Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kai wannan sarki, ka ɗakko aiki mai matuƙar wahala. Amma ina so kayi min bayani dalla-dalla akan yadda zamu fara tunkarar Barban, kuma muyi nasara ba tare da an samu matsala ba. Abu na farko da zaka duba a ina muka san zamu samo Barban?"
Sarki Ayubu yai dariya ya ce, "Dangane da ƙarfin sihirin Barban abubuwa kaɗan ka sani. Fiye da bokaye dubu arba'in suka taru a cikin wani ƙaton kogon tsafi, suka haɗa dukkanin ƙarfin sihirin tsafinsu a waje guda domin su gano ainihin Barban da inda yake. Tsahon kwanakin uku suka ɗauka suna wannan aiki, amma daga ƙarshe kogon tsafin ne yayi bindiga yayi jifa dasu gaba ɗaya saboda ƙarfin sihirinsu bai kai suyi arba da Barban ba.
"Duk duniya babu wanda ya taɓa arba da ainihin fuskar Barban hatta iyayensa kuwa, domin yana sauƙowa duniya wannan aljani ya sauya masa kamanni. Akwai wanda suke tunanin Barban ɗan ƙabilar banu Kuyuru amma a zahiri ba haka bane, saboda Barban ta tabbata dai raggo ne ba jarumi ba. A tarihin gidan Kuyuru ba'a taɓa samun raggo a zuri'arsa ba.
"Yadda zamu fara tunkarar Barban? Tarihi ya tabbatar da cewa Barban mahaifinsa ya fara yiwa sata, daga nan ya yiwa sarki Meher daga shi kuma sai sarki Kim Sam na birnin Sin. Sarki Meher ya mutu, bamu san a ina zamu sami mahaifinsa ba, wataƙila ma ya mutu. Amma mun san inda zamu sami sarki Kim Sam a birnin Sin.
"Kayi sani cewa babu wanda aka haife shi da iyawa. Kowa a wannan duniya yake koyan komai. Tabbas na san cewa a cikin waɗannan sata guda uku da Barban ya fara yi a rayuwarsa, akwai kura-kuren da ya tafka. Saboda a wancan lokaci bai gama ƙwarewa a harkar satan ba. Ka san meyasa na ce, kaine wanda zai iya taimaka min na cimma wannan buri nawa?
Boka Ruguzan ya kaɗa kai cikin mamaki.
Sarki Ayubu ya ci gaba, "Saboda kai kaɗai ne kayi saura daga cikin ƴaƴan boka Shashamu. Zaka yi mamakin yadda aka yi nasan wannan sirri."
Koda boka Ruguzan yaji wannan suna daga bakin sarki Ayubu sai ya ɗago kansa ya kalli sarkin, cikin tsananin mamaki. Daga bisani kuma ya miƙe tsaye ya nuna sarki Ayubul Zairiy da hannu yana ja da baya, yana cewa.
"Tabbas ba kaine sarki Ayubul Zairiyn da na sani ba. Ƙarfin sihirinka da sanin sirrukanka yafi na wancan Ayubu. Wancan ya kasance mai tsoron sarki Kuffuru kuma yana tsananin ƙaunar sarki Ratanam ya za'ayi ace duk abubuwan nan guda biyu sun kau? Haka kuma idan na kusanci wancan bana jin ƙanshin sihirin dake tashi a jikinka yanzu. Ina ainihin sarki Ayubul Zairiy yake?"
Koda jin wannan batu sai sarki Ayubul Zairiy ya bushe da dariya mai amo da amsa kuwwa, ya rufe idanunsa ya buɗesu ya yiwa boka Ruguzan wani kallo. Nan take boka Ruguzan ya dawo ya zauna akan wannan kujera, ya risina saboda ikon da ya gani a cikin idanun.
"Ya kai wannan boka. A har kullum mutumin da ya yarda da ƙarfinsa, da kuma ƙarfin shirinsa. To ɓoye kansa yake yi. Inda ace na bayyana asalin ƙarfina da ƙarfin sihirina da yanzu na jawowa kaina abokan gaba da yawa. Ina so ka sani cewa kowa a wannan duniya tamu, yana da aljaninsa wanda ZANEN ƘADDARARSU, RA'AYINSU da BURINSU yazo ɗaya.
