Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

min, shiyasa ta duba magani ta bani sannan tace, "ai al'ada ne ya zo mata, kuma da alamu ya zo mata da gardama domin ciwon al'ada ba ya denawa har sai an kai mutum Wakin Mijinshi, Allah yasa ma abun ya zo da sau™i an yi auren, amma ga wannan maganin a ri™a ji™a mata tana sha zata rage jin raWaWin ciwon, Allah ya sawwaka."

"Amin AMin." Duk suka amsa mutanen sasan

Sannan Baffa ya bata kuWin maganin nata bayan ta faWa mishi. Ya dubi Inna Lami yace, "don Allah a kula da ita yanda yakamata, Allah ya bata lafiya, Ni bari in je sai in Yi ma Baban sasa bayanin halin da ake ciki."

A cikin mintuna ashirin har ciwon ya lafa min wani wahalallen barci ya Wauke Ni. Lokacin da na tashi gaba Waya jikina ya ji™e da jini, duk kunya ya kama Ni tunda ina jin abun da aka ce ya same Ni, Ni wato nawa bai zo a cikin sirri ba sai da mutanen gida suka sani, ashe wancan ba jinin Al'ada bane, mai sosan yana gaba

Nafisa na zaune gefe na tana kallona, tun lokacin da ta ga na motsa hankalinta ya dawo gare Ni, sai ta soma min sannu tare da cewa, "Inna tace idan kin tashi akwai ruwan zafi a coolern ta na kichen ki Wiba kiyi wanka, sannu gaskiya na tausaya miki domin naki ya zo da wahala, mu kuwa kinga duk cikin mu babu mai ciwo sai dai mu ga ya zo, kinga Ni na wata uku fa na taSa yi, sai in yi wata biyu ma ban sake yi ba, shiyasa nake murna wlh don Ni na tsani jinin nan inga yana zuba, sai duk hankalina ya tashi, ke ma yanzu kin shiga sahun mu kin zama babba." Ta ™are maganar kuma tana dariyan sha™iyanci; kasancewar ta da son wasa da raha

Ni dai ban ce mata komai ba illa ™o™arin tashi zaune da nayi, sai nayi shiru ina tunanin yanda zan tashi in fita a wannan halin

"Ko in sake miki ruwan wankan ne in kai miki?"

GyaWa mata kai nayi batare da na kalle ta ba, domin wlh kunyan haWa idona da kowa nake ji

Haka ta sake min ta dawo ta faWa min, "ruwan yana bayi in je in yi."

Dole na na tashi ba don ina so ba, sai kare jikina nake yi ina harharWe ™afafu na gaza fita

Nafisa tana ganin yanda jinin yayi min sai ta zaro ido tare da cewa, "Kai! Haka jinin yayi miki? Kinga yanda ya Sata miki jiki kuwa?"

Kamar in nutse a ™asa haka nake ji, har hawaye ne suka soma taruwa a kwarmin idanuna saboda maganar da Nafisa take min

Ita kuwa bata lura ba sai ™ara kururuta yawan jinin take yi tana mamakin yawan shi, "wai kuwa kinga yanda ya Sata miki jiki? Kai ji be ma wurin da kika tashi, ko dai ciwo kika ji?" Ta ™are maganar tana kallo na, sai ta ga yadda nake hawaye kashirSan ™iris nake jira in fashe da kuka, nan kuma hankalinta ya tashi ta soma tambayana abun da ke faruwa? ganin na kasa magana jikina sai rawa yake yi sai ta fita da sauri ta je ta sanar da Innarta

Sai ga su sun dawo da Inna Lami, itama ganin yanda jinin ya zuba ta tausaya min, ta kalle Ni tace, "to mene ne na kukan ko har yanzu kina jin ciwon ne?"

Girgiza mata kaina nayi ina kai dukka hannayena saman fuskata; tare da share ruwan hawayen da ke Wiga min

"To wuce ki je kiyi wankan, Allah ya kyauta gaba, ke kuma Nafisa fito da katifan ki wanke mata."

