Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

faɗowa Marganu a rai, amma bai sami amsoshinsu ba.
Yana tsakiyar wannan kukan takaicin yaji takun sawaye sun nufo inda yake, cikin tsananin mamaki ya ɗaga kansa sama domin ganin masu zuwa.
Aljani Duksum ya gani akan gaba, sarki Kuffuru da wani baƙon sarki wanda baisan waye shi ba, sun tunkaro wannan ɗaki da yake ciki. A hannun sarki Kuffuru ya kalli wani abu a cikin jakar-tsafi, babu abinda wannan abu yafi masa kama da shi kamar dungulmin kan mutum.
"Fiddo mana shi," sarki Kuffuru ya baiwa aljani Duksum umarni. Aljanin yaje ya dafa ƙofar shiga wannan ɗaki da hannunsa, take ƙofar ta buɗe ya kamo Marganu da ƙarfi ya fiddo shi, sannan ya mayar da ƙofar ya rufe.
Marganu ya ƙarasa inda sarki Kuffuru da sarki Darwazu ke tsaye, a wannan lokaci babu komai a jikinsa face bante, wanda ko gwiwowinsa bai kai ba. Hakan ne ya bayyanar da murɗaɗɗiyar surarsa ta jarumtaka wacce zata kusan ta sarki Kuffuru.
Sarki Kuffuru ya ƙare masa kallo daga sama har ƙasa sannan ya dakawa aljani Duksum dake gefe guda tsawa, "Kai Duksum! Anƴa ka yiwa wannan jarumin azaba-uku kuwa?" Aljani Duksum ya turɓune fuskarsa ya ce, "Wannan wacce irin tambaya ce, don me ka ajiye ni a cikin wannan kurkukun?"
Sarki Kuffuru ya yi dariya ya ce, "Ba komai. Yanzu kam duniyar gaba ɗayanta ma zai bari."
Yana faɗin haka ya matso kusa da yarima Marganu, tazarar dake tsakaninsu bata wuce taku huɗu ba.
"Soyayya tushen wahala ce, duk wanda ya zaɓi soyayya ƙarshenta bata yi masa daɗi. Ka sanƴawa kanka soyayyar wacce bata san ma kana yi ba. Duk wahalar da ka sha, ko sau ɗaya bata taɓa koda tausayinka ba. Me kake nema ne a wajenta? Shin ita kaɗai ce budurwa a wannan duniya? Soyayyar gimbiya Jaanu ta janƴo ma muggan abokan gaba kamar su sarauniya Rauziyya da ni ɗinnan. Ka samu ka kubcewa sarauniya Rauziyya a hari na farko da ta kawo maka, amma a yanzu babu buƙatar ta kawo maka wani harin.
"Mahaifinka ya fusata bisa ganin cewa muna wulaƙanta masa ɗansa a kurkuku, wannan yasa yayi mana tawaye. Ka san hukuncin da nake yankewa duk wanda yayi mini tawaye?"
Sarki Kuffuru na zuwa nan a zancensa ya fiddo kan sarki Ratanam ya wurgawa yarima Marganu shi, sannan ya juya ya nufi ƙofar fita daga wannan kurkuku. Sarki Darwazu ya take masa baya.
Aljani Duksum ya ɗauki Marganu ya sake jefa shi cikin wannan ɗaki na uku, ya kulle.
Marganu ya zauna a ƙasa ya sakawa wannan dungulmin kai idanu, a karon farko bai yarda cewa kan mahaifinsa bane.
Amma daga baya ya ɗinga tuno abubuwan da suka faru da mahaifin nasa. Tabbas ko shakka babu wannan kayi dake hannunsa na mutumin da ya haife shi ne. Sanadiyar soyayyarsa ta jawo fusatar mahaifinsa wanda a ƙarshe ya rasa rayuwarsa. Wai shin wanne kallo mahaifinsa zaiyi masa idan ya kasance shi ne silar mutuwarsa?