"Sarki Kuffuru yana da aljani Buƙalshiyu Djinn. Barban yana da wannan ɓoyayyen aljani wanda yake taimaka masa. Nima ina da nawa aljanin. Idan baka manta ba nace maka duk duniya babu wanda ya kaimu sanin tuggu, to ra'ayin wannan aljani nawa kenan watau sanin tuggu.
"A halin yanzu zaiyi wuya wani abu ya faru a wannan duniya, wannan aljani bai kawo min labari ba. Abinda ya ɗaure min kai shi ne tunda aka sace ƴata wannan aljani bai kawo min labarin yadda akai ba. Da na tambaye shi ce min yayi shi kansa bai san yadda abubuwan suka faru ba, amma yana kyautata zaton wannan shu'umin aljani dake tare da Barban shi ne ya ɓoye komai.
"Ya kai wannan boka kayi sani cewa, irin sihirin tsafin dake jikin aljani Barzas. Bincike ya tabbatar da cewa lallai boka Shashamu ma yana da irinsa. Wato yana iya samar da taswira wacce zata bi diddigin duk inda mutum yake. A halin yanzu kaine kaɗai wanda ya rage daga ƴaƴan Shashamu kuma lallai akwai irin wannan sihiri a jikinka. Abinda nake so da kai shi ne kaje kayi shiri, kazo mu tafi birnin Sin wajen sarki Kim Sam domin samun bayanan yadda Barban yayi masa sata. Akan hanƴa duk zamu ƙarasa sauran bayanan."
Koda Ruguzan yaji wannan batu daga bakin sarki Ayubul Zairiy sai ya gasgata cewa lallai wannan sarki, shi ne ba wani ba. Kawai dai ƙarfin sihirin tsafi ne da kuma shiri. Bokan yayi sallama da sarkin sannan ya tashi ya fice daga cikin ɗakin.
*****
A ɓangaren Aymanul Faris kuwa, koda ya gama gano AURAN ZIYAS shi ne sarki Kuffuru sai ya cika da tsananin mamaki, ya mayar da littafin cikin aljihunsa sannan ya jawo bargo ya lulluɓe jikinsa gaba ɗaya. Faruwar hakan keda wuya barci mai nauyi yayi gaba da shi.
Washe gari da sassafe ya farka, ya shiga banɗaki yayi wanka. Ya sanƴo tufafinsa ya nufo ɗakin da su jaruma Riya suke ciki. Yana shigowa ɗakin ya iske jaruma Riya ita kaɗai zaune ta saka abincin kalaci a gaba. Gaban Aymanul Faris ya sara, yaje kusa da ita ya zauna.
"Ina kwana, masoyina?" inji jaruma Riya cikin tattausan harshe.
Sai da kalmar ƙarshe tayi yawo akan Aymanul Faris kafun ya amsa mata da lafiya, ya tambayeta ina mahaifiyarsa take. "Tana wanka!" inji ta.
"Jiya da dare kayi barci kuwa?" Jaruma Riya ta tambaye shi.
Aymanul Faris ya yi murmushi. "Me zai hana? Kar dai kice bakiyi bacci ba."
Jaruma Riya tayi murmushi wanda ya ƙara nuna kyawunta ta ce, "Ai idan nayi barci jiya da dare, ban kyautawa soyayyarmu ba. Bari faɗa ma jiya kwana nayi cikin farin ciki, ina tunanin ranar da za'a ɗaura mana aure..." Bata rufe bakinta ba taga yanayin Aymanul Faris ya sauya.
Shi kansa bai san me yasa ba amma da zarar an kawo labarin soyayya babu abinda yake saurin faɗowa a ransa kamar GIMBIYA JAANU, hakan ne ya tabbatar masa da cewa lallai ya kamu da mahaukacin ƙaunarta. A halin yanzu abinda yafi ɗugunzuma masa hankali shi ne tayaya zai sanar da jaruma Riya yana son gimbiya Jaanu? Tayaya zai sanar da mahaifiyarsa? Shin mahaifiyarsa zata yi maraba da wannan soyayya kuwa? Waɗannan tambayoyi su ne suke sakawa Aymanul Faris ciwon kai.
