Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Saboda tsananin hasken wannan halitta kai kace rana ce a tsakiyar sararin samaniya.
Saboda haka dole Aydenlik da gimbiya Firziyya suka kawar da idanunsu daga kallon wannan halitta. Amma, abin mamaki duk wannan tsananin haske nata baya yiwa Marganu komai.
Tunda ya shigo cikin kogon suka ƙurawa juna idanu shi da wannan aljani. Wannan aljani shi ake kira ISIKA; aljanin haske, kuma shi ne aljanin sarki Ratanam kamar yadda sarki Kuffuru keda Djinn haka shima yake da wannan aljani.
Koda aljani Isika ya fuskanci hasken jikinsa na cutar da waɗanda ke tare da Marganu saiya tafa hannayensa take haske ya ragu ainun, ya samar da waɗansu kujerun alfarma guda uku ya umarci Marganu, Aydenlik da Firziyya su zauna akai.
"Barkan ku da zuwa fadata, na daɗe ina jiran zuwanku. Marganu sannu da rashi! Wace ce wacce kuke tare da ita?" inji aljani Isika.
Marganu ya ce, "Masoyiyata ce, gimbiya Firziyya ƴar sarki Kuffuru."
"Ƴar sarki Kuffuru kuma?" aljani Isika ya yamutse fuska. "Bani hujjoji masu ƙarfi da zasu sa ka amince da jinin Kuffuru dukda cewa shi ne ya raba ka da mahaifinka."
Isika aljani ne mai tsananin hikima, tun shigowar su Marganu cikin wannan kogo ya gano wace ce Firziyya sannan ya kalli dukkanin manufofin dake cikin ranta. Amma, yana so ya gwadawa Marganu yadda take tsananin ƙaunarsa ne.
"Akwai hujjoji," inji Marganu. "Na farko ita ce wacce ta cetoni daga hannun arnan-daji a lokacin da suke daf da sare min kai. Na biyu ta zaɓi tayi rayuwa dani dukda cewa a yanzu ayyukan da suke gabana suna da yawa da kuma wahala. Watau ta bar rayuwar daula ta matsayin gimbiya ta zaɓi rayuwar jarumtaka.
"Waɗannan hujjoji guda biyu da na kawo sun wadatar ko dai na ƙara faɗo wasu?" ya tambayi Isika.
Aljani Isika ya yi murmushi ya ce, "Eh to, waɗannan hujjoji naka zan iya cewa sun yi, amma dole sai na yiwa wannan gimbiya abu guda, idan ta amince?"
Gimbiya Firziyya ta dube shi cikin ƙarfin zuciya irinta Gandiz ta ce, "Na amince a yi min kowanne irin abu matuƙar ba zai cutar dani ba."
Marganu da Aydenlik suka yi shuru suka ƙyale gimbiya Firziyya da aljani Isika kawai suna musayar zance.
Isika ya samar da wata hula ta haske akan tafin hannunsa ya miƙawa ita gimbiya Firziyya ya ce, "Karɓi wannan hula ki saka akanki. Zata haska har cikin ƙwaƙwalwarki ta nuna mana abinda ke ranki. Idan da gaske kike ƙaunar yarima zatayi koren haske, idan kuwa da wani shirin kika zo jan haske zata nuna."
Gimbiya Firziyya tayi murmushi cikin yarda da kai ta karɓi wannan hula ta saka akanta. Tsahon ƴan daƙiƙu tana farin haske kafun daga bisani ta juye izuwa koren haske, yadda ka san koren ganƴe.
Marganu na ganin haka yaji wani sanƴi a cikin ransa ya tabbatar da cewa lallai wannan gimbiya da gaske take ƙaunarsa.
Aljani Isika ya yi murmushi ya ce, "Tun kafun kuzo wannan wuri na san wace ce ke, da abinda ke cikin ranki. Abinda yasa kika ga nayi miki wannan gwaji shi ne ina so na tabbatarwa Marganu cewa da gaske kike tsananin ƙaunarsa. Saboda naga akwai kwakwanto a cikin ransa amma tabbas yanzu wannan kwakwanto ya kau."
Marganu ya yi ajiyar numfashi ya ce, "Haka ne, mahaifina ne ya ce nazo na sameka?"
"Na sani," inji Isika. "Tunda kuna tare da ƴar sarki Kuffuru ai anyi mai sauƙi. Gimbiya amsa mana waɗannan tambayoyin.