Wanne irin kallo mahaifinsa zaiyi masa idan ya ci gaba da ƙaunar gimbiya Jaanu a cikin ransa?
Anƴa mahaifinsa zaiyi alfahari da shi kuwa, ace duk sadaukantarsa da ƙarfin damtsensa ya ƙarar dashi wajen mallakar mace, wacce a ƙarshe ta ruguza masa rayuwarsa da ta mahaifinsa gaba ɗaya?
Idan zai iya haƙuri da duk wani abu da aka taɓa yi masa a duniya, ba zai taɓa yafewa duk wanda keda sa hannu wajen kashe mahaifinsa ba.
Marganu ya tuno cewa tun daga farkon wahalar da ya fara sha a dajin Djinn, Shiwazu, tsaunin Barzasa, azabobin kurkukun mutuwa da azabobin kurkukun azaba-uku duk soyayyar gimbiya Jaanu ce ta janƴo masa. Sannan kuma, ace abun bai tsaya iya kansa ba, har ya tsallaka kan mahaifinsa dake tsananin ƙaunarsa.
Wai ma ace ba wani abu aka yiwa mahaifinsa ba, face kisan gilla mafi muni. Kai! Marganu ya kamata yasan meye yake yi.
"NA TSANE KI,
"NA TSANE KI,
"NA TSANE KI, gimbiya Jaanu." Shi ne abinda Marganu ke maimaitawa.
Ya sake ƙurawa wannan dungulmin kayi idanu, nan take kansa yayi tsawa ya zube ƙasa sumamme. Bayan kamar sa'a huɗu Marganu ya sake farfaɗowa, cikin sauri ya haƙa kabari a cikin wannan ɗaki ya binne wannan kayi na mahaifinsa domin idan ya ci gaba da kallon kan, akwai yiwuwar ya iya zaucewa.
Marganu ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa ya tashi tsaye, ya gwara kansa da ƙarafunan wannan ɗaki, goshinsa ya fashe jini ya fara zubowa. Ya saka hannunsa ya tari jinin sannan ya shafa shi akan damtsen hannunsa na hagu.
"NA RANTSE DA JININ MAHAIFINA DA AKA ZUBAR SAI NA KAWAR DA SARKI KUFFURU DAGA DORON DUNIYA,
"NA RANTSE DA JININ MAHAIFINA DA AKA ZUBAR SAI NA YIWA GIMBIYA JAANU FYAƊE SANNAN NA SARE KANTA,
"NA RANTSE DA KABARIN MAHAIFINA, SAI NA ZAMO BABBAN SARKI A WANNAN NAHIYAR KUMA SAI NA HALLAKA DUK WANDA YAYI FARIN CIKI DA MUTUWAR MAHAIFINA."
Marganu na gama ɗaukar waɗannan alƙawarurruka ya durƙushe bisa gwiwowinsa ya fashe da matsanancin kuka, yana mai ƙurawa daidai inda ya binne wannan dulgulmin kayi idanu. Nan take jikinsa ya fara tsuma, zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata ƙone saboda tsananin fusata.
A wannan lokaci ba batun soyayyar gimbiya Jaanu yake ba, ko kuma batu akan komawa gadon mulkin da mahaifinsa ya bari ba. A wannan lokaci tunanin waɗanne hanƴoƴi ya kamata ya bi domin fara shirye-shiryen ɗaukar fansa akan sarki Kuffuru.
Tabbas ya san cewa kawar da sarki Kuffuru ba ƙaramin aiki bane, dole yana buƙatar lokaci mai yawan gaske domin yaje yayi gagarumin shiri. Babban abinda ke damunsa a yanzu shi ne, tayaya zai iya guduwa daga wannan gidan kurkuku?
