Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunda ta ji kamar mutanen gidan ne suka dawo.
[2/10, 10:46 AM] Oumahira: =؎=؎=؎=؎=؎=؎=؎=؎
*RAYUWAR MADINA* =ا
=؎=؎=؎=؎=؎=؎=؎=؎


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
_(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* <

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS=ت)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A
'*





*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga an uwana Mata waWanda suka fuskanci uuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana arshen wahalar rayuwa._






*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 280
2gb. 550
3gb. 840
4gb. 1120
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.
















______________ *EPISODE 24*
_____Dukkansu kallon Umma suka hau yi suna mai mamakin ganin ta a cikin Falon; batare da sun amsa sallaman da tayi ba,
Dayake ita Sharhabila bata san ta ba shiyasa take mata kallon mamaki da tsoron ganin ta a cikin gidan su, ko kafin tayi magana Yaya Yunus yayi magana yana mai amsa gaisuwar Umman da take mishi cike da fara'a,
Sai shima ya saki fuskar sabida ya gane wace ce bazai taSa manta fuskarta ba, yace, "Umma Asiya ke ce a gidan namu yau?"

"Wlh kuwa, yau Ni ce a gidan naku." Tayi maganar tana isowa ciki sosai tare da zama a saman Kujeran,
Shima sai ya zauna suka soma gaisa wa cikin mutunta juna, duk da a hasashen shi bai kawo tunanin Mahaifiyata ba ce sabida sam ya manta cewan an ce mishi ar wajen Babansu Sule aka aura mishi

Sharhabila ganin haka itama sai ta zauna tana kallon Umman tare da amsa gaisuwar nata, kasancewar a lokacin Umman ta mayar da kallonta gare ta tana gaishe ta itama

Ni kuma tuni na nufi saman dining na ajiye coolern ina gyara wa kamar yadda na ga Aunty Sharhabila tana yi, yayinda Sadam ya biyo NI yana tsalle-tsalle da min surutun sa yana bani labari,
Ni dai ban bi ta kanshi ba don hankalina yana a kan su Umma, har na gama na nufi hanyar kitchen don kwaso plates

Lokacin tuni itama Yaya Haula ta fito falon; ta nufi inda suke ta dua har asa tana gaishe su,
Shi dai Yaya Yunus amsa ta kawai yayi amma bai gane wace ce ba, but da ya ga kamar muna kama shiyasa ya bi Ni da kallo yana sake kallon Yaya Haulan, a nan take mamakin ganin Umman a gidansa ya gushe sabida ya gano dalilin zuwan nasu

Ita kuma Sharhabila sai cika take yi tana batsewa tana faman taSe baki ganin bain wanda ta gama tabbatarwa dole an uwansa ne, tunda ga kama nan a fuskar Yaya Haula itama, shiyasa ta tashi tsam tana shige wa Wakinta tare da kiran sunan Mubashir da Sadam suka bi bayanta

Yaya Yunus Wan sakin fuskarsa kaWan yayi yana cewa, "tun Wazu ku ka zo ko yanzu ne Umma?"

"A'a mun Wan jima, shi ne Madina tace min kun fita tun safe, amma yanzu ma zamu tafi."

Bai ce komai ba kuma bai yi tunanin tsayar da su ba balle yayi musu tayin abinci, kawai kuWi ya ciro cikin aljihun sa har naira 3k ya mia wa Haula yace, "ke amsa, Umma sai ku ara kudin mota, mun gode da ziyara."

Murmushi Umma tayi tare da masa godiya har ya mie yabar wurin, kana ta kalli Yaya Haula tare da mayar da idanunta a kaina, don nima tuni na zo na gurfana a kusa da Yaya Haulan, tace, "to Madina zamu wuce, sai wani lokacin kuma, tunda mun ga gida insha Allahu za ki ria ganin mu a kai- a kai, sai ki kula ki ci gaba da hauri, Allah ya baku zaman lafiya."