"Meya faru naga jikinka yayi sanƴi? Wani abu na damunka ne?" Riya ta tambaye shi.
Aymanul Faris ya ɗago kansa ya dubeta yayi mata murmushi mai taushi, wanda yasa duniyarta tayi haske. "A duk lokacin da aka kawo min maganar aure, babu wanda nake tunowa face maganganun mahaifina, ya kan ce min yana so ya kalli jikokinsa kafun ya mutu..." Hawaye ya zubowa Aymanul Faris. Ya yi shuru kawai.
Jaruma Riya ta dafa hannunsa guda ta ce, "Ya kai masoyina, ka kwantar da hankalinka. Kayi sani cewa komai daren-daɗewa sai mun ɗauki fansar kisan gillar da aka yiwa iyayenmu, ƴan-uwanmu da jama'armu akan teku. Tabbas wataran zamu koma birnin Damashkar mu saro kan sarki Ayubul Zairiy sannan mu kamo ƴarsa ta dawo kuyanga a garemu, mai hidima." Kalmomin ƙarshe da Riya da nufi ta faɗe su domin tana so taga ko Aymanul Faris yana son gimbiya Jaanu?
Kamar Aymanul Faris ya gano manufarta, kawai murmushi yayi ya jawo kwanon abinci gabansa, ya fara ci.
A daidai lokacin ne Hajriya ta shigo cikin ɗakin, sanƴe da fararen tufafi. Aymanul Faris ya gaishe da ita cikin girmamawa.
Ba tare da ɓata lokaci dukkansu suka fara cin abincin kalacin, suna ta hira har suka gama.
****RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 32: *Saiful Shiradu (1)*
*
*
✍️✍️✍️Umar Sangaru✍️✍️✍️
*
*
Bayan sun gama cin wannan karyawa kuma sun ɗan taɓa hira, Aymanul Faris yayi sallama da mahaifiyarsa ya koma cikin ɗakinsa ya zauna akan wata kujera. Ya fiddo wannan littafi wanda ke ɗauke da tarihin sarki Kuffuru da bayanan takobin Saiful Shiradu daga cikin aljihunsa, ya buɗe littafin ya ci gaba da karantawa daga inda ya tsaya. Watau daga inda sarki Kuffuru ya fara yin basaja a matsayin AURAN ZIYAS yana zuwa tsibirin Gazwar a matsayin bafatake.
((Alaƙar kasuwanci mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin sarki Kuffuru (Auran Ziyas) da mutanen tsibirin Gazwar domin yana sayan kayayyaki masu yawan gaske kuma da farashi mai kyau, wannan dalilin yasa ya zamo babban ɗan kasuwa a tsibirin, kuma sunansa ya shahara sosai. Duk inda kaje sai dai kaji ana labarinsa.
Sannu-a-hankali dai har ya fara jawo mutanen dake tsibirin izuwa gidansa da ya saya, suna yi masa aiki. Kai wataran har kwana ma suke a gidan.
Duk wannan nasibi da kararramawa da Auran Ziyas ya samu a tsibirin Gazwar, ko sau ɗaya bai taɓa yin arba da Hasanul Jalwar ba. Wannan abu yana damunsa matuƙa, da ya tambaya sai aka ce masa ai sarkin baya yawo, kuma babu mai zuwa wajensa face da izininsa. Aka ce bai cika mu'amala da baƙin attijirai dake zuwa tsibirin sayayya ba.
Auran Ziyas ya cika da tsananin mamaki, amma yayi shuru bai ce komai ba. Ya ci gaba da zama a wannan tsibiri tsahon wata da watanni, yana sayan buhuhhunan amfanin gona yana tarawa. Koda ya sami kamar wata bakwai sai ya ce yana so, ya koma birninsu domin ya dubo matarsa da ƴaƴansa.
Amma kafun ya tafi sai ya nemi mutanen wannan tsibiri su taimaka masa, su rakashi koda zuwa gaɓar teku ne, don baisan yadda zai iya kwashe kayayyakin da ya saya shi kaɗai ba. Mutane suka shaida masa indai yana so ayi masa wannan rakiya, dole ne yaje har gidan Hasanul Jalwar ya same shi ya roke shi alfarma.