Yana cikin wannan tunane-tunane ne sarki Kuffuru tare da sarki Darwazu suka dawo ƙofar wannan ɗaki. Sarki Darwazu ya fiddo wata hoda daga cikin aljihunsa ya busawa yarima Marganu. Nan take barci mai nauyi ya sace shi, daga wannan lokaci bai san abinda ke faruwa ba.
Sarki Kuffuru na ganin haka yayi dariya, sannan yayi tsafi, irin wannan doki mai fuka-fuki guda biyu suka bayyana. Ya hau kan guda ɗaya ya zauna, sannan sarki Darwazu ya ɗauki Marganu ya saɓa akan kafaɗarsa shima ya zauna akan guda ɗayan.
Nan take waɗannan dawakai masu fuka-fuki suka tashi dasu sama, suka nufi yankin inda tsaunin Barzasa yake.
Duk wannan abu da ya faru, gimbiya Firziyya na can bisa wani dogon tsauni dake can nesa tana kallo. Koda taga sun ɗauki Marganu sun tafi dashi, sai hankalinta yayi mummunan tashi. Ta saƙƙo daga saman tsaunin tana kuka, ta nufi cikin wani baƙin daji.
***
Lokacin da wannan guguwa mai ƙarfi tayi jifa da sarauniya Rauziyya sai hankalinta ya ɗauke, ta fita a hayyacinta. Daga wannan lokaci bata san kuma abinda ya sake faruwa ba. Tana buɗe idanunta ta tsinci kanta a cikin wannan gidan bauta wanda gunki Barzasa yake cikinsa. A gaban wannan gunki wanda Marganu ya fillewa kai ta sami kanta a durƙushe.
Ta ɗago kai ta kalli gunkin hawaye masu zafi suka zubo daga idanunta, cikin sauri ta miƙe tsaye ta nufi ƙofar fita, bata ƙarasa bakin ƙofar ba taji muryar aljani Barzas. "Kin san dalilin da yasa ba kiyi nasara akan buɗe wannan ƙofa ta gilashi ba?"
Ta juyo da sauri ta ce, "Ni kaina nayi mamaki ace duk ƙarfin sihirin tsafinka wannan ƙofa ta gagareka?"
Muryar aljani Barzas ta bushe da dariya daga ta kowanne ɓangare na wannan gida. "Ba wanne lokacin da ya dace mu kamo Marganu ba, mun gano cewa nan gaba su da kansu zasu kawo miki shi, tare da tayin wani aiki mai tsananin wahala."
"Aiki kuma?" inji Rauziyya. "Wanne irin aiki kenan, harda ka kira shi mai wahala?"
Muryar aljani Barzas ta sake amsawa, "Kiyi haƙuri sai lokacin zuwan nasu yayi, za ki san kowanne irin aiki ne. Ni dai abinda nake buƙata daga wajenki shi ne, suna kawo yarima Marganu da zarar ranar-yanka ta kewayo ki sa a yanka min shi. Saboda jinin yarima Marganu zai ƙara min ƙarfin sihiri da ƙarfin damtse, na kai wani babban matsayi a fannin tsafi wanda a halin yanzu waɗanda keda irin wannan matsayi mutum uku ne kawai a duk faɗin duniya."
Sarauniya Rauziyya ta gyada kai cikin fahimta ta ce, "Na gane me kake nufi ya mai-girma."
Da wannan suka yi sallama da aljani Barzas ta fice daga cikin wannan gidan bauta. Daga wannan rana ta ci gaba da gudanar da sha'anin mulkinta ta manta da batun yarima Marganu gaba ɗaya. Sauran dakarun da ta kaiwa kurkukun-mutuwa da su kuwa, da ɗaiɗaiya suka ɗinga dawowa cikin wannan birni har suka gama dawowa.
Sarauniya Rauziyya mace ce mai cikakken shiri, tun sa'adda aljani Barzas ya bata labarin cewa akwai aikin da su sarki Kuffuru zasu kawo mata kuma ta amince, daga wannan lokacin ta ɗauki takobinta kullum a cikin ƙara baiwa kanta horo take.
