Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Boka Ruguzan ya yi murmushi ya ce, "Ba ku san wannan sarauniya ba shiyasa kuke ta mamakin abubuwan da tayi. Bari na faɗa muku kaɗan daga cikin labarinta.
"Asalin mutanen dake rayuwa bisa tsaunin Barzasa ƴan wata ƙabila ce da ake kira Edwan. Mutanen wannan ƙabila basu da yawa sosai don baza su fi dubu goma ba gaba ɗayansu, gaba ɗaya rayuwarsu a saman tsaunika suke gudanar da ita amma ance suna da kyakkyawar alaƙa da baƙaƙen aljanun dake rayuwa bisa tsaunikan. Ance saboda tsananin yadda suke da dangantaka da aljanun suna iya aron ƙarfin aljanun suyi yaƙi dashi kamar yadda wannan sarauniya ta yi wani ɓakin-tsafi tayi nasara akan sarki Kuffuru. Mutanen ƙabilar Edwan basu da abubuwan bauta a kullum kamar waɗannan baƙaƙen aljanu dake taimaka musu.
"Duk faɗin duniya babu ƙabilar da ta kai Edwan sadaukai masu ƙarfin damtse har na Allah ya isa, shiyasa zaku gansu gajeru kuma murɗaɗɗu. Har yau har gobe mamakin yadda akayi Marganu ya iya ratsawa ta cikin babban birninsu nake, kuma ya fice lafiya. Wannan sarauniya ainihin sunanta shine Rauhanul-Ziyya Edwan. Ita aljani Barzas ya zaɓa a matsayin wacce zata na amfani da ƙarfinsa, shiyasa da tayi ɓakin-tsafi a kurkukun mutuwa gunkin aljanin ya bayyana kuma ya shige jikinta. Ahalin yanzu bamu san wanne hali take ciki ba, shin ta mutu ne lokacin da wannan kayan tsafi sukayi jifa da ita? Bamu sani ba. Kuma naga ko kaɗan sarki Kuffuru bai ɗauki wannan sarauniya da muhimmanci ba, maimakon ya fara tunanin ɗaukar-fansa akanta. Yanzu haka ƙoƙarin kamo shugaban ɓarayin duniya yake.
"Aljani Barzas yana da wata irin hikima ta dabam, yana iya yin tsafi taswirar duk inda mutum take a faɗin duniya ta bayyana. Irin wannan tsafi yayi ya samar da taswirar yarima Marganu wacce zata nuna duk inda yake a faɗin duniya. Sarki Ratanam idan baka manta ba boka Hubbazu ya nuna maka wannan taswira a madubin tsafinsa lokacin da kuka je neman tsari kai da Marganu."
Sarki Ratanam ya gyaɗa kai alamun hakane.
Boka Ruguzan ya ci gaba da bayani, "Da irin wannan taswira sarauniya Rauziyya take amfani tana bin diddigin yarima Marganu, kuma babu inda zai shiga a duniya ya guje mata."
Ashram ya dube su gaba ɗaya ya ce, "Yanzu wacce muka yanke? Shin zamu ƙwato Marganu daga kurkukun azaba-uku ko kuma zamu ƙyale shi a ci gaba da gana masa azaba?"
Shi dai Ashram ya kasance babban sadauki a birnin Hirtoliya kuma sarkin yaƙin birnin, ku san kullum yana tare da sarki Ratanam saboda akwai abokantaka mai ƙarfi a tsakanin su. Mutum zai iya cewa Ashram yafi kowa baƙin-ciki da wulaƙancin da aka yiwa Marganu, a ganinsa tamkar anci mutuncin masarautar Hirtoliya ne tunda an wulaƙanta yarima mai jiran gado. Babu yadda Ashram bai yi da sarki Ratanam ba akan su shirya rundunar mayaƙa suje har kurkukun mutuwa su ƙwato Marganu amma sai sarki Ratanam yaƙi saboda yafi kowa sanin Kuffuru.
