Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gindin wannan bishiya kuwa, zamuga mutum na farko dake zaune, saurayi ne da ba zai wuce shekaru ashirin da biyar a ido ba, amma idan ka san asalinsa yafi shekaru tamanin da ɗoriya, kawai dai baiwar rashin tsufa ce. Mutum na biyu kuma, saurayi ne kyakkyawa mai kwantaccen baƙin-gashi da farar-fata mai ɗaukar hankalin kowacce mace.
Idan mutum ya san Aymanul Faris da Barban zai ga su ne zaune a gindin wannan bishiya, ba wasu ba.
"Tsarin mulkin wannan birni naga ya sauya fa," inji Barban. "Anƴa sarki Ayubu yana nan kuwa? Ko sau ɗaya ban kalli dakaru su na dukan jama'a ba."
Aymanul Faris ya gyaɗa kai, "Hakane. Ni abinda ya bani mamaki shi ne, wai shin ma ina Gimbiya ta tafi, alhalin na san cewa kullum tana cikin wannan lambu tana kallon halittun Ubangiji. Shin idan muka jira na tsahon daƙiƙu ɗari da tamanin bata zo ba, zamu shiga har cikin gidan sarautar tasu?"
Barban ya yi dariya ya ce, "Babu abinda zai hanata zuwa wannan wuri, matuƙar tayi arba da wannan tsuntsuwa da na aika mata..." Kafun ya ƙarasa rufe bakinsa suka ga kyakkyawar gimbiya sanƴe cikin alkyabba ta iso gindin wannan bishiya a guje.
Koda Barban ya ganta kuma yaga tsananin kyawunta, sai yayi murmushi ya tashi daga wannan waje, ya nufi bakin wani tafkin-wanka inda yake hango kofunan shayi, ya ƙyale su su biyu a wannan waje.
Aymanul Faris ya miƙe cikin fara'a da murna ya buɗe hannayensa biyu, gimbiya Jaanu na ganin haka ta ruga da gudu ta faɗa kan ƙirjinsa suka rungume juna cikin tsananin so da ƙauna, da kuma murnar sake saduwa bayan doguwar rabuwa.
Tsahon daƙiƙu ɗari uku da talatin babu wanda yace uffan a cikin su, kuma har a wannan lokaci a ƙanƙame suke da juna, kai kace ba zasu taɓa rabuwa ba.
Lallai soyayya mai ƙarfi ta gama ginuwa a zuƙatan waɗannan masoya guda biyu; sun zamo tamkar jini da hanta.
Daga can Aymanul Faris ya janƴe jikinsa daga nata ya dubi fuskarta wadda tuni ta gama jiƙewa sharkaf da hawayen farin-ciki.
"Masoyiya ta da fatan mun same ki lafiya?" ya faɗa cikin murya mai sanƴi.
Gimbiya Jaanu ta goge hawayen idanunta, "Lafiya ƙalau. Nayi kewar ka sosai masoyina, tamkar zan rasa rayuwata. Ba da ban an samar min da mutum-mutuminka ba, da ban san wanne hali zan shiga ba. Wai shin ina ka shiga ne, ko labarinka ban sake ji ba? Babu ƙasar da a duniya ban tura fatake su samo min labarinka ba amma shuru?"
Aymanul Faris ya yi murmushi mai taushi ya ce, "Ai ko aljanu za ki saka su nemo ni bazasu taɓa kallona ba. Ya kike? Ya garin naku?"
Gimbiya Jaanu tayi murmushi ta ƙurawa Aymanul Faris idanu ta gagara cewa komai.
A karon farko na haɗuwarsu Aymanul Faris yana cikin damuwa; sanadiyar kashe musu mutane da aka yi, da kuma tsare mahaifiyarsa da aka yi a kurkuku. Wannan yasa baya cin isasshen abinci, kuma baya samun isasshen barci. Saboda haka a wannan lokaci a rame yake.
Amma, yanzu hankalinsa a kwance yake. Jikinsa ya gama ginuwa izuwa murɗaɗɗen saurayi, farin fatar jikinsa ya gama bayyana tamkar na Hajriya. Sannan uwa-uba ga wannan kwantaccen baƙin gashi dake kansa wanda ke ɗaukar hankalin kowacce irin mace.
"Hmm, ina lafiya. Ya maman mu? Ya sauran jama'arku da su jaruma Riya, da fatan kowa yana lafiya?" ta ce.
