Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yasa ya faɗa hannun wannan shaiɗaniya sai dai wani ba shi ba.
Koda sarauniya Rauziyya ta matsa sosai wajen ƙoƙarin buɗe wannan ƙofa sai wannan guguwa ta sake bayyana a gefenta, guguwar ta kanannaɗeta ta ɗagata sama tayi jifa da ita can cikin gajimare kamar yadda akaiwa sarki Kuffuru. Kai da gani ka san cewa iyaka ta wuce na amfani da wannan kayan tsafi.
****RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 22: *Boka Balwaz*
*
*
✍️✍️✍️ Umar Sangaru ✍️✍️✍️
*
Kafun Aymanul Faris wanda ke goye da Barban ya faɗa cikin wannan ƙorama, tuni ya sume sakamakon ƙarfin iskar dake kaɗawa. Yana faɗowa cikin wannan ƙorama ya nutse izuwa ƙarƙashinta, igiyar ruwa mai tsananin gudu ta ɗauke shi ta fara tafiya da shi, izuwa cikin wani ƙwararo wanda wannan ruwa yake wucewa ta cikinta. Aymanul Faris dai bai san abinda ke faruwa ba, kuma har a wannan lokaci Barban na goye a bayansa bai faɗi ba. Suna zuwa bakin wannan ƙwararo suka wuce ta cikinsa suka faɗa cikin asalin wannan ƙatuwar ƙorama wadda cibiya ta babban kogin garin.
Wani irin ƙatoton kifi mai tsananin girma ya bayyana ya haɗiye Aymanul Faris da Barban gaba ɗaya tamkar wanda ya haɗiyi abinci loma biyu, kifin ya yi nutso izuwa can ƙarƙashin ƙoramar inda yafi ko'ina zurfi sannan ya fara wani azababben gudu tamkar harba shi ake.
Sai da wannan kifi yayi tafiya ta tsahon sa'a bakwai a can ƙarƙashin wannan ƙorama cikin azababben gudu na gaban kwatance sannan ya ɗago sama, bisa mamaki sai ga shi ya bayyana a tsakiyar wata ƙatuwar teku kusa da wani ƙaramin tsibiri. Wannan ƙaton kifi ya amayar da su Aymanul Faris daga cikin bakinsa, suka faɗo kan wannan ƙaramin tsibiri. Kifin yayi girgiza ya rikiɗe izuwa siffar aljani Ranganu sanƴe cikin sulken yaƙi.
Aljani Ranganu yaje kan Aymanul Faris ya fiddo kayayyakin aikin likita ya fara ɗiɗɗinke raunikan dake kan cikin Aymanul Faris, sannan ya shashshafa masa magunguna akan sauran raunikan. Ranganu ya watsawa Barban ruwan sihiri, take Barban ya buɗe idanu cikin tsananin mamaki da kaɗuwa. Koda ya tsinci kansa bisa wannan tsibiri, kuma ya yi arba da aljani Ranganu sai ya cika da tsananin mamaki.
"Ya shugabana, ashe dama zaka iya cetonmu ka bari muka kusa rasa rayuwarmu a cikin wannan husumiya?" Inji Barban.
Aljani Ranganu ya yi murmushi mai cike da iko ya nuna Aymanul Faris ya ce, "Wannan ne ya ceci rayuwarka daga hallaka har sau biyu a wannan tafiya amma bani ba. Tabbas koda yanzu kaga dalilin da yasa na ce maka magajin RUHIN Samudul Ansari shi ne jarumin da muke jira. Yanzu dai wannan aiki ya kammala, farin lu'u-lu'u ta shigo hannunmu. Yi maza ka kira hadiman aljanunka uku su ɗaukeka kai da Aymanul Faris su mayar daku maɓoya, kayi jiƴƴar Aymanul Faris har ya warke sannan ku tafi aiki na biyu. Da fatan dai yana baka haɗin kai ba tare da gardamar komai ba?"