Dama abinda sarki Kuffuru yake jira kenan, ya tambayi mutanen tayaya za'a yi masa iso wajen sarki. Mutane suka shaida masa cewa dole ne yaje ya samu sarkin yaƙi Jarata domin shi ne wanda yafi kowa kusanci da sarki. Auran Ziyas ya yi godiya sannan ya nufi gidan sadauki Jarata, dama yasan gidan.
***
A daidai wannan lokaci da KUFFURU ke ƙoƙarin neman izinin ganawa da Hasanul Jalwar, a wani ƙaton gida na ƙarƙashin ƙasa kuma wani abun al'ajabi ne ke faruwa. Wani kyakkyawan saurayi ne mai dogon gashi, ke zaune a gaban wani ƙaton rami wanda wata azababbiyar wuta keci a ƙasansa. Zafin wannan wuta ya gauraye ɗakin gaba ɗaya, don haka dole ne mutum yayi mamakin yadda akai wannan saurayi ya iya zama a cikin ɗakin.
Saurayin a zaune yake ya tankwashe ƙafafu kuma ya rufe idanunsa, kai da gani ka san wata halwa yake gudanarwa.
Tsahon rabin sa'a, wannan azababbiyar wuta ta fara yin bulli tana aman wata narkakkiyar dalma, harshen wannan wuta ya ɗinga tasowa sama yana tunkaro wannan saurayi. Amma wani abin al'ajabi shi ne tamkar ba shi wannan wuta ta tunkaro ba, ko a jikinsa.
Saura kamu uku wannan wuta ta ƙaraso inda yake ta tarwatse ta zamo wannan narkakkiyar dalma. Dalmar ta fara haɗewa a waje guda tana bayar da siffar takobi, har tsahon ɗan lokaci sannan ta gama haɗewa ta bayar da siffar zabgegiyar takobi mai tsaho da kaifin bala'i. Wani irin baƙin ƙarfe mai nauyi yayi tsalle daga ƙarƙashin wannan wuta ya shige cikin takobin, take wani nauyi mai ban tsoro ya shigeta. Tsahonta da tsininta ya ƙaru ainun.
Takobin ta taho a hankali akan iska ta tunkaro inda wannan saurayi ke zaune, kai kace tsuntsuwa ce mai fuka-fuki. Tana daidai saurayin ta dira akan hannunsa, jikinsa na taɓa ƙarfen takobin tayi wani haske mai ban al'ajabi wanda ya gauraye wannan ɗaki gaba ɗaya.
A sannan ne saurayin ya buɗe idanunsa, ya miƙe tsaye ya ƙarasa bakin wannan ƙaton rami ya tsaya. Faruwar hakan keda wuya wata siffa ta wani shirgegen aljani ta bayyana a cikin wannan wuta.
"Na tayaka murnar ƙarfafa takobin Saiful Shiradu!" inji aljanin cikin wata murya mai kama da ƙarar ƙonewar wuta.
Saurayin ya ce, "Ya kai Nara, ƙarfin wannan takobi ya kai yadda ake buƙata kuwa?"
Aljani Nara yai dariya ya ce, "Kwarai ma kuwa. Ina tabbatar maka a yanzu babu wani abu da wannan takobi ba zata iya hudawa ba. Walau dutse ko ƙarfe. Saboda da wuta aka ƙera takobin, ka san cewa kuma babu abinda wuta bata iya ratsawa ta cikinsa. Komai ƙarfin sihirin tsafin mutum, kuma komai maganin tsarin dake jikin mutum indai aka sare shi da wannan takobi sai tayi masa illa. Duk wanda ya mallaki wannan takobi zai samu kyautar aljanun-wuta guda goma wanda zasu na yi masa bauta, kuma zasu bi dukkan wani umarninsa.
"Ya kai HASANUL JALWAR ka kula da wannan takobi, kada ka kuskura ka rabu da ita dare da rana. Kayi sani cewa domin kada ku sha wahala yasa mai girma SAMUDUL ANSARI ya bamu ajiyar wannan takobi, kuma yace lallai mu tabbatar mun damƙata ga jininsa. In dai kana tare da wannan takobi babu wanda ya isa yayi nasara akanka, babu irin gumurzun yaƙin da baza ka iya shiga ba. Komai ƙarfin ƙato bai isa ya kai ka ƙasa ba.