Aymanul Faris ya ce, "Kowa da kowa yana lafiya. Ya naga kamar tsarin mulkin wannan gari naku ya sauya? Anƴa mahaifinki yana nan kuwa?"
Gimbiya Jaanu na jin haka tayi murmushi ta kama hannunsa, ta jashi wani ƙasaitacce wuri, wanda aka ƙawata da kyawawan kujeru da teburan cin abinci. Suna zuwa wajen, suka zauna akan waɗansu kujeru guda biyu masu fuskantar juna.
Gimbiya Jaanu ta zubawa Aymanul Faris lemu mai sanƴi a cikin wani kofin-gilashi ta miƙa masa. Ya karɓa ya ɗan sha.
"Mahaifina baya nan; ya yi tafiya mai tsahon gaske izuwa birnin Sin kuma hatta ni kaina bai faɗa min abinda yaje yi acan ba. Abubuwa da dama sun faru a gareni bayan rabuwar mu; Na farko sarki Kuffuru ya kamo Marganu ya tsare shi a kurkuku anyi masa wulaƙanci saboda ni, wannan yasa sarki Ratanam ya taso yazo birninmu domin a tattauna akan yadda za'a ɓullowa wannan lamari.
"Wannan tattaunawa bata yi daɗi ba, domin kuwa an sami rashin fahimta tsakanin mahaifina da abokinsa Ratanam. Saboda sun matsa min kuma sun tilasta min akan na faɗa musu dalilin da yasa na tsani Marganu.
"Cewa da nayi, ina da wanda nake so yasa zuciyar sarki Ratanam ta tunzuro ya tashi daga wannan taro ya fice shi da sarkin-yaƙinsa. Nayi mamaki matuƙa da na kalli mahaifina baiyi fushi da ni ba, amma da yayi min wata tambaya take hankalina ya tashi, na gigice, na rasa abinda zan ce masa..."
Koda tazo nan a zancenta sai tayi shuru ta ƙurawa Ayman idanu. Shi kuma tuni ya afka cikin tsananin mamaki gami da wasu-wasi. Abubuwan da yake mamaki da wasu-wasi su ne;
Mene ne dalilin da yasa sarki Ayubul Zairiy ya kaiwa sarki Kim Sam na birnin Sin ziyara?
Mene dalilin da yasa sarki Kuffuru ya tsare Marganu?
Shin wannan kalma ("INA DA WANDA NAKE SO") da gimbiya Jaanu ta faɗa shi ne ya janƴo silar rugujewar alaƙar dake tsakanin birnin Damashkar da birnin Hirtoliya? Wai hakan yana nufin ta baiwa mahaifinta labarinsa kenan?
Kamar gimbiya Jaanu ta san tambayoyin da Aymanul Faris yake yi a cikin ransa kenan, ta fara jawabi.
"Ina tunanin ziyara ce ta kai mahaifina wajen sarki Kim Sam. Sannan dalilin da yasa sarki Kuffuru ya kamo Marganu shi ne, idan zaka tuna Barban ya taɓa bamu labarin cewa, sarki Kuffuru bai amince ya baiwa Marganu mahaifiyarka ba, sai akan sharaɗin cewa zai kamo Barban ko kuma kai da Riya. Ka san cewa bai cika wannan sharaɗi ba, wannan shi ne babban dalilin da yasa Kuffuru ya tsare Marganu."
Aymanul Faris ya gyaɗa kai cikin fahimta ya ce, "Amma lokacin da aka kira ki wannan tattaunawa, kin basu labarina ne?"
Gimbiya Jaanu ta kaɗa kai, "Ban basu labarin ka ba. Wannan ita ce tambayar da mahaifina yayi min wacce tasa na birkice a wannan wuri. Ban san tayaya zan bashi labarinka ba?"
Aymanul Faris ya yi ajiyar numfashi ya ce, "Babu buƙatar ya san dani a matsayin masoyinki, har zuwa sa'adda zan sare kansa."
Nan take wannan kalma ta ƙarshe ta tsayawa gimbiya Jaanu a rai, idanunta suka ciko da kwalla, ta ɗago kai ta kalli Aymanul Faris.
