Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Akwai dakarun-tsaro aƙalla dubu tamanin masu tsaron wannan kurkuku. Waɗannan dakaru girmansu ya kai girman dakarun-masifa na kurkukun-mutuwa, sannan kuma an raba su gida huɗu ne. Dubu ashirin suna tsaron ƙofar shiga kurkukun, dubu ashirin-ashirin suna tsaron katangar gabas da ta arewa da ta yamma, kowacce katanga akwai dakaru dubu ashirin masu tsaronta.
"Kurkukun azaba-uku ƙarama ce sosai, saboda ance gaba ɗaya girmanta bai wuce ta ɗauki ɗakuna ashirin da biyar ba. Duk wanda kaga an kaishi wannan kurkuku to gagarabadau ne. Babu wanda ya taɓa shiga wannan kurkuku ya fito da rai.
"To, amma a yadda muke samun labari, ko badakare guda ɗaya babu a cikin wannan kurkuku. Wannan aljani da ake kira Duksum mai siffofi guda uku shi ne ke tsaron wannan kurkuku, kuma shi ne wanda yake ganawa fursunoni azaba.
"An ce azabobin da Duksum yake yi kala uku ne. Tunda aka gina wannan kurkuku tsahon shekaru ashirin ba'a samu fursunan da ya iya jure waɗannan azabobi guda uku ba. Fasalin kurkukun ɗakuna guda uku-uku ne a jere, kowanne fursuna ɗakuna guda uku ake bashi.
"Duk wanda ya haura waɗannan azabobi guda uku, ance sarki Kuffuru yana iya sallamarsa daga kurkukun, amma abun mamaki har yau har gobe ba'a sami jarumin da ya iya jurewa ba."
Cikin kaɗuwa sadauki Ashram ya dubi Ratanam ya ce, "Ya shugabana, indai hakane. Ya zamo mana dole muje mu dubo halin da Marganu yake ciki, kada fa su kashe mana shi!"
Sarki Ratanam ya ce, "Bamu da tabbacin sun kashe shi ko kuma yana nan da rai. Nima wannan abun shi ne ya tsaya min a rai, tabbas kafun mu yaƙi sarki Ayubul Zairiy akwai buƙatar muga halin da Marganu yake ciki, don kada muyi aikin banza sun kashe shi. To, amma tayaya zamu iya shiga kurkukun azaba-uku ba tare da wata matsala ba?"
Sadauki Ashram ya ce, "Ya shugabana bana shakkar waɗannan dakaru guda dubu tamanin dake tsaron wannan kurkuku, abinda nake shakka kawai shi ne wannan aljani mai gangar jiki guda uku kuma lallai shi nake tunanin zai zamo mana matsala idan muka shiga kurkukun."
Sarki Ratanam ya ce, "Ko kaɗan aljani Duksum ba zai zamo mana matsala ba, saboda ina da kyakkyawar alaƙa dashi, matsalar mu kawai ita ce mu samu mu shiga kurkukun."
Da jin haka sadauki Ashram yayi dariya ya ce, "Mu je kurkukun nasan abinda zanyi mu tsinci kanmu a cikinta komai ƙarfin kafin dake jikinta kuwa." Sarki Ratanam ya zaro idanu cikin mamaki ya ce, "Me zaka yi kenan?"
Sadauki Ashram ya yi murmushi ya ce, "Sai mun je can zaka gani ya shugabana, amma ka sani cewa na yarda ɗari bisa ɗari da wannan shiri nawa kuma nasan zamuyi nasara."
Tsahon dan lokaci sarki Ratanam yayi shuru yana tunani. Ya san waye Ashram sarai, yasan mutum ne mai kyakkyawan shiri da sanin abinda yake yi. Ko kaɗan bai cika ganganci ba, baya aiwatar da abu sai ya tabbatar da cewa zaiyi nasara.
"Na amince zamuje kurkukun amma kafun nan muje birnina tukunna, naga halin da yake ciki." Sadauki Ashram yayi murmushi ya kama hannayen sarki Ratanam yana godiya.
