Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan koke-koken da firgita gaba Waya na Waga musu hankali babu natsuwa a tattare dani kullum cikin damuwa?"
Sosai ya lallaSa Ni yana son sanin me ke damuna,
Amma sam na kasa buWan baki in sanar mishi, domin idan nayi yunkurin faWa sai in ji kamar ana rie min maoshi, sai kawai na fashe da kuka sabida bazan iya musu bayani ba, ina son furta musu yanayin da nake ji amma na gagara.
Kuka sosai nake yi a wannan lokacin da ya matsa min,
Shi kansa hankalin sa ya tashi ya rasa inda sai saka kansa ya ji dad'i, ba aramin tausaya min yake yi ba, matua yana son sanin damuwana domin ba ya son ya ara ganina a irin mugun yanayin nan, a yanzu yana murna da farin cikin haihuwana ne, wanda tuni ya yanke shawarar zai soma jawo Ni a jiki fiye da yanda yake min yana nuna irin kulawa wanda dole zan fahimci meye a ransa, daga arshe kuma ya sanar min ta yanda zai ci nasaran da zan amsa mishi, amma kuma yanzu ga wani abun da ya kunno kai wanda na kasa sanar mishi bare ya taimaka min, wlh a yanda ya ga ina irin wannan kukan ji yake yi tamkar ya zubar min da hawaye don tausayi,
Bai san lokacin da ya sanya hannu ya kamo nawa ba yana cewa, "don Allah ki yi shiru haka nan Madina, na dena tambayar ki tunda ba ki so, please ki dena wannan kukan yana Waga min hankali fiye da tunanin ki, kina son nima in yi kukan ne?"
Sai a lokacin na sassauta da kukan ina shashshea amma na kasa Wago kaina bare in iya kallonsa,
Sai yayi shiru ya tasa Ni a gabansa yana jin sautin muryata wanda ke kara masa damuwa da unci, har ga Allah yana matuar aunata wanda bai taSa jin irin sa a kan kowacce Mace ba, ji yake yi tamkar ya janyo Ni ya rungume Ni ya rarrashe Ni ta yanda zan iya sanar mishi da damuwata, amma ya san hakan bazai taSa yiwuwa ba, hannuna ya dame am yana jin wani irin yanayi mai tattare da shaui gami da tsantsan aunar da yake min, a lokacin ya gaza yin magana har sanda ya ga na dena shashshean na Wago kai mun haWa ido dashi,
Sai ya sakar min murmushin da ya fi kuka ciwo sabida a ransa yana jin kamar ya mayar da dukkan damuwana a kansa,
Ni kuwa tuni na mayar da kaina asa sabida kunyansa, na gaza Wagowa koda yace in Wago in kalle sa, sai na ji yana cewa, "Madina, Ni fa Yayanki ne, ko ba ki yarda cewan Ni yayanki bane mai share miki hawaye a dukkan halin da kika shiga? Ko nima kina kallona a irin mutanen da zasu iya cutar da ke ne?"
Da sauri na girgiza mishi kaina hawaye na ci gaba da zuban min, wlh shi kaWai ne mutumin da nake jin zan iya yarda dashi bayan Ummana da Yaya Haula a cikin rayuwata, domin har cikin raina na yarda dashi wanda na ba shi Matsayin Wan uwana wanda muka fito ciki Waya tare, irin kulawan da ya bani shine yasa na gama sakankance wa dashi, wanda a halin yanzu babu wani SurSushin tsoronsa illa zallan yarda da kuma kunyansa a raina, ina son in faWa masa amma na kasa, domin bazan iya ba, koda ya ara ce min, "Madina don Allah ki rie Ni a matsayin wanda bazai taSa cutar da ke ba a rayuwarki, ki rie Ni a matsayin wani bangon jinginan ki wanda zai kawo miki haske a rayuwa, ki taimaka ki faWa mana dalilin shiganki wannan halin, mun damu da ke, kinga baza mu ji dad'i ba muna ganin ki a wannan halin amma kin kasa sanar mana da abun da ke damun ki, wlh ki faWa min ko nawa zan kashe domin ganin kin samu lafiya, kinji don Allah ki faWa min?"
Bakina na rawa batare da na sake duban sa ba nace, "Ni ban san mai ke damuna ba, ba na jin dad'i ne, zuciyata kamar zata fashe."
Na are maganar ina fashe wa da wani irin kuka mai cin rai,
Hankalinsa sosai ya tashi fiye da da, bai san lokacin da ya kamo kafaWuna ba yana oarin rungume Ni, amma sai yayi saurin dakata wa sabida tuna abun da yake kokarin yi, da sauri ya ciro handkerchief a aljihu ya fara share min hawayen yana cewa, "shiii! Ban son in sake jin wannan kukan naki kinji ko, babu abun da zai same ki sai alkhairi, bari yanzu zamu je a sake gwada ki domin gano me ke damun ki, ki yi shiru haka nan nace, sorry."
Yanda yake lallaSa Ni da sanyin muryansa tuni nayi shiru ina jan numfashi, haka ya Wauke Ni ya mayar dani wani Wakin, shi da kansa yayi min duk gwaje-gwajen da yake hasashen maybe ko zuciyata ce ta samu matsala, sai dai a irin halin da na shiga bai ga wani matsalar da zai iya cewa zuciyar ce da matsala ba, tunda yanzu magungunan da yayi min amfani dasu ya taimaka min sosai a kan matsalar tawa,
Amma hakan nan ya rubuta min wasu don bamu baro asibitin ba sai da ya tabbatar ya kwantar min da hankali sosai,
Ni kuma sabida yanda ya nuna damuwa tsantsa a kaina shine yasa na Soye komai da ke raina na dena kukan da nake yi,
Ko kafin mu koma sai da ya kaini wani babban shago yayi min siyayya mai yawa, Ni kaina a yanzu na soma tsarguwa da irin wannan kulawar nasa, duk da kwata-kwata hasashena bai taSa kaiwa inda tunanin sa yake ba, amma tsoro ne ke Wawainiya dani da irin abubuwan da yake min, sau tari nakan zauna nayi tunani amma rashin kaifin basira ba ya saka wa in gane komai, sai wani tunanin da nake yi kamar yana haka ne da wata manufa, sai dai zuciyata ta kasa yarda akwai cutarwa a tattare dashi, zaman nan da nayi tare dashi na fahimci yana da kirki sosai, a jininsa yake taimakon; tunda tun haWuwar mu yake taimaka min bai taSa gajiya min ba, shiyasa nake ganin girmansa sosai na Wauke shi a matsayin Yayana kamar yadda yake faWa,
Shi da kansa ya sani dole na amshi kayan na wuce dashi gida.***

