Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jarumin da RUHIN Samudul Ansari ya zaɓa a matsayin magajinsa ya sameta. Babu buƙatar a koya masa yadda zai sarrafa takobin, kamar tsafi komai zai shiga kansa. To, shi Aymanul Faris ya riga ma ya karance bayanan takobin, tun kafun ya mallake ta.
Cikin kwanciyar hankali da yarda da kai Aymanul Faris ya kaiwa iska sara da wannan takobi, nan take waɗannan aljanu guda huɗu dake yawo a cikin iska suka tunkari waɗannan dakaru guda huɗu gadan-gadan.
Kafun dakarun su ankara tuni aljanun guda huɗu sun riske su. Kamar an jefa kara a cikin wuta, haka waɗannan aljanu suka babbake dakarun guda huɗu. Abinda su Aymanul Faris suka sake gani kawai shi ne zubewar tokar waɗannan dakaru a ƙasa.
Aymanul Faris ya yi murmushi sannan ya mayar da takobin cikin kufenta, suka nufi hanƴar fita shi da Barban.
Ashe dukkanin abinda ya faru wazirin sarki Kuffuru da sarkin yaƙinsa suna kallo, saboda haka suka yi gaggawar sanar da dakarun sarki Kuffuru kada su yi gangancin tunkarar waɗannan mutane guda biyu saboda hatsabibancin su yafi ƙarfin a yi gaba-da-gaba da su.
Barban ya cewa Aymanul Faris, "Kada ka kashe kowa face wanda yazo mana da niyyar cutarwa."
Ana kallon-kallo tsakanin wazirin sarki Kuffuru, sarkin yaƙinsa da dakarun su da kuma su Barban. Cikin kwanciyar hankali su Aymanul Faris suka zo giftawa ta gaban waziri da sarkin yaƙi.
Sarkin yaƙin cikin tsananin fusata ya daka wawan tsalle sama ya kaiwa Barban sara da takobinsa a kafaɗa, da nufin ya tsarge Barban gida biyu.
Wataƙila Barban bai kalli wannan sara ba, ko kuma ya kalla kawai tsananin yarda da kai ce tasa ya ƙi motsawa.
Saura ƙiris wannan takobi ta dira akan kafaɗar Barban, kawai aka ga bayyanar wata zabgegiyar mai ƙarfen wuta, ta raba takobin sarkin yaƙi gida biyu. Sannan ta wuce ta fille wuyansa.
Kamar cikin wuta aka sa kan sarkin yaƙi, haka kayin ya guntule sannan ya faɗo kasa a gashe.
Lamarin ya sake ɗugunzuma hankalin waziri da sauran dakaru kenan, suka ja baya a tsorace. Suna ji suna gani, Aymanul Faris da Barban suka fita daga cikin wannan fada.
"To, ya muka iya duk wanda yace zai sha gabansu abinda ya faru da sarkin yaƙi, shi zai faru da shi. Mu jira sarki ya dawo kawai mu bashi labari." wazirin sarki Kuffuru ya ƙare yiwa jama'a bayani.
Barban da Aymanul Faris suna zuwa bayan gari, Barban ya shafi wannan kambu nasa su aljani Hubbus Dawan suka bayyana, ya basu umarnin kai su birnin Darul Barban inda mahaifiyar Aymanul Faris da jaruma Riya suke rayuwa.
Idan bamu manta ba, lokacin da Barban yaje ɗaukar Aymanul Faris a wajen su jaruma Riya mun ji cewa, yayi alƙawarin duk bayan makonni biyu zasu na kawowa su Hajriya ziyara domin ganin yadda suke.
A tsakiyar wannan birni, Hubbus Dawan ya sauƙe su Aymanul Faris sannan suka ɓace ɓat!
"Kayi haƙuri Ayman," inji Barban. "Tabbas na ɓoye maka wani abu. Gaba ɗaya mutanen dake cikin wannan birni, babu bare ko kuma ɗan wata ƙabila dabam. Dukkanin su ƴan-uwanku ne - ƴan ƙabilar Kuyuru da suka yi saura a birnin Shaha-Deher kuma su ma asalin jinin Samudul Ansari ne.
