Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

waɗanda suka saba sakawa mutanen da za'a baiwa wannan gunki nasu jininsa, suka sakawa Marganu. Mutum biyu daga cikinsu suka cicciɓi Marganu suka ɗaga shi sama, suka ɗaure shi a jikin wani murtuƙeƙen itace, suka ɗauki itacen suka nufi wannan gidan bauta inda gunki Barzas yake.
Waɗannan mutane suka kewaye Marganu domin tabbatar da tsaro dukda cewa a ɗaure yake a jikin itace. Har suka iso wannan gidan bauta Marganu bai fita a hayyacinsa ba kuma yana ganin dukkan abinda ke faruwa.
A wannan rana wannan gidan bauta a cike yake maƙil da mutane, ana ta buga ganguna, suna wata irin rawa wacce suka saba yi a duk lokacin da ranar-yanka tazo.
A tsakiyar su kuma an bar wani fili inda gunki Barzas yake, wani narkeken ƙato na tsaye a gefen gunkin riƙe da wani zabgegen gatari wanda suka saba fille kan mutane da shi.
Har a wannan rana, ba'a gyara kan wannan gunki da Marganu ya fille a watanni baya ba. Waɗannan ƙoƙunan dake jere a gefen gunkin kuma babu komai a cikinsu. Ga dukkan alamu idan aka sarewa Marganu kai, a cikin su za'a zuba jininsa.
Nan take waɗannan mutane guda biyu suka kunce Marganu daga jikin wannan dogon itace, suka ɗauko shi tamkar sun ɗauko tsumma, suka zo suka kwantar da shi akan wani tudu dake kusa da wani kasko. Tudun ya ɗan ɗara kaskon a tsayi da kaɗan, saboda haka ana yanka Marganu jininsa cikin wannan kasko zai shiga.
Ana kwantar da Marganu wannan sadauki mai riƙe da zabgegiyar gatarin nan ya matso kusa, ya gyara kwantar da Marganu kansa ya fuskanci wannan gunki sosai.
Gaba ɗaya mutanen dake cikin wannan gida suka durƙusa kan gwiwowinsu, suka zubawa wannan sadauki idanu suna jira ya cika umarnin abin bautarsu. Sadaukin ya ɗaga gatarinsa sama, ya kalli wannan gunki nasu sannan ya fara addu'a.
"Da sunan mai kashewa da rayawa, ubangijin halittun dake rayuwa bisa tsaunika da doron ƙasa da ƙarƙashin tekuna. Kamar yadda ka umarce mu, kamar yadda sarauniyarmu ta umarce mu, nemo jinin ISRABIL. Mun cika wannan umarni. Da sannu duniya zata dawo ƙarƙashin ikonka, mai girma. Da sannu duniya zata risina ma. Ka karɓi wannan yanka namu, ka bamu lada ya maigirma. Ka bamu sa'a a al'amuranmu, ka kare mu daga sharri. Ka tsare sarauniyar mu a duk inda take sannan ka dawo da ita gida lafiya." ya kammala wannan addu'a amma a cikin yaren su.
Sauran mutanen dake wannan wuri suka amsa da AMIN amma ta yarensu.
Duk wannan abu da ya faru Marganu yana gani kuma yana ji, amma babu abinda zai iya yi face kukan baƙin ciki. Marganu ya rufe idanunsa cikin saduda da jiran jin wannan gatari ya datse masa wuya.
Wannan sadauki na gama wannan addu'a ya taƙarƙare ya tattaro ƙarfinsa waje guda, yana niyyar yiwa Marganu sara guda ɗaya wanda zai fille kansa nan take.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani gaba ɗaya mutanen dake wannan wuri suka ga wata irin farar dusar ƙanƙara ta fara zubowa cikin wannan gida. Duk wanda wannan dusar ƙanƙara ta taɓa sai kaga nan take ya sandare a inda yake tsaye.
Wannan dusar ƙanƙara tana da tsananin yawan gaske tamkar ruwan sama haka take sauƙowa, don haka kafun waɗannan arnan-daji su gama ankarewa tuni ta lulluɓe su gaba ɗaya.
Daga kan wannan sadauki mai shirin sare kan Marganu har zuwa kan sauran dukkanin jama'ar dake wannan wuri, duk sun sandare a inda suke tsaye basu ma san abinda ke faruwa ba.
