Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi sai sarkin-yaƙinsa.
Koda sarki Ratanam ya fuskanci cewa idan yaci gaba da zuba idanu lallai dakarunsa gaba ɗaya ƙarewa zasuyi, sai ya zaro zabgegiyar takobinsa ya sauƙa daga dokinsa ya ruga tsakiyar waɗannan dakaru.
Nan take suka sake buɗe sabon gumurzun yaƙi wanda yafi na farko ɗaukar hankali, domin a wannan karon sarki Ratanam ya bayyana a tsakiyar waɗannan dakaru zuciyarsa a tafashe. Nan fa ya shiga gididdiba su yana raba su gida biyu, ko kuma kaga ya fille musu kai.
Wannan takobi dake hannun sarki Ratanam zamowa tayi tamkar fitilla saboda tsananin haskenta. Komai tazarar dake tsakaninsa da mutum indai ya kai masa sara da wannan takobi, to fa sai ya same shi. Kuma wannan takobi sara ɗaya kawai take yiwa mutum ya halaka.
A takaice dai, shigowar sarki Ratanam wannan yaƙi ya sauya akalar wannan yaƙi gaba ɗaya. A da in banda karkashe dakarunsa babu abinda ake, amma yanzu da ya shigo suka ga yadda yake hallaka abokan gaba sai su ma hankalinsu ya kwanta suka sami kwarin-gwiwa suka shiga kashe dakarun sarki Kuffuru.
Kafun a jima tuni wannan yaƙi ya sauya salo, sarki Ratanam da dakarunsa suka soma cin karensu babu babbaka. Nan take dakarun sarki Kuffuru suka soma zubewa ƙasa matattu, ba wai waɗannan dakaru ne ke hallaka su ba, a'a, wannan rantsatstsiyar takobi dake hannun sarki Ratanam ita ce ta gallabe su.
Idan muka yi duba izuwa ga hannun sarki Ratanam zamu iya cewa babu komai a hannunsa, face haske. Wannan takobi dake hannunsa ta haske ce, haske mai haskawa.
Dukda ya san cewa shi ne yake yin nasara a wannan lokaci, amma ko kaɗan hankalinsa bai kwanta ba. Ba don komai ba, sai domin ya gano cewa har yanzu shugaban waɗannan dakaru bai bayyana ba.
Koda fuskantar hakan sai sarki Ratanam ya kira babban ɗalasimin tsafinsa, nan take irin wannan takobi dake hannunsa kusan dubu arba'in suka bayyana a saman iska.
Dakarun sarki Kuffuru suka ɗaga kawunansu suna kallon waɗannan takkubba waɗanda ke tsaye a cikin iska kamar taurari. Kowa a cikin su ya fara wuridi a cikin ransa yana neman tsari. In dai kamar yadda suke ji a labari hakane, to, tabbas ƙarshensu na gab da zuwa.
Sarki Ratanam ya ciji babban dan yatsansa, jini ya fara zubowa. Yana ganin haka ya soma ɗiga wannan jini akan wannan takobi tasa ta haske.
Faruwar hakan keda wuya waɗannan takubba dake yawo a cikin iska, suka soma yiwo ƙasa cikin azababben gudu, kafun waɗannan dakaru na sarki Kuffuru su ankara tuni takubban sun fara tsire cikinsu.
Nan take suka soma kwarara uban ihu, jinin jikinsu ya fara yin feshi sama, kayan cikinsu suka fara zubowa ƙasa.
Kafun cikar rabin sa'a tuni waɗannan takubba na haske guda dubu arba'in, sun hallaka dukkanin dakarun sarki Kuffuru. Dakarun sarki Ratanam na ganin haka, suka fara kwarara uban ihu, irin wanda jarumai keyi idan suka samu nasara a filin daga.
Shi kuma sarki Ratanam a durƙushe yake bisa gwiwowinsa yana aman jini, sakamakon amfani da wannan ɗalasimi da yayi. Zaka iya cewa wannan yaƙi yazo ƙarshe tunda sarki Ratanam yayi amfani da babban ɗalasimi ya hallaka dukkanin dakarun-adawa da suka kawo musu farmaki.