"WANNE IRIN ALJANI SARKI KUFFURU KE SARRAFAWA?
"DA WACCE IRIN TAKOBI YAKE YAƘI?
"WANNE MATAKI YAKE A HARKAR TSAFI, DAGA ƊAYA ZUWA GOMA?
"MEYE BABBAN BURINSA A YANZU?
"A HALIN YANZU A INA YAKE?"
Hawaye masu zafi suka zubowa gimbiya Firziyya ta sunkuyar da kanta ƙas. Daga can ta ɗago ta dubi Isika ta ce.
"Aljanin da mahaifina yake sarrafawa shi ne ALJANIN-DUWATSU; Buƙalshiyyu Djinn.
"Takobin da yake yaƙi da ita kuwa, ita ce takobin Siwod-del-bulod.
"Yana mataki na takwas a harkar tsafi.
"Babban burinsa a duniya shi ne kamo sarkin ɓarayin duniya Barban domin mulkar ƙasashe guda tamanin da uku.
"A halin yanzu bansan haƙiƙanin inda yake ba amma nafi kyautata zaton yana kogon Hubbaz wajen aljani Sheezuwa tunda sun ɗauko sarauniya Rauziyya; cikon SADAUKAI UKU da zasu iya kamo Barban."
Aljani Isika ya jinjina kai cikin tsananin mamaki ya ce, "Aljanin-duwatsu. Siwod-del-bulod. Lallai shirin sarki Kuffuru babba ne. Amma zamu iya maganinsa idan har kun bayar da himma, kun ɗauko abubuwan da zamu umarce ku da ɗaukowa."
Isika yana zuwa nan a zancensa ya juya ya dubi Marganu ya ce, "Kamar yadda mahaifinka yake sarrafa ni, haka sarki Kuffuru ke sarrafa aljanin duwatsu. Ni jikina na haske ne, Djinn kuma jikinsa na duwatsu ne. Kuyi sani cewa duk duniya babu makamin da zaiyi tasiri akaina face makami guda ɗaya. Haka shima Djinn babu makamin da zai iya kashe shi face wata rantsatstsiyar takobi guda.
"Babu yadda za'ayi ku iya kashe mutum ma'aboci ifritu, ba tare kun fara hallaka shi ifritun ba. Abinda yasa kuka ga an kashe sarki Ratanam ba tare da an kasheni ba, shi ne Ratanam ya riga ya sadaukar dani wa ɗansa Yarima.
"Saboda haka dole ne ku fara kashe aljani Buƙalshiyyu Djinn kafun ku sami nasara akan kashe sarki Kuffuru. Kafun na ƙarasa muku sauran bayanan, Marganu fara ƙaddamar dani a matsayin aljaninka tukunna."
Koda jin haka sai Marganu ya dubi Aydenlik yana so ya tambaye shi, tayaya zai ƙaddamar da aljanin? Aydenlik yayi masa bayani dalla-dalla.
Marganu yaje gaban wannan karaga ta aljani Isika ya tsaya, sannan ya ɗaga hannunsa guda sama. Shi kuma aljani Isika saiya durƙusa a gaban Marganu bisa gwiwowinsa, ya rufe idanunsa yana karanto ɗalasimai.
Tsahon ɗan lokaci, kafun daga bisani jikin aljani Isika ya fara juyewa izuwa haske, yana gama zamowa haske, ya shige jikin Marganu. Nan take jikin Marganu ya fara yin haske tamkar hasken rana a sararin samaniya.
A lokacin wani irin zogi ya soma ratsa shi yaji tamkar za'a yayyaga shi, amma saiya jure cikin tsananin jarumtaka bai ƙwala ihu ba.
Gimbiya Firziyya da tsoho Aydenlik suna ganin dukkanin abinda ke faruwa cikin tsananin mamaki, har tsahon rabin sa'a sannan wannan haske ya fita daga jikin Marganu.
Hasken na gama ficewa surar jikin Marganu ta ainihi ta bayyana sai dai amma an ɗan samu ƴan sauye-sauye. Na farko wani hatimi mai tsananin haske ya bayyana akan damtsen hannunsa na hagu, sannan idanunsa sun ɗan canja launi, suna bayar da haske mai sanƴa kwarjini a zuciyar duk wanda ke kallon su.
