Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a gidanmu ba Waya ba; ba biyu ba, irin ciwon da suke yi da wahalar da suke sha, duk da su ba zubar musu ake yi ba Sarewa yake yi, don haka tsoron wahalar da zan sha yasa na ji sam bazan taSa yarda ba, wai yau Ni ce da cikin haihuwa; zuciyata ta kasa yarda da hakan ji nake yi kamar mafarki wai ina da ciki, ™an™ame cikin nayi ina mai runtse idanuna sosai tare da jin zullumin abun da zai faru a gaba, ashe shiyasa na ga cikin nawa ya kumbura ashe dalili kenan?

Koda na ganmu a gida har ajiyar zuciya na sauke ina jin sanyi a raina,
Tunda na ganmu a gida na sadakar ya ha™ura kenan,
Sai dai kalamansa da a yanzu yake faWa min, "in na shiga in haWa kan kayana zai mayar dani ™auye."
Wani irin sara wa gabana yayi, domin ba ™aramin tashin hankali ne ya riske Ni ba tunda ya furta zancen ™auye, amma babu fuskar magana don tuni yabar motan ya wuce cikin gida,
Dole nima na fita na nufi ciki don in yi abun da yace

A lokacin da Yaya Yunus ya sanar da Sharhabila, "yau zai mayar dani ™auye."
DaWi ta dinga ji, don dama har zata sauke kwandon bala'i sabida ganin mun jima bamu dawo ba, amma tunda ta ji haka sai farin cikin ta ya bayyana, tace, "ai gwara haka, don na gaji wlh da ganin ta, ai zaman nata yayi haka gwara a mayar da ita ™auye can ta ™arata. Allah ya raka taki gona, Ni da kaina zan nemo wacce zata maye gurbinta, kuma Ni ba na bu™atar budurwa don hankalina bazai taSa kwanciya da su ba, babban mace zan samo."

Yaya Yunus dai bai kula ta ba, tuni ya tafi Wakinsa zai shirya, hakan yasa itama ta bi bayansa tana masa magana

Ni kuwa ina can Waki na kasa kwantar da hankalina, ban san sanda kuka ya kufce min ba don wlh ba na son koma wa wancan ™auyen, gwara ya mayar dani wajen Ummana amma bazan iya komawa can ™auye ba,
A haka na haWa kayana ina matse hawaye na fito muka tafi,
Dayake babu su Mubashir tunda satin Hutu ne suna can an kaisu gidan su Sharhabila,
Ina ji ina gani muka bar gidan a raina ina jin farin cikin yau wahalar da nake fuskanta a gidan ya ™are min, sai dai kuma ban san mai zan tarar a can ™auye ba, da nan da can duk babu gwara a gare Ni, shiyasa baki na Sari nayi ™o™arin sanar mishi da cewan, "don Allah yakaiNi wurin Ummana ba ™auye ba."

Amma sam Yaya Yunus bai kula Ni ba sai ma wani banzan kallo da ya sauke min, a haka ya durfafi ™auye ina ji ina gani ya mayar dani can,
A lokacin da ya isa Mutanen gidan sun yi mamakin ganin mu da wannan yammacin, lokaci Waya maganar dawowan mu ta bazu ga ´an uwa nan da nan mutane suka cika gidan ana cewa, "a zo a ga Madina."
Tunda tun jinyar da nayi aka Wauke Ni yau kimanin shekara Waya da rabi da barina ™auye,
Shiyasa na zamar musu wata iriya na sauka daga Madinan da suka sani, domin a yanda suka ganni yau ba ™aramin bazata na basu ba, irin girman da nayi musu a fuska da kuma jikin da nayi kowa in ya kalle Ni ri™e baki yake yi,
Ni kuwa kunya ya hana Ni sakin jiki sabida yadda na ga suna bina da ido suna faWin yanda na girma,
Inna Asabe har da cewa, "lallai kam! Birni ya amshe ki Madina, ´ar tselen ´a; ji be yadda fa ta haSake nan da nan tayi mama har da ajiye wasu kumatu, yo Ni gani fa nake yi kamar ciki ne da ita."