"To Inna." Nafisan ta amsa mata tana yin abun da tace

Ni kuma tuni na fice daga Wakin na wuce makewayi. Daga bayin ina jin Inna Lami tana sanar da su Inna Asabe halin da nake ciki, sai Allah ya kyauta suke min

Inda har Inna Habibah take cewa, "ai sau™in ta ma an yi mata aure za a huta, ko matsalolin ciwon cikin ma zai ragu."

Wankan nayi tsab sai na Waura Wankwalin kayan nawa a ™uguna; tunda skirt Wina ya Saci, a haka na fito jikina a buWe illa daga ™uguna zuwa cinyana dana rufe, kuma ban damu ba tunda na saba yin hakan kasancewar ganin bani da komai da zan iya Soyewa, kunyata kawai yanda na fara Al'adan nan kowa ya sani, har ba na son haWa idanu da mutanen sasan

Inna Lami ta taimaka min ta nuna min duk yanda zan yi, har ™unzugu ita tayi min da tsumma na saka da wando, gaba Waya a ranan ji na nake yi a wani irin ba™on yanayi, sam na kasa sakin jiki na saboda jin yanda ™asana yake a takure; sakamakon saka tsumma da kuma jinin da nake fitar wa, a haka na wuni sukuku babu wata walwala a tattare da Ni, duk da dama Ni ba Mutum bace mai yawan magana sai idan ina tare da Yaya Haula ko Ummana, da su kaWai nake iya sakin jikina; a wajen mutane kamar farar Kura haka nake; ga miskilancin tsiya

Kwana na biyu ina wannan halin, har Yaya Haula ta zo ta gaishe Ni duk da jikina da sau™i amma jefi-jefi ina fama da ciwon ciki

A rana na uku ne na samu sau™i jinin ya Wauke gaba Waya, shiyasa nayi wanka kamar yanda aka koya mana a islamiyya

A kuma ranan ne sai ga Alh. badamasi ya zo gaishe Ni; kasancewar Baffa ya sanar mishi halin da nake ciki. A falon Baffan ya jira Ni kamar yanda ya saba zuwa

Bai jima ba nima na shigo falon ina sanye da riga da zani na atamfa ba™a da kalan yellow a jiki wanda aka yi kwalliya, duk da kayan sun koWe amma sun amshi farar fatana sun yi min kyau, har Waurin Wankwali Fatimah tayi min ga sabon gyale na Nafisa da na saba saka wa duk idan zan je, nayi kyau fuskata da hoda da tozali sai man baki

Shi kansa alamu ya nuna ya ji daWin gani na a haka, nan da nan ya washe bakinsa yace, "in matso kusa dashi."

Babu musu na isa inda yake amma na kasa zama, sai ya kama hannuna ya zaunar da Ni a saman cinyansa kamar yanda yake min, ya kalle Ni da murmushi bayan ya Wago fuskata yace, "kin yi kyau Matata, yau har da kwalliya kika yi min?"

Ban san sanda nayi murmushi ba har ™asan gemu na yana lotsawa, wanda sosai yake ™ara min kyau idan nayi murmushi ko nayi dariya ya fito, sai na sunkuyar da kaina ina wasa da hannuna

"Na ji daWin ganin ki a haka, dama Baffanki ne yace min kina fama da rashin lafiya shiyasa na zo duba ki." Sai yayi wani murmushi har da sauti yana ™ara cewa, "Ashe Amaryan tawa ta girma ne?".
[2/2, 9:23 AM] OumŠahira: =ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ
*RAYUWAR MADINA* =Ĝ§Ü
=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
_(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>ĜŬŬ*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* <Ĝß

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS=ĜŞÜ)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A
'ŝ*





*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ´an uwana Mata waWanda suka fuskanci u™uban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ™arshen wahalar rayuwa._



















______________ *EPISODE 8*
_____Saurin rufe idanuna nayi sabida kunyar abun da ya faWa

Shi kuma sai yayi dariya, alamun hakan bai dame shi ba, ya sake cewa, "Oh ´ar Amaryata ta girma yanzu, bani da wata matsala tunda ko yanzu aka bar Ni dake za ki iya dani, ko kin fi son nayi ma Baffanki magana ya bani ke mu tare a gidana?"