Sai dai kuma a daidai wannan lokaci ne, wani mutum ya bayyana a cikin iska, bisa wani ingarman doki mai fuka-fuki. Sanƴe yake cikin baƙaƙen kaya masu beza ta wuya, a bayansa kuma zabga-zabga takubba ne guda biyu a ɗaure.
Sarki Ratanam ya ɗago kansa ya kalli wannan mutumi, nan take ya haɗe fuska domin ya gano cewa ba kowa bane illa SARKI KUFFURU na Kufa.
"Iyakacin ƙarfin damtsen naka da jarumtakar taka kenan," inji sarki Kuffuru. "Da wai naso na baka dama mu ɗan fafata, tunda kayi tsaurin ido ka aika min wasiƙa, amma a yadda naga ƙarfinka da ƙarfin sihirinka. Nafi ƙarfin na fafata da kai."
Sarki Kuffuru na zuwa nan a zancensa ya kirawo ɗalasimin ƙabilar Gandiz, nan take farar dusar-ƙanƙara ta fara zubowa a wannan waje. Sarki Ratanam da duk sauran waɗanda suke wannan waje suka sandare a inda suke, babu wanda yasan abinda ke faruwa.
Dokin sarki Kuffuru mai fuka-fuki ya yiwo ƙasa-ƙasa daidai inda sarki Ratanam ke durƙushe, Kuffuru ya saka hannunsa ya riƙe gashin kan sarki Ratanam sannan ya fille kan da takobinsa. Gangar jikin sarki Ratanam ta zube ƙasa shirim a wannan wuri, kan nasa yayi ta lilo a hannun sarki Kuffuru.
A wannan wuri, a wannan lokaci, sarki Kuffuru ya kawo ƙarshen rayuwar sarki Ratanam, mahaifi a wajen jarumi Marganu masoyin gimbiya Jaanu.
Sarki Kuffuru ya shafi wuyan wannan doki, take dokin ya buɗe fuka-fukinsa ya tashi sama dashi. Kuffuru ya tafi hannunsa ɗauke da dungulmin kan sarki Ratanam.
****RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 41: *Gidan Ƙarkashin Ƙasa*
*
*
UMAR SANGARU
*
~Ɓangaren Aymanul Faris.
*
Aymanul Faris bai farfaɗo daga wannan barci da yake yi ba, bayan kammala karatun wannan littafi (TARIHIN SARKI KUFFURU DA BAYANAI AKAN SAIFUL SHIRADU) sai da gari ya gama wayewa.
Yana buɗe idanunsa ya shige cikin banɗaki yayi wanka, sannan ya sanya kayansa, ya fito falo domin cin abincin safe. A wannan rana saiya tsinci kansa a cikin farin-ciki, ba don komai ba sai domin a wannan rana Barban zai dawo.
Tun kafin Barban ya tafi yayi masa alƙawarin idan suka zo komawa gida, zai kai shi birnin Damashkar domin ya gana da madubin zuciyarsa, gimbiya Jaanu. Gimbiyar kyawawa.
Yana isowa falo ya iske mahaifiyarsa ita kaɗai zaune a cikin falon, al'amarin da ya bashi mamaki kenan. Wai shin ina jaruma Riya ta tafi? Ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa.
Cikin girmamawa yaje ya kama sawayen mahaifiyarsa ya gaishe da ita, a yanayi irin na al'adar ƙabilar Kuyuru.
"Kana lafiya?" ta tambaye shi.
Aymanul Faris ya amsa mata. "Ina lafiya. Da fatan kema na same ki, cikin ƙoshin lafiya? Ina ƴar-uwata Riya?"
Hajriya ta yamutse fuska. "Ƴar-uwarka?" ta tambaye shi.
"Eh mana, mama." ya faɗa yana dariya.
Hajriya tayi murmushi. "Shi kenan, na yarda. Tana can cikin ɗakinta tana kuka, na rasa yadda zanyi da ita ta fito mu ci abinci."
Aymanul Faris ya cika da tsananin mamaki. "Amma, meyasa take kuka?"
