Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Jarata suna tare da shugaban ɓarayi na duniya.
Aymanul Faris da jaruma Riya ƴan ƙabilar banu Kuyuru ne, kuma jinin sadaukin sarki
Samudul Ansari ne. Kayi sani cewa idan akwai abinda sarki Kuffuru ya tsana fiye da
mutuwarsa a duniya bai wuce mutane masu wannan jini ba. Tabbas zaka bashi labarin
Aymanul Faris da jaruma Riya da haɗarin da suke tattare da shi ga rayuwarsa da ma
mulkinsa, idan kayi sa'a zai iya baka agajin dakaru da zasu yi maka rakiya a yayin
wannan tafiya taka. Ka sani cewa mutanen birnin Kufa ƴan asalin birnin Shàha-Meher,
sadaukan gaske ne kuma zaratan jarumai ne. Lallai idan ka samu irinsu a wannan tafiya
taka, zasuyi maka amfani.
"Dangane da batun ƙetarewa ta cikin dajin Djinn da dajin Shiwazu kuwa, sarki Kuffuru ne
kaɗai zai iya baka sirrukan waɗannan dazuzzuka da yadda ake ƙetarewa ta cikinsu.
Saboda a cikin dajin Djinn aka haife shi sannan aka raine shi a dajin Shiwazu. Wato dai a
taƙaice ina so na fayyace maka cewa nasarar da zaka samu a wannan tafiya tana
tattare da amincewar sarki Kuffuru ɗari bisa ɗari, dole ne kayi masa biyayya akan
dukkanin abinda ya umarceka matuƙar kana so ka mallaki gimbiya Jaanu. Shin ka
gamsu da bayanaina ko kuma kana da tambaya?" Koda jin haka sai yarima Marganu ya
yi wuf ya ce, "Akwai tambayoyi kuwa. Mene ne sharuɗɗan sarki Kuffuru? Shin a
tunaninka zai buƙaci wani abu daga gareni? Meye al'adar arnan daji dake kan tsaunin
nan dake gaba da dajin Shiwazu?" Boka Ruguzan yayi shuru gami da kurawa yarima
Marganu idanu yana mamakin tsantsar basirarsa da hikimarsa. "Sharuɗɗan sarki Kuffuru
a bayyane suke baya son raini, baya son takura, baya son gardama. Yana son ganin
mutum jarumi, mai son sayar da rayuwarsa kamar kai ɗinnan. Abubuwan da na sani
dangane da sharuɗɗan Kuffuru kenan amma ka bi shi a hankali. Amsar tambayarka ta
biyu ita ce ba zai buƙaci komai daga gareka ba face ka kawo masa kan Aymanul Faris
da jaruma Riya, saboda ya tsani ƴan ƙabilar banu Kuyuru kamar yadda ya tsani
mutuwarsa. Amsar tambayarka ta uku ita ce, waɗannan arnan daji babu wanda yasan
asalinsu, al'adarsu kuma ita ce a duk ƙarshen mako sai sun yankawa wani gunkinsu jinin
bil'adama guda biyu, ya sha jininsu sannan hankalinsu yake kwanciya. Gunkin bai damu
da inda suke samo jinin ba shi dai damuwarsa kawai a yanka ko kuma ya sauƙe musu
bala'i da masifa, saboda haka hatta ƴaƴan su ƙananu suna yanka masa. Ya kai babban
jarumi, sarki Kuffuru ya fini sanin komai dangane da waɗannan dazuzzuka guda biyu da
birnin arnan daji, saboda haka shi zai maka bayanin komai matukar ya amince. Ina
ganin sai muyi sallama da juna sannan kayi haramar tafiya, tare da aljanina wai shi aljani
Gulzab." Koda boka Ruguzan yazo nan a zancensa sai ya shafi wani mulmulallen ƙarfe
dake jikin karagar mulkinsa, take ƙasa ta tsage wani narkeken aljani ya ratso ta cikinta,
ya zo ya tsaya kikam a gaban Ruguzan.