"Kurkukun azaba-uku ba zata ɓallu da ƙarfin tsiya ba, akwai sojoji masu yawan gaske dake tsaron kurkukun. Haka kuma akwai kafin tsafi mai ƙarfi wanda waɗansu baƙaƙen aljanu suka haɗa. Babu mai shiga ko fita daga wannan kurkuku ba tare da umarnin sarki Kuffuru ba. Don haka tunanin ƙwato Marganu da ƙarfi mu ajiye shi a gefe," inji boka Ruguzan cikin nutsuwa. "Abinda ya kamata ayi shi ne sarki Ratanam da sarki Ayubul Zairiy suje da kansu har fadarsa su bashi haƙuri. Wataƙila zai amince ya saki Marganu."
Sarki Ratanam ya kaɗa kai ya dubi Ayubul Zairiy ya ce, "Abokina, shin idan Marganu ya fito daga kurkuku ka amince zaka aura masa ƴarka Jaanu?"
Koda jin wannan tambaya sai fuskar sarki Ayubul Zairiy tayi duhu, annurinta ya kau. Ya sunkuyar da kansa ƙasa ya gagara cewa komai. Tabbas shi kansa ya gamsu cewa da gaske Marganu ke son gimbiya Jaanu amma baya so yayi mata auren-dole. Ko ba komai ita kaɗai ce ƴarsa, dole ya ƙaunaceta fiye da komai a rayuwarsa.
Amma iya nacin duniyar nan Marganu ya nace akan aurenta, wannan abu yana bawa sarkin mamaki gami da tsoro. Shin ita kaɗai ce a duniya da har Marganu zaiyi ta hauka haka akanta?
"A har kullum maganata ba zata sauya ba," inji sarki Ayubul Zairiy. "Abinda gimbiya ta ce dashi zamu yi aiki. Idan ta amince, na amince. Idan kuma bata amince ba, ni ba zanyi mata dole ba."
Jin wannan batu na sarki Ayubul Zairiy ba ƙaramin ɓatawa sarki Ratanam da Ashram rai yai ba. Suka dubi junansu cikin ƙunan-rai.
Sarki Ratanam ya ce a ransa, tabbas na tabbatar da cewa Ayubul Zairiy ba ƙaunata yake ba. Sau takwas ina zuwa har birninsa neman auren ƴarsa amma ace bai bani ba, kullum magana ɗaya ko kunƴata baya ji. Duk wannan masifa da ɗana ya shiga akan kuɓutar da ƴarsa daga hannun ɓarayi bai gani ba bare ya tausaya masa, ya bashi auren Jaanu. Amma ba komai daga yau zan yanke duk wata alaƙa dake tsakanina dashi, kuma nayi alƙawari - komai daren-daɗewa sai na aurawa ɗana Marganu wannan ƴa tasa ko yana so, ko baya so.
Sarki Ratanam na cikin wannan zance a zuciyarsa ne, gimbiya Jaanu tare da wannan kuyanga suka shigo cikin ɗakin. Kuyangar tai sallama da gimbiya sannan ta juya ta fice.
Koda gimbiya Jaanu tayi arba da mutanen dake cikin wannan ɗaki sai gabanta ya faɗi, zuciyarta ta soma dukan uku-uku. A hankali ta ƙarasa kan ɗaya daga cikin kujerun ta zauna. Bayan ta gama gaishe da mutanen wurin sai ta sunkuyar da kanta ƙasa tana tunani.
Wata baƙuwar murya ce ta doki kunnenta, wanda ta sa tayi firgigit cikin razana.
"Gimbiya ki faɗa mana abinda Marganu yayi miki, kika tsane shi har kika ƙi yarda ki aure shi a karo na takwas. Dukda cewa mahaifinki da sarki Ratanam suna so ayi auren?" inji ɗaya daga cikin waɗannan sadaukan.
Gimbiya Jaanu ta gagara ɗago kanta balle ta basu amsar wannan tambaya, ga dukkan alamu kunƴa take ji ko kuma amsar wannan tambaya tana da nauyi sosai.
"Magana ake miki! Ki bamu amsa kin ji? Don ba ki san irin garari da tashin hankalin da yarima Marganu ya shiga akan ki ba" inji sarki Ratanam cikin tsawa.
Daga jin muryarsa ka san ransa a ɓace yake kuma zuciyarsa tana ta tafarfasa, don yana magana ne kamar zai tashi ya rufe gimbiya Jaanu da duka.
"Yarima bai yi min komai ba!" inji gimbiya Jaanu cikin sassanƴar murya.
