Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

asirinsa ya tonu bisa wannan dalili ne ya fara tunanin me
ya kamata yayi. Marganu ya ƙarewa dakarun dake tsaron fadar kallo yaga basu wuce
mutum talatin ba, alhalin a jiya da dare sun kusa mutum dubu uku a wajen, koda ganin
haka sai yayi farin ciki. Ya lallaɓo ta bayansu yasa takobinsa ya fillewa biyar daga
cikinsu kai, jini yayi tsartuwa ya ɓata sauran. Koda suka ga sai suka yi kukan kura suka
afkawa yarima Marganu da yaƙi, nan fa suka garƙame da gumu aka yi ta ɗauki ba daɗi.
Da ƙyar da siɗin goshi yarima Marganu ya kashe goma daga cikinsu sauran kuma suka
gudu. Yarima Marganu ya tabbatar da cewa lallai zuwa zasu yi su kirawo sauran ƴan
uwansu domin su zo su yi masa taron dangi, nan take ya falfala da azababben gudu ya
taka wani mumbari dake gindin ginin fadar ya daka wawan tsalle ya fice. Ya fitowa daga
cikin gidan sarautar ya falfala da azababben gudu ya nufi hanƴar da zata kaishi bayan
gari.
A daidai wannan lokaci ne wannan sarauniya tare da dakaru dubu goma suka iso inda
wannan keji yake, koda sarauniya taga yadda Marganu ya karkashe dakarunta sai ranta
ya ɓaci. Ta dakawa sauran dakarunta tsawa ta ce, "Kada su bari Marganu yasha ruwa."
Nan take aka buɗe ƙofar gidan sarautar dakarun nan suka yi ta fitowa suna bazuwa
cikin gari, nan take aka fara busa wani ƙaho mai tsananin ƙara wanda ya cika birnin da
amsa kuwwa gaba ɗaya. Yarima Marganu na cikin gudu ya jiwo ƙarar busa wanna ƙaho
da kuma takun sawayen dawakai tamkar ƙasa zatayi girgiza ta haɗiye duk abinda ke
samanta. Da yake baisan garin ba sai ya kiɗime ya rasa ma ina zai fara tunkara, duk
hanƴar da ya kama sai yaga bata ɓullewa.
Kwatsam! Sai ya hango tahowar waɗansu dakaru kimanin su ɗari uku da ɗoriya bisa
dawakai sun nufo inda yake tsaye, kowannensu na riƙe da kaifaffen gatari ko mashi.
Marganu yaga ai ko ya juya da gudu bai isa ya tserewa waɗannan dakaru ba, don haka
kawai dakewa yayi a inda yake tsaye yana mai ƙara ƙanƙame takobinsa da kyau.
Dakarun nan na ƙarasowa da gudu suka kawowa yarima Marganu sara da ko'ina cikin
baƙin zafin nama ya daka tsalle ya fice daga tsakaninsu ya bangaje wasu suka faɗo
daga kan dawakan, kafin su miƙe ya fille musu kawuna. Koda sauran suka ga abinda ya
faru sai suka harzuƙa suka ƴanƴame yarima Marganu da sara da suka ta ko'ina shikuma
ya wanzu yana mai kare saransu gami da mayar da martani, haƙiƙa inda ace Marganu
bai kasance sadauki ba da tuni waɗannan dakaru zasu yi masa kisan farat ɗaya saboda
yawansu. Nan fa Marganu ya shiga zille-zille a tsakaninsu gami da yin tsalle-tsalle
kamar tsuntsu yana sarar jikinsu gami da kare kansa, a duk lokacin da ya sari jikinsu sai
wurin ya tsage jini yayi feshi amma dakarun basa faɗuwa ƙasa saboda tsananin
juriyarsu da nacinsu. Marganu ya fuskanci cewa indai ba fille musu kai yayi ba basa
mutuwa, sai ya daina saran ko'ina a jikinsu idan ba wuyansu ba. Koda dakarun suka
fuskanci haka sai suka daina yarda yana saransu a wuya, lamarin da ya sake
ɗugunzuma hankalin Marganu a karo na uku kenan.
