Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idan ba haka ba sai su ce mu muka kashe ta."

"Innalillahi wa'inna ilaihi taji'un! Ina zamu saka kanmu?"
A cewar Lantana hankalin ta a matu™ar tashe

A lokacin sai ga Jummai mai magani ta shigo gidan tana kwaWa sallama

Jin muryanta yasa Lantana ta fita da sauri tana cewa, "Jummai don Allah ki zo ki yi ceton rai, yarinyar nan fa ta mutu ina gani domin jini ya tsinke mata, na dawo na tarar da ita ba ta nimfashi ban san mai ya same ta ba."

Da jin haka sai Jummai ta nufi Wakin itama da sauri suka shige zuwa wurin Madina; wacce suke tunanin rai yayi halin sa.
*****

Alh. Badamasi kai tsaye daga nan wurin Bokansa ya nufa, bayan ya bayyana a gabansa ya zayyane masa cika aikin da yayi a yau

Boka ya bushe da dariya yace, "madalla aikin ka ya zo gargara, domin a wannan lokacin zaka ga cikan aikin ka da zaran ka sanya ™afa kabar ™auyen nan,ka tafi duk inda zaka je ko'ina kake son zama arzikin ka na can, babu haufi a Wan ™an™anin lokaci zaka ga cikan burinka, abu biyu ya rage maka ka saki yarinyar saki uku, sannan wannan layan da zan baka; ka kasance da ita duk inda zaka je, babu kai babu talauci, zaka yi mamakin samun Waukakar ka."
Ya ™are maganar yana dariya mai ™ara da amsa kuwa

Farin ciki kuwa ya cika Alh. Badamasi tsaban dad'i, domin har hankalin sa ya kwanta sabida jin aikin nasa ya zo ™arshe, yanzu sai biyan bu™ata, don haka ya amshi layan kamar yanda Bokan ya mi™a masa, ya sake cewa, "amma maganar da ka faWa min cewa yarinyar babu ita babu aure, yanzu ya zan yi? Wanne taimako zaka bani Boka domin kar yarinyar tayi aure bani da labari?"

Idanunsa ya zare a kansa yana kallonsa da jajayen idanunsa masu ban tsoro, cikin amon muryansa yace, "ba auren ta bane matsalar ka, daga zaran da aka kusance ta ™adarin aikin ka zai karye, sai dai a sake sabon aiki, kuma aikin dole da ita za a sake, domin ita ce ™addaran arzikin ka, dole sai ka sake auren ta sannan zaka sake samun wani arzikin. Tana da ™ashin arziki yarinyar; duk wanda ya aure ta sai ya tabbatar da hakan."

Jin haka hankalin Alh. Badamasi ya tashi ainun, domin babban aiki ne a gabansa, idan aikin sa ya Saci taya ya zai iya samo ta har ya aure ta? Shiyasa yace ma Bokan, "Boka babu wani hanya sai wannan dole? Bazan iya auren wata ba dole sai ita?"

Fuska ya Waure tamau yace, "ita ce ™addaran ka, ko baka ji mai nace maka bane? Dole da ita za a sake aiki, kuskurenka ka bari wani ya kusance ta."

Zufa ya sharce daga fuskarsa, hankalin sa ya ™ara tashi sosai yake duban Bokan, sai yace, "to Ranka ya daWe ka taimaka kayi min aikin da babu wanda zai iya kusantan ta har abada, domin cikan burina na har abada, zan baka ko nawa ne ko me kake so a duniyar nan."