Da waɗannan idanu babu abinda Marganu ba zai gani ba. Komai tsananin duhun waje ba zai hana shi kallon abinda ke wajen ba, kuma komai tsananin zurfin teku ba zai hana shi kallon halittun dake ciki ba.
"Na taya ka murnar ƙaddamar dani a matsayin aljaninka. Daga yau babu mai iya kashe ka, ba tare da yaga bayana ba. Duk duniya babu halittar dake sarrafa haske kamar ni, komai duhun waje zan iya sakawa yayi haske, sannan komai hasken waje zan iya zuƙe shi ya koma duhu duɗum. Kaima daga yau zaka iya amfani da irin wannan ƙarfin sihiri nawa." inji Isika.
Aydenlik da Firziyya suka matso kusa da Marganu su ma suka taya shi murnar samar da aljanin haske a matsayin hadiminsa.
"Yauwa, duk lokacin da kake so kayi amfani da ƙarfina ko kuma ka kirawo ni, kawai wannan hatimin haske dake kan damtsenka zaka shafa da wannan niyya." Isika ya ce.
Marganu ya gyaɗa kai cikin fahimta ya ce, "Na fahimce ka. Yanzu sai kayi mana bayanin abubuwan da zamu nemo wajen kawar da sarki Kuffuru daga doron duniya?"
Aljani Isika ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Kamar yadda gimbiya ta amsa mana waɗannan tambayoyi ɗazu. Sarki Kuffuru da abubuwa guda uku yake taƙama; aljani Shiyyu, Siwod-del-bulod da kuma mataki na takwas a harkar tsafi.
"Kamar yadda na faɗa muku ɗazu, takobi guda ɗaya ce zata iya kashe aljani Shiyyu Djinn. Idan har ba mu mallaki wannan takobi ba, babu yadda za'ayi mu iya yin nasara akan sarki Kuffuru.
"Wannan takobi kuma da ita Marganu zaiyi amfani wajen karawa da sarki Kuffuru gaba-da-gaba ba tare da halittu guda talatin na takobin Siwod-del-bulod sun illata shi ba.
"A halin yanzu Marganu a mataki na uku kake a harkar tsafi, kaga kenan, ba zaka iya karawa da mai mataki na takwas ba. Amma, idan ka sha tsumin tsafin boka Rohishmu a take zaka kai mataki na bakwai. Meye bambancin tsakanin bakwai da takwas?
"Takobin da zata iya hallaka aljani Djinn kuma ta iya yin gaba-da-gaba da Siwod-del-bulod mallakin wani gagarumin mayaƙi ne kuma boka da yayi zamani shekaru aru-aru da suka shuɗe. Wannan boka kuma mayaƙi ya kira kansa da suna SADAUKI GAYAWA-JINI.
"Gayawa-jini baƙin fata ne, a nahiyar baƙaƙen fata ya taso. Wannan takobi Gayawa-jini ya kirata da suna tarwatsa-komai. Ba don komai ya saka mata wannan suna ba, sai domin duk abinda aka sara da wannan takobi tarwatsewa yake tamkar an saka masa nakiya.
"Kun san cewa babu irin makamin ƙarfen da zaiyi tasiri akan dutse, amma, kun san dutse yana iya tarwatsewa yayi daga-daga. Kamar haka ne, babu irin makamin ƙarfen da zai iya hallaka aljani Djinn, amma ko ya ya aka sari jikinsa da takobin tarwatsa-komai bindiga zaiyi ya tarwatse.
"Saboda haka dole ne kuyi shiri ku tafi har zuwa nahiyar baƙaƙen fata domin ɗauko wannan takobi wacce sadauki Gayawa-jini ya ajiye a cikin wani gidan tarihi na wani birni da ya jima da rushewa, ko kuma nace, ya jima da zamowa mallakin waɗansu halittu masu shan jini."
Marganu ya dubi Isika ya ce, "Ka faɗa mana amfanin wannan takobi amma baka faɗa mana nisan tafiyar da zamu shafe kafun muje wannan birni ba, sannan baka faɗa mana haɗarurrukan dake kan hanƴa ba. Wai shin ma wanne birni ne wannan da zamuje kuma waɗanne irin halittu ne suka mamaye birnin?"
Aljani Isika yayi murmushi cikin jin daɗin wannan tambaya da Marganu yayi masa, dama da saninsa ya ɗan yi shuru domin ya baiwa Marganu damar yin wannan tambaya.