Maigida Barban ya dubi Aymanul Faris cikin tsananin mamaki da jinjina jarumtakarsa ya ce, "Ɗari bisa ɗari ma kuwa. Duk abinda na umarce sa da yai, yana yi." Aljani Ranganu ya ce, "Da kyau, yanzu sai ku koma maɓoya domin jiyyarsa." Yana gama faɗin haka ya ɓace. Barban ya shafi kambun dake hannunsa take waɗannan aljanu guda uku suka bayyana a gabansa suna masu risinawa, Barban ya daka musu tsawa ya ce, "Meyasa sa'adda na kiraku cikin wannan husumiya ba kuzo ba?" Ɗaya daga cikin aljanun ya ce, "Ba mu da ikon yin gaba da gaba da ƙarfin sihirin tsafin boka Balwaz shiyasa bamu bayyana, don idan muka bayyana hasken dake jikin wannan akwati zai ƙona mu gaba ɗaya." Barban ya yi murmushi ya ce, "To ku ɗauke mu ku mayar da mu fadata." Bai gama rufe bakinsa ba, waɗannan aljanu suka lulluka dasu cikin gajimare.
Lokacin da jaruma Riya taga yadda Aymanul Faris ya raunata sai hankalinta yayi mummunan tashi ta rasa sukuni. Ta gagara zaune ko tsaye. A wannan lokaci akan wani gado aka kwantar dashi, kusa da gadon mahaifiyarsa. Dukkansu jaruma Riya ta ci gaba da kula da lafiyarsu.
Bayan ɓacewar su Barban da hadimansa da tsahon daƙiƙa ɗari biyu kacal, waɗansu irin fararen aljanu guda uku suka bayyana akan wannan tsibiri. Dukkaninsu sun kasance manƴa-manƴa masu ƙira ta ƙarfi da ban tsoro. Jikinsu yadda ka san dutse haka yake saboda tsananin tauri, idanuwansu jajawur tamkar garwashin wuta.
Ɗaya daga cikin aljanun ya dubi ƴan-uwansa ya ce, "Duk yadda akayi waɗannan ɓarayi basu jima da barin wannan wuri ba. Amma binciken mu na tsafi ya tabbatar mana da cewa suna wannan wuri, ya akai haka?" Wanda ke tsaye a gefensa ya jinjina kai ya ce, "Duk yadda aka yi wannan kifi da ya haɗiye su ba dabba bace, lallai ina kyautata zaton wani shu'umin aljani ne." Na ƙarshen nasu ya dube su ya ce, "To yanzu meye abin yi?"
"Abin yi shi ne," inji na farkon. "Mu koma wajen shugaba Darwazu mu sanar dashi abinda ke faruwa. Wataƙila zai san yadda zaiyi tun da waɗannan ɓarayi sun bar ƙarƙashin ikonmu tunda sun fice daga cikin ruwa." Bayan kai komo suka amince su je su faɗawa sarki Darwazu abinda ya faru.
Zaune yake bisa wata hamshaƙiyar karaga ta mulki a tsakiyar wata makekiyar fada wadda aka shafe kusan shekaru huɗu ana ginata. Fadar ta ƙawatu sosai yadda komai iya bayar da labarin mutum bai isa ya wassafa kyawunta ba. Komai ka gani a fadar da zinare aka yi shi don haka in banda ɗaukar idanu babu abinda take. Sarki Darwazu na zaune bisa wannan karaga ya saka doguwar alkyabba baƙa mai beza ta wuya, fuskarsa na ɗauke da firgici da razana. Babu kowa a wannan fada daga shi sai kayan tsafinsa, wataƙila hakan ya samo asali ne saboda da daddare ne a wannan lokaci.
Ana cikin wannan hali waɗannan fararen aljanu guda uku suka dira a fadar, dukkaninsu suka durƙushe a gaban sarki Darwazu cikin tsananin biyayya. Har sun buɗi baki zasu fara magana ya dakatar da su. "Ba sai kun faɗa min abinda ke tafe daku ba, na san komai. Ku je na sallame ku. Kuma nagode bisa amsa buƙatata da ku kayi." Inji sarki Darwazu. Aljanu guda uku suka sake risinawa sannan suka ɓace ɓat.
Sarki Darwazu ya zaro wani madubin tsafi daga cikin jakar tsafinsa, ya shafi madubin tsafin da hannunsa na hagu. Madubin yayi wani haske sannan ya nuna hoton fuskar wani mutum mai tsananin kwarjini.
