Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fara zubowa daga jikinsa.
Kabilar SHUMBUL - kabila ce mai tsohon tarihi kuma mafi yawa daga cikin mutanen wannan kabila mata ne. Sai dai za'a iya cewa mata ne ammafa kamar maza domin jarumai ne, kuma basu da tsoro. Tun kafin yaki tsakanin sarki Deher da sarki Meher wannan kabila ta fara shafewa, kai sai da ta kai ta kawo cewa in banda cikin asalin birnin Shaha bangaren Kudu babu inda zaka samu mutanen wannan kabila, wato bangaren da sarki Meher yake mulki. Wannan yaki da aka gwabza shi ne sanadiyar shafewar mutanen wannan kabila gaba dayansu, amma kafun nan tuni sarki Meher ya auri daya daga cikinsu, kuma ita ce wacce yayi dacen samun magaji da ita. Sarki Meher ya san me ake kira da yaki, ya san cewa wurin da ake yaki ba wajen zuwan mace mai ciki bane. Wannan shi ne dalilin da yasa ya nuna mata boyayyiyar hanya ta karkashin kasa ta gudu, domin kada a kashe ta. Wannan mace ita ce yar kabilar SHUMBUL da tayi saura a duniya, kuma ba wata bace illa KABSHIYA mahaifiyar sarki Kuffuru wacce ta haife shi.
Sarki Kuffuru ya dago fuskarsa a murtuke ya ce, "Me kake so kace? Mahaifiyar tawa guda daya zan salwantar don samun kariya daga sharrin Hasanul Jalwar, babu jan magana babu ja-in-ja, wannan ba zai yiwu ba. Ka nemo wata hanyar dabam wacce zamu wannan tsari, amma ba wannar ba domin ba zan taba yarda ba. Mahaifiyata ita kadai ta rage min a duniya, kada ka manta a daji ka tsinto mu, wannan birnin ba namu bane babu wanda na sani anan babu wanda zan kalla naji dadi face mahaifiyata. Tayaya kake ganin zan so na rasata?" Koda Djinn yaji haka sai yayi murmushin mugunta ya ce, "Kuffuru kayi sani cewa sarki baya cika sarki face ya kasance mai sadaukarwa. Sarki shi ne wanda rayuwarsa da ta iyalansa ba'a bakin komai take ba, a kowanne lokaci abokan-gaba zasu sami nasarar kashe su. Kuffuru a matsayinka na babban sarki, mai babban buri, salwantar da rayuwar mahaifiyarka ba wani abu bane. Saboda idan ba kayi hakan ba, akwai yiwuwar ka rasa rayuwarka." Sarki Kuffuru ya kada kai ya ce, "Ba zan yadda da wannan hasashe ba, face na gwabza yaki da Hasanul Jalwar naga ban sami nasara ba. Mu ajiye batun salwantar da rayuwar mahaifiyata, ka kaini kauyen Gazwar tabbas zan baka mamaki." Aljani Bukalshiyu Djinn yai dariyar mugunta ya ce, "Ni na san abinda kai baka sani ba. Amma ba'a kwacewa yaro garma... kai Hasamul-Sawaz dauke shi ka kaishi LUSLEL." Aljani Bukalshiyu Djinn na gama fadin haka duwatsun da suka samar da jikinsa suka tarwatse, kowanne dutse ya koma gurbinsa.
Aljani Hasamul-Sawaz ya dubi sarki Kuffuru ya ce, "Da kyau namiji. Tabbas ka tafiyar da al'amuranka cikin hikima da basira, in banda rashin hikima da sanin me yake, waye zai salwantar da rayuwar mahaifiyarsa?" Sarki Kuffuru ya yi murmushi ya ce, "Hakane. Abinda nakeso da kai shi ne ka samar min da sulken yaki da zabgegiyar takobi, kafun ka kaini LUSLEL." Aljani Hasamul-Sawaz ya saka hannu cikin jakar tsafinsa ya fiddo sulken-yaki da zabgegiyar takobi ya baiwa sarki Kuffuru. Kuffuru ya saka wannan sulke sannan ya rataya wannan zabgegiyar takobi a gadon bayansa. Hasamul-Sawaz ya sunkuya shi kuma ya haye gadon bayansa, suka dawo bakin gabar teku. Hasamul-Sawaz yai sallama dashi shi kuma ya shiga jirgin kwale-kwale, wannan shi ne dalilin da yasa sarki Kuffuru ya dawo kauyen Gazwar.