Saurin girgiza masa kaina nayi bayan dana buWe idanuna, ba wai don na fahimci mai yake nufi ba

Murmushi yayi yace, "har yanzu kina nan ba ki yarda dani ba ko? Na ce ki Wauke Ni kamar Babanki amma kin kasa sakin jikin ki dani, ko kina tunanin zan yi miki wani abu ne idan kika koma gidana?"

Shiru nayi masa ina sake sunkuyar da kaina

Sai ya Waura hannunsa a saman ™irjina yana shafawa, ina jin sanda ya saki numfashi tare da kawo bakinsa kusa da kunne na yace, "to faWa min, kin gama jinin da kike yi ne?"

Ban san sanda na runtse idanuna na ™an™ame shi ba tsaban kunya kamar in nitse

Shima hannu yasa dukka biyun ya kama Ni sosai yana raWa min, "´an Matana kin cika jin kunya wlh, naga ranan da za ki saba dani, shiyasa na ™osa a kawo ki gidana ko don mu ri™a yin wasa ko? Kina son mu ri™a wasa tare?"
Jin nayi shiru ina ta ™ara Soye fuskata a jikinsa, sai yace, "kin cika jin kunyana, ki rage kinji? Ko ba kya son in ri™a siyo miki ´ar tsana a birni ne? Da wannan chocolate Win da na siyo miki?"

"Ina so."

"Yauwa ko ke fa, to Wago kanki ki dena jin kunyana."

Šagowa nayi kamar yanda ya bu™ata. Sai yace, "gobe zan tafi birni, ban manta da al™awarin ki na kaya ba, zan siyo miki in na dawo, ki ri™a min irin wannan kwalliyan kinji zan ji dad'i."

Kaina na gyaWa mishi ina jin farin ciki a raina

Shima sai yayi murmushi yace, "yauwa ´ar gatan Babanta, to yi min addu'ar tsari idan na tafi in samo kuWi masu yawa kinji ko?"

Murmushi nayi na Waura hannuna a saman fuskata, a hankali na furta, "Allah ya ba ka abun da ka je nema."

"Amin Amin Amaryata, na ji daWin addu'ar ki, ina sonki sosai, za ki ji dad'i idan kika zo gidana, komai zan ri™a miki in kina min biyayya." Ya ™are maganar yana ci gaba da shafa Ni

Ba tare da Ni na damu da abun da yake min ba, sabida ko kaWan ban kawo komai a abinda yake min ba, Ni dai ina farin ciki sabida abubuwan da yayi min al™awarin zai siyo min. Sai da ya sallame Ni sannan na tashi na tafi

Yau ma sun yi tunanin zan shigo da wani abun ne, shiyasa Inna Asabe ta kasa ta tsare tana gani na sai ta taho wuri na tana tambayana, "ko ya bani wani abun ne?"

Nace mata, "a'a."

Sai ta ja tsaki ta wuce abun ta tana surutai kamar ta aike Ni

Haka su ma su Nafisa suna ganin na shigo daki suka soma tambaya na,
"Allah yasa dai ya kawo miki wannan abun mai shegen daWin tsiya? Ke kam kin more wlh Madina."

Zama nayi a gefen katifana ina yaye gyalen jikina, tare da furta, "bai bani komai ba yau."

