Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Jalwar wannan mata da wannan ƴa basa raye.
Bayan wannan mutumi ya shaƙi numfashi sosai, sai ya miƙe zaune ya rarrafa kan gawar matarsa da ƴarsa yana girgiza su, yana kuka gami da ambaton sunansu.
Kwallar tausayi ta zubowa Hasanul Jalwar da Jarata suka koma gefe da wannan mutumi, suka shiga rarrashinsa. Bayan ɗan lokaci ya daina kuka, suka ɗauki waɗannan gawarwaki guda biyu suka koma cikin wannan ƙauye, aka toni kabari aka binne su.
Hasanul Jalwar ya baiwa wannan mutumi masauƙi mai kyau, aka kai masa abinci da abinsha na alfarma. Hasanul Jalwar ya ce a barshi tsahon kwanaki uku ya huta, kafun a tambaye shi, shi waye.
Bayan kwanaki uku Hasanul Jalwar ya keɓe da wannan mutumi a cikin fadarsa, suka fara tattaunawa. A wannan rana siffar wannan mutumi ta gama bayyana.
Mutumin ya kasance dogo, mai yawan gemu da ƙasumba. Gashin kansa ruwan toka ne, idanuwansa kuwa tamkar na zaki. Wannan mutumi ya yiwa Hasanul Jalwar kama da attajiri Auran Ziyas saboda abubuwa guda biyu; na farko kalar gashin kansa da kuma tsahon da kaurinsa.
"Ya sunanka?" inji Hasanul Jalwar.
"Suna na Haidar Ziyas daga birnin Saizar nake!" inji mutumin.
Jin wannan suna yasa Hasanul Jalwar yaji kamar ya miƙe ya cakwamo kolar mutumin.
"Haidar Ziyas?" Hasanul Jalwar ya yamutse fuska. "Me ya kawo ka wannan ƙauye...?"
Haidar Ziyas ya zube ƙasa ya fara karkarwa ya ce, "Ya shugabana, meyasa daga jin sunana zaka harzuƙa? Kayi sani cewa wani ɗan-uwana nake nema fiye da watanni goma yabar garinmu ya tafi fatauci izuwa kan tsibirurruka, nayi yawo akan teku har na gaji amma ko labarinsa ban ji ba. Rannan ina yawo akan teku sai matata take bani labarin wannan tsibiri na Gazwar da abubuwan da ake samu akan tsibirin. Na san ɗan-uwana sosai da son sayen amfanin gona shi ne nace bari nazo tsibirin na duba ko yana nan, bisa rashin sa'a raƙuman ruwa suka taso suka kifar da jirginmu har kuka tsince mu, anan na rasa matana da ƴata. A halin yanzu bani da kowa kuma bani da komai a dunkya, ɗan-uwana ya ɓata, matana da ƴata duk sun mutum. Ban ga sauran amfanin rayuwata a duniya ba." Haidar ya fashe da kuka lokacin da yazo nan a zancensa.
Da yake sarki Hasanul Jalwar ya kasance mai tsananin tausayi sai yayi tsammanin duk abinda Haidar ya faɗa masa gaskiya ne, shima har idanunsa suka ciko da kwalla.
"Tabbas ɗan-uwanka yazo wannan tsibiri, amma hatta mu kanmu bamu san meya faru gare shi ba. Ya zauna na tsawon watanni bakwai, yayi mana sallama muka haɗa shi da dakaru guda hamsin suyi masa rakiya akan hanyarsu aka yi musu fashi. Mun rasa dukkanin dakarunmu guda hamsin amma bamu ga gawar ɗan-uwanka ba." Hasanul Jalwar ya ce.
Haidar Ziyas ya kwarara uban ihu yana cewa, "Na shiga uku, na lalace. Tabbas dodo Haiƙalu ya samu nasarar kama Auran Ziyas dama sai da na hana shi tafiya wannan fatauci amma ya ƙi, ga shi yanzu Haiƙalu ya kama shi a banza. Ina zan saka rayuwa ta?"
Hasanul Jalwar ya dafa kafaɗar Haidar Ziyas ya ce, "Kwantar da hankalinka, ka bani labarin Auran Ziyas da abinda yasa wannan dodo ke farautarsa. Idan na gamsu da zancenka zan yi maka sutura na baka muhalli da gona a ƙauye na."
