Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

auren sai a sake mata, to dukka-dukka Madina har nawa take da za a dage sai tayi aure? a barta kar a ara mata maganar, yanzu ta lafiyarta suke yi."
Wannan ne yasa daga ranan aka dena maganar kwata-kwata,
Daddy kuma yace, "idan ta samu saui sosai jikin alhamdulillah; gwara ta koma makaranta ta ci gaba da neman ilimi, wata rana idan da rabo sai tayi."

To wannan ne dalilin da yasa aka janye zancen auren Madina, shima Yaya Yunus iyayensa sun ja mishi kunnen gwara ya mayar da Matarsa ko ya nemi wata, amma shi ya dage dole sai Madina, yace, "zai jira ta koyaushe ne idan ta tashi auren."
Don haka ya ara aimi wajen shiga jikinta da kyautata mata,
Ga shi yanzu har ta Waura karatun ta a nan sabon gari wata private school da Daddy ya sama mata, tunda ta samu lafiya yanzu komai alhamdulillah sai dai rashin walwala da farin ciki, mai napep Daddy ya sama mata yana kaita ya Wauko ta, abunda Yaya Yunus ya so yayi amma ta i ba shi dama, abun da ke haWa ta dashi kawai gaisuwa ne, baya ga haka bata mishi magana don gani take yi ya takura mata sabida irin shishshigin da yake mata,
Daga karatu sai karatu ta saka a gaba yanzu, idan ta je ta dawo school kullum tana tare da littafan ta tana duba wa, sauin ta kenan da hakan ta soma rage uncin da take ciki, har yanzu bata yawan magana ta zama miskilan arfi da yaji, in kaga murmushinta kuwa sai dai idan Khalifa ne a kusa da ita tana mishi wasa

Yau da gobe kwanaki na tafiya haka watanni, ga shi yanzu har an shafe shekaru uku Madina ta kammala S.S.C.E Win ta.
[1/9, 8:18 AM] My Airtel Numb: =؎=؎=؎=؎=؎=؎=؎=؎
*RAYUWAR MADINA* =ا
=؎=؎=؎=؎=؎=؎=؎=؎


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
_(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* <

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS=ت)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A
'*





*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga an uwana Mata waWanda suka fuskanci uuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana arshen wahalar rayuwa._






*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 270
2gb. 500
3gb. 800
4gb. 1100
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.













______________ *EPISODE 59*
_____Zuwan Madina gidan su Mashkur, ya famo mata wani ciwo da ta daWe tana fama dashi a zuciya, dama irin wannan ranan take gudu sabida har yanzu ji take yi kamar baza ta iya rayuwa babu Mashkur ba, zuciyarta ta i aminta da cewan ta rasa shi har abada, sai dai nisan da yayi mata wanda baza ta taSa kamo shi ba,
Soyayyar da take mishi ya zame mata wani miki mai wahalar warke wa, a kanshi ta rasa farin cikinta da jin daWin ta, wanda idan har ta tuna shi koyaushe ne sai ta sha kuka na ban mamaki, yau sai ga ta gidansu wanda rayuwarta na baya ya dawo mata sabo, a lokacin da take cikin gidansu irin kulawar da yake bata da duk abin da ya faru, hakan yasa hankalinta yayi mugun tashi zuciyarta ta fara mata wani irin suka mai zafi, duk oarin ta na jure wa ta kasa, musamman lokacin da tayi arba da hotonsa a babban falonsu,
Sai ta zube a asa kawai tana wani irin kuka mai ban tausayi, kukan da ke fitar da irin ciwon da ke arashin zuciyarta,
Khairiyya da Nabeela ne suka zo suka Waga ta hankalin su a tashe sabida tunanin wani abu ne ya same ta,
Duk rarrashin da suka yi mata ta gaza yin shiru sai da suka kira Mummy,
Ita kanta sai da zuciyarta ta tsinke hawaye suka cika mata idanu,
Kamo ta tayi ta rungume ta tana cewa, "I'm so sorry Madina, ki dena wannan kukan haka ba na son ganin ki a haka, me aka yi miki uhm tell me what's wrong with you?"