Dukkan su fuskokin su ta nuna rashin jin daWin su,
Amma sai suka share suka ci gaba da hiran su, don dama hiran wata ™awarsu suke yi na cikin anguwa, Hansai,
Dayake jiya Luba ta je gidan su; shine take basu labarin abun da ta gani a gidan, tana tsegunta musu yanda ta ga tana yi da wanda aka yi musu baiko, gidan babu kowa Allah ya faWo da Luba ta biya ta gidan da Innarta ta aike ta, shine fa ta gansu suna iskanci,
Ita kuma yanzu take shafa wa su Nafisa labari,
Har wani rage murya take yi don kar su Inna Lami su ji

Ni kuwa jin abun da take faWa, shiyasa nima na kasa kunne ina sauraro duk da ban gama fahimtar maganar sosai ba, tunda ba dani aka somo ba

Inna Amarya ce ta le™o tana cewa, "wai ku uwar mai kuke yi a Waka baza ku fito ku sha iska ba?
Munafurcin mai kuke yi?"

"Wlh Inna babu komai." A cewar Luba tana watsa hannaye,
Yayinda su ma dukkan su suka basar suna Sashe baki kamar ba abun da suke yi,
Har Binta tana ™arawa da faWin, "Inna Amarya labaran duniya muke yi shiyasa kika ji mu mun nitse ciki."

"Ku dai ku ka sani, ke Madina taso ki Webo min ruwa a rijiya in tace ™ullun nan."
Tayi maganar tana sakin labulen tare da wuce wa

Nima kuma sai na amsa mata ina mike wa tsaye, tare da ajiye gyalen Nafisa a jakar kayanta, na fice da sauri,
Dama hakan ke faruwa dani kodayaushe, ba sa son su ga na huta ko mis™ala-zarratan, Ni kaWai ce baiwa a gidan, kuma dayake ba na ™yuya sannan bani da son jiki, tuni na Wauki bokitin na nufi hanyar rijiya da ke cikin gidan a can wani makewayi ta bayan sasan Baba Iro,
Can na nufa na saka ™atuwar gugan da ke Waure a rijiyan, cikin ™an™anin lokaci na cika farin bokitin, na Wauro shi a kaina na kawo mata

"Yauwa, kinga yanzu sai in tace har in gama in le™a gidan Abashe, tunda na ji an ce Matarsa ba lafiya."

"Wai da gaske ne ashe? Šazu Yusuf yake sanar min ina ce ™arya ne tunda na ji maganar bata shigo cikin gidan ba."
A cewar Inna Habibah da ta fito daga ban-Waki tana ri™e da buta, ta samu wuri ta zauna a saman dutse kusa da kichen

Ita kuma Inna Amarya take bata tabbacin, "da gaske ne wlh, Wazu Baraka ta shigo take faWa min, wai jikin ma ya matsa mata kuwa. Madina Wauki sake min ruwan a wannan Bawon ki ™aro min sahu Waya."

"To." Na amsa mata ina juye wa kamar yanda ta bani umarni, na Wauki bokitin na koma rijiyar, har na je na dawo suna maganar rashin lafiyar ne,
Inda Inna lami ma ta fito daga Waki rike da Wankwali a hannu tana tsulma musu baki, fuskar nan nata ta tasa da alamun daga barci ta tashi,
Tana gani na tace, "zubo min ruwa a buta Madina, nima in yi sallan nan sai mu le™a su.
Ina su Nafisa? Kuna ina; baza ku fito kuyi sallah bane kuna jin har an kira lokaci zai ™ure?"

"Gamu nan Inna."
A cewar Nafisan ita da Fatimah da suka amsa a tare

Su kuma suka ci gaba da hiran su har na kawo ma Inna Lami ruwan, sannan na juya na Wauki butan nima na shiga bayi,
Zu™una wa nayi ina fitsari amma wani irin zafi ne yake tsarga min, hannu na tara a fitsarin nawa na ji zafi kamar an tafasa, abun ya bani mamaki amma ban kawo komai a raina ba, illa tunanin meyasa fitsari na yake zafi yanzu kamar an saka a wuta? Ga kuma wurin yana min zugi har da ™ai™ayi, hannu na sa na dinga sosa wa kamar zan ™wantale fatar jikina, azaban ya ishe Ni hakan yasa na saka hannu biyu ina gurzan jikina sabida azaban ™ai™ayi, kamar zan yi kuka haka na dage ina ta abu Waya,
Har sai da na ji muryan su Nafisa suna maganar, "na bar su a tsaye zasu zaga na ™i fitowa."
Dole nayi tsarki na mayar da wandona na fito daga bayin,
A nan bakin kofan na tsaya zan soma alwalan