Haidar Ziyas ya goge hawayen idanunsa ya ce, "Ya kai wannan shugaba mai yawan adalci, kayi sani cewa asalinmu mu ƴan ƙabilar Adbéncan ne. Shekaru uku da suka wuce ƙabilar GORGON suka yiwa birninmu dirar mikiya suka hallaka kowa da kowa dake garin, tun daga wannan lokaci ake farautarmu ana kaiwa dodo Haiƙalu dake tsakiyar tekun Saizar. Bamu san meyasa ba amma tun daga wannan lokaci wannan dodo ke farautar rayuwarmu ruwa-a-jallo kuma ko shakka bana yi, shi ne ya kama Auran Ziyas ya kuma kashe waɗanda suke tare dashi."
Hasanul Jalwar yayi jim yana jinjina maganganun Haidar a cikin ransa, gaba ɗaya maganar babu abin kamawa a ciki. Haka kawai a ce dodo yana farautar su? Hasanul Jalwar ya ƙudurce a ransa daga baya zaiyi bincike sosai akan Haidar Ziyas, idan ya gano wani abu mara kyau dangane dashi to tabbas sallamarsa zaiyi.
Daga wannan rana aka baiwa Haidar Ziyas wurin zama a cikin ƙauyen Gazwar kuma aka bashi gona, ya ci gaba da zama a ƙauyen yana taya jama'a noma.
Wani babban kuskure da Hasanul Jalwar yayi shi ne, kwata-kwata bai baiwa aljani Nara labarin Haidar Ziyas ba kuma bai bayyanawa kowa ainihin sunan Haidar ɗin ba.
Wannan yana daga cikin kuskuren da Hasanul Jalwar yafi tsana a rayuwarsa, kuma yana daga cikin abinda ya ƙara zafafa ƙiyayyarsa ga Kuffuru domin illar da yayi masa a wannan ƙauye.
Watanni uku bayan zuwan Haidar Ziyas tsibirin Gazwar matar Hasanul Jalwar ta sami juna-biyu, farin ciki wajen Hasanul Jalwar ba'a cewa komai. Ya daina zuwa ko'ina ya dawo kula da matarsa shi kaɗai.
Bayan kwanaki biyu sarkin-noma yayi gayya zuwa gonarsa domin a taya shi noma. Mutane aƙalla ɗari suka amsa wannan gayyata ciki har da Haidar Ziyas, Hasanul Jalwar bai san meke faruwa ba.
Tsahon ɗan lokaci ana ta noma, kowa ya himmatu ana ta aiki. Idan ba'a manta sarkin-noma shi ne mahaifin matar Hasanul Jalwar wato Hajriya.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani, aka ji Haidar Ziyas ya furta waɗansu kalmomi wanda shi kaɗai yasan abinda ya faɗa. Kalmomin sun fi kama da samfurin ɗalasimi don haka wani babban iko ne ya sauƙa a wannan gona. Irin ikon da ƴan-ƙabilar Gandiz suke amfani dashi su yi nasara a filin yaƙi.
Faruwar hakan keda wuya dukkanin jama'a suka tsaitsaya a inda suke tsaye, ba tare da kowa ya motsa daga inda yake ba. Cikin rashin imani Haidar Ziyas ya bushe da dariyar mugunta ya fiddo wannar takobi tasa, yayi ta sokawa jama'a a ƙahon-zuci har ya hallaka mutane ɗari ɗinnan ciki harda sarkin-noma. Abin mamaki su kansu mutanen basu san abinda ya faru ba, sun dai san cewa kawai kashe su aka yi. Lallai wannan ɗalasimi na ƙabilar Gandiz abin tsoro ne.
Haidar Ziyas na gama kashe waɗannan mutane ya kwaɓe rigarsa ya jiƙata da jini sannan ya ruga da gudu ya faɗa cikin ruwan-teku ya ɓace. Jinin jama'ar da ya kashe ya fara kwaranya yana shiga cikin ƙauyen Gazwar.
Ana cikin harkoki kawai aka ga jini kamar ruwa yana ta gudu, nan fa jama'a suka ɗimauce suka fara ihu suna gudu. Kan kace me tuni ƙauyen Gazwar ya hargitse da hayaniya gami da koke-koke.