A ranan da na cika kwana arba'in da daya da haihuwa, wata ranan da ya zama kamar almara da rikitarwa a wurin mu, a ranan Baba Mamuda da Baba Haruna suka zo tafiya dani, in takaice muku sai ya zamana kamar an rufe bakin Umma a kan babban al'amarin da suka zo mata dashi,
Ni kaina koda suka tasa Ni gaba suka ce, "in haWo an kayana kaWan in biyo su su tafi."
Wlh babu musu na soma haWa wa jikina na rawa, domin a yanda nake ji daga asan zuciyata burina kawai in bi su, musamman don maganar da suka zo dashi na cewan, "an mayar da aurena da Alhaji Badamasi."
A lokacin Ni dai na san kaina yayi gingirim gabana yayi wani irin bugawa kamar zuciyata zata yi tsalle ta fito, a lokacin ban san me ke damuna ba amma tabbas na san bani a cikin hayyacina, kawai umarni ne daga wani Sangare da ya zame min tilas in aikata shi, domin samun sassauci daga uuban yanayin da nake ji,
Inda suka yanke shawarar barin yaron a wurin Umma ta kula dashi tunda aure yanzu nayi, bazai yiwu a ce na tafi da yaro inda zan je ba, a cewarsu, "wannan kamar alfarma ne Alh. Badamasi zai yi min, duk da ada ya cutar dani amma yanzu basu ga wani laifin sa ba sabida abubuwan da suka faru a baya, wannan abun kamar Ni ce na jawa kaina tunda ga sakamakon abun da na aikata, shi kansa Wan uwana ya bada shaidar hakan, a yanzu dai da nake da Wa Wan gaba da fatiha ya zame min dole in zauna da Alh. Badamasi, tunda shi ne zai rufa min asiri, bare yanzu ba kamar da bane ya zama babban mutum."
Ita dai Umma bata ce komai ba amma zuciyarta tana ta tafarfasa da bain ciki, ta rasa mai yahau kanta ta kasa yin musu dasu, har suka bar gidan sannan ta soma zubar da hawaye tana jin babu daWi a ranta, tana jin kamar bata kyauta ba, wai me ya hau kanta da har ta yarda ta mia Madina a wajen waWannan mutanen? Ta rasa yadda zata yi wawaran motsin da zata fito da abun da ke cikin ranta, kamar an WaWWaure ta da jijiyar jikinta, sai dai unan yana ranta, shiyasa ta kasa jurewa ta fashe da kuka a wannan lokacin, ga shi babu kowa a gidan a wannan lokacin don Baba yana wurin aikin sa bai dawo ba, su kuma su Hassana suna makarantar islamiyya, Umma jugum tayi tana tunanin abun da zai je ya dawo da tafiya na, gaba Waya ta rasa mai ke mata daWi