"Abinda ya sa na ɓoye su a wannan birni shi ne saboda naga duk duniya babu inda zasu zauna, su sami kwanciyar hankali kamar nan ɗin."
Aymanul Faris ya cika da tsananin mamakin abubuwa guda biyu - abu na farko shi ne wai shin tun suna rayuwa a ƙauyen Gazwar, Barban ya kafa wannan birni? Abu na biyu me Barban yake nufi da cewa 'ƴan-uwanku ne' kenan yana nufin shi ba ɗan ƙabilar Kuyuru bane?
Aymanul Faris yana shirin tambayar Barban kenan. Ya ji muryar Barban a kunnensa. "Saboda haka, idan kazo gabatar da wannan takobi gaba ɗaya mutanen wannan gari zaka tara!"
Yana gama faɗin haka, ya wuce gaba Aymanul Faris ya bi shi a baya suka nufi unguwar BARBANUL KUYUR. Duk inda suka wuce sai dai kaga mutane suna ta zubewa suna kwasar gaisuwa a wajen Barban.
Aymanul Faris ya cika da tsananin mamaki, idan a ce duk waɗannan mutane jinin Samudul Ansari ne, mene ne dalilin da yasa zasu ɗinga girmama Barban haka?
Amma da ya tuno abinda Barban ya faɗa masa cewa, tun suna yara yake ceto su daga wajen yaƙi ya kawo su wannan birni ya yi musu sutura. Sai hankalinsa ya ɗan kwanta.
Haka dai suka ci gaba da tafiya, Aymanul Faris yana ta saƙe-saƙe a cikin ransa, shi kuma Barban yana ta karɓar gaisuwar jama'a. Har suka iso wannan unguwa ta zallan mutanen Gazwar.
Kai tsaye suka ƙarisa bakin ƙofar shiga wannan gida, waɗannan dakaru guda huɗu suka buɗe musu ƙofa, suka shige cikin wannan gida.
Tun ana saura kwanaki uku wannan rana tazo, jaruma Riya ta fara shiri. A da kullum mutum zai kalleta a cikin sulken yaƙi, tana sanƴe da gajerun adduna a kunkuminta. Amma tun sa'adda ta bayyanawa Aymanul Faris sirrin zuciyarta ta ajiye batun kayan yaƙi a gefe.
A wannan rana ta saka baƙaƙen kaya, wannan sutura ba ƙaramin kyawu tayi mata ba. Gashin kanta baƙi ne, idanuwanta baƙaƙe ne sidik, leɓɓan bakinta kuma kamar ruwan zuma haka suke.
Tana zaune ita da Hajriya suna tattaunawa akan zuwan Aymanul Faris. Kamar daga sama suka hango shigowar su Aymanul Faris da Barban cikin wannan gida.
Jaruma Riya bata san sa'adda ta fara murmushin farin ciki ba, ita kuma Hajriya ƙamewa tayi saboda ganin takobin dake ɗaure a gadon bayan ɗan nata.
Hajriya tana daga cikin mutanen da suka rayu a shekarar da aka samar da wannan takobi, kuma ko ba komai ita ce matar Hasanul Jalwar mutumin da ya fara amfani da wannan takobi. Saboda wannan dalili ita ma tasan sirruka da yawa akan wannan takobi.
Jaruma Riya bata jira Aymanul Faris ya ƙaraso wannan wuri ba ta ruga da gudu ta rungume shi, Barban ya dube su yayi murmushi sannan ya wuce inda Hajriya ke zaune suka yi gaisuwar bayan rabuwa.
"Gaskiya naga wannan yarinƴar ta zaƙe da yawa fa," inji Barban.
Hajriya ta tari numfashin sa ta ce, "Bar batun yaran nan a gefe, a ina kuka samo wannan takobi mai daraja ta mijina?"
Barban ya yi murmushi ya ce, "Wannan takobi tana daga cikin makaman yaƙi guda huɗu da zamu nemo domin cika burin da mijinki ya mutu da shi."
A ɗaya ɓangaren kuwa, tsantsar soyayya ce jaruma Riya take nunawa Aymanul Faris. Ta ƙanƙame jikinsa harma ya rasa ya zaiyi ya janye jikinsa daga nata.