Dariya ya bushe dashi yana girgiza jikinsa tare da ware hannunsa, sai ya dube sa yace, "an gama da aikin ka, biyan bu™atarka zata biya babu ita babu wani mahalukin da zai kusance ta har abada, koda tayi aure dubu ne, don haka ka je kayi rayuwarka a duk inda kake so ka Wauka bu™atarka ta biya, ka gaggauta zuwa ka cikasa aikin ka yanzu kar lokaci ya ™ure maka."
Daga haka Bokan ya sallame sa tare da Sacewa Sat a wurin

Don haka kai tsaye Alh. Badamasi jiki na rawa bayan ya koma cikin ™auyen, sai ya samu wuri ya Soye Jakar kayansa sannan ya nufi kansa tsaye gidan su Madina,
A ™ofar gida ya tarar da Baba Iro da Nasir suna magana a tsakaninsu, a tsaye ma suke da alamun tsayuwar su kenan, shi Nasir yana ri™e da fatanya zai tafi gona shi ne Baba Iro yake tambayar sa a kan maganar takin da zasu je su siyo a birni,
A nan ya ™ariso wurin batare da yayi musu sallama ba fuskarsa babu walwala a turSune

Ganinsa ne yasa Baba Iro ya faWaWa fara'an sa yana cewa, "ah ah! Alh. Badamasi kai ne tafe ashe?"

Yaya Nasiru gaishe sa yayi cikin girmamawa yana mai gyara fatanyan sa da ke ma™ale a kafaWa

Alh. Badamasi ya amsa har yanzu bai saki fuskarsa ba yake cewa, "dama magana ce ta kawo Ni."

"To fa, Allah yasa lafiya? To ko zamu zauna ne? Yaya Ali ma na cikin gida bari in sa a kira sa."

"A'a ba zancen da ya kawo Ni kenan ba, maganar da ke tafe dani idan ma na faWa muku ya wadatar ai, a kan maganar ita wannan yarinyar ne da aka kaimin ita, to zancen gaskiya bazan iya zama da ita ba sabida ban zaci haka daga gare ta ba, an munafurce Ni an cuce Ni, maganar da nake muku yanzu bazan iya zama da ita ba, da naso in jure in danne in rufa mata asiri mu zauna a haka, amma na ga abun ba mai yiwuwa bane, shiyasa na yanke shawaran sanar muku domin in yanke hukuncina, sai dai kuyi ha™uri tunda kun cuce Ni tun farko baku faWa min ita yarinyar ta san wani a waje ba kafin ku aura min ita, idan da kun faWa min gaskiya zan iya hakura in zauna da ita, amma wannan ba maganar wasa bane tunda har na same ta ba cikakkiyar budurwa ba, a ce kamar yarinyar nan ta san Maza da yawa kafin tayi aure?"
Sai ya girgiza kansa yana mai nuna munin abun daga kan fuskarsa

Daga Baba Iro har Yaya Nasiru da yayi ninyar juya wa ya bar su suyi zancen nasu, jin abun da yake faWa yasa shi dakata wa yana sauroron su, ashe mummunar labarin nan ne zasu ji wanda yasa gaba Wayansu gabansu yayi mugun faWuwa, tashin hankali ya bayyana a fuskokin su duk kansu sun kaWu sun gaza yin magana koda jin zancen da ya gama fita daga bakin Alh. Badamasi, sai suka yi shiru suna bin sa da kallo cike da mamakin furucin sa, taya hakan zai faru yace an cuce sa Madina bata je masa a cikakkiyar budurwa ba? Wannan wanne irin mummunar sharri ne wanda hankali bazai Wauka ba?

"Wai ka san kuwa mai kake faWa Alh. Badamasi?" A cewar Baba Iro da yayi ™arfin halin furta hakan cikin tsananin ruWu da tashin hankalin sa da ya nuna a muryansa

"˜warai kuwa na sani, ai shiyasa na zo na faWa muku tun kafin abu yayi nisa, kar kuma ku ga laifina Ni bazan iya zama da ita ba, na sake ta saki uku ku je ku Wauki yarinyar ku daga gidana."

