Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har wani lokacin ma Falak faWa take mata,
Amma da™yar Madina ta iya cire kunya ta sanar mata tana kuka; saboda idan ta ci gaba da barin abin a zuciyarta mutuwa zata yi, tana son ta fitar da shi ko don ta samu salama,
Falak ta tausaya mata matu™a don bata taSa tunanin wannan abun ke azabtar da ita ba, ita kanta sai tayi mamakin wai dama akwai ire-iren su Madina masu rashin jindaWin wannan abun?
To ko dai akwai laifin Mijin ne ko kuma ita Madinan da har ake samun wannan matsalar? But duba da yanda ta sanar mata, "duk sanda suka kasance tare sai jini ya fita a jikinta ga azaba da take ji."
Cikin tausaya mata tace mata, "ai bai kamata ta zauna batare da ta nemi magani ba, su maza baza su tausaya mata ta wannan fannin ba, irin haka ma sai ta saka a yi mata kishiya tana zaune lafiyarta."
Haushin maganar yasa Madina ta banka mata harara tare da cewa, "to ina ruwana da kishiyar da zai yi min? Cewa nayi ina sonshi? Wlh da zai sake ni a yau ya auro Mata huWu da na fi kowa murna."
Falak sai ta ™yal™yale da dariya sabida ganin yanda Madinan ta harzu™o tayi maganar, sai tace, "Allah ya ba ki hakuri, amma duk da haka ai Mata da Miji sai Allah Madina, ba ga shi kuna tare ba har yanzu tsawon wata huWu? Kema kin san Ansar kyakykyawar saurayi ne wanda kowacce Mace zata yi fatan ta samu kamar..."

Katse ta Madina tayi cike da takaici tana cewa, "ba na son wulakanci, ba na faWa miki don ki yi min wannan sharhin bane, na faWa miki ne domin samun sau™i a cikin zuciyata kuma don kin matsa min."
Dafa ta Falak tayi tace, "I'm so sorry ™awata, but duk da haka matsalar ki dole ne ki je ki ga likita, ta yiwu ma infection ne tunda an ce ba abun da ba ya saka wa."
Shiru Madina tayi sabida itama ta yarda maybe shi ne, amma ai tayi magani kala-kala a baya ko haka yake da naci?
Sai ta dubi Falak cike da damuwa tace, "kin san babu irin maganin da ban yi ba a kan cutan nan, but ya ci ace na rabu dashi, kawai dai ni ban yi sa'a bane, duk Mazan da suke kasancewa dani suna azabtar dani ne a kan hakan, ni ban san me ake ji ba a wannan tarayyan, ba na son wannan abun Falak, ji nake yi tamkar zan kashe kaina idan na tuna dole zan rayu da irin wannan abun ne, shiyasa tun farko na tsani in sake aure Falak, amma su Umma sun kasa gane wa, ni kuma haka rayuwata zata kasance cikin u™uba Falak? Wlh na gaji kowa na tsane shi a duniyar nan ban san mene ne amfanina ba, Allah ka Wauki raina ko na huta."
Yanda take wani irin kuka mai fitar hayyaci lokaci guda, sai da Falak ta rufe mata baki ita kanta kukan tausaya mata take yi

"Don Allah ki dena kukan nan haka Madina, ki yi hakuri ki yi hakuri, wlh ko a Film ban taSa haWuwa da wata wacce ta sha wahala kamar ki ba, ki yi hakuri dan Allah domin ki cinye wannan jarabawar, kar ki butulce wa Allah, ki yi hakuri insha Allah akwai maganin damuwarki a duniya, wata rana za ki ji dadi ™awata."


