Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ayubul Zairiy ke ƙulla aniyar yaƙi da mutanen ƙabilar banu Kuyuru. A wani ɓangare dabam na kudancin duniya kuwa, cikin wani ƙasurgumin baƙin daji wani gagarumin abu ne ke faruwa, a cikin wani katon tsauni dake tsakiyar wannar baƙin dajin. Tsauni ne ƙaton gaske wanda yake da faɗi da tsaho na ban al'ajabi, daga cikin tsaunin kuma aljanu sun fafe shi sun gina wani katafaren gida. Kai idan ka tsinci kanka a cikin wannan tsauni sai ka rantse kache ba'a dokar daji yake ba, saboda tsananin daular da aka shirya a wannan wuri. A tsaya bayyana wannan daula kuma sai a cika littafi mai shafuka dubu.
Wani matashin saurayi wanda dakyar ya wuce shekaru ashirin da biyar, zaune akan wata karaga ta mulki da aka ajiye a cikin fadar. Saurayin ya kasance kyakkyawa na kwatance, yana da dogon gashi wanda ya zubo har gadon bayansa, shi ba siriri bane kuma ba kakkaura ba, madaidaici. Jikinsa a sake yake ko kaɗan bashi da wata sura ta jarumta. Sai dai amma a damtsensa na hagu akwai wani kambun tsafi kore ɗaure, a wannan lokaci ya sa doguwar riga fara wadda aka yiwa ado da alharini.
Wani ƙaton allon tsafi ne aka kafe a gabansa yana kallon abinda ke faruwa a cikin fadar birnin Damashkar tsakanin sarki Ayubul Zairiy da boka Ruguzan, yana ganin duk wata tattaunawa da suke yi da kuma dukkanin wani shiri da suke ƙullawa. Saurayin ya bushe da dariya ya dubi dakarun da ke gefensa, abun mamaki ba wasu bane face su sadauki Rashbir da sukaje leken asiri tsibirin Gazwar.
"Dangane da binciken da nayi akan wannan baƙon jarumi, na gano cewa shi ne jarumin da na ɓata shekaru goma ina jiran bayyanarsa. A halin yanzu sarakuna guda uku sun ƙulla aniyar yaƙi da ƙabilarsa kuma tabbas za'a iya shafe su daga doron ƙasa. Yanzu haka nan da cikar mako guda dakarun sarki Ayubul Zairiy zasu yi DIRAR MIKIYA a tsibirin Gazwar, zasu kashe mazaje sannan su kama ƙananan yara da mata a matsayin bayi, kamar yadda yace. Ba lallai mu shiga wannan faɗan ba, tabbas na san cewa zaiyi wuya su kashe Aymanul Faris da mahaifinsa, ba tare sun gana musu azaba ba. Zamu yi amfani da wannan dama wajen kuɓutar da Aymanul Faris sannan mu kwaɗaita masa sana'armu." Inji wannan matashi a lokacin da yake shan ruwan inibi mai sanƴi.
****
A ƙauyen Gazwar akwai wata kyakkyawar yarinya mai suna Riya, 'yar wani babban sadauki da ake kira Jarata. Wannan yarinya ta kasance kyakkyawa ta gaban kwatance don anyi imani kaf, kabilar banu Kuyuru babu mai kyawunta. Tana da baiwar gashi wanda ya zubo har ƙasan kwankwasonta kuma baƙi ne sidik tamkar na Aymanul Faris, kullum gashin a gyare yake kuma a ɗaure. Gashin girarta yana da yawa sosai, idanuwanta kuma na nuna alamun kafiya da sadaukantaka wacce ta gada a wajen mahaifinta, sadauki Jarata. Jaraga sadauki ne na gaske, ya kasance mai baiwa yaran ƙabilar horon yaƙi a wani fili dake gabar teku. Tun da Aymanul Faris ya cika shekaru goma sha tara sai ya koma karbar horo a wajen Jarata.
A kullum sai Aymanul Faris ya yi arba da Riya a cikin waɗannan yara masu koyon yaƙi, a kullum sai yaga ta kura masa idanu tana murmushi. Riya ta gado mahaifinta a wajen sadaukantaka da sanin dabarun yaƙi domin ta kere dukkanin sauran daliban da take daukar horon dasu. Aymanul Faris ne kaɗai ya fita ƙarfi da iya yaƙi, saboda ya girmeta da tsahon shekaru biyu kuma tun yana ɗan karamin yaro ya fara karbar horo.