Wataran tayi wasan takobi, wataran ta wasa ɗalasiman tsafinta, wataran kuma tayi ta baiwa kanta horon kokawa.
Sannu-a-hankali lokaci ya ci gaba da tafiya, har sarauniya Rauziyya ta fara ƙosawa da rashin zuwan su sarki Kuffuru, domin ta ƙagu taji wanne irin aiki ne wanda maigidanta ya ce ta amince zata yi shi.
Mutum zai iya cewa gaba mai tsanani zata iya shiga tsakanin sarauniya Rauziyya da sarki Kuffuru tunda a watannin baya sun ɗan fafata wadda ƙarshenta bata yiwa kowannensu daɗi ba.
To, amma shi sarki Kuffuru yana buƙatar sarauniya Rauziyya domin tana cikin sadaukai uku da zasu haɗa kai su kamo Barban. Ita kuma sarauniya Rauziyya tun daga tasowarta babu abinda ta sani kuma tayi imani dashi kamar aljani Barzas, kowanne irin umarni zai bata a shirye take tsaf domin yinsa. Kai koda cewa yayi ta kashe kanta, babu abinda zai hanata aiwatar da hakan saboda tsananin yadda tayi imani dashi.
Watarana da yammaci, sarauniya Rauziyya ta fita bayan gari rangadi. Ba zato taga sararin samaniya ta fara kaɗawa ta gabas, wani irin baƙin hadari ya fara tasowa. Wannan abu yayi matuƙar bata mamaki ba kaɗan ba, a saninta dai tunda suke rayuwa a saman wannan tsauni fiye da shekaru ɗari biyu da ɗoriya ba'a taɓa yi musu ruwa mai ƙarfi ba.
A ce haka kawai taga hadari ya taso ai dole zatayi mamaki. To, amma ga dukkan alamu wannan hadari ba hadari ne wanda ke ɗauke da ruwa ba. Idan ta lura da kyau waɗansu halittu guda biyu take kallo suna saƙƙowa saman wannan tsauni kuma ko shakka babu su ne suka haifar da wannan hadari.
Sannu-a-hankali kuma sai wannan hadari ya fara disashewa, su kuma waɗannan halittu guda biyu suna daɗa bayyana. Jin kaɗan sai ga manƴa-manƴan dawakai guda biyu masu fuka-fuki sun diro bisa wannan tsauni, a sannan ne kuma wannan hadari ya gama disashewa.
Mutum na farko dake ɓangaren dama sarki Kuffuru ne, wanda ke gefensa kuma sarki Darwazu ne. Ga sadauki Marganu kwance akan wuyan wannan doki yana ta sharar barcin dole bai ma san abinda ke faruwa ba.
Ba tare da ɓata lokacin komai ba, sarki Kuffuru da sarki Darwazu suka saƙƙo daga kan waɗannan dawakai, sarki Kuffuru ya sallami dawakan, suka tunkari inda sarauniya Rauziyya ke tsaye, Marganu na saɓe bisa kafaɗar Darwazu.
Duk tsananin jarumtakar sarki Kuffuru da kwarjininsa sai yaji ko kaɗan baya son kallon cikin idanun sarauniya Rauziyya saboda basayi masa kama da komai face na kyanwa. Haka kuma idan yana ganin zubin tsarin jikinta saiya ɗinga jin tsikar jikinsa tana tashi.
Sarauniya Rauziyya, mace mai kamar maza, matsafiya uwar shaiɗanu.
Suna isowa inda take tsaye, sarki Darwazu ya kwantar da Marganu a gabanta sannan ya kama hannunta guda ya sumbata, shima Kuffuru na ganin haka ya miƙa hannu zai kamo hannun nata ya sumbata amma sai tayi caraf ta kamo nasa ta sumbata a wani salo mai nuna biyayya.
