Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ci gaba da wasanni kala-kala har tsahon sa'a guda. Babu abinda nake
ayyanawa a raina kuma nake fata kamar sarauniya Amra ta kira ni. Kamar daga sama
sai naji an daka min tsawa, "Sarauniya tana son ganin waɗannan wasannin naka, amma
kafun nan sai ka gana da mijinta domin yana so ya san kai waye." Wani narkeken ƙato
tsaye rike da takobi yayi wannan furuci.
"Katon ya sakani a gaba, ni da dan-saurayin da muke wasa da shi. Da zuwanmu kofar
fada sai muka cika da tsananin mamaki sakamakon arba da gungun dakaru birjik suna
ta kai-kawo sai muzurai suke, nan fa na tabbatar da cewa ko yaya asirina ya tonu tofa
sai dai uwata ta haifi wani. Aka saka wata katuwar kuba aka bude mana kofar gidan
sarautar, nan take ta bude wanwar. Daga inda muke ina hango sarki Meher zaune bisa
karaga, ga matarsa Amra a gefensa.
"Babban abinda ya taimakemu shi ne ikon Amra kawai ke aiki a wannan fada tunda ta
mallake sarkin, amma da daga kallon farko zai gane mu. Narkeken ƙaton nan sai da ya
kawo mu har gaban sarki sannan ya juya. Aka yi kallon-kallo tsakanina da sarki Meher.
"Iyakacin daɗewata a birnin Shàha-Meher ban taba ganin ka ba, shin kai baƙo ne ko
kuwa?" Inji sarki Meher. Zuciyata ta buga da karfi na ce, "Baƙo kuma? Yanzu har akwai
baƙon da ya isa ya shigo wannan birni duk tsaron da aka bashi?" Sarki Meher ya yi min
kallon rashin yarda sannan ya dubi Amra yayi murmushi ya ce, "To ga wanda kika ce a
kawo miki nan an kawo. Sai ku fara kallon wasan ko!" Sarki Meher na gama faɗin haka
ya tashi ya fice daga fadar.
"Ni da ɗan-saurayi muka tashi muka fara baje kolinmu a wajen sarauniya, nan take ta
cika da tsananin farin ciki. Im banda kyalkyala dariya babu abinda take. Duk da cewa
sarki Meher baya nan amma dakarunsa sun zuba ido sosai akaina. Koda sarauniya taga
dokin tsafina mai tashi sama sai tace, "Shin kuwa nima zan iya ɗana wannan doki?" Na
ce "Me zai hana?" Ta taho zata hau kan dokin amma sai wannan narkeken kato ya shiga
tsakani. Ya ce shi sam bai yarda da wannan doki ba, "Sarki ya ce mu saka ido sosai
akan wannan matsafin!" Inji ƙaton.
"Bai ankara ba kawai sai yaji sauƙar mari a fuskarsa ashe ran sarauniya Amra ne ya ɓaci,
narkeken ƙaton ya rike kuncinsa cikin tsananin fusata. "To ai sai ka rama ko?!" Inji
sarauniya Amra cikin izza. Ya koma gefe kawai ya zuba mana idanu. Sarauniya Amra ta
hau kan wannan doki, na kai hannu zan taɓa wuyan dokin domin ya tashi sama. Tsawar
da naji an daka min ce tasa na janƴe hannuna da sauri. "Ku kama su!" Inji sarki Meher.
"Naje ɗakin tsafina nayi bincike akansa, shi ne ɓarawon da ɗan uwana sarki Deher ya
turo domin ya sace sarauniya!!!" Sadaukin nan ya daka tsalle ya dira a gabanmu yana
shirin kama mu.
"Ban san ya akai ba, kawai sai naga dokin wasan nan ya zuko mu ni da ɗan-saurayi
tamkar man karfe. Dokin ya cilla sama cikin azababben gudu tamkar tauraruwa mai
wutsiya. Wannan ita ce babbar sata da na taɓa yi mai matukar hadari ta farko.
"A fadar sarki Deher na tsinci kaina amma babu wannan ɗan-saurayi. Daga gefe kuma
gimbiya Amra ce daure cikin sarkoki har sarki ya gama yanke mata hukunci, "Ita ce ta sa
aka kashe manzo Razzan, baban Harsiya." Inji sarkin a lokacin da hauni ya fille kan
Amra.