Rannan Aymanul Faris ya gama karbar horo akan gudu da saran abokan gaba a lokaci guda, ya nufi gida bisa wani ƙaton doki. Bayan tafiyar rabin sa'a sai ya iso ƙofar gidan inda ya iske shugaba Hasanul Jalwar zaune tare da dattijan kabilar sunyi zugum tamkar masu zaman makoki. Aymanul Faris ya sauka daga kan dokinsa sannan yaje ya durkusa ya gaishe dasu ya ce, "Lafiya? Me ke faruwa naga gaba daya kun sauya? Shin wani mugun abun ne ya taso?" Hasanul Jalwar ya dube shi ya ce, "Ya kai ɗana, je ka cikin gida kawai abinka. Wannan abin bai shafeka ba." Aymanul Faris ya kasance mai tsananin biyayya ga mahaifinsa ko kaɗan baya ketare maganarsa, don haka sai ya tashi ya shige cikin gidan.
Tafiyar Aymanul Faris keda wuya shugaba Hasanul Jalwar ya fiddo wata wasiƙa a cikin aljihunsa ya sake dubata, sannan ya dago kai ya dubi dattijan kabilar ya ce, "Tabbas wannan buƙata ta sarki Ayubul Zairiy ba mai yiwuwa bace, ya za'ayi haka kawai, ya ce mu tashi mu bar wannan tsibiri. Alhali anan iyaye da kakanninmu ma suka yi zamaninsu, babu shakka so kawai yake ya taƙalemu da yaki domin yasan yafi ƙarfinmu. Shin kuwa kunsan cewa a duk fadin duniya wannan tsibiri shi ne yafi dacewa da zaman mutane irinmu? Kada ku manta asalinmu mu mutanen birnin Shaha-Deher ne. Ba mu san komai ba a duniya in banda noma da kiwo, ba ma shiga sabgar kowa kuma babu mai shiga tamu. Yanzu mene abinyi? Zamu amince da buƙatar sarki Ayubul Zairiy ko kuma zamuyi masa tawaye? Kada ku manta daga cikin mutanen birnin Shaha-Deher mu kaɗai ne muka yi saura, adadin mu ba zai wuce dubu uku ba. Lallai idan muka ce zamu tunkari wannan sarki da yaƙi tofa tabbas sai an shafemu, a matsayina na shugaban wannan ƙabila na yanke hukunci. Amma kafun nan ina so naji meye ra'ayinku?"
Shugaba Hasanul Jalwar yayi shuru yana mai kallon dattijan. Wani dattijo mai farin gemu ya ce, "Ya ku 'yan uwana kuyi sani cewa fa, mu mutanen birnin Shaha-Deher bamu da bambancin ra'ayi ko aƙida. Duk hukuncin da shugabanmu ya yanke dashi muke aiki kuma ko cewa yayi mu faɗa wuta to zamu faɗa, don haka ya shugabanmu fada mana abinda ka yanke kawai, mu kuma muyi biyayya." Sauran dattijan suka gyada kai alamun amincewa.
Shugaba Hasanul Jalwar ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Shawarar da na yanke ita ce zamu bar wannan gari, zamu koma birnin Misra, saboda can ma akwai irin wannan albarka ta ƙasa. Ba don komai na yanke wannan hukunci ba sai domin tausayawa ƙananun yaranmu da kuma matayenmu, tabbas idan muka ce yaƙi zamuyi tofa sai an shafe dukkanin mazajenmu, sannan a kame matayenmu da 'ya'yanmu a matsayin bayi. Kun ga kuwa da haka ta samemu ai gwara muyi hijira mu bar wannan wuri." Dattijan suka sake gyada kai alamun amincewa.
