Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

komai sarkin ya ƙirƙiri aljanun dake tsaron dajin ba sai domin su hana mutane da aljanu wucewa ta cikinsa, saboda a ƙarshen dajin mutum zai yi arba da mararrabar hanƴoƴi guda uku. Ɗaya ta nufi kudu, ɗayar kuma ta nufi arewa. Wacce mutum ke kanta kuma ita ce ta ɓullo daga gabas, a bakin kowacce hanƴa an kafe allon ƙarfe wanda aka yiwa rubutu akai. Hanƴar arewa ita ce zata sada mutum da dajin Shiwazu kuma anan ne mutum zai gwabza yaƙi da fararen aljanu masu zuƙar jini, ita kuma hanƴar da tayi kudu zata sada mutum ne da wani kogon dutse dake ƙarƙashin ƙasa, yi maka bayanin wannan hanƴa bata da wani amfani. Bari mu dawo kan hanƴar arewa. Ita dai wannan hanƴa ta arewa idan mutun ya fara tafiya akanta sai ya shafe tsahon sa'a bakwai cur yana tafiya, sannan zai isa ƙarshen dajin. Kana fara tafiya akan hanƴar fararen aljanu masu zungureren baki zasu fara kawo maka hari, kada ka kuskura wannan baki nasu ya samu nasarar huda jikinka. Idan kuwa ka yi ganganci har suka huda jikinka to tabbas zasu zuƙe jinin jikinka a cikin abinda bai wuce daƙiƙu biyu ba jal. Wannan shi ne taƙaitaccen bayani akan haɗarin dajin Djinn da yadda zaka tsallake sharrinsa.
"Shi kuma dajin Shiwazu asalinsa wani tafkeken teku ne, waɗansu ayari na gungun baƙaƙen aljanu suka zo suka gwabza yaƙi a cikinsa. Daga nan tekun tayi ambaliya, ta haifar da manƴa-manƴan koguna da ƙoramu. Saboda tsananin jin haushin rundunarsa basuyi nasara ba, yasa boka Balwaz yin wani sihiri wanda ya haifar da samuwar manƴa-manƴan kadoji da muggan halittun ruwa. Tabbas halittun dake cikin wannan koguna sihirtattu ne, sara da suka baya tasiri akansu babu yadda za'a yi kayi nasara akansu face tsananin sa'a da rabo. Saboda haka dole sai ka jajirce wajen saran kowanne ɓangare na jikin waɗannan halittu domin ka gano lagonsu. Da zarar ka ƙarar da halittun nan zaka isa tsaunin da yafi kowanne tsauni haɗari a duniya.
"Shi dai wannan tsauni a wasu littattafan tarihi an kira shi da suna tsaunin Barzasa. Barzasa sunan gunkin da arnan saman tsaunin ke bautawa ne. Waɗannan arnan daji sun shafe fiye da shekaru ɗari biyu da arba'in akan wannan tsauni, tun da suka wanzu ba'a taɓa samun mahaluƙi da ya ratsa ta cikin birnin nasu kuma ya fice a raye. Zaratan jarumai ne kuma sadaukai ne masu tsananin hikima da basira, komai shu'umancin jarumi da zarar ya tunkari wannan birnin Barzasa muggan tarkuna zasu cafke shi. Da zarar tarkunan nan sun kama shi, sai arnan dajin su fito su ɗaɗɗaure shi suje su yankawa gunkinsu jinin. Hanƴa ɗaya da ake tunanin mutum zai iya kubcewa waɗannan muggan tarkuna shi ne ya kasance yasan sirrukan daji matuƙa kuma ya laƙanci jin sautin komai ƙanƙantarsa. Idan ka fahimci zancena yanzu sai muje kurkuku na baka fursunan ka tafi."
Koda yarima Marganu ya gama jin jawaban sarki Kuffuru sai ƙirjinsa ya buga da ƙarfi don ya tabbatar da cewa aikin dake gabansa ba na wasa bane dole sai ya zage dantse, nan take jikinsa yayi sanƴi ya fidda rai ga samun nasara don gani yake bai isa ya iya shallake sharrukan dake cikin waɗannan dazuzzuka ba, bare har ya sami nasara a tsaunin Barzasa. Kwatsam sai gimbiya Jaanu ta faɗo masa a rai, ya tuna tsantsar kyawunta, nan take yaji wani sabon ƙarfi ya shige shi. "Muje kurkukun!" Inji yarima Marganu.