"Tana tunanin halin da zata shiga ne, bayan tafiyar masoyinta." Hajriya ta ce.
Aymanul Faris ya yi murmushi ya jinjina kai, yana faman buɗe kwanon abincinsa, yaji muryar Hajriya a kunnensa. "Kaje ka taho da ita, sai kuzo mu ci abincin tare ko?"
Aymanul Faris bai da ikon ja da umarninta don haka saiya miƙe ya nufi ɗakin da jaruma Riya take kuka a ciki. Yana zuwa ya risketa tsaye ta dafa ƙarafunan taga tana zubar da hawaye.
Jin motsin da tayi a bayanta, yasa ta juyo. Koda taga Aymanul Faris ne sai ta rugo da gudu ta rungume shi. Cikin sauri ya janƴe jikinsa daga nata. "Meyasa kike kuka? Kuma meyasa kika ƙi fita falo domin mu ci abinci?"
Jaruma Riya ta kama kafaɗunsa idanunta a cikin nasa, a cikin wani irin salo na nuna masa soyayyarta. "Ce min aka yi yau maigida zaizo ya ɗauke ka, ku tafi, hakane?"
"Kwarai kuwa, hakane. Kada dai ki ce min wannan shine dalilin da yasa kike kuka?" Aymanul Faris ya amsa mata.
Waɗansu hawaye masu zafi suka sake zubowa jaruma Riya. "Daidai da daƙiƙa ɗaya bana son rabuwa da kai. Shin idan kun tafi tsahon wanne lokaci zaka ɗauka, kafun ka dawo gare ni?" ta ce.
Aymanul Faris ya yi mata murmushi mai taushi, ya ce, "Ni kaina bansan tsahon lokacin da zamu ɗauka ba, abinda na sani dai shi ne ayyuka guda goma zamu gudanar, yanzu haka mun kammala guda biyu?"
Riya ta goge hawayenta ta ce, "Ina so kayi min alƙawari duk bayan sati guda zakana kawo min ziyara, ka amince?"
Aymanul Faris ya kaɗa kai, "Ba zan iya ɗaukar wannan alƙawari ba. Saboda bani nake iko da kaina ba, kin san cewa umarnin Barban nake bi." ya ce.
Hawaye na shirin sake zubowa jaruma Riya ya kama hannunta suka fice daga cikin ɗakin, suka nufi wannan falo inda mahaifiyarsa take jiransu.
Suna zuwa kowa ya zubawa kansa irin abincin da yake buƙata, suka fara ci. Tsahon ɗan lokaci kafun kowa ya ƙoshi.
Kafun su gama wanke hannayensu, wani irin farin haske ya bayyana a cikin wannan falo. Sannu-a-hankali siffar wani mutum ta fara bayyana a cikin wannan haske, tun tana bayyana dishi-dishi har ta gama fitowa fili ƙarara.
Ba wani bane illa Hodon wanda aka fi sani da Barban.
Nan take ya gaishe da mahaifiyar Aymanul Faris, shi kuma Aymanul Faris da jaruma Riya suka gaishe da shi.
Barban ya fara yiwa Hajriya jawabi cikin hikima, "Nayi farin ciki matuƙa da na same ku a cikin ƙoshin lafiya da farin-ciki. Tabbas na san cewa ku na jin daɗin zama a cikin wannan birni nawa. Ina fatan ku ci gaba da zama a cikin farin ciki haka.
"Ya ke Ummu-Ayman kiyi sani cewa nazo ne domin na ɗauki wannan ɗa naki kamar yadda muka alƙawarta sati guda da ta gabata. Da nayi niyyar na faɗa muku sirrin waɗannan ayyuka da muke yi amma sai maigidana ya hanani. Amma, tabbas kuyi sani cewa duk wani aiki da muka gudanar da Aymanul Faris yana da manufa, amma a yanzu ba zamu faɗi manufar ba, sai a ranar da muka kammala.
"Nayi muku alƙawari duk bayan makonni biyu zamu na zuwa ni da Ayman muna kawo muku ziyara, muna ganin lafiyarku, kuma kuna ganin tamu.