Hasanul Jalwar tare da Jarata da sauran manƴan ƙabilar suka je gonar sarkin-noma suka ga abinda ya faru. Nan ma duk suka sake fashewa da kuka. Wancan karon mutum hamsin, wannan karon mutum ɗari. A watanni uku kacal, sun rasa mutum ɗari da hamsin a wannan ɗan ƙaramin ƙauye wanda kwata-kwata basu wuce dubu uku ba.
A wannan karon Hasanul Jalwar bai ga laifin kowa ba face laifin kansa, don haka zubewa ƙasa yayi sumamme. Wannan mutuwa ta mutum ɗari tafi ta wancan mutum hamsin ɗin tashin hankali, da firgita mutanen ƙauyen Gazwar.
Sai da Hasanul Jalwar yayi kwanaki biyu bai ci ba kuma bai sha ba, domin nuna jimamin sa akan wannan mummunan abu da ya faru. Kai a ƙarshe ma tarewa yayi ya koma bayan gari ya zauna a gindin bishiya yayi ta kuka.
Rannan yana zaune a gindin bishiya yana kuka, yana kallon ruwan teku. Ba zato ya ji an dafa kafaɗarsa ta baya, cikin hanzari ya waiga take yai arba da matarsa Hajriya. Ta zauna a gefensa tasa hannunta ta share masa hawaye sannan ta kama kafaɗunsa ta ce.
"Kaifa shugaba ne, shugaba kuma baya kuka! A kullum shugaba baya nuna gazawarsa ga abokan gabarsa domin idan yayi hakan, zasu sami damar cin galaba akansa. Abinda ya faru ya riga ya faru, tashi mu koma cikin gari."
Hasanul Jalwar ya ce, "Ya ke matata, kiyi sani cewa, ba wai ina kuka akan mutanen da na rasa bane. Kuma ba wai ina kuka akan jininsu da ya zuba bane. Abinda yasa nake shi ne na gano cewa wani babban shiri aka yiwa ƴaƴan mai girma Samudul Ansari domin a mallaki tsarkaken ruhinsa ta kowanne hali. Babban abin takaicina shi ne na gagara gano waye wannan wanda ke zuwa har cikin wannan ƙauye yana yi mana ɓarna. A ce har mutum ɗari da hamsin sun mutu a ƙarƙashin mulkina kuma ina cikin ƙauyen ba wai wani waje naje ba? Kai, tabbas ko waye wannan taƙadari zai fuskanci hukunci..." Ya ƙare maganarsa hawaye masu zafi na biyo kumatunsa.
"Na san abinda zanyi, tashi mu tafi..." Ya ƙara da cewa.
Ba tare da ɓata lokaci ba suka kama hanƴar komawa cikin wannan ƙauye, shi da Hajriya. Suna shigowa Hasanul Jalwar bai tsaya a ko'ina ba, sai a gidan ƙarƙashin ƙasa inda aljani Nara yake. Yana tsayawa a bakin wannan ƙaton rami, wuta tayi feshi siffar aljani Nara ta bayyana.
Fuskar aljani Nara a murtuƙe take, zaka iya cewa Hasanul Jalwar bai taɓa ganin fusatar aljanin irin ta wannan lokaci ba.
"Ina ka shiga...?" Aljani ya daka masa tsawa, wadda tasa wuta tayi feshi daga cikin bakinsa.
Babu buƙatar bayani Hasanul Jalwar ya gano cewa, aljani Nara yaga dukkanin abinda ya faru tsakaninsa da Haidar Ziyas da sauran jama'ar gari.
"Ka san meye babban rauninka a duniya?" inji aljani Nara. "Kana da tsananin tausayi, dole abokan gabarka zasuyi amfani da wannan tausayi naka, su yaƙe ka. Ya za'a yi ka kalli ruwa ya ciwo mutane har guda uku, kuma suna tafiya a tare? Ya za'ayi ka kalli mutum mai kama da Auran Ziyas kuma baza kazo ka bani labarinsa ba. Tabbas kayi ganganci sosai da kayi saurin yarda da abinda Haidar ya faɗa ma domin duka ƙarya ya shirya maka. Ya kai Hasanu kayi sani cewa a halin yanzu a faɗin duniya babu jini mai tsarki, kamar na Samudul Ansari shiyasa ake neman jininku ruwa-a-jallo. Ina so kayi duba izuwa ga tafin hannuna..."
