Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

murna ya ce, "Na rantse da kabarin mahaifina yanzu aka fara. Babu abinda ke tsakanina da jinin Samudul Ansari in banda kisa. Babu gudu babu ja da baya."
Hasamul-Sawaz ya sake ɗaukar su Kuffuru ya mayar dasu birnin Kufa, sannan yayi sallama dasu ya ɓace. Ya ce duk lokacin da sarki Kuffuru ke buƙatar ganinsa kawai yaje bayan gari ya ƙwala masa kira sau uku.
Washe gari, sarki Kuffuru ya kira wani gagarumin taro na dukkanin sarakunan dake ƙarƙashin mulkinsa. Babu birni babu ƙauye. Duk wanda ke riƙe da muƙami komai ƙanƙantarsa sai da sarki Kuffuru ya tura a kirawo shi.
Musamman aka shirya wani ƙaton ɗakin-taro wanda aka cika da kujeru aƙalla dubu, daga can ƙarshensu kuma aka ajiyewa sarki Kuffuru wata karagar mulki ta musamman.
Ɗakin taro ya cika ya batse da masu-faɗa-aji, kowa ya yiwo wanka yana jiran zuwan babban sarki. Sarki Kuffuru.
Tsahon ɗan lokaci sannan Kuffuru ya shigo cikin ɗakin taron, shi ɗaya jal ba tare da dakaru masu tsaron lafiyarsa ba. Ya karasa kan wannan karaga ya zauna, ya yiwa waɗannan sarakuna barka da zuwa, kuma ya gode musu bisa amsa wannan kira nasa.
"Abinda yasa kuka ga na kirawo ku wannan taro shi ne..." Ya saisaita maƙwagoronsa kafun ya ci gaba.
"Ni ɗinnan da kuke kallo ɗan asalin birnin Shàha-Meher ne, waye a cikin ku bai san wannan birni ba?" Gaba ɗaya sarakunan suka yi shuru, babu mai magana.
"Kamar yadda kowa ya sani, babu yadda za'ayi ka zamo sarki ɗan sarki. Ba tare da ka samu abokan gaba ba, kamar yadda kowannenku ya san tarihin yaƙin da aka gwabza. Anyi yaƙin ne tsakanin ɗan uwan mahaifina da mahaifina, a zahiri mahaifina bashi da laifin komai. Wannan ɗan uwa nasa shi ne ya tsokalo shi yasa aka sato matar mahaifina sannan ya fille kanta. Meyasa nake baku wannan labari? Abinda nake baku wannan labari shi ne, INA SO NA SHAIDA MUKU CEWA DAGA YAU NA ƘULLA ANIYAR YAƘI DA MUTANEN ƘABILAR BANU KUYURU. Na rantse da jinin mahaifina da ya zuba, daga yau babu abinda ke tsakanina da waɗannan mutane in banda kisa. A matsayina na sarkin wannan birni, na bayar da umarnin duk inda aka kalli ɗan ƙabilar banu Kuyuru walau a cikin gari ko daji a kamo shi a kawo min shi fadata. Duk wanda yai nasarar kamo koda mutum ɗaya ne, zai sami kyautar dinare miliyan guda.
"Na ƙulla aniyar ƙarar da waɗannan shaiɗanu masu haddasa fitina a duniya, kuma na rantse sai na ƙarar dasu. Wannan shi ne dalilin kiranku wannan taro; NI SARKI KUFFURU DAGA YAU NA BAYAR DA UMARNIN KAMO ƳAN ƘABILAR BANU KUYURU a ko'ina aka kallesu a yankin wannan ƙasa tawa.
"Duk mutum ɗaya ladarsa dinari miliyan ɗaya, idan ka kamo mutum dubu. Zaka samu kyautar har dinari miliyan dubu. Wannan alƙawari ne."
Gaba ɗaya mutanen dake cikin wannan ɗakin-taro sai da suka gigice sakamakon jin kalaman sarki Kuffuru, kuma suka cika da tsananin mamaki amma babu wanda ya isa ya ce masa MEYASA YAKE SO YA ƘARAR DA SU?
