun mu isa birnin Hirtoliya sai mun kai dare, meye zai hana mu bari sai gobe da safe?"
Sarki Kuffuru ya yi dariya ya ce, "Ke yarinƴa ce shiyasa. Kiyi sani cewa ba'a taɓa zaki a zauna lafiya. Tunda Ratanam yayi mana tsaurin-ido babu abinda zai hana mu saro kansa sannan na sare kan ɗansa, Marganu."
Sarki Kuffuru na gama faɗin haka ya wuce izuwa inda waɗannan dakaru suke, ita kuma gimbiya Firziyya cikin gidan sarautar ta koma. Ga dukkan alamu bata da niyyar bin Kuffuru wannan yaƙi.
Cikin ƙanƙanin lokaci sarkin-yaƙin sarki Kuffuru ya gama zaɓo sadaukai guda dubu ɗari, zaratan gaske. Bayi suka kawowa kowanne sadauki doki, nan take suka hau dawakan kuma suka jeru a sahu-sahu.
Rana na gab da faɗuwa sarki Kuffuru ya jagoranci wannan runduna ta sadaukai dubu ɗari suka nufi hanƴar birnin Hirtoliya.
Idan ka hange su daga nesa zaka ɗauka baƙar guguwa ce mai tarwatsa maƙiya, saboda tsananin yawansu har sun tokare da ƙarshen dajin.
***
~Birnin Hirtoliya
***
Iska mai sanƴi ce ke kaɗawa tamkar tsakiyar hunturu, lokacin sarki Ratanam ya buɗe idanunsa daga wannan doguwar suma da yayi. Take yaji kansa yayi wani irin mugun nauyi sakamakon kumburin da yayi. Da ƙyar ya iya miƙewa zaune ya ƙarasa kan sadauki Ashram ya fara jijjiga shi domin ya tashi su shiga cikin wannan birni.
Amma ina, tuni jikin sadauki Ashram ya gama yin sanƴi tamkar wanda aka saka a cikin ƙanƙara, haka kuma fatarsa ta fara yin fari-sol. Koda sarki Ratanam ya lura da yawan jinin da ya zuba daga jikin sadauki Ashram sai ya tabbatar da cewa lallai ya mutu.
Sarki Ratanam ya taƙarƙare ya kwarara uban ihu mai firgitarwa da amsa kuwwa, ihun nasa ya cika wannan waje har cikin birninsa sai da aka jiwo. Ratanam ya rungume gawar sadauki Ashram ya fashe da kukan baƙin-ciki na rashin babban abokinsa kuma mai ba shi shawara.
Tsahon ɗan lokaci shima kansa ya buga ya sake sulalewa ƙasa sumamme.
Lokacin da ya farfaɗo saiya tsinci kansa kwance akan gadon mulkinsa, kuyangi sun kewaye shi suna ta yi masa fifita. Sarki Ratanam ya ɗinga kallon fuskokinsu ɗaya bayan ɗaya yana nazarinsu.
Idan ya kintata daidai gaba ɗaya waɗannan kuyangi dake cikin wannan turaka tasa, a cikin jimami da tsoro suke. Abinda ya ɗaure masa kai shi ne tsoron me suke? Ko kuma jimamin me suke? Shin dakarunsu da aka kashe suke yiwa jimami ko kuma tsoron kada waɗannan yan-fashi su sake kawo farmaki suke?
Sarki Ratanam na shirin tambayarsu, wazirinsa ya shigo cikin turakar riƙe da wata wasiƙa a hannunsa. Sarki Ratanam na ganin wannan wasiƙa gabansa ya faɗi, zuciyarsa ta buga da ƙarfi. Ya tashi zaune ya jingina bayansa da ƙarshen gadon sannan ya sallami dukkanin kuyangi dake cikin wannan turaka.
Kuyangin na gama ficewa waziri ya zauna kusa da sarki Ratanam ya ce, "Ya jikin naka?"
"Da sauki." inji Ratanam.
Wazirin ya ce, "Ya shugabana, wanne ganganci kake da rayuwarka? Meyasa kake son jefa kanka cikin masifa da bala'i, harma kake son jawowa mutanen ƙasar nan? Shin kafi kowa ɗa ne a duniya, don an wulaƙanta ɗanka shi aka fara wulaƙantawa ne? Ko kana tunanin duk bala'in da ɗanka yake ciki ba shi ya jawowa kansa ba?..."
Cikin rashin fahimta sarki Ratanam ya dakatar da waziri ya ce, "Ni fa ban gane ina ka dosa ba. Me kake so ka ce?"
Waziri ya haɗe fuska ya ce, "Ka manta manzon da ka turawa sarki Kuffuru ne tare da wasiƙa?"
"Manzo kuma?" inji sarki Ratanam a fusace.