"Zan yi baƙin ciki sosai, idan ka kashe mahaifina. Amma idan na tuno da irin kisan wulaƙancin da ya yiwa jama'arku da mahaifinka, sai zuciyata tayi sanƴi. Tabbas tsananin sonka dake cikin zuciyata zai danne baƙin cikin rabuwa da mahaifina." inji gimbiya Jaanu a lokacin da hawaye suke zubowa daga idanunta.
Aymanul Faris bai san sa'adda tausayinta ya kama shi ba, yaji tamkar ya janƴe wannan ɗauka da yake da niyyar yi akan sarki Ayubu amma sai zuciyarsa ta daka masa tsawa, take ya dawo hayyacinsa.
Ya kamo hannayen gimbiya Jaanu, ta sake ɗago kanta ta kalli cikin idanunsa, "Kiyi haƙuri masoyiya ta. Tabbas dukkan abinda zai faru a wannan rayuwa ta duniya, an riga an gama rubutawa. A tsarin rayuwar mutanen ƙabilata tun daga zamanin babban sarki Deher, kashe-kashe da zubar da jini baya daga cikin jadawalin ƙabilarmu.
"Tun daga wancan tsohon zamanin, in dai kika ga mun kashe mutane, to tabbas ɗaukar fansa muka yi akan abinda aka yi mana. Mahaifina, mahaifiyata da sauran mutanen ƙabilarmu zasuyi matuƙar alfahari dani, matuƙar aka ce ni na saro kan sarki Ayubu da hannu na.
"WANNAN SHI NE BABBAN DALILIN DA YASA NA KAWO MIKI WANNAN ZIYARA DOMIN NAYI MIKI WANNAN TAMBAYA; SHIN ZA KI CI GABA DA ƘAUNATA KODA ACE KIN KALLI KAN MAHAIFINKI A HANNUNA? Ko kuma hakan zai janƴowa soyayyarmu tangarɗa?"
Koda gimbiya Jaanu taji wannan tambaya daga bakin Aymanul Faris sai ta miƙe tsaye ta juya masa baya ta ce, "Na riga na baka amsar wannan tambaya. Mahaifina azzalumi ne, tsahon shekarun da na shafe ina ƙoƙorin gyara shi amma bai gyaru ba. Bansan wanne hukunci zan yanke akan zaluncinsa ba."
Aymanul Faris ya ce, "Kiyi haƙuri bisa ƙaddarar da rayuwa tazo miki da ita."
A daidai lokacin Barban dake can zaune a bakin wannan tafki yana shan shayi, ya miƙe tsaye, alamar ya gaji da zaman.
Aymanul Faris ya dubi gimbiya Jaanu ya ce, "Ga dukkan alamu maigidana ya gaji da zama acan, don haka zamu tafi. Ina mai ba ki shawara kije ki sake yin zama kiyi tunani akan wannan magana da nazo da ita, tabbas bayan watanni biyu zan dawo gareki, domin jin hukuncin da kika yanke. Kada kiyi gaggawar yanke hukunci, daga baya kiyi dana-sani."
Gimbiya Jaanu ta fashe da kuka tazo wurin Aymanul Faris ta haɗe bakinsu a waje guda, ta fara sumbatarsa kamar yadda suka taɓa yi, sa'adda ya sameta a wannan ɗaki ana gobe Marganu zaizo ɗaukarta.
"INA SONKA HAR CIKIN RAINA, wannan kalma ba zata taɓa gushewa daga bakina, zuciyata da ƙwaƙwalwata ba. Ka kula min da kanka!" inji gimbiya Jaanu cikin kuka. Tana gama faɗin haka ta nufi ƙofar fita daga wannan lambu.
Aymanul Faris ya bi ta da kallo kawai, idanunsa nata zubar da hawayen tausaya mata. Har ta fice daga cikin lambun.
A lokacin ne kuma Barban ya ƙaraso inda yake zaune. Ba tare da yace komai ba, ya shafi wannan kambu nasa, su Hubbus Dawan suka bayyana, kuma suka ɗauke su.
A wannan karon wani irin mugun jiri ne ya ɗebi Aymanul Faris ya zube ƙasa sumamme. Daga wannan lokaci kuma bai san abinda ke faruwa ba.
Lokacin da ya buɗe idanunsa saiya tsinci kansa a cikin wata ƙasaitacciyar fada, wadda ko a littatafan tarihi bai taɓa jin mai kyawunta ba. Ko shakka babu ta ninka asalin fadar Barban wacce suka kaiwa ziyara a baya sau uku.