"Kazo fadata akwai magana, ina jiranka!" Inji wannan mutumi. Kafin daga bisani fuskarsa ta ɓace ɓat. Sarki Darwazu ya mayar da wannan madubin tsafi cikin jakar tsafinsa. Sannan ya zaro wata dardumar tsafi ja, wannan darduma ta warware kanta sarki Darwazu ya haye kanta ya zauna. Nan take wannan darduma ta tashi sama da shi suka fice daga cikin wannan fada suka afka cikin gajimare suka yi ta tafiya.
Bayan kamar sa'a bakwai wannan darduma tana tsala azababben gudu ɗauke da sarki Darwazu sai ta dira a tsakiyar wani ƙaton daji, mai ban al'ajabi. Komai na cikin wannan daji a daskare yake da wata irin farar ƙanƙara, bishiyoyi manƴa da ƙanana duk sun ƙanƙare, haka ma tsaunika da koguna duk a ƙanƙare suke. Tabbas babu yadda za'ayi halitta ta rayu a cikin wannan daji saboda tsananin sanƴin dake ratsa ƙashi wanda ya wuce misali. Sarki Darwazu na dira ya nannaɗe dardumar tsafinsa ya cillata cikin jakar tsafin sannan ya tunkari wani ƙaton tsauni dake tsakiyar wannan daji.
Tsaunin ƙato ne domin duk ya kere sauran tsaunikan dake cikin wannan daji amma shima a daskare tamkar dutsen ƙanƙara, wani abin al'ajabi dangane da wannan ƙaton tsauni shi ne siffar mutum ce dashi. Siffar a zaune take ta tankwashe ƙafafu gami da ware hannayenta guda biyu gefe da gefe. Akan kowanne hannu akwai fitilar wuta na ci, dukda cewa da tsakar-rana ne amma hasken wannan fitila ya ƙara haskaka dajin. Sarki Darwazu na zuwa gaban wannan tsauni, idanun wannan siffa ta mutumi suka buɗe suka kalle shi, tsahon lokaci kafun ɗaya daga cikin hannayen mutumin ya yiwa ƙasa-ƙasa.
"Ya kai wannan sarki, ka dafa wannan fitila. Ita ce ƙofar shiga wannan fada tawa!" Muryar wannan boka ta sake dukan kunnen sarki Darwazu.
Nan take sarki Darwazu yayi kamar yadda aka faɗa masa ai kuwa take, wani irin farin haske mai kashe idanu ya bayyana a gabansa, tsahon daƙiƙa goma wannan haske ya disashe. Wata ƙofa ta haske ta bayyana akan iska, sarki Darwazu yai tsalle ya shige cikinta ai kuwa take ta ɓace daga wannan wuri.
A tsakiyar wata tangamemiyar fada sarki Darwazu ya tsinci kansa, komai na fadar irin na manƴan ƙasaitattun bokaye ne. Akan wata karagar mulki ya hango boka Balwaz zaune ya harɗe sawu kamar wani sarki.
Boka Balwaz ya kasance tsohon mutum ɗan kimanin shekaru tamanin da ɗoriya. Gashin kansa fari fat kuma ya zubo har gadon bayansa, yana da kaifafan idanu masu sanƴa tsoro da ƙunci, gashin girarsa murtuƙeƙe ne kuma shima tuni ya gama zamowa fari. Yana dogon gemu da murɗaɗɗen gashin baki wanda shima gaba ɗaya furfura ce. A wannan rana yayi shiga ta fararen tufafi masu ratsin baƙi a kafaɗa. Ba shi da tsaho sosai, amma kakkaura ne.
Yana ganin sarki Darwazu ya nuna masa wata kujera ta alfarma ya ce ya zauna akai. Sarki Darwazu ya zauna akan wannan kujera ba tare da gardamar komai ba. Zaman nasa keda wuya, farantan abinci da abin sha suka bayyana a gabansa cikin iska. Boka Balwaz ya yiwa Darwazu umarnin fara cin wannan abinci.
Bayan sarki Darwazu ya gama cin abincin ne kuma ya wanke hannunsa ya juyo ya dubi boka Balwaz zaiyi magana amma bokan ya dakatar da shi. "Na san abinda ke tafe da kai, shiyasa nace kazo har wannan fada tawa domin mu tattauna," inji boka Balwaz.