Madina ta kasa yin magana illa Waura kanta da tayi a saman cinyan Mummyn tana sauke numfarfashi gunun tausayi, duk yadda ta so ta dena kukan amma ta kasa,
Su kansu sun fahimci kukan mai take yi shiyasa duk idanunsu suka cika fam da hawaye, sai mutuwar Mashkur ya dawo musu sabo, Allah Sarki! mutuwa mai yankan auna, mai raba masoya,
Irin kukan da take yi kowa ya tausaya mata matua, kuma sun gaza rarrashinta dakyar Mummy ta samu tayi shiru,
Sai ta saka su Khairiyya su kaita Wakinsu su sake rarrashinta,
Gaba Waya suka tafi har Nabeela wacce ita ce ta Wauko ar jakar kayan Madinan,
A yanzu haka Nabeela tayi aure har da Wanta guda Waya, yanzu kuma tana da aramin ciki, ta auri wani Wan uwan Mahaifiyarta lokacin da ta koma can danginsu suka fara soyayya,
Yanzu in ban da tausayin Madina da ke zuciyarta ko kusa bata jin haushin ta, to wanda ya haWa su ya raba yanzu tunda shi kansa ba ya duniyar sai hakuri. Rayuwa kenan

Tun zuwan Madina gidan sai ya zama gaba Waya ta rasa karkashinta duk jikinta ya mace, ko irin shiga cikinsu bata yi sai dai ta zauna tayi shiru tana tunanin Mashkur, a Soye kuma tana share hawayen bain ciki da uncin da take ciki, don ma Hajiya Ummee ta ja mata kunne sosai a kan halin da ta shiga, sai da tayi mata faWa sosai sannan ta saki jikinta ta dena kukan, sabida halin da ta shiga nema take yi ta jawo ciwonta,
Allah yasa akwai magungunan ta a jaka aka Wauka aka bata,
Haka suka dinga kula da ita a ranan kafin jikin nata ya Wan samu saui,
Sai dai ko fita bata yi wuni tana kwance kwana biyu da zuwan ta, duk yanda su Khairiyya suka so su ja ta a jiki abun ya gagara, ko awayen Khairiyyan sun zo sun cika Wakin suna hidiman biki; bata saka baki a cikinsu duk hiran da zasu yi,
Kamar bata san ma hiran da suke yi ba, in suka cika ta da surutun sai ta wuce Wakin Hajiya Ummee ta zauna a can, to tare da Hajiyan ne ma take Wan magana har suyi hiran gida; Hajiyan tana bata labarai kala-kala don dai ta Wauke mata kewa

Dayake Daddy ba ya zama sosai sai dare yake dawowa gidan a kwanakin,
Sai da tayi kwana uku da zuwa sannan suka Wan yi hira da Madinan,
Yake tambayar ta harkar karatun ta da kuma abun da take so a yanzu?
Yace, "idan tana son sana'a ne ta faWa mishi ko nawa ne zai bata, in Kuma karatu take so ko kuma aure sai ta sanar mishi, shi yanzu tamkar uba ne a gare ta."
Hajiya da ke wurin tayi caraf tace, "ai sai dai aure Madina, don shi ya fi dacewa da ke kibar karatun nan kawai inyaso daga baya sai ki koma makarantar, tunda aure ba ya hana karatu haka shima karatun ba ya hana aure."
Daddy da ke murmushi ya dube ta yace, "wai haka Madina? Ko kina da wani zaSi ne na mijin da kike so?"
Kanta a asa ta girgiza kanta but ta kasa cewa komai,
Hajiya tace, "buWe baki mana ki yi magana Madina sai ka ce wata bare?"
Dakyar ta bude baki tace, "na fi son karatu."
Murmushi daddy yayi yana furta alhamdulillah,
Hajiya kuma tace, "kayya Madina, kina ganin hakan ya fi dacewa da ke? Ai komai ya rigada ya wuce Madina tunda Allah ya ba ki lafiya mai Waurewa auren shi ya fi dacewa da ke, ki yi tunani kinji ko? Zama haka a gare ki ba abu bane mai yiwuwa, darajar a Mace Wakin mijinta."
Daddy yace, "Ummee ai har yanzu Madina yarinya ce tunda bata wuce 20yrs ba har yanzu, don haka zata iya fara karatun daga baya sai tayi auren ta karisa a Wakin mijinta, har yanzu fa bata shiga jami'a ba kinga ai ba wata matsala bane, su Khairiyya ba ga su nan ba sai da suka gama sannan suka yi auren, ita Khairiyya ga shi nan har degree Win ta ta kammala, don haka insha Allah Ni zan ci gaba da Waukan nauyin karatun ki Madina, har sanda kika ga ya dace ki tsaya da kanki, yanzu abun da za a yi tunda suma anninki sun gama karatun su sai a haWa ku tare dukka ku fara, don haka ki je kuyi shawara dasu ku zaSi abun da kuke son karanta, ABU ko FCE duk wanda kuke son shiga a ciki sai ku fara zuwa, Allah ya shige mana gaba."