***
Ba tare da tsayawa jin wani ba'asi ba, Hasanul Jalwar ya juya zai tafi. Bisa mamaki yaji alamun tafiya a bayansa, yana waigowa yayi arba da wani ƙaton aljani mai jikin wuta tsaye a bayansa.
"Wannan shi ne hadimin-wuta Nara-ya. Ka tafi tare dashi, tabbas zaiyi maka amfani sosai a fafatawar ka da Kuffuru. Abinda nake so da kai shi ne kada kayi amfani da kowannen irin makami akan sarki Kuffuru face takobin Saiful Shiradu." inji aljani Nara a lokacin da gangar jikinsa ta tarwatse ta koma wuta.
Aljani Nara-ya ya durkusa Hasanul Jalwar ya haye gadon bayansu suka fice daga cikin ƙauyen Gazwar gaba ɗaya, suka tasarwa LUSLEL.
Sarki Kuffuru na tafe cikin kwale-kwale, yana wasa takobinsa gami da kallon hanya. Bayan shuɗewar kowacce daƙiƙa sai yayi wuridin sabuwar ɗalasimi a cikin ransa domin neman kariya da nasara.
Ba zato ba tsammani! Ya ji wani abu daga ƙarƙashin wannan teku ya ɗaga kwale-kwalensa sama, ya fyaɗata a cikin ruwa. Sarki Kuffuru da kwale-kwalen suka nutse izuwa ƙarƙashin tekun.
Bayan ɗan lokaci ya taso daga ƙarƙashin ruwan inda yayi arba da wani saurayi tsaye a cikin iska bisa wani shirgegen aljani. Saurayin ya kasance dogo kuma fari fat. Jikinsa a mummurɗe yake ya saka doguwar riga baƙa mai beza a hannu, yana rike rataye da zabgegiyar takobi a kafaɗarsa.
Dukkansu su biyun basu da buƙatar yiwa juna bayani domin sun san juna.
A fusace sarki Kuffuru ya buɗe hannayensa biyu take yayi sama tamkar tsuntsu, ya tsaya a cikin iska. Nan fa suka fara kallon-kallo cikin harara da ƙunar-rai.
Hasanul Jalwar ne ya fara jawabi da cewa, "Ka kashe min mutane har guda ɗari da hamsin. Kana matsayin babban sarki a wannan nahiya, amma baka ji kunyar dawowa gare ni ba. Babu ruwana da matsayinka sare kanka zanyi."
Sarki Kuffuru yai dariya ya ce, "Na san baka manta da abinda ya faru a tarihi ba. Kakanka shi ne ya tarwatsa birnin mahaifina, ya kashe kowa da komai. Kamata yayi ace nayi tasowa irinta yarima amma na ƙare rayuwata gaba ɗaya a cikin dokar-daji. Kana tunanin ba zan ɗauki fansar abinda yayi mana bane? Ka sake tunani. Ni Kuffuru, nayi alƙawari da ƙololuwar abin dogarona sai na hallaka dukkanin ƴaƴan Samudul Ansari da sukayi saura a duniya. Kuma na rantse sai na cika. Zan yi maka adalci guda ɗaya - ka zare wannan takobi taka, ka miƙo min ita sannan ka murɗewa kanka wuya. In dai kayi hakan, ka huta da shan azabar da zanyi ma."
Koda Hasanul Jalwar yaji kalaman sarki Kuffuru sai ransa ya ɓaci, ya zaro takobin Saiful Shiradu daga cikin kufenta. Nan take yanayin wannan wuri ya sauya, wani zafi mai kama da an buɗe tsohuwar rijiya ya fara fesowa. Sararin samaniya ta fara kaɗawa waɗansu jajayen gajimare masu kama da guma-guman wuta suka fara bayyana a cikinta. Ruwan teku dake ƙasa ya fara tafarfasa yana zaɓalɓala, kai kace shinkafa ake dafawa.
Fuskar Hasanul Jalwar ta sauya matuƙa, ƙwayar idanunsa ta fara ci da wuta. Gashin kansa ya fara hayaƙi ammafa ja. Wannan baƙar doguwar riga ta jikinsa ta koma jajawur kalar wuta. Waɗansu aljanu guda uku na wuta suka bayyana a bayansa suna fesar da wuta daga bakinsu suna yiwa takobin Saiful Shiradu kirari.