Sauran dakarun da sarauniya ta tura farautar Marganu sai suka yi ta zuwa wannan wuri
wanda ake ta gumurzu tsakaninsa da ƴan uwansu, koda Marganu ya fuskanci dakarun
nan ƙaruwa suke ba raguwa suke ba, sai ransa ya ɓaci zuciyarsa ta kufulo. Ya yi tsalle
sama ya doki ƙirjin wani badakare, badakaren yayi sama yaje ya doki waɗanda ke
bayansa dukkansu suka rikito daga kan dawakansu, ƴan uwansu suka tattakesu ba tare
da sun sani ba. Marganu ya hau kan wannan doki sannan ya juyo ya fuskanci dakarun,
ya zaro wani lafcecen gatarin dake daure a jikin dokin ya haɗa makamai biyu a
hannunsa. Ya yiwa dokin nan ƙaimi ya shiga tsakiyar dakarun suka sake ruguntsumewa
da sabon yaƙi, a wannan karo sai yarima Marganu ya zame musu guguwar annoba ya
shiga fille musu kai da wannan zabgegen gatari dake hannunsa. Nan fa kasuwar rayuka
ta buɗe, jini yayi ta tsiri izuwa sararin samaniya, kayukan bil'adama suka yi ta yawo
tamkar ana ruwan ƙwallon giginƴa. Yarima Marganu yayi ta kashe waɗannan arnan daji
amma kamar ƙara su ake, al'amarin da ya bashi tsoro kenan domin a cikin sa'a ɗaya
yana iya kashe dakaru ɗari uku da wani abu. Koda aka shafe sa'a bakwai ana wannan
gumurzu sai Marganu ya fara gajiya, ya duba waɗannan dakaru yaga har yanzu ko rabi
bai ƙarar ba.
Wani garjejen ƙato daga cikin waɗannan arnan daji wanda ke tsaye a gefe guda, ya zaro
wani mashi dake ɗaure a gadon bayansa ya saita ƙirjin Marganu dashi da kyau, cikin
tsananin ƙarfi ya jeho wannan mashi. Marganu na ta ragargazar dakaru yaga saura ƙiris
wani mashi ya tsire shi bisa dole ya kwanta akan wannan doki cikin zafin nama da nuna
bajinta, kaifin mashin ya yanki ƙirjinsa sannan ya faɗi a gefe ɗaya. Nan take jini ya fara
tsatstsafowa daga cikin wannan rauni na ƙirjin nasa, Marganu ya juyo ya kalli inda
wannan garjejen ƙato ke tsaye ya sukwani dokinsa da gudu yaje inda ƙaton ke tsaye ya
kawo masa wawan sara a wuya, ƙaton ya sunkuya cikin ƙwarewa, gatarin Marganu ya
sari iska. Kafin Marganu ya juyo tuni wannan ƙaton ya daka tsalle ya rungumo shi daga
kan dokin sun faɗo kasa a tare, makaman hannun Marganu suka faɗi gefe guda. Ƙaton
nan ya hau kan ruwan cikin Marganu ya take hannayensa biyu da ƙafafunsa yayi ta
gabzawa Marganu naushi a fuska, da zarar ya naushi fuskar sai kaga ta dauje jini yayi
tsartuwa daga cikin bakinsa ko hancinsa. Tun da Marganu yazo duniya bai taɓa haɗuwa
da sadaukin mutum kamar wannan ƙato ba, kafin a jima ya yiwa Marganu dukan kawo-
wuƙa, amma dukda haka bai tashi daga kan Marganu ba sai da yaga ya daina motsi
alamun ya mutu. Ƙaton ya miƙe tsaye yai ihu ya doki ƙirjinsa da hannayensa, ya dakawa
dakarun nan tsawa da wani irin yare nasu na arnan daji. Ya fiddo wata ƴar ƙaramar
daga ƙugunsa ya sunkuya da nufin yiwa Marganu yankan rago sannan ya cire kansa, ya
kaiwa sarauniya domin shine umarnin da ta basu.