"Tun da mun zo, ai sai ki sakeni naje na gaishe da umma ko?" inji Aymanul Faris yana ƙoƙarin janƴe jikinsa daga nata.
Jaruma Riya ta sake ƙanƙame jikinta a jikinsa tayi masa raɗa a kunne, "Yaushe za'a ɗaura mana aure?"
"AURE KUMA?" Aymanul Faris ya faɗa da ƙarfi lamarin da yasa hankalin Hajriya Barban ya karkato kansu kenan, suka juyo suka kalle su.
Maimakon jaruma Riya ta ji kunƴa, kawai sumbatar Aymanul Faris tayi a kumatu, Hajriya da Barban duk suna kallo.
Aymanul Faris ya kaikaici idonta, ya janye jikinsa da sauri sannan ya ruga inda su Hajriya ke zaune. Jaruma Riya ta bishi da gudu tana dariya.
Kafun ta iso shi tuni ya isa gaban Hajriya kuma har ya durƙusa a gaban kujerar da take zaune, yana gaishe da ita.
Hajriya ta dube shi cikin tsananin farin ciki ta ce, "Da fatan kun zo lafiya?"
"Lafiya ƙalau!" ya ce.
Hajriya ta bashi umarnin zama akan kujera, nan take ya bi wannan umarni ya zauna akan kujera gefen Barban. Kamar jaruma Riya jira take tana ganin ya zauna itama ta zauna a gefensa sannan ta ɗaura hannunta akan nasa.
"Yau da yamma zamu kira gagarumin taro a cikin wannan birni, domin mu gabatar musu da wannan takobi wacce Aymanul Faris ya samo." inji Barban.
Hajriya tayi murmushi mai nuna jin daɗi ta ce, "Ban damu da inda kuka samo wannan takobi ba, abin farin ciki shi ne kun samo takobin da mijina ya mutu da baƙin cikin rasa ta."
Haka dai suka ci gaba da hira kuma suna cin abinci, har tsahon ɗan lokaci.
***
@#@#@#@##@RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 50: *Ɗa magajin uba*
*
*
UMAR SANGARU
*
Tun kafun la'asar tayi Barban ya kirawo wani hadiminsa da ke wannan gari ya bashi umarnin ya kirawo dukkanin jama'ar dake cikin wannan gari su taru a fada, akwai gagarumar sanarwa wacce ta shafi kowa da kowa.
Hadimin ya amsa da na'am sannan ya tashi ya tafi cika wannan umarni. Nan take ya kirawo manzanni ya aika su unguwa-unguwa dake cikin wannan gari su isar da saƙo. Kafun ka ce me wannan tuni jama'a sun soma amsa kira.
Fadar wannan gari ta soma cika tana batsewa da jama'a. Dukda cewa wannan gari ƙarami ne amma fadarsa babba ce sosai, wajen mutum dubu ashirin ne suka taru amma duka sai da ta ɗauke su.
A saman wani dogon gini Barban da Aymanul Faris da wanna hadimi suka hallara. A ƙasan su ga dubbannin jama'a.
"Mutanen birnin Darul Barban, barka da wannan lokaci." Barban ya fara jawabi. "A yau zan gabatar muku da babban baƙo, wanda na shafe fiye da shekaru goma ina jiran bayyanar sa. Masu iya magana suka ce kyawun ɗa ya gaji ubansa.
"Idan ba ku manta ba, na baku labarin cewa shugaba Hasanul Jalwar ya faɗi, a harin mamaya da sarki Ayubu ya kai tsibirin Gazwar. Amma, kafun wannan shugaba mai adalci ya mutu sai da ya bar baya.
"Wannan jarumi da kuke kallo ba wani bane illa AYMANUL FARIS ƊAN HASANUL JALWAR. A matsayina na mai jagorantar wannan gari kuma wanda yake da burin sake kafa birnin Shaha, na binciko wannan yaro a duk inda yake a faɗin duniya.
"Ni da Aymanul Faris mun haɗa kai munyi wani babban aiki wanda ya dawo mana da takobinmu abin alfaharin mu." Barban na zuwa nan a zancensa ya dubi Aymanul Faris ya gyaɗa masa kai.
Aymanul Faris ya zaro wannan takobi ta Saiful-Shiradu daga cikin kufenta, ƙarfen wannan takobi ya yiwa jama'a sallama.