Cikin kuka tace, "sai yaushe Falak? Sai yaushe wannan ranan zata zo? Kullum haka kuke cewa. Umma tana faWa min hakan a koyaushe, itama Yaya Haula tana faWa min, sannan kema ga shi kina maimaita min; kuma hakan ta ™i faruwa, wannan ranan ta ™i zuwa har yanzu, kullum ni da sabuwar ™addaran da take zuwa min, babu hutu a rayuwata? Ko dai na yi wa Allah laifi ne yake hukunta Ni da..."
Rufe mata baki Falak tayi, sai ta rungume ta suna kukan a tare sun kasa tsagaita wa, Allah yasa a wurin da suka zauna babu mutane kusa dasu, amma jefi-jefi sukan wuce,
Wannan yasa Falak ta Wago kanta tana faman rarrashinta tare da furta, "ki yi shiru haka nan don Allah kar mutane su zo su ganmu a haka, ki yi hakuri, ki bari yau idan na koma gida zan sanar da Ammeena halin da kike ciki, na tabbata zata taimaka miki tunda itama Likita ne a kan Mata, idan ma akwai cutar da ke damunki zata bincika, zuwa gobe sai mu je asibitin mu same ta, kinji ki yi shiru haka nan don Allah."
Da™yar ta iya rarrashinta amma hawaye sun kasa tsayuwa a idanunta, sai suka yi shiru dukka a wurin duk surutun Falak ta kasa ™ara kowacce kalma,
Daga karshe sun kasa koma wa class bare su ™arisa lectures Win su, sai ta raka Madina shago ta siya ruwa ta sha maganinta sabida yadda take ta ™wannafi tana numfashi sama-sama alamun ciwon zuciyarta ya motsa, jikinta har ya Wauki zafi,
Karshe Falak ita ta mayar da ita gida tunda ita tana da Mota, bata jira a kira Direban Madina ba.

Dayake Ansar tun jiya yayi tafiya zuwa Baushi kan wani Shari'a, kuma bazai dawo ba sai jibi, kwana uku zai yi,
Madina ta fi kowa murna, don a daren jiya har barci mai daWi tayi har da munshari,
Shiyasa yau ma da ta koma gida sakamakon yanayin da take ciki sai ta kwanta a sashinta tayi barcinta ishashshe, da ta farka kuma sai ta ji dad'i babu abun da ke mata ciwo,
Kasancewar magriba tayi sai ta tsaya yin Sallah before ta wuce sashin su Hajiya,
Khalifa ma na tare da ita, Waya daga cikin ´ar aiki ta rako shi zuwa part Win tunda ya ji shiru bata zo ba,
Sai hayaniya yake mata da guje-guje shi kaWai, wannan ne yasa ta haWa shi da wayanta tace, "ya buga Game."
Ita kuma ta shiga wanka ta Wauro alwala a lokacin,
Tana fitowa ya shigo Wakin a guje da wayan a hannu yana ihun kiran sunanta,
Ta amsa shi tana cewa, "wai mene ne haka Khalifa? Lafiya?"

"Mama, Baba ne yake kira a wayanki, shine yace in kawo miki."
Da mamaki take bin wayan da kallo, sai dai bata ce komai ba ta mi™a hannu domin ya bata wayan, duba wayan tayi ta ga number ne kaWai, sam bata yi tunanin Ansar bane duk da baba yake ce mishi, but sai ta kara wayan a kunne tana jiran jin muryan waye,
Babu zato ta ji saukar muryansa yana kiran sunanta, da sauri ta Wago wayan tana sake duban numban, mamaki kwance a kan face Win ta, but bata tsaya dogon tunani ba tayi saurin kashe wayan, tana shirin kashe wayan gaba Waya sai kiran ya sake shigowa, sai tayi reject tana kashe wa gaba Waya fuskarta a turSune har da jan dogon tsaki

Khalifa da ke kallonta yace, "Mama ba ki Wauki wayan ba, Baba ne yace in kawo miki ku gaisa."
Wani kallo ta watsa mishi sai ka ce shi ne Ansar Win, ta harare shi da faWin, "oya shiga bayi ka Waura alwala muyi sallah an kira, ban son kuma ka dame ni da surutu."
Bai yi mata musu ba ya wuce cikin toilet Win yana Wauro alwala,
Ko kafin ya fito ta nemi riga ta saka; sai ta zura hijab sannan suka gabatar da sallan