Sarki Kuffuru ya ja da baya a razane cikin tsananin mamaki, don a wannan lokaci Hasanul Jalwar baiyi masa kama da kowa ba face shaiɗanin ifritun-aljani mai siffar wuta, wanda maganarsa kaɗai ta isa ta ƙone gari.
Ai kuwa nan take shima ya rintse idanunsa ya kira wani babban ɗalasimin tsafi. Wani ƙaton aljani mai siffar dutse ya bayyana a ƙasansa, Kuffuru ya haye kan aljanin. Wata zabgegiyar takobi da aka ƙera da zallar dutse ta bayyana a hannunsa. Wani sulke da aka ƙera da zallar dutse ta bayyana akan ƙirjinsa.
Hasanul Jalwar ya daka masa tsawa wacce tasa waɗannan aljanu guda uku dake bayansa suka feso wuta, wutar ta cika saman tekun gaba ɗaya. Ruwa ya ci gaba da tafarfasa.
"Ƙarya kake... Jinin Samudul Ansari yafi ƙarfin ya kashe kansa a gaban abokin-gaba. Ka je ka binciki tarihi da kyau, ka gano wanda ya fara tsokano wani tsakanin sarki Deher da Meher... In banda tsoro da mutuwar zuciya waye zai shigo ƙaramin ƙauye kamar Gazwar yana yiwa mutanen cikinsa kisan-mummuke? Kuma tabbas tunda ka kawo kanka, a wannan wuri zan sare kanka sannan na tsire kan a ƙofar fadarka domin hakan ya zamo izina ga sauran sarakuna irinka."
Hasanul Jalwar na gama faɗin haka ya ɗaga takobin Saiful Shiradu ya kaɗata a cikin iska, nan take iskar wannan wuri ta ɗauki ɗumi. Waɗannan aljanu guda uku dake bayansa suka raba kansu gida uku, ɗaya ya koma ɓangaren arewa, ɗaya kudu, ɗayan kuma gabas suka fara feso wuta. Nan fa wannan wuri gaba ɗaya ya koma ja, zafin wuta ya cika ko'ina. Babu abinda mutum zai kalla a wannan wuri face wannan wuta.
Kan kace me tuni zafi ya fara takurawa sarki Kuffuru, kafun ma a fara gumurzun ya fara nadamar tunkarar JARUMI mai TAKOBIN SAIFUL SHIRADU.
Hasanul Jalwar ya baiwa aljani Nara-ya umarnin afkawa sarki Kuffuru, nan take aljani Nara-ya ya kaɗa fuka-fukinsa yayi kan sarki Kuffuru da gudu, Hasanul Jalwar ya gyara riƙe takobin Saiful Shiradu da kyau. Idanuwansa na kafe akan sarki Kuffuru.
Koda sarki Kuffuru yaga babu sarki sai ALLAH, take ya kirawo ɗalasimin ƙabilar Gandiz. Wata farar ƙanƙara mai kama da dusar-ƙanƙara ta fara sakkowa a wajen.
Wohoho! Ga Hasanul Jalwar da aljanun-wuta, ga takobin Saiful Shiradu. Ga sarki Kuffuru da aljanin-dutse, ga kuma iko irin na ƙabilar Gandiz na sauƙa.