"Amin ya Allah."
Gaba Waya suka amsa falon,
Inda Madina ta fi kowa murna da farin ciki, wani irin sanyi ne ya shige ta nan da nan ta ji zuciyarta ta fara rage uncin da take ciki, ko ba komai Daddy ya faranta mata rai kuma yayi mata abun da baza ta taSa manta wa dashi ba, har da Wan wallan ta sabida farin ciki,
Sai da shi da kansa ya dakatar da ita wajen masa godiya, yace, "shi Mahaifi ne a gare ta kar ta sake mishi godiya."

Wannan ranan fa Madina tayi farin ciki matua don burinta kenan yanzu,
Sai ga shi ta Wan saki ranta har su Khairiyya sun samu kanta suna hira da ita,
Sai dariya suke yi suna ci gaba da zanta wa kan bikin, da kuma yanda zai kasance

Har wannan lokacin Madina bata taSa haWuwa da Ansar ba tunda ta zo gidan,
Kuma alamu ya nuna ba ya gidan ne yayi tafiya wani aiki,
Kamar yanda ya manta da ita itama ta manta dashi, don ko kusa bata tuna shi ba,
Koda ta ji ana maganar Ansar Win bata kawo shi bane sabida tunanin sa kwata-kwata ya shige mata, kuma ba hurumin ta bane na shiga maganar da ta ji su Khairiyya suna yin nashi,
Duk ta Wauka wani daban ne tunda ta ji suna kiransa da Uncle

Lokacin suna tare da su Khairiyyan awayenta suka zo gidan, tare da mai gyaran jiki tunda ana mata dilka kullum na gyaran Amarya, kuma Waya daga cikin awayenta ne mai gyaran, shiyasa idan za a yi sai su haWu gaba Waya ana yi ana hira da shewa,
Daga Khairiyya har Nabeela ake musu; duk da itama Madinan an ce a yi mata amma ta i yarda,
Mai gyaran tace, "ai dayake kyakkyawa ce dole ta i yarda, kyawunta ma kaWai ya isa."
Don da yawa awayen suma abun da suka ce kenan sabida ba aramin burge su Madina tayi ba, musamman da suka ga babu ruwanta shiru-shiru da ita, ga kyau da Allah ya bata, musamman fuskarta da ke jan hankalin su sabida yalwan sajen da suke gani,
majorityn su ta shiga ransu sun dinga kallonta kenan in har ta shigo Wakin,
Shiyasa itama da ta kula da hakan take yawan saka hijab a jikinta

Tun ciwon da Madina tayi har yanzu babu wani kumari a tattare da ita, ta zama siririya sai dai babu rama a jikinta, amma ta ara kyau matua tunda tana da shape na jiki mai Waukar hankali tubarakalla, abubuwa da dama sun sauya a tattare da Madina sabida idan ka santa a baya baza ka taSa cewa ita ce yanzu ba, ga wasu sabbin Wabi'u da ke tattare da ita musamman rashin magana da ta ara koya, miskila ce na buga wa a jarida kuma duk rayuwar da tayi na school kwata-kwata bata taSa yarda da wace Wiya mace sunan awa ba; bare kuma samari suke nuna suna sonta, ko kallo basu ishe ta ba, wannan ne yasa idan zata fita koyaushe bata fita babu niab da dogon hijab,
Takan kame jikinta a koyaushe a kuma duk inda ta tsinci kanta,
wannan ne yasa mutane da dama suke mata kallon ar hamshain mai kudi sabida kallon da suke mata da kuma irin kyawun da take dashi na usulin bafulatana,
Yawan tsantsenin ta da kuma kame kanta yasa ake mata kallon mai girman kai na wasu ya'yan masu kuWi,
Nan kuwa basu san ma daga ina take ba, dayake school Win na masu kuWi ne Daddy ya saka ta,
Haka yawancin an makarantar su da malamai suke mata kallo,
Har ta gama makarantar kuwa ta kasa yarda wani mutum Waya ya shiga jikinta, wasu ma da yawa har cikin malaman bata san sunan su ba sabida tsaban rashin son jama'a, dama a jininta yake na rashin aunar jama'a, kuma har yanzu bata sauya ba na rashin yarda da mutane; a War-War take dasu, su kuma suna mata kallon girman kai ne da nuna isa