Fadar a haskake take da waɗansu irin manƴa-manƴan fitilu masu haske. A tsakiyar fadar kuwa, an ajiye wata ƙatuwar karaga ta mulki.
Zaune akan wannan karaga kuma, aljani Ranganu ne, ya saka jar alkyabba irin tasu ta aljanu. Idan mutum zai iya tunawa a cikin wannan fada, muka taɓa ganin Hodon da aljani Ranganu lokacin da aljani Sheezuwa ya samar da taswirar Hodon a fadar Hubbaz wurin su Boka Hubbazu.
Ba kyawun wannan fada da ƙawatuwarta bane ya baiwa Aymanul Faris mamaki. Abinda ya ba shi mamaki shi ne, irin iko da ƙanshin tsafin dake tashi a wannan fada. Idan zai iya tunowa a waje ɗaya ya taɓa jin irin wannan iko na tsafi.
Idan zamu iya tunowa karon farko na haɗuwar Aymanul Faris da Barban a wannan ɓoyayyiyar fada, mun ga cewa Aymanul Faris ba shi da niyyar miƙawa Barban hannu domin su gaisa amma suna haɗa idanu da Barban ya miƙa masa. Ko shakka baya yi irin wannan ikon tsafi ne yake tasiri anan.
Barban ya zube ƙasa cikin girmamawa ya gaishe da Ranganu amma Aymanul Faris kuma na nan tsaye daram, yana kallon Ranganu.
Abin mamaki ba haka yaso a ransa ba, shima so yake ya yiwa Ranganu gaisuwa amma jikinsa ya ƙi ya bi umarnin sa.
Waɗannan abubuwa guda biyu da suka faru sun baiwa Aymanul Faris mamaki kuma sun jefa shi cikin wasu-wasi. Na farko lokacin da aljani Ranganu ya umarce shi da zama akan wannan ƙatuwar karaga wacce tafi sauran guda biyun nan, a cikin wannan ɗaki wanda ya fara bashi labarin SARAUNIYA ARYA a cikinta.
Na biyu kuma, mene ne dalilin da yasa jikinsa ya ƙi zubewa a gaban Ranganu ya kwashi gaisuwa? Waɗannan su ne tambayoyin da bai san wa zai tambaya amsoshinsu ba.
"Barkan ku da ƙarasowa fadata. A nan zan yi muku bayani akan SARAUNIYA ARYA da kuma yadda zaku samo abubuwa guda uku waɗanda zasu buɗe muku gidan ƙarƙashin ƙasa na sarki Kuffuru." inji aljani Ranganu.
Yana gama faɗin haka ya nuna musu wasu ƙasaitattun kujeru guda biyu dake gefe guda yace su zauna. Nan take kuwa, suka zazzauna.
"Ayman, duk wata tattaunawa da kuka yi kai da gimbiya a ɗazu, ina zaune a wajen amma bakwa ganina. Ba don komai naje wannan wuri ba, sai domin ina so na tabbatar da cewa, ko Jaanu ce magajiyar ARYA?" aljani Ranganu na zuwa nan a zancensa yayi shuru, ya ɗan baiwa Aymanul Faris dama ko zaiyi tambaya.
"Tun shekaran-jiya kake ta maganar wata ARYA, ARYA... Nifa har yanzu ban gane ina ka dosa ba. Waye ce ARYA? Waye ne TAU'RIN?" Aymanul Faris ya tambaya.
Aljani Ranganu yayi murmushi ya ce, "Wannan na daga cikin dalilan da suka sa na gayyato ku wannan fada tawa, domin ku san wace ce ARYA, da kuma abubuwan da zaku samo domin shiga wannan gida na ƙarƙashin ƙasa inda takobin mahaifinka take.
"ARYA: Wata sarauniya ce da tayi mulkin wata babbar ƙasa tun a zamanin sarki Samudul Ansari, kai wasu ma har suna cewa ita ce matar da Samudul Ansari ɗin ya aura. Wannan labari ma ba shi da inganci sosai saboda ba'a tabbatar ba, babu yadda za'a yi mutum ya tabbatar face ya karance tarihin Samudul Ansari kaf. Meyasa aka damu da sunan sarauniya ARYA?
