Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sarki Kuffuru da sadauki Zayyadu suka fara jiwo kururuwar dakaru daga can wajen wannan kurkuku gami da ƙarar karafkiyar ƙarafa, ga dukkan alamu dai yaƙi ake gwabzawa.
Sarki Kuffuru ya dubi sadauki Zayyadu cikin tsananin mamaki ya ce, "Me ke faruwa?" Sadauki Zayyadu ya ce, "Duk yadda akayi wani fursuna ake so a kuɓutar, ga dukkan alamu farmaki aka kawo amma bari naje na duba." Har Zayyadu ya juya zai tafi sai sarki Kuffuru ya kamo hannunsa ya ce, "Ban yarda da Marganu ba kuma ina kyautata zaton shi aka zo kuɓutarwa don haka ka ɗauke shi, ka kai shi wannan ɗaki na ƙarƙashin ƙasa wanda muka saba ɓoye gawurtattun masu laifi. Kafin kaje ka dubo bari na dubo abinda ke faruwa, idan farmaki aka kawo mana tabbas zan kama dukkan ƴan-tawayen."
Sadauki Zayyadu ya risina ya ce, "An gama mai duniya." Ya sunkuya ya saɓa Marganu bisa kafaɗarsa sannan ya falfala da azababben gudu ya nufi wani ɓangare na wannan kurkuku mai yawan dogayen itatuwa.
Sarki Kuffuru ya dubi gimbiya Firziyya ya ce, "Zo muje muga abinda ke faruwa." Yana gama faɗin haka ya falfala da gudu ya nufi inda yake jiwo wannan kururuwa ta mazaje, gimbiya Firziyya ta take masa, tana gudu tana waiwayowa tana kallon inda sadauki Zayyadu ya nufa ɗauke da Marganu.
***
A wajen wannan kurkuku kuma, wata baƙuwar runduna ce ta sadaukai ta bayyana sanƴe cikin baƙaƙen tufafi masu ratsin ja bisa waɗansu ingarmun dawakai suka afkawa dakarun dake tsaron kurkukun mutuwa da mugun yaƙi. Nan fa aka fara ɗauki ba daɗi, jini ya fara malala a ƙas... Ihu da kururuwar mazaje ta cika wannan daji gaba ɗayansa. Da yake a cikin sahara wannan daji yake, tuni gagarumar ƙura ta turnuƙe ko'ina ba'a ganin mutane sosai.
Waɗannan baƙin dakaru sun kasance masu tsananin naci, juriya da mugun iya yaƙi. Nan fa suka gallabi dakarun dake tsaron wannan kurkuku suka yi ta saransu da sukarsu kamar ba gobe, duk inda suka saka a gaba sai dai kawunan dakarun dake tsaron wannan kurkuku nata shawaƙi a sama, jini yana ta zuba. Amma saboda tsananin yawan dakarun dake tsaron wannan kurkuku sai kaga tamkar ƙarosu ake.
Ana cikin haka wata tsaleliyar budurwa ta bayyana sanƴe cikin sulke shuɗi, riƙe da zabga-zabgan takubba guda biyu. Nan fa wannan budurwa ta sauya salon wannan yaƙi gaba ɗaya, domin ta zamo tamkar shaiɗaniya a tsakiyar waɗannan dakaru. Duk inda ta sa gaba sai dai kaga mazaje nata zubewa ƙasa tamkar ana sassaɓe. Tana da tsananin zafin nama da iya yaƙi na gaban kwatance don yadda ka san walƙiya haka take ragargazar waɗannan dakaru suna ta zubewa, matattu.
Inda mutum zai sami dama kaɗan ya matsa kusa da wannan sarauniya ya ƙare mata kallo, zai fuskanci ba wata bace illa sarauniya Rauziyya mai mulkin tsaunin Barzasa.
Tabbas sarauniya Rauziyya da dakarunta sun kasance sadaukan gaske, don yadda suke ragargazar waɗannan dakaru kamar ba gobe. Kai kace ƴan aiken mutuwa ne.
Koda aka shafe sa'a biyu ana wannan gumurzu sai sarauniya Rauziyya da dakarunta suka yi fata-fata da waɗannan dakaru dake tsaron wannan kurkuku gaba ɗayansu, suka kashe na kashewa masu guduwa kuma suka gudu. Wani abin mamaki shi ne bai wuce mutum dubu kacal, sarauniya Rauziyya ta rasa daga cikin dakarunta ba. Lallai waɗannan dakaru sun cika MAYAƘAN ASALI, mazan ƙwarai.