****
A fadar sarki Ayubul Zairiy kuwa, boka Ruguzan ne ya bayyana fuskarsa a murtuke. Ya dubi sarki Ayubul Zairiy ya ce, "Ya kai wannan sarki. Shin me da me ka rubuta a wasikar da ka aikawa ƙabilar banu Kuyuru?" Sarki Ayubul Zairiy ya harare shi ya ce, "Na buƙaci su bar min kasata ko kuma na yaƙesu!" Boka Ruguzan ya daka masa tsawa ya ce, "Baka da hankali ne?! Ya muka yi da kai kwanakin baya? Na rantse da darajar tsafi idan ka kuskura mutanen nan suka gudu daga yankin kasarka, sai fushin mai-gidanka ya tabbata akanka kuma sai mafarkinka ya zama gaskiya!" Boka Ruguzan na zuwa nan a zancensa ya ɓace ɓat.
Shi kuma sarki Ayubul Zairiy sai zufa ta fara keto masa ta tsakar kai, idanunsa suka kada suka yi jawur, zuciyarsa ta fara tafarfasa. Ya dubi sarkin yakinsa ya ce, "Maza ka shirya min hawa tare da dakaru dubu goma." Sarkin yaki ya ce an gama. Ayubul Zairiy ya shige cikin gidansa domin fara shirin yaki.
****
Kafun cikar sa'a biyar tuni mutanen ƙauyen Gazwar sun gama haɗa nasu-inasu domin yin hijira, tuni shugaba Hasanul Jalwar ya tanadi manƴa-manƴan jiragen ruwa guda talatin domin yin wannan tafiya. Babu yadda Aymanul Faris baiyi ba wajen hana sarki wannan tafiya amma ina Hasanul Jalwar ya ƙi. A ganinsa yaƙin da ka san baza kayi nasara ba, barinsa ya fi.
Bayan an kammala shirye-shiryen komai, sai kowa da kowa ya shiga cikin jirgi suka yi bankwana da kauyen Gazwar suna kuka. Jirage talatin suka kama hanƴa suka nufi gabashin tekun cikin azababben gudu. Shugaba Hasanul Jalwar da ɗansa Aymanul Faris da sauran manƴan dattijan ƙabilar suna cikin jirgi guda wanda ke gaba, kowannensu na zaune akan kujera ta alfarma.
Lokacin da aka shafe sa'a biyu ana wannan tafiya sai rana ta fara disashewa tana duhu, ba wai magriba ce tayi ba. A'a ruwan kibbau ne suka saka rana tayi duhu. Kafun jama'a su ankara sai kawai suka ji sauƙar dubbanin kibiyoyi a kansu, nan fa suka fara ƙwala ihu suna mutuwa. Sadaukai suka yi kururuwa suka zaro garkuwowi suka tare kibban, amma duk da haka sai sama da mutum dubu suka mutu. Mafi yawa daga cikinsu mata ne da ƙananun yara.
Hasanul Jalwar ya ga yadda jama'arsa suka mutu sai ya fashe da kuka, ya kwarara uban ihu. Aymanul Faris ya zare takobinsa yana jiran bayyanar wadanda suka yi musu wannan ta'addancin.
Kwatsam! Ba zato sai ga bayyanar jiragen ruwa marasa adadi suna ta bullowa ta kowanne bangare, gabas da yama, kudu da arewa. Suka kewaye su Aymanul Faris suka yi musu ƙawanya. Akan kowanne jirgi akwai sojoji sama da ɗari biyu da doriya, kowanne soja ya rufe fuskar da rawani idanunsa kadai ake kallo. Kowannensu ya dame kwari da baka suna jiran umarni suyi harbi.
Ganin waɗannan dakaru ba ƙaramin dugunzuma hankalin su Aymanul Faris ya yi ba, domin sun tabbatar da cewa lallai an fisu karfi, yawa da makaman yaki. Wani narkeken kato ya ratso ta tsakiyar dakarun, abin mamaki fuskarsa ba'a rufe take ba.