Sarki Kuffuru da gimbiya Firziyya suka kalli junansu suka yi murmushi, sannan gimbiya Firziyya ta taso tazo har gaban Marganu ta dafa kafaɗarsa da hannunta guda ta ce, "Tun da nake a duniya bayan mahaifina, ban taɓa ganin mutum mai dakakkiyar zuciya kamar ka ba. Kayi sani cewa ka haura jarrabawa mai tsananin wahala wacce duk wanda ya haurata zai sami kusanci sosai a wajen mahaifina, wanda kuma ya faɗi hukuncinsa kodai a kashe shi ko kuma a kaishi kurkukun mutuwa. Tabbas na jinjina bisa wannan dakewar zuciya taka, kuma ina yi maka fatan samun nasara a wannan tafiya da zaka yi." Yarima Marganu ya yi murmushi ya ce, "Na gode, amma ban gane wacce jarrabawa ce wacce kika ce na haura ba?" Gimbiya Firziyya tayi murmushi sannan ta juya da baya ta ce, "Kayi tunani zaka gane." Ta koma inda sarki Kuffuru ke zaune. Yarima Marganu bai jima yana tunani ba ya gano abinda take nufi wato rashin biya mata buƙata da yayi jiya da dare shine jarrabawar.
Sarki Kuffuru ya tafa hannayensa, wani ƙaton aljani ya bayyana ya ɗauke su su uku suka nufi kurkukun mutuwa. Yarima Marganu na zaune bisa wannan aljani yana mamakin yadda ake cewa wannan sarki ya kasance azzalumi, kuma sadauki shidai bai ga alamun zalunci a tattare da sarkin ba amma yaga alamun sadaukantaka kam, saboda tunda yake bai taɓa jin labarin mutum mai murɗaɗɗen jiki da tarin ƙwanji kamar Kuffuru ba. Yarima Marganu ya lura da cewa gimbiya Firziyya na satar kallonsa, da zarar ya ɗago kai sun haɗa idanu sai ta sunkuyar da kanta. Lamarin da ya bashi mamaki da tsoro kenan, domin bai ga abinda kyakkyawar ƴar sarki kamar wannan zatayi da shi ba kuma ko ba komai ai ta girme shi. Abinda ya manta shi ne SO babu ruwansa da kyawu, shekaru ko matsayi.
Bayan tafiyar sa'a biyu cif wannan ƙaton aljani ya dira a cikin wani gabjejen daji mai yawan sahara. Dirarsu keda wuya ƙura ta turnuƙe sararin samaniya baka ganin komai, jim kaɗan kuma sai komai ya lafa. Yarima Marganu ya hango wani ƙaton gini a can nesa kaɗan daga inda suke. Gini ne wanda aka yi shi da zallar duwatsun wuta masu taurin gaske, kuma ginin yana da tsaho sosai tamkar hasumiya. Yarima Marganu ya hango waɗansu zabga-zabgan mutane masu kama da mutanen farko suna ta kaiwa da komowa ta kowacce ƙusurwa dake cikin dajin, tun da uwar yarima Marganu ta haife shi bai taɓa jin labarin mutane manƴa masu ƙirar ƙarfi kamar waɗannan dakaru ba. "Tabbas yanzu na gane dalilin da yasa su Aymanul Faris basu yi gangancin tunkarar wannan kurkuku ba." Marganu ya faɗa a cikin ransa. Bayan tafiya ta kimanin taku ɗari biyu sai suka iso baƙin ƙofar wannan kurkuku wacce aka yi ta da zallar mulmulallen baƙin ƙarfe mai ƙaurin gaske, ko giwa bata isa ta karya wannan ƙofa saboda kaurinta. Waɗansu dakaru guda bakwai masu kama da ɗan aiken mutuwa suka risina a gaban sarki Kuffuru suka ce, "Me kake da buƙata ya shugabanmu?" Sarki Kuffuru ya kallesu ya ce, "Ku buɗe min wannan ƙofa ina so naje na ɗauko wannan fursuna ƴar ƙabilar Banu Kuyuru, fatan dai tana lafiya?" Wani murjeje daga cikinsu mai jajayen idanu ya ce, "Ya shugabana, akwai fursunan da ya taɓa shiga cikin wannan kurkuku ya zauna lafiya?" Sarki Kuffuru ya harare shi ya ce, "To ai sai ka buɗe min kofa koh?" Barden ya yi dariya sannan ya dakawa waɗansu bayi guda arba'in da ke gefe guda tsawa, ya ce su buɗe. Take waɗansu ƙarti majiya ƙarfi guda arba'in suka miƙe tsaye suka fara waina wani ƙaton ƙarfe, dukkaninsu a toɓe suke babu wanda ke sanƴe da riga. Lamarin da yasa ƙwanjin su suka kukkumbura kenan jijiyoyin jikinsu suka mimmike, kai da gani kasan cewa wahala suke sha wajen buɗe wannan kurkuku. Sai bayan shuɗewar daƙiƙa ɗari da tamanin sannan ƙofar ta gama buɗewa, yarima Marganu ya hango ɗakunan fursunoni a jere reras amma babu ko fursuna ɗaya a cikinsu.
***RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 8: *Kurkukun Mutuwa (2)*
*

*
✍️✍️✍️ Umar Sangaru ✍️✍️✍️
Sarki Kuffuru ya wuce kai tsaye izuwa cikin kurkukun, gimbiya Firziyya da yarima Marganu suka take masa baya. "Wai shin ina aljani Gulzab ya shiga ne, tun sa'adda aka kaini masauƙi ban sake kallonsa ba." Yarima Marganu ya tambayi gimbiya Firziyya ƙasa-ƙasa don kada sarki Kuffuru yaji. Gimbiya Firziyya ta yiwa yarima Marganu murmushi mai rikita ƙwaƙwalwar dukkanin wani cikakken namiji, amma taga ko gezau Marganu baiyi ba. Ta ce a ranta, "Anƴa wannan cikakken namiji ne kuwa?" Marganu ya ce, "Ya kika yi shuru?" Caraf sai ta ce, "Abbana ne ya tsare shi, sai sa'adda zamuyi bankwana da kai zai fiddo shi." Tana gama rufe bakinta suka iso cikin wani ƙaton fili, inda yarima Marganu ya yi arba da mutane birjik suna ta aiki. Babu batun mutum babba ne ko yaro, balle kuma batun mace ko namiji kowa ka gani a wurin aiki yake. Irin waɗannan murza-murzan dakaru dake tsaron bakin ƙofa na tsaitsaye cikin fursunonin, riƙe da bulali waɗanda aka ƙera da sirarun ƙarafu. Duk kuskuren da yasa fursuna ya daina aiki sai kaga waɗannan dakaru sun rufe shi da duka da waɗannan bulali dake hannunsu, bulalar tana taɓa bayan fursuna sai kaga wurin ya tsage, jini ya fara tsiyaya. Gaba ɗaya fursunonin bayansu yayi kaca-kaca da bulali, in banda kuka da ihu babu abinda suke. Sai dai kaga dattijo ko ƙaramin yaro na kuka yana ci gaba da aiki. Idan kuwa ajali ya taho sai kaga mutum ya mutu a wurin, amma babu wanda ya isa ya binne shi har ya gama ruɓewa ya zama ƙasa. Tabbas wannan kurkuku ta ci sunanta kurkukun mutuwa, saboda duk fursunan dake cikin wannan kurkuku zaka ga ya koma baƙi saboda wahala da dukan da yake sha. Waɗannan dakaru basu da imani ko kaɗan, da zarar sun ga fursuna ya gaji ya daina aiki ko kuma sun doke shi raɗaɗi ya hana shi aiki, sai su kafafunsu su ɗinga tamola da shi har sai ya dagargaje saboda wannan dalilin ne yasa babu fursunan dake gangancin daina wannan aiki. Aikin da suke ba na komai face, saran itace, yiwa makaman yaƙi kuɗa da sauran ayyukan wahala.
A rayuwar yarima Marganu bai taɓa tausayawa wani ba, hasalima ko kaɗan ba shi da tausayi amma da yaga yadda waɗannan fursunoni keta aikin wahala ba ji ba gani, sai yaji kwalla ta cika masa idanu. Ya ƙaryata kansa game da cewa baiga alamun zalunci a wurin sarki Kuffuru ba. Ba tare da ɓata lokaci ba suka wuce wannan fili, suka nufi wani ƙaton ɗaki mai raga-ragan ƙarfe. Kafun mutum ya isa bakin ƙofar ɗakin sai ya wuce ta cikin wani ƙaton keji wanda aka ajiye waɗansu ƙosassun zakuna guda bakwai a cikinsa, koda masu gadin suka ga sarki da kansa sai aka shaƙawa zakunan nan hodar banju suka fara barci. Sarki Kuffuru, gimbiya Firziyya da yarima Marganu suka shige cikin kejin sannan suka fice, suka iso bakin wannan ƙofa.