Hasanul Jalwar ya share hawayen idanunsa ya ɗago kansa ya kalli tafin hannun aljani Nara, take yayi arba da wani allon tsafi mai ɗauke da hoton wata ƙatuwar kwalba wacce aka ɗurawa jini. Babban abinda yafi bashi mamaki shi ne babu marufi a jikin kwalbar, to ta ina ake ɗura wannan jini? Kuma ma jininsu su waye?
"Kaga wannan kwalba? Sarki Gauhan Ansari babban abokin gabar Samúdúl Ansari shi ne wanda ya samar da ita domin cika babban burin rayuwarsa. Gauhan ba shi da burin da yafi ace shi ne wanda ya zauna akan karagar birnin Shaha, amma wannan buri nasa bai cika ba sakamakon baƙin sihirin da Samudul Ansari yayi wanda ya hana kowa zama akan wannan karaga. Babu yadda za'ayi wannan baƙin sihiri ya karye face Samudul Ansari da kansa ya karya shi, sanin kanka ne yanzu Samudul Ansari baya raye ammafa ruhinsa na nan. Duk wanda ya mallaki wannan ruhi, zai iya karya wannan sihiri kuma zai iya zama akan karagar mulkin harma ya gudanar da al'amuran mulkin.
"Sanin kanka ne don ku Samudul Ansari yayi wannan ɓakin-tsafi kuma don ku ya ɓoye wannan ruhi nasa domin ku gaje shi. To ka sani cewa ƴaƴan Gauhan da jikokinsa na nan a raye, kuma sun yi caa akan lallai su ma sai sun mallaki wannan ruhi.
"Idan mutum ya kasance jinin Samudul Ansari salin-alin zai mallaki wannan ruhi, ba tare da matsalar komai ba matukar aka ce ruhin ya zaɓe shi. To, amma ga ƴaƴan Gauhan Ansari da wani jini dabam da basu kasance asalin wannan jini ba, dole suna buƙatar ƙarfin jiki da wadataccen jini wanda zai taimaka musu matuƙa wajen mallakar wannan ruhi. Jinin da zai wadatar dole ne ya kai yawan gangar jiki dubu, wato jinin mutum dubu. A halin yanzu Haidar Ziyas ya hallaka mutum ɗari da hamsin saura masa mutum takwas da hamsin wannan kwalba ta cika, idan ta cika zai iya amfani da jinin da suka tara ya samar da gangar jiki wacce zata iya ɗaukar ruhin Samudul Ansari ba tare da ta tarwatse ba.
"Wannan jini da kake kallo, ba jinin kowa bane face na jama'arka da ka rasa. Wannan kwalba ta Gauhan Ansari tana zuƙar jinin ƴaƴan Samudul Ansari, da Auran Ziyas ko mahaifiyarsa suka kashe. Kuma zata cika matuƙar aka ce an hallaka mutum dubu. Cikin waɗannan watanni biyu da na faɗa ma, nayi bincike akan Auran Ziyas kuma na gano waye shi da kuma dalilin da yasa yake kashe mutanen wannan ƙauye."
Koda Hasanu ya gama jin batun aljani Nara sai zuciyarsa ta kama tafarfasa, jikinsa ya fara karkarwa. Yana matsayin shugaba kuma jagoran wannan ƙauye ace har za'a yiwo shiri daga wani wuri dabam, a zo ƙauyensa ana hallaka masa mutane? Lallai ko waye wannan shaiɗani dole ne ya hallaka shi, ko don ɗaukarwa jama'arsa da suka mutu fansa.
"Ka gaggauta faɗa min waye wanda ya aikata wannan ɗanyen-aiki domin na saro kansa?!" inji Hasanul Jalwar yana huci.
Kai daga jin kalamansa ka san ransa a tafashe yake, kuma a shirye yake yayi duk abinda ya kamata domin ɗaukar fansa. Zaka iya cewa babu abinda Hasanul Jalwar ke jira, kamar jin sunan wannan mutumi. Kuma lallai indai yaji sunan a take ma zai iya zuwa ya yaƙe shi.