"Ina ganin sai kuyi sallama da wannan masoyi naku domin lokaci yana tafiya." Barban na gama faɗin haka ya tashi ya fice daga cikin falon.
Hajriya da jaruma Riya suka rungume Aymanul Faris kamar yadda suka yi a lokacin zuwansu, sai dai amma a wannan karon tsahon ɗan lokaci suka ɗauka suna ƙanƙame da juna. Ba tare da ɓata wani lokaci ba, suka yi sallama da Aymanul Faris suna kuka yana kuka, ya fita daga cikin falon.
Barban na ganin ya fito ya shafi kambun tsafin dake hannunsa, su Hubbus Dawan suka bayyana. Barban ya basu umarnin su ɗauke shi, shi da Aymanul Faris su kaisu maɓoya.
Ba tare da ɓata lokaci ba suka ɗauke su, suka ɓace dasu a cikin gajimare.
Aljani Hubbus yayi ta tashi da su sama, tamkar ƙololuwar sama zaije, al'amarin da yayi matuƙar baiwa Aymanul Faris mamaki kenan. Yana shirin tambayar Barban ina zasuje kenan, wata iska mai sanyi ta doke shi. Nan take wani irin barci mai nauyi ya ɗauke shi, daga nan bai san abinda ya sake faruwa ba.
Yana farkawa daga wannan barci mai nauyi, ya tsinci kansa a cikin wata tangamemiyar fada, wacce bai taɓa ganin irinta a iya tsahon rayuwarsa ba. Wata zabgegiyar karaga ya gani ta mulki wacce saboda tsananin sheƙinta har kashe idanu take, an ajiyeta a tsakiyar fadar. Sannan kuma wani irin ƙamshi ne mai sanyaya zuciya ke tashi a cikin fadar.
Kilishin dake cikin fadar kuwa, idan mutum ya taka zaiji tamkar zai nutse saboda tsananin taushi. A takaice dai, wannan fada za'a iya kiranta da aljannar duniya.
Barban ya kama hannun Aymanul Faris suka nufi waɗansu kujeru guda biyu dake gefe guda na alfarma, suka zazzauna.
"Wannan ita ce asalin fadar sarkin ɓarayin duniya, wancan ita ce asalin karagar sarkin ɓarayin duniya. Wannan fada ba'a cikin asalin duniyarmu take ba, ko kuma zan iya cewa a cikin duniyar namu take, amma babu wanda ya isa yazo inda take. Ka san a cikin ina aka ginata?"
Aymanul Faris ya girgiza kai alaman bai sani ba.
Barban ya ci gaba da bayani, "Wannan fada a ƙarƙashin teku aka ginata, tamkar jirgin ruwa haka take yawo. Tana amfani da ƙarfin sihirin tsafi mai mataki na goma. Kayi sani cewa duk kayan tsafi da ya kai mataki na goma, yana iya sarrafa kansa. Don haka wannan fada tana sarrafa kanta, na rantse da darajar mahaifiyata idan akwai mai iya kama ni a duniya, Allah ya tsine min.
"Da zarar mutum ya gano maɓoyata, wato ya gano wannar fadar. Kafun ya iso inda take zata sauya muhalli kuma zata sake ƙarfafa ƙarfin sihirin jikinta. Kaga kenan babu wanda ya isa ya kama ni, ko kuma ya gano inda nake face da sanina.
"In dai kaga an kamani ko kuma an gano inda nake, to ni na so. A halin yanzu ko sarkin-mayu na duniya bai isa yaga inda nake ba, wato dai a takaice na ɓata daga duniya. Ka san meyasa muka zo wannan fada tawa, mai cikakken sihiri?"
Aymanul Faris ya sake girgiza kai, "A'a,"
"Saboda a halin yanzu an samar da taswira wacce zata bi diddigin duk inda nake a faɗin duniya. Wannan fada da birnin Darul Barban ne kaɗai inda wannan taswira bata aiki, da zarar ina waɗannan wajaje guda biyu, ɗaukewa take ta daina aiki."