Hasanul Jalwar ya hade gira ya harari sarkin ya ce, "Ayubul Zairiy? Me kuma yasa ka biyomu har nan, alhalin mun amince zamu bar maka kasarka? Ga shi yanzu har ka kashe mana jama'a wanda adadinsu ya kai dubu!" Ayubul Zairiy ya bushe da dariyar mugunta ya ce, "Tabbas ɗayanku anan ba zai tsira da rayuwarsa ba , sai na kashe ku gaba ɗaya, sannan na kona ku. Bani da burin da yafi na shafe mutanen birnin Shaha-Deher daga doron kasa, domin cika umarnin mai-gidana da kuma ramuwar abinda suka yiwa kakannina. Ya kai wannan sarki nasan baza ka manta da Yurbaru ba, kuma baza ka manta da Asasinu ba. Jinin wadannan mutane biyu yafi birnin Shaha-Deher da mutanen cikinsa daraja," Yana zuwa nan a zancensa ya juya dubi dakarunsa ya ce, "Ku kashe su gaba ɗaya. Har da wannan shugaba nasu da dansa, Aymanul Faris." Sarki Ayubul Zairiy na gama fadin haka ya juya ya koma tsakiyar dakarun.
Dakarun shugaba Hasanul Jalwar suka yi kururuwa suka afkawa abokan gaba, ba tare da sun jira umarni ba. Shi kuma Hasanul Jalwar kawai tsayawa yayi yana tunanin maganganun da Ayubul Zairiy ya faɗa masa, dukkan sauran kananun yara da mata sai suka dawo bayansa suka ɓuya.
Aymanul Faris ya yi kururuwa ya daga takobinsa sama ya faɗa tsakiyar dakarun nan, suka kacame da mugun azababben yaki sauran dakarunsu na take masa baya. Nan fa kasuwar rayuka ta bude, aka fara aika rayuka barzahu, jini ya fara yin feshi da fantsama izuwa cikin teku. Kururuwar maza da karafkiyar karafa ta cika dodon kunne, inda mutum na wannan wuri da tabbas sai ya kurumce sakamakon hayaniya da rugugin mazaje.
Sarki Ayubul Zairiy zama yayi akan wani katon dutse dake tsakiyar tekun, ya zubawa gumurzun idanu. Tuni ya cika da tsananin mamakin jarumtakar su Aymanul Faris, yana ayyanawa a ransa cewa, lallai waɗannan mutane ba ƙananun shaiɗanu bane.
Duk inda su Aymanul Faris suka saka a gaba sai dai kaga kawunan bil'adama suna tashi sama, jini yana feshi da kwarara a kan jiragen ruwan. Maza suna ta zubewa kasa kamar ana sassaɓe a gona, babu ko alamun zasu gaji. Aymanul Faris kawai sha'aninsa yake, ya sari gabas ko yamma duk inda yaso. An kasa samun sadauki guda a cikin wadannan dakaru da zai samu nasarar koda lakutar jikin rigarsa. Bayan Aymanul Faris akwai wata karamar yarinya mai irin shekarunsa itama ta gallabi wadannan dakaru kawai shaftare musu makwagoro take, da wata kaifaffiyar takobinta mai baki biyu. Babu abinda yafi ɗaukar hankali a wurin wannan yarinƴa kamar yadda take sarrafa takobi tamkar takobin ta kasance wani bangare na jikinta. Wannan yarinya ita ce RIYA.
Masu iya magana suka ce sarki yawa, yafi sarkin karfi. Koda aka shafe lokaci mai tsawo ana wannan azababben yaki sai dakarun su Aymanul Faris suka fara gajiya, aka fara saransu da sukarsu. Kwatsam! Sai wadansu bakin sadaukai guda goma suka bayyana a cikin rundunar Ayubul Zairiy suka fara kashe dakarun Aymanul Faris kamar ba gobe. Wadannan sadaukai fuskokinsu ba'a rufe suke ba, kuma dukkaninsu sun kasance zabga-zabgan karti masu karfi har na Allah ya isa. Ko rabin sa'a ba'a yi ba suka kashe kusan rabin dakarun Aymanul Faris. A lokacin ne hankalin Aymanul da jaruma Riya ya dawo kan waɗannan sabbin sadaukai guda goma.
Shugaba Hasanul Jalwar yana tsaye a gaban al'ummarsa duk gangancin da ya kawo dakarun Ayubul Zairiy kusa dasu sai kaga shi kaɗai ya tarwatsa su, ya kashe na kashewa. Wato dai bai shiga yaƙin ba amma yana tsaron al'umarsa.