"Ka san sarki Kuffuru na birnin Kufa?" Aljani Nara ya tambaye shi.
Jin wannan suna sai da yasa Hasanul Jalwar ya girgiza. Bai taɓa tsammanin haka ba, kuma ko a mafarki bai taɓa tunanin sarki kamar Kuffuru zai yi masa haka ba.
Wannan daula tana ƙunshe da garuruwa guda huɗu - birnin Damashkar, birnin Hirtoliya, birnin Hadriyan da kuma birnin Kufa.
A duk inda aka sami daula dole ne a sami birnin da yafi sauran ƙarfi kamar yadda ya zamo dole a samu ƙauyuka masu yawan gaske.
To, a wannan daula birnin Kufa yafi waɗannan birane guda uku ƙarfin mulki, tattalin arziki da sojojin yaƙi. Wannan dalilin shiyasa suke tsoron sarki Kuffuru kwarai da gaske.
Abinda ya ɗaurewa Hasanul Jalwar kai shi ne idan har da gaske sarki Kuffuru ne, ai zai iya haɗo runduna ta sojojin yaƙi masu yawan gaske azo a murƙushe su a dare ɗaya.
Sarki kamar Kuffuru mai mulkin babbar ƙasa kamar Kufa ace ya tsaya yiwa ƙaramin ƙauye kamar Gazwar yaƙin sunƙuru tabbas akwai dalili mai ƙarfi.
Hasanul Jalwar ya jinjina kai ya ce, "Waye Gauhan Ansari? Mene ne dalilin da yasa sarki Kuffuru bai ɗebo runduna suka zo suka shafe mu ba?"
Aljani Nara na jin haka ya nuna takobin Saiful Shiradu dake ɗaure a gadon bayan Hasanul Jalwar ya ce, "Wannan takobi ita ce amsar tambayarka; tabbas shakkar wannan takobi shi ne ya hana sarki Kuffuru kawowa wannan ƙauye mamayar-bazato. Gauhan Ansari? Shi ne babban maƙiyin Samudul Ansari kamar yadda yazo a tarihi. Ya kai Hasanu kayi sani cewa wannan takobi tana da matuƙar daraja sosai, ka fara ganin kaɗan daga cikin amfaninta. Sarki Kuffuru ba zai taɓa samun nasara akanka ba face ya rabaka da wannan takobi, wannan shi ne dalilin da yasa nace ka riƙe wannan takobi da kyau. Ba za'a taɓa samun nasara akanka ba face baka tare da ita. Wannan abu haka yake kuma nayi imani da haka."
Hasanul Jalwar ya gyaɗa kai ya ce, "Babu ruwana da waye Kuffuru. Babu ruwana da dalilin da yasa yake kashe min mutane. Abinda na sani kawai shi ne ya shigo ƙauyena, ya kashe min mutane, kuma dole zan ɗauki fansa. Babban abinda nake son sani shi ne tayaya zan shiga birnin Kufa ba tare da wata matsala ba?"
*****RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 35: *Mugun-gamo*
*
*
✍️✍️✍️ Umar Sangaru ✍️✍️✍️
*
Koda aljani Nara yaji wannan alwashi na Hasanul Jalwar sai yayi murmushin jinjina ya ce, "Da kyau namiji, haka nake son jin ƙarfin zuciya irin ta ƴaƴan Samudul Ansari. Kayi sani cewa sarki Kuffuru na da ubangida wani taƙadarin aljani kuma shi ne yake bashi umarnin zuwa wannan ƙauye. Ina so ka sake yin duba izuwa tafin hannuna."
Hasanul Jalwar ya sake duban tafin hannun aljani Nara, nan take yayi arba da wani garjejen ƙaton mutum cikin kwale-kwale ya tunkaro ƙauyen Gazwar kuma har ya iso LUSLEL. Mutumin ya yi shiga ta yaƙi mai kwarjinin gaske, ya lulluɓe jikinsa da sulke, sannan ya cika damatsan hannunsa da gurayen tsafi.