Aymanul Faris ya cika da tsananin mamaki ya ce, "Ya shugabana, tabbas kai cikakken hatsabibi ne wanda har yanzu duniya bata gama fuskantar waye kai ba. Hatta ni kaina da muke tare kullum har yanzu ban gama fuskantar waye kai ba. Idan babu damuwa ina so ka amsa min waɗansu tambayoyi."
Barban ya yi murmushi ya ce, "Ina jinka, faɗi duk abinda kake so ka tambaya, ni kuma zan kasance mai baka amsa."
"Meyasa ba muje birnin Damashkar wurin gimbiya Jaanu ba, kamar yadda kayi min alƙawari wancan makon akan zamuje domin na ganta?
"Naji da kazo yiwa mahaifiyata bankwana kana cewa, duk wani aiki da muka gudanar tare yana da manufa, shin kana da wata manufa dabam ne bayan ɗaukar fansa?
"Tayaya aka samu taswira wacce zata bi diddigin duk inda kake, kuma su waye suka samar da wannan taswira?
"Wai shin duniya wanne irin kallo take yi maka, kallon ɓarawo ko kuma mai taimako?"
Barban ya ɗago kansa ya kalli Aymanul Faris cikin tsananin mamakin jin waɗannan tambayoyi, tabbas karanta wannan littafi da yayi, yayi masa amfani matuƙa.
"Abinda yasa ba muje birnin Damashkar ba, shi ne akwai abinda nake jira nanda cikar mako guda. Tabbas rana irin ta yau, muna cikin birnin Damashkar kana wajen masoyiyarka.
"Waɗannan manufofi nawa babu wanda ya san su, daga ni sai maigirma Ranganu. Amma zaka cika da tsananin mamaki a duk lokacin da na sanar da kai su, kuma zakayi min godiya sosai.
"Kayi sani cewa duk faɗin duniya babu wanda sihirin tsafi baya tasiri akansa, hatta shi kansa wanda ya ƙirƙiri tsafi, tsafi ya ci shi. Sarki Kuffuru, ƴarsa Firziyya da boka Hubbazu su ne suka kama mahaifina, suka saka shi dole ya faɗa musu ainihin sunana, ainihin sunan mahaifiyata, inda aka binne cibiyata da inda za'a sami zanen yan-yatsuna.
"Ka sani cewa waɗannan abubuwa da na lissafo su ake buƙata wajen samar da taswirar da zata bi diddigin kowanne irin mutum a duniya, don haka nima sun mallaki taswirata. Bisa wannan dalili ne, ni da maigidana muka yi musu wani shiri wanda zai rikita su anan gaba. In banda wannan wuri da birnin Darul Barban babu inda zanje na tsirawa wannan taswira.
"A gaskiya a halin yanzu duniya kallon ɓarawo take min, amma nan gaba zan bayyana a matsayin jarumi kuma masoyin al'umma. Idan baka manta ba farkon haɗuwar mu na baka labarin cewa, ina da yara fiye da mutum dubu arba'in waɗanda suke aiki a ƙarƙashina, ka tuna?"
Aymanul Faris yayi shuru ya faɗa kogin tunani mai zurfi, daga can saiya numfasa ya ce, "Kwarai kuwa, na tuna. Tabbas ka taɓa bani wannan labari na yaranka guda dubu arba'in da kace suna yi maka aiki a kowanne birni."
Barban ya yi murmushi ya ce, "Haka ne. To ka sani cewa waɗannan yara nawa, ba ɓarayi bane. Zamu iya kiransu da sunan wakilan 'MAI-TAIMAKO' domin da wannan suna suke amfani, 'WAKILAN MAI-TAIMAKO'.
"WAKILAN MAI-TAIMAKO, mutane ne da zaka rinƙa samunsu a cikin kowanne birni dake faɗin wannan duniya tamu. Ba su da aiki face taimakon gajiyayyu; makafi, marayu, guragu, kutare da duk wani mutum mai buƙatar taimako. Zaka iya cewa sun san suna da ubangida amma tsahon shekaru ashirin basu san waye wannan maigida nasu ba.
"Abinda suka sani dai, shi ne duk ƙarshen shekara akwai hadiman aljanu dake kawo musu dukiya da duk wani abu da waɗannan gajiyayyun mutane suke buƙata."