"Innalillahi ŭ˙˙˙ 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~wa'inna ilaihi taji'un!" Su dukkan su suka furta hakan suna mai zare idanunsu daga kallon Alhjin cikin tashin hankali mara misaltuwa,
Ko kafin suyi magana shi tuni ya juya yabar wurin da saurin sa,
Babu mai ™arfin tsayar dashi daga cikin su sabida halin da suka shiga, jikinsu har rawa yake yi sai furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un suke yi

"Wai kuwa mafarki muke yi Nasiru ko da gaske ne abun da Alhaji ya faWa? Wannan wanne irin mummunar bala'i ne yake tunkaro mu?"

Idanun Yaya Nasiru har sun soma kaWa wa sabida tashin hankali, bai tsaya sauraron Baba Iro ba ya juya da sauri yayi cikin gidan hankalin sa a mugun tashe

Baba Iro ya bi bayansa yana ci gaba da salatin a fili, don yanayin da yake ciki yasa shi ruWewan da bai san cewa da ™arfi yake salatin ba.
[2/2, 9:30 AM] OumŠahira: =ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ
    *RAYUWAR MADINA* =Ĝ§Ü
=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
           _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>ĜŬŬ*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* <Ĝß

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS=ĜŞÜ)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A
'ŝ*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ´an uwana Mata waWanda suka fuskanci u™uban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ™arshen wahalar rayuwa._


















______________ *EPISODE 14*
_____Babu inda Yaya Nasiru ya zarce sai sashin Baban Sasa,
Lokacin yana zaune bakin ™ofan Wakin sa da buta a gaba zai yi alwalan sallan walha da ya saba yi, ya zauna tukunna yana aswaki before ya fara, sai ganin Nasiru yayi ya shigo sashin nasa kamar an jeho sa, har sai da ya ba shi tsoro ya Waga kai yana kallonsa tare da furta, "Subhanallah...! Nasiru, mene ne haka?"

"Baba, ba lafiya ba wlh, yanzun nan Alh. Badamasi ya zo Kofar gida ya tarar damu tare da Baba Iro...."
Nan ya kwashe komai ya sanar mishi

Tun kafin ma ya ™arisa zancen shima Baba Iro ya shigo sashin har lokacin hankalin sa a mugun tashe yake

Shi kansa Baban Sasa yanda ya ruWe tuni ya tashi a kan ™afafunsa yana salati da sallallami, sai yace, "ina shi Badamasin yake?"

Baba Iro yace, "wlh ya tafi, inata yin masa magana amma bai kula Ni ba, mu yanzu ya zamu yi da wannan abun tashin hankalin? Abun da zai yi mana kenan? Sakayyar da zai yi mana kenan?"

Shiru Baban Sasa yayi, domin ransa yayi mugun Saci da abun da Alh. Badamasi yayi musu, in ban da sharri taya ya zai ce sun Wauki yarinya a lalace sun ba shi? Abun da hankali ma bazai Wauka ba ai dole sai dai wula™anta su zai yi

Baba Iro ya sake cewa, "wlh Yaya kawai wula™anci ne irin na masu kuWi yau ya fado kanmu, amma ko ya ci amanar mu wannan mutumin, a ce da abun da zai saka mana kenan? Yanzu ya sakar mana yarinya kenan daga aure? Wannan wanne irin abun kunya ne ya jawo mana?"

Duban Nasiru Baban Sasa yayi, yace, "maza ka kira min Baffanku a sashin sa yanzu ya bar nan."

Yaya Nasiru ya amsa mishi da sauri yana yin gaba domin kiran Baffa

Ko kafin wani lokaci zancen ya soma yaWuwa, tunda gaba Waya sauran iyayen Maza suka taru a sashin; Baba Iro yana maida musu da zance,
Babu wanda hankalin sa ya fi tashi barin Baffa, tunda dole shi zai fi su shiga tashin hankali kasancewar Abokinsa ne Alh. Badamasi ™ut da ™ut, kuma shi yayi masa hanyar da ya samu Madina ya aura, amma kuma tun ba a je ko'ina ba aure kwana biyu kacal; don bata cika na ukun ba ma, amma ya sakar musu ´a, kuma ban da haka har da sharri, don haka tuni ya shuri takalma yabar gidan yana zage-zage da faWin, "Ni Alh. Badamasi zai yi wa haka? Wlh tallahi baza mu Wauki wannan wula™ancin ba; ba zamu taSa yarda ba, ko mene ne sai inda ™arfin mu ya ™are, bari in je in ji dalilin da zai wula™anta mana yarinya har da mata sharri."
Sai ya mi™a jiki ya tafi