Jim kaɗan da gama sauƙar wannan dusar ƙanƙara waɗansu mutane guda biyu suka shigo cikin wannan gida na bauta. Abin mamaki mutanen sun kasance guda biyu kacal, kuma budurwa ce da tsoho tukuf.
Budurwar ta kasance doguwa mai tsananin hasken fata, tana rataye da zabga-zabgan takubba guda biyu a gadon bayanta. Amma ta rufe fuskarta da wata irin hula wacce aka yiwa ƙofofin baki da hanci kaɗai. Dukda fuskarta ta a rufe take, amma idan mutum ya kalli idanunta da dogon hancinta zai tabbatar da cewa lallai kyakkyawa ce.
Wannan tsohon kuma, ya kasance tsoho tukuf domin har doro yake da, amma kana ganin idanunsa zaka tabbatar da cewa lallai tsohon-hannu ne a harkar tsafi.
"Yi sauri ki kwance shi, kafun aljanun waɗannan mutane su ƙaraso." inji wannan tsoho.
Budurwar na jin haka ta ƙarasa kan Marganu da sauri, ta tafa hannayenta sannan ta haɗe su a waje guda. Ta saita su daidai ƙirjinsa, nan take wani farin haske ya fara daga cikin hannun nata yana shiga ƙirjin nasa.
Tsahon ƴan daƙiƙu sannan ƙarfin jikin Marganu ya dawo, ya kalli wannan budurwa cikin tsananin mamaki. Idan ya kalli cikin ƙwayar idanunta sai yaga kamar ya taɓa ganinta, amma ya gagara tuno a ina ne?
Cikin tsananin fusata da harzuƙa Marganu ya tsitstsinke sarƙoƙin da suka daɗɗaure shi, ya miƙe tsaye cikin tsananin kuzari da taƙama da ƙarfi. Lallai ko shakka babu a wannan lokaci ƙarfin jikinsa ya gama dawowa, kuma a shirye yake domin ya gwabza yaƙi da waɗannan arnan-daji.
Marganu na shirin tambayar wannan budurwa wace ce ita kenan, yaga sararin samaniya tayi duhu tamkar hadari ne ya taso.
Marganu, wannan budurwa da wannan tsoho suka ɗaga kawunansu cikin tsananin mamaki domin ganin abinda ya tare hasken rana. Nan take suka yi arba da gungun waɗansu baƙaƙen aljanu kimanin su dubu tsaitsaye cikin iska.
Gaba ɗaya aljanun suna riƙe da makaman yaƙi amma na haske, sai wata irin walƙiya ne ke tashi a jikin waɗannan makamai.
A daidai lokacin kuma, wannan dusar ƙanƙara wadda ta lulluɓe waɗannan arnan-daji ta soma ɓacewa, suka fara dawowa cikin hayyacin su.
Koda suka ga waɗannan aljanu a sama, kuma suka ga wannan baƙuwar jaruma mai rufaffen fuska da wannan tsoho sai suka cika da tsananin mamaki. Babban cikinsu ya basu umarnin kewaye su Marganu, nan take suka cika umarni suka kewaye su Marganu a tsakiya.
Wannan budurwa ta matso kusa da Marganu ta zaro takubbanta guda biyu ta miƙa masa ta ce, "Karɓi waɗannan takubba, masoyina. Alhakkin kula da mayaƙan dake ƙasa yana hannunka. Ka barmu da waɗancan baƙaƙen aljanun ni da wannan ɗan tsohon."
Marganu na jin muryar wannan budurwa zuciyarsa ta buga da ƙarfi, saboda wannan murya ba ɓoyayyiya bace a kunnuwansa. Amma, sai ya ƙaryata kansa akan cewa babu yadda za'ayi mai wannan murya ta kasance wacce yake tunani.
Yana cikin wannan tunani ne yaji ƙarar zare makaman yaƙi, nan take ya kawar da tunanin daga ransa. Ya karɓi waɗannan takubba daga hannun wannan budurwa ya fuskanci waɗannan arnan-daji.
Budurwar da wannan tsohon suka buɗe hannayensu suka tashi sama tamkar tsuntsaye suka tsaya a gaban waɗannan baƙaƙen aljanu aka fara kallon-kallo.