Aljani Gulzab katon gaske ne, yana da kai irin na bil'adama. Amma hannayensa da
sawayensa irin na kosasshen kada ne, yana manya-manyan fuka-fuki guda hudu sannan
sai wata murtukekiyar jela irinta kada. Gangar jikinsa irinta gwaggon biri ce, ga tarin
kwanji da tafka-tafkan damatsa.
Aljanin ya risina a gaban boka Ruguzan ya ce, "Ga ni gareka ya shugabana, me kake da
bukata?" Boka Ruguzan ya ce, "Ina so ka ɗauki wannan sadauki, ka kaishi birnin Kufa.
Daga nan sai ku wuce izuwa dajin Djinn da dajin Shiwazu ku dangana da dajin Marsas
domin ya aiwatar da wata muhimmiyar buƙata tasa." Koda jin haka sai aljani Gulzab ya
kwarara uban ihu mai kama da sauƙar aradu, daga bisani ya fashe da kuka ya ce, "Haba
ya shugabana. Laifin me nayi maka kake son kaini ga halaka? Shin ka manta cewa duk
tsautsayin da ya kai aljani kusa da dajin Djinn ko dajin Shiwazu ƙonewa zaiyi nan take,
gaskiya ka yafeni amma wannan aiki yafi ƙarfina." Boka Ruguzan ya tuntsire da dariya ya
ce, "Ai ba cewa nayi sai ka shiga cikin dazuzzukan da shi ba, da zarar kun kusa isowa
sai ka sauƙe shi, ya ƙarasa da kansa, amma dole ne ka jira shi yaje ya dawo tsahon
kwanaki talatin. Idan bai dawo ba sai kayi naka wuri." Aljani Gulzab ya yi murmushi ya
ce, "Yawwa yanzu naji kan zancen." Kafun yarima Marganu ya ankara tuni yayi wuf, ya
sure shi sun ratsa ta rufin ginin ɗakin sun fice tamkar haske mai ratsa duhu.
Yarima Marganu ya tsinci kansa zaune bisa aljani Gulzab cikin kwanciyar hankali da
ƙoshin lafiya. In banda takobi da garkuwa babu wani makami da yarima Marganu ya
taho dasu. Shi ko aljani Gulzab sai keta giza-gizai yake tamkar tauraruwa mai jela, iya
rayuwar Marganu ko a labari bai taba jin labarin aljani mai gudu irin na Gulzab ba. Sai
da suka shafe sa'a bakwai suna tafiya ba tare da ɗayansu ya ce uffan ba. "Wai yanzu
duk gudun nan da kake ace har yanzu bamu isa birnin Kufa ba?" Marganu ya faɗa kasa-
kasa. Aljani Gulzab ya bushe da dariya ya ce, "Ka san nisan dake tsakanin birnin
Damashkar da birnin Kufa kuwa? Ina tabbatar maka da cewa inda akan raƙumi kake ko
doki sai kayi tafiyar kwana saba'in sannan zaka isa, nan ma babu yada zango." Yarima
Marganu ya jinjina kai ya ce, "To yanzu mun kusa isa can ɗin ne?" Aljani Gulzab ya ce,
kwarai ma kuwa.
Bayan shuɗewar kamar daƙiƙa ɗari bakwai da tamanin, sai yarima Marganu ya fara yin
arba da dogayen gine-gine a cikin gajimare. Al'amarin da ya bashi mamaki kenan, ya
dubi Gulzab ya ce, "Wai shin waɗannan gidajen kam, a cikin gajimare aka gina su ko
kuma suna tushe tun daga ƙasa?" Aljani Gulzab ya sake bushewa da dariya ya ce, "Ya
shugabana, ai waɗannan gidaje da kake kallo benayen sarki Kuffuru kenan. Duk duniya
shi kaɗai keda kalarsu." Aljani Gulzab na rufe bakinsa suka yi arba da wani murjejen
mutum tsaye bisa iska a gabansu.