Su Yaya Shamsu tuni sun mara masa baya sun bi shi, don suma ransu ya yi ™ololuwar Saci, bare akwai su da zuciya ´an gidan, dukka Samarin gidan suka bi hanya zuwa gidan Alh. Badamasi

Amma koda suka je sun tarar da wani babban tashin hankalin ne da ya Waga musu hankali fiye da wanda suke ciki,
Don a lokacin an fiddo da Madina za a kawo ta gida, kasancewar Jummai mai magani tace, "baza ta taSa ta ba har sai an mayar da ita gida."
Don a ganin su zuwa wannan lokacin Madina ta mutu tunda babu inda nata ke motsi, har lokacin kuma jini na zuban mata ta ™asan ta, sai nannaWo ta aka yi a zani kamar wata jaririya

Baffa yanda ya ruWe kamar zai saka hannu a ka ya kurma ihu, take su Shamsu suka Wauke ta suka wuce da ita gida,
Nan fa hankula ya ™ara tashi sabida ganin yanda Alh. Badamasi ya mayar musu da ´a,
Ga shi su ba zuwa asibiti suka saba dashi ba, don ™arshe sai dai aka kira Malam Bala na-Allah sabida Jummai ta kasa shawo kan matsalar; tunda ita tayi iya yin ta amma ta kasa

Matan gidan kowa jikinsa yayi sanyi sun yi jugum domin kowa yayi amanna Madina ta mutu, baza ta iya rayuwa ba a wannan halin da take ciki, Yaran gidan sai koke-koke suke yi,
Haka ma su Binta kuka kawai suke yi tunda duk suna sashin Baban Sasa inda aka ajiye Madinan a Wakin Inna Lami,
Duk sun yi jugum suna jiran su ga abun da hali zai yi,
Su kansu su Baban Sasa suna nan cikin sasan sun kasa zaune sun kasa tsaye

Su Yaya Ahamdi tuni sun bazama neman Alh. Badamasi, don sun ce, "wlh sai sun kashe sa har lahira in har ™anwarsu ta mutu, domin mutumin nan bai cancanci rayuwa ba, dabba ma ta fi shi tausayi a yanda ya wulakanta musu ™anwa, sai sun kashe sa."
Haka suka fita gidan ana kiran su amma inaa sun ™i tsaya wa sun tafi neman Alh. Badamasi

Basu san cewa shi tuni yabar garin ba, tunda ya san aika-aikan da yayi bazai taSa zama ba

Yusuf ne ya je ya shafa wa Yaya Haula labarin har gida, ai babu shiri ta rugo aguje ta taho gidan nasu tun a hanya take kuka,
Koda ta zo ta tarar da Madina a wannan halin, domin duk yanda aka yi a hana ta shiga Wakin ta™i sauraron mutane, tana kuka ta kutsa kai ciki tana kiran sunan ´ar uwanta, a lokacin da tayi ido biyu da ita sai ta yanke jiki ta faWi, domin halin da ta ga ´an gidan a ciki wanda zuciyarta ta bata shaidar ta rasa ´ar uwanta ne; tana ganin ta a kwance magashiyan ta zube a ™asa a sume, dama ga ta da ™aramin ciki, nan da nan jini ya Salle mata