Nan take gaba ɗaya jama'ar dake wannan wuri suka ruɗe da shewa suka yi ta yiwa Aymanul Faris jinjina, suka tabbatar da cewa lallai ya cika ɗa magajin uba.
Ganin yadda waɗannan jama'a ke tsananin murna ne yasa Aymanul Faris ya tabbatar da cewa lallai waɗannan mutane ƴan asalin birnin Shaha ne, kuma wannan abu ya bashi ƙwarin gwiwa matuƙa wajen ganin ya tsaya iyakacin iyawarsa don sake kafa babbar daular birnin Shaha.
Aymanul Faris ya ɗaga wannan takobi sama, hasken rana ya doketa take ta fara sheƙi. Mutanen na ganin haka, suka yi shiru tsit domin ga dukkan alamu magana yake so yayi.
"Jama'ar wannan gari. Ƴan uwana. Ni Aymanul Faris ɗan Hasanu jikan Kusufu, magajin ruhin mai girma Samudul Ansari. Daga wannan ta yau uku ga watan Oktoba, na ɗauki alƙawarin cika burin da mahaifina ya mutu dashi. Komai ruwa, komai iska, komai tsawa ba zan fasa cika wannan alƙawari ba.
"Birnin Shaha saiya sake dawowa ƙarƙashin mulkin mutum guda ɗaya. Ni da ku, zamu sake kafa wancan daula da ta rushe. Wannan alƙawari ne."
Aymanul Faris na gama ɗaukar wannan alƙawari ya sauƙe wannan takobi tasa, sannan ya juya ya shige cikin wannan gidan sarauta. Mutanen wannan wuri gaba ɗayansu suka ruɗe da shewa dattijan cikinsu suka fara yiwa Aymanul Faris addu'a da fatan samun nasara.
Barban ya ci gaba da yiwa jama'a jawabi yana kwantar musu da hankali, gami da nuna musu shirye-shiryen da suke shi da Aymanul Faris wajen daƙusar da sarki Kuffuru da sarki Ayubul Zairiy.
***
~Birnin Sin
***
Kamar yadda yazo a littatafan tarihi na wancan zamani, birnin Sin babban birni ne mai tarin manƴan gine-gine. Birnin na da yawan al'umma da kuma tarin sojojin yaƙi kamar zasu ci babu. A tattalin arziki kuwa, idan wannan birni na Sin baizo na farko ba, to, zaizo na biyu. Saboda haka babu talakawa da yawa a garin.
Sarkin dake mulkin wannan birni na Sin a wancan zamani, wani babban sarki ne kuma gawurtaccen boka. Ana kiran wannan sarki da suna Kim Sam. Mun taɓa jin labarinsa amma bamu taɓa kallonsa ba.
Duk tsananin girman wannan birni na Sin, abin mamaki ƙofar shiga birnin guda ɗaya ce. Sannan kuma babu wanda ake bari ya shiga cikin wannan birni face an caje shi, kuma dole saiya nuna shaidar shiga wannan birni.
Wani ɗan ƙaramin tanti aka keɓe a gefe, wanda mutane suke shiga ciki su bayar da bayanan su, sannan a yanka musu wannan shaida.
Ba don komai mutanen Sin suka yi wannan tsari ba, sai domin gujewa shigowar mugayen mutane ko kuma ɓarayi. Tun sa'adda Barban ya koyawa sarki Kim Sam hankali aka fara wannan tsari.
Abin mamaki wasu mutane guda biyu ne suka shiga cikin wannan tanti, kowa dake wannan wuri kallon su yake, saboda sai da aka ɗan yi cacar baki da su kafun su amince su shiga wannan tanti.
Abinda ya ɓatawa shugaban masu tsaron wannan wuri rai shi ne, mutanen guda biyu fuskokin su a rufe suke. In banda idanuwansu babu abinda ake kallo, sun saka baƙin rawani sun rufe fuskokin su.
Babu yadda ba'a yi dasu ba akan su buɗe fuskokin nasu amma sun ƙi. Saboda wannan dalili ne yasa shugaban waɗannan dakaru ya tura su cikin wannan ɗaki.