"ARYA ƴar wata ƙabila ce da ake kira ARYA wato tana amsa sunan ƙabilarta, mutanen wannan ƙabila ƴan-baiwa ne. Duk wanda ya auri ɗaya daga cikinsu, zai sami ɗaukaka, sa'a, kwarjini kuma zaiyi suna a duniya.
"Amma, inda matsalar take ba kowanne ɗan ƙabilar ne yake da irin wannan baiwa ba. Jefi-jefi take a cikin mutane.
"A yadda ake yaɗa jita-jita wai ana ganin ƙarfin jinin da Samudu ya samu, sanadiyar auren ƴar ƙabilar ARYA ne.
"Tsakanin ƙabilar ARYA da KUYURU akwai kyakkyawar alaƙa. Wasu har cewa ma suke sarauniya ARYA ce ta taimakawa Samudul Ansari wajen ƙirƙirar ƙabilar Kuyuru. Babu wanda ya san haƙiƙanin gaskiyar wannan al'amari face tsoho Samazan dake cikin kogon dutse yana rayuwa a yankin birnin Hindu.
"A lokacin tattaunawar ku da gimbiya Jaanu, na lura da waɗansu abubuwa guda uku; YADDA TAKE BAYAR DA AMSA, YANAYIN GASHIN KANTA da kuma KALAR ƘWAYAR IDANUNTA.
"Idan zata bayar da amsa bata tsayawa yin wani dogon tunani, a take bada amsa kuma sai kaga amsar ta dace da tambayar; wato tana da ƙarfin ƙwaƙwalwa. Sannan ta sadaukar da rayuwar mahaifinta saboda tsananin zaluncinsa, wannan yana nuni da cewa lallai tana da tsananin adalci bata ɗauko halayyar mahaifinta ba.
"Sannan a yadda na lura gashin kanta, asalinsa ba jajawur bane. Wannan yasa na ɗauki samfurin tauraruwarta naje na gudanar da bincike. Gimbiya Jaanu da wani irin gashi aka haifeta (blonde hair) kasancewar babu masu irin wannan gashi a wannan daula gaba ɗaya yasa sarki Ayubu yin saurin rina wannan gashi izuwa ja.
"Sannan duk wannan kyawun gimbiya Jaanu da mutane suke kallo rabi ne kawai akan ainihin kyawunta. Akwai wani hijabin sihiri wanda yake ɓoye ainihin kyawun nata.
"Idanuwanta kuma sak, yadda ka san na sarauniya Arya wacce tayi zamani da sarki Samudul Ansari. Ba su da wani bambanci tamkar an tsaga kara. Duk duniya in banda ƴan ƙabilar ARYA babu masu irin wannan idanu.
"Ayman, ka san dalilin da yasa na ce maka dole sai ka auri ARYA?"
Cikin tsananin mamaki Aymanul Faris ya girgiza kai alamar bai sani ba. Tabbas zuwansu wannan waje yana da matuƙar amfani ana ta fayyace masa ainihin Jaanu. Haba, shi kansa yayi mamaki da ya kamu da sonta farat ɗaya kuma ya gagara cire son nata daga cikin ransa.
"Saboda RUHIN SAMUDUL ANSARI ba zai taɓa zama a jikinka din-din-din ba face yana jin jinin ARYA yana yawo a jikinka. Kuyi sani cewa koda ka mallaki wannan ruhi idan baka auri Arya ba, zai na fita daga jikinka a duk sa'adda yaga dama. Kaga hakan kuma matsala ce, don zai iya kubce maka. Amma idan ya sami jinin ARYA a jikinka, to ya shiga kenan. Ba zai taɓa fita ba.
"Don haka ka zage damtse iyakar iyawarka wajen ganin ka auri Jaanu, domin idan babu ita ruhin kakanka zai na yawo a jikinka (ya fita, ya dawo)." Aljani Ranganu ya ƙara da cewa.
Har Aymanul Faris ya buɗi baki zaiyi tambaya amma sai aljani Ranganu ya dakatar da shi ya ce, "Yi hakuri ya babban jarumi. Zamu tattauna akan sarauniya Arya nan gaba idan kuka kammala waɗannan ayyuka guda goma. Yanzu mu dawo kan batun wannan gidan ƙarƙashin ƙasa na sarki Kuffuru.
"Kamar yadda na sanar da ku, wannan gida na da ƙofofin shiga guda uku masu haɗarin gaske. Ƙofa ta farko tana amfani da hoton fuskar sarki Kuffuru. Ƙofa ta biyu tana amfani da zanen yatsun sarki Kuffuru da kuma jininsa. Sannan ƙofa ta uku tana amfani da ƙarfin jini, kamar yadda muka sanar da ku.