Ai kuma sai tashin hankalin ya daWu musu, ga Haula a ™asa itama tana zubar da jinin,
Nan fa kowa ya fara salati itama aka kwashe ta su Inna Asabe suka Wibo ruwa aka zuba mata,
Dayake akwai Jummai a wurin ita ta soma duba ta, tana musu bayani, "cikin da ke jikinta ne ya zube."
Sai da aka yi ta zuba mata ruwa sannan ta farfaWo

Kuka sosai take yi tana kiran sunan ´ar uwanta tace, "a barta ta je ta ganta."
Amma haka aka ri™e ta ana bata baki,  but kwata-kwata ta kasa sauraron su, kuka take yi har da su majinu tana son mi™e wa amma jiri ya hana ta,
Inna Amarya ta kama ta tana cewa, "ki yi ha™uri mana Haula, ´ar uwanki bata mutu ba tana nan da ranta, yanzu haka ma ta fara motsi, idan ba ki kwantar da hankalin ki ba kuma kema kika shiga wani hali ya zamu yi umm? Wannan wanne irin bala'i ne?"

Baban Sasa ne yace, "Haulatu, zauna a nan kar ki tashi, kinga ke ma jikin naki babu dad'i, maza zauna bari a kawo miki maganin kema ki sha."
Sai ya dubi Jummai mai magani yace, "itama a haWa mata maganin ta sha tunda ga abun da ya faru da ita."

Haula haWa kai da gwiwa tayi ta dinga rera kuka gunun tausayi, kwata-kwata ba ta jin zafin ciwon da ke addabar ta, ta ™anwarta gudan jininta take tunani, wanne irin azaba Madina take sha a wannan halin? "Allah Sarki! ³ar ™anwata, tun ba a je ko'ina ba Allah na jarabtar ki ta fannoni daban-daban, don Allah ku taimaka ku ceto min ™anwata, ita kaWai ta rage min, bazan iya rayuwa babu ita ba."
Haka take faWa da ™arfi tana ihu har da birgima, don abun yayi mata ciwo da yawa, ba™in cikin ta halin da Madina take ciki Allah kaWai ya san azaban da take sha, idan ta tuna abun da Yusuf ya faWa mata sai hankalinta ya ™ara tashi ainun, ta Sarke da kuka tana kiran sunan Madina, sai ta yun™ura kamar zata tashi amma ta kasa sabida jirin da take gani a cikin idanuwanta, ga shi har lokacin su Inna Amarya suna ri™e da ita sun ™i sakin ta, don halin da ta shiga hankalin su ya tashi tamkar mara hankali ko wacce aljanu suka shafa

Kai sun ga tashin hankali mutanen gidan nan a Wan ™an™anin lokacin nan, bare yanda ake ta duba Madina duk wani taimako an bata amma har lokacin bata farfaWo ba, sai dai da™yar aka tsayar da jinin da ke zuba daga jikinta, mummunar fyaWe yayi mata wanda hankalin su Baban Sasa ya fi na kowa tashi, musamman da Malam Bala yace musu, "sai dai yanda hali ya yiwu, amma gaskiya ya cuce ta, ya rigada ya Sarka ta ya haWa mata wurin kashi da fitsari, in so samu ne a Winke mata wurin."

La haula fisha'atillah! Ban san wanne irin bayani zan yi muku a kan halin da suka shiga ba, bare ga su mutanen karkara basu yarda da wani asibiti ba, kawai dai magungunan gargajiya suka sani, kasancewar Jummai mai magani tana yin Winki idan hakan ta faru, tunda ita kamar anguwar zoma ce amma na ™auye, wasu abubuwan na asibiti duk ta sani, kuma ta saba ma mutane Winki in aka Sarka su aka yi musu fyaWe, sai ta samu igiyar buhu ta saka allura ta Winke mutum, cikin wannan azaban har Mace zata warke, idan da ™aren kwana ta samu lafiya, idan kuma ya zo da akasi sai ta kamu da lalura kala-kala, haka za a yi ta banka mata magani har ta warke, wata kuma a haka zata zauna da ciwon a rasa mai ke damun ta, ko kuma ta zauna a Sarke, shi wurin bai warke ba kuma bata samu lafiya ba na tsawon lokaci, shiyasa yawanci Matan karkaran kwata-kwata basu da galihu, rayuwa kawai suke yi a cikin duhun kai, ko da ganin su ka san cuta ta ci su har ta cinye, kuma Mazajen su ba sa kallonsu da daraja