Ashe yarima Marganu ba mutuwa yayi ba, lamo ya yiwa wannan sadauki. Koda ya buɗe
idonsa kaɗan a hankali sai yaga sadaukin na sunkuyowa zai yanke kansa da wata
ƙaramar wuƙa, Marganu ya taƙarƙare ya tattaro ƙarfinsa gaba ɗaya a waje guda ya
gabzawa sadaukin nan naushi a haɓarsa. Saboda ƙarfin naushin sai da wannan sadauki
yayi baya taga-taga kamar zai faɗi amma sai ya turje cikin tsananin jarumta, ya dubi
Marganu cikin wani kallo mai nuna tsantsar mamakin yadda akayi Marganu ya rayu.
Sadaukin ya jefar da ƙaramar wuƙan nan ya ɗauki wani zabgegen gatari a ƙasa ya daka
wawan tsalle ya kawowa Marganu sara a wuya, da nufin ya tsinke masa kai. Cikin zafin
nama Marganu ya sunkuya ƙasa gatarin ya sari iska, kafin sadaukin ya juyo tuni Marganu
ya kamo hannunsa wanda ke riƙe da gatari ya murɗa da ƙarfi, ya lankwaso hannun ta
baya sannan yasa gwiwar ƙafarsa ya karya hannun da ƙarfin tsiya. Sadaukin nan ya
kwarara uban ihu wanda ya cika birnin gaba ɗaya, Marganu ya sake kamo ɗaya hannun
ma shima ya karya shi, sadaukin ya durkushe bisa gwiwowinsa a lokacin da hawayen
wahala keta shatata bisa kumatunsa.
Marganu ya zagayo ta bayan sadaukin ya kama kansa da hannu biyu, ya murɗe masa
wuya sannan ya doki ƙirjinsa gawar sadaukin ta tafi ƙasa a hankali. Marganu ya dubi
sauran dakarun arnan dajin ya kurma uban ihu ai kuwa sai duk suka tarwatse suka koma
cikin wannan birni nasu, shi kuma sai ya fara tafiya a hankali tamkar wanda yasha giya
ya bugu sakamakon dukan da ya sha a hannun sadauki. Marganu na cikin tafiya ya iso
bakin wani ƙaton gida mai dogon gini kamar husumiya, kai tsaye yaje bakin wannan
ƙofar gida ya buɗeta da ƙarfin tsiya sannan ya kunna kai izuwa cikin gidan. Yana fara
tafiya a cikin gidan ya fara jin ƙaurin jini na tashi, kuma ya ɗinga ganin ƙwarangol din
bil'adama zube ko ta ina birjik, hakan ne ya tabbatar masa da cewa wannan shi ne
gidan bauta inda gunki Barzasa yake.
Koda ya iso tsakiyar gidan sai yayi arba da wani ƙaton gunki, an kewaye gunkin da wasu
ƙoƙuna na jini. Yarima Marganu yaji tsikar jikinsa ta tashi saboda ganin yadda ake rashin
imani zalla, yaga an ajiye wani zabgegen gatari a gefen wani kasko da alamu dai da
wannan gatari ake sarewa mutane kai, idan za'a baiwa wannan gunki jininsu. Marganu
ya ce a ransa, "Lallai yau zan kawo ƙarshen wannan baƙar bauta ta waɗannan arnan
daji." Yana gama faɗin haka ya ɗauki wannan ƙaton gatari yayi kan wannan gunki gadan-
gadan, a lokacin ne sararin samaniya tayi baƙi aka yi ta kwararo tsawa da walƙiya.
Marganu na ƙarisawa gurin wannan gunki yasa gatarin nan ya fille masa kai, faruwar
hakan keda wuya aka yi wata tsawa wacce ta girgiza tsaunin gaba ɗaya tamkar zai
tarwatse.
Shi kansa yarima Marganu sai da ya razana, ya jefar da gatarin nan a gefe guda a
lokacin da hantar cikinsa ta kaɗa. Su kuma sauran al'ummar wannan gari durƙushewa
suka yi gaba ɗayansu akan gwiwowinsu suna tuba. Har Marganu ya yunƙura zai fita
daga cikin gidan bautar, kawai yaga wani mahayi ya shigo cikin gidan a guje bisa doki.
Mahayin na riƙe da waɗansu irin zabga-zabgan takubba guda biyu masu tsananin kaifi,
gaba ɗaya jikinsa a lulluɓe yake da baƙaƙen tufafi hatta fuskarsa kuwa. Mahayin ya
sauƙo daga kan dokinsa ya fidda hular data rufe masa fuska, wani kyakkyawan gashi
yarima Marganu ya gani ya tarwatse a cikin iska. Nan take fuskar sarauniyar arnan dajin
nan ta bayyana.