Fa'iza tace, "idan kin gama ki bani butan."

Dayake Nafisa da Luba sun samu nasu butan, shiyasa ina fitowa Nafisa ta fara shiga bayin, daga baya Luba ta shiga bayan ta fito

Ni kuma ina gama wa na wuce daki nayi sallan nawa; sannan na fito ina amsa kiran Inna Asabe da take min,
Aiki ta sanya Ni na tsinke ganyen alayyahu wanda zamu yi miyan dare

Da Wai-Waya suke fito wa duk wanda ya idar da sallan,
Kowa ya kama aikin da ke gabansa tunda har biyar tayi,
Su Luba kuwa kai tsaye sashin su suka wuce su da Nafisa, suka koma can suka ci gaba da hiran su,
Babu wanda ya damu dasu a cikin su Inna Lami bare ya sanya su aikin, sai dai Ni Jaka, in da sabo ma na saba wlh,
Ina gama wa aka sanya ni share tsakar gidan,
Haka na Wauki tsintsiya na ™al™ale ko'ina, tun daga Wakunan su har filin sasan, na fice da sharan zuwa haraban tsakar gida, a can na tara ina kwashe wa sai ga su Baffa sun shigo shi da Baba Iro

"Ah! Wa nake gani haka kamar Madina? Shara da Magriba?"

Sannu da zuwa nayi musu ba tare da na amsa maganar nasa ba, illa ma sunkuyar da kai da nayi cikin ladabi

Suka amsa min, inda Baba Iro shi tuni ya wuce sashin sa tunda akwai kaya a hannunsa

Shi kuma Baffa ya tsaya yana min tsiyan yin shara a wannan lokacin, yace, "in ri™a yi da wuri ban da irin wannan lokacin."

Na amsa mishi da, "to."

"To maza ki kwashe ki tashi a wurin."
Ya ™ara furta wa yana yin gaba zuwa nashi sasan

Kafin ma in bar wurin haka Matasan gidan suma sai shigowa suke yi, kowa ya dawo daga aikin sa, duk wanda zai wuce sai nayi mishi sannu da zuwa,
Ina kwashe wa na zuba a kwandon sharan da ke hanyar ™ofan gida

Yaya Shamsu ne ya shigo a lokacin, firjan-jan tamkar wanda aka koro shi duk yayi biWi-biWi da alamu daga gona yake tunda yana rike da fatanya,
Har zai wuce ya ji siririyan muryata ina mishi sannu da zuwa, sai ya dawo da baya yana faWin, "wace ce nan?"

Da sauri na amsa mishi, "Ni ce Madina."

"Yauwa, shiga sashin mu ki ce wa Innar mu idan akwai ruwan zafi a zuba min yanzu, ki Wauko ki kawo min kofar daki na."

Amsa mishi nayi ina wuce wa, sai da na ajiye tsintsiyan hannuna sannan na wuce kai tsaye Sarayin Baffa, a can na haWu da su Nafisa suna alwala,
Shigowar Baffa ne ya kaWa su yace, "su yi alwala suyi sallah ana kira."
Kai tsaye dakin Inna Uwa na wuce, uwar gidan Baffa, har Wakin na shiga, ganin tana sallah shiyasa na fito muka ci karo da Baffa shima yayo alwalan yana sauri zai wuce masallaci, tunda a lokacin an kira,
Yace, "Madina me kike yi a nan ba ki Wauki buta kin yi alwalan ba ke ma?"