"Barkan ku da zuwa tsaunin Barzas, tsaunin da yafi kowanne tsauni a duniya tarin muggan bakaken aljanu." inji sarauniya Rauziyya.
Sarki Darwazu ya yi murmushi ya ce, "Da fatan mun same ki lafiya?"
"Lafiya ƙalau, kuzo muje fadata a baku masauƙi kafun naji abinda ke tafe da ku." ta ce.
Sarki Darwazu da sarki Kuffuru suka kalli juna cikin tsananin mamaki, ko a mafarki basu taɓa tunanin sarauniya Rauziyya zata yi musu tarɓa haka ba.
Ba tare da ɓata wani lokaci ba, ta shige gaba suna biye da ita a baya.
Sarki Kuffuru na tafe yana ta nazari, yana kuma tsananin mamakin yadda aka yi wannan sarauniya ta basu haɗin kai cikin sauƙi haka. A ransa ya ƙudurce tabbas cikin biyu za'ayi ɗaya;
Ko dai tana so tayi amfani da wannan dama ta yaudaresu gaba ɗaya, ko kuma, tun kafin su zo an bata labarin abinda ke tafe dasu.
Yana cikin wannan tunani a ransa ne, suka shigo cikin asalin birninta, jama'arta suka fara firfitowa suna ta kallonsu.
Koda suka ga yarima Marganu a sume bisa kafaɗar sarki Darwazu kuma suka ga ga dukkan alamu sarauniyarsu aka kawowa shi, sai suka ruɗe shewa, suka fara yi mata jinjina.
Dukda cewa sarki Kuffuru da sarki Darwazu basa jin yaren waɗannan arnan-dajin amma sun gano cewa kirari suke yiwa Rauziyya saboda ganin ta kamo tsinanne Marganu wanda gunkinsu ya ce a kawo masa jininsa.
Suna isowa fada, sarauniya Rauziyya ta karɓi Marganu daga hannun sarki Darwazu, ta ɗaga hannunta guda na hagu sama. Nan take wata baƙar walkiya ta fara katantawa daga sama ta nufo hannun nata, tana zuwa ta dira kan hannun sannan ta fara yawo. Sarauniya Rauziyya na ganin haka tayi murmushi sannan ta nuna Marganu da wannan walƙiya, nan take yaji wani irin zafi ya rufe shi. Bai san sa'adda ya buɗe idanunsa ba, kuma ya kwarara uban ihu.
Kamar da wasa yaji jikinsa ya fara mutuwa, ƙarfin jikinsa yana raguwa. Kafun kace me ya tafi ƙasa bisa gwiwowinsa, yana kallon su sarauniya Rauziyya dishi-dishi.
"Ko don wannar kyautar da kuka kawo min zan baku haɗin kai ɗari bisa ɗari," inji Rauziyya.
Tana faɗin hakan ta sake sana'anta wani keji, wanda aka ƙera da zallar duwatsu. Ta cilla Marganu cikin kejin, sannan ta bayar da umarnin a saka masa idanu sosai, babu dare ko rana, kowanne lokaci ya kasance akwai idanu akansa don kada yayi abinda yayi a farko.
Wata hadima ta musamman aka umarta ta kai sarki Kuffuru da sarki Darwazu masauƙi, suka kwanta suka huta.
Washe gari da sassafe sarauniya Rauziyya ta shirya musu zama a cikin wani ƙaramin tanti. Kuyanga tayi musu jagora har bakin wannan tanti, su kuma suka shige cikin tantin.
Suna shigowa suka iske sarauniya Rauziyya zaune bisa wata ƙatuwar karaga ta mulki, wani ɗan ƙaramin tsuntsu mai siffar shirwa na zaune bisa kafaɗarta. A gabanta kuma an tanadi wasu kujeru guda biyu da teburin alfarma wanda aka cika da kayayyakin abinci.
Sarki Kuffuru da Darwazu suka zauna kan waɗannan kujeru, ba tare da gardamar komai ba, suka ci wannan abinci suka ƙoshi.