A wannan lokaci sarki Ayubul Zairiy ya ɗago kansa daga kifuwar da yayi, ya dakawa gimbiya Jaanu wani harara wanda yasa tsikar jikinta ta mimmiƙe. Daga ganinsa ka san ransa a ɓace yake, saboda gani yake lallai wannan ƴa tasa ta raina masa hankali. A ce duk ƴaƴan sarakuna na wannan nahiya babu wanda ya burgeta, kuma ɗan babban amininsa yace yana sonta taƙi amincewa. Su dawo su kuma dawowa har sau takwas ace bata sauya ra'ayi ba, to wai me take nufi ne?
"Ki faɗa min hujja guda ɗaya wacce zata sa baza ki ƙaunaci Marganu ba, idan ba haka ba kuwa yanzun nan zan baiwa sarki Ratanam aurenki." inji sarki Ayubul Zairiy.
Maimakon gimbiya Jaanu ta bashi amsar wannan tambaya sai jikinta ya fara ɓari tamkar wacce aka saka a cikin ƙanƙara, idanuwanta suka ciko da ƙwalla ta fara kuka. Tabbas yau mahaifinta ya ƙureta, babu yadda ta iya dole ta faɗa masa gaskiya. Ita kanta bata san dalilin da yasa ta tsani Marganu ba, amma idan tuna tasirin SOYAYYA sai hankalinta ya kwanta. Ko kaɗan babu alamun wasa a cikin kalaman sarki Ayubul Zairiy kuma lallai indai bata bashi amsar da ta gamsar dashi ba, zaiyi abinda ya faɗa.
"Ina da wanda nake so!!!" inji gimbiya Jaanu.
Tsahon daƙiƙu ɗari da ashirin ɗakin taron ya ɗauka yana shuru, kowa yana jinjina maganganun da gimbiya Jaanu ta faɗa. Abu na farko da ya baiwa mutane mamaki shi ne duk cikin ƴaƴan sarakunan wannan nahiya babu wanda gimbiya ta zaɓa a matsayin mijin aurenta. Abu na biyu da ya ƙara basu mamaki shi ne gimbiya Jaanu bata yawo kullum tana cikin wannan gida nata, to a ina tayi arba da wanda ya burgeta har ta ji tana sonsa? Ga dukkan alamu waɗannan maganganu har cikin zuciyarta haka suke saboda sauyin yanayin da ta shiga.
"Kina da wanda kike so?" Sarki Ayubul Zairiy ya yamutse fuska. "Waye shi?"
Ashram ya ɗaga kai ya kalli sarki Ratanam ya jinjina masa kai, shima ya jinjina masa.
"Ba zan iya faɗa muku waye shi ba, a yanzu. Amma wallahi shi nake so, shi ne dalilin da yasa na ƙi na ƙaunaci Marganu!" inji gimbiya Jaanu tana zubar da hawaye.
Sarki Ayubul Zairiy ya sunkuyar da kansa cikin tsananin takaici, tabbas gimbiya Jaanu ta gama lalata alaƙar dake tsakaninsa da sarki Ratanam. Babu yadda za'ayi alaƙarsu ta ci gaba matuƙar aka ce gimbiya Jaanu ta auri wani ba Marganu ba, to wai shin waye ne wanda gimbiya ta kamu da sonsa? Shi dai a saninsa bata yawo, balle har ace zatayi arba da wani.
"Zance ya ƙare," inji sarki Ratanam. "Amma kiyi sani cewa gimbiya kin cuce mu, kuma kin wulaƙanta mu. Yanzu ace dama da akwai wanda kike so amma kika bari mukayi ta sawu-sawu izuwa birninku muna neman aurenki? Tabbas na fuskanci cewa mugunta aka min domin a rabani da ɗana, amma babu komai. Daga yau ba zan sake zuwa wannan birni naku ba, koda kece mace ta ƙarshe da tayi saura a duniya mun haƙura. Ki je ki auri wanda kike ƙauna. Amma ku sani cewa wannan wulaƙanci da kuka jawo aka yiwa ɗana, ba zai tafi a banza ba. Tabbas komai daren-daɗewa zamu ɗaukar masa fansa.