"Abun da zan faWa kenan kika riga ni Asabe, wlh ciki ne da yarinyar nan kun ga yadda ta sauya."
A cewar Inna Habiba tana ri™e baki,
Dayake duk a lokacin muna cikin sasansu yara sun tabaibaye Ni sun hana Ni zama sai murna suke yi,
Shi ne suka tasa Ni gaba suna ta maganganun da na kasa Wago kaina sabida kunya

A lokacin sai ga Yaya Haula wacce yara suka je suka kira ta don ta zo ta ganni, da farin ciki ta iso gidan goye da ´ar jaririyarta wacce ta haifa aka sanya mata Abeeda, da gudunta ta ture Yaran tana kiran suna na,
Koda muka haWa ido ai sai muka rungume juna cike da murna, Ni farin cikin ganinta sai na saki kuka nan take ina ™ara matse ta cike da tsananin kewarta da nayi tsawon lokuta,
Ita kuma farin ciki ya hana ta magana sabida ganin yadda na sauya bakin ta ya ™i rufuwa,
Sai da Inna Lami tayi magana tace, "mu zo mu zauna mun tsaya a tsaye kamar an coge mu."
Sannan ne muka zo muka zauna a kan ™aton tabarman da aka shimfiWa a tsakar sashin,
Sasan sai ™ara cika yake yi da mutane; hatta su Nafisa da suke gidan mazajen su sai da suka taho don ganina tunda an basu rahoto, kowacce ta bazamo gyale ta shigo don ganina ana murnan zuwan nawa

Shi kuwa Yaya Yunus can sashin Baban Sasa ya wuce tunda a lokacin mutanen gidan duk suna nan, su Baffa duk sun dawo daga gonakin su; suma suna jin labarin zuwanmu kowa ya fito daga sasasn shi, sai suka taru a falon Baban sasa ana gaisa wa,
Baffonmu Abdullahi yace, "to ai sai ka kira mana itama Madinan mu gaisa da ita a nan, tashi maza ka kira mana ita."

Baban Sasa da ke murmushi yace, "™warai je ka kira mana ita ta zo mu ganta."
Ya ™are maganar da fara'a don ba ™aramin jin daWin wannan ziyaran yayi ba, duk da dai an jima da auren amma ya ji daWi matu™a da zuwan nasu, alamu wata rana da sannu Wan nasa zai ri™a ziyarar su akai-akai tunda bai taSa yin makamanciyar irin wannan zuwan ba, yakan shafe fiye da shekaru uku kamar an yi masa baki bai zo ya duba su ba sai dai waya, yau kuwa ga shi albarkan wannan auren shekara Waya da watanni biyu da auren har sun soma kawo musu ziyara, ai abun farin ciki ne wannan,
Suna nan zaune sai ga Yaya Yunus Win ya dawo ina biye dashi a baya,
Da sauri na du™a har ™asa na soma gaishe su cikin girmamawa cike da kunyar da ke tattare da Ni

Suka amsa min a tare cike da farin ciki wanda ban taSa zaton hakan ba, domin a fargaban abun da zai biyo baya nake kasancewar abun da ya faru baya, amma sai na ga ba haka ba; domin kowannen su ya ja Ni a jiki sai tarin farin ciki da yake a fuskokinsu musamman in ka kalli na Baffa da na Baban sasa, sai tambayoyi suke min cike da jin daWi suna tambayana yadda nake da kuma irin zaman da nake yi a can?
Dole na bude baki na amsa musu cike da kunya ina ™ara du™ar da kaina

Baban Sasa da ke murmushi har lokacin yace, "ai haka ake so, Allah ya ™ara zaunar da ku lafiya gaba Wayan ku, yayi muku albarka, hakika na ji dadin ganin ku a wannan yanayin ba kaWan ba, dama burina kenan kuma ga shi Allah ya cika min, Allah ya albarkaci auren nan naku wata rana in ga zuri'a a tsakaninku..."