"Wannan birni da sadauki Gayawa-jini ya ɓoye wannan takobi, ana kiran birnin da suna Temisa. Daga wannan wuri da muke zuwa birnin Temisa tafiya ce ta tsahon wata uku, koda kuwa akan aljanin da yafi kowanne aljani sauri a duniya mutum zaije.
"Sannan sai mutum ya ratsa ta cikin gari-gari har guda bakwai, kuma akwai dazuzzuka masu mugun-haɗari da mutum zai bi ta cikinsu kafun mutum ya riski garin Temisa. Babu wanda ya taɓa ratsawa ta cikin waɗannan garuruwa guda bakwai ballantana a san haɗarurrukan dake cikin su.
"Amma, a yadda masu hasashe suke bayar da labari shi ne, ƙabilun arnan-daji ne masu yawan gaske a cikin waɗannan garuruwa shiyasa aka rasa mahaluƙi guda ɗaya da zai iya ratsawa ta cikin su.
"Su kuwa waɗannan dazuzzuka da mutum zai ratsa ta cikinsu babu komai a cikinsu face muggan namun-dawa marasa adadi. Idan mutum ya wuce waɗannan garuruwa guda bakwai da dazuzzukan nan zai riski birnin Temisa.
"Babu komai a cikin wannan gari na Temisa face waɗansu irin halittu. Halittun tamkar mutane haka suke amma kawunansu na dabbobin daji ne. Zaka ga murɗaɗɗen jiki na mutum amma da kan damisa ko zaki. Waɗannan halittu basu da abinci da abinsha face jini da naman mutane.
"Dole ne mu ratsa ta cikin waɗannan garuruwa guda bakwai sannan mu ƙetare waɗannan dazuzzuka domin mu isa gidan tarihi na birnin Temisa mu ɗauko takobin Tarwatsa-komai. Idan babu mai tambaya a cikin ku, zan yi mana bayani akan inda za'a je a sami tsumin boka Rohishmu."
Marganu ya tari numfashinsa ya ce, "Ka ce daga wannan wuri zuwa Temisa tafiya ce ta watanni uku kuma koda mutum zaiyi tafiya akan aljani saiya shafe watanni ukun. Ya aka yi haka ta kasance?"
Aljani Isika ya yi murmushi ya ce, "Waɗannan garuruwa guda bakwai su ne amsar tambayarka. Garuruwa guda uku na farko a haɗe suke, kana wuce su zaka riski garuruwa guda huɗu na ƙarshen. A tsakanin waɗannan garuruwa - uku na faro da huɗu na ƙarshe anan zaka riski waɗannan dazuzzuka. Waɗannan wurare guda bakwai suna da tsananin kafi irin na matsafan farko. Shiyasa babu wanda ya isa ya ƙetare su ta sama, dole sai dai mutum ya ratsa ta cikin su. Akwai wata tambayar?"
Marganu ya jinjina kai cikin fahimta ya ce, "Babu wata tambaya, kawai kayi mana bayanin tsumin boka Rohishmu."
Isika ya yi murmushi ya ce, "Daga nan zuwa wajen da wannan tsumi yake tafiya ce ta wata guda kacal. Sannan har mutum ya riski wannan waje ba zai haɗu da komai na hatsari ba. Kogon da aka ajiye wannan tsumi a cikinsa ma, ba shi da wani haɗari, hasalima mutane da yawa sun kai masa ziyara. Amma, har yau har gobe ba'a samu wanda ya taɓa amfani da wannan tsumi ba. Kun san meyasa?"
Marganu, Firziyya da Aydenlik suka girgiza kai alamun, a'a.
"Saboda tukunƴar da aka zuba wannan tsumi a cikinta da wani irin ƙarfe aka haɗata. Wannan ƙarfe ana kiransa da suna ilumni. Ƙarfen ilumni a tsakiyar wata teku ake samo shi bisa wani ɗan mitsitsin tsibiri. Da zarar halitta mai jini ta taɓa wannan tukunƴa ta ƙarfe, nan take ilumni zai zuƙe jinin halittar sannan ta faɗi a wannan wuri matacciya.
"Duk duniya babu wanda ya isa ya iya taɓa wannan tukunƴa face ni ko kuma Marganu. Duk wanda ya taɓata kuma, mutuwa zai yi. Abinda yasa ba zata iya zuƙe jininmu ba, shi ne zamu iya juyar da jikinmu izuwa haske.