A can auye kuwa koda muka isa kusan arfe 6 ne, ashe Alh. Badamasin yana can tare da su Baban Sasa yana jiran a kawo Ni sannan mu wuce, tunda tun safe aka Waura auren kamar yadda ya zo musu da buatar hakan, tare da basu hauri a kan duk abubuwan da yayi musu a baya kamar yadda Boka ya umarce shi, don haka koda ya zo ya basu hakuri babu wanda ya iya mishi musu, duk da a zuciyarsu suna jin ba sa son zancen amma sun gaza umarnin sa kawai suke bi sabida baza su iya aikata komai ba; a sakamakon asirin da aka yi musu wajen Waure musu baki,
Wannan babban al'amari ne mai girma da ya auku da kowa ke mamakin faruwar sa, musamman Mutan gidan waWanda babu daman su tanka su saka baki, su dai nasu idanu ne,
Haka suna ji suna gani aka taho dani gidan aka dama amanata a wurin Alh. Badamasi, yana washe baki da murna da jin daWi ya dunula musu kyautar kuWi wanda ya hargitsa musu lissafi, ya tafi dani a danareren motansa muka wuce Abuja a wannan yammacin, don ya fi son ya kwana a gidan sa domin cika umarnin Bokansa

Abun da ya faru a wannan ranan ya zama babban abun rikitarwa da kowa ya gaza gane kansa da har suka yarda da Alh. Badamasi, sai ya zamana su Baban Sasa sun kasa taSuka komai don a lokacin sai da suka zauna suna tattaunawa a kan amince masa da suka yi a karo na biyu, duk da abun da Madina tayi musu amma bai kamata su ara bada ita a wajen sa ba, suna jin kamar basu kyauta ba,
Su kansu samarin gidan jikinsu yayi sanyi matuka abun ya Waure musu kai da tunanin meyasa kan iyayen nasu suka juye suka kasa tuna baya ne?
Yaya Nasiru kuwa har waya ya Wauka bayan tafiyan su Alh. Badamasin ya kira Yaya Yunus don ya shaida masa, bayan sun gaisa ne yake ce masa, "ai yau aka Waura auren Madina da Alh. Badamasi tsohon Mijinta, shine ya kira ya sanar mishi."

Maganar ta girgiza Yaya Yunus wanda shi kansa bai san meyasa ya ji hankalin sa yayi ololuwar tashi ba, inda cikin sauri da mamaki yake cewa, "ban gane ba Nasir, wacce Madinan kake nufi an yi mata auren?"

"Madina dai wacce ka saka, yau aka Waura mata aure da Mijinta na baya, don har ta haihu yanzu an yi arba'in ma, shine ya zo da bukatar a sake musu auren, mu kanmu a cikin al'ajabin faruwar hakan muke wlh, abun ya Waure mana kai matua..."
Cike da hargitsi Yaya Yunus yake sauraron Nasirun, wanda yake jin zuciyarsa na bugawa 
kamar zai faso irjinsa, sam ba ya jin daWin zantukan nasa wanda bai san mai ya hau kansa ba a lokacin, zuciyarsa bayan bugawan da take yi har wani irin zafi ne ke huro mishi, saurin janye wayan yayi yana mai runtse idanunsa, addu'a yake son yayi amma ya gaza yi sabida halin da ya shiga, har numfashinsa ya soma sauya wa sabida zafin kishin da shi kansa bai san hakan ba, sai yayi saurin mayar da wayan cikin tashin hankali ya kira sunan Nasirun, yace, "meyasa tun farko baka faWa min ba sai yanzu Nasir? Wannan babban maganar meyasa ka Soye min?"
Cike da wani sabon mamakin da ya kunno masa kai Nasirun yake cewa, "taya ya zan sanar maka bayan na san hakan ba wani amfani zai yi maka ba? Kuma yau ne mutumin ya zo gida babu jingirta wa su Baba suka ba shi auren ta, nima sai yanzu ne na tuna na kira in sanar maka."
Bain ciki yasa Yaya Yunusan ya kashe wayansa zuciyarsa na masa zafi sosai,
Sai ya mie daga saman gadonsa da yake zaune yana jefar da wayan nasa, da arfi ya furta, "impossible! Don me za a yi mata aure batare da an tambaye Ni ba? Meyasa abun nan ya zo min a bazata haka?"