"Amfanin wannan takobi ba zasu lissafu ba, amma idan ka fita yaƙi da ita koda sau ɗaya ne zaka ga kaɗan daga ciki. Da wannan batu nake yi maka sallama, mu haɗu a gaba."
Aljani Nara na zuwa nan a zancensa jikinsa ya tarwatse ya zama wannan wuta, sannan ta haɗe ta ci gaba da zaɓalɓala.
Hasanul Jalwar ya rataya wannan takobi a kafaɗarsa yaje ya tattaka matattakalar da tayi sama, ya fice daga cikin wannan gida na ƙarƙashin ƙasa. Yana fitowa ya nufi fadarsa inda ɗaruruwan jama'a ke jiransa.
Yana shigowa fadar takobin Saiful Shiradu tai wa jama'a sallama, take aka ruɗe da shewa ana ta yaba Hasanul Jalwar.
Kai da gani ka san cewa dama sun san abinda yaje yi a cikin wannan gida na ƙarƙashin ƙasa, Hasanul Jalwar ya yi ta ɗagawa jama'a hannu har yaje kan karagar mulkinsa ya zauna. A lokacin ne fadar gaba ɗaya tayi tsit, kowa ya kasa kunne yana jiran kalaman sarkin.
Sarkin ya tashi tsaye daga kan karagar mulkinsa ya fara magana da cewa, "Ya ku ahalin maigirma Samúdúl Ansari, barkan ku da wannan lokaci. Ni Hasanu ina farin cikin sanar da ku cewa, na samu damar ƙarfafa takobin Saiful Shiradu wacce mai girma Samud ya bar mana a matsayin makamin mu da zamu yaƙi abokan gaba da ita, kuma zamuyi amfani da takobin domin zuwa inda tsarkakken ruhinsa yake domin mu sami damar sake kafa daular Sháha. Wannan abin farin-ciki ne ya same mu, kuma tabbas zamu tsaya tsayin-daka wajen ganin mun yi amfani da wannan takobi mai albarka wajen dawo da kimar daularmu data rushe."
Jama'a suka ɓarke da shewa suna ta yiwa sarkin jinjina, kowa ka gani a fadar farin-ciki yake. Ba su da burin da yafi ace daular su ta da ta sake kafuwa.
Hasanul Jalwar ya sallami dukkanin jama'ar da ke fadar, kowa da kowa ya watse. Ya rage saura shi, da sarkin yaƙi Jarata tare da wani mutum wanda bai kasance ɗan wannan ƙabila ba.
Koda Hasanul Jalwar ya yi arba da wannan mutumi, sai ƙirjinsa ya buga da ƙarfi yaji takaici ya rufe shi. Ba komai ne ya sa Hasanul Jalwar jin takaici ba face baya so wani bare dabam, ya san sirrinsu.
Mutanen birnin Shàha-Deher suna da sirri sosai, kuma basu cika bayyanawa baƙi aƙidar su ba. Don haka ganin Auran Ziyas a wannan wuri ba ƙaramin sosa ran Hasanul Jalwar yayi ba.
Sadauki Jarata da Auran Ziyas suka ƙarasa wurin karagar sarki, suka zube a ƙasa suka kwashi gaisuwa. Hasanul Jalwar ya dubi Jarata cikin mamaki ya ce, "Sarkin yaƙi, waye wannan kuke tare da shi? Ban taɓa kallonsa a cikin wannan ƙauye namu ba."
Jarata ya risina ya ce, "Ya shugabana, wannan da kake kallo shi ne bafatake Auran Ziyas wanda yazo wannan tsibiri namu fiye da watanni bakwai yana ta sayayya. Yanzu ya ce yana so ya dubo garinsu ne kuma abinda ya saya yayi yawa sosai babu yadda za'ayi ya iya ficewa da abun shi kaɗai, ba tare da an taimaka da ƴan-rakiya ba. Shiyasa ya nemi izinin ganawa da kai domin neman wannan alfarma, mai martaba."