Wata kyakkyawar mace mai dogon gashi ta dubi sarki Kuffuru ta ce, "Ya kai wannan sarki, mun ji umarninka kuma zamuyi biyayya amma tayaya zamu iya shaida ƳAN ƘABILAR BANU KUYURU?"
Kuffuru ya dubi matar ya ce, "Mutanen ƙabilar banu Kuyuru dabam suke da sauran mutane. Hasken fatar jikinsu ta dabam ce. Baƙin gashin dake kansu na dabam ne. Murɗewar jiki da sura ta sadaukantaka tasu duk dabam take da ta sauran mutane. Duk inda ku kalli mutum FARI MAI BAƘIN GASHI DA MURƊAƊƊEN JIKI ku kamo shi, ku kawo shi fadata. Ina so wannan umarni nawa ya karaɗe dukkanin yankin wannan ƙasa. Babu birni ba ƙauye wannan shi ne dalilin da yasa na kira kowa da kowa. Amma kafun nan kada ku manta ladar - duk mutum ɗaya daidai yake da dinari miliyan ɗaya."
Da wannan batu sarki Kuffuru ya sallami dukkanin waɗannan sarakuna amma sai ya nemi da wannan mace da tayi masa wannan tambaya ta tsaya, yana da magana da ita. Saboda yayi mamakin ƙarfin zuciyarta da har zata iya magana a gaban babban sarki kamarsa.
******RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 33: *Saiful Shiradu (2)*
*
*
✍️✍️✍️Umar Sangaru ✍️✍️✍️
*
A can ƙauyen Gazwar kuwa, bayan an gama binne waɗannan dakaru guda hamsin da rayuwarsu ta salwanta a rakiyar attajiri Auran Ziyas sai shugaba Hasanul Jalwar da manyan wannan ƙauye suka yi zama na musamman domin tattaunawa akan abinda yayi ajalin har dakarun guda hamsin. A cikin wani ɗaki suka zazzauna gaba ɗayansu, kuyangi suka kawo musu abinci da abinsha kala daban-daban. Bayan kowa ya gama kimtsa cikinsa an samu nutsuwa.
Shugaba Hasanul Jalwar yayi gyaran murya ya ce, "Da farko ina jajanta mana bisa wannan gagarumin rashi da muka yi, kuma da izinin maigirma Samud zamu gano wanda yayi mana wannan ɗanyen-aiki har mu hukunta shi. Wannan abu na da ban mamaki tsahon shekara arba'in da bakwai da wanzuwar mu a wannan tsibiri, ko sau ɗaya ba'a taɓa kawo mana hari ba, ko sau ɗaya ba'a taɓa yiwa dayanmu sata ba. A ce a rana guda har mun rasa mutum hamsin? Anya wannan kisa bata da alaƙa da wannan baƙon attajiri kuwa?"
Wani dattijo mai yawan gemu da dogon gashi ya ce, "Ya shugabana, mutuwar waɗannan ƴaƴa namu abin dubawa ne. Abu na farko kisan da aka yi musu duk kala ɗaya ne, kowannensu a ƙahon-zuciyarsa aka caka masa wuka. Kada muyi saurin zargin Auran Ziyas saboda shima bamu san wanne hali yake ciki ba, kuma zai yi wuya mutum daya ya iya hallaka mutane hamsin a cikin wannan ƙanƙanin lokaci kuma ace duk kisan da yayi musu kala ɗaya ne. Idan muka fuskanci Auran Ziyas attajiri ne wanda yake zuwa tsibirurruka daban-daban yana fatauci sannan ya ɗauki hajarsa ya koma garinsu ya sayar. Duk inda kuka kalli attajiri mai irin wannan dukiya ta Auran Ziyas tabbas muggan ƴan fashi suna fakonsa, kuma suna biye dashi a duk inda yake. Da zarar suka sami dama to tabbas afka masa zasuyi da yaki su hallaka shi sannan su kwashe dukkanin dukiyarsa."
Hasanul Jalwar ya dubi dattijon mutumin ya ce, "Tabbas maganarka haka take Amsar, amma kayi sani cewa ko buhu daya daga cikin dukiyar Auran Ziyas ba'a ɗauka ba. Wannan ya tabbatar mana zaiyi wuya idan ƴan fashi ne suka farmake su. Koma dai mene ne yau zanje na gana da aljani Nara naji abinda zai ce." Daga wannan batu wannan zama nasu Hasanul Jalwar yazo ƙarshe suka ajiye magana akan Hasanul Jalwar zai je ya sanar da aljani Nara abinda ya faru.