Shi sam Yaya Yunus ya dena jiyo zancen Baban Sasan sam, domin tunanin da ke ransa da irin abun da yake shirin aikatawa ya dama masa lissafin sa, amma ba shi da zaSi ne dole hakan zai yi domin a yakice masa yarinyar daga jikinsa salin-alin, idan ba haka ba a yanda ya ga irin tarin farin cikin da iyayensa suke yi ya san baza su taSa raba auren nan ba,
Shiyasa yayi shahaıÿÿÿ‚ƒ„…†‡ˆ‰Š‹Œ‘’“”•–—˜™š›œŸ ¡¢£¤¥¦§¨©ª«¬­®¯°±²³´µ¶·¸¹º»¼½¾¿ÀÁÂÃÄÅÆÇÈÉÊËÌÍÎÏĞÑÒÓÔÕÖ×ØÙÚÛÜİŞßàáâãäåæçèéêëìíîïğñòóôõö÷øùúûüışÿda ya soma bayyana ainihin abun da ya kawo sa gidan, yayinda ya sauya murya da yanayinsa domin su yarda da abun da zai ambata musu

Babu zato babu tsammani kalaman nasa suka soma ratsa kunnuwan su, wanda gaba Waya nan take annurin fuskokinsu ya Wauke gaba Waya, rikici da tashin hankali ya soma bayyana a kan fuskarsu,
Da sauri Baffa ya dakatar dashi da faWin, "kar ka raina mana hankali mana Yunusa, ya za ka ce tayi ciki kuma cikin ba naka bane; to na waye?"

Cikin tarin damuwa yace, "wlh Baffa cikin nan ba nawa bane, nima ban san ya aka yi Madina ta je tayi cikin nan a waje ba, kwatsam rana Waya muka tabbatar wanda Likita ne ya gwada ta da kansa."

Tsawa Baban Sasa ya daka mishi yana cewa, "kai ba ma son iskanci kaji ko? Taya ya zaka ce cikin ba naka bane bayan da hannunmu muka kaita gidan ka a matsayin Matarka; idan tayi ciki tana Matar aure ai dole kai ne uban cikin, idan ba kai bane uban waye?"

"Shine ai Baba nake son in Fahimtar da ku, Ni ban taSa sanin ta a Mace ba wlh, hasalima Ni ina tausaya mata ne a matsayin yarinya ™arama shiyasa kawai nayi ™o™arin ta zauna a wurina Ni da Matata muka Wauke ta tamkar ´armu, amma ashe tana fita tana bin Maza bamu sani ba, kawai sai ga ciki a jikinta Ni kuma na tabbatar ba nawa bane, cikin jikinta ba nawa bane Baba wlh zan iya rantse wa, don Ni gaskiya bazan iya zama da ita ba shiyasa na dawo da ita ku tuhume ta ga ta nan, kuma na sake ta saki biyu na ha™ura da auren ta".
[2/24, 12:05 AM] OumŠahira: =ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ
   *RAYUWAR MADINA* =اÜ
=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
_(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>Øİİ*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* <Øß

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR READERS')```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

          *P.W.A
'ş*






     *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ´an uwana Mata waWanda suka fuskanci u™uban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ™arshen wahalar rayuwa._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 270
2gb. 500
3gb. 800
4gb. 1100
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.
