Yanzu ma tana zaune tana jin hiransu but ta i tanka wa sai dai kallon yanda ake dilkan take yi,
Su kuma hira suke yi har shewa Khairiyya tana sanar da Waya daga cikin kawarta dawowar Ansar yau Win; tunda sun yi waya ya faWa mata,
Dayake ita awar tana sonshi ne matua, yawancin awancen su da Khairiyya ta samo asali ne tun ganin da tayi wa Khairiyya da Ansar Win a super market, wannan ne yasa ta shiga jikin Khairiyya tunda ta santa a school Winsu, kuma bata Soye mata komai ba na game da son da take mishi,
Yanzu ma da aka faWa mata yau zai dawo dad'i ta dinga ji while sauran awayen suna shewa da faWin, "Meenansar... Meenansar..."
Dayake sunan da suke kiranta dashi kenan tunda ta haWa sunanta da nashi ne, wato Meena & Ansar. Meena-nsar,
To hakan ke sa wa kanta yana faWi tana farin ciki tana musu kyauta tunda yar masu kuWi ne yarinyar

Abun sai ya koma ba Madina mamaki tunda har yanzu bata fahimci da wane suke yi ba,
Sai daga baya ne kuma da ta ji suna kiran sunanshi Ansar ba Uncle Win ba, irin maganganun su yasa ta gane da wanda suke yi,
Lokaci Waya fuskar Ansar ya dawo mata; tabbas ta tuna shi lauyan nan Wan Uwan Mashkur Winta,
Amma kuma daga haka bata sake bi takan zancen su ba, sai fita tayi a Wakin ta koma wajen Hajiya da suke zaune a can downstairs su da Mummy suna hira.
[1/9, 8:18 AM] My Airtel Numb: =؎=؎=؎=؎=؎=؎=؎=؎
*RAYUWAR MADINA* =ا
=؎=؎=؎=؎=؎=؎=؎=؎


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
_(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* <

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS=ت)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A
'*





*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga an uwana Mata waWanda suka fuskanci uuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana arshen wahalar rayuwa._






*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 270
2gb. 500
3gb. 800
4gb. 1100
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.