Budurwa ce kyakkyawa ta gaban kwatance, doguwa ce sosai sannan fatar jikinta fara ce
tas tamkar ta ƴan ƙabilar banu Kuyuru. Tana da fuska mai ɗauke da dara-daran idanu da
ɗan ƙaramin baki tamkar yankan wuƙa, shekarunta baza su wuce ashirin da ɗoriya ba. A
wannan lokaci fuskarta a murtuƙe sosai tamkar wacce aka aikowa da saƙon mutuwa.
Sarauniyar ta gyara riƙe takubbanta biyu ta dakawa Marganu tsawa ta fara magana da
cewa, "Ya kai wannan baƙo wane ne kai? Mene ne ya kawoka cikin wannan birni nawa
har kayi min wannan mummunar ɓarna?" Marganu ya yi murmushi mai nuna yarda da
kai ya ce, "Suna na Marganu, ba don komai nazo wannan birni naku ba sai domin babu
hanƴar da zan ratsa na wuce izuwa dajin Marsas face ta cikinsa amma maimakon ku
tarɓeni sai kuka kamani da ƙarfi ku kayi min dukan tsiya daƙyar na sha, bisa wannan
dalilin ne nayi muku wannan mummunar ɓarna domin na nuna muku cewa yau namiji ne
yazo!" Koda wannan sarauniya ta gama jin jawaban Marganu sai jikinta ya fara kakkarwa,
fuskarta ta fara gatsinewa ta dube shi ta ce, "Tabbas yau ka tsokano tsuliyar dodo,
kuma ka tsokanowa kanka masifa da bala'i mara iyaka. Ni sarauniya Rauziyya na ƙulla
aniyar yaƙi da kai daga yanzu kuma zaka fara fuskantar uƙubata." Koda sarauniya
Rauziyya tazo nan a jawabanta sai dako wani wawan tsalle ta kawowa yarima Marganu
sara da takubbanta guda biyu a tare, tazarar dake tsakaninsu akwai nisa sosai bai taɓa
tsammanin tsalle ɗaya kawai zata iso inda yake ba.
Cikin tsananin mamaki da zafin nama yarima Marganu ya yi tsalle gefe guda takubba
sarauniya Rauziyya suka sari iska, kafin ta juyo shima ya kawo mata sara da wannan
ƙaton gatari dake hannunsa, ba tare da ta juyo ta tale sawayenta gatarin ya sari iska.
Nan fa ta sake miƙewa tsaye suka kacame da sabon gumurzu wannan sarauniya ta
wanzu tana kawowa Marganu sara da suka cikin tsananin zafin nama, shi kuma yayi ta
karewa ba tare da ya samu damar mayar da martani ba.
Ko daƙiƙu ɗari biyu masu kyau ba'a shafe ana wannan gumurzu ba, yarima Marganu ya
raina kansa ya kuma raina jarumtarsa. Domin sarauniya Rauziyya ta fishi a komai, bugu
da ƙari ga shi yayi yaƙi har ya gaji ga dukan da ya sha a hannun wannan sadaukin. Nan
take hankalinsa yayi mugun tashi ya tabbatar da cewa lallai rayuwarsa na cikin haɗari,
ana cikin gumurzu sarauniya Rauziyya ta sami nasarar lafta wani wawan sara a gadon
bayansa saboda tsananin zogi da raɗaɗi Marganu baisan sa'adda ya yi jifa da wannan
gatari ba, ya kwarara wani wawan ihu. Kafin ya dawo hayyacinsa tuni tasa ƙafarta guda
ta doki cikinsa, wani irin sabon zogi yaji ya sake shiga cikin cikinsa tamkar ana
daddatsa masa kayan ciki, nan take ya durƙushe bisa gwiwowinsa yana mai riƙe cikinsa
da hannu guda, hannu ɗayan kuma sai ya dafe wannan rauni dake gadon bayansa.