"Sarki ya kirani ya bani kyautar dinare milyan, daga wannan lokaci ban sake talauci ba.
Sai da na nutsu na yiwa kaina wasu tambayoyi. Meyasa dokin tsafi ya zuƙe mu? Waye
ne wannan ɗan-saurayin? Domin a birnin Shàha-Meher na haɗu da shi.
"Kashe gimbiya Amra da sarki Deher yayi bai haifar da komai ba face mugun
azababben yaƙi tsakanin birnin Shàha-Deher da birnin Shàha-Meher, wannan yaƙi shi ne
sanadiyar karyewar daular birnin Shàha. Saboda jinin da ya kwarara kuwa sai da aka
rasa ruwan sha da abin da za'a ci. Bisa dole aka kauracewa wadannan birane biyu, har
yau har gobe akwai dubbanin kwarangwal a cikin biranen barkatai. Dama sarki Al-
Khamis ya bar wasiyar kada a kuskura a yi yaki a cikin birnin Shàha, idan kuwa aka yi
sai daular ta karye.
"Daga cikin mutanen ƙabilar Jenher da ƙabilar Huturu akwai waɗanda suka yi saura.
Sarki Ratanam ɗan ƙabilar Jenher ne, shi kuma sarki Ayubul Zairiy ɗan ƙabilar banu
Huturu ne. Sarki Kuffuru kuma yana daga cikin 'ya'yan sarki Meher.
"Lokacin da na tabbatar da cewa nifa ba sadauki bane, kuma yaƙi yayi tsamari kawai sai
na juya da baya na gudu izuwa cikin daji na ɓuya. Abin mamaki ina zuwa dokar daji,
naga wannan ɗan saurayin ya faɗo ƙasa kamar jeho shi akai. "Sunana aljani Ranganul
Fairarzas" Wannan wanne irin suna ne? Kamar yasan me nake tunani, ya ce "Zaka iya
kirana da Ranganu ko Fairaz. Ya kai wannan saurayi kayi sani cewa, ka burgeni matuƙa
bisa ganin yadda kake jajircewa wajen ganin ka sharewa kanka hawaye dukda
kasancewarka mai nakasa ta rashin jarumta. Daga yau zan ɗinga taimakonka akan
dukkanin harkokinka. Ga wannan kambu ka daura shi a damtsen hannunka na hagu, a
duk lokacin da kaga halaka ka shafe shi, hadiman Aljanu guda uku masu bauta masa
zasu fito su kareka. Wadannan aljanu suna da iko mai girman gaske, kuma sadaukai ne
na gani na fada. Kai dai ka kula da kambun kawai ya kasance a tare da kai kullum da
kuma a koda yaushe. Kasan meyasa akayi ragas a wannan yaki?" Na ce, A'a. Aljani
Ranganu ya ce, "A zahiri sarki Deher yafi Meher karfi da sojojin yaki amma Meher ya
samu taimako sosai daga sauran ƙabilun dake cikin wannan birni. Shiyasa akayi ragas.
Yanzu Meher ya mutu, Deher ma ya mutu amma kowanne a cikin matansu tana da ciki
kuma tabbas nan bada daɗewa ba 'ya'yansu zasu bayyana." Aljanin na zuwa nan a
zancensa ya fiddo wani koren kambu ya bani sannan ya bace bat!
Wannan shi ne takaitaccen tarihina da kuma tarihin birnin Shaha, da yadda sarkin
barayin Aljanu Ranganu yake taimaka min a fannin sata.
*******Ruhin Jarumtaka!!!
*
Babi na 4: *Ayman da Jaanu*

*
Umar Sangaru
*
Koda sarkin ɓarayi Barban yazo nan a labarinsa sai idanunsa suka ciko da kwalla, ya
tuno tsohon tarihin mahaifinsa da kuma yadda ya rasa mahaifiyarsa. "A duniya ku kaɗai
ne kuka san wannan tarihi nawa, ku kaɗai ne kuka san asalin sunana Aswàd. Ni da ku
'yan uwan juna ne, kasarmu ɗaya, kabilarmu ɗaya. Saboda haka dole ne mu hada kai
domin sharewa kanmu hawaye, abokan gabarmu suna da tsananin karfi." Inji sarkin
ɓarayi Barban.