A daren ranan kwata-kwata Madina bata sake kunna wayanta ba, duk da a zuciyarta tana cike da mamakin yanda aka yi Ansar ya samu numbanta, ta san bazai wuce su Hajiya ya tambaya ba, amma sam baza ta iya amsa wayansa ba, da ya san yanda take ji a kansa da bai shishshige mata ba, ko uban me zai gaya mata oho? Ita kanta abun ma mamaki yake bata a yanda ya sauya mata cikin ™an™anin lokaci haka, duk wulakancin da yayi mata a baya da irin zagin da yake mata a matsayin ta na ´ar ™auye, wacce aka haife ta a ™auye, sai yanzu ta tabbatar da maza basu da kunya ko kaWan, duk abubuwan da yayi mata yanzu ya manta sabida son zuciya irin nasa, idan ta tuna hakan har hawaye take yi sabida takaici da kuma rasa hanyar da zata yi ta rama, baza ta taSa yafe mishi ba domin baza ta taSa ™aunarsa ba, already ya rigada ya yi wa kansa ba™in fenti na har abada, kowa ma ta tsane shi in dai namiji ne, mutum Waya ne take mishi uzuri, koda ya dawo duniya ya yi mata abun da suka yi mata baza ta taSa tsanar shi ba, shi ne na daban a gare ta, ya nuna mata tausayi da soyayya wanda bata taSa ganin irin sa ba, a kansa ne kawai ta san shaukin so har takan iya dariya ba™in cikinta su gushe baki Waya, amma ya tafi kamar yanda ta san farin cikin ta bazai taSa dawowa ba, ta yi wa kanta al™awari zata ci gaba da rayuwa da Ansar a matsayin Mijinta ba don tana sonshi ba, sai don kar ta ™ara faWawa hannun wani namijin da bata san wanne hali zata shiga ba,
Shi yanzu ya sauya ta ga canji mai yawa a tattare dashi, amma baza ta taSa ™aunarsa ba har abada, domin har yanzu tana ganin kamar yaudara ne, mutumin da ya ™i ka a baya idan ya dawo yace yana sonka ku zauna lafiya, tana ga kamar akwai wata manufa a tattare dashi, duk da har yanzu bai taSa furta mata yana sonta ba, amma duk wani soyYyya da kula wa yana bata, wanda ita kanta kunyar kasancewar su tare take ji don ta kasa saba wa da maganganun da yake mata, but da ta fahimci haka shi rayuwarsa yake ya furta duk abun da ke zuciyarsa, haka nan take hakuri tunda bata da yadda zata yi.****

Washe gari bayan sun je school, daga can suka wuce asibitin su Falak, wato Family hospital Win su, tunda Falak tayi magana da Ammeenta, tace mata, "su zo su same ta da ™arfe 11."
After sun je school sun yi lecture Waya sannan suka wuce a motan Falak,
Lallai Madina ta ga abun mamaki sabida girman asibitin da suka je; ga kyau ga girma gunun sha'awa,
Ashe ganinsa a fili ya fi labarin da Falak take bata,
Lallai ta yarda cewa babban Family ne dasu duk da bata taSa zuwa gidansu ba,
Amma yanda Falak Win ta gabatar da ita da yawan mutanen da ke cikin hospital Win; ta yarda cewa ´ar dangi ne, tunda duk yawancin su daga tace mata Yayyinta ne sai wadanda suke matsayin Iyayenta, ga su duk suna kama masha Allah kyawawa dasu, ga aji da gayu uwa uba kuWi da ya zauna musu,
Sai da Falak ta gama nunnuna mata yawancin Familyn ta da suke duty a ranan; sannan kai tsaye suka wuce office Win Ammeen su,
Lokacin da suka isa ba™in ™ofan sai ta nuna mata wani office da ke kusa da na Ammeen tace mata, "na Daddynsu ne but ba ya zama sosai a kasar ma, sai jefi-jefi yake zuwa irin two months or three."