Sadaukan nan guda goma suna cikin zubar da dakarun Aymanul Faris sai kawai suka ji an doke su ta baya, gaba dayansu kuma a tare. Saboda karfin dukan sai da suka yi sama sannan suka faɗo kasa tim a karshen kwale-kwale, biyu daga cikin su suka afka cikin teku suna kurma ihu don sun tabbatar da cewa sun hallaka. Sauran guda takwas ɗin suka miƙe tsaye zumbur, suka juyo suka yi arba da Aymanul Faris da jaruma Riya sun rike ƙugu, idanunsu na kan waɗannan sadaukai guda takwas.
Wani narkeken ƙato daga cikin sadaukan ya yage rigarsa yayi ihu sannan ya daga lafcecen takobin dake hannunsa ya rugo kansu Aymanul Faris, jaruma Riya ta dubi Aymanul Faris kawai ta gyada masa kai. Sai da ya rage bai fi taku goma ba wannan sadauki ya iso inda su Aymanul Faris suke, jaruma Riya ta koma bayan Aymanul Faris, shi kuma ya sunkuya bisa gwiwowinsa ta rugo da gudu ta taka kafadarsa ta tashi sama tamkar an harbata daga majaujawa, kafun sadaukin nan ya ankare, tuni jaruma Riya ta saka takobinta ta shaftare masa makwagoro. Take ya fadi kasa yana ta shure-shuren mutuwa.
Wannan jarumta da Aymanul Faris da jaruma Riya suka yi, sai da tasa sarki Ayubul Zairiy mikewa tsaye cikin tsananin mamaki. Ya dakawa sauran dakaru bakwai ɗinnan tsawa ya ce, "Ku banzaye! Ku shigesu gaba daya mana." Sadaukan suka yi kururuwa suka afkawa Aymanul Faris da jaruma Riya a tare.
Har yanzu a gefe guda ma ana ta fafatawa tsakanin sauran dakarun Aymanul Faris da dakarun Ayubul Zairiy, saura kiris ma a gama da dakarun Aymanul Faris saboda anfi su yawa nesa ba kusa kuma sun gaji ainun sakamakon tsahon lokacin da aka ɗauka ana wannan yaƙi.
Koda Aymanul Faris ya juya yaga halin da mutanensa suke ciki sai ransa ya baci, zuciyarsa ta kama tafarfasa. Suna haduwa da wadannan sadaukai bakwai suka sake garƙamewa da mugun azababben yaƙi na gaban kwatance, suka shiga kaiwa junansu sara da suka da takubba da masu. A wannan rana jaruma Riya ta nuna baiwarta ta kwarewa a fannin takobi, domin ita kadai sai da yanki kowanne daga cikin waɗannan sadaukai bakwai. Su kuma yanka daya kawai suka yi mata a dantsen hagu, dukda cewa zogi ya shigeta amma sai ta jure ta ci gaba da yaki. Sadaukan nan suka kewaye Aymanul Faris da jaruma Riya suka yi ta kai musu mugayen hare-hare, suka hana su sakat. Kai in ba don Aymanul Faris da jaruma Riya sun samu mugun horo ba, da tuni sun zama tarihi. Saboda tsananin nacin dakarun.
Jaruma Riya ta sake duban Aymanul Faris ta gyada masa kai tare da yi masa wata inkiya da idanunta. Take Aymanul Faris ya sunkuya cikin zafin nama ya cafi sawayen Riya sannan ya ɗagata sama, yayi hajijiya da ita. Ita kuma tayi amfani da wannan dama ta shaftarewa wadannan dakaru bakwai makwagoronsu a lokaci guda, ba tare da sun ankara ba. Nan take suka zube ƙasa matattu ko shurawa basu yi ba.
A wannan lokaci ne aka gama kashe gaba ɗayan dakarun su Aymanul Faris, wani sadauki guda ɗaya jal ne kawai ya rage. Shi dinma anyi masa sara ta ko'ina jini na zuba, kai da gani kasan tsantsar jarumta ce kawai tasa ya ƙi faduwa. Jaruma Riya tana yin arba da wannan mutum idanuwanta suka ciko da kwalla, ba wani bane sai mahaifinta sadauki Jarata mai bada horo. A lokacin aka luma masa wata wuƙa a ciki ta ɓullo ta baya, Jarata ya tofar da kakin jini a lokacin da gaba daya jijiyoyin jikinsa suka kukkumbura suka yi burdin-burdin, ya sa hannu ya mangare wanda ya soka masa wuƙar sannan ya durkushe ƙasa, yana kyarma. Jaruma Riya ta daka tsalle ta dira inda yake, ta rungumeshi ta fashe da kuka. Sai dai kuma gawa kawai ta runguma domin tuni ya mutu bisa gwiwowinsa.