Aymanul Faris da jaruma Riya suka yi ajiyar numfashi, Aymanul Faris ya dubi sarkin
barayi Barban ya ce, "Ya kai Barban haƙiƙa mun ji tarihinka mai cike da abubuwan
tausayi. Amma sai dai ina da wasu tambayoyi a gareka?" Barban ya ce, "Faɗi
tambayoyinka." Aymanul Faris ya sake numfasawa ya ce, "A cikin tarihin da ka bamu
baka bayyana mana waye ne Yurbaru da Asasinu ba, wanda sanadiyarsu yasa Ayubul
Zairiy ya kashe min mahaifina. Tambaya ta biyu ita ce, tun da daular birnin Shaha ta
karye, ina sauran mutane ragowar yaki suka yi? Ya ya aka yi ka shahara har kayi ƙaurin
suna a duniya?" Koda sarkin ɓarayi Barban yaji wadannan tambayoyi sai ya yi
murmushi.
"Yurbaru shi ne kakan sarki Ayubul Zairiy wato mahaifin shugaban ƙabilar banu Huturu.
Da yake a wancan yaƙin guduwa nayi bansan abubuwan da suka faru a yakin ba, amma
dai an bani labarin cewa sarki Deher ne ya sare kan Yurbaru a gaban idanun shugaban
ƙabilar banu Huturu. Maganar gaskiya ban san waye ne Asasinu ba amma shima a
wannan yaƙi Deher ya hallaka shi. Sai dai waɗannan mutane guda biyu manyan attajirai
ne a ƙabilar banu Huturu, su suke ɗaukar ɗawainiyar komai na ƙabilar. Kuma ance kashe
su da sarki Deher yayi shine ya karyawa 'yan ƙabilar gwiwa a wancan yaƙin har akayi
ragas.
"Lokacin da aka gama kafsa wannan yaƙi, sai ruwan sha ya kafe. Amfanin gona ya kone,
kasa ta rine ta zama ja sakamakon yawan jinin da ya zuba akanta. Yunwa da fari ya
yiwa al'umar da suka yi saura yawa, bisa dole suka yi hijira suka shiga duniya. Ƙabilar
banu Kuyuru sun kasance kyawawan gaske. Hasken fatarsu da baƙin gashin kansu na
dabam ne, shiyasa zaiyi wuya kaga ɗan ƙabilar banu Kuyuru baka shaida shi ba. Su
kuma mutanen ƙabilar banu Huturu jan gashi ne dasu, kuma sun kasance gajeru basa
tsawo sosai. Bayan shekaru bakwai da kammala wannan yayki, sai aka farautar 'yan
ƙabilar banu Kuyuru ana kaiwa sarkin birnin Kufa, yana bayar da lada mai tsoka. Daga
wannan lokaci mutanen ƙabilar banu Kuyuru suke ɓuya basa bayyana kansu domin duk
inda aka gansu, farautarsu ake tamkar dabbobin daji.
"Dangane da shaharata a duniya kuma, abu ne mai matukar ban al'ajabi. Tunda nayi
bankwana da aljani Ranganu sai na kama hanyar tafiya birnin Sin, sai da na shafe
kwanaki sittin da bakwai ina tafiya sannan na isa can. Bani da komai na dukiya haka na
shiga cikin garin. Hakika na sha wahala sosai a birnin Sin saboda bansan kowa ba,
babu wanda ya sanni. A wancan lokaci wani azzalumin sarki ne akan karagar mulki, ya
sakawa 'yan ƙasar haraji mai yawan gaske. Saboda kawai yana so ya tara dukiya mai
yawan gaske don ya sayi wani katafaren gida da aka gina a birnin Kisra mai tsadar
gaske. Kai sai da ta kai ta kawo cewa, sarkin ya fara saka dakarunsa suna yiwa jama'a
kwacen amfanin gonarsu da kayayyakin da suke sayarwa, don kawai ya hada waɗannan
kudade.