Duk da a yanzu an sauya tsaruka da yawa; ga gine-gine da aka ™ara, amma kowanne likita da sunansa a bakin ™ofan da zaka shiga, na Daddynta da Madina ta duba an rubuta, "Dr. Uthman Noor Al'amin."
Na Ammeenta kuma an saka sunanta, "Dr. Šahira Al'amin Al'amin."
Sai sauran jerin offices da ke wurin birjik kowa da sunansa

Koda suka shiga ciki office ne mai girman gaske wanda haWuwar sa ya wuce kwatance, infact ma a lokacin Madina bata tsaya kallon office din ba sakamakon haWuwar su da Ammee da ke zaune tayi musu iso; face Win ta Wauke da murmushi wanda ya ™ara wa kyakykyawar fuskarta kyau da kwarjini,
Duk da Madina tana jin labarinta a wajen Falak but ganinta sai ya zame mata abun sha'awa, Matar ta matu™ar burge ta sosai, fara ce sosai duk da ba wata mai jiki bane, Kamilalliyar Mace mai kwarjini da cika ido, ba abun da ya fi jan hankalin Madina ga kallon Matar sai idanunta sabida sun kasance sky green masu daukan hankali, musamman da ta sanya eyeglasses ya ™ara ™awata idanun,
Ko kusa ma Falak bata yi kama da Matar ba sai dai jini da kuma kasancewarta Uwa a gare ta

Sai da Falak ta janyo ta sannan suka je suka zauna, Madinan tayi saurin yin ™asa da kanta tana gaishe ta,
Ammee wacce ke duban Madinan ta amsa ta cikin sakin fuska, tana cewa, "Auta, Wauko muku drinks mana."
Sai ta kira sunan Madinan tana cewa, "ita tayi fushi ma da ita saboda duk wannan tsawon lokacin bata taSa zuwa ta gaishe ta ba, babu wanda bai san labarinta a Familyn su ba sabida Falak tana sanar musu."
Madina kasa magana tayi sabida kwarjinin Matar sai murmushi take yi,
While Falak tana kare ta da faWin, "Oh Ammeena, ai tace zata zo har yanzu bamu samu time bane, but ba ga shi yanzu ta zo ba?"
Murmushi Ammee tayi tana cewa, "ke dai kawai ki ce kare ta za ki yi. Ki saki jikinki Madina nima tamkar uwa nake a wurin ki,
But yanzu ina da patient da zan duba zan je in dawo, sai muyi magana.
Auta ki kula da ita kinji ko?"

"Ok Ammee, sai kin dawo."
Daga nan tashi tayi ta fice ta bar su a office Win,
Sai Falak ta ja hannunta suka koma wurin kujerun huta wa tana shirya mata drinks kala-kala a gabanta tare da ce mata, "sai ta shanye su dukka, since Ammee tace ta kawo mata."
Madina kuwa dariya kawai take yi abun ta sabida ta san halin Falak, wani lokacin takan taSa halayyar su na ´an Auta.
[2/5, 9:21 PM] OumŠahira: =ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ
    *RAYUWAR MADINA* =اÜ
=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
           _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>Øİİ*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* <Øß
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS=تÜ)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A
'ş*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ´an uwana Mata waWanda suka fuskanci u™uban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ™arshen wahalar rayuwa._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 170
1gb 300
2gb. 580
3gb. 880
4gb. 1160
5gb 1460
6gb. 1760
Verlid for 30 days.