______________ *EPISODE 58*
_____Halin da Madina ta shiga da kuma komawarta makaranta; wannan ne yasa ba a sake yi wa Ansar zancen aurenta ba, wanda shi kansa a tunaninsa an bar maganar ne hakan ya sanya shi farin ciki, sai dai kuma koda ya sake zuwan ma Daddy da maganar komawarsa Riyadh,
Daddy ya nuna masa Sacin ransa ya kuma ce, "muddin ya sake zuwar mishi da maganar zai ga abun da zai masa, Riyadh ne bazai taSa komawa ba in dai don ya zauna a can ne gaba Waya."
Wannan ne yasa Ansar ya sake bijiro da maganar budurwansa da yake so a can, ya kuma ba shi hauri ya nuna nadamar sa a fili, amma Daddy ya i amince mishi, yace, "bazai hana shi aure ba ya je yayi, but sai dai ya kawo yarinyar nan ta zauna dasu."
Sanadin hakan ne yasa iyayen Samina suka i amincewa, a cewarsu, "arsu baza ta je Nigeria tayi aure ba, in har Ansar yana sonta dole ne ya dawo kusa dasu ya zauna, ko kuma ya nema mata wata asar, but ban da Nigeria, ba sa son Nigeria."
Sanadin haka Ansar yana ji yana gani ya rasa Samina, tun daga wannan lokacin yayi fushi bai sake yin wata soyayya ba, ya kuma udura a ransa bazai yi auren ba a nan har sai idan sun amince ya koma Riyadh,
Bai sake musu zancen aure ba haka suma su Daddy basu sake mishi maganar ba,
Amma ganin shekarun nan sun tafi Daddy ya sake kiranshi yace, "ya ji shi shiru har yanzu bai fito da matar aure yayi aure ba, ko dai har yanzu yana mu'amala da Matan banza ne?"
Shi kansa Daddyn ya san yanzu Ansar ba ya wannan Wabi'an, sabida yanda yasa aka yi ta bibiyanshi domin ganin ko ya canza hali, a fahimtar sa dai Ansar ya dena waWancan abubuwan,
Kuma hakan ne, sai dai shi Ansar Win ya san cewa Daddy yasa a ria bibiyanshi, shiyasa ya Wauke afansa da zuwa club ko wani yawo da bai dace ba, kuma yayi hakan ne kawai don bazai iya mu'amala da Matan Nigeria ba, domin yana ganin su gidadawa ne da kuma tuna abun da Shamsuna tayi mishi, wannan ne yasa yake taka-tsan-tsan kuma ya ja baya dasu, sai dai bain cikinsa yanda aka hana shi komawa Riyadh, tabbas da a can yake bazai taSa dena halayyarsa ba, kuma har yanzu yana shan sigari don ya zamar mishi kamar Wabi'a ne, duk da ya rage sosai kuma yana sha ne a lokacin da ya san babu mai ganinsa ko bibiyansa, sai yayi nesa da gida a zuwan ya tafi wajen aiki, a can yake sha sannan ya dawo gida lafiya, bai yarda yabar shedan da zai nuna har yanzu yana shan taba ba,
Ya yi wa Daddy rantsuwan duk ya dena komai,
Shi kuma Daddy tabbas ya amince dashi, sannan yace, "to idan bazai nemi matar aure yayi aure ba, maganarsa da Madina har yanzu tana nan, dama ya ba shi dama ne ko yana da wata budurwan sai ya kawo a yi musu aure, kafin har Allah ya kawo ranan auren shi da Madina tunda ita yanzu ta koma makaranta, ya fita hainsa ne shiyasa ya tambaye shi, kuma kar yayi ta zama babu matar shiyasa yayi masa haka, but tunda ya i ya jira lokacin auren shi da Madina."
Wannan yasa damuwar Ansar ya dawo sabo, kenan har yanzu maganar bata tafi ba? Ya Wauka an manta da zancen tsawon lokacin nan da ba a sake mishi maganar ba, ashe laSo suka yi, yayi bain ciki matua kuma yana ji a ransa shi fa bazai iya auren yarinyar da suke son laaba mishi ba, wacce a yanzu ya manta da kalarta ma tsawon wannan shekaru ukun bai sake sanya ta a idanu ba,
Domin Madina bata ara tako afanta zuwa gidansu ba, sabida abun da zai faru idan muddin ta je gidan su Mashkur, ta tabbata baza ta taSa manta shi ba, ba ta son ara kusanta kanta da gidan na har abada, shiyasa ko an ce ta je bata zuwa,
Amma har nan su Hajiya Ummee suna biyo ta su ganta, haka ma Khairiyya duk sanda Hajiya Ummee zata zo tare suke zuwa, wata rana ma Daddy yakan zo,
Mummy ne dai sau biyu ta ara zuwa tun bayan da Madinan ta samu saui,
Hajiya Ummee har yanzu tana can Kadunan bata dawo ba, gidanta sai dai aka saka haya,
Duk da an so a ba Baba ya zauna a ciki, amma ya nuna ba ya so bazai iya amsa ba, shiyasa koda aka saka an hayan sai ya zamana Hajiya Ummee ta dana mishi komai shi ke kula da gidan, kuma ta i amsar kuWin hayan tace, "ya rie nashi ne, wlh baza ta taSa amsar gidan nan ba tunda ya i komawa Ita dai ta mallaka mishi, a duk sanda ya so zai iya cire an hayan ya zauna, kuWi kuma nashi ne yayi duk abun da yake so."

Yanzu haka bikin Khairiyya za a yi wanda bai fi kwana goma ba,
Shine Umma tace, "dole Madina ta je tayi musu hutu kafin bikin ta zauna a can har sai an yi biki, inyaso idan ita ta zo tare da su Hassana sai su taho tare washe garin bikin."
Tunda su zasu zo ana gobe ne su kwana biyu,
Madina bata so ba don ta i amince wa, a cewar ta, "ita baza ta iya zuwa ba, zata jira har ranan da zasu je sai su tafi tare."
Umma tace, "bata isa ba tayi kadan, sai ta je wlh."
Wannan ne yasa Madinan ta roi alfarman zasu tafi tare da su Hassana gaba Waya,
But nan ma Umma ta i amincewa, tace, "ko Khalifa baza ta je dashi ba tunda shima bai samu hutu a makarantar su, Babanshi ma yace anjima zai zo ya Wauke shi zai yi mishi kwana biyu."
Haka nan Madina tayi shiru tunda Umman ta i amince wa, har a ranta bata son tafiyar duk da halin da Khairiyya take nuna mata da kuma kulawar da take bata, a shekaru dai ta girme ta amma ta Wauke ta tamkar awarta, duk wani abun bikin da ake yi sai Khairiyya ta kira ta ta sanar mata, kuma ta roe ta a kan ta zo tun ana sati amma Madinan ta amsa mata a cewar, "zata zo."
But ashe ba har zuciya bane, abu daya ne yasa ta kasa zuwa gidan, kuma bata marmarin ara ganinta a gidan, amma yanzu dole ne ta je tunda ya zamar mata dole bata da yanda zata yi