Sarki Darwazu ya gyara zama ya ce, "Waye ne ya sace min lu'u-lu'una?" Boka Balwaz ya yi murmushi sannan ya nuna wani ƙaton allon tsafi dake sakale a jikin bango. Take hoton surar Aymanul Faris da ta maigida Barban ta bayyana, dukkaninsu sanƴe cikin waɗannan baƙaken tufafi masu ɓoye siffa. "Wannan mutumi da kake kallo shi ne ɓarawon da yazo ya sace wannan lu'u-lu'u, tare da taimakon wannan yaro," inji boka Balwaz. "Sunan wannan mutumi shi ne BARBÀN na birnin Shàha-Deher, sakamakon taɓa akwatin sihirina da yayi dukkan bayanansa sun bayyana a gareni. Shi ne gagarumin ɓarawon da ya addabi sarakunan duniya gaba ɗayansu da sata. Babu wanda ya san ainihin fuskarsa babu wanda ya taɓa yin arba dashi face amintattunsa. Barban ya yiwa sarakunan duniya guda tamanin da uku sata, kuma a halin yanzu nemansa suke ruwa a jallo. Kaine sarki na tamanin da huɗu da wannan gagarumin ɓarawo ya yiwa sata. Wannan ɓarawo baya satan abubuwan da basu da tsada ko muhimmanci, abubuwan da yake sata abubuwa ne masu tsananin tsada. Ina tabbatar da maka da cewa a halin yanzu duk faɗin duniya babu gagarumin attajiri kamar Barban saboda tsananin dukiyar da ya tara a fannin sata.
"Barban ya shafe shekaru goma yana sata amma dai-dai da daƙiƙa guda bai taɓa haɗuwa da ɓacin rana ba, tabbas yau in ba don taimakon Aymanul Faris da tuni mun kama Barban a hannunmu. Ya kai wannan sarki kayi sani cewa, burinka na son sayen katafaren gida a birnin Kisra ya tarwatse. Barban ya sace maka abinda yafi dinare miliyan ɗari bakwai daraja a dare ɗaya..." Sarki Darwazu ya dakatar da boka Balwaz da hannu ya ce, "Haba ya kai wannan boka, kace ka san buƙatar da ta kawoni amma tun ɗazu sai wani bani labari kake akan Barban... Barban... Ni ina ruwana da ko shi waye, damuwata ita ce ya za'ayi na ƙwato farin lu'u-lu'una kuma na kama waɗannan ɓarayi."
Boka Balwaz ya bushe da dariya ya ce, "Gaggawar me kake? Ka taɓa ganin inda aka kama mai laifi, ba'a ko shi waye da hatsarinsa ba?" Sarki Darwazu ya kaɗa kai, "A ina zan kama Barban da Aymanul Faris?"
Boka Balwaz ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Wannan tambayar ita sarki Faizara ya min... Kuma wannan tambaya tambaya ita sarakuna guda tamanin da uku ke jira, INA ZA'A SAMU BARBÀN? Barban bai kasance jarumi ba, raggo ne. Barban baya taƙama da komai face ƙarfin sihirin tsafi da zallar hikima da basira.
"Fiye da shekaru biyar na shafe ina bincike akan inda maɓoyar ɓarawo Barban take amma har kwanan gobe ban gano ta ba. Tabbas Barban na da ƙarfin sihiri fiye da tunanin mai tunani kuma yana da tsantsar hikima ta gaban misali. Jiya-jiyan nan nayi bincike akan inda za'a gano shi, da yake na ɗan samu kaɗan daga cikin bayanansa. Na gano cewa Barban bai taɓa aure ba, ba shi da kowa ba shi da komai. Mutun ɗaya da ya ragewa Barban a duniya shi ne azzalumin mahaifinsa wanda ya kashe babarsa. Sa'adda Barban yazo shiga cikin birninka kafin aljaninsa ya batar da idanuna akansa, naga yana kuka sa'adda ya kalli wani dattijon mutum mabaraci. Duk yadda aka yi wannan mutum yana da nasaba sosai da Barban, ya zama dole ka nemo shi da kanka. Ya kai wannan sarki kayi sani cewa idan na samu bayanai sosai akan Barban zanyi bincike na gano hanƴar da za'a bi a kamo shi, don haka inaga samun wannan mutumi zai taimaka mana sosai wajen kamo Barban.