"Wannan na ɗaya daga cikin manƴan amfanin Isik, watau juyar da jiki izuwa haske. Indai jikin mu yana haske babu wani makami ko sihiri da zaiyi tasiri akan mu. Abubuwa guda uku ne kawai zasu iya yin tasiri akan mu. Na farko Siwod-del-bulod ta sarki Kuffuru, na biyu takobin Saiful Shiradu wacce take hannun sarki Kuffuru a yanzu, cikon na ukun nasu shi ne makaman yaƙin sarki Samudul Ansari dake cikin kogon tsafinsa a ajiye. Waɗannan abubuwa guda uku su ne kawai makaman yaƙin da zasuyi tasiri akan mu.
"Kaga kenan, sarki Kuffuru maƙiyin mu ne, zai iya amfani da makaman yaƙin nan guda biyu (Siwod-del-bulod da Saiful Shiradu) ya yaƙe mu. Sannan ga Aymanul Faris wanda bai da buri face mallakar ruhin Samudul Ansari da makaman yaƙinsa. Kaga kenan, idan ya mallaki waɗannan makaman yaƙi shima zai iya zamowa babban maƙiyinmu.
"Uwa-uba kuma, yana soyayya da gimbiya Jaanu. Kaga kenan, zaka iya cewa Aymanul Faris ne sanadiyar da yasa gimbiya ta ƙi karɓar soyayyarka, duk wahalar da ka sha ta tashi a banza. A ƙarshe har ta kai ga cewa ka rasa mahaifinka."
Marganu ya murtuƙe fuska baƙin cikin abinda ya faru a baya, ya fara taso masa. Jikinsa ya fara tsuma, jijiyoyin jikinsa suka kukkumburo. A da idan ya fusata, idanuwansa jajawur suke yi. Amma yanzu da ya fusata wani irin haske ne mai ɗaukar hankali ya fara fita daga cikin idanun nasa.
"Ai idan na gama da sarki Kuffuru, sarki Ayubu da gimbiya Jaanu kan Aymanul Faris zan koma, domin kuwa saiya biya wahalar da na sha masa lokacin da na mayar masa da mahaifiyarsa, sannan saiya biya sace gimbiya Jaanu da yayi." inji Marganu cikin ƙololuwar fusata irinta mazajen ƙwarai.
Aljani Isika ya yi murmushi. "Gaba zamu tattauna akan wannan lamarin. Yanzu idan kun fuskanci bayanan da nazo muku da su, ina so ku tafi izuwa garin Temisa domin ɗauko wannan takobi."
Isika yana zuwa nan a zancensa, jikinsa ya zamo haske ya ɓace ɓat daga cikin wannan fada.
Marganu ya dubi Aydenlik ya ce, "Kaimu garuruwa uku na farko daga cikin waɗannan garuruwa guda bakwai."
Aydenlik ya yi murmushi sannan ya doki iska da hannunsa, nan take su ukun suka rikiɗe suka zamo farin-haske. Hasken ya ɓace daga cikin wannan fada.
***
#######RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 48: *Tambayoyi masu amfani*
*

*
UMAR SANGARU
*
Barban da Aymanul Faris suna fitowa daga cikin gidan Tameer, suka wuce kai tsaye izuwa bakin wannan kogi inda Barban ya ƙyale wannar kwale-kwale. Da zuwansu ba tare da ɓata lokacin komai ba, suka shiga cikin kwale-kwalen.
Barban ya waina wannan mawani dake tsakiyar kwale-kwalen ta fara tafiya a hankali kafun daga bisani ta fara tsala azababben gudu tana keta ruwa, suka baiwa garin Rildaz baya.
Tsahon sa'a uku cir suna ta tafiya, ba tare da ɗayansu ya ce uffan ba. Shi Barban hankalinsa ya karkata akan tuƙin wannan jirgi da yake yi, shi kuma Aymanul Faris wannan littafin ya fiddo yana nazarin waɗansu abubuwa.
Can dai ya numfasa ya dubi Barban ya ce, "Ina da tambayoyi da yawa daga cikin littafin tarihin sarki Kuffuru amma ban samu damar yi maka su ba, saboda ba mu samu zama ba sai a yanzu."
Barban ya ɗan waiwayo ya ce, "Faɗi dukkanin tambayoyin ka, zan kasance mai amsa maka."