Da sauri Sharhabila ta arisa shigowa cikin Wakin tunda maganar nasa a kunnenta suka faWa, ta shigo tana bin sa da kallo da mamakin ganin yanda yake Safa da Marwa a wurin, "lafiya Husband, kai da waye?"

Idanunsa da suka gama sauya kala ya sauke a kanta, sai kuma yayi saurin haWiye yawun takaici da bain kishin da ke addabar sa, oarin Soye halin da yake ciki yayi before ya koma ya zauna a gefen gadon, batare da ya iya ce mata komai ba, don a lokacin bazai iya ma magana ba sabida Waci da tuuin da ya zo masa iya wuya,
Ita kuma sai ta zauna a gefensa tana son sanin mai ke damun sa, but duk iya tambayar da tayi masa amma ya gaza tanka ta, a lokacin ma ji yake yi kamar ya kwashe ta da mari don takaici da bain cikin da ke tattare dashi, amma sai ya daure ya mie yabar Wakin still bai kula ta ba,
Tarin mamaki ne ya cika Sharhabila ta saki baki tana kallonsa har ya fita, sai kuma ta mie don bin bayansa da sauri tabar Wakin.***

A wannan ranan su Alh. Badamasi suka isa Abuja can cikin dare wajen karfe sha biyu saura, don ma wai irin gudun da drivern nasa yayi ne har suka isa a wannan lokacin,
Wani irin tanamemen gida ne wanda ban taSa ganin irin sa a rayuwata ba sai a wannan lokacin, sai gani yau a cikin sa wanda tsoro yasa na kasa taka afafuna bare in bi bayan Alhajin,
Har sai da shi da kansa ya jawo hannuna muka isa cikin gidan tunda Matarsa Hajiya Lantana tana nan tana jiran zuwan sa, dayake ya faWa mata zai dawo komin dare, kuma bata san da mai zai dawo ba tunda yace, "da bauwa zai shigo tayi musu girki ta tanada musu duk wani abu mai daWi."
Ai kuwa hakan tayi kuma ta shirya masa a falonsa tana jiran isowan sa,
Har barci ya soma Waukan ta a babban falo sai ta ji bugun kofa, shiyasa ta taso ta buWe mishi tunda ta san bazai wuce shi bane,
Ilai kuwa shi ne ta gani tare da Ni wacce ta kasa shaida fuskata, duk da tana kallona tar daga hasken falon da ya hasko Ni, amma irin sauyawan da nayi a lokacin baya da ta sanni sam bata yi min kallon sani ba, mamaki ne ya bayyana daga kan fuskarta; inda ta bi mu da kallo ta gaza cewa komai

Shi kuwa Alhaji wanda yake cike da farin ciki ya dube Ni yace, "shigo Madina taho mu je ciki."
Haka na sanya afa na bi bayansa cike da zallan tsoro ga wani irin bugawa da irjina yake yi kamar zai faso, gaba Waya babu sukuni a tattare dani, a yadda nake zazzare ido dole ne ka san cewan a rikice nake, kawai umarnin sa nake bi har muka isa cikin falon,
Hajiya Lantana sai ta rufo kofan ta biyo bayanmu tana cewa, "Alhaji, wannan kuma wace ce? Aina ka samo ta?"

Bai bata amsa ba sai da ya bani umarnin zama a kan manyan kujerun da suka yi matukar awata falon, sannan ya dube ta yana cewa, "ai na manta ban yi miki bayani ba, don yanzu ma daga auye nake na je gyara Sarnan da nayi a baya, wannan Madina ce yarinyar Abokina Malam Ali tsohuwar Matata, ita ce yau na je na nemi auren ta a wurin su."