****
RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 36: *Fafatawa a saman teku*
*
*
✍️✍️✍️ Umar Sangaru ✍️✍️✍️
*
Maimakon wannan dusar-ƙanƙara ta rage zafin wannan wuta, narkewa ma ta fara yi kafun ta iso inda wutar take. Hasanul Jalwar ya yi dariya ya ce, "Babu abinda zaiyi tasiri a wannan wuri face ƙarfin takobin Saiful Shiradu, haƙiƙa kai wannan sarki ka tafka babban kuskure da ka tunkari wannan takobi ba tare da ka nemi wani tsari ba. Amma babu komai ni hakan ma yayi min, kaga zan ji dadin sare kanka cikin sauki." Hasanul Jalwar na faɗin haka ya daka wawan tsalle ya kaiwa sarki Kuffuru sara a wuya, nan take wani siririn layi ya bayyana akan tsinin takobin ya nufi wuyan sarki Kuffuru zai fille masa kai. Cikin kaduwa da rudewa sarki Kuffuru ya daga wannan takobi ta dutse ya tare saran, amma bisa mamaki wannan siririn layi ya ratsa ta cikin wannan takobi ta dutse ya wuce. Take takobin ta rabe gida biyu tamkar an raba tsakiyar tuffa, siririn layin ya yi kan wuyan sarki Kuffuru gadan-gadan zai tsarge shi. A firgice sarki Kuffuru ya daka tsalle daga kan wannan aljani na dutse ya tsaya cikin iska, wannan siririn layi ya ratsa ta cikin wannan katon aljani, duk girmansa da taurin jikinsa na dutse take ya rabe gida biyu, yana mai kwarara uban ihu. Kamar yadda wannan takobi ta rabe gida biyu, haka gangar jikin wannan aljani ta rabe gida biyu ta faɗa cikin wannan teku, ruwa yayi fantsama tamkar an jeho manyan tsaunika guda biyu daga sama. Hasanul Jalwar yayi dariya ya ce, "Wannan sara ɗaya kenan, babu abinda zai kwaceka a wannan wuri. Dole sai na sare kanka, lallai a yau zaka baƙunci lahira..." Yana gama faɗin haka ya sake kawowa Kuffuru sara a kwibin-cikinsa, a wannan lokaci wannan siririn layi bai bayyana ba amma wani mugun tiriri ne mai kama da an bude tukunyar dafa-kalwa ya doki sarki Kuffuru yaji tamkar an rufe shi a cikin tukunya. Nan take mugun ƙishirwa ya dokeshi, jijiyoyin jikinsa suka kukkumburo, wani gumi mai yawa ya fara zubo masa. Dakyar da siɗin goshi ya samu ya daka tsalle gefe ɗaya ya kaucewa wannan takobi, tiririn ya wuce.
Hasanul Jalwar ya murtuƙe fuska ya dakawa waɗannan aljanu guda uku dake ɓangarorin arewa, kudu da gabas na wannan daji tsawa, "Ku daure shi!!!." ya ce. Nan take waɗannan aljanu guda uku suka daina fesar da wuta, suka buɗe bakunansu suka fara rera waɗansu ɗalasiman tsafi cikin baiti mai ɗaukar hankali. Ba zato sarki Kuffuru yaji karfin damtsensa na raguwa, tamkar ana zare masa laƙa. Haka kuma sai yaga wata irin jar-wuta ta fara kama gurayen tsafin dake hannunsa tana kone su. Hasanul Jalwar ya sake bushewa da dariya ya dako wawan tsalle ya kawowa Kuffuru sara akan kirjinsa, Kuffuru ba shi da ikon kaucewa saboda dalilai guda biyu. Na farko ga wadannan dalasimai dake rage masa karfi, na biyu ga azabar wannar jar-wuta dake ƙone gurayen tsafin hannunsa. Amma dukda haka sai da ya ja baya a hankali takobin Saiful Shiradu ta sari ƙirjin Kuffuru amma saran baiyi zurfi sosai ba. Nan take wajen da ta sara ɗin ya dafe kuma ya kone, kai kace karfe aka saka a cikin wuta aka bari yayi ja sannan aka goga masa a wurin. Sarki Kuffuru ya kwarara ihun wahala saboda tsananin zogin da ya shige shi. Inda ace anan abun ya tsaya da da sauki, amma a daidai lokacin ya ji ɓarin jikinsa na dama wanda aka yiwa wannan sara, ya riƙe tamkar an ɗaure shi ko motsa ɓarin sosai baya yi. Sarki Kuffuru ya fara nadamar kawo kansa da yayi wannan wuri ba tare da kyakkyawan tsari ba, kuma ya tabbatar da cewa lallai ko shi ne sa'a bai isa ya kuɓuta daga sharrin wannan takobi ba. Saboda ya gwada amfani da dukkanin ɗalasimansa na tsafi amma basuyi tasiri ba, babu abinda ke tasiri a wannan wuri face ikon takobin Saiful Shiradu kaɗai. Hasanul Jalwar yayi dariya ya kirawo asalin dalasimin Saiful Shiradu ya kaiwa iska sara, take waɗannan aljanu guda uku dake rera wannan ɗalasimi suka tarwatse suka bi iska. Sarki Kuffuru na tsaye cikin wasu-wasi yaji muryar Hasanul Jalwar a kunnensa tana cewa, "Ko ka san cewa wannan takobi da sinadarai guda uku aka samar da ita? WUTA, DALMA dA BAKIN KARFE, kuma kowanne daga cikin waɗannan sinadarai guda uku makami ne mai zaman kansa. Kaga kenan babu wanda zaiyi nasara akanmu matukar aka ce muna tare da wannan takobi. Ba ma wannan ba kana tunanin laifin da ka aikatawa maigirma Samud na kashe jikokinsa, ruhinsa zai bar ka cikin salama?"