Bayan an yi wa Madinan Winki ne lokacin Yaya Haula ta koma gida ta ari wayan Mijinta ta kira Ummansu, haka tana kuka ta sanar mata da abun da ke faruwa, tace, "Umma don Allah ki zo ki taimaka kar Madina ta mutu a nan, kin san babu mai kaita asibiti a duba ta, wlh a haka zata mutu har yanzu bata farfaWo ba, ba ta ma iya motsa komai nata tana nan a yadda aka kawo ta, don Allah Umma ki zo ki cece ta kar ta mutu."

Kukan da take yi ya ™ara Waga wa Umma hankali, domin a lokacin da ta gama jin zancen itama fashe wa tayi da kuka sabida tsananin ruWu da jin halin da ´arta take ciki,
Ga shi a lokacin dare yayi sosai, babu yanda za a yi ta kama hanya ta zo ™auyen nan a daren, tunda hanya babu kyau ba a cika bin hanyar da dare ba,
Yanda ta tashi hankalin ta ko barci a ranan ta gaza yi, kai ba ita kadai ba hatta su Hassana da Babansu basu runtsa ba, tunda a halin da Umma take ciki hankalin su suma yayi matu™ar tashi ainun, su Hassana sai kuka suke yi tausayin ´ar uwansu ya cika su

Da sassafe suka kama hanya zuwa ™auyen, da ita da Baban su Hassana, su kuma su Hussaina suka zauna a gida, duk da sun so su bi su a tafi dasu su ga halin da Madinan take ciki, amma Baba yace, "baza su je ba, su zauna a gida har su dawo."
Haka suka tafi suka bar su suka nufi ™auyen a cikin keke napep

Kafin karfe takwas sun isa cikin ™auyen,
A lokacin da suka je har yanzu hankalin mutanen gidan a tashe yake, don a wannan lokacin suna sashin Matan Baban Sasa sun yi cirko-cirko,
Kasancewar a lokacin na farfaWo ina ta yanka ihu da kururuwan azaba, bakina sai furta sunan Ummana nake yi, duk yanda suka so su samu kaina nayi shiru na ™i, aka kira mai maganin domin ya duba Ni, amma abun ya cutura ihun azaba nake yi ina kiran sunan Ummanmu da Yaya Haula

Ga Yaya Haula a wurin ta ri™e ni itama tana ta kukan tana kiran sunana

Ana haka sai ga su Umma sun shigo sasan,
Ai da gudu Umma ta nufi hanyar Wakin tunda ta ji muryan Madina daga can take fitowa, tun kafin ma mutanen su ankare da ita har ta shige itama tana kiran sunan Madinan, hankalin ta a mugun tashe,
Lokacin da ta isa inda ta hange ni kwance babu ko kaya a jikina, an Waure min Wuwawu kamar an yi min nafkin sabida kar jini ya Sata wurin gaba Waya, shine da aka yi min Winki sai aka toshe mini Wuwawun da tsummokarai,
Yaya Haula tana zaune kusa da Ni ta ™an™ame Ni muna kukan a tare,
Tsaban wahala duk na firgice na fita a hayyacina, kuma ba na gane kowa zafin ciwo ne yasa nake kiran sunayen mutanen gidan, wadda sunan Ummanmu ne ya fita a bakina