Tangamemen ɗaki ne wanda babu haske sosai a cikinsa, wanda ke cikin ɗakin zai na hango na waje amma wanda ke waje ba zai hango na ciki ba. Sarki Kuffuru ya yi murmushi ya ce, "Wannan ɗakin shi ake kira ɗakin duhu, ba ma tsare mutane a cikinsa sai mutanen sun kasance masu haɗari ko kuma muna tunanin za'a iya kawo musu ɗauki don a kuɓutar dasu." Gimbiya Firziyya ta yi murmushi ta ce, "Shin akwai wanda ya taɓa guduwa daga cikin wannan kurkuku ko kuma aka kuɓutar da wani?" Sarki Kuffuru ya amsa, "A'a tunda mahaifina ya gina wannan kurkuku ba'a taɓa samun mahaluƙin da ya taɓa tserewa ba, amma an sha kawo mana farmaki domin a kuɓutar da wasu. Sai dai ko sau ɗaya ba'a taɓa kuɓutar da waninl ba, waɗanda ke kawo farmakin ma suma kama su muke, mu tsare su. Akwai ɗakin da aka gina a cikin ƙarƙashin ƙasa, nan nake so na tsare shugaban barayin duniya idan na kama shi." Sarki Kuffuru na gama rufe bakinsa, wani ƙaton mutum ya fito daga cikin wannan ɗaki. Shi dai wannan mutumin yafi dukkanin dakarun dake tsaron wannan kurkuku tsaho, girma da kauri. Idonsa guda ya tsiyaye, fuskarsa kullum a murtuke take, ya shafeta da baƙin shuni. Kallo ɗaya ake yiwa wannan mutumi a tsorata, saboda ko kaɗan bai yi kama da masu alamun imani ba.
"Ya shugabana me yake tafe da kai?" Inji mutumin cikin wata murya mai kama da ana hura ziga-zigi a maƙera. Sarki Kuffuru ya kalle shi cikin jinjina ya ce, "Ya kai Bandaru ajiyata, nazo ɗauka." Sadauki Bandaru yayi wani murmushi wanda ya ƙara nuna tsantsar rashin imaninsa ya ce, "Ya zaka zo mana da sabon abu, ka taɓa ganin an shigo da tsinannen jinin Samudul Ansari cikin wannan kurkuku ya fita a raye?" Sarki Kuffuru ya haɗe gira sannan ya ɗora hannunsa akan takobinsa ya fara shafata ya ce, "Umarnina za'a bi a wannan kurkuku ko naka?" Koda sadauki Bandaru yaga haka sai ya murtuƙe fuska sannan ya buɗe ƙofa, sarki Kuffuru da su Marganu suka shige cikin ɗakin. A zuciyar Marganu yana mamakin yadda basamuden ƙato kamar Bandaru ke tsoron sarki Kuffuru, lamarin da yasa ya daɗa sallamawa sarki Kuffuru kenan.