"Kama ɓarawo Barban zata zo mana har da riba guda uku... Riba ta farko ita ce, zamu yi amfani da shi mu sami dukiyar da ya sata ya ɓoye a cikin taskokinsa wacce ake hasashen duk wanda ya mallaketa ba ma jikokinsa ba hatta tattaɓa-kunnen sa baza suyi talauci. Idan muka sami wannan dukiya zaka zamo gagarumin attajirin da babu kamarsa a duniya.
"Riba ta biyu ita ce, idan muka Barban zanyi amfani da jinin dake jikin wannan yaro da suke sata tare, na cimma babban burina a duniya. Kayi sani cewa wannan yaro ɗan wata ƙabila ce da ake kira Kuyuru. Kakansu na farko ya kasance sadauki uban sadaukai, ana kiransa Samudul Ansari. Bincike ya nuna wannan yaro shi ne magajin Samudul Ansari.
"Riba ta uku ita ce, waɗannan sarakuna guda tamanin da uku da Barban ya yiwa sata zasu dawo ƙarƙashin ikonka saboda ka kama bala'in da ya addabe su tsahon shekara da shekaru. Ya kai wannan sarki idan kayi la'akari da waɗannan ribobi da za mu samu kaga kenan ya zamana dole mu zage dantse mu kama Barban da yaronsa."
Sarki Darwazu ya yamutse fuska. "Ban gane ribobin da zamu samu ba? Tayaya kake tsammanin sarakuna gar guda tamanin da uku zasu ƙarƙashina ni ɗaya? Na san wayene Samudul Ansari kuma nasan haɗarinsa, duk wanda ya gaji wannan sarki sai ya zamo gagarabadau a duniya. Idan na fuskanceka so kake kayi amfani da jinin Aymanul Faris domin ka gaji Samudul Ansari, hakane?" Boka Balwaz ya tuntsire da dariya ya ce, "Duk abinda ka faɗa hakane, so nake na gaji Samudul Ansari ko kana adawa da hakan ne?"
Sarki Darwazu ya yi shuru yana tunani har tsahon ɗan lokaci sannan ya numfasa ya ce, "Wato dai a takaice, so kake kayi amfani da ƙarfin Samudul Ansari ka mulki wannan nahiya tamu gaba ɗaya, hakane?" Boka Balwaz ya sake bushewa da dariya ya ce, "Duk abinda ka faɗa hakane. Meyasa kazo wurina? So kake na taimaka maka ka kamo Barban, hakane? Meyasa kake so ka shiga cikin sha'anin da babu ruwanka. Ruhin Samudul Ansari babu mai gadonsa face ya kasance jinin Samudul Ansari ɗin, tayaya kake zaton irina wanda bai kasance asalin wannan jini ba zai gaje shi? Daga ji ka san akwai matsala don zan iya rasa rayuwata a wannan tafarki. Amma dukda haka na ƙuduri niyyar zanyi don haka ka barni nayi kawai." Sarki Darwazu yaji jikinsa yayi sanƴi saboda jin kalaman boka Balwaz. "To, yanzu faɗa min meye abin yi idan muna son kamo Barban?" Boka Balwaz ya ce, "Ka koma birninka ka nemi wannan tsohon mutumi, kayi masa tambayoyi akan Barban duk amsoshin da ya baka sai kazo ka sanar da ni zansan yadda zanyi, na gano mana inda wannan gawurtaccen ɓarawo yake domin mu mori dukiya da ƙarfin sihirin tsafi."
Koda sarki Darwazu yaji haka sai ya yi yaƙe yace, "Naji ɗazu kamar ka ce riba ta farko zamu gaji dukiyar da ya sata ko?" Boka Balwaz ya ce, "Kwarai kuwa." Darwazu ya ce, "Amma wannan dukiya ta kai dinare miliyan nawa?" Boka Balwaz ya ce, "Wa ya sani? Amma dai kayi lissafin ɓarawon da ya shafe shekaru goma yana satar irin wannan farar lu'u-lu'u taka?" Darwazu ya riƙe baki cikin tsananin mamaki. Da wannan suka yi bankwana da boka Balwaz, sarki Darwazu ya fito daga cikin wannan tsauni. Ya warware jar dardumarsa ta ɗauke shi, ta cilla da shi cikin gajimare.