Marganu ya taƙarƙare ya kwarara uban ihu ya ɗaga waɗannan takubba guda biyu, ya falfala da azababben gudu ya tunkari dandazon arnan dajin nan. Ai kuwa suna ganin haka suka ce da wa aka haɗa mu?
Mayaƙan cikinsu suka tasowa Marganu aka haɗe a tsakiya. Nan take suka ruguntsume da azababben yaƙi mai matuƙar ban tsoro.
Marganu ya wanzu a tsakiyar su yana ta kai musu sara da suka cikin baƙin zafin nama da bajinta, tamkar ba shi ne ɗazu a kwance suna niyyar yanka shi ya gagara taɓuka komai ba.
Lallai a wannan rana Marganu a matukar fusace yake wannan yaƙi, don haka saiya zamewa waɗannan arnan daji guguwar masifa da bala'i. Duk inda yasa a gabansa babu abinda mutum zai na gani face fantsuwar jini da kuma tashin sassan jikin bil'adama.
Duk tsananin yawan waɗannan arnan daji da tarin makaman yaƙinsu sai ya zamo na banza domin sun gagara yiwa Marganu komai, Marganu ya ci gaba da sharafinsa a tsakiyar su.
Haka dai Marganu ya ci gaba da karkashe su har tsahon rabin sa'a amma tamkar babu abinda ya kashe. Dukda cewa aƙalla ya kashe ya kai sadaukai dubu da ɗoriya.
Kwatsam! Daga can sama aka ga bala'i kala-kala yana ta zubowa kan waɗannan arnan-daji. Nan take suka soma kwarara uban ihu suna mutuwa. Wata irin ƙawanƴar wuta mai faɗin gaske ta diro kan mutane, kamar an gasa kaji haka wannan wuta ta gasa su.
Sauran arnan-daji na ganin haka suka nemi hanƴa, suka cika wandunansu da iska.
Ba komai ne ya haddasa wannan bala'i ba, face fafatawar da ake yi a sama tsakanin waɗannan baƙaƙen aljanu dasu wannan tsoho.
Saboda tsabar bala'i Marganu ma, guje-guje da kauce-kauce ya fara domin kada abin ya ritsa da shi. Wannan budurwa na ganin haka ta nuna Marganu da hannu, take wani shingen tsafi ya saƙƙo ƙasa ya lulluɓe shi. Wannan shinge na lulluɓe shi, duk bala'in da ya yiwo kansa, baya iso shi yake kaucewa.
A sararin samaniya kuwa, wata fafatawa ce mai ɗaukar hankali ke wakana. A duk sa'adda waɗannan aljanu suka jehowa wannan budurwa ko kuma wannan tsoho wutar tsafi ko mashin tsafi, sai kaga sun kira ɗalasimin tsafi sun samar da makami kwatankwacin wancan. Makaman suna haɗuwa a tsakiya, za'a kwararo tsawa sannan su zubo ƙasa.
Wannan dattijo duwatsun haske guda huɗu ya samar akan hannunsa ƙanana, kuma dasu yake kaiwa waɗannan aljanu hari kuma yake kare kansa.
Wannan budurwa kuma, irin wannan dusar ƙanƙara ce ta lulluɓe jikinta gaba ɗaya duk abinda ya tunkarota, baya isowa yake kaucewa da kansa.
Abin mamaki shi ne tsahon wannan rabin sa'a da aka yi ana wannan fafatawa wannan dattijo da wannan budurwa ko sau ɗaya basu maidawa waɗannan aljanu martani ba. Kawai kare kansu suke.
Haka dai aka ci gaba da wannan gumurzu har tsahon wata rabin sa'ar, wato sa'a guda kenan. Wannan sa'a na cika wannan datijjo ya dubi budurwar nan ya gyaɗa mata kai.
Nan take ta rintse idanunta shima ya rufe idanunsa, suka fara kiran sunayen aljanunsu a cikin zuci.
Wani irin allon-haske mai girman gaske ya bayyana a gaban wannan budurwa, ita kuma ta dinga aikawa waɗannan aljanu dusar ƙanƙara. Wannan dusar ƙanƙara nata yana fitowa daga hannunta yake shigewa cikin wannan allon-haske, yana shiga cikin allon hasken yake ɓacewa.
Waɗannan suna tsaitsaye suna kallon ikon ALLAH kawai sai suka ji jikinsu ya soma sandarewa. Kafun su ankara irin abinda ya faru da mayaƙan nan ɗazu su ma ya dira akansu. Sun sandare a sararin samaniya basu ma san abinda ke faruwa ba.