Hasanul Jalwar na gama faɗin haka gangunan waɗannan aljanu guda uku ta bayyana a cikin iska ammafa a matsayin sinadarai - ɗaya a siffar dunƙulen wuta, ɗaya kuma dunƙulalliyar dalma kamar nakiya, ɗayan kuma siffar wani ƙaton karfe mai siffar ƙwallo. Sarki Kuffuru na ganin haka ya fara karkarwar razana, shi kuma Hasanul Jalwar murmushi yayi ya murza takobin Saiful Shiradu, waɗannan sinadarai guda uku suka kewaye sarki Kuffuru suka saka shi a tsakiya. Nan fa alamun tsoro da saduda suka bayyana ƙarara akan fuskar sarki Kuffuru don ya tabbatar da cewa, lallai yau ƙarshensa yazo. Hasanul Jalwar yayi dariya ya ce, "Shin kana da wata wasiyya kafun ka isa lahira? Ina ƙarfin mulkin naka da ji-ji da kan naka? Ka ƙwaci kanka mana idan ka isa... TUN DAGA FARKON KAFUWAR BIRNIN SHAHA, JININ SAMUDUL ANSARI SU NE MAFIYA ƙARFI KUMA SU NE SHUWAGANNI. DA KAI DA SHASHASHUN KAKANNINKA BA KOMAI BANE FACE BAYI MASU BIYAYYA GA AHALIN SAMUDUL ANSARI. TABBAS KASHEKA DA ZANYI ZAI TABBATARWA DA SAURAN MASU TSAURIN IDO IRINKA CEWA, A KULLUM DA KOWANNE LOKACI JININ SAMUDUL ANSARI SHI NE BABBA. ZAN KASHEKA YANZU A NAN SANNAN NA ƊAUKI KANKA NA MAYAR DASHI BIRNIN KUFA, DAGA YAU AN SHAFE MULKINKA. RAGON SARKI KAWAI... RAGO KAWAI..."
Wadannan kalmomi da Hasanul Jalwar ya fada suka tsayawa sarki Kuffuru a wuya, yaji wani irin gagarumin baƙin-ciki ya rufe shi. Yana matsayin sarki mai mulkin babbar ƙasa amma ace shugaban wata ƙabila dake rayuwa a ƙaramin ƙauye yana faɗa masa baƙaƙen maganganu? Sai dai yana cikin wannan tunani ne waɗannan sinadarai guda uku suka yi bindiga, tafashashshiyar dalma, wuta mai zafi da baƙin-ƙarfe wanda tuni ya gama gasuwa ya zamo jajawur suka yiwo kansa gadan-gadan zasu narka shi. Sarki Kuffuru ya rufe idanunsa cikin saduda da jiran mutuwarsa.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani, gangar jikin wani ƙaton aljani mai siffar dutse ta taso daga ƙarƙashin ruwan wannan teku, ta shiga tsakanin sarki Kuffuru da ruwan waɗannan sinadarai guda uku. Ai kuwa take ruwan ya dira akan aljanin, take ya wangame bakinsa ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa, kai kace tsawa mai ƙarar gaske ta faɗo ƙasa lokacin da ake tsaka da ruwa.
Aljanin ya lulluɓe sarki Kuffuru sannan suka ɓace ɓat, abinda Hasanul Jalwar ya gani kawai shi ne zubowar jini mai yawa daga jikin aljanin sakamakon taɓa shi da waɗannan sinadarai suka yi.
Dukda cewa Hasanul Jalwar ya san sarki Kuffuru bai mutu ba amma farin-ciki yake, saboda ya nunawa sarki Kuffuru ainihin waye shi da kuma ƙarfinsa. Kuma tabbas sarki Kuffuru zai ƙara tsinkewa da al'amuransa, don ya tsaga bai ga jini ba.
Ya baiwa aljani Nara-ya umarnin komawa cikin ƙauyen Gazwar. A daidai wannan lokaci ne kuma wannan wuta ta daina ci, guma-guman gajimaren nan suka ɓace. Ruwan teku ya daina tafasa.