Aymanul Faris cikin mamaki ya ce, "Waye ne MAI TAIMAKO?"
Barban yai dariya ya ce, "Bar wannan magana a gefe, mu dawo kan maganar takobin Saiful Shiradu, abin harin mu na uku.
"Shin ina aka ajiye wannan takobi? Wanne irin tsaro aka bata? Shin inda aka ajiye ta yana da kafin-tsafi ko ba shi da? Na samo amsoshin waɗannan tambayoyi a cikin mako da nayi ba ma tare. Yanzu abinda nake buƙata daga gareka shi ne nutsuwa, kamar yadda ka bani nutsuwarka a hari na farko da na biyu."
Barban na zuwa nan a zancensa ya tafa hannayensa take kofin shayi mai zafi ya bayyana akan hannunsa ya kurɓi shayi, shi kuma Aymanul Faris saiya gyara zama.
"Tun sa'adda sarki Kuffuru ya mallaki takobin Saiful Shiradu saiya gagara sarrafa ta, saboda ba shi sirri irin na jinin ƴaƴan Samudul Ansari. Kayi sani cewa ƴaƴan Samudul Ansari a cikin jininsu, suke jin wannan takobi da zarar sun riƙeta. Saboda wannan dalili ne yasa sarki Kuffuru ba zai iya sarrafata ba, face ya cika wannan kwalba da zallar jinin ƴaƴan Samudul Ansari.
"Saboda wannan dalili ne yasa sarki Kuffuru ya gina wani gida a ƙarƙashin ƙasa mai mugun tsaro. Ba don komai ya gina wannan gida ba, sai domin adana wannan takobi ta Saiful Shiradu.
"Wannan gida na ƙarƙashin ƙasa yana fasali guda uku ko kuma nace ƙofofi guda uku na shiga. Waɗannan ƙofofi guda uku suna da mugun haɗari, kuma kowacce ƙofa da amfaninta da kuma yadda take bayar da tsaro.
"Ƙofa ta farko da zallar gilashi aka ƙerata, yanayin yadda take buɗewa shi ne rabewa biyu take ta samar da hanya a tsakiya. A jikin wannan ƙofa akwai ɗan ƙaramin madubi a daidai tsahon fuskar mutum. Duk duniya fuskar sarki Kuffuru ce kaɗai zata iya buɗe wannan ƙofa ta gilashi, wato da zarar ya saita fuskarsa da wannan madubi wannan ƙofa zata buɗe ya wuce.
"Ƙofa ta biyu kuma, da zallar dutse aka ginata. Kamar yadda ƙofar farko take da wannan madubi, haka wannan ƙofa ta biyu take da wata ƴar alama a tsakiyarta. Shi dai wannan ɗan alama zanen tafin hannun mutum ne dashi, da zarar mutum ya ɗora tafin-hannunsa akan wannan alama, wannan ƙofa zata ɗauki yanayin jininsa da zanen hannunsa. Duk duniya in banda jinin sarki Kuffuru babu jinin da ya isa ya buɗe wannan ƙofa.
"Ƙofa ta uku ma da gilashi aka ƙerata, amma ita yadda take buɗewa shi ne, ƙofar ne take nutsewa cikin ƙasa ta samar da hanya. Bata amfani da zanen-yatsu ko kuma jini wajen buɗewa, abinda kawai take buƙata ƙarfin zuciya da yaƙinin cewa zata buɗe. Idan mutum ya kuskura yace zai buɗe wannan ƙofa a tsorace ko kuma cikin kwakwanto, to, tabbas wuta ce zata ƙone shi.
"Ya kai Ayman wannan shi ne taƙaitaccen bayani akan waɗannan ƙofofi guda uku kamar yadda maigirma Ranganu ya bani labari, shin ka san abinda zai faru da mutum idan ya kasance ya saita fuskarsa da wannan madubi dake jikin ƙofar gilashi, ko kuma ya ɗora tafin-hannunsa akan wannan ƙofa da aka gina da dutse?"
Aymanul Faris ya girgiza kai alamun bai sani ba.