"Wani dattijon mutum ne ya ɗaukeni ya kaini gidansa kuma ya bani labarin irin zaluncin
sarki 'Kim Sam'. Wannan dattijo yana da rumbu cike da alkama da 'ya'yan itatuwa, a
bayan gidansa. Watarana da tsakar dare muna kwance muna barci, kawai sai muka
jiwo hayaniya a bayan wannan gida, cikin hanzari muka farka muka je muka duba.
Dakarun sarki Kim Sam muka gani tsaitsaye a gaban wannan rumbu, biyu daga cikinsu
sai loda kayan rumbun suke cikin wani amalanke. Dattijon nan ya faɗi kaysa yana neman
alfarmar a bar masa kayan abincinsa, saboda su kaɗai yake da kuma ba shi da kuɗin
sayan wasu. Dakarun nan suka rufe shi da duka suka ce bai da hankali ne? Zai ja da
umarnin sarki!
"Nan dai suka kwashe dukiyar nan kaf suka tafi, saboda tsabar bakin ciki dattijon nan
sai da ya suma. Na yi sauri na yayyafa masa ruwa, sannan ya farfaɗo. Daga wannan
lokaci na ci alwashin sai na ruguza burin wannan sarki nason mallakar katafaren gida a
birnin Kisra.
"Tun daga lokacin bani da gurin zuwa da ya wuce fadar garin, ina nazarinta. In takaice
muku labari sai da na kwashe dukiyar sarkin nan kaf, na rabawa jama'ar birnin a
sirrance ba tare da ya sani ba. Saboda tsananin bakin ciki, sai da ya kulle kansa a ɗaki
ya yi kuka har tsawon kwanaki uku. Akwai wani hatimi da aljani Ranganu ya bani, yace a
duk inda nayi sata ina ajiye wannan hatimi domin ya zamo shaidata. Wannan hatimi ba
komai bane face wadtansu baƙaƙen rubutu da wani tsohon yare na aljanu, ni kaina
bansan me suke nufi ba." Sarkin barayi Barban na zuwa nan a zancensa ya fiddo kalar
wannan hatimi ya nunawa su Aymanul Faris. "Tun daga wannan lokaci na zamo
gawurtaccen ɓarawo, duk inda nayi sata sai na ajiye wannan hatimi. A halin yanzu
manƴan sarakuna tamanin da uku ne ke nemata ruwa a jallo, sakamakon satar da nayi
musu. Bokayen duniya sun gama iya bincikensu akan su gano inda nake amma abu ya
ci tura, na gagari kowa!" Barawo Barban na zuwa nan a zancensa yayi shuru.
Aymanul Faris ya yi ajiyar numfashi ya ce, "Ya shugabana, haƙiƙa mun jinjina maka bisa
wannan gagarumar bajinta da kayi, kuma tabbas ka cancanci muƙamin sarkin ɓarayi na
duniya. Amma ya batun zuwa birnin Damashkar domin ƙwato mahaifiyata wacce ke
tsare a gidan kurkuku? Nifa duk a cikin kwanakin nan bana samun isasshen barci,
abinci ma bana koshi saboda kawai tunanin mahaifiyata. Ya ya zamu yi mu kuɓutar da
ita?"
Koda jin wannan tambaya sai sarkin barayi Barban yayi ajiyar zuciya ya ce, "Yi hakuri
babban jarumi na gobe, tabbas ina sane da buƙatar ka ta kuɓutar da mahaifiyarka daga
gidan kurkuku. Amma ka sani cewa komai na buƙatar lokaci da kuma shiri. Na faɗawa
aljani Ranganu buƙatar kuɓutar da babarka, yanzu haka bayanan kurkukun yake hada
min da kuma na gidan sarautar. Ka sani fa cewa shiga gidan sarautar birnin Damashkar
yafi sauƙi akan shiga gidan kurkuku. Dubi wannan allon tsafin domin ganin gagarumin
tsaron dake wannan gidan kurkuku." Sarkin barayi Barban ya nuna wannan allon tsafi
dake kafe a tsakiyar fadar sa.