Ai kuwa waɗannan dakaru na gama ƙarewa ƙofar kurkukun mutuwa ta fara buɗewa da kanta. Sarauniya Rauziyya da dakarunta suka jeru a layi guda suka riƙe makaman yaƙinsu da kyau, suna jiran wannan ƙofa ta gama buɗewa.
Ƙofar na gama buɗewa dakaru guda arba'in da huɗu suka bayyana, tsaitsaye bisa dawakai cikin mahaukacin shiga ta yaƙi. Akwai waɗansu mutum biyu na tsaye a gabansu, ba tare da sun hau dawakai ba. Waɗannan mutum guda biyu sun kasance mace da namiji wato sarki Kuffuru da ƴarsa Firziyya.
Nan fa aka fara tsakanin sarki Kuffuru da sarauniya Rauziyya, da kuma dakarunsu. Cikin kwanciyar hankali sarki Kuffuru ya tako yazo har gaban su sarauniya Rauziyya ya dubeta cikin nutsuwa ya ce, "Da gani ke sarauniya ce. Meye haɗinki da wannan kurkuku har da za ki kawo mana farmaki?"
Sarauniya Rauziyya ta murtuƙe fuska ta ce, "Ya kai wannan sarki. Kayi sani cewa tsinanne Marganu muke nema kuma tabbas yana cikin wannan kurkuku don haka ku bamu shi, sai mu ƙyale ku ku rayu sannan muyi tafiyar mu. Idan kuma kun ƙi...." Tana cikin taji an daka mata tsawa. "Ke! Dakata!" Inji sarki Kuffuru. Ya nuna ta da ɗan yatsa guda ya ce, "Kinsan a gaban waye kike kuwa? Ki shiga taitayinki ko kuma na kamaki na tsare a cikin wannan kurkuku. Kamar yadda na tsare Marganu." Sarauniya Rauziyya ta bushe da dariya ta juya ta dubi dakarunta ta ce, "Wai ni za'a kama a tsare a kurkuku?!" Dakarun nata ma sai suka fara dariyar sarki Kuffuru. Al'amarin da ya baƙantawa sarki Kuffuru rai kenan, ya dubeta ya ce.
"Ke yarinƴa me kike ɗaukar kanki? Ga dukkan alamu ke baƙuwa ce a wannan nahiya tamu amma kamata yayi kije kiyi bincike akan waye ne sarki Kuffuru? Da ina da niyyar ba ki Marganu amma tun da naga harma dariya kuke min to ku ƙwata da ƙarfi. Tabbas yau ɗinnan ni kaɗai sai na tarwatsa wannan shashashun runduna taki, sannan na kama ki na tsareki a cikin wannan kurkuku tawa."
Sarki Kuffuru na gama faɗin haka ya kwaɓe alkyabbar dake jikinsa, ya bayyana a cikin waɗansu kayan yaƙi jajaye. Wata zabgegiyar takobi ya zaro daga gadon bayansa, yai kururuwa ya ruga da guda kan su sarauniya Rauziyya.
Maimakon waɗannan dakaru su afko masa, kawai sai aka ga sarauniya Rauziyya ita kaɗai ta ruga da gudu ta tunkari sarki Kuffuru tana ɗaga takubbanta guda biyu sama, gami da kwarara uban ihu.
Kai da ka san cewa tabbas haɗuwar waɗannan sadaukai guda biyu za'a gwabza mummunan yaƙi, amma a ganin ido kam, sarki Kuffuru yafi sarauniya Rauziyya sura ta ƙarfi da sadaukantaka.
****RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 21: *Kuffuru vs Rauziyya*
*
*
✍️✍️✍️ Umar Sangaru ✍️✍️✍️
*
Lokacin da sarki Kuffuru da sarauniya Rauziyya suka haɗu sai suka ruguntsume da azababben yaƙi mai tsananin firgitarwa, suka wanzu suna masu kaiwa junansu sara da suka cikin baƙin zafin nama, juriya da bajinta. Nan fa faɗan nasu ya fara daɗin kallo saboda tsantsar iya yaƙi ne ta haɗu da zallar sadaukantaka.