Wannan budurwa da wannan tsoho suka saƙƙo ƙasa suka ɗauki Marganu. Sannan wannan tsoho ya doki iska da hannunsa, nan take su ukun suka zamo haske suka ɓace daga wannan wuri. Kafun su ɓace wannan budurwa ta jefi waɗansu gangunan mai dake gefe guda da wuta.
Suna gama ɓacewa daga cikin wannan gidan bauta, wannan gangunan mai suka fara bindiga suna haifar da gagarumar wuta.
Kafun kace me wannan tuni gidan bauta ya gama ƙonewa ya ratattake ya tarwatse. Har da sauran wannan gunki na Barzas dake cikinsa ya gama zamowa toka.
***
A tsakiyar wata ƙasaitacciyar fada suka bayyana, wacce zata ninka fadar sarki Kuffuru a ginuwa da tsaruwa sau uku. Wannan budurwa ta kwantar da Marganu akan wata doguwar kujera sannan ta ɗakko magani ta fara shasshshafa masa akan raunikansa.
Tana gama shafa masa wannan magani, ta bashi wani sinadari mai ƙarfi ya sha. Yana shan wannan sinadari barci mai nauyi ya ɗauke shi, daga wannan rana wannan budurwa da wannan tsoho suka ci gaba da jiƴƴar yarima Marganu a cikin wannan ƙasaitacciyar fada. A duk lokacin da ya farfaɗo kafun ma ya ce wani abu wannan budurwa zata sake shayar da shi wannan sinadari ya sake komawa barci. Har tsahon sati uku sannan Marganu ya gama murmurewa ya samu cikakkiyar lafiyarsa, murɗaɗɗen jikinsa na asali ya sake bayyana. Kai, saboda yadda wannan budurwa da wannan tsoho suka kula da shi, saida jikin nasa yafi na da kyawu.
A wannan rana da Marganu ya farfaɗo bata ba shi wannan sinadari ba, abinci kawai ta kawo masa mai rai da lafiya. Sai a wannan lokaci ne Marganu ya gama nutsuwa kuma ya yiwa wannan fada da suke ciki kallo mai kyau. Yana gama cin wannan abinci, wannan budurwa da tsohon nan suka zo gabansa suka zauna bisa waɗansu kujeru masu fuskantar sa. Abinda ya ɗaurewa Marganu kai shi ne tsahon waɗannan kwanaki da yayi a cikin wannan wuri ana jiƴƴarsa, bai taɓa kallon fuskar wannan budurwa ba, kullum fuskarta a rufe take da wannan hula.
"Kafun na ce komai, zanyi amfani da wannan dama domin na gode muku bisa ceton rayuwata da kuka yi a lokacin da nafi kowa buƙatar na rayu. Dukda cewa bansan su waye ku ba, amma ina ji a jikina kamar na san ku ko kuma na taɓa ganinku. Shin dan ALLAH ko zaku yi min bayanin kanku, nagode." inji Marganu cikin tattausan harshe.
Wannan dattijo ya dafa kafaɗar Marganu ya ce, "Yarima, muna jajanta maka bisa rashin gwarzon mahaifinka da kayi. Kayi sani cewa a duniya in banda iyayenka da suka haifeka babu mai tsananin ƙaunarka kamar wannan budurwa da muke tare. Wannan budurwa ita ce taje ta sameni har kan tsaunin Dulwein, ta kwashe labarin duk abinda ya faru da kai ta sanar dani, sannan ta ce a halin yanzu su sarki Kuffuru sun ɗauke ka sun tafi da kai tsaunin Barzasa domin su bayar da kai ga sarauniya Rauziyya a yi tsafi da jininka. Ya ɗauke mu tsahon kwanaki biyu muna shiri, daga ƙarshe ta ƙaddamar da jinin ƙabilar Gandiz dake jikinta, muka je ceto ka.