Sarki Kuffuru basamuden kato ne, yana da faffaɗan kirji da manƴan kafadu waɗanda
suka dace da girman kirjin nasa. Gaba ɗaya jikinsa a cuccure yake kamar an jera
duwatsu, sai wasu irin jijiyoyi da suka yi burdin-burdin. Gashin kansa jajawur ne irin na
gimbiya Jaanu, idanuwansa farare ne ƙal. Duk inda ake neman riƙaƙƙen sadauki da an
samu wannan mutumin an gama. Yana riƙe da wata zabgegiyar takobi mai kaifi biyu, a
hannunsa. Idanuwansa na nuna tsantsar kafiya da jajircewa, a wannan lokaci kallon su
yarima Marganu kawai yake da wani irin kallo wanda da ƙyar ya fahimci na mene.
"Kuyi min bayanin kanku kafun na fille kawunanku!!!" Inji sarki Kuffuru cikin wata
kakkausar murya mai kama da ana goga ƙaton ƙarfe a maƙera. Tuni cikin yarima
Marganu da na aljani Gulzab ya ɗuri ruwa, saboda tsananin kwarjinin sarki Kuffuru.
Muryar yarima Marganu na rawa ya ce, "Sunana Marganu ɗan Ratanam, nazo gareka da
wata muhimmiyar buƙata. Wannan kuma shi ne aljani Gulzab abokin tafiyata ne."
Murmushin mugunta Kuffuru yayi ya ce, "Marganu? Haka ka girma?" Yarima Marganu ya
samu nutsuwa a ransa yana ganin kamar sarkin ya amince dasu. "Faɗa min buƙatar
taka na gani komai yiwuwa ce." Inji sarki Kuffuru har yanzu yana tsaya ƙyam a cikin iska
kamar wanda ke tsaye a ɗakin matarsa. Marganu ya yi murmushi ya ce, "Ya shugabana.
Ina ganin muje fadarka idan muka sami nutsuwa sai nayi maka bayani dalla-dalla."
Fuskar sarki Kuffuru ya gani ta fara sauwaya daga fari izuwa baƙi tamkar wanda baƙin
cikin shekara da shekaru ya addaba. Ya daka masa tsawa ya ce, "Kai ba shawara nake
ba ka ba, umarni nake ba ka. Faɗa min kafun wannan takobi nawa tasha jininku!" A
firgice aljani Gulzab ya dubi yarima Marganu ya ce, "Ba ka san a gaban wa kake tsaye
bane? Yi maza ka faɗa masa buƙatar ka."
Yarima Marganu ya ce, "Buƙatata a gareka ya kai wannan sarki, ita ce ina son kayi min
izini naje gidan kurkukunku na ɗauko fursunar nan ƴar ƙabilar banu Kuyuru domin na
kuɓutar da rayuwar masoyiyata gimbiya Jaanu, ƴa a gurin sarki Ayubul Zairiy. A yanzu
haka wannan ƴa tasa tana hannun sarkin barayin duniya, da ba'a san ko shi waye ba.
Indai kayi min wannan izini ya shugabana ko meye kake so a gareni zanyi maka." Tun da
Marganu ya fara magana sai sarki Kuffuru ya bishi da kallo kawai, zuciyarsa tana
tafarfasa. "Ban amince da wannan buƙata taka ba." Inji sarki Kuffuru. Ya ƙara da cewa,
"Babu abinda ke tsakanina da jinin Samudul Ansari in banda kisa, akan rayuwar wata ƴar
ƙaramar yarinƴa bazan bari jinin Samudul Ansari ya kubce min, na aikata babban zunubi.
Kaje ka cewa mahaifinka da sarki Ayubul Zairiy ban amince ba, kuma sai na hukunta
sarki Ayubul Zairiy saboda umarnin fille kan wannan fursuna nace yayi, ba wai ya kaita
gidan kurkuku ba." Ya ƙare maganarsa yana kallon su Marganu yana jira su juya su tafi.