Kuka Umma ta fashe da shi ta saka salati, sai ta rungumo ni tana girgiza Ni hannunta a saman fuskata tana kiran suna na, "Madina, Madina, ki buWe idanunki Ummanki ne, Madina Madina..."
Sai kiran suna na take yi tana kuka kashirSan saboda tsananin ruWewa, "shikenan, innalillahi wa'inna ilaihi taji'un... Kun kashe min ´a kun cuce ta kun gama da ita, abun da na guda kenan tun farko, Madina yarinya ce amma tsaban mugunta ku ka nuna dole sai kun yi mata aure, kuma ku rasa wanda zaku bata sai wanda ya girmi Ubanta, a haife yayi jika da ita, wlh tallahi bazan yarda ba, idan ´ata ta mutu wlh sai nayi Shari'a da ku tunda kashe min ´a zaku yi, bazan taSa ha™ura ba."
Maganar take yi tana kuka da girgiza Ni, ita kanta bata san mai take furta wa ba sabida halin ruWe wa,
Sai ta mike kuma zata fitar da ni Wakin, ta rungume Ni a cikin jikinta zata fitar da ni

Baban Sasa yace, "Asiya, ki dawo hankalin ki mana, wannan abun da ya faru ™addara ne bamu da yanda zamu yi, duk da mun san zafin abun da aka yi mata ne kike faWin haka amma dole ki yi hakuri ki Waura wa kanki dangana, ki ajiye ta ina za ki je da ita kuma kin san ana duba ta ne?"

Kallonsa tayi idanunta jawur fuskarta tayi jaSe-jaSe da hawaye, a fusace tace, "asibiti zan kaita mana, tunda na ga baku da alamar ceton ta kun barta a nan sai ta mutu tukunna, Ni kuma bazan barta a nan ba wlh tunda Ni ce uwarta."
Sai ta sake fashe wa da wani sabon kuka tana surutai, "iyee wannan wanne irin zalunci ne? Shikenan kun cuce ta kun gama da ita, wlh Allah ya isa bazan taSa yafe wa ba..."

Tun kafin ta idasa maganar Baban Sasa ya daka mata tsawa, yace, "ke Asiya ki shiga taitayin ki, duk maganganun da kika yi bamu ce komai ba hakan bazai yiwu ki zauna kina gaya mana magana ba, har da Allah ya isa ki dubi tsaban idanunmu kina gaya mana wannan kalman don ba ki da mutunci? Don haka duk da kina mahaifiyarta babu inda za ki je da ita tunda mu bamu gaza ba, yanzu ma taimako ake bata kuma da ikon Allah yarinya zata warke ta tashi da ™afafunta, ba ma son maganar banza bamu nemi taimakon ki ba, wannan yarinya dai in har muna da rai baza ki yi iko da ita ba tunda mu ne dolen ta, ki ajiye ta baza ki kaita asibiti ba babu inda za ki matsa da ita, bamu hana ki zuwa ki duba ta ba amma ba ki da wannan hurumin na daukar ta ki kaita wani wuri."

Umma tace, "wlh tallahi bazan ajiye ta ba, ai wannan zalunci ne, don me yarinya tana cikin wani hali amma baza ku kaita asibiti ba? Don kawai kuna rayuwa kamar jakuna baku san inda kanku ke muku ciwo ba sai a tauye wa ´ata hakkinta?"

Ran Baban Sasa ya ™ara Saci ainun, bama shi kaWai ba hatta sauran sabida yanda Umma take kuka tana zagin su, ya sake daka mata tsawa yace, "wlh summa tallahi idan ba ki ajiye ta ba sai na wanka miki mari Asiya, ke ba ki isa ki zo nan kina mana rashin kunya ba, kuma daga yau tunda ba ki da mutunci ba ki san ragowan sa ba, zan nuna miki Madina mun fi ki iko da ita, daga yau nayi miki iyaka da ita har abada, kar ki ™ara tako ™afanki ki zo inda take, ki ajiye ta kibar mana gida yanzu."

Wasa-wasa fa magana ta zama tsiya, domin furr Umma ta shafa wa idanunta toka tace, "wlh baza ta taSa ajiye

Please Login or Register in order to submit comment