"Ni suna na, AYDENLIK. Ni ne babban hadimin mahaifinka wanda yake kula da aljaninsa. A kaf faɗin birnin Hirtolia babu wanda ya taɓa kallona, saboda a can saman tsaunin Dulwein dake bayan gari nake rayuwa. Shi kansa sarki Ratanam a sati sau ɗaya kacal yake kawo min ziyara. Kafun sarki Ratanam yayi ƙaura a ziyarar da ya kawo min ta ƙarshe ya bani waɗansu abubuwa guda uku ya ce, na damƙa maka su a duk sa'adda na haɗu da kai sannan ya roƙi alfarma a wajena akan na kula da kai, har zuwa sa'adda zaka kai babban matsayi a wannan nahiya tamu. Na amsa da na'am bisa wannan ƙuduri da yazo mini da shi."
Aydenlik yana zuwa nan a zancensa ya zira hannu cikin aljihu ya fiddo wata wasiƙa nannaɗaɗɗiya, ya miƙawa Marganu wasiƙar. Cikin hanzari Marganu ya karɓa saboda ya gano wasiƙar waye ne. Kafun ya buɗeta Aydenlik ya sake miƙo masa wata takobi. Abin mamaki babu ƙarfen takobin, kawai iya mariƙin ne. Hawayen farin ciki ya zubowa Marganu saboda ya gano wannan takobi, yasan cewa dama wannan takobi bata da ƙarfen-takobi kawai haske ne yake wanzuwa a maimakon ƙarfen, a duk lokacin da aka fara gumurzu ko kuma mai ita yake son amfani da ita. Wannan takobi ita ce muka gani a hannun sarki Ratanam a lokacin fafatawarsa ta ƙarshe.
"Waɗannan su ne biyu daga cikin abubuwa ukun da ya bani. Na ukun nasu aljanin mahaifinka; aljanin haske ISIKA. Aljani Isika yana can cikin kogon dutse a birnin Hirtoliya, zamu je wajensa domin ka ƙaddamar dashi a matsayin aljaninka." inji Aydenlik.
Marganu ya karɓi wannan takobi ya ɗaureta a kunkuminsa sannan ya yiwa tsoho Aydenlik godiya bisa cika wannan umarni na mahaifinsa da yayi. Ya juya ya dubi wannan budurwa ya ce, "Dukda cewa ba ki bayyana fuskarki a gareni ba, amma na fara fuskantar kamar na ganeki. Sannan dukda cewa ban gama gano wace ce ke ba, na amince ɗari bisa ɗari da soyayyarki. Yanzu buɗe fuskar ki muyi magana."
Wannan budurwa na jin kalaman Marganu waɗansu hawaye suka gangaro daga cikin idanunta, har suka soma jiƙa wannan hula da ta rufe mata fuska. Ta miƙe tsaye ta juyawa Marganu baya sannan ta fidda wannan hula amma sai ta gagara juyowa ta kalle shi. Ta fara magana da cewa.
"Tun daga ranar da nayi arba da kai zuciyata ta kamu da tsananin ƙaunarka. Ban taɓa tsammanin zan nemeka da kaina ka ƙi biya min buƙatata ba, kayi sani cewa wannan ita ce jarrabawar da nake yiwa dukkan samarin da suka zo birninmu amma babu wanda ya taɓa haura wannan jarrabawa face kai. Ba wai ina nufin na taɓa tarawa da wani bane. Duk wanda na fuskanci cewa jikina yake so ba wai ni ba, sa wa nake mahaifina ya kore shi daga wannan birni namu. Daga lokacin da ka nuna jikina sam bai burgeka ba, na ji duk duniya babu wanda ya burgeni idan ba kai ba.
"Tun daga lokacin dafin sonka ya shiga zuciyata, a kullum bani da aiki face tunani da zulumi akan halin da ka tsinci kanka a ciki. Na rantse da kabarin mahaifiyata tun daga lokacin da mahaifina yasa aka kulleka a kurkuku hankalina bai sake kwanciya ba, tsorona shi ne kada su cutar min da kai ko kuma su kasheka. YARIMA INA SONKA. Na zaɓi nayi rayuwa da kai cikin farin ciki, baƙin ciki, wahala ko ƙunci akan na zauna tare da mahaifina wanda kullum ba shi da buri face bin son zuciyarsa da abinda ta raya masa na zalunci.
"Mahaifina azzalumi ne na ƙarshe. Ya salwantar da rayuwar mahaifiyarsa akan cikan burinsa, sannan ya salwantar da rayuwar mahaifiyata akan burinsa. Tabbas idan ban nisance shi ba, wataran rayuwata zai salwantar.