Yarima Marganu ya sake matsowa kusa har kan wuyan aljani Gulzab ya ce, "Ya
shugabana, kafin mu tafi ina da magana. Shin ka san waye ne Aymanul Faris Kuyuru da
jaruma Riya?" Sarki Kuffuru ya murtuƙe fuska ya ce, "Aymanul Faris kuma....waye shi?
Jaruma Riya? Su waye waɗannan? A sanina dai umarnin da na baiwa sarki Ayubul Zairiy
na kashe duk ɗan ƙabilar banu Kuyuru ya kammala kuma naga sa'adda duk ya karkashe
su. Saboda haka bansan su waye waɗannan ba." Hankalin yarima Marganu ya sake
ɗugunzuma ya ce, "Anƴa ka kalli ƙarshen wannan yaƙi kuwa? Ni dai a sanina akwai
aljanun da suka zo suka ceci rayuwar Aymanul Faris da sauran ƴan ƙabilar su." Sarkin
yayi shuru tsahon ɗan lokaci sannan ya ce, "Wai shin ina ka dosa ne? Mece ce buƙatarka
a gareni? Idan ka tsaya min kame-kame wannan karon zan sare kanka." Kai tsaye
yarima Marganu ya ce, "Abinda nake buƙata shi ne ka bani wannan mata domin nayi
amfani da ita wajen kamosu Aymanul Faris na kawo maka su, ka kashe su."
Sarki Kuffuru ya ce, "Zan ɗauke ku na kaiku izuwa fadata, da safe zanyi bincike domin
gano gaskiyar al'amari." Yana gama faɗin haka ya yiwa su yarima Marganu jagora suka
nufi fadarsa, har yanzu dai Kuffuru akan iska yake tafiya tamkar mai taka turba.
Suna isa fadar aka baiwa yarima Marganu masauƙi mai kyau, aka kawo masa abinci ya
ci ya ƙoshi. Ya shiga bayi yayi wanka, sannan ya fito ya kwanta bisa wani ƙaton gado
mai laushin gaske. Yana lumshe idanunsa yaji an taɓa kirjinsa, cikin tsananin
ɗimaucewa ya miƙe zaune.
Koda yayi arba da wanda ta taɓa kirjin nasa sai ya ƙame ƙyam kamar gunki. Wata
zabgegiyar budurwa ce mai tsananin kyawu. Sanƴe take cikin fararen kaya shara-shara
masu bayyana tsiraici. Marganu ya tuna cewa ƙofar wannan ɗaki a kulle take, hatta
tagogi ma duk a kulle suke. Tayaya wannar tsaleliyar budurwa haka zata shigo min
ɗaki? Ya ƙare mata kallo yaga ai dole ma ta girme shi domin aƙalla zata kai shekaru
ashirin.
"Wace ce ke?"
*****Ruhin Jarumtaka!!!
*
Babi na 7: *Kurkukun Mutuwa*
*
*
✍️✍️ Umar Sangaru ✍️✍️
Ɓangaren gimbiya Jaanu da jaruma Riya kuwa tuni sun zama manƴan ƙawaye, tun sa'adda Aymanul Faris ya fice daga cikin ɗakin wasanni kawai suke kala dabam-dabam. A karon farko a rayuwarta gimbiya Jaanu ta tsinci kanta a cikin farin cikin wasa da sa'anninta domin a can gidan sarautar sarki Ayubul Zairiy kullum a tsare take, a cikin gida daga ita sai kuyanginta. Nan take gimbiya Jaanu ta ayyana aranta ina ma ace zata kasance a wannan wuri har izuwa tsahon ƙarshen rayuwarta, saboda wurin ya burgeta matuƙa. Bugu da ƙari ga Aymanul Faris wanda kallonsa kaɗai ke ɗebe mata duk wani baƙin ciki na rayuwarta.