****
A dai-dai wannan lokaci da ake ƙoƙarin cin nasara akan mutanen Aymanul Faris, a cikin wannan ɓoyayyen baƙin daji kuwa, cikin wannan ƙaton tsaunin. Wannan saurayin ne ya murza kambun dake daure a damtsen hannunsa na hagu, take waɗansu aljanu guda uku suka bayyana. Kowanne ɗaya daga cikinsu ya kai girman bishiyar kuka, suna da kai, hannaye da kafafu irin na bil'adama amma sauran siffar tasu duk ta bakaken aljanu ce. Suka risina a gaban saurayin.
Saurayin ya dube su ya ce, "Ku je ku taho min da Aymanul Faris da sauran mutanen ƙabilar banu Kuyuru da suke fafata yaƙi a yanzu haka, a tekun birnin Damashkar." Aljanun suka risina sannan suka bace bat.
***
Aymanul Faris na tsaye kawai yaji kururuwar mahaifinsa daga can gefe, cikin tsananin hanzari ya waiwaya. Kawai sai gani yayi sarki Ayubul Zairiy ya cakawa mahaifinsa wuƙa a kahon zuci, baisan sa'adda sarki Ayubul Zairiy ya bace ba. Ayubul Zairiy ya yi murmushi ya ce, "Na ɗaukarwa Yurbaru da Asasinu fansa abinda kuka yi musu, kuma na cika umarnin mai-gidana." Yana gama fadin haka ya sake ɓacewa. Aymanul Faris bai ankara ba kawai sai yaji tahowar wuƙa ta bayansa, zata huda shi. Cikin bakin zafin nama ya rike hannun sarkin, a lokacin da saura kiris ta huda shi. Nan fa sarki Ayubul Zairiy ya gama danna iya karfinsa akan ya caka wukar amma ya kasa, shi kuma Aymanul Faris ya gagara murde hannun sarkin. Nan fa ƙwanjinsu ya mimmiƙe, idanuwansu suka soma kaɗawa suna komawa ja. Har a wannan lokaci jaruma Riya na rungume da gawar mahaifinta tana ta rusa kuka, shima Hasanul Jalwar ya fara kakarin mutuwa. Ran Aymanul Faris ya yi mugun ɓaci, zuciyarsa ta harzuƙa. Ya sa ƙafarsa guda ya doki 'ya'yan marainan sarki Ayubul Zairiy sannan ya ruga da gudu kan mahaifinsa. Ayubul Zairiy ya durkushe bisa gwiwowinsa saboda tsananin zogin da yake ji.
Aymanul Faris ya tallafi mahaifinsa a lokacin da ransa ke kan gargara. "Ya kai ɗana! Tabbas ina baƙin ciki bisa ganin cewa zan mutu nabar ɗawainiya akanka ta kula da wannan ƙabila. Tabbas muna da manƴan abokan gaba a wannan nahiya musamman ma SARKI KUFFURU, SARKI RATANAM da SARKI AYUBUL ZAIRIY, waɗannan sarakuna basu da burin da yafi a wayi ace babu ɗan ƙabilar banu Kuyuru a duniya. Wasiyyata a gareka ita ce, ka sare kan kowanne daga cikin waɗannan sarakuna guda uku, amma kafin nan ka binciki tarihin kowanne daga cikinsu domin ka ji gabar dake tsakaninmu dashi. Wasiyyata ta ƙarshe a gareka ita ce ka kula da babarka!!!" A dai-dai lokacin numfashin Hasanul Jalwar ya dauke, idanuwansa suka kafe, jikinsa ya sandare. Aymanul Faris ya kwarara uban ihu ya rungume gawar mahaifinsa ya fashe da matsanancin kuka.