"YARIMA INA FATAN WANNAN ABU DA NAYI MAKA ZAI SA KA MANTA GIMBIYA JAANU, MATSAYIN DA KAKE NEMA A WAJENTA KA BANI WANNAN MATSAYI. NA RANTSE DA GIRMAN MAHAIFIYATA ZAN KULA DA KAI FIYE DA YADDA ZAN KULA DA KAINA. ZAN ƘAUNACEKA KAMAR YADDA UWA TAKE ƘAUNAR ƊAN DA TA HAIFA. ZAN RAYU DA KAI, ZAN MUTU KOMAI WAHALA KOMAI ƘUNCI.
"Ka kula dani, kayi sani cewa na rabu da azzalumin mahaifina na dawo ɓangarenka. Ina fatan zaka yi maraba da ni a rayuwarka, zaka bani matsayi. Sannan ina fatan ba zaka bani kunƴa ba."
Wannan budurwa ta na zuwa nan a zancenta ta juyo ta kalli Marganu fuskarta sharkaf da hawaye. Ba wata ba ce illa GIMBIYA FIRZIYYA ƳAR SARKI KUFFURU.
Koda Marganu yaga cewa ƴar sarki Kuffuru ce sai zuciyarsa ta fara tafarfasa kamar zata ƙone. Baƙin cikin kisan gillar da aka yiwa mahaifinsa ya taso masa, yaji kamar ya tashi ya kamo gimbiya Firziyya ya ɗauki fansa akanta, amma sai zuciyarsa ta daka masa tsawa.
“Kai Marganu! Duk wacce zata rabu da rayuwar daula da jin daɗi irin wannan ba maƙiyarka ba ce.
“Wadda zata iya rabuwa da babban sarki kamar Kuffuru saboda kai, ba ƙaramar masoyiyarka ba ce.
“Wai shin ka manta ba don tazo ta ceceka ba, da yanzu kaima kana barzaƙu?
“Mene ne ribarka idan har ka kasheta? Biyu babu zaka yi; baka da masoyiya kuma baka da mai taimaka maka.
“Tabbas wannan gimbiya zata san sirrukan sarki Kuffuru da yawa, meye zai hana ka haɗa kai da ita, ku kawar da shi daga duniya?
“Idan har ka kawar da sarki Kuffuru, tabbas zaka zamo babban sarki a wannan daula mai mulkin birnin Kufa da birnin Hirtoliya.”
Koda Marganu yazo nan a zancen zucinsa saiya saƙƙo ya dubi gimbiya Firziyya ya ce.
"Zan yi maraba dake a rayuwata idan har za ki cika waɗannan sharuɗɗa guda uku; daga yau za ki manta da sarki Kuffuru a matsayin mahaifinki, za mu haɗa kai ni da ke muyi masa kyakkyawan shiri domin mu tarwatsa mulkinsa. Sannan tsakanina da ke babu cin amana, yaudara ko ƙarya, kowannenmu zai san sirrukan ɗan uwansa kuma zamu riƙe sirrin juna. Sannan bayan mun kawar da mahaifinki, mulkin birnin Kufa ƙarƙashin ikona zai dawo ba wai naki ba.
"Idan kin amince da waɗannan sharuɗɗa guda uku; INA SONKI INA ƘAUNARKI nima."
"Na amince!" inji gimbiya Firziyya. "Tabbas za ka ji daɗin haɗa kai dani domin cikar burinka, domin duk duniya babu wanda ya kaini sanin sirrukan mahaifina amma tunda ya nuna zai iya salwantar da rayukan masoyansa a kowanne lokaci, a shirye nake da na bayar da gudunmawa a kawar da shi."
Marganu ya bi gimbiya Firziyya da kallon mamaki kawai, bai taɓa tsammanin zata amince da waɗannan sharuɗɗa da wuri haka ba.
Tsoho Aydenlik ya dafa kafaɗar Marganu ya ce, "Babban jarumi, ina tayaka murnar samun masoyiyar kwarai mai son cikan burinka. Kafun mu fara shirye-shiryen komai akan aikin dake gaban mu, ka je ka karanta wannan wasiƙa ta mahaifinka."
Yana gama faɗin haka ya fice daga cikin wannan fada, gimbiya Firziyya tazo ta sumbaci hannun Marganu itama ta fita daga cikin fadar, suka bar Marganu shi kaɗai zaune yana ta tunani.