Tuni hawaye sun soma cika min ido jin abun da take cewa, kamar zan fashe da kuka sabida yanda nayi da fuskata, cikin rauni na furta, "Umma tun yanzu don Allah? Don Allah kar ku tafi ku barni zan bi ku."

"Bin mu kuma Madina? Ko kin manta aure kike yi a nan? Ki yi hakuri kin ji ko ai zamu ria zuwa muna duba ki, Haula tashi mu je kar lokaci ya ure mana; tunda ke gida za ki wuce yau."

A haka ina ji ina gani su Umma suka bar gidan, har bakin gate na raka su har da share hawayena, domin ji nake yi tamkar na bi su amma babu hali, haka ina gani suka tafi dole na dawo ciki,
A lokacin mutanen gidan duk sun fito suna saman dining suna cin abinci,
Lokacin Sharhabila tana tambayar Yaya Yunus Win mutanen da suka fita ne? Shi kuma yana bata amsa, shiyasa tayi kicin-kicin da fuska tana bala'i tana zage-zage tare da cewa, "gaskiya bazai saSu a ria kwaso mana kare da dogi cikin gida ba, idan yarinyar baza ta yi aiki ita kaWai ba to babu dole tabar musu gida, don ba an kawo ta don dangi su ria biyo ta suna ganin abun da suke ci bane, haka kawai a ria saka mata ido?"
Tunda na ji waWannan kalaman nata sai na tsargu na gane da Ni take yi, a hankali na taka na yi saurin shige wa Waki ban tsaya jin abun da Yaya Yunus yake faWa mata ba,
Yayinda na zauna gefen gadona na fashe da kuka sabida tsaban kewan su Umma da nake ji, sai da nayi kukana ma'ishi sannan na share hawayena na shiga bayi na Waura alwala, ko sallan ma ban yi ba na ji kiran Aunty Sharhabila a kunnena, da sauri na saka hijabin jikina na fita da gudu don amsa kiran nata..**

To a wannan yanayin rayuwata ta ci gaba da gudana cikin daWi da akasin sa, to ba dai zan ce ina shan wahala sosai ba; duba da rayuwar da nayi a baya, wannan zan iya cewa mai saui ne sosai a kan rayuwata ta baya, tunda a kan ayyukan da nake gani masu wahala ba komai bane a kan ayyukan da nake fama da su a gidanmu, rayuwar tawa ta sauya fiye da baya, don baza a haWa ba ma; kawai dai farin ciki ne yayi min aura wanda na kasa samu daga Matar gidan, don gaba Waya yanda take azazzala min da irin muguntan ta sam ba na samun farin ciki, har sai idan nayi mata abu daidai nake tsallake wa daga hukuncin ta, don har takai ta kawo wani lokacin dukana take yi da igiyar wayar wuta, abun da tun tasowa ta ba a taSa min ba; domin kasancewata mai biyayya da rashin yuya, amma duk oarina Aunty Sharhabila ba ta gani, kuma Yaya Yunus bai taSa Waga kai ya kalle mu don ya hana ta hukunta Ni ba, tamkar ma bai san abun da ke faruwa ba, babu ruwansa da Ni balle yace don me take duka na? Gaskiya ina iya oarina wajen yin mata biyayya, da haka rayuwar ta ci gaba da tafiya ga shi har na share kusan watanni uku da zuwana gidan,
Sai a lokacin Ummanmu ta sake zuwa ta duba Ni, sabida lokacin da ta zo ma ba sa nan mutanen gidan suna wurin aiki, yaran kuma suna makaranta, Ni kaWai ta samu, kuma mai gadi bai hana ta shiga ciki ba sabida ganin wancan lokacin ma sun shiga lafiya mutanen gidan basu kawo mishi orafin kar ya sake barin su ba, shiyasa ya barta ta shiga,
Kuma bata bari ma mutanen gidan sun dawo ba tayi min sallama ta tafi, duk da wannan lokacin ma ji nayi tamkar na bi ta, amma babu hali, nasiha kawai da ban baki ta dinga yin min, wannan karon ma ta kawo min tsaraba kamar wancan lokacin, duk da a waWancan ma ban yi amfani da kayan miyan da ta siyo min ba, sai Soye wa da nayi ban ara bi ta kansu ba, a wannan karon ta tambaye Ni, "shin nayi amfani da su na kar'ar?" Nace mata, "eh." Kawai tunda bazan iya faWa mata zaman da nake yi a gidan ba,
Koda ta faWa min waWanda suka bata kuWin nayi mamaki matua, yayinda a raina sai na ji daWi matua sabida soyayyar da Hajiya Ummee take nuna min, barin ma yau da ta kawo min dambun nama tace min, "Hajiyan tace a haWa min musamman a kawo min."
Sosai nayi godiya ina ta murna da jin daWi,
A haka Umma ta tafi tabar Ni, yayinda na Soye duk abubuwan da ta bani,
Dama ban da matsala da Aunty Sharhabila a kan duk abubuwan da ta ga ina saka wa, musamman suturu domin bata taSa tambayana ba; bare ta damu da ganin kalolin kayan da nake saka wa, tunda itama Aunty Sharhabila tana son tsabta ba ta son azanta, ganin ina kiyaye wa tunda ta ja min kunne shiyasa bata damu ta bincike Ni ba tunda ta san da abuna na zo, ba Mijinta ya siyan min ba.