"Kayi haƙuri ya kai abokina wannan ita ce ranar ƙarshe ta abotarmu. Tabbas wannan cin mutunci da wulaƙanci da aka nuna min ba zaisa na ci gaba da hulɗa da kai ba. Daga yau ka manta dani, ka manta da duk abinda ya faru a tsakaninmu a baya. Ka ɗauke ni a matsayin sarki Samudul Ansari a rayuwarka. Na barku lafiya." Sarki Ratanam ya ƙare zancensa yana miƙewa tsaye gami da yafito Ashram da hannu suka nufi hanƴar ficewa daga fadar.
Sarki Ayubul Zairiy ya zauna kamar wanda aka zarewa laka ya gagara miƙewa ya bi bayan sarki Ratanam kuma ya gagara cewa komai, har sarki Ratanam da sadauki Ashram suka fice daga fadar. Tun yana hango keken dokinsu har suka fice daga cikin gidan sarautar gaba ɗaya.
Hawaye masu ɗumi suka fara zubowa daga idanun gimbiya Jaanu tazo har gaban sarki Ayubul Zairiy ta durƙusa tana mai fashewa da kuka, gami da neman yafiyarsa bisa abinda ta furta ɗazu wanda ya janƴo ƙarshen abokantakarsa da sarki Ratanam.
Tsahon ɗan lokaci sarki Ayubul Zairiy ko kallonta baiyi ba, yana ta tunani a cikin ƙwaƙwalwarsa. Daga bisani ya dubeta ya ce, "Tashi ki koma ki zauna kan kujerarki!"
Babu musu gimbiya Jaanu ta koma kan wannan kujera ta zauna. Sarki Ayubul Zairiy ya sallami sadaukan nan guda biyu dake zaune a ɗakin, suka risina sannan suka tashi suka fice. Ya rage daga shi sai boka Ruguzan da gimbiya.
"Ba kiyi min laifin komai ba ƴata." inji sarki Ayubul Zairiy. "Ra'ayinki kika faɗa mana don haka banga laifinki ba. Tayaya zan ƙi abinda masoyiyata take so, nayi mata dole? Na san illar soyayya kuma na san hatsarinta. Abinda sarki Ratanam da Marganu basu fahimta ba shine SO babu ruwansa da matsayi ko kyawu. Babu yadda za'ayi ka so mutumin da zuciyarka bata ƙaunarsa. Ni nasan komai daren-daɗewa alaƙar dake tsakanina da sarki Ratanam da sarki Kuffuru sai tazo ƙarshe saboda dukkaninsu kowa son zuciyarsa yake bi. Abinda ya kwantar min da hankali yasa na gagara yiwa sarki Ratanam magana kuma yasa na gagara dakatar dashi shine kince akwai wanda kike so. YANZU SHI NE NAKE SO KI FAƊA MIN WAYE WANNAN WANDA KIKE SO? Saboda so nake wata mai kamawa nayi miki aure, na huta da surutan abokaina."
Koda gimbiya Jaanu ta ji wannan tambaya daga bakin sarki Ayubul Zairiy sai ta gigice, gabanta ya faɗi, zuciyarta ta ci gaba da bugawa kamar zata faɗo ƙasa saboda tsananin tsorata da kuma nauyin faɗa masa sunan wanda take so.
Ganin wannan sauyin yanayi a tattare da gimbiya Jaanu yasa jikin sarki Ayubul Zairiy yayi sanƴi, ya tabbatar da cewa lallai akwai wani abu mai nauyi wanda gimbiya take tsoron faɗa masa. Kuma lallai yadda ta gigice ɗinnan idan ya ce zai matsa mata, zata iya faɗuwa a wurin ko kuma ta zauce.
"Tashi ki je, zan neme ki zuwa anjima." Ya ce.
Gimbiya Jaanu ta miƙe tsaye tana tafiya tana karkarwa kamar zata faɗi ta fice daga cikin wannan ɗaki, ta bar sarki da boka Ruguzan suna zaune.
"Akwai matsala..." inji sarki Ayubul Zairiy.
Boka Ruguzan ya ce, "Babbar matsala ma kuwa, na farko ka rasa babban abokinka sarki Ratanam. Na biyu ƴarka ta kamu da son mutumin da take tsoron faɗa ma."