****
Sarki Kuffuru ne kwance akan wani katafaren gado, wata zabgegiyar budurwa sanƴe da kayan likitoci na tsaye a kansa, tana ta gyagygyara masa wannan rauni na kan ƙirjinsa wanda tuni ya fara zubar da ruwa. A gefe guda kuma waɗansu mutane guda biyu ne a zazzaune bisa kujeru sun rufe fuskokinsu da baƙin-rawani.
Tsahon ɗan lokaci wannan budurwa ta ɗauka tana gyagygyara raunin sarki Kuffuru sannan ta kammala, ta juyo ta dubi waɗannan mutane guda biyu ta ce, "Na kammala, nan da wata guda zai iya miƙewa. Wannan wuta da ta ƙona shi ba irin kowacce wuta ba ce. Wuta ce da aka samar daga asalin dutsen wuta wanda ke ƙasashen baƙar-fata."
Ɗaya daga cikin waɗannan mutane biyu ya dubi matar ya ce, "Gaishe ki shugabar likitoci, lallai yau kin yi aiki mai kyau."
Daga wannan rana waɗannan mutane guda biyu suka ci gaba da jiƴƴar sarki Kuffuru, basa zuwa ko'ina kullum idanunsu na kan sarki Kuffuru har tsahon wata guda sannan ya warke.
Rannan da yammaci waɗannan mutane guda biyu suka keɓe da shi, ɗaya daga cikinsu ya cire rawanin kansa. Sarki Kuffuru yayi arba da fuskarsa nan take ya shaidata. Ba wani bane illa aljani Buƙalshiyu Djinn a siffar mutum.
"Kaga karambani ko?" inji Djinn. "Na ce maka takobin Saiful Shiradu tafi ƙarfinka, amma kayi min taurin-kai ka tafi, in ba don naje na ceci rayuwarka ba da tuni yanzu kana lahira. Kayi sani cewa taɓa ni da waɗannan sinadarai guda uku suka yi, na rasa kaso hamsin na ƙarfin damtsena da ƙarfin sihirina. A duk faɗin duniya ni ne aljani guda ɗaya da wannan takobi bata iya hallakawa a lokaci guda, amma idan waɗannan sinadarai suka ci gaba da taɓani, za'a kai munzalin da ƙarfina gaba ɗaya ya ƙare ba zan iya taɓuka komai a duniya ba. Yanzu wacce shawara ka yanke, zaka sadaukar da rayuwar mahaifiyarka ko kuma zaka bari wataran Hasanul Jalwar ya kawo maka harin-bazata ya hallaka ka? Na baka sa'a guda da rabi, kayi shawara!"
Aljani Buƙalshiyu Djinn na gama faɗin haka ya ɓace ɓat. Sarki Kuffuru ya sunkuyar da kansa ƙasa yana tunani, tabbas abubuwan da Buƙalshiyu Djinn ya faɗa gaskiya ne, to amma waye zai so ya salwantar da rayuwar mahaifiyarsa?
Yana cikin wannan hali ne wannan aljani dake gefe ya dafa kafaɗarsa, Kuffuru ya ɗago ya dubi aljanin. Ashe Hasamul-Sawaz ne.
"Ya kai magajin Gauhan, wacce shawara ka yanke?" inji Hasamul-Sawaz. "Kayi sani cewa mahaifiyarka ta tsufa, a kowanne lokaci ta Allah zata iya kasancewa akanta. Sarki Gauhan ya ƙarar da rayuwarsa gaba ɗaya domin cika wannan buri nasa wanda bai kammalu ba, a halin yanzu kaine wanda yake da babbar dama ta cika wannan buri nasa. A da nayi tsammanin ko babu tsari a jikinka zaka iya cin nasara akan Hasanul Jalwar amma a yanzu na tabbatar hakan ba zai yiwu ba, domin fafatawar da kuka yi a saman teku babu abinda ka taɓuka, inda Djinn bai cetoka ba da tuni yanzu an shafe labarinka.
"A nawa ganin gaskiya ka bi wannan umarni na Djinn, saboda idan baka yi hakan ba. Duk ranar da Hasanul Jalwar ya kawo ma harin-bazata mutuwa zakayi."
Sarki Kuffuru ya ɗago kansa ya dubi Hasamul-Sawaz ya ce, "Mayar dani ƙasata, na san abinda zanyi..."