A cikin wannan ɗaki babu komai face waɗansu manƴa-manƴan akwatuna guda uku a jere, sadauki Bandaru ya buɗe ɗaya daga cikinsu ya ɗauko wani abu mai kama da almakashi amma yafi almakashi kaifi nesa ba kusa ba. Ya ruga inda aka ɗaure wani mutum akan wata kujera yasa wannan almakashi ya datse babban yatsan mutumin, da yake fuskar mutumin a rufe take su yarima Marganu basu gane waye bane amma da yayi ƙara sai suka ji muryar mace. Jini yayi feshi daga dungulmin ɗan yatsan, Bandaru ya bushe da mahaukaciyar dariya ya ce, "Ba zan bari ku tafi da ita, ba tare da nayi mata mummunan illa ba wanda bazata taɓa mantawa da ta shigo wannan kurkuku ba." Yana gama faɗin haka yasa hannunsa ya cire baƙin ƙyallen da aka rufewa matar nan fuska da shi. Nan take fuskarta ta bayyana, jini sai zuba daga hancinta da bakinta yake da alamu ta sha naushi a fuska sosai. Duk da cewa wannan mata ta kasance fara ƙal amma sai da ta fara komawa baƙa saboda tsabar wahala, idanuwanta sai gudun ƙwalla suke wanda har alama suka yi na zuba akan kumantunta. Sadauki Bandaru ya sake gabza mata naushi a fuska, saboda ƙarfin naushin sai da kanta ya kalli sama jini yayi tsartuwa daga bakinta. Har ya sake yunƙura zai ƙara gabza mata wani naushin, amma sai yaji an riƙo hannunsa ta baya. Yayi yayi ya kwace amma ya kasa. "Au ƙoƙarin kwacewa ma kake, bari ka gani." Bandaru yaji muryar Kuffuru daga bayansa. Kuffuru ya riƙe hannun da kyau sannan ya murɗeshi da ƙarfin tsiya, lamarin da yasa Bandaru yayi ƙara kenan kuma ya durƙushe bisa gwiwowinsa. Sarki Kuffuru yazo daidai kunnensa ya yi masa raɗa, "Wannan kurkukun mallakina ce, ikona kaɗai ke aiki a cikinta kayi taka tsantsan." Yana gama faɗin haka ya sake hannun Bandaru sannan yaje ya kwance mahaifiyar Aymanul Faris dake ɗaure.
"Anƴa wannan zata sake moruwa kuwa, azabar da aka yi mata tayi yawa." Yarima Marganu ya tambayi gimbiya Firziyya. Murmushin mugunta gimbiya Firziyya tayi ta ce, "Ai wannan azabar da aka yi mata mai sauƙi ce, da ace kaga yadda aka kashe Kusuful Jalwar in akwai tausayi a cikin ranka daidai da kwayar zarra sai kayi kuka. Shiyasa da zarar abbana ya samu nasarar kamo ƴaƴan Samudul Ansari kafin a kawosu wannan kurkuku suke kashe kansu saboda tsananin tsoron azabar da za'a musu." Yarima Marganu yayi shuru yana jinjina maganar gimbiya Firziyya a ransa, wai shin wacce irin gaba ce wannar wadda bata ƙarewa ace tun iyaye da kakanni amma har yanzu bata ƙare ba, ya tambayi kansa.
Sarki Kuffuru ya ɗauko Hajriya akan kafaɗarsa tamkar wanda ya ɗauko tsumma saboda yadda ta rame. Koda yazo wucewa daidai inda sadauki Bandaru ke tsaye sai ya dube shi, ya ce, "Yi haƙuri Bandaru wannan fursuna daka ga na ɗauka, ƙarin wasu zata kawo ma. Ka jira kawai." Sadauki Bandaru yayi ƙwafa ya ce, "Da fatan dai ba za ku jima ba, kafin ku kawo min ƙarin wasu. Kuma idan so samu ne akawo min harda mazaje, jarumai domin naji daɗin karya gadon bayansu suna ihu." Sarki Kuffuru ya yi murmushi sannan ya fice, gimbiya Firziyya ta bi bayansa koda yarima Marganu yazo wucewa ta gaban Bandaru sai da suka yi kallon kallo sannan ya sunkuyar da kansa ya wuce.
Ba tare da ɓata lokaci ba suka fito daga cikin gidan kurkukun, masu gadi suka mayar da ƙofa suka rufe. Wannan ƙaton aljani ya sake ɗaukarsu ya nufi birnin Kufa dasu, sarki Kuffuru ya jefar da Hajriya gefe guda kan wannan aljani a wulakance, babu wanda ya sake ko kallonta har suka iso birnin Kufa.
Hajriya sai da ta gwammace da ma tun a birnin Damashkar aka fille kanta da ya fiye mata alheri akan azabobin da ta sha a kurkukun mutuwa a hannun sadauki Bandaru, har a wannan lokaci jini na ɗiga kaɗan-kaɗan daga dungulmin ɗan yatsan nata. Hajriya ta ƙudurce a ranta, idan akwai abinda zata buƙata a wajen ɗanta bai wuce tasa ya fille kan duk wanda keda sa hannu wajen kawota wannan kurkuku ba.