______________ *EPISODE 32*
_____Ni har ga Allah ban san wanne irin sharri ne Yaya Yunus ya danganta Ni dashi ba, tabbas na taSa jin makamancin hakan a lokacin da Alh. Badamasi ya sake Ni ina cikin ciwo, na taSa jin makamancin wannan kalmar wajen Ummana, amma sam ban fahimta ba balle in san girman zunubin bin Mazan da ya danganta Ni dashi, abun da na sani kawai furucin sakin da yayi min shine ya soma kaikawo a cikin raina wanda ya saka Ni nayi tsam da raina na gaza gane a cikin farin ciki nake ko akasin sa, farin ciki zan yi ko kuka? Domin bazan ce ina mai ba™in ciki da jin furucin sakin ba,
Sai dai kuma kalaman da Baban Sasa yake min a yanzu shi ya sake dawowa dani cikin tunanina wanda na kasa amsa tambayoyin da yake jefo min, har sai da Baffa ya kira suna na cike da tashin hankali yake cewa, "Madina, baza ki yi magana ba? Abun da Yayanki ya faWa gaskiya ne ko ™arya? Wannan cikin na waye a jikinki?"
Shiru nayi na gaza cewa komai ina mai jin tsoron ™aryata Yaya Yunus sabida ban san dalilin sa na cewan hakan ba, kamar yanda ya faWa min cikin ba nasa bane dole in yarda da hakan tunda Ni na zaSa ya bar min abuna, bazan yarda ya zubar min ba, sam ban yi tunanin idan na amsa cewan ba cikin sa bane dole a tuhume Ni da sanin na waye, ™arshe ™aryan da yayi min zasu yarda da gasken ne, Ni kuma sam ban san illan hakan ba, ban san cewa zai zame min musiba da illata rayuwata ba, don koda Baban Sasa ya daka min tsawa sabida jin nayi shiru na kasa basu amsa, cikin kausashshiyar murya yake ™ara tambayana, "da gaske cikin jikina ba nashi bane kamar yanda ya faWa?"
A lokacin na gama ruWewa da tsawan da yayi min, bakina na rawa na amsa musu da cewan, "eh."
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un salati suka saka gaba Wayansu zuciyoyin su na ™una da tafasa, sam sun kasa yarda da maganar musamman Baffa, don har sake ce min yayi, "Madina, kar ki ji tsoro ki faWa mana cikin jikin ki na wane ne? Kin tabbatar ba cikin Yunusa bane? To cikin waye?"
Na kasa cewa komai tunda ban san mai zan ce ba, sai ma du™ar da kaina da na sake yi kamar wata muna-fuka

Baba Haruna dayake duk ya fi su zafi yace, "shegiya Wago kai ki kalle mu kamar wata muna-fuka, don ubanki waye yayi miki cikin idan ba shi bane? Taya ya kike fita da auren ki kika je wani yayi miki ciki? Yau idan ba ki faWa mana wanda yayi miki cikin nan ba sai mun kassara ki mun kashe banza, baza ki yi magana ba?"
Ya mi™e da nufin duka na don har ya soma nannaWo igiyar rediyon Baban Sasa da ke can wurin socket,
Amma sai Baban Sasa ya dakatar da shi yana cewa, "ai ba zaka taSa ta ba Haruna zauna kawai, idan hankalin mu zai Wauki maganar nan taya ya shi Yunusan yayi saken da har wannan ta'asan ta faru? Ba amana muka baka ba? Taya ya ka barta ta fita a gidanka da hankalinka ta je ta jawo mana abun kunya? Kai ne mutumin banza wanda muka dan™a maka amanar ´armu amma ka ci amanar mu, dayake baka Wauke mu da muhimmanci ba abun da muka yi maka ka nuna mana bamu isa da kai ba Yunusa, sai da ka nuna mana iyakanmu yau ka janyo mana abun kunyar da baza mu iya Wauka ba."
A yanda yake furucin cikin tsananin Sacin rai da fushi, shiyasa Yaya Yunusan yayi saurin cewa, "wlh Baba ban sani ba, Ni ban san tana fita ba, Ni kaina ban san wanda ya aikata mata hakan ba, ba laifina bane..."