A duk sa'adda sarki Kuffuru ya kawowa sarauniya Rauziyya sara da takobinsa sai kaga ta sa takobinta ta tare amma saboda ƙarfin saran takobin sarki Kuffuru sai ta durƙushe bisa gwiwanta guda, sannan ta maida masa martani cikin baƙin zafin nama shima yayi amfani da takobinsa ya kare saran. Nan fa suka wanzu suna kaiwa junansu mugayen hare-hare masu matuƙar hatsari, amma ko sau ɗaya basu sami damar yanka ɗaya daga cikinsu ba. Al'amarin da yayi matuƙar ɓatawa sarki Kuffuru rai kenan domin sarauniya Rauziyya ita ce bil'adama ta farko da ya gagara hallakawa a cikin rabin sa'a kacal, saboda tsananin iya yaƙinta da yadda ta iya sarrafa waɗannan takubba guda biyu nata.
Tun da sarki Kuffuru yake gumurzu da mazaje bai taɓa yin arba da wanda ya iya yaƙi kamar sarauniya Rauziyya ba, duk salon da ya ɓullo mata da shi sai yaga ta ƙware sosai akansa, al'amarin da yayi matuƙar bashi mamaki kenan kuma ya fusata shi. Ya ci gaba da kaiwa sarauniya Rauziyya sara da suka ba ƙaƙƙautawa, ita kuma ta wanzu tana mai kare sara da sukan nasa cikin kwanciyar hankali tamkar ta san ta inda zai kawo kata hare-haren.
Har tsahon sa'a ɗaya da rabi dai, ana abu ɗaya. Tsakanin sarki Kuffuru da sarauniya Rauziyya babu wanda ya sami nasarar koda lakutar jikin ɗan uwansa. Cikin tsananin mamaki sarki Kuffuru ya daka tsalle baya, ya tsaya ƙyam yana ta nazarin sarauniya Rauziyya. Ai kuwa ita ma sai ta tsaya ta ƙura masa idanu suka fara nazarin salon faɗan da zasu yi dashi wajen samun nasara. Kamar haɗin baki sai suka rugo da gudu suka nufo kan juna, sarki Kuffuru na ɗaga zabgegiyar takobinsa ita kuma sarauniya Rauziyya na ɗaga takubbanta guda biyu sama, dukkaninsu suna kwarara uban ihu.
Koda ya rage saura taku huɗu, dukkansu suka daka tsalle sama suka kaiwa junansu munanan hari. Sarki Kuffuru ya kaiwa sarauniya Rauziyya sara a wuya da nufin ya tsinke mata kai, ita kuma sarauniya Rauziyya ƙirjin sarki Kuffuru ta kaiwa sara domin ta farke shi. Saura ƙiris takobin sarki Kuffuru ta fillewa sarauniya Rauziyya wuya ta sunkuya, takobin ta yanki wani ɓangare daga gashin kanta ya zubo ƙasa. Sarki Kuffuru ya ja da baya a hankali takobin sarauniya Rauziyya ta sari iska amma kafun ya sake wani motsi, tuni ta dankara masa sara akan kafaɗarsa ta hagu. Take wannan wuri da ta sara ya tsage jini yayi feshi, sarki Kuffuru ya kwarara uban ihu ya faɗo kasa yana mai dafe hannunsa guda na hagun.
Sarauniya Rauziyya ta dira a bayansa tana murmushin mugunta. Kuffuru yaga yadda jini keta malala daga cikin wannan rauni, sai ransa yayi mummunan ɓaci yasa hannu ya yage rigar jikinsa ya ɗaure wannan rauni dake kan damtsensa na hagu, ya juyo ya dubi sarauniya Rauziyya cikin tsananin fusata tamkar wanda baƙin cikin shekara da shekaru ya tasowa a lokaci guda. Ya taƙarƙare ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa ya ce, "Kin karya min alkadarina, na fita yaƙoƙi aƙalla tamanin da bakwai amma ko taɓa rigata abokin gaba bai taɓa yi ba. Tun da nake rayuwa a duniya, jinina bai taɓa zuba a filin daga ba, amma yau kin karya wannan alkadari. Tabbas sai na kamaki da ƙarfin tsiya nasa anyi miki fyaɗe sannan na gana miki azabobi kala ɗari kafin na fille kanki. Yau za ki ga fushin namijin duniya." Sarki Kuffuru na zuwa nan a zancensa ya ɗaga hannayensa biyu ya nuna sararin samaniya, yana karanto waɗansu baƙaƙen ɗalasimai daga bakinsa. Nan take waɗansu irin manƴa-manƴan tsaunika guda biyu suka bayyana acan ƙololuwar sama suka fara sauƙowa a hankali, suna ƙara yiwo ƙasa suna ƙara girma.