Waɗannan mutane guda biyu suna shigowa cikin wannan ɗaki, suka tsinci kansu a tsakiyar waɗansu gabza-gabzan sadaukai guda goma, sun kewaye su waɗansu mutum guda biyu dake zaune a gaban wani teburi sun saka tulin takardu a gaba.
Babu gardama waɗannan mutane guda biyu suka zauna akan kujeru guda biyu. Mutane guda biyu masu ɗaukar bayanai suka ɗago kai suka dubi waɗannan mutane guda biyu.
Ɗaya daga cikin su ya yamutse fuska. "Don kun raina mana hankali shi ne zaku zo wannan wuri da rufaffiyar fuska? Aka ce muku birnin Sin kamar sauran biranai ne?"
Na gefensa ya harari mutane biyun ya ce, "Idan kun ga kun sami shaidar shiga birnin Sin, ku tabbatar da cewa kun buɗe fuskokin ku!"
Aka baiwa waɗannan mutane biyu tsahon daƙiƙa talatin domin su buɗe fuskokin su, amma sun ƙi. Har waɗannan mutane guda biyu sun dubi sadaukai guda goman nan, sun gyaɗa musu kai akan su hukunta waɗannan mutane.
Kawai sai aka ji ɗaya daga cikin mutane biyun nan ya yi magana. "Mu baƙin sarkin ku ne, kuma baƙi masu daraja. Meye amfanin ɓata mana lokaci wajen bin layi da kuma samun wannan shaida alhali mu ba ɓoyayyun mutane bane?" ya ce.
Cikin maganganun wannan mutumi akwai hikima don haka sai waɗannan mutane dake shirin afka musu, suka ɗan dakata.
"Sarki ya san da zuwanku? Meye ma'anar ɓoye fuskar da kuke yi, idan har kun kasance baƙi masu daraja?" inji ɗaya daga cikin masu shigar da bayanan nan.
"Idan har na buɗe fuskata, kun yarda ba za ku razana ba?" mutumin da yayi magana da farkon nan ya tambaye su.
"Razana?" inji mai shigar da bayanai. "Kana tunanin a gaban ƙananun jarumai kake ne? Wanne irin sadauki ne bamu kalla a duniya ba?"
Mutumin yayi murmushi, sannan ya ɗan buɗe fuskar sa kaɗan. Abin mamaki ba wani bane illa sarki Ayubu mahaifin gimbiya Jaanu, wanda ya kashe Hasanul Jalwar.
Waɗannan mutane guda biyu suna ganin fuskarsa suka miƙe tsaye cikin tsananin mamaki, sadaukan nan guda goma kuma, suka zare waɗansu kulaken ƙarfe na duka zasu afka musu.
Tsakanin birnin Sin da birnin Damashkar tafiya ce mai tsananin tsahon gaske. Amma, saboda yadda wannan daula tasu tayi ƙaurin suna, duk duniya babu inda ba'a san waɗannan manƴan sarakuna guda uku ba. Wato sarki Kuffuru, sarki Ayubul Zairy da kuma marigayi Ratanam.
A daidai wannan lokaci ne aka jiwo sukuwar dawakai da yawa a wajen wannan tanti, lamarin da yasa waɗannan dakaru dakatawa kenan da ci gaba da tambayar su sarki Ayubul Zairiy.
Ɗaya daga cikinsu ya leƙa ta waje ta cikin wata ƴar ƙaramar taga, ya hango abinda ya haddasa wannan gagarumar sukuwa ta dawakai.
Cikin tsananin razana ya dubi ƴan uwansa ya ce, "Sarki ne da kansa yazo wannan wuri, tayaya aka yi ya samu labarin waɗannan baƙi?"
Kafun su amsa wannan tambaya, suka kalli wani hadimi ya shigo cikin wannan tanti, ya dubi su sarki Ayubul Zairiy da boka Ruguzan ya ce, "Sarki na jiran ku a waje."
Sarki Ayubu da boka Ruguzan suka yi murmushi suka kwance wannan rawani da ya rufe musu fuska sannan suka miƙe tsaye suka bi bayan wannan hadimi. Suna fitowa suka yi arba da sarki Kim Sam.