Suna cikin wasanninsu sai Aymanul Faris ya dawo cikin ɗakin, ya kira jaruma Riya gefe guda yana sanar da ita yadda suka yi da sarkin ɓarayi Barban. Gimbiya Jaanu ta ƙurawa Aymanul Faris idanu ko kiftawa bata yi, murmushi kawai tayi saboda tsananin kyawun Aymanul Faris. Gashin kansa baƙi na nan kwance, dara-daran idanunsa na bayar da haske da tsantsar kyawu. Fuskarsa ma'abociyar murmushi sai bakinsa dake ta faman magana wanda bata ji. Ɗago kai kawai yayi suna haɗa idanu, ya fashe da murmushi sannan ya fice daga ɗakin. Jaruma Riya ta bi bayansa, a guje itama gimbiya Jaanu ta biyo bayansu inda ta iske Aymanul Faris ya ƙwabe riga a cikin wani ƙaton fili wanda aka tanada musamman domin horon yaƙi.
Wata zabgegiyar takobi wadda aƙalla sai ƙarti arba'in sun taru zasu iya rabata da ƙasa, taga Aymanul Faris yana ƙoƙarin ɗagawa. Nan fa ƙwanjin maza suka tashi, jijiyoyin nan suka kukkumbura suka yi burdin-burdin. Sai ya sami nasarar raba takobin da ƙasa amma sai nauyinta ya rinjaye shi ta sake suɓucewa. "Tun safe yake ta ƙoƙarin ɗaga wannan takobi amma ya kasa." Inji jaruma Riya tana dariyar Aymanul Faris ɗago kai yayi ya dubeta, ya ce, "Ke ai ko yunƙurin ɗaga wannan takobi ba zaki yi ba saboda ba za ki iya ba, amma ni kuma a juri zuwa rafi. Tabbas na san wataran sai na ɗagata." Ita dai gimbiya Jaanu faffaɗan kirjin Aymanul Faris ta ƙurawa idanu tana mamakin yadda jikinsa ya ginu ainun, tun kafin ma ya girma. "Kowanne irin sadauki za'ayi idan wannan saurayin ya girma?" Ta tambayi kanta a cikin zuciyarta.
A daidai wannan lokaci ne mai gida Barban ya fito daga cikin ɗakin da yake, yaga Aymanul Faris na ta fama da wannan zabgegiyar takobi. Sai yayi murmushi sannan ya kira Aymanul Faris cikin wannan ɗaki. Ya ce, "Ya kai sadauki ɗan sadaukai, je kayi sallama da su gimbiya yanzun nan zamuje birnin Darul Barban domin kaga mutanenka." Aymanul Faris ya ce, "Hakan yana da kyau." Sannan ya fice. Yana fita mai gida Barban ya fiddo wani abu mai kama da madubin tsafi, sai ga jerin fuskokin mutane barkatai akan wannan abu. Take ya zaɓi fuskar wani mutumi mai gemu da saje, take fuskarsa ta rikiɗe ta koma irinta wannan mutumin. Aymanul Faris na dawowa cikin ɗakin yayi arba da wannan fuska sai yayi murmushi saboda yasan ikon mi gida Barban ne.
Take Barban ya shafi kambun dake ɗaure a damtsen hannunsa, waɗannan aljanu guda uku suka bayyana suna risinawa a gabansa. Ya dube su ya ce, "Ku ɗauke mu ku kaimu birnin Darul Barban." Kafun ya rufe bakinsa aljanun nan sun ɓace dasu.