Haka dai na ci gaba da musu bauta tun ban saba da rayuwar gidan ba har dai yanzu na saba, na kuma saba da wahala da muguntan Aunty Sharhabila, don in ya motsa mata babu kalan cin ubana da bata yi, ta dinga zagina kenan tana are min tanadi ko a gaban Yaya Yunus ne bazai taSa tanka wa ba, tunda aka kawo Ni kuma babu wanda ya taSa zuwa ya leo ni a auyen mu idan aka cire Yaya Haula da Umma, babu wanda ya taSa zuwa, wani lokacin dai sau Waya Baban Sasa ya kira Yaya Yunus ya bani wayansa muka gaisa, ya sake jan min kunne yana tambayar halin da nake ciki? Na faWa masa babu komai tunda a lokacin akwai Yaya Yunus Win ya tsare Ni a gabansa yana sauraron abun da nake ce wa, a lokacin har sai da ya tambaye Ni, "ko Yaya Yunus Win ya siyan min kayan Waki kamar yanda ya ba shi umarni? Kuma yayi min kayan akwati da komai? Don ya fi so ya tabbatar a bakina ne?"
Ko jingirta wa ban yi ba na amsa mishi da eh don ban ga fuskar da zan iya in amsa wa ba, kar in ja ma kaina ya ci ubana ina zaune alau haka kawai

Shi kuwa Yaya Yunus ganin ban Sallo mishi ruwa ba har sauke numfashi yayi, yana ganin na gama wayan sai ya amsa ya juya ya tafi dakin sa, Ni kuma dama ina kitchen ne ina aiki ya zo ya mia min wayan, sai na ci gaba da aikin nawa ina tunanin tambayoyin da Baban Sasa yake min, a raina nace, "tab wanne kayan Waki zai yi min Ni da ba Matarsa ba? Nima wlh ba na buata ya rie kayansa, zamana a haka ya fi min alkhairi."
Sai kuma na koma tunanin duk sanda Matarsa ta san cewa akwai auren Mijinta a kaina na tabbata kashe Ni zata yi, baza ta taSa barina da rai ba a yadda dai na santa da mugunta.
A haka dai na ci gaba da ayyukan nawa har na gama na wuce Wakin Yaran na gyara musu nayi musu wankin kayan su a cikin ban-Wakin su, sannan na gyara Falon kasancewar babu kowa tunda ana hutu Yaran an kaisu gidan su Aunty Sharhabila, kuma yanzu safe ne yanzu haka Aunty Sharhabila bata tashi ba, don akwaita da shegen barci yanzu tunda ta soma aiki, da zaran sati da Lahadi sun yi ranan Hutu ne a kwance zata wuni, komi Ni zan yi duk da dama Ni nake yin komai yanzu, babu abun da ban iya ba na daga cikin gidan, a takaice ma har kayan Yaya Yunus yanzu Ni nake wanke mishi, tare zan haWa da kayanta da nashi in wanke tass sannan in goge, haka ma na yaran, yanzu har takai ta kawo ta sakar min Wakin shi Ni nake shiga na gyara idan sun fita,
Kuma duk wadannan abubuwan da nake mata wani lokacin sai ta ci gyara na ko ta wawwanka min mari wai ban yi mata dai-dai ba, ko kuma ta bani abu ban yi a kan kari ba, shiyasa yanzu har na saba da zafin nama, komai nawa ina yin sa ne cikin sauri da zafin nama gudun samun matsala, kafin ka ce me na gama, ko kusa wahalhalun gidan ba ya bani wahala, domin idan da sabo ya ci a ce na saba, kawai dukan da take min ne yake cin min rai,
Tun zuwana gidan ban taSa saka afafuna a waje na fita wajen gidan ba, kullum ina cikin gidan Ni nake musu komai, yanzu ga shi kusan watanni takwas da kawo Ni gidan, tun ma ina irga kwanaki zuwa watanni har yanzu ya Sace min,
Ummanmu sau uku kenan ta taSa zuwa duba Ni, Yaya Haula kuma sau Waya, duk da ta so zuwa amma babu hali Mijinta bai barta ba