"Rufe mana baki mutumin banza shashasha wawa kawai, ai duk laifinka ne, kai kaja ka watsa mana ™asa a ido ka nuna bamu isa ba, ta dalilinka komai ya faru, kuma har ka zo gabanmu ka sake ta don baka da mutunci, da kai da ita duk sai na ci Ubanku domin bazan Wauki wannan abun kunyar ba, baza a Sata mana suna ba."
Sai ya dube Ni wanda Ni tsaban tashin hankali kuka nake yi a lokacin na ™ara takure wa jikina sai rawa yake yi kamar mazari, tsawa ya daka min yace, "don ubanki Maza nawa kike bi; su waye suka yi miki wannan aika-aikan? Tarbiyyar da muka ba ki kenan? Abun da za ki saka mana dashi kenan Madina? Abun da kika koya kenan kika jawo mana abun kunya har da cikin shege Madina? Ki faWa mana waye yayi miki cikin nan don babu yanda za a yi mu bari sai mun Wauki mataki?"

Kuka na saka jikina na rawa hankalina ya soma tashi sabida fushin da na ga Baban Sasa ya nuna, sai a yanzu na soma fahimtar abun da suke faWi; wanda ya ™ara ruWani lokaci Waya sabida rikicewa da tsoron su nace, "wlh Ni ban bi kowa yayi min ciki ba, Ni ban bi kowa ba..."
Hannu Baba Haruna yakai min ya kwashe Ni da marin da yasa na tsandara ihu tsaban azaban da ya huro min, yana cewa, "tambayar mai zamu yi mata bayan ga shi ta amsa da kanta? Shi taya ya Yunusan zai yi mata sharri tunda maganar ba daga bakin sa muka taSa ji ba? Yaya ko ka manta ne haka Alh. Badamasi ya taSa ce mana; amma bamu kama ba sai ga shi Yunusan ya ™ara faWa mana makamancin hakan; ga shi har da sheda tunda ga ciki a jikinta ya bayyana, ai kawai ta rigada ta tona mana asiri ta wula™anta mu; ta ja mana abun kunyar da bai taSa faruwa a gidan nan ba."

Nan shima Baba Mamuda ya amsa zancen yana cewa, "yanzu mu Madina zata ja mana abun kunyar da ya fi ™arfin mu? Yarinya ™an™anuwa wacce bamu taSa tunanin zata aikata mana hakan ba; sai ga shi ta je ta kwaso mana abun da ya fi ™arfinmu, to wlh ba nan gidan ba, duk yanda za a yi sai dai ta koma wurin uban cikin yasan yanda zai yi da ita?"

Haka suka dinga faWa wanda ya jawo hankulan mutanen gidan har suka soma sanin abun da ke faruwa,
Ni kuwa na rakuSe a gefen Baffa wanda ya kare Ni ya hana a taSa Ni sabida dukan da Baba Haruna yake ta son yayi min a dole sai na faWa wanda yayi min cikin, a cewarsa, "tunda bin Maza nake yi gwara suyi min dukan Kawo wu™a watakila in sun kashe Ni zasu fi samun kwanciyar hankali, da irin wannan abun kunyar da na jawo musu gwara su kashe Ni su huta."
Hankalin mutanen gidan ya soma tashi wanda tuni sun soma fahimtar abun da ke faruwa, kowa salati yake yi da tunanin girman zancen da ya hautsina musu kwanya,
Yaya Haula kuwa tsaban kiWima ta kasa ma gane abun da ke faruwa, ta rasa yadda zata yi ta saka abun a mizanin hankali don ta yarda da zancen da ke fitowa daga bakunan mutane, domin ta yarda cewan bazan taSa aikata wa ba dole ba Madina ™anawarta da ta sani bane, taya ya za a ce Madina yarinyar da bata san komai ba a ce tayi cikin shege, sai kawai ta saka kuka zuciyarta kamar zata fashe don ba™in cikin kalaman da ke ™ara hauhawa na mutanen gidan, da yanda wasu suka yarda da zancen tunda babu wanda zai ™aryata ga Yaya Yunusan da kansa ya faWa haka, ada dai basu yarda da ™aryan ba a lokacin da Alh. Badamasi yayi min, amma yanzu zancen ya ratsa musu zuciya wanda sun tabbatar cewan Yaya Yunus bazai yi min ™arya ba, tunda ga shi an ce na amsa da kaina kuma na ™i faWan wanda yayi min