Koda sarauniya Rauziyya taga haka sai ta ƙyalƙyale da dariya ta ware hannayenta kuma ta rufe idanunta, ta fara motsa bakinta a hankali. Ai kuwa take waɗansu manƴa-manƴan takubba guda biyu suka bayyana a can ƙololuwar sama suka tunkaro ƙasa cikin masifaffen gudu. Sarauniya Rauziyya ta buɗe idanunta ta kaɗa ɗan yatsanta guda, take wata guguwa mai ƙarfi ta bayyana kuma ta kewayeta, idan ka hangeta daga waje zaka yi tsammanin guguwar ɗaukarta tayi amma idan ka ganta ta ciki zaka ganta cikin ƙoshin lafiya.
Tsaunikan sarki Kuffuru na dira dajin gaba ɗaya yayi girgiza tamkar ƙasa zata tsatstsage komai ya rufta cikinta, a daidai lokacin ne kuma manƴa-manƴan takubban sarauniya Rauziyya suka bayyana a gabanta. Ba tare da jira komai ba ta nuna waɗannan manƴa-manƴan tsaunika guda biyu da tafukan hannayenta biyu, lamarin da yasa takubban suka tafi cikin iska da gudu kenan suka tunkari waɗannan tsaunika. Sarki Kuffuru ma ya nuna sarauniya Rauziyya da hannayensa biyu, manƴa-manƴan tsaunikan suka tunkareta da gudu zasu matse ta.
A tsakiya manƴa-manƴan takubban sarauniya Rauziyya da manƴa-manƴan tsaunikan sarki Kuffuru suka haɗu, wata ƙara mai kama da sauƙar aradu ta cika dajin gaba ɗaya. Tsaunikan sarki Kuffuru suka yi bindiga suka tarwatse, wata iriyar jar wuta tayi feshi cikin dajin. Nan fa gobara ta kama ta ko'ina. Takubban sarauniya Rauziyya kuma suka kumbura suka fashe wata azababbiyar dalma tayi feshi.
Sarki Kuffuru ya murtuƙe fuska, ya haɗe hannayensa a guri guda ya fara kiran sabbin ɗalasimai. Nan take waɗansu manƴa-manƴan tsaunika guda bakwai suka sake bayyana acan sararin samaniya suka tunkaro ƙasa, saboda girman tsaunikan sun yiwa komai dake cikin dajin rumfa. Sarauniya Rauziyya na ganin haka ta haɗe tafin hannayenta a waje guda, ta durƙusa bisa gwaiwarta guda ta fara karanto ɗalasimai a sirrance. Nan take aka hango waɗansu manƴa-manƴan takubba guda bakwai sun bayyana a can ƙololuwar sama suna dannowa ƙasa da gudu fiye da na farko.
Koda sauran dakarun sarauniya Rauziyya da dakarun-masifa suka ga abinda ke shirin faruwa sai duk suka ruga da gudu suka bar filin yaƙin gaba ɗaya don kada bala'in azababbiyar dalma da feshin jar wuta ya narkar dasu ko kuma ya ƙone su. Ai kuwa waɗannan takubba guda bakwai suna haɗuwa da manƴan tsaunika bakwai, abinda ya afku da farko ya sake afkuwa sai dai amma a wannan karon feshin wannan jar-wuta sai da ta ƙone filin yaƙin gaba ɗaya, nan fa ta kama gawarwakin dakarun dake kwakkwance a wurin ta fara ƙone. Wutar na cikin cinƴe su wannan dalma ta dira akansu duk ta narke su. Tabbas dakarun sarauniya Rauziyya da dakarun-masifa ba ƙaramar dabara suka yi da suka gudu, don inda ace suna tsaye a wannan da tuni tasu ta ƙare.