Shugaba Hasanul Jalwar ya yiwa Auran Ziyas kallon tsaf, sannan ya ce, "Ya kai wannan baƙo, meyasa tsahon daɗewarka a cikin wannan ƙauye baka nemi izinin ganawa da ni ba? Meyasa kake so a haɗa ka da ƴan-rakiya alhali yawancin attajirai masu irin wannan dukiya taka suna da yara masu yawan gaske da kuma dakarun dake basu tsaro? Daga wacce ƙasa kake? A ina ka samu labarin wannan tsibiri namu har da zaka zo ka fara sayayya a cikinsa?"
Koda Auran Ziyas ya ji waɗannan tambayoyi sai gabansa ya sara, zuciyarsa ta buga. Amma sai yayi sauri ya ɓoye bai bari su Hasanul Jalwar sun gane ba. "Abinda ya sa ban nemi iznin ganawa da kai ba shine naji ance baka yawo, kuma ba'a zuwa wajenka ba tare da izininka ba. Wannan shi ne dalilin da yasa ban nemi ganawa da kai ba sai da ta kama dole. Ya kai wannan shugaba mai adalci, kayi sani cewa bani da kowa a duniya dukkan ƴan-uwana da mutanen garinmu sun mutu sakamakon wani gumurzun yaƙi da aka gwabza da mutanen ƙabilar GORGON. Asalina ni ɗan birnin SAIZAR ne. Wannan shi ne takaitaccen bayani akaina." Ya ce.
Hasanul Jalwar ya yiwa Auran Ziyas wani kallo mai nuna yarda ya ce, "Tabbas na amince da bayanan nan naka, domin a shekarun baya akwai lokacin da ƙabilar GORGON suka addabi ƙasashen duniya da kisa. Haka kawai sai su afko birni suyi ta kashe jama'a."
Auran Ziyas ya risina ya ce, "Na gode bisa yardarka. An amince za'a bani taimakon ƴan-rakiya?"
Hasanul Jalwar ya yi shuru yana tunani, kafun daga bisani ya ce, "Me zai hana? Amma da akwai sharadi guda - iyakar inda mutanena zasuje shi ne LUSLEL."
LUSLEL wani ɗan ƙaramin yanki ne a cikin wannan teku, daga wurin mutum zai na hango bakin gaɓa kuma anan jiragen ruwa suke tsayawa.
"Na amince kuma ina godiya." inji Auran Ziyas.
Ba tare da ɓata lokaci ba, sadauki Jarata ya zaɓo zaratan-jarumai guda hamsin daga cikin dakarun wannan tsibiri suka ɗebowa Auran Ziyas dukiyarsa gaba ɗaya suka loda a cikin jiragen ruwa, sannan suka tuƙa jiragen ruwan suka nufi LUSLEL inda sarki ya basu umarnin tsayawa.
Sai dai amma tafiyar waɗannan dakaru aka kalla amma ba'a kalli dawowarsu ba, tun da hantsi har bayan la'asar. Shuru babu su, babu labarinsu.
Bisa wannan dalili ne yasa sarki Hasanul Jalwar tare da sadauki Jarata da waɗansu zaɓaɓɓun dakaru suka bi sawu.
Koda suka iso LUSLEL sai duk suka fashe da kuka sakamakon arba da abinda suka gani. Ba komai suka gani ba face gawarwakin waɗannan dakaru guda hamsin gaba ɗayansu akan allunan jiragen ruwa. Sannan ga waɗannan buhuhhuna na attajiri Auran Ziyas suna ta yawo a saman ruwa.
Wani abun mamaki shi ne gaba ɗaya waɗannan dakaru kisa kala ɗaya akayi musu, wato wuƙa aka sokawa kowannesu a ƙahon-zuci. Sannan kuma babu gawar Auran Ziyas amma akwai rigar da ya saka tayi face-face da jini. Hakan ne ya tabbatar da su Hasanul Jalwar shima attajirin ya mutu.
Cikin baƙin ciki da kuka mai tsuma zuciya, su Hasanul Jalwar suka kwashe gawarwakin waɗannan dakaru suka koma cikin ƙauyen Gazwar.
Koda jama'a suka yi arba da gawarwakin mutanensu sai suka yi ta kuka, suka yi ta tsinewa wanda yayi musu wannan ɗanƴen-aiki.