"Yaya Shamsu ne ya aiko Ni wurin Inna, shine zan sanar mata."

"To Wauki buta ki yi alwalan kafin ta idar da sallan, nima na shiga na ga tana sallah."
Yana ida maganar ya wuce da saurin sa ya fita sashin yana gyaran murya

Nima sai na wuce nayo alwalan,
A lokacin Inna Uwa ta idar da sallan har ta fito tana tambayana, "me Shamsun yace?"
Shine na faWa mata sa™on sa

"To ai bai gama zafi ba, bari ki jira sai in sake mishi kikai mishi."

"To Inna."
Alwalan na ™arisa, na koma kusa da su Fa'iza da ke tsakar sasan sun baza tabarma suna sallah a wurin, nima na tayar da kabbara, ina idar wa ban jira nayi addu'a ba tunda na ji Inna Uwa tana kwaWa min kira, shiyasa na tashi da sauri na wuce kichen Win su

"Šauka ga shi nan na zuba mishi, kar kuma ya ji shiru."

Šaukar bokitin nayi Wakyar na nufi sashin Samarin gidan, a bakin kofan sa na ajiye masa ina kwaWa sallama, da alamun basu dawo daga masallaci ba shi yasa nima na wuce abuna na koma sashin mu.
***

_____Sai ™arfe tara muka haWu muka ci abincin dare kamar yanda muka saba, kowa ya baje a tsakar gidan ana ta raha da hira,
Dukka Iyalan Baban sasa ne sai mu ´an Matan da muke kwana a sashin,
Masu saurin barci tuni sun soma hamma, wasu har sun kwanta a wurin,
Nima har dani tunda ban da jimirin zaman hira, tun ina jin su Binta sama-sama suna magana da shewa, har dai na ji Wib na dena jiyo su, tuni wani nannauyan barci ya kwashe Ni

Sai can sama-sama na ji ana tashi na in koma daki,
Haka na mi™e na koma dakin mu na kwanta na ci gaba da barcina, sai asuba na farka nayi sallah,
Daga nan kuma ban sake samun damar koma wa ba sai aiki kamar yadda na saba

Haka rayuwar ta ci gaba da tafiya tun ina ™irga kwanakin dawowar Alh. Basamasi har na cire ran ganin sa, tunda ga shi kusan sati biyu babu labarin sa,
Sai da muka yi wata Waya curr sannan ya zo gidan, dama da abun a raina na kayan da yace zai kawo min, shiyasa tunda aka zo kira na yana jira na, shiyasa na dinga murna, a raina ina addu'ar, "Allah yasa har da kayan dad'i ya kawo min."

Ilai kuwa, leda sha™e ya zo dashi na tsaraban da yayi min, bai manta alkwari ba har kayan saka wa sai da ya zo min dasu guda biyar, dogayen ruguna ne ´an kanti dai-dai jikina, guda uku sai riga da skirt guda biyu, dukka sababbi a ledan su, sai takalma guda biyu da gyale guda biyu, sai kuma ledan sweets da chocolates bakitin Waya

A sanda ya nuna min kayan; wani irin dad'i ne ya rufe Ni, tuni na washe baki na bi ina WaWWaga kayan, cikin yarinta irin nawa nake ce mishi, "wannan duk nawa ne wai?"

"Kwarai kuwa Amaryata, wannan duk naki ne, na siyo miki ki min kwalliya da su."

Baki na washe ina kallonsa, cikin farin ciki da Woki nace, "wlh ba a taSa siyo min irin wannan kayan ba, ko na sallana waWannan sun fi kyau."

Dariya yayi cike da nishaWi, yace, "in taso in zauna a kan cinyansa."