Aymanul Faris ya tsinci kansa a tsakiyar gajimare, idan ya leƙo ƙasa sai ya ɗinga arba da shuɗin ruwan teku da manya-manyan duwatsu. Nan take ya tsinci kansa a cikin tsananin farin ciki, yana cikin wannan hali ne yaji muryar Barban a kunnensa, "Shin kuwa Ayman," inji Barban. "kasan wane ne sarki Samudul Ansari?" Aymanul Faris ya yi saurin bayar da amsa. "Ban ma taɓa jin mai wannan sunan ba." Mai gida Barban yayi murmushi ya ce, "Asalin sunansa *Kuyurul Samudu* shine mutumin da ya fara kafa ƙabilar banu Kuyuru a wani ƙaramin ƙauye da ake kira Salwaza. Samudul Ansari mutum ne sadauki tun daga tasowarsa, yadda ƴan ƙabilar banu Kuyuru haka shima yake. Ance a zamaninsa sai da ya yaƙi sarakunan dake nahiyar nan kaf, ya cisu da yaƙi. Lokacin da ya fara tsufa ne hankalinsa yayi mugun tashi saboda ya tabbatar da cewa indai ya mutu sai sarautarsa ta bar hannun ƙabilarsa ta koma wata ƙabilar saboda haka yaje yayi wani sihirin tsafi ya kashe kansa, ko ince ya ɓatar da kansa aka neme shi aka rasa. Tarihin wannan mutumi bai inganta ba shiyasa babu cikakken tarihin sai ɗan guntu wanda na baka a yanzu. Amma ance tun da ake a wannan nahiya ba'a taɓa yin gwarzon mayaƙi kuma sadaukin sadaukai kamar Samudul Ansari ba. Mutum ɗaya ne ake kyautata zaton yana da gaskiyar tarihin, ba wani bane face tsoho Samazan dake cikin kogon dutsen birnin Hindu. Idan muka sami nutsuwa zamu kaiwa wannan mutumi ziyara domin muji gaskiyar al'amari saboda Samudul Ansari yana da nasaba da ƴan ƙabilarmu shiyasa sarki Kuffuru yake kashe duk wani jinin Samudul Ansari." A daidai wannan lokaci ne suka fara hango birnin Darul Barban daga nesa.
Birni ne ƙarami wanda aka gina shi gaba ɗaya a saman wani ƙaton tsibiri da yake da nisan zango da sauran garuruwan mutane, saboda yawan ruwan tekun da ya zagaye wannan birni ya saka ba'a san dashi sosai ba a duniya. Kome mutanen wannan birni suke buƙata akwai hadiman aljanu dake zuwa manƴan birnanen duniya suna kawo musu, wannan birni har kirari ake masa da birnin aminci. Babu ɓarawo ba kwarto a garin, ba'a ta'addanci balle a zubar da jini. Mafi yawa daga cikin mutanen birnin marayu ne waɗanda suke rasa iyayensu a yayin yaƙe-yaƙe.
Wannan fuska da mai gida Barban ya saka ita ce fuskar mutumin dake ceto waɗannan marayu, tun suna ƙananun yara ya kawo su wannan birni sannan ya ɗauki dukkanin ɗawainiyarsu. A duniya babu abinda mutanen birnin Darul Barban ke ƙauna kamar wannan mutumi saboda ya kawosu wurin da ya fi ko'ina ni'ima a duniya.
Wata unguwa suka nufa da ake kira BARBANUL KUYUR, duk inda suka wuce ta sama bisa aljanun nan sai kaga jama'a nata ɗaga hannu suna ta yiwa Barban kirari, suna nuna tsantsar kaunarsu a gare shi. Nan take Aymanul Faris ya cika da tsananin mamakin wannan abu, ya ce a ransa, "Tabbas wannan ɓarawo ya cika abin tsoro. Yaushe ya gina kyakkyawan birni irin wannan har ya tara al'umma masu yawa haka a cikinsa?" Aymanul Faris ya sake lura sai yaga ai duk cikin wannan birni babu inda ya kai wannan unguwa ta Barbanul Kuyur ƙawatuwa, nan take ya sake cika da tsananin mamaki yana cewa a ranshi, "Yanzu duk girman birnin nan a ce mutum ɗaya ne ya gina shi? Wacce irin dukiya ya ɓarnatar a nan?" Haka dai Aymanul Faris ya ci gaba da yiwa kansa tambayoyi, ba tare da ya sami amsoshinsu ba. Har waɗannan aljanu suka dire bisa turba, sannan suka ɓace ɓat. Waɗansu zaratan dakaru ne guda goma suka rugo suka kewaye mai gida Barban, suka saka shi a tsakiya tare da Aymanul Faris a lokacin da suka shiga cikin wannan unguwa.