Bayan sun gama watsewa Hasanul Jalwar ya miƙe tsaye ya shige cikin gidansa, bai tsaya a ko'ina ba sai a cikin wannan ɗaki inda ƙofar wannan gida na ƙarƙashin ƙasa take. Ya sunkuya ya buɗe ƙofar sannan ya tattaka waɗannan matattakala yayi ƙasa ya shige cikin gidan.
Yana shigowa cikin gidan ya wuce bakin wannan ƙaton rami ya tsaya, faruwar hakan keda wuya siffar aljani Nara ta bayyana a cikin wannan wuta.
"Wane ne ya kashe min dakaru har guda hamsin?" inji Hasanul Jalwar.
Aljani Nara ya yi shuru yana ƙura masa idanu, ya sake tambayarsa har sau uku amma aljanin bai ce ƙala ba.
Daga bisani ya buɗi baki ya ce, "Mutum ɗaya ne ya hallaka waɗannan dakaru guda hamsin da aka kashe, amma nayi iya bincikena akan na gano wayene na gagara. Ko ma dai waye shi tabbas yana da haɗari sosai, kuma wani babban shiri yake akan ahalin maigirma Samúdúl Ansari."
Hasanul Jalwar ya haɗe fuska ya ce, "Baka san waye shi ba? Na tabbata basu wuce LUSLEL ba, kuma ka ce duk abinda ke tsakanin LUSLEL da wannan ƙauye namu kana ganinsa, ya akai haka?"
Aljani Nara ya jinjina kai ya ce, "Hakane, duk abinda ke tsakanin wannan wuri yana kan idanu na. Amma abinda baka fuskanta ba shi ne da wani baƙin sihirin tsafi aka yi amfani aka ɓoye duk abinda ya faru a wannan wuri, kuma aka rufewa waɗannan dakaru idanunsu har aka gama abinda aka yi. Ka bani lokaci kaɗan, zan binciko mana dukkan abinda ya faru sannan na sanar da kai."
Hasanul Jalwar ya murtuƙe fuska ya ce, "Nifa hankalina bai kwanta da wannan baƙon attajiri ba, kuma shi nake zargi."
Aljani Nara ya jinjina kai ya ce, "Tabbas Auran Ziyas abin zargi ne, amma na tabbata idan shi ne ya aikata wannan ɗanyen-aiki zai dawo, ba don komai ba sai domin ci gaba da aikin da yake. Mu jira mu gani zuwa watanni uku, idan ya dawo to tabbas shi ne, idan kuma bai dawo ba kafun nan zan gama bincike na gano ko waye ne."
****
A daidai wannan lokaci da Hasanul Jalwar da aljani Nara ke tattaunawa akan wanda ya kashe dakarunsu guda hamsin, a birnin Kufa kuma wata zama ta musamman ce ke gudana tsakanin sarki Kuffuru da wannan baƙuwar mace, wacce tayi masa tambaya ɗazu a ɗakin-taro. Dukkaninsu suna zazzaune kan ƙasaitattun kujeru na alfarma sun saka wani teburin ƙarfe a tsakiya, wanda aka ajiye waɗansu kofunan zinari akansa.
Wannan mace ta kasance doguwa kyakkyawa, tana da dogon gashi baƙi da dara-daran idanu. Tana sanye da doguwar riga baƙa mai beza ta wuya.
"Ya sunanki?" inji sarki Kuffuru.
"Suna na sarauniya Anisa mai mulkin ɓangaren arewa na wannan ƙasa." Ta amsa cikin zazzaƙar murya mai ɗimauta mai sauraro.
Sarki Kuffuru ya yi murmushi ya ce, "Ashe ke ce Anisan da ake bani labarin babu mace mai kyawunta a duk faɗin ɓangaren arewa?"