***
******RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 47: *Wasiyyar sarki Ratanam*

*
UMAR SANGARU
*
Tsahon sa'a guda da rabi tsoho Aydenlik da gimbiya Firziyya suka baiwa Marganu a cikin wannan fada domin ya samu damar karanta wannan wasiƙa cikin nutsuwa. Sa'a guda da rabin na cika suka koma cikin wannan fada inda suka iske Marganu a zaune, fuskarsa har gatsinewa take saboda tsananin fusata.
Yana ganin sun shigo ya dube su ya ce, "Ku zo mu tafi wajen aljani Isika saboda aikin dake gabana ba na wasa bane." Tsoho Aydenlik ya dafa kafaɗarsa ya ce, "Kwantar da hankalinka babban jarumi, kada kayi gaggawar yanke hukunci. Bamu labarin wasiyyar da mahaifinka ya bar maka domin mu baka shawarwarin da suka dace. Ka san baka da abokan shawarar da suka fimu."
Marganu ya gyaɗa kai sannan ya fara basu labarin abinda ya karanta a cikin wannan wasiƙa. "Mahaifina ya gargaɗe ni akan kada na kuskura na ce zan koma birnin Hirtoliya na hau gadon mulkin da ya bari, ba tare da nayi kyakkyawan shiri ba. Saboda idan nayi hakan sarki Ayubu da sarki Kuffuru zasu iya haɗa kai su hamɓarar da mulkina.
"Mahaifina ya shaida min cewa akwai hannun sarki Ayubu dumu-dumu a cikin wannan farmaki da sarki Kuffuru ya kai birnin mu har ya kashe shi. Saboda haka ya ce, bayan na gama da sarki Kuffuru abokin gabata na gaba sarki Ayubu ne.
"Mahaifina ya bani labarin irin wulaƙancin da sarki Ayubu da ƴarsa gimbiya Jaanu suka yi masa a lokacin da yaje tattaunawa akan maganata. Sannan ya ce min kafun na fara shiri akan ɗaukar fansa akan sarki Kuffuru yana da kyau nasan sirrukansa domin hakan zai taimaka min.
"A ƙarshe ya bayyana cewa abinda yasa baiyi amfani aljaninsa a wannan yaƙi ba shi ne ya riga ya sadaukar da wannan aljani a gareni. Don haka zuwa wajen aljani Isika shi ne abinda zamu fara yi na farko.
"Aljani Isika shi ne zai bayyana abubuwan da zamu nemo wajen kawar da sarki Kuffuru. Idan muka je wajensa gimbiya kece zaki zayyane masa dukkanin sirrukan azzalumin mahaifinki. Idan kika yi hakan zan baki matsayi a cikin zuciyata wanda na tanadarwa gimbiya Jaanu." ya ƙarasa maganarsa yana kallon Firziyya.
Wasu hawayen taƙaici suka zubowa gimbiya Firziyya. "Masoyina kada ka ji shakkun komai a kaina. Mu tafi wajen wannan aljani domin a fara wannan aiki. Tunda mahaifina ya hallaka mahaifiyata bani da burin da yafi ace shima rayuwarsa ta durƙushe." ta ce.
Marganu ya jinjina kai. Lallai a wannan lokaci zuciyarsa ta soma yarda ɗari bisa ɗari da gimbiya Firziyya. Ba tare da ɓata wani lokaci ba, Marganu ya baiwa tsoho Aydenlik umarnin kai su wajen aljani Isika.
Aydenlik ya doki iska da hannunsa, nan take su ukun suka rikiɗe suka zamo haske, hasken ya cilla cikin gajimare. Ba su sauƙa a ko'ina ba sai a tsakiyar wani ƙaton daji mai yawan kogunan duwatsu barkatai babu adadi.
Aydenlik ya riƙe hannun Marganu shi kuma Marganu ya riƙe hannun gimbiya Firziyya, nan take suka sake zamowa haske. Hasken ya ratsa ƙasa ya shige cikinta.
A tsakiyar wani ƙaton kogon dutse suka tsinci kansu wanda komai nasa na haske ne; bangwaye, duwatsu, tsirrai da komai dake cikinsa. A can ƙarshen kogon suka hango wata shirgegiyar halitta zaune akan karaga ta mulki.

Please Login or Register in order to submit comment