Sakaka Lantana tayi da baki ta gaza furta komai a wannan lokacin sabida mamakin furucin Alhajin, inda ta bi Ni da kallo don ta tantance abun da ke fitowa daga bakin sa, tabbas ta ga kamanni a kan fuskata, amma koda wasa bata taSa kawowa Ni ce wannan a gabanta nayi wannan girman ba, abun ya Waure mata kai matua wanda yasa dayar ta iya cewa, "Alhaji, yanzu yarinyar da ka wulakanta ka saka a baya, ita ce yanzu ka je ka sake auro ta a karo na biyu? Mene ne amfanin hakan?"

"Ikon Allah! Kin ji min ke kuma da wata magana, mene ne amfanin haka kuma? Ai ko kowa ya tambaya ke bai kamata ki tambaya ba tunda kin san tsohuwar Matata ce, kuma abun da yasa na yanke shawaran sake auren ta sabida na ji labarin auren da suka yi mata wancan ya mutu ne, to a irin abun da nayi mata shiyasa na tausaya mata a yanzu na basu hakuri na ce su aura min ita a karo na biyu, don haka wannan ba abun mamaki bane Lantana babu abun da Allah ba ya yi, Ni dai kawai hakuri zan ba ki sabida ban sanar miki ba, amma kin san na cutar da ita shiyasa bai kamata na yale ta haka ba dole in taimaka mata, shine kawai yasa na auro ta sabida tausayi."

"Tirashi...! Amma wlh ka bani mamaki Alhaji ban taSa zaton haka daga gare ka ba, wannan abun da kayi tamkar ka wulakanta Ni ne tunda har ka je kayi aure babu sanina, meyasa a wancan lokacin ka sake ta sai yanzu zaka je ka dawo da ita? To wlh baza ta saSu ba Ni bazan zauna da kishiya a gidana ba, a yanzu da da ba Waya bane don in Ada na jure yanzu bazan iya jure kishi da wannan yarinyar ba, kana ganin yadda ta sauya ta koma wato yanzu ta zama Mace shine idonka ya illa ya gani har ka dawo da ita? Wlh bazan yarda ba Alhaji, bazan taSa yarda in zauna da aramar yarinya a matsayin kishiya ba, tun wuri ma ka sauya tunani don a yanzu komai zan iya yi."
Ta are maganar cike da bain kishi da irin tsanar da take min

Wanda shi Alhaji ko kusa bai damu da zancen ta ba, don shi a yanzu bai da wannan lokacin yana son fara aikin sa a wannan daren, don yana da shirin zuwa gobe yabar gidan dani sabida ba a nan zai ajiye Ni ba gudun matsala, musamman da ya ji zantukan Lantana, don haka yace mata, "Ni yanzu bani da lokacin ki Hajiya Lantana, ki bari gobe zamu yi magana amma ban da yanzu, ki je ki kwanta sai da safe."
Sai ya dube Ni yace, "tashi Madina muje."

Ai kuwa Lantana tana ganin mun bar wurin ta fara zazzaga bala'i tana cewa, "wlh zai ga abun da zai faru don baza ta taSa bari in zauna a wannan gidan ba, su zuba su gani."
Sabida bain ciki ma zama tayi a wurin zuciyarta na tafarfasa da jin tsanata a ranta, ranta yayi mugun Saci hankalin ta ya tashi ainun, a yanzu ta Wauki alwashin ita kaWai ce a gidan Alhaji don haka babu Macen da zata shigo muddin tana raye, wannan dukiyar da daulan nata ne ita kaWai da aanta dole ne ta Wauki mataki