Nan take ginin wata katuwar kurkuku ya bayyana akan allon tsafin. Kurkuku ce makekiya
da aka gina da zallar duwatsun wuta, an ginata a tsakiyar wani katon daji mai yawan
sahara. Wadansu irin samudawan dakaru na ta kaiwa da komowa ta kowacce kusurwa,
suna ta muzurai kamar zasu ci babu. Ko'ina ka duba irin waɗannan dakaru ne sun cika
ko'ina na daji. Shi kuwa ginin wannan kurkuku a shafe yake sumul, kai da gani ka san
cewa zaiyi santsi sosai. Kai tsawon ginin wannan kurkuku kaɗai abin dubawa ne, domin
zai kai zira'i metan.
Babu ta inda mutum zai ɓullo a cikin wannan daji ba tare da ya faɗa hannun dakaru
masu tsaron nan ba. A cikin kurkukun kuma dakuna ne birjik, a jere layi-layi. Akwai irin
wadannan samudawan dakaru a ciki kurkukun, suna kula da fursunoni. Duk tsautsayin
da yasa suka kama fursuna da laifi tofa sai dai uwarsa ta haifi wani, wadannan dakaru
horon da aka yi musu na dabam ne. Basu san komai ba in banda kisa.
Koda Aymanul Faris ya gama yin arba da wannan kurkuku sai ya sha jinin jikinsa ya
tabbatarwa da kansa cewa, lallai shiga wannan kurkuku ba zai yiwu ba. Balle har yayi
tunanin kuɓutar da mahaifiyarsa.
"Ya shugabana, yanzu mene abin yi?" Inji Aymanul Faris yana duban sarkin ɓarayi
Barban. Har sarkin ɓarayi Barban ya budi baki zai ce wani abu kawai sai suka ga an jeho
wasiƙa cikin fadar. Barban ya dauki wasiƙar ya budeta.
Babu komai a jikin wannan wasiƙa face zanen taswirar gidan sarautar sarki Ayubul
Zairiy, a kasan taswirar kuma an yi rubutu kamar haka:-
"Ya kai Barban ina maka barka da wannan lokaci da kai da waɗanda suke tare da kai.
Hakika nayi bincike akan bukatar da kazo mini da ita, ta son kuɓutar da fursuna daga
gidan kurkuku. Wannan aiki yana da mugun haɗari, domin wannan kurkuku ba'a
ƙarƙashin birnin Damashkar kaɗai take ba. Ƙasashe hudu ne suka yi haɗaka suka
ginata, haɗarin da ke tattare da wannan aiki na kubutar da fursuna yana da wahalar
gaske. Ko yaya aka samu matsala a wannan aiki, kashe fursunan zasu yi. Saboda haka
muka yi bincike muka sauwake muku wannan wahala. Maimakon kuɓutar da fursunan,
mu ma zamu yi garkuwa da 'yar wannan sarki wato gimbiya Jaanu.
"Ga taswirar gidan sarautar, sai kuyi tunanin yadda zaku sato 'yar sarki Ayubul Zairiy.
Tabbas idan kuka yi nasarar sato gimbiya Jaanu tamkar kun kuɓutar da wannan
fursunar ceh. Zamu ci gaba da taimakonku a kowanne lokaci. Wasika daga Ranganu."
Koda sarkin barayi Barban ya gama karanta wannan wasika, sai ya dubi su Aymanul
Faris ya ce.
"Kun dai ji abinda mai gidana yace, shin kuna da shawara ko kuma ja... akan wannan
umarni nasa?" Koda jin wannan tambaya sai Aymanul Faris da jaruma Riya suka dubi
juna, sannan Aymanul Faris ya ce, "Ba mu da wani ja... akan wannan umarni nasa."
Barban ya yi murmushi ya ce, "Haka nake son ji, yanzu sai ku matso kusa domin mu
fara nazarin wannan taswira." Da jin wannan batu sai Aymanul Faris da jaruma Riya
suka matso kusa da wani teburi wanda aka shimfide wannan taswira akai.
A jikin taswirar akwai zanen gidan sarauta, wanda yake da ƙofofin shiga guda huɗu rak!