Sarki Ayubul Zairiy yai ajiyar numfashi ya ce, "Samun matsala da abokina Ratanam ba wani abu bane, dama na san haka zata faru komai daren-daɗewa. Babu yadda za'ayi ace ƴata taƙi amincewa da Marganu har sau takwas kuma ace alaƙarmu ta ci gaba. Na san wannan ba zai yiwu ba. Abinda ya ɗaure min kai shine WAYE NE WANDA ƳATA TA KAMU DA TSANANIN ƘAUNARSA amma ta gagara faɗa min?"
Boka Ruguzan ya ce, "Nima abinda ya bani mamaki kenan, anƴa ba a cikin kuyanginta bane tayi arba da wani ko kuma cikin dakaru?"
Sarki Ayubul Zairiy ya kaɗa kai ya ce, "Zaiyi wuya gaskiya. Duk cikin kuyangin gimbiya babu namiji ko guda ɗaya gaba ɗaya mata ne. Haka kuma zaiyi wuya ta ƙaunaci ɗaya daga cikin dakaruna saboda ka san ba irin mutanen wannan ƙasar tamu bace. Irin mutanen birnin Rum ne dogaye manƴa-manƴa. WAYE WANNAN ZAI KASANCE?"
Boka Ruguzan yayi ajiyar zuciya ya ce, "Ajiye wannan batu a gefe, kana ganin samun matsalarka da Ratanam ba zata janƴo ma wani abun ba?"
Sarki Ayubul Zairiy yai dariya ya ce, "Babban boka. Kayi sani cewa a duk faɗin wannan nahiya babu babban sarki kamar sarki Kuffuru, daga sarki Kuffuru sai NI. Ratanam tamkar yaronmu haka yake, taimakonsa muke ba shi yake taimaka mana ba. Bari na faɗa ma wani abu, ina da sirrukan tsafi da ƙarfin dantse kamar Kuffuru. Yiwa sarki Kuffuru biyayya da nake yi, ina yinta ne kawai domin wata manufa amma ba don haka ba, da tuni na daina yi masa biyayya. Ko yanzu so nake koda sau ɗaya wataran ya gwada tunanin tunkarata da yaƙi, lallai zan bashi mamaki. In banda ragontaka da mutuwar zuciya fa wai sarauniya Rauziyya ce fa tayi jifa dashi uwa-duniya. Wannan wanne irin abun kunƴa ne?"
Boka Ruguzan yayi kasake yana jin maganganun sarki Ayubul Zairiy cikin tsananin mamaki. Wai yau ace sarki Ayubul Zairiy ne yake tunanin tunkarar sarki Kuffuru da yaƙi? Me sarki Ayubul Zairiy yake taƙama dashi?
"Babban boka. Ina da wani babban buri a duniya. Duk duniya babu wanda ya san wannan buri nawa, daga ni sai zuciyata. Amma yau zan faɗa maka wannan buri nawa, amma sai kayi alƙawarin zaka taimaka min ɗari bisa ɗari?" Inji sarki Ayubul Zairiy.
Boka Ruguzan ya zaro idanu cikin mamaki, don gani yake kamar ba sarki Ayubul Zairiy bane zaune a gaban shi.
"Meye wannan buri naka?"
****
RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 31: *Burin sarki Ayubu*
*
*
✍️✍️✍️Umar Sangaru✍️
*
"Ba zan faɗa maka wannan buri nawa ba, face kayi alƙawarin zaka taimaka min ɗari bisa ɗari. Saboda duk duniya babu mai iya taimaka min na cika wannan buri nawa face kai." inji sarki Ayubul Zairiy.
Boka Ruguzan yayi shuru ya faɗa kogin tunani. Ya za'ayi ya ɗauki alƙawarin da bai da tabbacin cikawa, kuma ba ma wannan ba; akan me zai ɗauki alƙawarin balle har yayi tunanin cikawa?
Yana cikin wannan tunani ne muryar Ayubu ta doki kunnensa. "Kada kayi tunanin wani abu ne mai tsananin wahala. Wannan buri nawa shi zai ɗaga kimarka da darajarka a duniya kuma kaima zaka iya cika burinka da shi. Abinda nake buƙata kawai shi ne yardarka ɗari bisa ɗari."