Tun daga wanzuwar ƙauyen Gazwar ba'a taɓa samun abun baƙin ciki da ya kai na wannan rana ba. Mutuwar matasa jarumai masu jini a jika har guda hamsin a irin wannan ɗan ƙaramin ƙauye ba wasa bane. Nan dai aka shiga hidimar binne gawarwakin nan kamar yadda ƙabilarsu ta tanadar.
***
A can wani ɓangare na gabashin duniya kuwa, bisa wani tafkeken teku. Wani murgujejen aljani ne keta tsala azababben gudu ɗauke da waɗansu mutane guda biyu bisa gadon bayansa. Abin mamaki waɗannan mutane biyu sun kasance mace da namiji ne. Namiji ya kasance saurayi dogo mai manƴa-manƴan gaɓɓai da sura ta sadaukantaka mai ɗaukar hankali. Ita kuwa macen ta fara manyanta, hakanne zai tabbatar da cewa mahaifiyarsa ce.
Inda mutum zai sami dama kaɗan ya ƙarewa fuskar wannan saurayi kallo, zai fuskanci ba wani bane illa SARKI KUFFURU NA BIRNIN KUFA. Wannan mace dake zaune a gefensa kuwa ba wata bace illa Kabshiya wacce muka gani tana gudu a cikin daji, lokacin da zata haife shi.
"Ya kai ɗana, tayaya ka iya ɓatar da kamanninka har ka zauna a ƙauyen Gazwar tsahon watanni bakwai ba tare da an ganoka ba?" Kabshiya ta tambaye shi.
Sarki Kuffuru yai dariya ya ce, "Zuwa nayi aka rina min gashin kaina ya koma ruwan-toka, sannan na aske gemuna da ƙasumbata. Na ce musu sunana Auran Ziyas daga birnin SAIZAR, shugaban nasu in banda ɓatan basira wai baya hulɗa da baƙin mutane. Hakan ne ya bani dama na baje kolina a garin, nayi ta sayan amfanin gona kamar ba gobe. Sai da na bari na tara kaya masu yawan gaske sannan na nemi iznin zuwa wajen sarkin, har ya amince ya bani dakarun rakiya guda hamsin." Sarki Kuffuru yayi shuru ya dubi Kabshiya ya ce, "Ya ke ummata kinsan yadda akayi na iya hallaka mutane hamsin a lokaci guda kuwa?"
Cikin tsananin mamaki Kabshiya ta girgiza masa kai alamun a'a.
Sarki Kuffuru yai murmushi ya ce, "Kisan sunƙuru nayi ta musu wato ɗauki ɗai-ɗai, kuma dukkansu a ƙahon-zuci na caka musu wuƙa. Ni kaina nayi mamakin zafin namata a wannan lokaci domin cikin abinda bai wuce rabin sa'a ba, duk na hallaka tsinannu!"
Hasamul-Sawaz dake ɗauke dasu yai dariya ya ce, "Wannan kaɗan ne daga cikin jarumtakar magajin shugaba Gauhan. Lallai yanzu ma aka fara. Sarakunan duniya da masu iko a cikinta sai sun durƙusa gaba ɗayansu sunyi mubaya'a ga KUFFURU jinin GAUHAN."
A daidai wannan lokaci ne ya dira a cikin wannan ƙaton daji. Hasamul-Sawaz yayi tsafi ƙasa ta tsage shi da su sarki Kuffuru suka shige cikinta. Suna shiga suka tsinci kansu a cikin wannan ƙaton dutse wanda aka gina a ƙarƙashin ƙasa.
Sarki Kuffuru da gimbiya Kabshiya suka cika da mamaki gami da farin ciki a lokaci guda, bisa ganin yadda wannan ƙatuwar ƙwalba ta fara samun jini. Don a wannan lokaci jinin dake cikin ƙwalbar ya kusa tsahon mutun.
"Tabbas waɗannan sadaukai hamsin da ka kashe," inji Hasamul-Sawaz. "Sun kasance asalin jinin Samudul Ansari kuma irinsu wannan ƙwalba take da buƙata, indai kana samun irinsu ina mai tabbatar maka da cewa ba zaka ɗauki lokaci mai tsawo ba wannan ƙwalba zata cika. Ka ga tana cika kuma babban burinka na duniya ya cika."
Sarki Kuffuru yai tsalle ya kwarara ihun

Please Login or Register in order to submit comment