Haka dai suka ci gaba da tafiya suna tattaunawa akan shirye-shiryensu na farmakan sarki Ayubul Zairiy da kuma kuɓutar da Marganu, har tsahon sa'a goma sha-ɗaya sannan suka soma hango ganuwar birnin Hirtoliya. Sannu-a-hankali suna ƙara matsawa kusa da birnin katangar birnin tana ƙara bayyana.
Abinda ya basu mamaki shi ne meyasa dakarunsu suka sauya samfurin-kayan dakaru na ƙasar. Samfurin kayan dakarun ƙasar Hirtoliya shi ne, shuɗin sulke ne da wando mai ratsin fari, sai kuma hatimin sarauta na tambarin ƙasar Hirtoliya akan ƙirjin kowacce riga.
To, amma waɗannan dakaru da suka hango acan bakin ƙofar shiga ƙasar, kayan jikinsu baƙaƙe ne kuma idan suka lura sosai kamar fuskokinsu ma a rufe suke.
Sadauki Ashram ya dubi sarki Ratanam ya ce, "Ya shugabana. Tabbas waɗancan da muke hangowa ba dakarunmu bane. Tabbas ina kyautata zaton dakarun-sumame ne ko kuma ƴan fashi."
Sarki Ratanam ya murtuƙe fuska ya ce, "Yau kuma? Tabbas zan koyawa waɗancan dakaru hankali kuma sai sunyi nadamar kawo kansu ƙasata."
Tun kafin su ƙarasa bakin-ƙofa suka fara yin arba da gawarwakin dakarun su a jejjefe a ƙasa, jini yana ta malala wanda tuni ya rina ƙasar wannan wuri. Sarki Ratanam da sadauki Ashram suka fito daga cikin wannan keken-doki suka zare takubbansu sannan suka ruga da gudu zuwa inda waɗannan dakarun-sumame suke.
Abin mamaki waɗannan dakaru basu yi wani yunƙuri na afkawa su sarki Ratanam ba, a gefe guda shugabansu ne a zaune akan wata kujera yana ta shan ruwan giya, waɗansu dakaru kimanin guda goma kuma suna ta ɗura kayayyakin wadannan dakaru da suka kashe a cikin buhu.
Wannan abu shi ne ya ɗaurewa su sarki Ratanam kai suka gagara ƙarasawa kan dakarun-sumamen. Aƙalla akwai sadaukai guda dubu goma tsaitsaye a wajen, ace sun rasa abinda zasu sata sai sulken waɗannan dakaru waɗanda tuni sun mutu? Tabbas dole ne ayi mamaki.
"KAI!" sarki Ratanam ya daka musu tsawa.
"Su waye ku? Me kuke yi haka? Meyasa kuka kashe min dakaru?" ya ƙara tambayarsu.
Shugaban dakarun yayi jifa da tulun giyan dake hannunsa ya taso ya nufo inda su sarki Ratanam ke tsaye. Mutumin ya kasance zabgegen ƙato mai ƙira ta ƙarfi. Yana riƙe da zabgegiyar takobi a hannunsa.
"Au tambaya ma kake su waye mu?" inji shugaban yan fashin. "To, masu neman kayan sakawa ne, mun cire kayan waɗannan dakarun kuma ku cire naku ku bamu, idan kuwa kun ƙi zamu ƙwata da ƙarfi kamar yadda muka ƙwata a jikin waɗannan dakaru naku."
Sarki Ratanam ya bushe da mahaukaciyar dariya ya ce, "Ku kuma ta nan kuka ɓullo kenan, amma kun ji kunƴa, ace duk yawan wannan runduna taku kun rasa meye zaku sata sai sulken-yaƙi. To, koma da meye kuka zo lallai kun haɗu da daidai ɗinku, mu biyu kacal ɗinnan mun isa mu tarwatsa wannan shashashun runduna taku."
Shugaban ƴan fashi na jin haka ya juya ya dubi ƴan uwansa ya ɗaga takobinsa sama ya kwarara uban ihu, su ma suka amsa masa. Ya ce, "Ga dukkan alamu wannan sarki ma taurin gare shi kamar waɗannan dakaru nasa, ina so shima a yanko min kansa sannan a cire sulken dake jikinsa domin wannan sulke nasa shine ya kawo mu wannan birni."