Sarki Ayubul Zairiy ya miƙe tsaye cikin tsananin fushi, ya zare wata zabgegiyar takobi dake ɗaure a bayansa. Ya daka tsalle ya dira a bayan Aymanul Faris ya kawo masa sara ta baya, da nufin ya raba shi gida biyu. Aymanul Faris ko motsawa baiyi ba, kai kace bashi aka kawowa wannan mummunan hari ba. Saura ƙiris takobin Ayubul Zairiy ta tsarge Aymanul Faris gida biyu kawai sai yaji an riƙe wannan takobi sannan an ɗaga shi sama, an fyaɗa shi a jikin kwale-kwale. Saboda karfin dukan sai da Ayubul Zairiy ya fasa kwale-kwalen sannan ya nutse cikin ruwa.
Yanayin wajen ya sauya, hasken rana ya kau. Iska mai sanƴi ta soma kaɗawa. Wadansu jibga-jibgan aljanu guda uku suka bayyana suka kwashe ragowar mutanen Aymanul Faris da shi kansa. Suka ɓace ɓat.
Sauran gawarwakin da suka mutu kuma, sai ruwan teku ya fara tsiri yana kifar da jiragen duk ya hadiye su.
****Ruhin Jarumtaka!!!
*
Babi na 3: *Sunana Kiláwud Barbàn!!!*
*

Umar Sangaru
*
Aymanul Faris ne zaune akan wata kujera a tsakiyar wata hamshaƙiyar fada wacce ba'a
san inda take ba a fadin duniya, an dai san cewa a cikin wani ƙaton tsauni aka ginata.
Duk bayan dakika sai Aymanul Faris ya miƙe tsaye da nufin fita daga fadar amma sai
wadansu hadimai su dakatar da shi.
"Ka jira shugaba yazo mana." Inji hadimin dake zaune a gefensa.
"Duk jama'arku suna zaune a cikin wannan fada cikin koshin lafiya, don me zaka daga
hankali?" Wani hadimi dake fesa turare ya tambayi Aymanul Faris.
Aymanul Faris ya harari hadimin. "Ka san me kake fada kuwa?" Inji Aymanul Faris. "A ina
muke nan?" Shima ya tambayi hadimin.
A dai-dai lokacin ne wani saurayi, kyakkyawa ya shigo cikin fadar. Fuskarsa cike da
annuri. Sanƴe yake cikin fararen kaya da aka yiwa ado da jar zinare ta wuya, a
kafafunsa kuma irin takalman mutanen birnin Misra ne. Idanunsa na bayar da tsantsar
kwarjini da kamala, ko kadan ba shi da wata sura ta jarumta amma har kullum kambun
tsafi na daure a damtsen hannunsa na hagu.
"Barka da zuwa, fadar sarkin ɓarayin duniya. Ayman." Inji saurayin a lokacin da ya
mikawa Aymanul Faris hannu don su gaisa. A zahiri Aymanul Faris bashi da niyyar
gaisawa da wannan saurayi amma suna haɗa idanu ya mika masa hannu suka gaisa.
"Daga yau ka zamo babban abokina." Inji saurayin. Ya kama hannun Aymanul Faris suka
nufi wannan ƙatuwar karaga suka zauna a tare.
"Waye kai?" Inji Aymanul Faris.
Saurayin ya yi dariya sannan ya ce, "Idan kana bukatar ka san ko ni waye dole sai ka saki
jikinka ka samu nutsuwa tukunna." Yana gama faɗin haka ya tafa hannayensa, wani
ƙaton teburi cike da farantan abinci ya bayyana a gabansu. Saurayin ya yiwa Aymanul
Faris bismilla sannan suka fara ci, bayan sun koshi sai teburi ya bace. Wani ƙaton kofi ya
sake bayyana cike da ruwan sanyi, nan ma suka sha.
"Je ka kwanta ka huta, kayi bacci. Gobe da safe zan sa a dawo da kai nan. Domin ka
san waye ni da abubuwan da nake so na cimma, da kuma dalilin da yasa na kawo ka
nan." Inji saurayin. Babu musu Aymanul Faris ya tashi ya bi bayan wani hadimi suka nufi
cikin gidan sarautar. Har sun zo kofar fita sai Aymanul Faris ya juyo ya dubi saurayin ya
ce, "Ina sauran mutane na suke?" Saurayin yayi murmushi ya ce, "Suna wani bangare
dabam

Please Login or Register in order to submit comment