Baban Sasa da kansa yace, "bazan zauna a gidan ba tunda bazan haifa musu abun kunya a gida ba, gwara in koma gaban Mahaifiyata tunda haka na zaSa, su sun yi iya ™o™arin su amma da abun da zan saka musu kenan, babu duka babu zagi amma gwara in bar gidan don hankalinsu ya kwanta, idan suna kallona komai zasu iya min."
Da kansa ya saka Yaya Shamsu da Yaya Manniru, yace, "su Wauke Ni yanzu a daren nan su kaini wajen Ummana."

Haka suka saka Ni a gaba ina ji ina gani ina kuka muka bar gidan, suka tasa Ni har zuwa gidan Ummana, a lokacin dare yayi don har an yi sallan isha'i sannan muka isa gidan

Hankalin Umma idan yayi dubu to ya tashi a wannan lokacin, domin tun kafin zuwan mu yaya Haula ta kirata ta sanar mata da abun da ke faruwa, ba™in ciki ma ya hana ta furta komai sabida takaici da tsantsan nadamar auren da tayi a ™auyen nan, yau ta ™ara tabbatar da mutanen nan jahilai ne basu san abun da suke yi ba, kamar Madina a ce tayi cikin shege bayan da aurenta don kawai tana auren Wansu shiyasa zasu yarda da maganarsa, ta tabbata sharri yayi mata babu yanda za a yi Madinanta ta bi wani Mutum bayan Mijinta, me ta sani a rayuwar da zata aikata wannan babban laifin da zasu danganta ta dashi? ta kasa jure wa dole ta fashe da kukan takaici sabida abun yayi yawa,
"Lallai mutanen nan basu da imani kuma baza su taSa sauya wa ba, Allah zai saka mata sabida wula™anta mata rayuwa, wlh Ni kaina bazan taSa yafe musu ba har abada, da wanne zamu ji Ni Asiya na shiga uku!"
Kuka sosai Umma take yi kamar ranta zai fita don tsaban ba™in ciki

Shi kansa Baba ya girgiza da jin maganar duk da ba ´arsa bane na cikinsa, amma abun yayi masa ciwo yace, "Asiya wannan abun Allah ne kaWai zai saka ma Madina, ™addaranta ne a haka amma Ni kaina nayi imanin yarinyar nan baza ta taSa aikata wannan mummunar aika-aikan ba, kuma da Mijinta don su jahilai ne su ce cikin shege? To yaushe tayi wayon da zata yi wannan ta'asan a inda bata san ma mutanen wurin ba? Ki dena wannan kukan bai da wani amfani, tunda sun ce zasu dawo da ita Ni bazan hana ta zama a nan ba, insha Allahu zan taya ki ri™e ta Allah yasa hakan shi ya fi alkhairi."

Lokacin da muka iso gidan; Umma rungume ni tayi tana kuka ina kuka, "sharrin da wannan bawa zai yi miki kenan Madina? Ina kika ga wayon da za ki iya bin Maza a waje har ki samo cikin shege? Wlh su da Allah sai Allah ya saka mana, insha Allahu kuma kin dawo wurina kenan har abada baza ki taSa koma wa wurin su ba, ke dasu har abada su je su da Allah har shi Yunusan, in yayi da kyau shi da Allah idan ma akasin sa ne Allah zai saka miki."
Ni dai tunda na lafe a jikinta kuka kawai nake yi kamar raina zai fita, na rasa inda ke min daWi sabida ba™in ciki da tunanin irin wannan mummunar ™addaran da ke cikin rayuwata