Kamar yadda aka san mutanen birnin Sin, haka wannan sarki ma yake. Wato gajere ne sosai, sannan yana da ƙiba da manƴan gaɓɓai. Kansa babu gashi ko sili guda yasha ƙwal-kobo.
A wannan rana ya saka baƙaƙen kaya, waɗanda aka yiwa ɗauri da farin yanki a kunkumi.
Sarki Kim Sam bai jira su sarki Ayubu suka ƙaraso inda yake tsaye ba, ya taka da kansa yaje inda suke.
Cikin tsananin farin ciki da aminci suka miƙawa juna hannu suka gaisa a karon farko.
"Sunana Kim Sam ɗan Jiu Sin mai mulkin birnin Sin, nayi bincike akan ka a cikin madubin tsafina tun kafin ka iso wannan birni nawa. Kayi haƙuri da ɓata ma lokaci da dakaruna suka yi, tabbas basu san kai waye bane shiyasa." inji sarki Kim Sam.
Sarki Ayubul Zairiy ya yi murmushi ya ce, "Babu buƙatar na gabatar da kaina, tun da ka riga ka sanni. Abinda ya kamata na sanar da kai shi ne abinda ya kawo ni amma bazan faɗa maka anan ba, face ka sa an kaimu masauƙi mai kyau. Mun kwanta mun huta. Idan muka sami nutsuwa sai mu tattauna."
Sarki Kim Sam ya yi murmushi ya ce, "Dama ai ban ce zamu tattauna a wannan wuri ba, nazo ne domin nayi muku tarɓa."
Yana gama faɗin haka ya juya, ya shige cikin wani ƙasaitaccen keken doki, yasa aka kawowa sarki Ayubu da boka Ruguzan ma nasu keken dokin.
Suna shiga cikin wannan keken dokin, boka Ruguzan ya dubi sarki Ayubu ya ce, "Ka ce akan hanƴa zamu ƙarasa sauran bayanan amma baka ce dani komai ba, ga shi har mun iso wannan birni na Sin?"
Sarki Ayubu ya yi murmushi cikin yaƙe ya ce, "Dalilin da yasa ban sanar da kai yadda aikin zai kasance ba shi ne, ina so naga yadda sarki Kim Sam zai tarɓe mu ne. Idan na sanar da kai sirrukan yadda aikin zai kasance kuma sarki Kim Sam ya ƙi ya bamu haɗin kai, akwai yiwuwar ka baiwa wani bayanan, ya tafi kamo Barban. Yanzu sai ka nutsu da kyau domin jin bayanan."
Boka Ruguzan ya gyara zama cikin tsananin mamaki wannan hikima ta sarki Ayubu, sannan saida ya girgiza bisa ganin duk yadda yake da kusanci da wannan sarki ace bai yarda shi ba.
"Abu na farko da zamu fara tambayar sarki Kim Sam shi ne wannan hatimi wanda Barban ya ajiye masa, sa'adda ya sace dukiyarsa gaba ɗaya. Na tabbata a wancan lokaci Barban da hannunsa ya taɓa wannan hatimi, saboda haka za'a sami zanen yatsunsa a jiki.
"Abu na biyu shi ne, zamu kaiwa boka Biu Lin ziyara, domin ku haɗa ƙarfi da ƙarfe kai da shi, ku samar mana da taswira wacce zamu bi diddigin Barban da ita." Sarki Ayubu na zuwa nan a zancensa aka tsayar da wannan keken doki. Ashe har sun iso wannan masarauta ta sarki Kim Sam.
Gidan sarauta ne mai girman gaske, komai nasa an tsara shi kamar yadda mutanen birnin Sin suka saba gina gidajen sarakunan su tun a tarihi.
Sarki Kim Sam yasa wannan hadimi nasa ya kai sarki Ayubu da boka Ruguzan wani ƙasaitaccen gida na alfarma dake gefen gidan wannan sarauta. Kuyangi suka kai musu abinci da abinsha na alfarma.
Tsahon kwanaki biyu aka barsu a cikin wannan gida, suka kwanta suka huta sosai.
A ranar kwana ta biyun ne da yammaci, sarki Kim Sam ya turo wannan hadimi nasa ya gayyace su izuwa cin abincin dare. Ayubu da Ruguzan suka amsa da na'am zasu zo wannan gayyata.