Abinda ya bambanta wannan mutumi da Auran Ziyas kawai shi ne, gashin kansa jajawur ne saɓanin na Auran Ziyas da ya kasance ruwan-toka. Sannan kuma kalar ƙwayar idanunsa shuɗi ce maimakon ta Auran Ziyas mai kama da na mage.
Hasanul Jalwar ba shi da buƙatar a faɗa masa wannan mutumi ko wane ne, domin kuwa ya riga ya gano waye shi. Abinda ya rage mana shi ne mu masu karatu mu gano waye wannan mutumi.
Idan muka matsa kusa sosai zamu ga mutumin ya kasance saurayi mai manyan gaɓɓai, fuskarsa na bayar da kwarjini da ƙanshin sarauta. Duk wanda yasan sarki Kuffuru zai ga shi ne a cikin wannan kwale-kwale ba wani ba.
Abinda ya baiwa Hasanul Jalwar mamaki shi ne, mene ne ya dawo da sarki Kuffuru izuwa ƙauyensa shi ɗaya jal? Idan muna son amsar wannan tambaya dole sai mun koma baya sa'a guda kafun Hasanul Jalwar ya shigo wannan gida na ƙarƙashin ƙasa.
****
Bayan sarki Kuffuru ya faɗa cikin wannan teku, bayan ya gama hallaka waɗannan mutane guda ɗari sai ya fara iyo ya nufi wani ƙaramin tsibiri dake can nesa. Abin mamaki tazarar dake tsakaninsa da wannan tsibiri ta kai tafiyar zango goma amma cikin ƴan dakiku ya dira akan tsibirin.
Yana isa ya ƙarasa gindin wata bishiya ya zauna, ya kwalawa aljani Hasamul-Sawaz kira sau uku. Nan take aljani Hasamul-Sawaz ya bayyana a gabansa cikin girmamawa, Kuffuru ya umarci aljanin da ya kaishi kogon tsafin sarki Gauhan domin ganin ci gaban da aka samu bayan hallaka waɗannan mutum ɗari.
Ba tare da ɓata lokacin komai ba, Hasamul-Sawaz ya ɗauke shi suka lulluka cikin gajimare basu sauƙa a ko'ina ba sai a cikin wannan ƙaton kogo wanda babu komai a cikinsa face wannan ƙatuwar kwalba.
Sarki Kuffuru yayi mamaki matuƙa sakamakon ganin yadda jinin ya ƙaru sosai a cikin wannan kwalba, ammafa har a wannan lokaci ko kaso ɗaya cikin huɗu na wannan kwalba, jinin bai kai ba.
Aljani Hasamul-Sawaz ya sake durƙusawa ya ɗauki sarki Kuffuru suka fice daga cikin kogon, suka bayyana a saman dajin.
Sai dai kuma a daidai wannan lokaci ne, duwatsun dake cikin wannan daji suka fara ɓuɓɓugowa daga ƙarƙashin ƙasa suna tashi sama cikin iska. Hasamul-Sawaz ya zaro zabgegiyar takobinsa cikin shirin ko-ta-kwana, a iya saninsa dai a duk lokacin da irin wannan abu ya faru tabbas wani babban ifiritu ne ke faman bayyana.
Sarki Kuffuru yai dariya ya ce, "Kwantar da hankalinka babban hadimi, tabbas na san abinda ke faruwa. Kada ka damu wannan aljani da zai bayyana ba mai cutarwa bane a gare mu, dama ina so zan gabatar da kai a gare shi."
Sarki Kuffuru na rufe bakinsa wadannan duwatsu suka fara curewa a waje guda suna bayar da siffar aljani Bukalshiyu Djinn, shi dai aljani Hasamul-Sawaz sai yai kasake yana kallon abinda ke faruwa cikin tsananin mamaki. Karo na farko a rayuwarsa yaga yadda halitta take samuwa daga duwatsu, lallai al'amarin Bukalshiyu Djinn abin tsoro ne. Bukalshiyu Djinn na bayyana yai tsawa tamkar an kwararo aradu guda goma a tare, duk tsananin jarumtaka da dakewar zuciya irinta sarki Kuffuru saida hantar cikinsa ta kada, saboda tsananin razana. Zaka iya cewa tunda sarki Kuffuru ya hadu da Bukalshiyu Djinn bai taba ganin bacin ransa irin na wannan lokaci ba. Shi kuma Hasamul-Sawaz hade gira yayi yana kallon aljani Bukalshiyu Djinn, yana mamakin waye shi harda zai dakawa sarki Kuffuru tsawa?