______________ *EPISODE 71*
_____Dr. Nafisat Al'amin Al'amin wacce aka fi sani da Dr. Šahira, Mace ce wacce tayi zurfi a sanin matsalolin Mata ciki da waje, kuma tana taimakon Mata da kowanne irin matsalolin su, musamman issues na fyaWe don shi ta fi shiga harkan shi, domin babu irin hanyar da baza tabi ba domin ta ™wato wa ya'ya Mata ha™™in su, yanzu kuwa tayi shura sosai a irin wannan taimakon, Mata da yawa sukan kawo Mata matsalar su domin ta magance musu,
That's why a bayanin farko da ta saka Madina ta bata labarin komai na rayuwarta, sai ta gano matsalar ta, da kuma abun da zai sa ta shiga irin wannan condition, gaskiya ta tausaya mata matu™a, kuma ta ga ™okarin yarinyar, lallai Allah ya jarabbe ta da yawa wanda ba kowa zai iya jure wa ba,
Don haka ta saka a ranta zata taimaka mata domin a yanzu Madina tana bu™atar taimako matu™a, bama ita kaWai ba, majority irin wannan halin da Madina ta shiga, hakan na faruwa ne sakamakon kaciya da ake yi wa Mata a ™auyaku; wanda mutane bila adadin sun Wauke shi a matsayin Al'ada, da addini a rayuwarsu,
Wannan matsalar ta faro ne tun lokacin da aka yi mata kaciya, sai kuma aka yi rashin Sa'a ita ya zo mata da matsala, ga kuma auren da aka yi mata a wannan condition Win; wani mara imani ya ci zalunta a matsayin ta na Wiya Mace wacce take tsananin bukatar taimako, babu kulawa bare samun magani wanda ya haifar mata da matsaloli da dama, irin hakan ne mace zata ri™a rayuwa ne cikin wani yanayi tamkar ba Mace ba, musamman idan tayi aure zata ri™a samun ™alubale wurin kasancewarta da Mijinta, irin hakan na shafan lafiyarta baza ta iya amsa sunan mace ba sabida an illata mata rayuwa, to irin haka ne ya faru da Madina, wato tana fama da Mental and physical health challenges,
ita nata ya zo da matsala wanda ya haifar mata da wannan cutar mai mugun warke wa, duk wani sha'awa nata zai gushe ne,
But Ammee tayi mata bayani dalla-dalla yadda zata gane ta fahimci matsalarta domin tayi ya™i dashi,
Sannan ta Wauki al™awarin dole zata kai ™aran kauyen su domin a Wauki mummunar mataki a kan wannan kaciyar, ba zai yiwu a ci gaba da cutar da Mata ta wannan fannin ba, wanda ba addini ne ya zo dashi ba,
Ko *RAYUWAR MADINA* zai zame musu izna su hankalta, domin a yanda suka tauye mata ha™™inta suka azabtar da ita ta fannoni da dama, ita kanta Ammee tayi tur da wannan halayyar nasu, baza ta taSa bari ba, abun yayi mata ciwo

Madina kuwa har da kukanta da ta ji ™udurin Ammee a kan Waukan matakin da za a yi, ko babu komai yanzu zata ga karshen wannan zaluncin, hakan na nufin ´an uwanta ´an baya baza su sha wahala kamar yanda ta sha ba, lallai zata fi kowa farin cikin da™ile wannan abun, wlh ko ma™iyinta baza ta so ya fuskanci u™uban da ta sha ba, yau ga shi a sanadin ta wasu zasu shiga farin ciki, lallai Allah shi ne abun godiya, sosai tayi farin ciki, farin cikin da ya gusar mata da ™unci da damuwar da ta rayu dasu tsawon lokaci, Allah shi ne abun godiya

Kuma yawan zubar jinin da take yi hakan na faruwa ne sakamakon Cancern bakin virgina da ta kamu dashi, sannan da yawan infection a jikinta wanda ke saka wa wajen ya bushe har a ji mata ciwo,
Dole ne su zauna da Mijinta domin samun maslaha in dai ana son lafiyarta,
Don haka bata bar asibitin ba sai da Ammee ta amshi numban wayan Ansar, Allah yasa ya kira Madinan tana da numban shi bata goge ba, sai ta lalubo ta mi™a wa Ammee, daga nan ta sallame ta tace mata, "gobe zasu fara investigation a kanta, sai sun fara gano matsalolin ta tukunna a Waura ta a kan magani."