Aljani Hasamul-Sawaz ya ɗauke shi, ya dawo dashi birnin Kufa. Sarkin Kufa na isa gida ya samu mahaifiyarsa kwance cikin halin rashin lafiya. Likitoci aƙalla guda bakwai na tsaye akanta, amma sun gagara gano wannan cuta.
Ana ganin sarki Kuffuru aka buɗa masa ya ƙarasa inda take kwance, ya kalleta. Fatar jikinta tayi fari-sol kuma a duk bayan daƙiƙa fatar ƙara fari take, babu buƙatar tambaya ka san cewa jininta ne yake raguwa.
Tsahon ɗan lokaci sarki Kuffuru na rungumeta da ita, kafun ta ce ga garinku. Sarki Kuffuru ya kwarara uban ihu ya rungume gawarta, yana kuka.
Bayan kwanaki biyu aka haƙa kabari aka binneta, sarki Kuffuru yayi kwana goma cir yana jimami kafun daga bisani ya wartsake.
Watarana da yammaci sarki Kuffuru ya kaiwa kabarin Kabshiya ziyara shi ɗaya jal, dama a cikin wani ƙaton daji aka binneta a gindin wani ƙaton tsauni. Sarki Kuffuru na durƙushe a gaban kabarin yana ta addu'o'i kawai wannan ƙaton tsauni ya motsa, kuma ya rikiɗe ya koma siffar aljani Buƙalshiyu Djinn.
"Kayi tunani mai kyau, tabbas haka ake so sarki ya kasance." inji Djinn.
Sarki Kuffuru ya harare shi ya ce, "Ya aka yi ka karanta abinda ke cikin raina, a lokacin da na yanke shawarar salwantar da rayuwar mahaifiyata?"
Djinn ya yi murmushi ya ce, "Kada ka manta nifa aljani ne, kuma a cikin aljanun ma ni ifiritu ne. Kada ka manta ni ne aljaninka tayaya karanta abinda ke ranka zai bani wahala?"
Sarki Kuffuru ya haɗe fuska ya ce, "Kaga ba surutu nake son ji ba, tunda ka zuƙe jinin mahaifiyar tawa. Ina maganin tsarin da ka haɗa?"
Djinn ya yi dariya sannan ya ɗaga hannunsa sama wata zabgegiyar takobi ta bayyana. Takobin doguwa ce sosai amma bata da faɗi, anyi mata ado da ruwan jini. Tana da tsananin kaifi da tsini.
Ya mikawa sarki Kuffuru takobin ya ce, "Wannan ita ce takobin Siwod-del-bulod, wato takobin jini. Kamar yadda aka samar da takobin Saiful Shiradu daga wuta, ita kuma wannan takobi daga jini aka samar da ita. Jinin sadaukan bil'adama guda goma, da jinin sadaukan aljanu guda goma, da kuma jinin manƴan namun-dawa guda goma aka haɗa a waje guda aka ƙirƙireta. Jinin mahaifiyarka kawai ado aka yi mata dashi amma yafi sauran amfani saboda takobin Saiful Shiradu bata isa tayi tasiri akanta ba."
Sarki Kuffuru ya yi sallama da Djinn ya karɓi wannan takobi ya koma cikin birnin Kufa. Yana shigowa gidan sarautarsa wata kuyanga ta taho da gudu ta tarye shi, ta faɗi a gabansa tayi gaisuwa.
"Ranka shi daɗe, gimbiya ta samu juna-biyu." inji kuyangar.
Sarki Kuffuru yai dariyar farin ciki sannan ya ƴanta wannan kuyanga, ya nufi ɗakin da Anisa ke kwance.
****
Hasanul Jalwar na isa gida, kafun ya isa gidan ƙarƙashin ƙasa inda aljani Nara yake tuni Hajriya ta tare shi. Ta rungume shi sannan ta ja shi gefe, suka zauna a cikin wani falo.
"Wai ina kaje ne haka?" ta tambaye shi.
Hasanul Jalwar ya yi murmushi ya ce, "Naje yiwa wani mara-kunƴa kashedi ne."
Hajriya ta dube shi cikin rashin fahimta ta ce, "Mara kunƴa? Waye kenan?"
"Labari ne mai tsahon," inji Hasanul Jalwar. "Manta kawai, kije turakarki zan zo na same ki. Aljani Nara yana jira na."


Please Login or Register in order to submit comment