Shi kuwa Alhaji bai san ma tana yi ba, don muna shiga falon shi yace min, "in zauna."
Haka na samu wuri na zauna na takure jikina sai rawa yake yi sosai, gaba Waya na kasa kwantar da hankalina a firgice nake sosai,
Ganin haka ne yasa ya koma lallaSa Ni yana cewa, "ko dai yunwa nake ji? Bari ya kawo min abinci in fara ci."
Inda Lantana ta jera abincin da ta girka mishi a saman wani daining, can ya nufa zai zubo min abincin, sai kuma ya koma ya cire malun-malun Win jikinsa sannan ya ajiye, ya zubo min abincin a plate, tare da gasashshen kaza danareriya guda Waya, ya sako wua da cokali a ciki, ya kawo min, cikin farin ciki yace min, "in ci."
Dayake mugun tsoron sa da shakkarsa nake ji a wannan lokacin, sam ba na iya mishi musu, haka na soma oarin ci kamar yanda yake bani umarni ba na iya musa wa,
Inda shi kuma ya koma wurin daining Win, kwalin lemo ya buWe ya zuba maganin duk yana hankalce dani har ya gama abun da zai yi sannan ya dawo wurina, jiki na rawa ya zauna a gefena fuska a washe yake ce min, "yauwa Madina ta, ga lemon nan ki shanye sai ki ci gaba da kora abincin naki."
Noewa nayi na kasa amsa kaina na asa, dama ba wani abincin nake ci ba domin tunda nayi loma biyu na kasa ara na uku, yanayin da nake ji sam babu dad'i kaina sai wani irin sarawa yake yi; jiri na son mamaye idanuna, hakan ne yasa na kasa amsa mishi kaina a asa na gaza Wago wa,
Shi kuma sai murmushi yake yi yana cewa, "ai yanzu kunya ta are dani da ke Madina, don haka zo in ba ki da kaina."
Sai ya janyo Ni jikinsa yana oarin Waura Ni a saman cinyansa,
Lokacin sai na ji kamar an zare min wani abu a jikina tunanina ya fara dawowa cikin hayyacina, na soma fahimtar a inda nake wanda nan take irjina yayi mugun bugawa sabida ganin fuskar Alh. Badamasi a kusa dani, a lokacin yayi oarin saka min kofin lemon a baki, a nan take nayi wani irin zame wa na zille a jikinsa ina ihu,
Yadda jikina ke rawa na gaza tashi a wurin ma sai jan kafafu nayi idanuna tuni sun ara fitowa waje, sai wurwurga ido nake yi ina kallon inda nake, da sauri kuma nayi yunkurin tashi in gudo amma sai yayi saurin kamo Ni yana cewa, "ina zan je?"

Kuka na saka ina faWin, "wayyo Allah! Don Allah ka sake Ni kar kayi min komai, mene ne ya kawo Ni nan na shiga uku?"
Kuka sosai nake yi a wannan lokacin sabida gani nake yi kamar mafarki nake yi, yanda na ruWe na rikice ina ihu da kururuwa ina son wace wa, amma sam na gaza domin Alhajin ba aramin arfi ya sa min ba, ya gane cewan aikin da Boka yayi masa ne ya are tunda yace mishi bayan aure zamu tuna komai, bakunan mu zasu buWe, don haka ya soma kici-kicin cire min kaya tun a nan don ma kar ya Sata lokaci,
Ganin na gaza tsaya wa ne ya zabga min marin da sai da nayi asa na zube, ji na da ganina suka Wauke na Wan wani lokaci, daga baya wani irin kuka ya kufce min na soma oarin laluba hanya domin tseratar da kaina, a halin da nake ciki sam ba na iya fahimtar abun da ke faruwa, burina kawai na samu kufce wa a hannun wannan mugun da ya WanWana min azaban mutuwa, wanda ba na fatan sake ganin fuskarsa, tabbas idan ya ci galaba a kaina mutuwa zan yi, bazan iya ci gaba da rayuwa ba, sam hankalina ba ya jikina domin a wannan lokacin da nayi oarin tashi ko ganin Wakin ba na yi sabida marin da na sha, ina laluba hannuna sai na kamo wuan da ke saman faranti, gam na rie wuan ina mai oarin buWe idanuna da suka shanye ga hawaye a cikin su, dayar nake iya gani tunda na fahimci wua ne tuni zuciyata ta aiyana min abun da zan yi, don babu wata gardama ina jin ya saka hannu zai Wago Ni na juya da arfina na luma mishi a saitin irji. A tare muka kurma ihu wanda Ni tsaban rikice wa ne yasa na fasa aran ina ihu gunun tausayi,
Shi kuma azaban da ya ratsa shi a ahon zuciya shine ya fasa uban aran da sai da gidan ya amsa, haka ya faWi ya soma shure-shure nan da nan jini ya soma fito mishi ta hanci ta baki,

Please Login or Register in order to submit comment