Sarki Kuffuru da sarauniya Rauziyya suka bayyana a sama cikin iska, a ƙasansu wannan jar-wuta ce keta ci ta ko'ina ganga-ganga. Sarki Kuffuru ya murtuƙe fuska don ga dukkan alamu ƙarfin sihirinsa da na sarauniya Rauziyya yazo ɗaya. Sarki Kuffuru ya nuna sarauniya Rauziyya da ɗan yatsa guda ya ce, "Ke! Ƙaryarki ta sha ƙarya tabbas ni zanyi nasara akanki. Tun da ƙarfin sihirin tsafinmu yazo ɗaya me zai hana mu jarraba ƙarfin damtsen da Allah ya bamu?" Sarauniya Rauziyya ta bushe da dariya ta ce, "Na amince! Mu jarraba ƙarfin damtsen, tabbas yau zan baka mamaki. Kuma tabbas sai kayi nadama da tun farko ka bani Marganu mun tafi." Tana gama faɗin haka ta falfalo da gudu akan iska shima sarki Kuffuru sai ya tunkareta.
Suna haɗuwa a tsakiya suka ruguntsume da azababben yaƙi suna kaiwa juna duka hannu da ƙafa, nan fa suka fara zille-zille da gocewa cikin zafin nama. A duk sa'adda sarki Kuffuru ya kawowa Rauziyya duka sai kaga ta goce cikin baƙin zafin nama da ƙwarewa, sannan ta mayar masa da martani. Nan take fa faɗan nasu yazo ragas, sarki Kuffuru yafi sarauniya Rauziyya ƙarfin damtse nesa ba kusa amma inda matsalar take ita kuma ta fishi zafin nama da iya zillewa. Al'amarin da yayi matuƙar ɓatawa sarki Kuffuru rai kenan. Ya sake ja da baya, ya ƙurawa sarauniya Rauziyya yana so ya tabbatar anƴa mutum ce?
Sarauniya Rauziyya ta dube shi ta bushe da dariya ta ce, "Ya kai wannan sarki, a karo na ƙarshe inaso ka ɗauko min Marganu domin na tafi." Kuffuru ya murtuƙe fuska ya ce, "Idan kika ga na baki Marganu ki tabbatar da cewa kanki ya bar wuyanki. Kai kefa dole ne ma yau ɗinnan na kashe ki, domin karya alkadarina da kika yi da kuma kawo farmaki kurkukuna." Yana gama faɗin haka ya falfalo da azababben gudu kan sarauniya Rauziyya yayi ta kawo mata duka hannu da ƙafa cikin baƙin zafin nama. Ai kuwa take ta tare shi suka ci gaba da kwabsawa.
Amma a wannan karon sarki Kuffuru a matuƙar fusace yake, don haka sai ya fara samun lagon sarauniya Rauziyya. Har yayi mata kyakkyawan naushi guda ɗaya a ciki, sarauniya Rauziyya ta durƙushe bisa gwiwowinta, tana aman jini. Sarki Kuffuru yasa hannunsa guda ya zabga mata mari wanda yayi cilli da ita ƙasa zata faɗo cikin wannan wuta, amma cikin hanzari ya kamota yayi ta gabza masa mata naushi har sai da ya tabbatar da cewa ta suma sannan ya nufo ƙasa bakin ƙofar, yana zuwa kai tsaye ya shige cikin kurkukun.
Dama abinda sarauniya Rauziyya take jira kenan, shiyasa ma tayi masa lamo kamar ta suma. Yana shigowa cikin wannan kurkuku ta kaikaici idonsa ta tattaro ƙarfinta gaba ɗaya waje ɗaya ta gabza masa wani wawan naushi a baki, saboda ƙarfin wannan naushi sai da haƙoran sarki Kuffuru guda biyu na ƙasa sukayi fitar burtu, jini ya zubo daga bakinsa. Baisan lokacin da ya saki sarauniya Rauziyya ba ta faɗi kasa, ya durƙushe bisa gwiwowinsa yana mai dafe bakinsa.
Tabbas sarauniya Rauziyya ta kasance BASADAUKIYA, MACE MAI KAMAR MAZA. Domin a tarihin sarki Kuffuru ita ce mutum ta farko da ta taɓa samun nasarar fitar masa da jini, ga shi har cire masa haƙora guda biyu.
A fusace sarki Kuffuru ya miƙe tsaye ya yayyage dukkan suturar dake jikinsa ya rage daga shi, sai wani farin bante wanda bai kai ko gwiwa ba. Ya ɗaga kansa sama ya kwarara wani uban ihu wanda ya cika wannan daji gaba ɗaya da amsa kuwwa. A daidai lokacin ne gimbiya Firziyya ta fito daga cikin wani loko na cikin wannan gidan sarauta koda taga yadda sarki Kuffuru yake, sai ta fusata ta zare takobinta zata afkawa sarauniya Rauziyya amma sai sarki Kuffuru ya daka mata tsawa ya ce ta koma da baya. Cikin kallon fushi da harara Firziyya ta ja baya tana hararar Rauziyya.