Sarauniya Anisa ta sunkuyar da kanta ƙasa tana murmushi, ga dukkan alamu ta kusa samun babban matsayi. A duk faɗin birnin Kufa babu matar da bata da burin ta auri sarki Kuffuru, saboda a wannan lokaci yana kan ganiyar ƙuruciyarsa. Na farko ga shi kyakkyawa, ga murɗaɗɗen jiki, ga mulki ga dukiya. Babu abinda mace zata nema bata samu a wajen Kuffuru ba, in dai a ɓangaren namijin aure ne.
"Ni ce." inji Anisa.
Sarki Kuffuru ya sake yin murmushi ya kamo hannunta yana shafawa ya ce, "Kin san dalilin da yasa nace ki tsaya ina so na gana da ke?" A karon farko sarauniya Anisa ta ɗago kanta ta kalli fuskarsa ta ce, "A'a."
Sarki Kuffuru ya ci gaba da matsa tattausan hannunta ya ce, "Lokaci yayi da zan nemi matar aure, amma kafun na aureta sai na gwada ƙarfin ruhinta ta hanyar jima'i. Saboda idan nayi kuskure na auri wadda jininta bai da ƙarfi babban burina na duniya zai ruguje. Ke ƴar wacce ƙabila ce?"
Sarauniya Anisa ta zare hannunta daga cikin nasa, cikin rashin fahimta ta ce, "Ban gane jima'i kafun aure ba, kana nufin dani zaka tara don ka gwada ƙarfin ruhina? Wannan wacce irin maganar rainin hankali ce, idan ruhin bai yi ƙarfin da ake buƙata ba fa?"
Sarki Kuffuru ya yi shuru ya bi sarauniya Anisa da kallo kawai, yana ji a jikinsa lallai wannar babu buƙatar gwaji ruhinta zaiyi.
"Faɗa min sunan ƙabilar ta ki?" Ya ce.
Sarauniya Anisa tayi ajiyar numfashi ta tuna wanda ke zaune a gabanta, ta ce, "Ni ƴar ƙabilar Gandiz ce."
Sarki Kuffuru ya yi murmushi ya ce, "Ƙabilar Gandiz? Ko za ki iya bani labari kaɗan daga cikin ƙarfin wannan ƙabila?"
Anisa ta yi murmushi a karon farko ta ce, "Kalmar Gandiz ta samo asali ne daga wani tsohon yaren wasu mutane dake rayuwa a saman wani ƙaton dutse, ana kiran yaren Hézér. Kalmar tana nufin 'ƙarfin iko' a wannan yare na Hézér. Duk ɗan ƙabilar Gandiz yana da wani ƙarfin iko wanda yake amfani dashi wajen cin galaba akan abokan gabarsa, iya ƙarfin jinin Gandiz a jikin mutum iya ƙarfin wannan iko. Wani ɗalasimin tsafi ake kira a tsayar da abokin gaba da komai dake wannan wuri, hakan zai bawa ɗan ƙabilar Gandiz dama yayi duk abinda yaso akan wannan abokin gaba, ba tare da wannan abokin gaba yasan abinda ya faru ba."
Koda jin wannan batu sai sarki Kuffuru yai dariya ya ce, "Babu buƙatar gwaji ta hanyar jima'i, ke ce matar da na daɗe ina jira tun daga hawana kan wannan karaga ta mulki. Abinda nake so dake shi ne ki koma birninki ki fara shirin ZAMOWA MATAR BABBAN SARKI. Nan da cikar watanni uku za'ayi gagarumin biki irin wanda aka jima ba'a gani ba, zan zamo mijinki ke kuma matata."
Sarauniya Anisa na gama jin kalaman sarki Kuffuru ta miƙe ta faɗa kan ƙirjinsa suka rungume juna. Tun da sarauniya Anisa take bata taɓa tunanin auran babban sarki kamar Kuffuru ba. A ce duk girman birnin Kufa ya dawo ƙarƙashin ikonta wace ce zata ƙi wannan tayi? Matar sarki, sarauniya ce.
Kafun cikar watanni uku tuni labari ya gama karaɗe dukkanin ƙasashen dake wannan nahiya, kai har ma da na ketare. Kowa ba shi da burin da yafi yaga auren SARKI KUFFURU da SARAUNIYA ANISA domin ansan za'ayi gagarumin biki irin wanda ba'a taɓa kamarsa a birnin Kufa ba. Tuni birnin Kufa ya cika ya batse da baƙin sarakuna waɗanda suka amsa gayyata daga ɓangarori daban-daban na duniya.