"Tun kafun ku zo, mai gidana ya bani labarin zuwanku amma bai sanar dani abinda ke tafe da ku ba. Shin zaku sanar dani dalilin da yasa manƴan sarakuna kamar ku suka taso suka zo har ƙasata neman alfarma?" inji sarauniya Rauziyya.
Sarki Darwazu ya yi gyaran murya ya ce, "Na san cewa kema kina da labarin Hodon?"
Cikin tsananin mamaki sarauniya Rauziyya ta zaro idanu ta ce, "Hodon? Tayaya aka yi kuka san ainihin sunan mutumin da yafi kowa ƙarfin sihiri da ƙwaƙwalwa a duniya? Kuyi sani cewa ko mu kanmu masu hulɗa da baƙaƙen aljanu bamu gama sanin wannan mutumi ba."
Sarki Darwazu ya gyaɗa kai, "Wannan mutumi shi ne ɓarawon da ya addabi dukkanin ƙasashen duniya da sata. Duk duniya babu wata babbar daula, da bai shiga yayi sata ba. Yafi shekaru goma yana sata amma ko sunansa ba'a sani ba, saida ya shigo ƙasata yayi sata daga nan asirinsa ya fara tunowa.
"Kiyi sani cewa ababen dogaronmu sunyi bincike akan yadda za'a kamo wannan ɓarawo, kuma sun tabbatar mana da cewa; SADAUKAI UKU ƴan baiwa su ne kawai zasu iya haɗa ƙarfi-da-ƙarfe su kamo wannan mutumi, koda kuwa yana tare da aljaninsa.
"Sadauki na farko shi ne Kuffuru, na biyu kuma ni ɗinnan ne. Cikon ta uku kuma, kece uwar sadaukai da matsafa.
"Ana buƙatar sarki Kuffuru saboda takobinsa ta Siwod-del-bulod, mai samar da sadaukai guda goma, jinin Infiro.
"Ana buƙatata saboda tsafi baya tasiri akaina sosai, ni ne kawai wanda zai iya ratsawa duk cikin wani kafin tsafi wanda Hodon ya gina har mu riske shi.
"Ana buƙatar ki saboda fasaharki ta taswira. Duk duniya babu wanda zai fahimci taswirar Hodon face ke ɗinnan. Idan har ba ma tare da ke, ba zamu taɓa gano ainihin inda Hodon yake ba."
Sarauniya Rauziyya ta gyaɗa kai cikin fahimta ta ce, "Haka ne. Zan amince da wannan buƙata da kuka zo min da ita, saboda ɓarawo tamkar gobara daji haka yake. Idan ba kayi ƙoƙarin kasheta ba wataran zata iso har inda kake. Abinda nake son sani shi ne, mene ne sakamakon da kowannen mu zai samu sakamakon kama wannan ɓarawo.
"Kun sani, na sani cewa; Hodon ɗan baiwa ne. Duk inda aka samu mutum mai baiwa irin Hodon, to, ba'a rasa alkhairai da yawa a tattare dashi. Binciken da muka gudanar ni da masana a wannan birni fiye da shekaru goma da suka wuce. Mun gano cewa babu mai arziki a duniya kamar Hodon, babu mai ƙarfin sihirin tsafi kamar Hodon, babu jini mai ƙarfi kamar jinin Hodon (idan ka cire jinin Samudul Ansari).
"A cikin mu kowa sai ya faɗi abinda yake buƙata daga cikin waɗannan abubuwa guda uku; dukiya, ƙarfin sihiri ko kuma jini."
Sarki Kuffuru da sarki Darwazu suka kalli junansu, sannan suka sunkuyar da kawunansu kowa ya faɗa kogin tunani. Tabbas tun haɗuwarsu ta farko basu tattauna akan wannan abu ba.