"Tunda na hadu da kai," inji Bukalshiyu Djinn. "Na taba barinka ka taho da wani a yayin ganawarmu? Idan zaka iya tunawa a karon farko na haduwata da kai, mahaifiyarka tana cikin dajin amma ban nemi ka taho tare da ita ba. Kayi min bayanin wannan aljani kafun na rumurmushe shi."
Koda sarki Kuffuru yaji haka sai ya murtuke fuska ya ce, "Na san abinda nakeyi shiyasa nace wannnan aljani ya tsaya domin na gabar dashi a gareka. Kayi sani cewa idan babu wannan aljani ba zamu san inda kogon Gauhan yake ba balle har mu fara dura mata jini. Manta da batun wannan aljani ka fada min abinda ke tafe da kai don wannan aljani shi ne ginshikin nasararmu." Djinn ya murtuke fuska ya harari Hasamul-Salwaz sannan ya dubi sarki Kuffuru ya ce, "Ya muka yi da kai kafun ka koma kauyen Gazwar? Na ce maka idan ka koma ka san yadda zakayi ka sato takobin SAIFUL-SHIRADU amma baka bi wannan umarni ba, dukda karfin jinin Gandiz da ka samu. To, ka sani cewa wannan abu da kayi ka tafka babban kuskure yanzu haka Hasanul Jalwar da aljaninsa sun gama gano waye kai, kuma suna can suna ta shirye-shiryen kawo maka farmaki. Idan har bamuyi da gaske ba, tabbas haduwarka da mai takobin Saiful-Shiradu ba zata yi ma dadi ba. Babu yadda muka iya ko muna so, ko bama so Hasanul Jalwar da aljaninsa sai sun kawo mana farmaki. Abinda zamu mayar da hankali akansa shi ne yadda zamu kare kanmu daga sharrin wannan rantsatstsiyar takobi. Ka sani cewa asalin wannan takobi daga wuta aka samar da ita sannan aka yi mata ado da tafashashshiyar dalma,sai aka lullubeta da bakin karfe. Babu wani abu a wannan duniya da takobin Saiful-Shiradu ba zata ratsa ta cikinsa ba ko mene ne, kama daga kan dutse, karfe, itace, kankara, iska da wadansun wadannan. Kaga kenan idan kana gwabza yaki da mamallakin wannan takobi, idan ya kawo ma sara ka tare da taka takobin, wannan takobi raba takobinka gida biyu zatai. Tun lokacin da sarki Samudul Ansari ya samar da wannan takobi na dauki samfurinta kuma nake ta bincike akanta. Kayi sani cewa a duk fadin duniya kabila daya ce take da kwarin jiki wanda wannan takobi ba zata iya ratsawa ba, in dai ba jinin wannan kabila muka samu muka yi maka tsari dashi ba. Babu makawa Hasanul Jalwar zai sami nasara akanka..."
Maimakon fuskar sarki Kuffuru ta nuna alamun damuwa kawai murmushi yayi ya ce, "Da sauki ma ai, tunda akwai jinin kabilar da zatayi mana maganin wannan takobi. Fada min a duk yan wannan kabila suke, ni kuma nayi alkawarin kamo daya daga cikinsu domin mu gudanar da wannan tsari." Bukalshiyu Djinn yai dariya ya ce, "Babu tabbacin wannan jini zaiyi, kuma a halin yanzu abinda nake tunani shi ne, duk fadin duniya dan wannan kabila guda daya jal ya rage. Sunan kabilar dai ita ce, SHUMBUL." Sarki Kuffuru ya karkata kai alaman baiji abinda Bukalshiyu Djinn ya ce ba. "Ka ce sunan kabilar mene?" ya ce. Djinn ya sake maimaita masa sunan kabilar wato SHUMBUL! Jikin sarki Kuffuru ya fara karkarwa idanunsa suka sauya, ya nemi wuri ya zauna, zufa ta

Please Login or Register in order to submit comment