A zuwan da Umma tayi wannan karon ne muka samu matsala da Aunty Sharhabila, tunda a lokacin da Umma ta zo shab na manta ta bani aikin gyaran kayan sif Win ta, don cewa tayi, "kaf in ciro kayan in sake goge mata su sannan in mayar in shirya."
Sai ta ware min masu datti waWanda zan wanke,
To a lokacin tunda suka tafi na fara aikin gidan har na share falon tsab na gyara Wakin Yaya Yunus dana su Mubashir, sai na je kitchen na fara Waura girkin shinkafa da miya da tace shi zan yi, sannan sai in haWa musu da ferfesun kayan ciki da ta bar min, na je Waura wa kafin in je in gyara mata Wakin, ga shi lokacin na tashi ba na wani jin daWi, sabida ciwon da ya kunno min na mara da na saba yi, duk da zuwana gidan sai daga baya na fara yi yanzu kusan sau uku nayi, amma da ya Wauke gaba Waya ba na yi, sai watanni ukun baya ya dawo min ba aramin wahala na sha ba a waWannan ranakun, kuma babu damar in faWa musu tunda ban ga fuska ba, a haka nake daure wa in ta shan kuka a Waki ina Soye halin da nake ciki, tunda yawanci ma da dare yake tashi min, kafin safe sai ya lafa min, sai wani lokacin kuma ya sake tashi min har sai na ga jini ya fito, to wannan ranan tunda na ji marata tana karta wa na tabbatar shi zai zo, don abu ne mai wuya in yi ciwo haka kawai sabida ban saba yawan ciwo ba, tunda na ji haka na san shi ne,
Har na Waura farar shinkafan sai kuma cikina ya fara ciwo sosai, dole na nufi falo na kwanta a asa ina birgima da yarfe hannu, sai kuka nake yi kamar zan mutu, don a halin da na shiga na manta wace ce Ni bare in tuna abun da nake yi, sai da can kamar zan mutu sannan can ya lafa min na soma dawowa daidai, duk na haWa gumi nayi wujiga-wujiga idanuna sun yi ja, ganin bai ara murWa min bane sai na mike a daddafe na koma kitchen Win, lokacin abincin har ya caSe ya sha ruwa sosai ya dafu ya tafke ma kamar za a yi tuwo, da sauri jikina na kerma na sauke hawaye na bin fuskata sabida ganin yadda shinkafan tayi, na san na kaWe a hannun Aunty Sharhabila tunda bata san kuskure ba, tabbas sai ta hukunta Ni a kan wannan abun da nayi mata, jikina babu wari haka na fara gyara kayan miyan har na jajjaga na Waura miyan

A wannan lokacin ne kuma Ummana ta zo, nayi murnan ganin ta wanda yasa na manta da halin da nake ciki, farin ciki da Woki ya hana Ni wani tunani, tuni na maale mata ina murna

Ita kuma kallo Waya da tayi min ta gane kamar akwai abun da ke damuna, don yadda ta ga idanuna sun yi ja sai tahau tambayata tana sake taSa min jiki ganin da Wan zafi, sai tace, "Madina ba ki da lafiya ne; na ji jikin ki da zafi haka?"