Sarauniya Rauziyya ta bushe da mahaukaciyar dariya ta zagayo ta gefensa ta tsaya, tana
cewa, "Tabbas ba zan kasheka ta farat ɗaya ba, face nayi gutsin-gutsin da sassan
jikinka saboda laifin da ka aikata min. Ka sare kan gunki Barzasa wanda muke bautawa
tun zamanin kakana na farko. Bari yanzu na sassara ƙafafunka da hannayenka kamar
yadda ka kakkarya min sarkin yaƙina sadauki Jautaru." Tana gama faɗin haka ta ɗaga
takobinta guda ta kawowa hannun Marganu wanda ke gadon bayansa sara da nufi ta
tsinke hannun, tuni yarima Marganu ya gama saduda ya mutu. Saboda ƙarfinsa ya ƙare,
ba shi da wani sauran kuzari a jikinsa sakamakon jinin dake ta zuba a gadon bayansa.
Saura ƙiris takobin sarauniya Rauziyya ya tsinke hannun yarima Marganu, kwatsam! Ba
zato ba tsammani sai taga anyi wuf an ɗauke Marganu an tashi sama dashi. Koda ta
ɗaga kanta sama sai ta hango wani murgujejen aljani yana ta kaɗa fuka-fukinsa cikin
iska da gudu, wani irin hawayen baƙin ciki ya zubowa sarauniya Rauziyya ta jefi wannan
aljani da takobinta, a lokacin da tuni ya ɓace a cikin gajimare. Ta kwarara uban ihu ta
ɗaga murya da ƙarfi ta ce, "Na rantse da mai girma Barzasa, ba zan daina farautarka a
duk inda kake fadin duniya ba. Hankalina ba zai kwanta ba face na saro kanka nazo na
nunawa mai girma Barzasa. Ka ci gaba da saurarona a duk inda kake a faɗin duniya,
tabbas wataran sai na riskeka."
Duk da cewa yarima Marganu baya cikin hayyacinsa sosai amma ya jiwo wannan
ALWASHI NA SARAUNIYA RAUZIYYA. Cikin tsananin mamaki ya dubi aljanin da ya ceci
rayuwarsa ai kuwa sai yaga ashe aljani Gulzab ne, yarima Marganu yayi ajiyar zuciya ya
ce, "Kai wannan aljani wai nikam dame zan saka maka ne...?" Bai gama rufe bakinsa ba
ya kife akan aljani Gulzab saboda wani irin mugun jiri da ya ɗebe shi sakamakon raunin
dake gadon bayansa. Cikin hanzari aljani Gulzab ya dira a saman wani dutse, ya fiddo
zare da allura ya ɗinkewa yarima Marganu raunin dake gadon bayansa sannan ya shafe
shi da magani. Sannan ya bi duk kumburin dake jikin yarima Marganu ya shashshafa
masa magani, aljani Gulzab sai da ya tausaya yarima Marganu saboda yadda ya sha
wahala sosai a garin arnan daji. Gulzab yayi tsafi ruwan zafi ya bayyana a cikin wani
kasko ya dinga ɗanɗana da kaɗan-kaɗan yana shafawa yarima Marganu akan kumburin
jikinsa. Saboda tsananin wahalar wannan magani da aljani Gulzab yake yiwa Marganu
sai da ya suma sau uku, yana farfaɗowa. Aljani Gulzab ya ce, "Na jinjina maka ya kai
babban jarumi tabbas ka cika sadauki abin kwatance. Kuma ka kafa tarihi tunda kaine
bil'adama na farko da ya taɓa ratsawa ta cikin dajin Djinn da dajin Shiwazu da kuma
tsaunin Barzasa a raye kuma ka fito a raye." Yarima Marganu yayi murmushin ƙarfin hali
ya dubi mahaifiyar Aymanul Faris yaga ta kusa warkewa daga raunikanta. Ya sake
duban aljani Gulzab ya ce, "Tabbas na ƙetare waɗannan dazuzzuka amma bala'i da
masifun da na gani bana fatan sake ganinsu a rayuwata. Na ji wannan sarauniya tana ta
cika baki kamar a mafarki, shin da gaske ne?" Aljani Gulzab ya ce, "Kwarai ma kuwa."