Da ranar biki tazo aka cika gidan sarautar sarki Kuffuru gaba ɗaya da kayayyakin ado na zinari da tagulla. Taro yayi taro, malaman dake ɗaura aure suka hallara.
A al'adar aure ta wancan zamanin ta ƴan ƙabilar Gandiz, ango ne zai sami ƙaton gatari aka kawo masa ƙaton bujumi ya fille kan bujumin, ana so jinin wannan bujumi ya wanke sawayen wani gunki. Da zarar anyi hakan sai ango da amaryar su zube a gaban wannan gunki suyi sujjada, indai suka yi haka AURE YA ƊAURU A TSAKANINSU.
To, amma abun mamaki kowa ya gama hallara a wannan wuri, daga kan amarya har zuwa kan masu ɗaura aure amma shuru babu ango Kuffuru babu labarinsa. An duba gaba ɗaya cikin gidan sarautar baya nan, an duba cikin gari ma bayanan.
Dakarun da suka je nemansa suka shigo wurin ɗaurin auren, suka ce basu ganshi a cikin gari ba. Babban malamin garin ya dube su ya ce, ku je cikin daji ku duba mana.
Waɗannan dakaru basu da ikon cewa, a'a, don haka sai suka risina suka fice daga cikin gidan sarautar suka yanki daji. Tsahon rabin sa'a kacal, suna tafiya suka fara jiwo ƙarar sauƙar aradu daga can nesa cikin wani daji. Wannan abu yayi matuƙar basu mamaki domin a wannan rana, rana ta gama ɓallewa kamar zata gasa mutane. Ko alamun gajimare guda ɗaya babu a sama balle ayi tunanin jin tsawa. Shugabansu ya ce su ƙara azama su dubo abinda ke faruwa cikin wannan daji.
Abin mamaki suna ƙara matsowa gaba ƙarar wannan aradu tana ƙaruwa, kuma wata siffa ta wani aljani mai jikin duwatsu na bayyana. Koda ya rage saura baifi taku arba'in su shiga cikin wannan daji ba, wannan halitta mai jikin dutse ta juyo tayi musu wani kallo mai cike da ma'ana.
Take waɗannan dakaru gaba ɗayansu suka zubo ƙasa daga kan dawakansu, suka fara karkarwar razana. Idan zasu iya tunowa a waje guda ɗaya suka taɓa yin arba da wannan siffa, ba'a ko'ina bane sai a lokacin da aka yiwa sarkinsu juyin mulki aka ɗaura sarki Kuffuru.
A cikin wannan daji kuma, sarki Kuffuru ne da aljani Buƙalshiyu Djinn ke tattaunawa akan auren Anisa da kuma sake komawa izuwa ƙauyen Gazwar.
"Ka san meyasa na ce maka, dole sai ka auri ƴar ƙabilar Gandiz kafun ka sami nasarar ƙarfafa jininka yadda zaka sake komawa ƙauyen Gazwar ba tare da ka fuskanci wata matsala ba?" Aljani Buƙalshiyu Djinn ya tambayi Kuffuru.
Sarki Kuffuru ya ce, "Babu abinda na sani, face wanda ka sanar dani."
Buƙalshiyu Djinn ya yi dariya yace, "Akwai wani shaiɗanin aljani a cikin ƙauyen Gazwar, ƙiris ya hana ya gano dukkanin shirinmu amma na ɓoye komai. Yanzu idan kayi gangancin komawa wannan ƙauye ba tare da cikakken shiri ba, Hasanul Jalwar zai ganoka, idan kuwa ya ganoka burina da burinka ya wargatse domin kashe ka zaiyi."
Sarki Kuffuru ya yi murmushi ya ce, "Wai me kake ɗaukata ne? Kana ta maganar Hasanul Jalwar zai iya kashe ni, dubi irin illar da nayi musu fa lokaci guda?"