Da yamma sai ga Yaya Yunus ya zo gidan tafiya da Khalifa; kamar yanda ya kira Umma ya sanar mata,
Har wannan lokacin kuma Yaya Yunus yana fama da Madina a kan amince masa a karo na biyu, amma ta i ba shi dama,
Tuni Sharhabila ta koma Wakinta tunda ta gane baza ta iya rayuwa babu shi ba, wannan yasa da kanta ta je ta ba shi hakuri, ta kuma sanya iyayenta suka ba shi hakuri, sannan ta amince da sharaWin sa a kan zamanta a can auyen su,
Wannan ne yasa ta koma Wakinta ta tare a auye, ta tafi da udurin zata shawo kansa ya mayar da ita cikin birni, amma har yanzu abu ya gagara yanzu kusan shekara Waya da komawar ta,
Wanda shi Yaya Yunus yana hasashen Madina ne a cikin gidan nan nasa, ita kaWai yake hango wa kuma bazai taSa yarda Sharhabila ta tare a gidan ba; har sai idan Madina ta shiga kuma ta amince, in kuma bata amince ba sai ya siyan mata wani gidan itama ta dawo nan, amma a yanzu ba ta ita yake yi ba, zuciyarsa da idanunsa sun makance a kan Madina,
Wacce sam tayi kunnen uwar shegu dashi ta nuna kamar bata san me yake yi ba,
Yanzu ma koda ya zo tunda ta gaishe shi ta shige Waki abun ta,
Bata ara fitowa ba har sai da Khalifa ya zo ya kira ta yana cewa, "Daddyn shi na kira."
Sai lokacin ta tashi daga kwancen da take, ta ajiye littafin da ke hannunta tana duban shi, cikin sanyin muryanta da har yanzu bata sauya ba tace, "me zan mishi ne kake son sai na je?"

"Mama yace ki je ki Wauko min kaya Ni bazan iya ba, yana waje wurin motansa, shine yace in kira ki."
Hannunsa ta kama ta zaunar dashi a jikinta tana cewa, "shi bazai iya shigowa da kayan bane sai Ni ce zan je? Ni nake buatar ya baka?"
Umma daga waje tace, "na hana ki irin wannan maganar a gaban yaron nan amma ba kya jin magana, na ga alamun kin fara sauya hali Madina kwata-kwata ba kya sanin me ya kamata ki furta, kin san halin yaron nan da shegen Waukan zance amma ki yi ta sakin zance a gabansa, shi Yunusan ai Yayanki ne in baza ki Wauke shi a matsayin Uban Wanki ba,
Ki fito ki zo ki je ki amso kayan; ya fasa tafiya dashi tunda na faWa mishi zancen tafiyarki Kaduna, yace ranan da za ki tafi zai zo ya dauke shi."
Mie wa Madina tayi batare da tace komai ba, ta fara neman hijabin ta zata saka but gaba Waya fuskarta ta haWe alamun ranta a Sace ne,
Da sauri Khalifan ya Wauko mata hijabin da ke kan gado yana cewa, "Mama ga hijabin nan a nan."
Juyawa tayi ta amsa ta saka sannan ta fita ta zura slippers tayi waje,
Umma ko kula ta bata yi ba illa kaWa kai da tayi tana duban Khalifa da ke saurin zura nashi soson takalmin zai bi ta,
Tace, "taho nan kar ka bi ta: ka bari ta dawo,
su Hassana sun kusa dawowa islamiyya zasu kaika wurin Iro ya baka biscuits, taho ko iyeee Wan Baba."
Hakan ne yasa ya fasa fitan ya nufe ta yana murna

Madina kuma tana fita ta same shi a cikin mota, tsayawa tayi jikin motan ta i kallon inda yake,
Sai yace, "shigo mana Madina muyi magana, akwai abun da zan faWa miki."
Kallonshi tayi, sai dai ta Wan saki fuskarta

Please Login or Register in order to submit comment