Yarima Marganu yayi murmushi ya ce, "Kowanne lokaci tazo a shirye nake, kuma tayi
sa'a dazu a gajiye nake amma da sannu zan nuna mata wane ne yarima Marganu."
Aljani Gulzab ya yi murmushi ya ce, "Hakane. Yanzu saura tafiya wuni daya cur zamu
riski dajin Marsas inda sarkin ɓarayi na duniya yake, so nake koda sau ɗaya nayi arba da
wannan mutumi wanda ya gallabi duniya gaba ɗayanta." Yarima Marganu ya yi
murmushi ya ce, "Nima haka kuma ina son ganin wayene Aymanul Faris ɗinnan da
jaruma Riya waɗanda boka Ruguzan ya bani labarinsu." Aljani Gulzab ya ce, "To yanzu
me muke jira? Mu ƙarasa dajin Marsas kawai domin mu ga wannan ɗan-baiwa." Yarima
Marganu ya jinjina masa kai sannan ya ranƙwafa ya hau kansa, dama Hajriya kam ko
sauƙowa bata yi ba. Aljani Gulzab ya buɗe fuka-fukinsa ya tashi sama ya nufi dajin
Marsas inda sarkin ɓarayi, aljani Ranganu, Aymanul Faris, jaruma Riya da kuma gimbiya
Jaanu ke ɓoye.
****Ruhin Jarumtaka!
*
Babi na 13: *KILAWUD BARBAN*
*
*
Umar Sangaru
*
Duk wannan jarumtaka da yarima Marganu yayi a dajin Djinn, dajin Shiwazu da tsaunin
Barzasa maigida Barban, Aymanul Faris, jaruma Riya da gimbiya Jaanu suna kallo a
cikin wani ƙaton madubin tsafi. A cikinsu babu wanda ya kai Aymanul Faris farin ciki
saboda ganin cewa ya kusa ya sadu mahaifiyarsa, ita kuma gimbiya Jaanu sai ta ce a
ranta, "Lallai yarima Marganu ba shi da hankali, yanzu saboda ni ya sayar da rayuwarsa
har ma ya shiga cikin irin waɗannan masifu da bala'i? Tabbas yayi wahalar banza domin
nikam tuni Aymanul Faris ya gama mallakar zuciyata." Koda tazo nan a zancen zucinta
sai idanunta suka ciko da kwalla ta dubi inda Aymanul Faris ke zaune, ta tuno irin
wulaƙancin da yayi mata ɗazu, sunkuyar da kanta ƙasa kawai tayi bata yarda sun ga
hawayenta ba. Gimbiya Jaanu ta kamu da matsanancin ƙaunar Aymanul Faris kuma ita
kanta tasan cewa shima yana ƙaunarta amma babu damar suyi soyayya saboda
matsananciyar gabar dake tsakanin ƙabilunsu. Wai meyasa wannan gaba ba zata ƙare
ba? Ace gaba tun zamanin iyaye da kakanni amma har tazo kansu su da suke tasowa
yanzu? Hawaye ne kawai ya ci gaba da sartu akan kyawawan kumatun gimbiya Jaanu.
Duk wannan hali da ta shiga Aymanul Faris na gani, kuma har cikin ransa yana jin wani
iri, shi kansa ya tabbatar da cewa da gaske gimbiya Jaanu amma idan ya tuno da
kalaman aljani Ranganu sai yaji ta fita a ransa. "To ai wannar yarinƴa ce ƙarama, bata
da wani laifi. Da yake maganar da ma kashe mahafiyata maimakon a kaita wannan
kurkuku baisan azaba maficiya bace, yanzu a dalilin gimbiya Jaanu zan sake yin arba da
mahaifiyata kuma yana daga cikin wasiyyar da mahaifina ya barmin wato na kula
babata." Aymanul Faris ya ci gaba da zancen zuci yana mai satar kallon gimbiya Jaanu,
da zarar ta juyo zata kalle shi sai ya kawar da kansa. Tuni gimbiya Jaanu ta cika da
tsananin farin ciki a cikin ranta domin ta gama fuskantar Aymanul Faris yana ƙaunarta,
saboda yadda yake yawan kallonta.
Maigida Barban ne ya fara jawabi da cewa, "Ya kai jarumi uban jarumai, kayi sani cewa
gobe da sassafe yarima Marganu zai ƙaraso cikin wannan daji tare da mahaifiyarka.