Sarki Darwazu na dira a ƙofar birnin Askandariyya ya kirawo masu tsaron a gefe guda, cikin waɗansu dogayen bishiyoyi suka zazzauna.
"Ranar sha-tara ga wata waye yayi aiki da safe?" Inji sarki Darwazu.
Nan take waɗannan suka nuna wani badakare suka ce shi ne. "Kuffan? Lokacin da kake aiki da safe baka tare wani tsohon mutum baƙo ba, wanda yake bara? Inji Darwazu.
Koda Kuffan yaji haka sai zufa ta fara keto masa don yana tsammanin ko wannan tsohon mutumi wani babban laifi yayi. "Ran sarki ya daɗe. Tabbas ni ne wanda ya caje wannan mutumi, da fatan dai ba wani laifi yai ba?" Sarki Darwazu yayi murmushi sakamakon jin amsar Kuffan.
"Ko kaɗan. Ina fatan zaka iya bayyana mana siffofinsa domin a binciko shi a cikin wannan birni. Akwai bayanan da nake son samu a wajen wannan mutumi."
Kuffan ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Zan iya bayyana siffofinsa amma ba duka ba, don banyi masa ƙwaƙƙwaran kallo ba." Sarki Darwazu yayi murmushi sannan ya dafa kafaɗar Kuffan suka ɓace ɓat daga wannan wuri.
*****RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi 23: *A ina nake?*
*
✍️✍️✍️ Umar Sangaru ✍️✍️✍️
*
Tinjim! Ya faɗo cikin kogin sannan ya nutse izuwa ƙarƙashinsa. Daga ganin yadda ya faɗo cikin kogin da kuma yadda ya nutse kasan daman a sume ya faɗo. Koda ya yi nutso na tsahon kamu arba'in sai ya farfaɗo nan take ya soma yiwo ninkaya yana tasowa sama daga ƙarƙashin kogin, daƙyar da siɗin goshi ya samu ya taso saman kogin ya shaƙi numfashi.
Kana kallon fuskar mutumin zakaga a cike take da wasu-wasin yadda akayi ya faɗo cikin wannan kogi, wataƙila bada saninsa aka jeho shi ba. Idan ka ƙarewa fuskarsa kallo zaka ga ba wani bane illa sarki Kuffuru na birnin Kufa wanda ke fafata gumurzu da sarauniya Rauziyya har tayi amfani da babban ɗalasimin tsafi tayi jifa da shi uwa-duniya.
A fusace sarki Kuffuru ya fice daga cikin wannan kogi ya zauna a bakin-gaɓa yana mai tsananin mamakin irin ƙarfin sihirin sarauniya Rauziyya. "Ace sarki kamar ni ɗinnan, mai ƙarfin sihiri da ƙarfin mulki ace an samu nasara akaina. Kuma abin haushi ma ace mace ne, ba namiji ɗan-uwana ba... Kai..." Ya faɗa a cikin ransa, baisan sa'adda ya ɗaga kansa sama ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa ba.
Kash... Rashin sani yafi dare duhu. Inda ace sarki Kuffuru yasan abinda zai biyo baya, bayan kwarara wannan uban ihu da bai yi shi ba.
Yana gama wannan ihun ne yaga waɗansu irin samudawan dakaru masu kama da dakarun kurkukun-mutuwa suna firfitowa daga can saman wani dogon tsauni dake can nesa, sarki Kuffuru ya yiwa dakarun nan kallon raini. Ya laluɓa inda takobinsa ke ɗaure yaji batanan, maimakon ya damu kawai murmushi yayi. Koda ya duba jikinsa sai yaga ai babu komai a jikinsa face wannan bante, amma dukda haka kwarjininsa na nan.
Samudawan dakarun nan na ƙarasowa suka kewaye sarki Kuffuru a tsakiya gami da ritsa shi da makaman yaƙinsu, suka gagara afka masa saboda tsananin murɗewar jikinsa na JARUMTAKA da ƙanshin-sarauta dake tashi a jikinsa.
"Ya kai wannan baƙo mai ban al'ajabi, wane ne kai? Ya akai kazo nan?" Inji wata murya mai kaushi.