Koda ƴan fashi suka ji wannan umarni na shugabansu sai suka rarrabu suka saka sarki Ratanam da sadauki Ashram a tsakiya, kowannensu ya zare makamin yaƙinsa, wasu takubba, wasu masu, wasu gatura da gudumomi.
Sarki Ratanam da Sadauki Ashram suka haɗe bayansu a waje guda kowannensu ya riƙe takobinsa da hannu biyu suka sakawa ƴan fashin nan idanu suna jira su ga ta ina za'a fara farmakarsu. Shi ko shugaban waɗannan ƴan fashi can baya ya koma ya zauna akan wani ƙaton doki, ya zubawa sarki Ratanam da yaransa idanu.
Ƴan fashi suka kwarara uban ihu a tare suka afkawa sarki Ratanam da sadauki Ashram da mugun-yaƙi. Nan fa suka ruguntsume da azababben yaƙi, waɗannan dakaru suka ƴanƴame sarki Ratanam da sadauki Ashram da sara da suka. Sarki Ratanam da sadauki Ashram suka kurma ihu suka shiga tsakiyar dakarun nan suka hau su da sara da suka, duk inda suka saka a gaba sai dai kaga mazaje na zubewa tamkar ana sassaɓe a gona. Haƙiƙa sarki Ratanam da sadauki Ashram sun kasance gawurtattun mayaƙa kuma sadaukai na gani na faɗa.
Kafun kace me wannan tuni sun fara zamewa waɗannan ƴan-fashi guguwar bala'i, don in banda jini da sassan jikin waɗannan ƴan-fashi babu abinda yake tashi a wannan wuri. Nan take gawarwakinsu suka soma yawaita a wannan wuri.
Masu iya magana sun ce, sarkin yawa, yafi sarkin ƙarfi.
Koda aka sami sa'a ɗaya da rabi ana wannan gumurzu sai waɗannan dakaru suka soma cin ƙarfin su sarki Ratanam har suka yiwa sadauki Ashram kyakkyawan sara guda ɗaya a gadon bayansa, nan take wurin ya farke jini mai yawa yayi feshi.
Ashram ya kurma uban ihu ya zube ƙasa kan gwiwowinsa sakamakon jiri da yake ɗibarsa sanadiyyar wannan jini mai yawa da yake zuba daga bayansa. Koda sarki Ratanam yaga haka sai hankalinsa ya ɗugunzuma saboda ko kaɗan baya so sadauki Ashram ya rasa rayuwarsa.
Kuma a halin da ake ciki a yanzu indai ba ɗauki ya kaiwa sadaukin ba zai iya rasa rayuwarsa, idan ma waɗannan yan-fashi basu hallaka shi ba, wannan jini dake zuba a jikinsa zai iya sanadiyar mutuwarsa.
Amma sai dai kash! Sarki Ratanam na cikin shawara a cikin zuciyarsa akan abinda ya kamata yayi, yaji an doka masa wata ƙatuwar guduma a tsakiyar kansa. Nan take jini da ƙwaƙwalwa suka haɗu a waje ɗaya, sarki Ratanam ya zube ƙasa sumamme. Ba wani bane ya doka masa wannan guduma illa shugaban waɗannan ƴan-fashin.
Zaka iya cewa waɗannan ƴan-fashi sun sami babbar dama wacce zasu iya kashe su Sarki Ratanam. Tunda ga sarki Ratanam a kwance a ƙasa sumamme, ga kuma sadauki Ashram durƙushe akan gwiwowinsa jini nata malala daga raunin gadon bayansa. Shugaban ƴan-fashin ya sake ɗaga gudumarsa ya dokawa sadauki Ashram a tsakar kai, take shima ya sulale ƙasa sumamme.
Bisa mamaki sai wannan shugaba nasu ya dube su ya ce, "Ku tuɓe kayan jikin waɗannan sarakai, maigida bai ce mu kashe su ba."
Koda jin wannan umarni sai waɗannan ƴan-fashi suka cire kayan jikin sarki Ratanam da kayan jikin sadauki Ashram suka barsu a wannan wuri kwakkwance a sume, daga su sai gajeran wando.