Mun san abinda ke cikin zuciyar Marganu munsan umarnin da sarki Kuffuru don haka
gobe zamu nuna masa lallai bai isa ba, in banda wauta da rashin wayo ya za'ayi ya iya
kama ɓarawon da yafi shekaru goma yana sata ba tare da ya haɗu da ɓacin rana daidai
na daƙiƙa guda ba. Koda yake soyayya ce ta rufe masa idanu, kuma tabbas ya kama
turba mai baƙar wahala. Dubi fa ku gani duk wannar wahalar da ya sha akan kawai
gimbiya Jaanu ta amince da buƙatarsa ta aure shi, yanzu idan taƙi amincewa da
buƙatarsa ya ya zaiyi?" Maigida Barban ya dubi inda Aymanul Faris ke zaune yana so ya
nuna masa illar soyayya. Barban ya ci gaba da cewa, "Tabbas soyayya tushen wahala
ce, sai mai rabo ke tsallake haɗarurrukan dake cikinta. Shawarar da zan baku ita ce duk
abinda zaka so kada ka zurfafa sosai, kuma kada kuce zaku yiwa mutum dole a
soyayya.
"Ya kai Aymanul Faris da zarar mahaifiyarka ta dawo hannunmu, hankalinka ya kwanta.
Za muje birnin Askandariyya muyi wata babbar sata, wacce na yiwa tanadi tsahon
shekaru goma. Wannan sata tana buƙatar jarumi kamarka, sannan tana buƙatar mutum
mai hikima kamar ni ɗin nan, zan yi maka bayanin komai bayan-gobe da yammaci.
Tabbas ya zama dole a hukunta sarki Darwazu saboda tsananin zaluncinsa akan
talakawa, fiye da shekaru goma shima yana tsanantawa ƴan ƙasarsa haraji kuma yana
ƙwace amfani gonarsu. Kai dai zan yi maka cikakken bayani idan muka sami nutsuwa.
Kayi sani cewa ayyuka guda goma zamu yi tare da kai, sannan ka tafi neman ruhin
kakanka Samudul Ansari..." Maigida Barban yayi shuru yana kallon Aymanul Faris da
alamu akwai maganganu sosai a bakinsa amma baya so su jaruma Riya da gimbiya
Jaanu su san sirrukan aikinsa.
Haka dai suka ci gaba da hira a cikin wannan falo har dare ya raba sannan kowa yaje ya
kwanta, gimbiya Jaanu na kwance a cikin ɗakinta ita kaɗai sai juye-juye take ta gagara
barci tana ta tunanin abinda zai faru gobe. Idan ta tuna cewa daga gobe ta rabu da
Aymanul Faris sai hankalinta yayi mugun tashi saboda ko kaɗan bata so ta daina
kallonsa, tana cikin wannan hali na tunani taji an buɗe ƙofar ɗakin, cikin alamun tsoro ta
miƙe zaune. Koda taga wanda ya shigo cikin ɗakin sai ta cika da tsananin farin ciki, ba
wani bane illa Aymanul Faris.
Gimbiya Jaanu ta dube shi cikin murmushi mai nuna tsantsar so da ƙauna ta ce, "Ya kai
masoyina, abin begena tabbas nasan cewa kana sona kuma abinda kayi min ɗazu a
fada a gaban su aljani Ranganu kayi ne domin ka nuna musu cewa kana bin umarninsu
saboda yadda suka taimaka maka sosai wajen ƙwato mahaifiyarka, haka ne?" Aymanul
Faris ya zauna a gefen gadon yana ƙurawa fuskar gimbiya Jaanu idanu, ya ce, "Yake
wannan ƴar sarki nazo gareki ne domin mu tattauna maganganu masu muhimmanci.