A bakin kowacce ƙofa akwai zanen dakaru masu tsaro da yawan gaske. Gidan sarautar
a rabe yake gida biyu, gefen dama shi ne ɓangaren da fadar sarki take da kuma
ɗakunan dakaru, bayi da kuyangi. A gefen hagu kuma nan ne inda turakar sarki da ta
gimbiya take, a jikin taswirar an zana hotunan dakaru masu yawan gaske a wurin, kuma
anyi alamu a jikin kuyangin dake aikace-aikace a wurin, cewa su na dabam ne kuma
basu da yawa.
Sarkin ɓarayi Barban ya nuna waɗannan kofofin shiga guda huɗu, ya ce, "Daga cikin
waɗannan ƙofofi ta wacce ƙofa ce, bayi da kuyangin gidan sarautar suke shiga da fita?"
Aymanul Faris ya dube shi yace, "Ya shugabana, bamu da masaniyar komai akan
wannan gidan sarauta. Ba ma yawo iyakar mu tsibirin Gazwar." Kamar sarkin ɓarayi
Barban baiji abinda ya ce ba, "Yaushe da yaushe gimbiya Jaanu ke fitowa daga
turakarta? Adadin dakaru nawa ne suke tsaron lafiyarta? Wadanne irin hadimai ne suke
shiga cikin turakarta kai tsaye? Waɗannan tambayoyi suna buƙatar amsa kafun mu
samu nasarar sato gimbiya Jaanu." Sarkin ɓarayi Barban na zuwa nan a zancensa ya
mike tsaye, ya ce, "Ku shirya yanzu hadimaina zasu dauke mu su kaimu birnin
Damashkar." Yana gama fadin haka ya murza kambun dake daure a hannunsa na hagu.
Nan take wadannan aljanu guda uku suka bayyana a gabansa suna masu risinawa cikin
biyayya.
"Ku dauke mu, ku kaimu izuwa cikin birnin Damashkar yanzu!" Inji Sarkin barayi Barban.
Kafun ya gama rufe bakinsa tuni wadannan aljanu sunyi sama dasu su ukun, sun lulluka
cikin gajimare. Aymanul Faris da jaruma Riya dai kawai jiri suka ji ya ɗebe su, suka fita
daga hayyacinsu. Suna bude idanunsu kawai suka tsinci kansu a tsakiyar birnin
Damashkar, tare da wata zabgegiyar budurwa mai tsananin kyawu wacce basu san ko
wace ce ita bah, sanƴe cikin tufafi koraye.
Birnin Damashkar katon gaske ne, a cike yake da manya-manyan gine-ginen benaye,
kuma ko ina a tsare yake. Babu cunkuson gidaje ko shagunan kasuwa, komai a jere
yake layi-layi abin sha'awa.
Aymanul Faris ya dubi wannan bakuwar budurwa cikin mamaki ya ce, "Ke kuma wace
ce ke? Ya akayi kika zo inda muke? Wai shin ma nan ɗin wanne birni ne?"
Budurwar tayi murmushi ta ce, "Haba abokina, yanzu har ka manta ƙarfin sihirin tsafina?
Ina iya sauya siffa izuwa dukkanin abinda nakeso albarkacin wannan kambu dake
hannuna, wannan siffa da kuke kallo ba siffar kowa ba ce face ta kuyangin gidan
sarautar sarki Ayubul Zairiy. Yanzu take zamu wuce izuwa cikin gidan sarautar, zan
tsafeku ku koma 'yan mini-mini yadda zan iya sanya ku a cikin aljihuna." Budurwar na
zuwa nan a zancenta hankalin su Aymanul Faris da jaruma Riya ya kwanta don sun gane
waye ne.
Ba tare da bata lokaci ba, ta dafa kafaɗan Aymanul Faris da jaruma Riya a tare. Take
suka kankance suka zamo 'yan mini-mini tamkar 'ya'yan tsana, ta sunkuya ta daukesu
sannan ta jefasu izuwa aljihunta. Kai tsaye ta wuce cikin kasuwa ta sayo kayan marmari
a cikin kwando sannan ta nufi gidan sarautar sarki Ayubul Zairiy.