Buƙalshiyu Djinn ya kaɗa kai ya ce, "Rashin sanin ƙarfin takobin Saiful Shiradu yasa kake tunanin zaka iya cin galaba akan Hasanul Jalwar, kayi sani cewa a halin yanzu babu abinda ƴan ƙabilar Kuyuru suka dogara dashi kamar wannan takobi. A duk lokacin da aka ƙarfafa wannan takobi suna kasancewa cikin tsananin farin ciki, suna tunanin zasu iya amfani da wannan takobi wajen cimma muradinsu. Idan muka gama kimtsaka ka koma ƙauyen Gazwar ka tabbatar da cewa ka sato wannan takobi ko kuma ka raba sarki Kuffuru da ita, in dai kayi haka ka gama mana komai. A kowanne lokaci zamu iya kashe Hasanul Jalwar wanda na tabbata jininsa kaɗai zai iya kai rabin wannan ƙwalba ta sihiri. Yanzu ka koma cikin birninka a ɗaura muku aure kai da Anisa, ka tabbatar a kowacce rana ka tara da ita sau uku har tsahon kwanaki uku, hakan zai sa jininta da naka ya haɗu wato ƙarfin ƙabilar Gandiz ya shiga jikinka. In dai ka samu ƙarfin wannan ƙabila sace takobin Saiful Shiradu ba zai yi maka wahala ba."
Aljani Buƙalshiyu Djinn na zuwa nan a zancensa waɗannan duwatsu na jikinsa suka tarwatse kowanne dutse ya koma gurbinsa.
Sarki Kuffuru ya haye kan dokinsa ya nufi hanyar komawa birnin Kufa, koda yazo giftawa ta gefen waɗannan dakaru wanda kallon aljani Buƙalshiyu Djinn ya firgita su, sai ya daka musu ya ce, ku tashi mu tafi. Take suka mimmiƙe kowa ya haye kan dokinsa suka nufi fada.
Kowa a wurin wannan taro ya gama ƙosawa da jiran sarki Kuffuru, har wasu sun fara tunanin anƴa Kuffuru zaizo kuwa? Babu wanda ya kai sarauniya Anisa damuwa da rashin ganin Kuffuru saboda bata da burin da yafi ace ta aure shi. Ko ba komai birnin Kufa zai dawo ƙarƙashin ikon su su biyu.
Ana cikin haka aka jiwo sukuwar dawakai, a duba haka sai ga sarki Kuffuru tare da waɗannan dakaru da suka tafi nemansa.
Kamar jira ake nan take makada da mawaka suka shiga aikinsu. Aka yi ta ƙwaɗa sarkin kamar ba gobe. Kowa a wannan wuri ya zube ƙasa kan gwiwowinsa don nuna biyayya ga sarki Kuffuru.
Kuffuru ya wuce kai tsaye izuwa inda wannan ƙaton gunki yake, aka kawo wani zabgegen gatari da kuma ƙaton bujumi. Kuffuru ya karɓi gatarin da hannun ɗaya ya jinjina shi. Aka matso da bujumin kusa, Kuffuru yasa gatarin ya fille kan bujumin jini yayi feshi izuwa kan sawayen wannan gunki. Faruwar hakan keda wuya sarki Kuffuru da sarauniya Anisa suka zube a gaban wannan gunki suka yi sujjada, tsahon daƙiƙu ɗari biyu da goma sannan suka ɗago.
Dukkanin jama'ar dake wannan wuri suka ruɗe da shewa suna ta yiwa sarki Kuffuru da Anisa jinjina.
Kuffuru ya kama hannun Anisa suka je suka zauna kan waɗansu kujeru guda biyu, baƙin sarakunan da suka zo suka yi ta kawo kyaututtuka suna baiwa sarki Kuffuru da sarauniya Anisa.
Tun ana tarawa a gaban su sarki Kuffuru har sai da wurin ya cika, bayi suka ɗinga ɗiba suna kaiwa taska.
A haka dai har dare yayi kowa da kowa ya watse, aka kaiwa sarki Kuffuru amaryarsa ɗaki aka barta ita kaɗai.
Kuffuru ya shiga cikin wani ƙaton tafki wanda aka cika da ruwan-ɗumi yayi wanka, ya sako wata doguwar riga ya nufo turakar gimbiya Anisa.