Bayan sake wata tafiyar sa'a biyu, wannan ƙaton aljani ya dira a tsakiyar fadar sarki Kuffuru. Aljanin yayi sallama da sarki ya ɓace ɓat. Kuffuru ya dubi yarima Marganu ya ce, "Kaga kurkukuna kaga azabobin cikinta, kayi taka tsantsan da aikin da zaka min." Yana gama faɗin haka ya dubi inda Hajriya ke kwance a wulakance ya ce, "Sai ka ɗauki wannan banzar, ka ɓace min da gani." Sarkin ya kama hannun gimbiya Firziyya suka nufi ƙuryar gidan sarautar. "Ina abokin tafiyata yake?" Inji yarima Marganu cikin kakkausar murya. Cikin tsananin mamaki sarki Kuffuru da ƴarsa Firziyya suka yiwa yarima Marganu kallo mai cike da ma'ana. Kuffuru ya ce, "Ka je bayan gari ta ɓangaren yamma zaka same shi, sai ku kama hanƴa. Ka san yadda zakayi kayi jiƴƴar wannar banzar idan ba haka ba kuwa mutuwa zatayi kafun ku isa dajin Marsas, sannan kada ka manta da sharaɗina." Yana gama faɗin haka ya fizgi hannun gimbiya Firziyya suka shige cikin gidan.
Ran yarima Marganu a ɓace yaje ya ɗauki Hajriya ya goyata a bayansa, sannan ya kama hanƴar fita daga cikin gidan sarautar. Wani badakare ya rugo a guje ya kawo masa doki, yarima ya karɓi dokin. Ya hau sannan ya sukwane shi ya nufi bayan gari. Bayan tafiyar rabin sa'a ya iso cikin wani ƙaton daji inda yayi arba da aljani Gulzab, gindin wata bishiya yana hutawa.
A wannan lokaci ne yarima Marganu yaji Hajriya ta daina motsi, cikin tsananin firgici ya sunce ɗaurin da yayi mata sannan ya kwantar da ita akan rairayin dajin. Cikin hanzari ya fiddo magani daga cikin jakar guzurinsa ya bata tasha, sannan ya shafa mata akan raunikan dake jikinta. Yarima Marganu ya dubi aljani Gulzab ya ce, "Buƙatarmu a birnin nan ta biya, don haka zo ka ɗaukeni mu tafi dajin Djinn." Aljani Gulzab ya yiwa yarima Marganu kallon jinjina ya ce, "Na gaisheka jarumi, zo mu tafi amma ka tuna cewa ba zan isa har cikin dajin Djinn da kai ba. A nesa kaɗan da dajin, zan ajiyeka idan ka tarwatsa rundunar fararen aljanun nan sai ka dawo na sake ɗaukarka mu wuce izuwa dajin Shiwazu. Daga nan sai mu dangana da tsaunin arnan daji."
Aljani Gulzab na gama faɗin haka ya ranƙwafa, yarima Marganu ya hau bayansa tare da Hajriya. Cikin tsananin taƙama da ƙarfi aljani Gulzab ya buɗe fuka-fukinsa ya tashi sama ya lulluka cikin gajimare, ya fara tsala uban gudu na gaban kwatance.
****Ruhin Jarumtaka!
*
Babi na 9: *Shiga dajin Djinn (1)*
*
*
✍️✍️ Umar Sangaru ✍️✍️
*
Aymanul Faris da mai gida Barban basu bar birnin Darul Barban ba, sai can da yammaci. Aljanun nan guda uku suka sake bayyana suka ɗauke su, suka dawo dasu cikin kogon Razman. Kafin su iso tuni duhu ya soma, amma idan ka kalli cikin kogon sai ka ɗauka da tsakar rana ne, saboda tsananin hasken fitillun dake ci a cikinsa. Dirarsu keda wuya waɗansu kuyangi na aljanu suka kawo musu abinci da abin sha, suka kimtsa cikinsu. Nan take Aymanul Faris da mai gida Barban suka buɗe shafin hira, suka yi ta maganganu akan abinda zai faru bayan sun kuɓutar da mahaifiyar Aymanul Faris.