Da zuwa bakin ƙofar shiga gidan sarautar, sai dakaru masu tsaro suka buɗe mata ƙofa,
ba tare da anyi mata tambayoyin komai ba. Wannan budurwa ta shige kai tsaye cikin
gidan sarautar nan, ta kama hanya tayi ta tafiya. Sai da ta tabbatar tayi nisa da dakarun
nan sannan ta fiddo zanen taswirar gidan sarautar ta kura mata idanu. Abinda ta
fahimta shi ne ta ƙofar gabas ta shigo gidan sarautar, kuma ta nan ne babu tsaro sosai.
Daga wannan wuri da take tsaye zuwa inda turakar gimbiya Jaanu take, tafiya ta kusan
sa'a biyu. Al'amarin da ya dugunzuma hankalinta kenan, kuma kafin taje inda turakar
take dole sai ta ratsa ta cikin fadar sarki Ayubul Zairiy saboda daga cikin fadar, akayi
wata kofa wacce zata sada mutum da yankin gimbiya.
Ba tare da bata lokaci ba, wannan budurwa ta kama hanya kawai ta ci gaba da tafiya,
don gudun kada asirinta ya tonu. Duk inda ta gifta sai taga dakaru birjik nata kaiwa da
komowa, amma da yake tana sanye da kalar kayan kuyangin gidan sarautar babu mai
tsayar da ita ko kuma yi mata tambayoyi. Tana cikin tafiya taga wani ƙaton badakare ya
yiwo kanta gadan-gadan, al'amarin da yasa ta tsaya cak kenan, zuciyarta ta fara
bugawa saboda tsananin tsorata.
Lokacin da wannan badakare ya iso gabanta, sai ta gane waye ne. Aljani Ranganu ne a
cikin shiga irinta dakarun gidan sarautar. "Ya kai Barban kayi sani cewa, kuyangin gidan
sarautar nan basa zuwa yankin gimbiya saboda tana da kuyanginta na musamman
amintattu. Idan aka ganka a yankin gimbiya tofa lallai asirinka ya tonu, za'a gano cewa
ba kuyangin gidan sarautar bane. Sa'ar da muka yi ita ce sarki Ayubul Zairiy yayi baƙo a
halin yanzu shiyasa basa tare da gimbiya, don haka sai ka san dabarar da zaka yi ka
saceta kafin baƙon nan ya tafi." Aljani Ranganu na gama fadin haka ya wuce, ya nufi
wani bangare dabam.
Shi ko Barban kawai ci gaba da tafiyarsa yayi tamkar ba shi aljani Ranganu yazo ya yiwa
gargaɗi yanzu ba. Sai da ya shafe tafiyar sa'a daya cur sannan ya iso fadar birnin
Damashkar.
Fada ce kasaitacciya mai cike da kayan alatu iri-iri. Ginin fadar da zallar danyen yakutu
aka yi shi, sai sheki da walwali yake. A tsakiyar fadar an girke wata hamshakiyar karaga
ta mulki wacce aka kera da zallar farin zinari mai tsadar gaske irin wanda ake haƙowa
daga tsibirin Gazwar. Zaune akan wannan karaga sarki Ayubul Zairiy ne tare da wani
mutum wanda kallo daya zaka yi masa ka tabbatar da cewa shima sarki ne saboda
suturar dake jikinsa da kuma hular sarautar dake kansa. A gefen wannan mutumi wani
yaro ne wanda ba zai wuce shekarun Aymanul Faris ba, zaune bisa wata kujera ta
alfarma. Kallo ɗaya zaka yiwa yaron ka tabbatar da cewa ɗan wannan mutumin ne
saboda yadda suke tsananin kama.
A wannan lokaci dai fadar babu mutane sosai, daga sarakunan nan biyu sai dakarun
dake tsaron lafiyarsu. Daga gefe kuma sai fadawansu da 'yan majalisa.
"Ya kai babban abokina ba don komai, na taso daga kasata ba nazo kasarka sai domin
nemawa ɗana Marganu auren ƴarka gimbiya Jaanu a karo na takwas. Ina fatan dai
wannan karon zaka tausaya mana, ka dubi halin da wannan yaro nawa yake cika ka
amince mana." Wannan ita ce maganar da Barban ya fara ji daga bakin wannan sarki,
wato baƙon da yazo.