Koda gama aiwatar da wannan aiki sai waɗannan ƴan-fashi gaba ɗayansu suka haye kan dawakansu suka juya suka nufi cikin ƙungurmin daji da gudu. Suka bar sarki Ratanam, sadauki Ashram da gawarwakin waɗannan dakaru kwakkwance a wannan wuri, zigidir babu wanda ke sanƴe da riga ko sulke.
***
A can birnin Kufa kuwa, wani mahayi ne tafe bisa ingarman doki ya nufi gidan sarautar sarki Kuffuru. Abin mamaki kayan jikin wannan mahayi samfurin birnin Hirtoliya ne dasu.
Koda ya iso bakin ƙofar shiga wannan fada, sai dakaru suka tare shi. Ɗaya daga cikinsu ya tambaye shi, "Ya kai wannan mahayi, waye kai?"
"Ni manzo ne daga sarki Ratanam na birnin Hirtoliya." wannan manzo ya amsa.
"Manzo? Meke tafe da kai?" inji wannan badakare. "Ina shaidar ka?"
Koda jin haka sai wannan manzo ya zira hannu a cikin aljihu ya fiddo wani hatimi mai ɗauke da zanen tsaunika guda uku ya nunawa waɗannan dakaru, ai kuwa suna ganin wannan hatimi suka buɗe masa ƙofa.
Ɗaya daga cikinsu yayi masa jagora, suka nufi fadar sarki Kuffuru.
Sarki Kuffuru na zaune bisa karagar mulki sanƴe da jar-alkyabba mai beza a wuya, gimbiya Firziyya na zaune a gefensa ta saka korayen-tufafi, ana tafiyar da harkokin mulki kamar yadda aka saba.
Kwatsam! Sai ga shigowar badakare mai jiran-kofa tare da wannan manzo.
Koda sarki Kuffuru yaga kalar kayan dakarun birnin Hirtoliya a jikin wannan manzo, sai ya murtuƙe fuska don ya tabbatar da cewa sarki Ratanam ne ya aiko wannan manzo.
Wannan manzo na ƙarasowa gaban karagar sarki Kuffuru ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa, sannan ya ɗago ya zaro wata wasiƙa ya miƙawa magatakarda.
Sarki Kuffuru na ganin wannan wasiƙa ya murtuƙe fuska, ya dubi hauni dake tsaye a gefe guda, ya gyaɗa masa kai.
*******RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 39: *Ƙabilar Huturu, Shugabannin tuggu*
*
UMAR SANGARU
*
Magatakarda ya buɗe wannan wasiƙa ya fara karantata kamar haka;
"Wasiƙa daga sarkin birnin Hirtoliya, sarki Ratanam, zuwa ga sarki Kuffuru na birnin Kufa.
"Ya kai wannan sarki ina fatan kana lafiya, kamar yadda nake lafiya. Ba don komai na rubuto maka wannan wasiƙa ba sai domin nayi maka gargaɗi akan ka saki ɗana Marganu daga kurkuku.
"Idan kuwa ka ƙi..." koda magatakarda yazo nan a karatun wasiƙar sai yayi shuru ya gagara ci gaba da karantawa kuma ya ɗago kai ya kalli sarki Kuffuru. Kai da gani ka san cewa tsoron karanta abinda ke gaba yake. Sarki Kuffuru ya gyaɗa masa kai ya ce, ya ci gaba.
"Idan kuwa ka ƙi, zan haɗo gagarumar runduna ta sadaukai irin wacce aka jima ba'a gani ba, muje har gidan kurkukun azaba-uku mu ƙwato shi da ƙarfi. Tunda na turo maka uwar-matsafa Rauziyya batayi nasara ba.
"Zan zo da kaina na ƙwaci ɗana idan har baka sake shi ba nan da kwanaki biyu rak!" Sarki Kuffuru ya taso a hasale ya ƙwace wannan wasiƙa daga hannun magatakarda ya fara dubata da kansa domin bai yarda da abinda ake karantawa ba. Duk yadda sarki Ratanam ke tsananin tsoronsa a ce ya turo masa wasiƙar tawaye?