Idan muka yi duba zuwa baya, zamu ga cewa sarki Darwazu da boka Balwaz a tattaunawarsu, hankalin sarki Darwazu yafi raja'a akan dukiya. Sannan idan muka yi duba izuwa ga yanayin ƙabilarsa ta Adbéncan ƙarfin sihiri bai dame su sosai ba. Bisa waɗannan dalilai zamu iya cewa sarki Darwazu dukiya zai zaɓa.
A ɗaya ɓangaren kuma zamu ga cewa, sarki Kuffuru izza da mulki yake buƙata a yadda yake baiwa boka Hubbazu labari bayan haɗuwarsa da sarki Fairaz (jagoran sarakuna tamanin da uku) waɗanda suke farautar Barban. Tunda mun ji cewa sarki Fairaz ya ce, in dai yayi sanadiyar kamo Barban, waɗannan sarakuna tamanin da uku zasu dawo ƙarƙashin mulkinsa. Idan muka duba kuma zamu ga cewa duk wanda ke buƙatar mulki kamar wanda sarki Kuffuru ke ra'ayi, to, tabbas yana buƙatar ƙarfin sihirin tsafi mai ƙarfin gaske.
Idan muka yi duba zuwa ga tsarin rayuwar mutanen ƙabilar Edwan, ƙabilar su sarauniya Rauziyya. Zamu ga cewa mutane ne da suka yi imani kacokan da ƙarfin sihirin aljanu. Su kuma aljanu kowa ya san abinda suke buƙata wato JINI.
Don haka babu buƙatar ji daga bakin waɗannan mutane, mun san abinda kowa yake buƙata.
Sarki Darwazu dukiya.
Sarki Kuffuru sirrin tsafi.
Sarauniya Rauziyya ingantaccen jini.
Bayan kammala wannan tattaunawa sai suka miƙe gaba ɗayansu suka fice daga cikin wannan tanti.
Sarki Kuffuru ya sake samar da irin waɗannan dawakai masu fuka-fuki guda uku. Ya hau kan guda, ya baiwa sarauniya Rauziyya da sarki Darwazu guda-guda.
Kafun sarauniya Rauziyya ta haye kan dokinta, ta nemi izini wajen su sarki Kuffuru ta koma fadar ƙasarta, tayi wani taro na gaggawa. Dukkan masu faɗa-aji na ƙabilar Edwan suka taru a gaban karagar mulkinta.
"Tafiya ta taso min wacce bani da ikon ƙin yinta, domin tana daga cikin umurnin maigirma Barzas. Daga yau na bar ƙasata a hannunku, ku tafiyar da harkokin mulki kamar yadda na saba.
"Yau Lahadi, ranar Laraba da yammaci ina mai baku umarnin a ɗakko Marganu daga cikin wannan kurkuku da na tsare shi, a yankawa gunki Barzasa jininsa. Waɗannan su ne umarnina a gare ku." inji sarauniya Rauziyya.
Kowa dake cikin wannan fada ya ɗora hannunsa bisa ƙirjinsa sannan suka sunkuyar da kawunansu; wannan shi ne ke nuna alamar bin umarnin sarauniyarsu.
Nan take ta koma wajen su sarki Kuffuru suka haye bisa waɗannan dawakai masu fuka-fuki, suka tashi sama suka nufi kogon Hubbaz inda zasu riski aljani Sheezuwa domin ya ƙarasa musu bayanin yadda za'a kamo Barban kuma ya baiwa sarauniya Rauziyya wannan taswira tayi mata gyare-gyare.
Wannan taswira dama can cikin kogon Hubbaz, ba'a fitowa da ita, saboda tsaro.
****RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 44: *Sarauniya Jaanu*
*
*
✍️✍️✍️UMAR SANGARU✍️✍️✍️
*
~Birnin Damashkar.