Sarki Ayubul Zairiy ya yi shuru ya faɗa kogin tunani mai zurfi, yana mai kallon yarima
Marganu. Kamar ba zai ce komai daga can sai ya numfasa ya ce, "Ya kai abokina kayi
sani cewa na tausaya muku kwarai da gaske. Amma ka sani kamar yadda kake
tsananin ƙaunar wannan yaro naka, baka son komai ya same shi, haka nima nake ƙaunar
'yata. A har kullum bani da burin da yafi ace 'yata ta auri ɗan sarki gagarumi kamar
wannan ɗa naka, amma ba zan yi mata dole ba. Abinda take so shi za'ayi. Don haka
yanzu zan tura a kirawo ita gimbiya, domin muji abinda zata ce." Sarki Ayubul Zairiy na
zuwa nan a zancensa ya daga kansa ya dubi kuyangar dake tsaye ya ce, "Ya ke Luwaisa,
na umarceki da kije turakar gimbiya ki taho min da ita." Barban a siffar kuyanga
Luwaisa ya zube kasa ya ce, "An gama mai duniya." Ta mike ta shige cikin kofar da
zata sada ta da yankin gimbiya.
Wannan shi ake kira SA'A, tun sa'adda sarkin barayi Barban ya shigo cikin wannan fada
yake ta zuru-zuru ya rasa ya zaiyi domin ya shige yankin gimbiya amma ga shi a karon
banza sarki da kansa ya bashi damar shiga, yana tsammanin kuyangarsa ce.
Lokacin da Barban ya shiga cikin yankin da gimbiya Jaanu take sai ya cika da mamaki
saboda ganin irin kayan alatun da aka shirya a wurin wanda ya ninka na ko'ina a cikin
gidan sarautar. Shuke-shuken furanni ne ta ko'ina masu tsananin kamshi da ban
sha'awa, wadansu kyawawan tsuntsaye nata shawakyi a sama, gwanin sha'awa.
Duk badakaren da ya kalli kuyanga Luwaisa a yankin gimbiya sai ya cika da tsananin
mamaki, domin ba'a taba kallonta a wurin ba. Hakan ne yasa dakaru suka dinga tare ta
suna yi mata tambayoyi amma sai tace dasu sarki ne ya turota ta dauki gimbiya domin
suje wurin yarima Marganu, duk wanda yaji wannan batu sai ya kama gabansa ya
kyaleta.
Sannu-sannu dai har Barban ya iso bakin ƙofar turakar gimbiya Jaanu inda ya sake yin
arba da wannan badakare wanda ya fara tare shi da farko (wato aljani Ranganu a siffar
dakarun gidan sarautar) Ranganu ya ce, "Ya kai Barban kada ka kuskura kace zaka
ɗauki gimbiya Jaanu izuwa gurin mahaifinta domin idan kayi hakan, damar saceta ya
kubce maka. Lallai ya zama dole ka san yadda zaka yi ka saceta daga nan, kayi amfani
da wannan taswira domin sanin wacce hanya ya kamata ka bi. Sannan ina mai sanar da
kai cewa idan ka samu nasarar saceta kada ka tsaya a ko'ina sai a kogon Razman
domin nan ne kaɗai inda zamu iya boyeta ba tare da ta bamu matsala ba. Haka kuma
kada ka manta da ajiye hatiminmu, da wannan batu nake maka sallama." Take aljani
Ranganu ya bace bat!
Barban ya tsaya cak ya shiga kogin tunani akan abinda ya kamata yayi, ya fiddo wannan
taswira ya ƙura mata idanu. Daga inda turakar gimbiya Jaanu take zuwa kofar fita daga
cikin gidan sarautar babu nisa sosai, inda matsalar take wannan kofa ita ce kofa mafi
tsaro a gidan sarautar kuma babu mai shiga da fita ta kofar daga sarki sai gimbiya da
sauran ahalinsa. Barban ya yi tunani yaga babu yadda za'ayi ya shawo kan gimbiya ta
amince ta fita ta

Please Login or Register in order to submit comment