Da kaina na Ware saman cinyan nasa, bayan na Wauki sweet Waya na buWe na saka a baki ina jin wani irin daWi na ratsa Ni

Shima kuma nan ya ™an™ame Ni a jikinsa yana labarta min, "in har zan ri™a yin abun da yake so, komai zai siyo min, idan ma sallah ta zo wanda ya fi wannan kyau zai kawo min."

Ai nan na dinga jin daWi, a raina kuwa har Allah - Allah nake yi Yaya Haula ta zo in bata labari ta ga kayan

Dayake shima Alhajin sauri yake yi, yau bai jima ba ya sauke Ni a jikinsa yace min, "zai wuce, amma zan gansa aka-akai yanzu tunda yana gari."

Murmushi nayi masa nace, "na gode Baba."

"Babu komai Amaryata, duk abin da kike so kawai ki ri™a faWa min za ki ga na kawo miki kinji?"
Ya ™are maganar da shafa kaina yana wani irin murmushi mai nuna tsantsan farin cikin sa da jin daWin sakin jikina da nayi, alamun burinsa ya kusa cika nan bada jima wa ba,
Daga nan tafiya yayi Ni kuma na kwashe kayan na wuce,
Har na isa sashin mu babu wanda ya ganni sai da na koma sasan mu

Suna zaune su Inna Habibah a tsakar gidan na shigo da kayan,
Hakan ne yasa duk suka bi Ni da kallo,
Inda Inna amarya take cewa, "wai har ya tafi ne?"

Kai na gyaWa mata tare da cewa, "eh ya wuce."

Inna Asabe tace, "kawo kayan mu gani, yau kuma tsaraban da yawa aka kawo mana kenan?"

Wurin ta na nufa ina mi™a mata ledojin,
Nan fa sai suka hau buWe wa har da su Binta suna cewa, "kai! Wlh Madina ta fi mu more wa, Wan dattijo sai mata hidima yake yi."

"Iyee! Lallai kam, abun na yi ne, kun gani fa har da kayan saka wa ya siyo mata."
A cewar Inna Asabe tana WaWWaga kayan, don ita har da hassada ma yake sanya wa take saka min ido

Lokacin ne Inna Lami ta fito daga kitchen itama ta samu wuri ta zauna a kujeran zu™uno tana cewa, "oh! Shi kuma ko meye na yi mata sutura haka oho? Sai ka ce ya ganta a fatare?"

Inna Habibah tace, "to ban da abun ki Yaya, ai a fataren yake ganin ta, ba kya ganin kayan jikinta ne duk sun koWe kullum a haka take zuwa masa, dole yayi tunanin bata da kayan ne, ai gwara ya siyo mata wlh, yana son ya ganta Was-Was."

Haka suka dinga duba kayan suna surutai, Inna Asabe tuni ta Sarka ledan kayan za™in ta soma rabo sai ka ce nata, sai da ta raba wa kowa a wurin sannan ta mi™o min sauran tana cewa, "to ai dole kowa ya dangwali fa'ida, ba ga shi mun sha ba zamu mayar da yawun mu, suma kayan za a daukar wa Fatimah da Nafisa sai su saka."

Inna Lami tace, "a'a gaskiya ki bar mata abun ta, idan an basu su Fa'izan kuma fa? Sannan ma ya san kayan da ya siya mata in ya ga bata sanya ba zai iya tunanin mun hana ta ne, ki bata kayan ta kawai tunda mun sha wannan ya ishe mu."

Ni dai ina tsaye ina kallonsu bani da bakin cewa wani abu, yanda suka bani haka zan karSa, farin ciki na ma yanda ta bani sauran da Wan auki, zan iya sha har in ajiye wa Yaya Haula da Ihsan,
Tana bani kayan na wuce cikin Wakin mu na zuba a cikin kayana na Soye ko Waya ban sha ba, sai idan Yaya Haula ta zo sannan zan raba in sha nawa

Su Fa'iza ne suka biyo bayana, suka zauna suna tsokanata wai, "sai na faWa musu hiran da muke yi da Alhaji

Please Login or Register in order to submit comment