Boka Ruguzan ya ɗago kai ya dubi sarki Ayubu ya ce, "Ya shugabana. Burinka, nawa ne! Ni bawanka ne mai biyayya ga dukkanin umarninka. Tun daga ranar da ka bani muƙamin babban boka a wannan birni, nayi alƙawarin zan taimaka maka ɗari bisa ɗari a komai da komai naka. Duk da banji wannan buri naka ba, amma na sallama rayuwata, ƙarfina da dukiyata wajen ganin wannan buri naka ya cika. NAYI ALƘAWARI DA KABARIN MAHAIFINA ZAN TAIMAKA MAKA ƊARI BISA ƊARI. Yanzu kai nake jira kawai faɗa min wannan buri naka."
Sarki Ayubu yai murmushin jin daɗi, ya sa hannunsa ya dafa kafaɗar boka Ruguzan. Nan take boka Ruguzan yaji wani babban iko na sihiri ya buge shi, wata iska mai kama da sanƴin-hunturu ta cika wannan ɗaki. Tagogi da ƙofofi suka rurrufe kansu. Boka Ruguzan ya sake ɗago kai ya kalli sarki Ayubu cikin tsananin mamaki, domin gani yake kamar an sauya sarkin ne da wani sarki dabam. Mai Cikakken Iko.
"Ka san meyasa na ce maka bana shakkar sarki Kuffuru?" ya tambayi boka Ruguzan.
Ruguzan ya kaɗa kai alaman bai sani ba.
Sarki Ayubu ya yi murmushi ya ce, "Meyasa sarki Kuffuru ya wakilta ni a matsayin wanda zai jagoranci dakarun-sumame, a lokacin da muka karkashe ƴan ƙabilar banu Kuyuru? Ai indai ƙarfin damtse da iya yaƙi ne, Kuffuru yana tunanin ya fini amma meyasa bai je da kansa ba, ya kashe Hasanul Jalwar? Amsar wannan tambaya ita ce saboda ba zai iya ba.
"Ya kai Ruguzan kayi sani cewa, inda ace ni ne naje dajin Marsas nayi gaba-da-gaba da Barban dasu Aymanul Faris babu abinda zai hana ni kama su gaba ɗayansu. Ka san dalilin da yasa na ƙyale Marganu yayi wannan tafiya duk da cewa bani da tabbacin zai samu nasara, kuma idan bai samu nasara ba rayuwar ƴata tana cikin haɗari?
"Amsar wannan tambaya ita ce saboda ba wannan ne, lokacin da ya dace ace na kamo Barban ba. Akwai abinda nake jira.
"Tsahon waɗannan shekara da shekaru sarki Kuffuru fa, ɗauka yake wai tsoronsa nake ji shiyasa nake yi masa biyayya. Hmm. Biyayyar da nake yiwa sarki Kuffuru tana da manufa akwai abinda nake jira ya mallaka muyi baran-baran da shi. Ko ya bani wannan abu ko kuma na yaƙe shi, na ƙwata da ƙarfi."
Boka Ruguzan ya yi ajiyar zuciya cikin tsananin mamaki ya ce, "Ya shugaba, nifa ban gane ina ka dosa ba. Kana nufin duk jimawar da kayi kana yiwa sarki Kuffuru biyayya don wata manufa ce? Naga ai kaima gabar dake tsakanin ƙabilar banu Kuyuru da sarki Kuffuru ta shafeka sosai tunda kaima ɗan ƙabilar Huturu, kuma tun asali akwai wannan gaba a tsakaninku. Saboda haka ko sarki Kuffuru bai baka umarni ba, zaka iya kashe ƴan ƙabilar banu Kuyuru." Sarki Ayubu ya dakatar da boka Ruguzan da hannu yace.
"Babban boka. A tunaninka wane ne ya kashe sarki Deher? Kana tunanin ƴan ƙabilar banu Kuyuru ƙananan shaiɗanu ne? Kakan sarki Kuffuru sarki Meher babu irin ƙoƙarin da bai yi ba a wannan yaƙi domin sare kan sarki Deher amma baiyi nasara ba. Dole ƴan ƙabilata ya nema suka taimaka masa ya kashe sarki Deher, duk da ya haɗa kai da ƴan ƙabilata sai da suka sha baƙar wahala kafun su kashe sarki Deher, kuma a ƙarshe ma ragas suka yi. Tun a wancan zamanin; sarki Deher yafi sarki Meher ƙarfi, juriya da tsantsar jarumtaka. Shiyasa har yau har gobe, jinin sarki Deher yafi jinin sarki Meher ƙarfi nesa ba kusa ba.