"Yauwa," inji Aymanul Faris. "Tayaya aka yi takobin Saiful Shiradu ta salwanta daga hannun mahaifina? Tayaya aka yi sarki Kuffuru ya rasa matarsa? Meyasa aka daina batun Auran Ziyas kwata-kwata a ƙauyenmu, bayan yayi mana muguwar lamba wacce ba zata goge ba. Ina aljani Nara yake a halin yanzu? Meyasa sarki Kuffuru ya daina amfani da takobin Siwod-del-bulod a yanzu? Duk waɗannan tambayoyi da na zayyano maka babu amsoshinsu a cikin wannan littafi."
Koda Barban yaji waɗannan tambayoyi sai yayi murmushi ya ce, "Waɗannan tambayoyi su ne dalilin da yasa aka ce ka karanta wannan littafi har ƙarshen sa. Lallai kayi ƙoƙari da ka iya zaɓo tambayoyi masu muhimmanci haka a cikin wannan littafi, kuma lallai kana da tsananin hikima da zurfin nazari.
"Amsar tambayar ka ta farko; yadda aka yi takobin Saiful Shiradu ta salwanta shi ne, mahaifinka da mahaifiyarka suna kwance suna barci, ɗan ƙanin mahaifinka ya shigo cikin wannan gida nasu ya saceta ya gudu. Ba don komai ya sace wannan takobi ba, sai domin ya samu labarin wata gasar-jarumtaka da za'a gudanar a watanni masu zuwa a birnin Hadriyan. Idan baka manta ba, na taɓa baka labarin wannan gasa ta jarumtaka wadda na ce maka a birnin Kufa aka gudanar da ita, har sadauki Sharr ya hallaka wannan baƙon jarumi. Sarki Kuffuru ya mallaki takobin saiful-shiradu a banza.
"A zahirin gaskiya a wancan lokacin ba'a birnin Kufa ya dace a yi wannan gasa ba, a birnin Hadriyan ne. Amma, da sarki Kuffuru ya samu labarin akwai jarumin da ya taho daga tsibirin Gazwar kuma yazo ne tare da takobin Saiful Shiradu, sai farin ciki ya kama shi, ya kirawo alƙalan wannan gasa ya basu umarnin dawo da gasar izuwa birninsa. Alƙalai suka yi yadda ya ce, aka dawo da wannan gasa birnin Kufa.
"Duk da haka sarki Kuffuru bai haƙura ba, sai da yayi shiri ya tafi har saman wani dogon tsauni inda wani ƙasurgumin ɗan fashi yake rayuwa, ana kiran wannan ɗan fashi da suna Hafaru. Kuffuru ya ɗakko hayar Hafaru ya biya shi kuɗaɗe masu yawan gaske, sannan yasa aljani Djinn ya tsuma shi da tsumin tsafi mai ƙarfin gaske, shima yazo a matsayin jarumin gasa ya sauya suna, ya ce sunansa Sharr.
"Tunda Jillas Kuyuru ya fara wannan gasa kullum idanun sarki Kuffuru na kansa, Kuffuru ya gama nazarin salon yaƙinsa da ƙarfin tsafinsa, kafun wasan ƙarshe yazo sarki Kuffuru ya gama yiwa Jillas shiri. Ana fara wannan wasa na ƙarshe tsakanin sadauki Sharr da Jillas Kuyuru, aka ga Sharr ya fille kan Jillas Kuyuru. Kowa da ke wannan wuri sai da ya cika da tsananin mamaki saboda muhimmiyar rawar da sadauki Jillas ya taka a wannan gasa bai kamata ace anyi masa kisan farat ɗaya ba.
"Abinda mutane basu sani ba shi ne, sarki Kuffuru ne yayi wani baƙin tsafi irin na ƙabilar Gandiz ya tsayar da Jillas Kuyuru a waje ɗaya, ya baiwa Sharr damar fille masa kai cikin sauƙi.
"Dama ƙa'idar wannan gasa shi ne, duk jarumin da ya mutu a wannan gasa, dukiyarsa da makaman yaƙinsa duk sun zamo mallakin sarkin da aka gudanar da gasar a birninsa, kamar dai yadda na faɗa ma kwanaki.
"Wannan shi ne yadda aka yi takobin Saiful Shiradu ta salwanta. Na amsa tambaya ta farko.