*
Tun ranar da sarki Ayubu da boka Ruguzan suka bar wannan birni, gaba ɗaya tsarin mulkin garin ya sauya. Mulkin gimbiya Jaanu na dabam ne, saboda ta kasance mai tsananin adalci.
Mutanen wannan birni suna tsananin jin daɗin wannan mulki nata, wanda yake da bambanci matuƙa da na azzalumi Ayubu.
Wasu daga cikin mutanen garin, tunani suka fara akan anƴa ba za'a tumɓuke sarki Ayubul Zairiy daga kan wannan karaga a ɗaura ƴarsa ba? Saboda bambancin mulkinta da nasa tamkar bambancin dake tsakanin ƙanƙara da wuta ne.
Watarana gimbiya Jaanu tana zaune a fada akan karagar mulkin mahaifinta, ta sanƴa alkyabba ruwan-toka mai farin-beza ta wuya. Gashin kanta kuma, anyi masa wani gyara an ɗaure shi da wani abun ado mai kyau.
Aka ci gaba da tafiyar da harkokin mulki kamar yadda ta saba cikin adalci.
Kwatsam! Ba zato taga shigowar ɗan ƙaramin tsuntsu mai tsananin kyawun gaske, tana ganin kalar wannan tsuntsu ta shaida shi. Ko shakka babu irin wannan tsuntsu ne wanda Aymanul Faris ya ce mata ya gani, a farkon haɗuwarsu a cikin gidanta.
Abinda ya ɗaure mata kai shi ne, har kan hannun wannan karagar mulki tsuntsun ya sauƙa, amma a yadda ta lura ita ɗaya jal ce take kallonsa. Sauran mutanen dake fadar basu ma san da wanzuwarsa a wajen ba, kowa harkokin gabansa yake.
Kyakkyawan tsuntsun ya tashi daga kan karagar mulkin, ya shige ta cikin wannan ƙofa wacce zata sada mutum da yankin gimbiya Jaanu.
Gimbiya Jaanu na ganin haka ta miƙe da sauri ta bi bayan wannan tsuntsu, ba tare da ta yiwa kowa dake wannan fada magana ba. Tana shigowa cikin yankin nata, ta fara yin arba da dakarun dake tsaron yankin a kwakkwance suna barci.
Al'amarin da ya yi matuƙar bata mamaki kenan, ta tabbatar da cewa, lallai akwai baƙin da suka shigo cikin wannan gida nata. Su waye? Wannan tambaya ce da bata sami amsarta ba.
Saboda dalilai guda biyu, gimbiya Jaanu ta gagara yin gaggawar sanar da abinda ke faruwa. Dalili na farko shi ne tana tunanin anƴa ba mai-gidan Aymanul Faris bane ya kawo mata ziyara? Tunda idan zata iya tunowa karon-ƙarshe da ta kalli kalar wannan tsuntsu, wannan mai-gidan nasa ne ya turo shi. Dalili na biyu shi ne duk wanda ya kawo mata wannan ziyara bada niyyar cutarwa yazo ba; don inda ace da cutarwa yazo da kashe waɗannan dakaru zaiyi ba sanƴa musu barcin dole ba.
Koda tazo giftawa ta gefen lambun gidanta, sai ta tsaya cak, ta juya da sauri ta ƙurawa cikin lambun idanu. Idan zata lura da kyau, tabbas mutane guda biyu take hangowa acan gindin wata bishiya, suna zaune suna hira.
Abinda ya bata mamaki shi ne su waye waɗannan mutane? Kuma me suke taƙama dashi da har zasu shigo cikin lambunta su zauna a gindin bishiya su kama hira?
Idanun gimbiya Jaanu na ƙara zuwa kan wanda ke zaune a gefen dama, ƙirjinta ya buga da ƙarfi. Tabbas ta fara tabbatar da abinda take zargi. Waɗansu hawayen farin-ciki suka zubo mata ta ruga da gudu cikin lambun.
Idan muka yi duba izuwa ga

Please Login or Register in order to submit comment