Bisa mamaki sai yaga irin rubutun mutanen birnin Hirtoliya sak a jikin wannan wasiƙa, kuma yaga sa-hannu da hatimin sarki Ratanam a ƙarshen wasiƙar, hakan ne ya tabbatar masa da cewa; Lallai wannan takarda daga hannun sarki Ratanam take.
Sarki Kuffuru ya dubi hauni ya sake gyaɗa masa kai, nan take hauni ya zare takobinsa cikin zafin-nama ya fille kan wannan manzo. Sarki Kuffuru ya dubi magatakarda ya ce, a ɗauki kan wannan manzo, a haɗa da wasiƙar-raddi a kaiwa sarki Ratanam kuma ace bayan-gobe i warhaka rundunar sarki Kuffuru zata dira a ƙofar birninsa.
****
SA'A GUDA, BAYAN FITOWAR SARKI RATANAM DA SADAUKI ASHRAM DAGA BIRNIN DAMASHKAR.
****
Sarki Ayubul Zairiy ne zaune a cikin wannan ɗaki wanda suka gama tattaunawa da su sarki Ratanam a cikinsa, yana ta tunani gami da nazari. Har kusan rabin sa'a sannan ya tafa hannayensa sau huɗu ya kirawo wani ɗalasimin tsafi a zuciyarsa.
Nan take ƙasa ta tsage wani ɗan ƙaramin aljani ya ratso ta cikinta ya fito. Sarki Ayubul Zairiy na ganin wannan aljani ya zube a gabansa ya kwashi gaisuwa.
Aljanin ya kasance ɗan gajere kuma siriri tamkar iska zata ɗauke shi tayi jifa dashi. Baida ko fuka-fuki guda daya. Kai a takaice dai, kana ganinsa kaga ragon aljani wanda da wuya ya iya kashe koda kare.
*
Wannan aljani shi ake kira JIZID HUTUR, shi ne mai-gidan sarki Ayubul Zairiy. Kamar yadda sarki Kuffuru yake da aljani Buƙalshiyyu Djiin, haka shima sarki Ayubul Zairiy yake da wannan aljani mai suna Jizid.
A wannan daula akwai manƴan sarakuna guda uku - sarki Kuffuru, sarki Ratanam da sarki Ayubul Zairiy.
Kowanne ɗaya daga cikin waɗannan sarakuna babban sarki ne, mai cikakken iko da kuma shiri. Kowanne daga cikinsu yana da babban-hadimin aljani wanda yake taimaka masa, kuma suke da buri da manufa iri ɗaya.
Sarki Kuffuru yana da aljani Buƙalshiyyu Djinn wanda suke da buri iri ɗaya - mallakar RUHIN sarki Samudul Ansari domin kuɓutar da aljani Djinn daga ƙangin-bauta wanda sarki Samudul Ansari ya saka shi.
Sarki Ayubul Zairiy yana da aljani Jizid amma har yanzu ba muji burinsu ba.
Har yanzu ba'a bayyana mana aljanin sarki Ratanam ba, wataƙila sai wasiƙar sarki Kuffuru ta riske shi sannan wannan aljani zai bayyana.
*
Aljani Jizid ya dubi sarki Ayubul Zairiy ya ce, "Meyasa tun kafin kuyi wannan tattaunawa baka neme ni ba?"
Sarki Ayubul Zairiy ya ce, "Ka gafarce ni ya shugabana, ban yi tsammanin wannan zama da muka yi zata rincaɓe haka ba."
"Hmm," Jizid ya yi murmushi. "Wanne shiri kake akan sarki Ratanam don naga kamar baya cikin lissafin maƙiyanka?"
Sarki Ayubul Zairiy yayi murmushi ya ce, "Ratanam? Ai wannan ban ɗauke shi a matsayin komai ba face ƙaramin-ƙwaro wanda a duk lokacin da naga dama zan iya saka ƙafata na take shi."
Aljani Jizid yayi dariya ya ce, "Haka ko? Zo muje wani wuri mana, ka sha mamaki."
Yana gama faɗin haka ya dafa kafaɗar sarki Ayubul Zairiy, nan take su biyun suka rikiɗe suka zamo waɗansu ƴan ƙananun tsuntsaye guda biyu, ba tare da jiran komai ba suka buɗe fuka-fukinsu suka tashi sama, suka fice daga cikin wannan fada suka hanƴar da su sarki Ratanam suka nufa.