Kwatsam! Bazato sai suka ga aljani Ranganu ya diro cikin fadar, fuskarsa a murtuƙe tamkar bai taɓa dariya ba. Al'amarin da ya ɗugunzuma hankalin mai gida Barban da Aymanul Faris kenan domin basu taɓa ganin fuskar Ranganu a murtuƙe haka ba, Barban ya zube a gabansa cikin tsananin biyayya ya ce, "Ya shugabana, lafiya kazo mana a cikin wannan yanayin?" Koda jin wannan tambaya sai aljani Ranganu ya nuna Aymanul Faris da yatsansa guda ya ce, "Haƙiƙa ka bani kunƴa da idanuwanka suka rufe har ka fara son ƴar babban maƙiyinka, kayi sani cewa so ba hauka bane. A duniya idan akwai abinda zaka tsana, bai wuce ƴaƴan ƙabilar banu Huturu da ƙabilar Jenher ba, ba ka da maƙiyan da suka fi su. Eh, na san cewa saboda wannan yarinƴa ta ceci mahaifiyarka daga hukuncin kisa shiyasa ka fara sonta ko? To ka sani cewa da kasheta a kayi a wannan lokaci, da ya fiye mata sauƙi akan kurkukun da aka kaita. Ina son kayi duba izuwa ga wancan allon tsafi domin ganin halin da mahaifiyarka take ciki." Aljani Ranganu na zuwa nan a zancensa ya nuna wani ƙaton allon tsafi dake kafe a tsakiyar fadar.
Nan take hoton yarima Marganu da aljani Gulzab ya bayyana a sararin samaniya suna ta tsala uban gudu, a gefe guda kuma Aymanul Faris yayi arba da wata mace kwance idanuwanta a rufe. Duk da cewa kamanninta sun sauya sosai kuma ta rame matuƙa sai da Aymanul Faris ya gane cewa mahaifiyarsa ce, har a wannan lokaci raunikan jikinta na zubar da jini amma kaɗan-kaɗan kasancewar yarima Marganu ya saka mata magani. Jikin Aymanul Faris ya fara ƙyarma, zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata ƙone saboda tsananin fusata, idanuwansa suka kaɗa suka yi jawur. Aymanul Faris ya ji ya tsani kansa, saboda ya gagara ceton mahaifiyarsa daga wannan uƙuba da aka yi mata, baisan sa'adda ya kurma wani uban ihu ba wanda ya cika kogon dutsen gaba ɗaya. Aljani Ranganu ya matso kusa da shi ya ce, "Tayaya zaka so mutanen da basu da burin da yafi su shafe dukkanin wani mutum mai jinin Samudul Ansari, kakanku? Tayaya zaka so mutanen da basu da tausayi ko kaɗan, kalli irin wulaƙancin da suka yiwa mahaifiyarka ba tare da tayi musu laifin komai ba. Aƙalla sai tayi jiƴƴa ta tsahon shekaru biyu zuwa uku kafin ta samu cikakkiyar lafiyarta, kuma babban ɗan yatsan da aka cire mata, har abada tabonsa ba zai goge ba. Wanne hali kake tsammanin mahaifiyarka zata tsinci kanta, idan ta ji labarin kana son ƴar sarakunan da suka sa aka yi mata wannan wulaƙancin?" Koda aljani Ranganu yazo nan a zancensa sai jikin Aymanul Faris yayi sanƴi yaji ya tsani dukkanin wani ɗan ƙabilar banu Huturu, a daidai wannan lokaci ne gimbiya Jaanu da jaruma Riya suka shigo cikin ɗakin a guje. Koda suka ga Aymanul Faris a fusace sai suka sha jinin jikinsu suka tabbatar da cewa lallai wani abu na faruwa. Jaruma Riya ta tako tazo har gabansa ta tsaya ta kama kafaɗunsa ta ce, "Ya kai ɗan uwana, shin menene yake faruwa na ganka a cikin wannan hali?" Aymanul Faris ya nuna mata abinda ke faruwa akan wannan allon tsafin, koda taga mahaifiyar Aymanul Faris bata shaidata ba. "Waɗannan kuma su waye? Waye wannan jarumin? Wace ce wacce ke kwance a gefensa cikin mawuyacin hali?" Jaruma Riya ta tambayi Aymanul Faris cikin murya mai nuna tausayi. "Wannan matar da kike kallo mahaifiyata ce..." Ya faɗa cikin sanƴin murya kamar baya son magana. Ita dai gimbiya Jaanu a gefe guda ta rakaɓe, jikinta sai tsuma yake

Please Login or Register in order to submit comment