Ai kuwa rana na faɗuwa, wata kuyanga tayi musu jagora izuwa cikin gidan sarautar sarki Kim Sam, suna shigowa wannan hadimi ya tarye su, sannan ya nufi hanyar da zata kai shi wani babban ɗaki. Sarki Ayubu da boka Ruguzan suka take masa baya.
Suna shigowa cikin wannan ɗaki suka tsinci kansu a tsakiyar wani ƙatoton wuri wanda aka ajiye wani ƙaton teburi a tsakiyarsa. An cika wannan teburi da kayan abinci wajen kala ashirin. Dukda cewa a wannan lokaci da dare ne, amma idan ka kalli cikin wannan ɗaki zaka ɗauka da tsakar rana ne saboda tsananin haske.
Sarki Kim Sam na zaune bisa wata kujera dake tsakiyar wannan teburi ya saka kwanon abinci a gaba. Yana ganin sun shigo yayi murmushi sannan ya nuna musu wajen zama a gefensa. Wannan hadimi nasa ya risina sannan ya fice daga cikin wannan ɗaki.
Sarki Ayubu da boka Ruguzan suka zubawa kansu abinci a cikin faranti, sannan suka fara ci. Sarki Kim Sam yayi murmushin jin daɗi sannan shima ya zubawa kansa abincin.
Bayan shuɗewar ɗan gajeren lokaci dukkanin su, suka koshi sannan suka fuskanci juna.
"Yauwa, yanzu sai mu tattauna akan abinda ya kawo ku wannan birni nawa?" inji sarki Kim Sam.
Sarki Ayubul Zairiy ya yi gyaran murya ya ce, "Ya kai wannan sarki mai daraja, kayi sani cewa ba komai ne ya kawo mu wannan birni naka ba, face tattaunawa akan yadda zamu kamo gagarumin ɓarawon da ya yi maka sata a shekarun baya, ya tarwatsa maka babban burinka na duniya a wancan lokaci."
Sarki Kim Sam na jin haka ya miƙe tsaye a fusace, sannan jikinsa ya fara tsuma. Ga dukkan alamu duk lokacin da aka kawo masa wannan baƙin labari da ya wuce yana shiga irin wannan hali.
"Me kuke so ku ce? Ku na tunanin idan muka haɗa kai zamu iya kamo shi ne? Abinda manƴan bokayen duniya suka gagara yi shi ne kuke tunanin mu zamu iya?" inji Kim Sam.
Sarki Ayubul Zairiy ya yi dariya ya ce, "A yadda muka yi imani a daularmu, duk duniya babu abinda ba zai yiwu ba, sai dai a gagara yin abun. Wai, a tunani na duk girman wannan birni naka da ƙarfin mulki naka, ace mutum ɗaya yazo yayi maka sata kuma ya gudu sannan ace baka farauto shi a duniya ba, sai nake ganin kamar abin kunƴa ne.
"Ni nan da kake kallo, watannin baya da suka wuce ƴata yazo ya sace. Shi ɓarawo tamkar wutar daji haka yake, idan ba'a haɗu an kashe ta ba, wataran sai ta shafe duniya gaba ɗaya.
"Kada ka manta, idan muka kamo wannan ɓarawo dukiyarka zata dawo, sannan zamu samu ƙarfin mulki irin wanda babu mahaluƙin da ya taɓa samu ba."
Sarki Kim Sam ya ɗan yi shuru yana tunani, daga bisani ya numfasa ya ce, "Kana ta maganar kamo wannan ɓarawo. Ta ina zamu fara nemo shi, mutumin duk duniya babu wanda ya taɓa kallon sa, idan ba amintattunsa ba?"
Sarki Ayubul Zairiy ya yi murmushi ya ce, "Idan har abinda muka imani yi da shi a nahiyarmu gaskiya ne, wannan abu ne mai sauƙi. Abubuwa guda uku muke buƙata domin samar da taswirar da zata bi diddigin wannan ɓarawo, har mu isa inda yake mu kamo shi.
"Abu na farko zanen yatsunsa, abu na biyu cibiyarsa, abu na uku, shekarar haihuwarsa da sunan mahaifiyarsa."


Please Login or Register in order to submit comment