"Babu yadda za'a yi ƙofa ta farko ta buɗe face an sami fuskar sarki Kuffuru. Kun san wannan abu ne wanda zaiyi matuƙar wahala, amma a bisa binciken da muka gudanar, muna tunanin fuskar mutum-mutuminsa zata iya buɗe wannan ƙofa. Wannan yasa muka samar da mutum-mutumi mai tsarin halitta da zubi irin na sarki Kuffuru abinda kawai ba mu samu ba shine fuskar da zata dace da wannan mutum-mutumi da kuma ainihin zanen ƴan yatsun sarki Kuffuru.
"Zan iya cewa waɗannan abubuwa guda biyu su ne abubuwan da zaku tafi nemowa a cikin duniya; ainihin fuskar sarki Kuffuru da zanen yatsunsa." Aljani Ranganu na zuwa nan a zancensa ya sake yin shuru ya baiwa Barban da Aymanul Faris damar yin tambaya.
Cikin nutsuwa Barban ya dube shi ya ce, "Tayaya waɗannan abubuwa guda biyu zasu yiwu, bayan duk duniya in banda sarki Kuffuru babu mai irin fuskarsa, kuma babu mai irin zanen-yatsunsa?"
Aljani Ranganu yayi murmushi ya ce, "Kuyi shirin tafiya zuwa garin Rildaz da garin Sulken."
Cikin mamaki Barban ya dube shi ya ce, "Mai girma. Garin Rildaz da Sulken fa kace, wajen waye da waye zamuje?"
Aljani Ranganu ya yi murmushi maimakon ya baiwa Barban amsar wannan tambaya kawai saiya tafa hannayensa sau uku, nan take wani mutum-mutumi ya bayyana a tsakiyar wannan fada a gabansu. Tsarin jikinsa da yanayinsa duk irin na sarki Kuffuru ne, amma daidai fuskarsa da tafukan hannayensa duk a shafe suke.
"Kunga wannan mutum-mutumin? Idan har muka kammala shi, tamkar mun shiga wannan gida na ƙarƙashin ƙasa ne. Abubuwa da za ku nemo shi ne fuskar da zata dace da shi, da kuma ainihin zanen-yatsunsa.
"A bisa binciken da muka gudanar duk duniya Tameer ne kaɗai zai iya zana mana taswirar fuskar sarki Kuffuru wacce zata yi daidai da ta ainihin sarki Kuffurun; tamkar an tsaga kara. Tameer na zaune a can garin Rildaz, dole ne kuje ku same shi domin ya samar mana da wannan taswira ta fusakar Kuffuru, aikin Tameer yana da mugun tsadar gaske.
"Sannan batun samun zanen yatsun sarki Kuffuru kuwa, dole kuje garin Sulken ku sadu da sarkin-mayu Jadukar ya samar muku da kurwar sarki Kuffuru.
"Barban akan hanƴarku ka yiwa Aymanul Faris bayani akan wajajen da za'a ratsa kafun a isa Rildaz da Sulken. Idan babu mai tambaya a cikinku zan sa a mayar da ku ɓoyayyiyar fada."
***RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 45: *Tafiya zuwa garin Rildaz*
*
*
UMAR SANGARU
*
A wannan karon ma wani irin mugun jiri ne ya sake ɗibar Aymanul Faris ya sulale ƙasa sumamme, yana buɗe idanunsa ya tsinci kansa kwance a tsakiyar ɓoyayyiyar fadar Barban. Yana tashi zaune ya kalli Barban zaune akan wannan karaga ya ƙurawa wata takarda dake shimfiɗe akan wani teburi idanu.
Barban ya yafito shi da hannu, ya taho ya zauna gefen Barban bisa wannan karaga. Shima saiya ƙurawa wannan taswira idanu. A jikin taswirar hoton wani ƙaton kogi ne wanda ya kewaye wani ɗan ƙaramin gari, kamar dai yadda teku ta kewaye tsibirin Gazwar.
"Kaga wannan kogin? A yankin birnin Zaryen yake. Wannan kogi kuma akan sa ne zamuyi tafiya har mu riski garin Rildaz inda Tameer yake. Wannan kogi ƙatoton gaske ne domin zamu iya yin sati guda akan sa muna tafiya bamu isa garin Rildaz ba, wai ma ace bamu haɗu da muggan halittun dake rayuwa a cikinsa ba.