Yana shigowa ya samu an gama jejjera musu abinci fiye da kala goma, nan ya zauna suka ci suka ƙoshi. Sannan suka koma kan gado, suka kashe fitilar ɗakin suka morewa rayuwarsu.
Washe gari da sassafe kafun sarki Kuffuru ya fita fada sai da ya sake tarawa da Anisa, tana kuka saboda tsananin zafin da take ji. Budurwa ce ɗanya sharaf, Kuffuru ne ya fara saninta ƴa mace saboda haka dolene taji zafi.
Ana tsakiyar fadanci da rana tsaka, sarki Kuffuru ya sake shigewa gida ya samu Anisa tana wanka cikin ruwan-zafi ya sake afka mata, ya biya buƙatarsa da ita. Da dare ma da yazo kwanciya sai da ya tara da ita.
A taƙaice dai, sai da sarki Kuffuru yayi kwana uku cir kullum sai ya tara da Anisa sau uku sannan hankalinsa yake kwanciya, ba wai yin kansa bane kawai yana bin umarnin aljani Buƙalshiyu Djinn ne.
A cikin waɗannan kwanaki guda ukun, tuni ya gama yin daga-daga da Anisa. Ko'ina a jikinta ciwo yake yi mata, kullum tana kwance. Sai da Kuffuru ya nemo ƙwararrun likitoci waɗanda zasuyi jinyarta.
A ranar kwana ta ukun ne aka nemi sarki Kuffuru a birnin Kufa aka rasa, amma sai wazirinsa yazo ya zauna akan karagar mulki. Koda jama'a suka ga haka sai hankalinsu ya kwanta, sun san cewa sarki Kuffuru wani waje mai muhimmanci ya tafi, kuma da wuya ya dawo da wuri tunda har ya bar wazirinsa akan karaga.
*****RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 34: *Ƙarfin takobin Saiful Shiradu*
*
*
✍️✍️✍️Umar Sangaru✍️✍️✍️
*
Tsahon watanni uku cir, Hasanul Jalwar da aljani Nara suna jiran dawowar attajiri Auran Ziyas amma shuru babu shi, babu labarinsa. Hakan ne yasa Hasanul Jalwar ya haƙura kuma ya rungumi ƙaddara ya tabbatar da cewa abu ne mawuyaci Auran Ziyas ya dawo.
Bayan cikar watanni ukun ne aka ɗaurawa HASANUL JALWAR aure da HAJRIYA ƴar sarkin-noma na garin. Aka yi biki irin na ƴan ƙabilar Kuyuru aka watse, aka bar ango da amaryarsa cikin farin-ciki.
Kwanaki uku bayan wannan ɗaurin-aure Hasanul Jalwar tare da Jarata suka fito bayan gari shan iska, suka sami gaɓar teku suka zauna. Nan suka shiga hirar duniya, suka saka ruwan-teku a gaba.
Abin mamaki bayan shuɗewar rabin-sa'a suka hango ruwa ya ciwo waɗansu mutane guda uku, suna kwance akan ruwan shirim kamar gawarwaki cikinsu ya gama cika da ruwa.
Hasanul Jalwar da Jarata suka yi tsalle suka faɗa cikin tekun suka fara iyo, suka kamo waɗannan mutane guda uku suka dawo dasu kan gaɓa suka kwantar. Mutanen guda uku sun kasance babban mutum guda ɗaya, da matarsa da kuma ƴarsu guda ɗaya.
Cikin hanzari Hasanul Jalwar da Jarata suka fara daddana cikin waɗannan mutane domin su amayar da ruwan da ya cika musu ciki, da zarar sun danna cikin sai kaga ruwa mai yawa ya zubo daga bakin mutanen.
Tsahon ɗan lokaci sannan suka gama amayar da ruwan, sai dai amma numfashinsu bai dawo ba. Hasanul Jalwar ya saka bakinsa a cikin bakin wannan mutumi, ya hura masa iska. Bisa mamaki numfashin mutumin yayi doguwar ajiyar zuciya sannan ya buɗe idanu.
Jarata ma ya saka bakinsa a cikin na wannan mata ya hura mata iska, amma shuru babu labari. Haka ma wannan ƴa tasu. Hakan ne ya tabbatarwa da su Hasanul

Please Login or Register in order to submit comment