Tsuntsayen biyu suka ci gaba da tsala azababben gudu a cikin iska suka nufi wannan daji, wanda keken su sarki Ratanam ke tafiya a cikinsa.
Sannu-a-hankali har suka iso cikin wannan daji, sannan suka saki fuka-fukinsu suka yi ƙasa luu... Suna yiwo ƙasa-ƙasa suka fara hango wannan keken doki nata tafiya. A hankali suka sauƙa akan wannan keken-doki ba tare da sun haifar da wata ƙara ba. Hakan ne yasa kwata-kwata su sarki Ratanam basu san da dirarsu ba.
Duk wata tattaunawa da ta gudana tsakanin sarki Ratanam da sadauki Ashram waɗannan tsuntsaye guda biyu sun ji, suna zuwa ƙarshen wannan daji waɗannan tsuntsaye suka tashi daga kan wannan keken doki suka dira akan wani ƙaton tsauni.
Sai da suka tabbatar da cewa wannan keken doki yayi nisa sosai, sannan suka rikiɗe izuwa siffar aljani Jizid da sarki Ayubul Zairiy.
Jizid ya yi murmushi ya ce, "Ya ka ji tattaunawar da suke akan ka?"
Sarki Ayubul Zairiy ya yi ajiyar numfashi ya kaɗa kai ya ce, "Lallai aboki yana iya zamowa maƙiyi a kowanne lokaci, yanzu duk irin dangatar dake tsakanina da sarki Ratanam ace shi ne yake ƙoƙarin kawar da mulkina. Hmm. Bana taɓawa ragawa maƙiyana, lallai wannan sarki zaiyi nadamar tunkarata da batun yaƙi."
Aljani Jizid ya yi dariya ya ce, "Abin kunƴa ne a gare mu ace mun yaƙi sarki Ratanam gaba-da-gaba saboda mun fi ƙarfinsa nesa ba kusa ba. Lallai wani ya kamata ace mun saka ya kawar da mulkinsa. A ganinka waye ya kamata ace mun saka wanda zai hallaka mana shi?"
Sarki Ayubul Zairiy ya yi shuru gami da faɗawa kogin tunani mai zurfi, tsahon ɗan lokaci kamar ba zai ce komai ba. Daga can sai ya numfasa ya ce, "A ganina sarki Kuffuru shi ne wanda zaifi dacewa da wannan aiki, amma na san ba zai taɓa amincewa ba face mun shiryawa sarki Ratanam tuggu wanda ba zai iya tsallakewa ba. Babbar abin damuwata yanzu ita ce, wanne irin tuggu zamu shirya masa wanda ba zai iya tsallakewa ba?"
Aljani Jizid ya sake bushewa da mahaukaciyar dariya ya ce, "Wannan ai abu ne mai sauƙi. Idan ka bar wannan wuri kada ka tsaya a ko'ina sai a dajin Huzluf, ka samu ɗan fashi Kauzur ka haɗa kai da shi, ka bashi kyautar dinari miliyan ɗari takwas da hamsin. Na tabbata idan ka ba shi kyautar zai yarda ya haɗa kai da kai.
"Abu na farko shi ne su je ƙofar birnin Hirtoliya su karkashe dakarun sarki Ratanam sannan su kwashe kalar kayan jikin dakarun, idan so samu ne su haɗo har da na sarkin.
"Abu na biyu zamu rubuta wasiƙa mu aikawa sarki Kuffuru, dole ne a jikin wannan wasiƙa a samu sa-hannun sarki Ratanam da hatiminsa. A wasiƙar zamu ce mun baiwa sarki Kuffuru kwanaki biyu rak, ya saki Marganu idan kuwa ya ƙi zamu kai farmaki.
"Abu na uku a ranar da aka kaiwa sarki Kuffuru wannan wasiƙa, a wannan rana za'a kaiwa wannan kurkuku farmaki domin a kuɓutar da Marganu.