Waziri ya yi murmushin takaici ya ce, "Kwarai ma kuwa. Yanzu ga shi can ya aiko kan wannan manzo tare da wannar wasiƙar." Ya miƙawa sarki Ratanam wannar wasiƙar. Hannayensa na karkarwa ya karɓi wasiƙar ya karanta ta gaba ɗaya.
"Kan uba!" inji Ratanam. "Na rantse da kabarin babana, tuggu aka shirya min. In ma dai sarki Kuffuru ne ke son kawar dani ko kuma wani maƙiyin nawa ne dabam."
Waziri ya ce, "Yanzu mene ne abin yi ka san dai babu abinda zai hana sarki Kuffuru kawo mana hari."
"Muje naga kan wannan manzo da ya kai wannan wasiƙa, domin nikam ban aiki kowa ba." inji sarki Ratanam lokacin da ya tashi tsaye daga kan wannan gado.
Ba su tsaya a ko'ina ba sai a cikin ɗakin-gani inda sarki Ratanam ke ganawa da ƴan-majalisarsa musamman idan muhimmin abu irin wannan ya taso. Suna shigowa cikin ɗakin, suka iske dukkanin manƴan wannan ƙasa zazzaune sunyi jugum-jugum. A bisa wani teburi kuma kan wannan manzo ne da aka sarewa kai a birnin Kufa aka ajiye.
Ƴan-majalisa na ganin sarki tare da waziri suka mimmiƙe tsaye gaba ɗayansu cikin girmamawa, ko kallonsu sarki Ratanam baiyi ba, ya wuce kai tsaye izuwa inda wannan dungulmin kai yake. Ya ɗaga dungulmin kan ya kura masa idanu, tsahon ɗan lokaci kafun daga bisani ya juyo ya dubi waziri da ƴan-majalisarsa.
"Shin a cikin ku akwai wanda yasan wannan manzo, wanda ya kaiwa sarki Kuffuru wasiƙa?" sarki Ratanam ya tambaye su.
Waziri ya murtuƙe fuska ya ce, "Haba ya shugabana, ya za'ayi mu san wannan manzo naka? Mu fa ba maganar wannan manzo ba ce ta tara mu a nan, mun taru ne domin muyi magana akan yadda zamu ɓullowa wannan yaƙi. Kun san cewa ko mun ƙi ko mun so sai sarki Kuffuru yazo wannan birni namu tare da sojojin yaƙinsa."
Sauran ƴan-majalisu suka gyaɗa kai cikin amincewa da maganganun waziri. Sarki Ratanam ya ƙarasa kan wannan karaga tasa ya zauna ya dube su gaba ɗaya yace, "A yi shirin yaƙi. Tuggu dai an riga an shirya mana, yaƙi kuma babu makawa saiya afku. Abinda ya kamata shi ne muyi ƙoƙarin kare kanmu." Yana zuwa nan a zancensa ya juya ya dubi sarkin-yaƙi.
"A YI SHIRIN GWABZAWA!!!" Yana faɗin haka ya tashi ya fita daga cikin ɗakin-taron.
Daga wannan lokaci sarkin-yaƙi yaje ya buga gangar-yaƙi, nan take dakaru suka soma taruwa a ƙofar fada. Da wannan jama'ar birnin Hirtoliya suka soma shirye-shiryen yaƙi da sarki Kuffuru wanda basu san makasuɗin haddasa shi ba, sun dai san cewa ya aiko wasiƙar-raddi mai zafi tare da kan wani manzo.
***
Sarki Kuffuru da rundunarsa ta sadaukai dubu ɗari, basu iso birnin Hirtoliya ba sai da tsakiyar dare. Suna isowa sarki Kuffuru ya baiwa waɗannan dakaru umarnin a kewaye birnin Hirtoliya gaba ɗaya, nan take suka cika umarni suka saka birnin Hirtoliya a tsakiya Sarki Kuffuru ya bayar da umarnin a yiwa birnin Hirtoliya ruwan-kibbau masu ci da wuta.
Nan take ƴan-baka kimanin mutum dubu goma sha-biyar suka fiddo kwari da bakansu, suka fara ɗana kibiyoyi masu ci da wuta, suna harbawa cikin birnin Hirtoliya. Kibiyoyi masu tsananin yawan gaske suka fara tashi sama cikin iska, suna dira a cikin birnin Hirtoliya.
Waɗannan ƴan-baka sun ƙware matuƙa a iya harbi, kuma suna da tsananin zafin nama. Kafun kace me wannan tuni sararin samaniyar birnin Hirtoliya ta cika da kibiyoyi masu tsananin yawan gaske. Saboda tsananin yawansu idan kaga kibiyoyin a sama zaka yi tsammanin taurari ne a daren wata goma sha-biyu.