"Idan mutum ya saita fuska wadda bata kasance ta sarki Kuffuru ba a jikin wannan madubi, waɗansu sirarrun kibbau ne masu mugun-dafi zasuyi fitar burtu su cake idanunsa, da zarar sun cake idanunsa zai makance sannan ya zube ƙasa matacce sakamakon ƙarfin wannan dafi.
"Haka kuma idan ya ɗora tafin-hannunsa akan wannan ƙofa ta dutse wanda bai kasance hannun sarki Kuffuru ba ko na ƴarsa ba, nan take takubban duwatsu zasu fito daga cikin wannan ƙofa su cake shi.
"Wannan aiki da zamu yi yana da matuƙar wahala, shiga wannan gida na ƙarƙashin ƙasa yafi komai tashin hankali. Saboda wannan dalilin ne yasa maigirma Ranganu ya shirya bamu horo na musamman ni da kai, tsahon mako guda zamu ɗauka a cikin wannan fada muna karɓar horo. Yau sha-ɗaya ga watan Satumba, ranar sha-takwas ga wata zamuje birnin Damashkar, ranar biyu ga watan Oktoba kuma zamu afka gidan ƙarƙashin ƙasa na sarki Kuffuru da aka gina a ƙarshen fadarsa."
Aymanul Faris ya cika da tsananin mamaki, ya ruɗe ya rasa ma meye zaiyi tambaya akai. Tabbas wannan aiki da zasu tafi mutum zai iya cewa anƴa zasu iya kuwa?
A ina zasu sami fuskar da zata yi daidai da fuskar sarki Kuffuru wacce zata buɗe ƙofar gilashi?
A ina zasu sami tafin-hannu mai ɗauke da yanayin jinin sarki Kuffuru da zanen hannunsa?
Domin jin amsar waɗannan tambayoyi sai mu jira lokacin shigarsu wannan gida na ƙarƙashin ƙasa mu gani.
***
Washe gari bayan wannan tattaunawa tsakanin Aymanul Faris da Barban, suna zaune a cikin wannan ƙasaitacciyar fada suna cin abinci, aljani Ranganu ya saƙƙo cikin fadar sanye da fararen tufafi.
Barban da Aymanul Faris suka zube ƙasa suka kwashi gaisuwa, aljani Ranganu ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Ina da magana da kai, kazo ka sameni a ɗakin can. Barban kayi haƙuri ka jiramu anan, maganata da TAURIN mai tsaho ce."
Aljani Ranganu na gama faɗin haka ya nufi cikin wani ɗaki dake gefe ɗaya, Aymanul Faris ya kalli Barban sannan ya bi bayan Ranganu. Shi kuma Barban da murmushi kawai ya bi su don yasan abinda Ranganu zai faɗawa Aymanul Faris.
Aymanul Faris na shiga cikin wannan ɗaki, ya tsinci kansa a cikin wata sabuwar aljannar duniyar wadda ya gagara kwatanta kyawunta da komai. Waɗansu karagu na mulki ya kalla guda uku a jere a ƙarshen ɗakin. Amma karagar da take tsakiya tafi sauran guda biyu dake gefenta girma da ƙawatuwa.
Mutum zai cika da tsananin mamaki idan ya kalli aljani Ranganu akan ɗaya daga cikin karagu ƙanana dake gefen wannan ƙatuwar karaga. Abin tambayar anan shi ne meya hana shi zama akan wannan karaga ta tsakiya? Na farko dai girman jikinsa yafi dacewa da wannan karaga, na biyu kuma shi ne maigidan Barban. Barban kuma kowa yasan shi ne maigidan Aymanul Faris.
Shima Aymanul Faris saiya tunkari ɗaya daga cikin ƙananun karagun, bai tunkari babbar tasu ba. Amma bisa mamaki sai yaji muryar aljani Ranganu, "Zauna akan wannan karaga ta tsakiya saboda babu mai zama akanta face kai."
Cikin tsananin mamaki Aymanul Faris ya zauna akan wannan karaga amma bai ce komai ba.
"Ka gafarce ni, Ayman. Tabbas a cikin dajin Marsas naso na tafka wani babban kuskure da nayi

Please Login or Register in order to submit comment