"Sarki Kuffuru ya sha gwabza yaƙi da Hasanul Jalwar amma bai taɓa samun nasara akan shugaban ba. Sun gwabza yaƙi ya kai sau ashirin amma kullum kare jini, biri jini suke yi. Ƙarfinsu, iya yaƙinsu da ƙarfin sihirin tsafinsu yayi kunnen-doki. Wannan abu yayi matuƙar baiwa Hasanul Jalwar mamaki domin ko ba komai shi fa jinin Samudul Ansari ne, kuma ɗan asalin ƙabilar Kuyuru. Abinda Hasanul Jalwar bai sani ba shi ne sarki Kuffuru yana da aljanu ɓoyayyu da suke taimaka masa, shiyasa zaiyi wuya kaga anyi nasara akan sarki Kuffuru, kuma wannan shi ne dalilin da yasa ya yiwa dukkanin sarakunan wannan nahiya tamu kwarjini.
"Ni kuma ɗan asalin ƙabilar Huturu ne, a duniya babu wanda ya kaimu ƙarfin zuciya da sanin tuggu. Mu ne muka haɗa sarki Deher da sarki Meher yaƙi a shekarun baya har suka yi ragas, kowa a cikinsu ya rasa karagar mulkin. Don haka babu wanda yasan sirrin ƙabilar banu Kuyuru kamar mu. Kayi sani cewa da wani ɗalasimin tsafi nayi amfani a lokacin da na kashe Hasanul Jalwar, babu mai irin wannan ɗalasimi a duk faɗin duniya sai ƴan asalin ƙabilar Huturu.
"Idan mutum ya kira ɗalasimin zai ɓace daga inda yake tsaye ne, ya bayyana a duk inda ya so. Ba tare da an ankara ba. Hasanul Jalwar da duk wanda ke wannan wuri, bai ga sa'adda na ɓace ba. Abinda kawai aka gani shi ne bayyanata a bayan Hasanul Jalwar tare da takobin da na caka masa a ƙahon-zuci.
"Ba zan cikaka da surutu ba, babban boka. BABBAN BURINA SHI NE NAFI KOWA DUKIYA A DUNIYA, KUMA BIRNINA YAFI KOWANNE BIRNI KYAWU A DUNIYA, KUMA NAFI KOWA ƘARFIN MULKI, KWARJINI DA ISA.
"Wannan buri nawa ba zai cika ba face na kama ɓarawo Barban na tsare shi a kurkukuna. Abubuwa guda uku su ne zasu sa Barban ya zamo sanadin cikar wannan buri nawa. Abu na farko shi ne duk faɗin duniya babu wanda ya kai Barban dukiya, saboda dukiyar da ya tara mai tsananin yawa a wannan harka ta sata. Abu na biyu shi ne duk faɗin duniya babu aljanin da ya kai aljanin-Barban ƙarfin sihirin tsafi da cikar kwarjini da kamala. Duk wanda ya bautar da wannan aljani zai zamo gagarumin sarkin da babu kamarsa domin babu ƙasar da zata gagare shi ci da yaƙi, kuma babu abinda aljanin ba zai iya yi masa. Walau gina ƙatoton birni, gida da sauransu. Abu na uku shi ne mutum zai iya amfani da Barban yayi ta cimma burinkansa na duniya, saboda duk duniya a yanzu, babu ɗan-baiwa kamar Barban. Zaka iya amfani da Barban ka samo sirrukan abokin gabarka, zaka iya amfani da Barban ka sato duk abinda kake so a duniya. Amfanin Barban ba zai lissafu ba."
Boka Ruguzan ya ja dogon numfashi ya ce, "Ya shugabana, lallai wannan buri naka babba ne. Kuma zaiyi matuƙar wahala. Idan kayi la'akari da ƙarfin sihirin Barban, zaka ga abun akwai rikitarwa. Na farko tun bayyanar Barban fiye da shekaru goma yana sata, amma ko sunansa ba'a sani ba sai wannan karon. Na biyu duk da ansan sunan Barban amma ba'a san inda yake ba, babu wanda ya san kamanninsa balle har a iya shaida shi. Na uku koda mutum ya san inda Barban yake, zaiyi shakkar zuwa ya kama shi saboda wannan shu'umin aljani dake tare da shi. Tabbas

Please Login or Register in order to submit comment