Duba da cewan Ammee ta san Iyayen Ansar, tunda ba Soyayyun mutane bane; kasancewar Daddy tsohon gwamna ne kuma sun yi zaman taro dashi sau ba adadi wajen taimakon jama'a a kan harkan fyaWe, Mummy ce dai basu taba haWuwa fuska da fuska ba, sai dai a Tv Mummy takan kalli program na Ammee; a kan abubuwan da take yi na wayar da kan jama'a, ko kuma idan an gayyace ta, While Mummy kuma ba Mace bace mai son shiga jama'a, that's why da yawan mutane a lokacin da Daddy yake mulki basu santa ba, sai dai sunanta da suke ji amma basu taSa ganin Matarshi ya nuna ta ba, babu ruwanta ko taro ba ta shiga, shima kuma Daddy dayake mutum ne mai kishi shiyasa bai takura mata a kan dole sai ta bayyana kanta ba,
Wannan haWuwar da Ammee ta shirya domin gana wa da iyayen Ansar don su san matsalar da ke damun Madina domin a samu mafita, hakan bai zo da wata matsala ba tunda already sun san waye Ammee? Babbar Likita da ake ji da ita wurin taimaka wa Ya'ya Mata, uwa uba Familyn su da yayi shura ya zagaye ko'ina a faWin Nigeria, babu mai girman Familynsu duk faWin Kaduna, zai yi wuya a ce maka *Doctor's Family* batare da ka sansu ba, sabida sun yi abun da baza a taSa manta wa dasu ba, sun kafa tarihi mai girma suna da abun mamaki matu™a,
Familyn da suka kasance duk yawanci Likitoci ne, tun daga kan Kakannin su har izuwa iyaye da ya'ya da jikoki, idan har ka ga wani ya karanci wani abun to dole bayan ya zama Likita ne sannan ya koma ya karanci hobby Win sa, wannan shi ne tsarin dangin su, tabbas sun kafa tarihi wanda baza a taSa manta wa dasu ba, kowa yana jin sha'awar ahalin matu™a


Shima Ansar bayan ya dawo daga tafiyan nashi ya je ya gana da Ammee kamar yanda ta bu™ata, kuma ta sanar mishi da dukkan matsalolin Madina da kuma illan da zai yi mishi shima in har ba a sama mata lafiya ba,
Tayi masa bayani yanda zai fahimta da kuma yanda zai ™aurace mata har a samu a yi mata maganin matsalarta,
Ansar shi kansa ya ji dad'i don yana bu™atar kulawa mai kyau wurin Matarsa, ya san dole dama akwai cutar da ke damunta don yana mamakin halin da take shiga da yawan zubar jinin nata, don haka bai ja da maganar ba ya amince kuma ya bi shawarar Likitan da iyayensa da suka yanke hukuncin Madina zata koma part Win su Mummy ta zauna, har sanda zata samu lafiya,
Duk da Ansar yana ganin zai cutu sosai domin a yanzu babu abun da ya fi bu™ata sama da Madina, a Wan wannan tafiyar da yayi ya gane cewan yana matu™ar ™aunarta wanda bazai iya rayuwa babu ita ba, already ta shiga jikinsa tunaninta ya hana sa sukuni, komai idan zai yi sai ya tuna da ita, har yana jin kamar ya shekara ne bai ganta ba, bai san cewa tana da muhimmanci a rayuwarsa ba sai da suka yi nesa da juna, sai ya zama komai nata shi ne abun tunawarsa ya ji dad'i, wannan ne yasa ya nemi numbanta don ya kira ta but ta kashe mishi waya, shiyasa a ™age ya gama kwana Wayan da zai yi ya dawo, tare da burin bayyana mata matsayin da take dashi a zuciyarsa, tunda shi mutum ne mara Soye-Soye bare jira.
**** ***** ***** ****