Bisa rashin sa'a waɗansu kibiyoyi masu yawan gaske, suka fara dira a sansanin da sarki Ratanam yake ajiye ɗanyen-mai wanda suke makamashi dashi. Ai kuwa kibiyoyi masu wuta kimanin guda ɗari na dira akan waɗannan gangunan-mai, suka fara yin bindiga suna haifar da wata jar-wuta mai tsananin zafi.
Tuni mutanen birnin Hirtoliya sun gama farkawa a firgice, mazajen-fama na zuwa fada, suna shirin tarar wannan baƙuwar da basu san ko su wane ne ba. Su dai a saninsu sarki Kuffuru sai bayan kwanaki biyu zai iso.
Kafun kace me wannan, tuni gagarumar wuta ta kama ci a cikin birnin Hirtoliya. Sannan kuma ƙarar fashewar waɗannan ganguna ta soma yawaita.
Mutane da ke ta guje-guje da iface-iface kuma waɗannan kibbau masu ci da wuta suka fara dira akan su suna hallaka. Haka kuma wannan wuta dake ci a sansanin wannan ɗanyen-mai ta fara yin tsalle tana dira akan gidajen mutane tana haifar da gagarumar gobara, mutane suka fara babbakewa suna mutuwa.
Tunda mutanen birnin Hirtoliya suke basu taɓa ganin gagarumin bala'i irin na wannan dare ba, amma inda ace sun san bala'in da zai biyo bayan wannan, da sun gwammace basu wanzu a wannan birni ba.
Sarki Kuffuru ya bayar da umarnin a karya ƙofar birnin Hirtoliya sannan a afka cikin birnin da ƙarfi, duk wanda ya tsaya akan hanƴarsu su kashe shi, daga nan kada su tsaya a ko'ina sai a fadar sarki Ratanam.
Dakaru suka yi kuwwa, suka daƙƙo waɗansu manƴa-manƴa guma-guma itace, kamar mutum ɗari sai su rike gungume ɗaya. Idan suka ja baya, sai su taho da gudu su doki ƙofar da ƙarfi. Dukda haka saida suka ɗan ɗau lokaci kafun wannan ƙofa ta karye, ta faɗi cikin birnin Hirtoliya ta haifar da gagarumar ƙara.
A daidai lokacin ne kuma, rundunar sarki Ratanam ta iso wannan waje. Da yake da tsakar-dare aka kawo musu wannan farmaki, kuma basu gama shiryawa ba, gaba ɗaya yawansu bai wuce dakaru dubu ɗari uku ba.
Ko cacar baki waɗannan rundunoni guda biyu basu yi ba, suka afkawa juna da mummunan yaƙi. Nan fa ihun mazaje, karafkiyar ƙarafa gami da kururuwa ta yawaita a wannan waje.
Mutanen da sarki Kuffuru ya taho dasu zaɓaɓɓu ne, kuma gawurtattun sadaukai ne. Ana matuƙar ji dasu a birnin Kufa, musamman sarki Kuffuru ya basu horo na musamman kuma ya tsuma da tsumin-tsafi mai ƙarfin gaske.
Amma dakarun sarki Ratanam gama-garin dakaru ne waɗanda basu da wani tsari sosai a jikinsu, kuma ga shi irin wannan farmaki da aka kawo musu da tsakar-dare ne. Wasu suna barci, wasu kuma suna tarawa da matansu. Wato, a takaice dai basu gama shiryawa ba.
Koda aka ɗan ɗauki lokaci ana wannan gumurzu, sai dakarun sarki Kuffuru suka soma kashe dakarun sarki Ratanam. Kisa mai muni, sai dai kaga badakare guda ya shigar tsakiyar kamar dakarun sarki Ratanam guda goma, ya tarwatsa su da ƙarfin tsiya. Wasu su mutu wasu kuma su kakkarye.
Kafun ka ce me wannan, tuni aka fara ragargazar dakarun sarki Ratanam ana ta karkashe su, nan fa wannan yawa nasu ya dawo na banza. Mutum zaiyi mamaki idan aka ce masa duk wannan gumurzu da ake sarki Ratanam na tsaye a gefe yana kallo, kai kace ma ba dakarunsa ake kashewa ba.
Idan ka lura da kyau zaka ga nazarin wannan yaƙi yake. Sarki Ratanam mutum ne mai cikakken shiri, kuma ko ba komai shi babban sarki ne a wannan daula. Ya san me ake kira da yaƙi.
Ya san cewa babu yadda za'ayi kayi nasara akan abokin-gabarka idan baka san waye shi ba. Wannan shiyasa ya tsaya yana nazarin da su waye yake yaƙi.
Sarki Ratanam ya gagara gano salon-yaƙin waɗannan dakaru, kuma ya gagara gano da yanayin mutanen waɗanne ƙabila suke kama. Lallai waɗannan dakaru na sarki Kuffuru ababen tsoro ne. Duk faɗin wannan daula babu wanda ya san su, daga

Please Login or Register in order to submit comment