"Kayi sani cewa garin Rildaz wani wuri ne a duniya mai cike da albarkatun ƙasa har na ban al'ajabi. Duk wanda ya samu a rayuwar sa ya kaiwa garin Rildaz ziyara koda sau daya ne tofa ya gama zamowa gawurtaccen attajiri wanda hatta ƴaƴansa baza su san babu ba. Abinda aka fi samu a wannan gari shi ne ɗanyen-zinari wanda ake sarrafawa izuwa kowanne irin kayan ado.
"Wannan kogi a wasu littatafan tarihi an kira shi da suna RIL, yana da tsohon tarihi. Abinda yasa mutane basa ratsawa ta cikin kogin Ril kuma basa son zuwa garin Rildaz shi ne, a cikin kogin Ril akwai wata zabgegiyar macijiya mai kawuna bakwai, wacce take iya kifar da jirgin ruwa komai girmanta, kuma take iya haɗiye mutane goma a lokaci guda.
"Su kansu mutanen dake rayuwa a garin Rildaz suna matuƙar tsoron wannan macijiya kuma su ma basu isa su fito daga wannan gari ba, a yadda nake samun labari a shekarun baya akwai ƙarancin abinci a wannan gari, kowa daga cikinsu ya tara dukiya mai yawan gaske amma ta banza ce don babu abinda zasu yi da ita. Su kansu zasuyi farin ciki idan aka ce yau an sami wanda ya kashe wannan macijiya.
"Don haka ya zamo dole a gare mu, mu sare kan wannan macijiya sannan mu kaiwa ita Tameer a sirrance ba tare da kowa a wannan gari ya gani ba, in dai muka yi haka na tabbata zai amince ya zana mana taswirar fuskar sarki Kuffuru. Saboda idan aka kalli kan wannan macijiya a hannunsa za'a ɗauka shi ne wanda ya kasheta a karrama shi a wannan gari, sannan a bashi babban matsayi wannan yana daga cikin burin Tameer a duniya, wato samun matsayi.
"Ai maganar tsadar aiki da maigirma Ranganu ya kawo abinda yake nufi kenan, wato kashe wannan macijiya. Idan baka da tambaya zansa a kaimu bakin wannan ƙaton kogi na Ril sannan wanne irin makami kake buƙata domin yaƙar wannan macijiya da shi?"
Aymanul Faris ya ce, "Dangane da batun tafiyar mu izuwa garin Jildaz na fahimci komai amma tambayar da nake son nayi akan maganganun da muka tattauna da masoyiyata Jaanu ne. Naga ko tambayata akan abubuwan da muka tattauna baka yi ba, bayan kuma akwai tambayoyi da yawa waɗanda nake tunanin kaine kaɗai zaka amsa min su."
Barban ya yi murmushi ya ce, "Faɗi tambayoyinka, ai banyi tsammanin kun tattauna akan wani abu wanda ya shafe ni ko ya shafi aikinmu ba."
"Shin kana da labarin cewa sarki Ayubul Zairiy ya tafi kaiwa sarki Kim Sam na birnin Sin ziyara? Shiyasa lokacin da muka je birnin ka kalli yanayin mulkin garin ya sauya ai sarauniya Jaanu ce akan karagar."
Barban ya yi murmushi ya ce, "Bani da labari, amma na san abinda yasa ya kaiwa Kim Sam ziyara. Yana so su haɗa kai ne domin suyi farauta ta. Abinda bai sani ba shi ne tuni ya makara, domin yanzu waɗanda suke farautata suna da tsananin yawan gaske. Ga su sarki Kuffuru da su sarauniya Rauziyya. Ka bar batun wannan sarki kawai, wahalar banza zai sha kuma a ƙarshe zaiyi nadamar ɗauko wannan aiki da yayi. Faɗa min kalar makaman da kake so domin yaƙar wannan macijiya?"
Aymanul Faris ya yi murmushi ya ce, "Ƙananun adduna guda biyu kawai nake buƙata." Barban ya ɗaga hannunsa sama nan take waɗansu adduna guda biyu suka bayyana. Ya miƙawa su Ayman, yana karɓa Barban

Please Login or Register in order to submit comment