Da farko ina mai neman yafiyarki bisa abinda nayi miki ɗazu da safe a fada, tabbas
raina ne ya ɓaci sakamakon ganin yadda aka wulaƙanta min mahaifiya amma koda na
nutsu nayi tunani sai na gano cewa ai baki da hannu a cikin wannan al'amari. Sarki
Kuffuru, sarki Ratanam da mahaifinki su ne keda hannu ɗari bisa ɗari a wannan hukunci
da aka yiwa mahaifiyata. Shin kin yafe min abinda nayi miki?" Gimbiya Jaanu ta matso
kusa da shi ta ce, "Na yafe maka laifin da ka min da wanda zaka min a gaba, ko kaɗan
raina bai ɓaci ba sakamakon wannan abu da ka min. Ina ƙaunarka. Ƙaunar da nake yi
ma ta wuce yadda kake tsammani, ina tabbatar maka da cewa koda zaka yi gutsin-
gutsin da jikina, ba zan daina sonka a cikin zuciyata ba. Don haka ka faɗi abinda ke tafe
da kai?" Aymanul aris yayi murmushi mai nuna jin daɗi a cikin ransa ya ce, "Wasu
tambayoyi nake so nayi miki...Shin kina ƙaunar yarima Marganu? Shin wanne hukunci
kika yanke a cikin zuciyarki dangane da makomar soyayyarmu? Idan har kina ƙaunata a
cikin ranki wanne mataki kike ganin ya kamata a ce mun ɗauka dangane da
soyayyarmu?" Koda gimbiya Jaanu taji waɗannan tambayoyi daga bakin Aymanul Faris
sai tayi murmushi ta ce.
"Amsar tambayarka ta farko ita ce, bana ƙaunar yarima Marganu. Na tsane shi saboda
shi ɗin azzalumi ne ko kaɗan ba shi da tausayi, na rantse da darajar soyayyar da nake yi
maka da na auri yarima Marganu gwara na mutu mushe a cikin daji tsuntsaye su
tsatstsageni. Hukuncin da na yanke a cikin zuciyata ita ce, ina ƙaunarka ɗari bisa ɗari
kuma da zarar na koma birninmu zan shaidawa mahaifina abinda ke cikin zuciyata. Nifa
idan ba dole ba da ba zan bar wannan daji ba saboda kai, bana son nayi nisa da kai.
Amsar tambayarka ta uku kuma dole ne sai mun sami lokaci ni da kai domin muyi
tunanin matakin da ya kamata mu ɗauka akan wannan soyayya tamu."
Koda Aymanul Faris ya gama jin jawaban gimbiya Jaanu sai ya cika da tsananin farin
ciki ya ce, "Madallah. Da masoyiya ta ƙwarai mai dumbin hikima da basira." Yana gama
faɗin haka ya rungumeta a ƙirjinsa, sai da suka jima a manne da juna sannan ya janƴe
jikinsa daga nata ya ce, "Tabbas zan yi kewar wannan kyakkyawar fuska taki mai cike da
tsantsar ƙauna a gareni, shin me zaki bani wanda zai ɗebe min kewarki?" Koda gimbiya
Jaanu taji wannan tambaya sai ta haɗe bakinta da bakin Aymanul Faris ta fara
sumbatarsa har tsahon ɗan lokaci sannan tazo daidai kunnensa tayi masa wata raɗa a
kunne, Aymanul Faris ya cika da tsananin farin ciki ya miƙe tsaye da nufin ficewa daga
cikin ɗakin. Gimbiya Jaanu ta sake kamo hannunsa ta sunkuyo da kansa ƙasa tayi masa
sumbata a kumatu sannan ta sake shi, ya fice daga cikin ɗakin cikin tsananin farin ciki.
Gimbiya Jaanu ta koma kan wannan gado ta kwanta cikin tsananin farin ciki, tana cewa
a ranta wannan rana ita ce ranar da tafi kowacce rana farin ciki a rayuwata. Bata jima
da kwanciya ba barci mai nauyi yayi gaba da ita. Shima Aymanul Faris yana komawa
cikin ɗakinsa ya kwanta ya kama sharar bacci abinsa cikin tsananin jin daɗi da
kwanciyar hankali.
Kashe gari tunda duƙu-duƙun safiya, maigida Barban ya sa hadiman cikin kogon nan
shirya abincin kalaci mai kyau, kafin rabin sa'a sun gama shirya komai. Suka jejjera
abincin akan wani teburi wanda kujeru suka kewaye, maigida Barban ya bi ɗakunan su
Aymanul Faris da kansa duk ya tashe su daga

Please Login or Register in order to submit comment