Sarki Kuffuru ya dube su ya yi murmushi ya ce, "Kafun nayi muku bayanin ni waye, shin zaku iya faɗa min A INA NAKE?"
"A ina kake? Kana nufin kace baka san inda kake ba?" Inji wannan badakare mai kaushin murya.
Sarki Kuffuru ya harare shi, "Daga ganin yanayin kayan da suke jikina, da yadda nake kallonku. Na yi maka kama da ɗan-yankin wannan ƙasa ta ku?" Ya ce.
"Kana yankin ƙasar Fairul-Faizar, birnin sarki Fairaz ɗan Kan'ana." Inji ɗaya daga cikin dakarun wanda ya fuskanci abinda sarki Kuffuru yake nufi.
"Ni ne sarki Kuffuru mai mulkin birnin Kufa, shin zaku iya kaini wajen sarkinku domin na gana da shi?" Inji sarki Kuffuru.
A firgice waɗannan dakaru suka ja da baya suna mayar da makaman yaƙinsu cikin kufe, sannan suka zube ƙasa gaban sarki Kuffuru suna masu biyayya.
"Tuba muke sarkin-sarakuna!"
"Da ace munsan kaine da bamu yi wani yunƙuri na cutar da kai ba"
"Ka yafe mana tabbas sarki Fairaz bashi da wani buri da ya wuce ya sadu da kai."
Shi dai sarki Kuffuru kawai bin waɗannan dakaru da kallo yayi, yana mamakin yadda yayi ƙaurin-suna a duniya. Daga birnin Kufa zuwa birnin Fairul-Faizar tafiya ce ta kusan watanni bakwai akan raƙumi ko doki, don haka ba nahiya ɗaya suke ba. Ace sunansa yazo har wannan wuri ai abin farin-ciki ne.
"Na ji. Nagode. Ku kaini wajen sarki Fairaz ɗin. Nima ina son ganin wane ne shi? Domin ina jin labarinsa." Inji sarki Kuffuru.
A guje waɗannan dakaru suka kawowa sarki Kuffuru ingarman doki ya haye, sannan suka yi masa jagora bisa dawakansu suka nufi bayan wannan dogon tsauni.
Bayan ƴar-gajeruwar tafiya suka kewayo ta bayan wannan tsauni inda sarki Kuffuru yai arba da wani ƙaton birni a can nesa kaɗan dasu. Irin waɗannan samudawan dakaru ya gani tsaitsaye a bakin ƙofar shiga garin suna gadi, da zuwansu bakin wannan ƙofa ƴan-uwansu suka ce su buɗe sarki Kuffuru ne. Nan take aka buɗe masa ƙofa suka afka cikin birnin Fairul-Faizar waɗannan dakaru na take masa baya gami da nuna masa hanƴa, har tsahon ɗan lokaci sannan suka iso wata makekiyar fada wacce zata iya yin kunnen-doki da ta sarki Kuffuru a kyawu da ƙawatuwa.
Duk inda su sarki Kuffuru suka ratsa a cikin wannan birni sai kaga jama'a sai bin sarki Kuffuru da kallo kawai suke, saboda tsananin kwarjininsa da kuma ƙirarsa ta jarumtaka.
A bakin ƙofar shiga wannan fada aka tsayar da sarki Kuffuru, ɗaya daga cikin dakarun nan ya shige cikin fadar domin ya yi masa iso a wajen sarki.
Da farko sarki Fairaz bai yadda da abinda wannan badakare ya faɗa masa ba, don a yadda yake jin labarin sarki Kuffuru da buwayarsa abu ne mawuyaci a ce ya tako da sawayensa yazo har birninsa. Amma da wannan badakare ya ce, ai ga shi can a ƙofar fada aje a duba idan ƙarya yake. Sai sarki Fairaz ya tashi da kansa ya nufi ƙofar fadan, fadawansa na take masa baya.
Sarki Fairaz ya kasance dogon saurayi kuma ƙaƙƙaura, yana da murɗaɗɗen jiki da tarin ƙwanji. Gashin kansa irin na sarki Darwazu ne wato ruwan toka, idanuwansa tamkar na mage haka suke wato ba baƙaƙe bane.
Sarki Kuffuru na tsaye kawai yaga

Please Login or Register in order to submit comment