A wannan rana Aymanul Faris kuka yi ɗinga yi saboda yadda ya ɗinga arba da abokansa waɗanda basu mutu ba, da kuma ƴan uwansa. Da zarar sun yi arba da juna sai su cika da tsananin farin ciki, a wannan rana ne hankalin mutanen ƙabilar Banu Kuyuru ya sake kwanciya da wannnan birni saboda bayyanar shugabansu Aymanul Faris kuma ya shaida musu babu matsalar komai.
******
Koda jin wannan tambaya sai wannan budurwa ta kamo hannun yarima Marganu, a lokacin da yaji wani irin abu ya shige shi ta ce, "Ni ce gimbiya Firziyya ƴa a gurin sarki Kuffuru. Na jima ina sauraron zuwan wannan rana da zaka zo har birninmu domin ka biya min buƙata ta......" Yarima Marganu ya yi saurin janƴen hannunsa daga cikin nata ya ce, "Wacce buƙata kenan?" Gimbiya Firziyya ta ce, "Ka gane mana, ina nufin jin dadi tsakanin namiji da mace!" Marganu ya harareta ya ce, "Wannan ba zai taɓa yiwuwa ba, ina jin kunƴar baba Kuffuru ba zan iya cin amanarsa ba. Kiyi haƙuri yake Firziyya, mace ɗaya ce zata mallakeni a duniya kuma ita kaɗai nake so na sani ƴa mace." Koda gimbiya Firziyya taji wannan batu na yarima Marganu sai ta cika da tsananin mamaki domin shi ne namiji na farko, da ya taɓa yin arba da kyakkyawar surar jikinta. Ga shi ta neme shi da kanta amma yana ƙoƙarin watsa masa ƙasa a ido. "Ba zai yiwu ba, dole ne kayi abinda nake so. Idan ba haka ba kuwa zan yi maka sharri a wajen abbana gobe yasa hauni ya sareka." Bisa mamaki sai taji yarima Marganu ya ƙyalƙyale da dariya ya ce, "Mutuwata ta fiye min alheri akan na sadu da wata, wacce bata kasance gimbiya Jaanu ba. Kiyi haƙuri ki tafi, ko kuma na fitar dake ta ƙarfi." Koda gimbiya Firziyya taji wannan batu na yarima Marganu sai tayi murmushi ta ce, "Tabbas baka da rabo, yanzu kana ganin wannan kyakkyawan jiki zai wuce ka a banza?" Marganu ya ce, "Ke kike ganin kyawunsa amma nikam wanda yafi kowanne kyawu a wannan duniya." Yana gama faɗin haka ya rintse idanunsa, take barci yayi awon gaba da shi. Gimbiya Firziyya tana ganin yayi barci ta fice daga ɗakin, ta cikin wata ɓarauniyar hanƴa ta ƙarƙashin ƙasa.
Kashe gari tun da sassafe yarima Marganu ya farka daga wannan barci, yana buɗe idanunsa yayi arba da abincin kalaci bisa teburi. Wata kuyanga ya gani tsaye, a gefen gadon tana ganin ya buɗe idanunsa ta ce, muje ciki ayi ma wanka ko! Yarima Marganu ya sauko sannan ya shige cikin wani ƙasaitaccen ban ɗaki, kuyangi suka yi masa wanka aka kawo masa kayan yakinsa ya sanya. Ya zauna akan wata kujera ya ci abincin kalacin nan, sannan wani hadimi yazo yayi masa jagora suka nufi fadar sarki Kuffuru. A iya rayuwar yarima Marganu bai taɓa ganin ƙawataccen gidan sarauta kamar na sarki Kuffuru ba, take ya ji inama ace a wannan wuri zai ɗebe kewar amarcinsa da gimbiya Jaanu. Wata zuciyar ta daka masa tsawa ta ce, "Baka da hankali ne, ka fara mallakar gimbiyar tukunna." Yana cikin wannan sake-sake a ransa suka iso tsakiyar fadar.