˜arshe a wani irin yanayi muka kwana a gidan nan babu wanda zuciyarsa yake masa daWi,
Ni kuwa har wani zazzafan zazzaSi ne ya rufe Ni sabida halin da nake ciki, ga dai shi idanuna sun soye babu wani hawayen da ke fita a wannan lokacin amma kuma halin damuwa da zafin zuciyar da nake ciki jikina gaba Waya ya ™i daWi, duk da irin ban baki da ha™urin da Umma take bani, wanda har Baba yayi iyakan yin sa suna ta kwantar min da hankali amma kawai jin su nake yi ba na iya cewa komai sai kallo da ido, yanda jikina yayi mugun zafi dole Baba yace, "gwara a kaini asibiti a duba Ni Ko don halin da nake ciki."
Dalilin da yasa dole Umma tayi min wanka ta saka Ni a gaba na canza kaya sannan muka shirya muka wuce asibitin tare da ita,
Su dama su Hassana tun safe suka tafi makarantar su;
Sai da muka je asibitin da ke nan ™ofan doka ABU hospital; har mun samu ganin likita sannan Umma ta kira Hajiya Ummee ta sanar mata halin da take ciki, a lokacin hawaye take yi sabida damuwa da halin da Likitan ya sanar mata ina ciki

Ba ™aramin girgiza itama Hajiya Ummee tayi da jin zancen ba, salati kawai take yi tana ™ara maimaita kalman sakin da kuma maganar cikin, sai kuma tace, "kinga kuna ina ne yanzu? Sai in zo yanzu in duba ku? Ki yi min kwatance Asiya ina nan zuwa yanzu."

Nan Umma ta sanar mata da Asibitin da suke, sannan ta kashe wayan tana mai mayar da hankali a kaina cike da tsananin tausayina, ta san wannan shi ne ™alubale na, babu yanda suka iya da ™addara, amma ba ™aramin tausayina ke ™ara ninkuwa a zuciyarta ba, musamman abubuwan da doctor ya sanar mata dole a kiyaye a kaina, tabbas a ™an™anuwar shekaruna abubuwan sun yi min yawa dole zuciyata baza ta Wauka ba, tana fatan a ce Allah ya tayar da kafaWuna komai ya wuce,
Hannu tasa tana shafa fuskata da tayi rama ta ™ara firit kamar na mage, a hankali ta furta, "Allah zai ba ki lafiya Madina, Allah ya tashi kafaWunki, wata rana sai labari insha Allahu, ba yanda za a yi mu canza wannan ™addaran naki domin bawa bai isa ya tsallake mata ba in har ta zo mishi, haka Allah ya tsara mana dole muyi ha™uri ko don mu cinye jarabawar nan."
Shiru tayi daga nan sabida kukan da ya taho mata, sai ta sanya hannu a bakinta hawaye na ci gaba da kwaranya a fuskarta,
Daga nan kuma ta Wauki wayan nata ta koma kiran Baba don ta sanar mishi halin da ake ciki.
***** ***** ***** ***** *****

__________A wannan halin abubuwan da Boka ya faWa ma Alh. Badamasi sun soma afkuwa; batare da shi kansa ya soma ankare wa ba, kasancewar tun tafiyarsa komai na har™alla ya soma bun™asar mishi, tun zamanshi a Abuja tunda dama sana'ar sa kasuwanci ne; majority ya fi har™alla a can, zuwansa da neman sa'an da yayi a wurin Boka ha™i™a ya ga albarkan abun a ™an™anin lokaci, wanda hakan ne yasa bayan ya kama hayan gida sai yayi tunanin zuwa Wauko Iyalansa,
To bayan nan komai ya soma canza wa

Please Login or Register in order to submit comment