"Amsar tambayarka ta biyu; yadda aka yi sarki Kuffuru ya rasa matarsa shi ne, na san ka karanta a cikin wannan littafi lokacin da aka yi mugun gamo tsakanin sarki Kuffuru da mahaifinka. Koda sarki Kuffuru yaga bala'in da mahaifinka ya samar sunyi yawa, saiya kirawo ɗalasimin Gandiz wannan farar dusar ƙanƙara ta fara sauƙa a wurin. Amma, wannan dusa ta ƙanƙara bata rage komai a wurin ba, ana tsakiyar fafatawa dai, har takobin Mahaifinka, ta kusa ta hallaka sarki Kuffuru amma sai aljani Djinn yazo cece shi.
"Na san ka ji aljanin yana cewa sanadiyar bari da yayi waɗannan hare-hare suka dira a jikinsa yasa ya rasa kaso hamsin na ƙarfinsa hakane?"
Aymanul Faris ya gyaɗa kai ya ce, "Lallai anyi haka."
"To, ana nan, ana nan. Sarki Ratanam da sarki Ayubu suka bayyana a wannan daula, su ma suka kafa biranensu. A da can kasan cewa wannan daula gaba ɗaya ƙasa guda ɗaya ce, amma da sarki Ayubu da sarki Ratanam suka bayyana sai aka raba ƙasashen uku masu shugabantar wannan nahiya.
"A sirrance sai da sarki Kuffuru ya kaiwa waɗannan sarakuna guda biyu harin-sumame domin ya hallaka su amma baiyi nasara ba, dukda cewa yana da aljani Djinn da takobin Siwod-del-bulod.
"Da ya faɗawa aljani Djinn wannan magana, Djinn ce masa yayi don ya rasa kaso hamsin na ƙarfinsa ne, yasa baiyi nasara akan waɗannan sarakuna guda biyu ba. Kuffuru ya ce to tayaya kaso hamsin ɗin zai dawo. Djinn ya ce dole a ba shi jinin ƴar ƙabilar Gandiz yasha.
"Wannan shi ne dalilin da yasa sarki Kuffuru ya salwantar da rayuwar matarsa ya baiwa aljaninsa jininta, dukda cewa a wannan lokaci tana da jaririya ƙarama mai shan nono. Na amsa tambaya ta biyu.
"Amsar tambayarka ta uku ita ce, Hasanul Jalwar ne yasa aka daina batun Auran Ziyas a ƙauyen Gazwar, saboda ta tabbata dai, Auran Ziyas shi ne sarki Kuffuru. Hasanul Jalwar baya so mutanen wannan ƙauye su gano haka, wasu daga cikin su suyi tunanin kaiwa Kuffuru hari, saboda baza su yi nasara ba. Wannan shi ne dalilin da yasa aka daina batun Auran Ziyas a ƙauyen Gazwar.
"Lokacin da aljani Nara ya fuskanci cewa, sarki Ayubul Zairiy ya aiko wasiƙa amma maimakon Hasanul Jalwar yazo yayi shawara da shi, sai ya yanke hukunci da kansa. Wannan abu ya ɓatawa aljani Nara rai yasa ya tashi daga ƙauyen Gazwar ya koma asalin gidansa dake birnin Shaha a cikin gidan sarautar sarki Al-Khamis.
"Har aka gama wannan yaƙi aljani Nara bai bayyana ba, amma yayi baƙin ciki matuƙa da aka kashe mutanen ku. Yanzu haka yana can asalin birnin Shaha a wani gida na ƙarƙashin ƙasa kullum cikin jiran zuwan mutumin da ruhin jarumtaka ya zaɓa a matsayin magajinsa yake. Na amsa tambayoyi huɗu.
"Maganar gaskiya ban san dalilin da yasa sarki Kuffuru ya daina amfani da takobin Siwod-del-bulod ba. Wataƙila akwai abinda yake jira yayi amfani da takobin."
Barban na gama amsa waɗannan tambayoyi ya juya ya ci gaba da tuƙi, shi kuwa Aymanul Faris yayi shuru yana ta nazarin waɗannan amsoshi na Barban.
Haka dai suka ci gaba da tafiya a cikin wannan kogi, Aymanul Faris yana ta yiwa Barban tambayoyi shi kuma yana ta amsa masa. Har tsahon kwanaki bakwai suna tafiya, idan sun gaji sai su sami tsibiri su zauna, su huta.
A ranar kwana ta bakwai

Please Login or Register in order to submit comment