Gaba ɗaya ginin fadar da farin zinari aka yi shi, irin zinarin da ake haƙowa a tsibirin Gazwar. Fadar bata da wani girma sosai amma sai dai ta ƙawatu sosai, a har kullum babu jama'a sosai a cikin fadar. Daga sarki Kuffuru sai ƴarsa gimbiya Firziyya da sauran fadawansa, indai kaga gama-garin mutane a cikin fadar to shari'a ake.
Sanye yake cikin baƙaƙen tufafi mara nauyi sosai, fuskarsa cike da murmushi amma na mugunta. Gimbiya Firziyya na zaune a gefensa cikin korayen tufafi da baƙaƙen takalma, kayan sun matseta ainun, lamarin da yasa kyawawan surorinta suka muraran a fili kenan. A wannan lokaci ne gimbiya Firziyya ta ƙarewa yarima Marganu kallo daga sama har ƙasa. Yarima Marganu zabgegen ƙato ne, yana da ƙira ta ƙarfi da murɗewa. Daga inda yake tsaye kana hango mariƙin takobin dake ɗaure a bayansa.
Bayan ya zube ya ƙwashi gaisuwa sai sarki Kuffuru ya yi murmushi ya ce, "Jiya nayi bincike akan waye Aymanul Faris da jaruma Riya kuma naga gaskiyar al'amari. Tabbas waɗannan yara suna da mugun haɗari a gareni, da ma gurin mahaifinka da sarki Ayubul Zairiy. Saboda haka dole na san matakin da zan ɗauka akansu. Ba zan manta da abinda kakanninsu suka yiwa zuri'ata ba. Ya kai wannan sadauki na yarda da abinda kake cewa, kuma na amince kaje gidan kurkukun nan ka ɗauki mahaifiyar Aymanul Faris amma bisa sharaɗi guda..." Sarki Kuffuru ya saisaita maƙwagoronsa, sannan ya ci gaba. "Dole ka kamo min Aymanul Faris da jaruma Riya a raye ko a mace. Ko kuma ka kamo min sarkin ɓarayin duniya a raye. Idan ka amince da wannan sharaɗi sai mu shiga daga ciki domin nayi maka ƙarin bayani akan dazuzzukan da za'a gifta kafin a isa dajin Marsas domin saduwa da sarkin ɓarayi na duniya."
Lokacin da yarima Marganu ya ji wannan batu na sarki Kuffuru sai yayi farat ya ce, "Na amince da wannan sharaɗi! Amma ina son nasan hukuncin da za'a min idan na gagara cika sharaɗin." Sarki Kuffuru ya yi murmushin mugunta ya ce, "Ba zan faɗa maka hukuncin ba a yanzu, sai ka gagara cika sharaɗin zaka gani. Ina mai sanar da kai cewa ka ci gaba da addu'ar kada ka gagara cika wannan sharaɗi domin mutumin da ke kabari sai yafi ka jin daɗi." Sarki Kuffuru na gama faɗin haka ya kama hannun gimbiya Firziyya suka nufi cikin ɗakin gani da aka gina a gefen fadar, sarkin yana mai yafito yarima Marganu.
Suna shiga ɗakin yarima Marganu ya tsinci kansa a cikin wani ƙawataccen wuri mai cike da kayan alatu da abubuwan more rayuwa. Waɗansu kujeru guda goma ya gani a jere a gaban wata ƙatuwar karaga, da alama dai akan waɗannan kujeru ƴan majalisar ƙasar ke zama a yayin gudanar da taro. Sarki Kuffuru ya zauna akan wannan karaga tare da ƴarsa, shi kuma yarima Marganu sai ya zauna akan ɗaya daga cikin kujerun nan.
Sarki Kuffuru ya yi ƙyaran murya sannan ya fara yiwa yarima Marganu jawabi kamar haka, "Asalin dajin Djinn mallakin babbar abokin gabata ce, sadauki Samudul Ansari. Ba don

Please Login or Register in order to submit comment