"Gaba ɗaya wannan aiki Kauzur da yaransa ne zasu gudanar, sannan kuma suturun dakarun sarki Ratanam shi zasu sanya. Kaga kenan sarki Kuffuru da hadimansa zasuyi tsammanin sarki Ratanam da dakarunsa ne suka jagoranci kai wannan hari."
Koda sarki Ayubul Zairiy ya gama jin wannan jawabi na aljani Jizid sai ya bushe da mahaukaciyar dariya ya ce, "Ko sarki Ratanam shi ne sa'a bai isa ya tsallake wannan tuggu da zamu shirya masa ba. Tabbas ya shugabana ina ƙara godiya bisa wannan shiri da ka kawo."
Aljani Jizid ya yi murmushi sannan ya ɓace ɓat. Shima sarki Ayubun sai ya shafi damtsen hannunsa nan take shima ya ɓace.
Bai bayyana a ko'ina ba sai a cikin wani ƙaton daji mai yawan duhuwowi da ƙoramu da kwazazzabai. Yana bayyana yaji wani tsuntsu yayi kuka daga can saman wata bishiya.
Faruwar hakan keda wuya yaga an bubbuɗe ƙofofi daga ƙarƙashin ƙasa, waɗansu irin girɗa-girɗan mutane nata firfitowa. Kowannensu riƙe da zabgegen makami.
Kafun ka ce me wannan sun kewaye sarki Ayubul Zairiy a tsakiya. Yawan ƴan-fashin zai kai dubu goma da ɗoriya.
Sarki Ayubul Zairiy ya yi dariya ya ce, "Ni ba yaƙi bane ya kawo ni wajen ku ba. Ina shugabanku yake?" Ƴan-fashin suka yi kamar basuji abinda ya ce ba, suka ɗaga makamansu sama zasu afka masa, amma kamar daga sama sai suka ji an daka musu tsawa.
Bisa dole suka tsaitsaya domin sun san mai wannan tsawa, nan take suka dare wani murjejen ƙato ya ratso ta cikinsu ya fito. Ba wani bane illa shugabansu.
Shugaban nasu ya dubi sarki Ayubul Zairiy ya ce, "Ya kai wannan hamshaƙin sarki, lallai abinda yasa ka taso da kanka ka shigo cikin wannan daji nawa ba kaɗan bane. Wannan dalili shiyasa ba zamu afka maka ba, domin ga dukkan alamu da ƙaruwa kazo mana. Ina jinka faɗa min abinda ke tafe da kai?"
Sarki Ayubul Zairiy ya yi dariya ya ce, "Lallai kamar yadda nake samun labari, ka kasance mai tsananin hikima. Tabbas inda ace kunyi gangancin tunkarata da yaƙi, da babu abinda zaku samu a wajena face mu kai ruwa rana. Amma a yanzu na taho muku da babbar kyauta ta dinari miliyan ɗari takwas.
"Ya kai Kauzur tattaunawata da kai mai tsaho ce, kuma bana so kowa yaji face amintattun ka."
Ɗan fashi Kauzur ya yi murmushin jin daɗi ya ce, "Dinari milyan ɗari takwas? Wanne aiki kake so a yi ma? Wani babban sarkin kake so a je a yashe ne?"
Sarki Ayubu ya yi dariya ya nuna wani ƙaramin tanti da ke gefe guda ya ce, "Muje cikin wannan tantin mu tattauna, ina ganin zaka fi fuskantata sosai."
Ɗan fashin ya gyaɗa kai sannan ya wuce gaba cikin wannan tanti, sarki Ayubul Zairiy ya biyo shi a baya.
Suna shigowa cikin tantin, sarki Ayubul Zairiy ya tafa hannayensa sau uku, nan take wani ɗan-wadan aljani ya bayyana ɗauke da wata ƙatuwar jaka ta fata, ya ajiye jakar a gaban sarki Ayubu sannan ya ɓace ɓat.
Sarki Ayubu ya buɗe jakar sannan ya turata gaban ɗan-fashi Kauzur, nan take ɗan-fashin yayi arba da zallar dinari jajawur cunkushe a cikin wannan jaka. Cikin tsananin mamaki ya zaro idanu sannan

Please Login or Register in order to submit comment