Sarki Kuffuru ya dako wani wawan tsalle ya dira a gaban sarauniya Rauziyya, kai idan kaga wannan tsalle da yayi sai ka cika da tsananin mamaki saboda akwai tazara mai yawan gaske tsakaninsa da ita. Sarki Kuffuru na dira ya shaƙo wuyan sarauniya Rauziyya da hannayensa biyu ya ɗagata sama, a lokacin da idanunsa suka kaɗa suka yi jawur. Nan fa sawayen sarauniya Rauziyya suka fara wutsil-wutsil a sama, idanuwanta suka yi ɓulu-ɓulu suka yi jawur. Numfashinta ya fara sarƙewa. Kuffuru ya riƙe da ƙarfi iyakar iyawarsa, ga dukkan alamu ba shi da burin sakinta sai ya tabbatar da cewa ta mutu dukda ba hakan yaso ba.
Koda sarauniya Rauziyya ta fuskanci cewa indai aka ƙara ƴan daƙiƙu a haka tabbas mutuwa zatayi, sai ta tattaro ƙarfinta gaba ɗaya ta sa ƙafarta guda ta doki ƴaƴan marainan sarki Kuffuru. Take wani irin zogi ya shige shi ta ƙasa, bai san sa'adda ya jefar da ita ba. Ya durƙushe bisa gwiwowinsa, yana ɗora hannayensa a ƙasansa. Ita kuma sarauniya Rauziyya sai ta fara shafa wuyanta a hankali tana ƙoƙarin daidaita numfashinta.
Gimbiya Firziyya na ganin haka ta falfalo da gudu tazo kan sarauniya Rauziyya ta ɗaga takobinta sama zata tsire cikin Rauziyya, saura ƙiris wannan takobi ta caki cikin sarauniya Rauziyya kawai sai ta mirgina cikin baƙin zafin nama. Takobin gimbiya Firziyya ta nutse a cikin ƙasa, kafun ta zaro tuni sarauniya Rauziyya ta miƙe zaune ta sa hannu guda ta nausheta a ƙirji, Firziyya ta faɗi da baya a wurin da ƙarfin, bayanta ya doki ƙasa da ƙarfi. Rauziyya ta zaro wannan takobi ta Firziyya ta kawo mata mummunan sara a gefen ƙirjinta. Firziyya ta kauce da sauri amma dukda sai da takobin ta tsarge rigarta, ta bayyana babu riga mamanta a waje. Lamarin da yasa ɗan kunƴa ya rufeta kenan, sarauniya Rauziyya ta bushe da dariya ta daka tsalle ta dira a gaban Firziyya, ta shaƙota da hannu biyu kamar yadda sarki Kuffuru ya sheƙeta. Nan fa Firziyya ta fara wutsil-wutsil ranta na faman fita.
Kwatsam! Ba zato sarauniya Rauziyya taji an doki sawayenta biyu da ƙarfi saboda ƙarfin dukan sai da tayi sama ta faɗo kasa acan gefe guda. Sarki Kuffuru ta gani ya nuna gimbiya Firziyya da hannunsa guda take waɗansu korayen kaya suka bayyana a jikinta suka rufe tsiraicinta. Ya juyo ya dubi sarauniya Rauziyya wacce ke kwance ƙasa cikin galabaita ya ce, "Duk wanda ya kalli tsiraicin Gimbiya sakamakonsa mutuwa." Yana gama faɗin haka ya nuna sarauniya Rauziyya da hannunsa guda take wata jar-wuta ta yiwo kanta gaɗan-gaɗan zata ƙoneta. Sarauniya Rauziyya tayi murmushi ta tafa hannayenta biyu, wata ƙanƙara mai sanƴin bala'i ta kewayeta. Da zarar wannan jar-wuta ta sarki Kuffuru ta doki ƙanƙarar sai ginin wannan kurkuku gaba ɗaya yayi girgiza tamkar zai tarwatse. A haka dai har wannan jar-wuta ta gama ƙarewa.