       
______ *AFTER TWO YEARS*
Abubuwa da dama sun faru a waWanan gajerun shekarun, ciki kuwa har da samun ci gaban lafiyar Madina, ba dai za a ce ta warke ba, amma abubuwa da dama sun yi sau™i matu™a gaya, sai dai fa illa ce an rigada an yi mata, dama cuta takan shiga lokaci Waya ne, but lafiya a kan Wauki tsawon lokaci ba a same ta ba,
To alhamdulillah za a ce yanzu tunda ba kamar a baya yanda take samun matsaloli da dama ba, kuma suna zaune da Ansar lafiya duk da har yanzu ta kasa sakin jiki dashi Wari bisa Wari ta yafe mishi abubuwan da yayi mata a baya, ba wai don shi kaWai ba, dukkan laifin da Maza suka yi mata shine yasa har yanzu ta ™i yarda da wani Wa namiji, ciki kuwa har da Ansar, a Wari-Wari take dashi, duk da sau da dama takan samu shawarwari daga wurin Falak a kan zamantakewar su, sabida ita ta fi ta wayewa sosai, kuma a yanzu duk ta san sirrikan ta,
Amma dai yanzu Madina Mace ce mai wuyan sha'ani matu™a, shi kansa Ansar yana matukar hakuri da ita a yanzu, sai dai ba yanda zai yi tunda yanzu Allah ya Waura mishi matsananciyar ™aunarta, zai yi wuya ya ga laifinta, domin duk abun da tayi a wurin sa burge shi take yi, komai nata abun so ne, a yanzu ba ya kallonta a matsayin Bagidajiya mara wayau ko sanin abun da ya kamata, a yanzu ko'ina zai iya shiga da Madina ya nuna Matarsa ce, bare yanzu ta amsa sunan Mace don a yanzu take ™ara cika Mace matu™a, tabbas baza ka taSa cewa ita bace sabida yanda rayuwa ta sauya mata, ta mulka ™iba sabida jin dadi da hutu, ta sake haske tayi fresh tamkar ka latsa ta jini ya zuba a jikinta, tabbas a yanzu babu abun da ke damunta tunda tana samun kulawa matu™a wurin Ansar, bare ta gane yana sonta sai abun da ta so take yi, ita kanta takan zauna sau tari tayi wa kanta tambayoyin, "dama wannan ranan zata zo? Ko kuma gaskiyar su Umma ne?"
Ko su idan sukai mata wannan maganar kasa basu amsa take yi sai dai tayi murmushi kawai tana tuna baya, ga dai shi kamar komai ya sauya amma zuciyarta ta ™i sauya wa sabida tana tare da Ansar ne har yanzu amma ta gagara sanya soyayyarsa a ranta ta amshe shi hannu bibbiyu kamaıÿÿÿ‚ƒ„…†‡ˆ‰Š‹Œ‘’“”•–—˜™š›œŸ ¡¢£¤¥¦§¨©ª«¬­®¯°±²³´µ¶·¸¹º»¼½¾¿ÀÁÂÃÄÅÆÇÈÉÊËÌÍÎÏĞÑÒÓÔÕÖ×ØÙÚÛÜİŞßàáâãäåæçèéêëìíîïğñòóôõö÷øùúûüışÿr yanda yake nuna wa a yanzu, gaskiya hakan zai Wauki tsawon lokaci

Yanzu da suka kammala karatun su shine zasu wuce Riyadh, Ansar zai koma can ya ci gaba da kula da Companin Mummy kamar yanda yake yi a baya,
Itama kuma Madina sai ta ci gaba da karatun ta a can, duk da ba ta son nesa da gida amma

Please Login or Register in order to submit comment