Sarki Kuffuru ya zare ido cikin tsananin mamaki wannan jar-wuta ita ce ƙololuwar abin dogaronsa a ɓangaren tsafi, ba ma mutum ɗaya hatta birni guda sarki Kuffuru na iya ƙone shi da wannan jar-wuta. Don haka dole ne ya cika da tsananin mamaki idan wannan wuta ta gagara yiwa Rauziyya illar komai.
Sarauniya Rauziyya ta miƙe tsaye ta karkaɗe ƙurar jikinta, sannan tayi wani baƙin tsafi. Waɗansu kwallayen haske guda huɗu baƙaƙe suka faɗo cikin wannan kurkuku, lamarin da yasa kurkukun gaba ɗaya tayi girgiza tagogi da ƙofofi suka buɗe da ƙarfi, ƙura ta gauraye ko'ina. Waɗannan baƙaƙen kwallaye guda huɗu suka haɗe suka bayar da siffar gunki Barzasa a gaban sarauniya Rauziyya.
Nan take ta zube a gaban wannan gunki tayi sujjada ta tsahon daƙiƙa goma kacal sannan ta miƙe. Gunkin ya sake rikiɗewa ya koma waɗannan baƙaƙen kwallaye guda huɗu suka shige cikin jikin sarauniya Rauziyya. Nan take ta bayyana a cikin waɗansu irin baƙaƙen tufafi masu sheƙi da walwali. Gashin kanta ya ƙara tsaho da baƙi sosai, wata irin bezar gashi ta bayyana a idonta wanda ya ƙara mata kwarjini matuƙa. Sarauniya Rauziyya ta nuna sarki Kuffuru ɗan yatsa guda, nan take ginin kurkukun dake bayan sarki Kuffuru ya ruguje.
Koda ganin haka sai ta bushe da dariya ta ce, "Bani da niyyar amfani da ƙarfin jinin ƙabilata amma sai da ka kaini bango, don haka a sauƙa lafiya." Tana gama faɗin haka ta juya ɗan yatsanta, wata irin guguwa ta kanannaɗe sarki Kuffuru tayi jifa dashi can ƙololuwar sama har ya ƙule a cikin gajimare. Sarauniya Rauziyya ta bushe da dariyar mugunta ta nuna gimbiya Firziyya da hannu guda ta ce, "Koma gida!" Nan take wannan guguwa tayi jifa da ita, can birnin Kufa.
Sarauniya Rauziyya ta fara tafiya a hankali a cikin wannan kurkuku, duk takunta guda ɗaya yana haifar da girgiza ta ƙasa wadda take rusa ɗakunan kurkukun. Kafun a jima tuni ta gama rushe kurkukun mutuwa gaba ɗayanta. Gaba ɗaya wurin ya zama fili fetal, dukkanin dakarun dake tsaron wannan kurkuku durƙushewa suka yi a gaban sarauniya Rauziyya suna tuba, don tamkar abin bauta haka suke kallonta.
Babu irin neman da sarauniya Rauziyya bata yiwa Marganu ba amma bata ganshi ba, lamarin da ya fusata ta kenan ta dakawa dakarun dake tsaron kurkukun tsawa.
"Ina aka ɓoye yarima Marganu?!"
Sadauki Zayyadu ya risina ya ce, "Ya shugabata, a ƙarƙashin ƙasa aka ɓoye kuma sarki Kuffuru ne kaɗai yasan ɗalasimin da ake karantawa ƙofar gilashin ta buɗe." Sarauniya Rauziyya tayi murmushi ta nuna ƙasar kurkukun da hannunta a lokacin ƙasar ta daddare, yarima Marganu ya bayyana a cikin wani ƙato na gilashi wanda aka rufe da waɗansu ɗalasimai.
Sarauniya Rauziyya tayi-tayi wajen ganin ta fasa wannan ɗaki na gilashi domin ta fiddo Marganu amma abu ya faskara domin wannan ɗakin gilashi, tsafi baya tasiri akansa, kaifi ko tsini baya tasiri akansa. Rauziyya ta dafa ƙofar wannan gilashin da hannunta guda ta rintse idanunta tana karanto ɗalasimai a zuci, wani irin haske ya fara fita daga cikin hannunta yana narka ƙofar wannan gilashi.
Tsahon rabin sa'a ta ɗauka tana ƙoƙarin buɗe wannan ƙofa amma abu ya faskara. Ƙofar ta ƙi narkuwa. Marganu dai na cikin wannan ɗaki sai karkarwa yake, don ya tabbatar da cewa duk tsautsayin da

Please Login or Register in order to submit comment