Saurin girgiza mata kaina nayi ina mai mayar da kaina saman kafaWanta na kwantar da shi,
Sai ta sake Wago Ni tare da cewa, "a'a ban yarda ba, da alamu ba ki da lafiya, kinji yanda jikinki yayi kuwa? Ga idanunki nan fa har sun sauya; mene ne me ke damunki?"
Cike da son Soye halin da nake ciki sai nace mata, "Umma wlh babu komai, kaina ne dai yake Wan min ciwo shiyasa kika ga jikina ya Wauki zafi."

"Ai ba kawai bane Madina, ciwo kowanne iri ne ciwo sunansa, kin sha magani ne?"

Sai nayi arya nace mata, "na sha." Don dai ba na son ta ci gaba da min wasu tambayoyin, don ban san me zan ce mata ba

Sai ta ja numfashi tace, "nima ba daWe wa zan yi ba kinga yanzu zan tafi, dama nace ne bari in leo in duba ki tunda na dade ban zo ba."

Cike da shagwaba don ba aramin taSara nake dashi ba muddin na ganni a gaban Ummana, don jina nake yi kamar wata aramar yarinya, kwata-kwata ba na girma in dai a gabanta ne, haka ma Yaya Haula, su kaWai ne nake iya sakin jikina da su in ji kamar in koma cikinsu don taSara, don ji nake yi bani da wata sauran gata in har ba ina gabansu bane, shiyasa da na sanya ta a gaba dole sai da ta ara lokaci kafin ta tafi,
Ni kuma sai na koma kichen na arisa sauran aikina,
Kamar jira ake yi na gama sai marata da cikina ya hau karta, aikin da ban arisa ba kenan ban tuna da sauran gyaran Wakin Aunty Sharhabila da tabar min ba, kuma tabbas da na tuna koda zan mutu ne sai nayi sa, amma halin ciwo yasa na manta gani nake yi kamar na gama komai, Wakina na shige na dinga kuka ina murkususu a asa kamar zan mutu, ban san iya adadin lokutan da na Wauka a wannan yanayin ba sabida azaban ciwo, sai can ya Wan lafa min barci ya Wauke Ni batare da na motsa daga inda na kwanta a asan Wakin ba, kaina a kife a saman hannuna fuskata tayi sharkaf da hawaye

Barcin da ya Wauke Ni ne ban san lokacin da suka dawo ba mutanen gidan,
Sai can kamar a mafarki na ji wani irin zugin azaba ya tsarga min a bayana, ko kafin in tantance abun da ke faruwa da Ni; tuni muryan Aunty Sharhabila ya doki kunnena, da sauri na yunura zan tashi, amma ina wani irin azaban ciwo da kuma bulalan da ta zula min ya haWe min a lokaci guda, wani irin uban ihu na tsandara ina mai gantsare bayana,
Ita kuma sai ta ci gaba da narka min wayan wutan da ke hannunta cikin fushi da Waga murya tana cewa, "dan kutmar uban ki har Ni zan saka ki aiki ki zo ki kwanta kina barci? Sannan kika Sata min abinci kika mayar min dashi tuwo? Halan ubanki ya siyan mana shiyasa kika wulaanta mana tunda ba ki da asara? ar matsiyata auye basu saba ci ba, yau sai nayi miki dukan da baza ki sake yunkurin kamanta min irin wannan ba, har in sa ki abu ki i yi ko? Wuyanki ya isa yanka kenan?"

Tun Yaya Yunus yana jin muryata daga Wakinsa yadda nake Sarka kukan kamar zan tsaga gidan, tun yana jure wa sai kuma ya kasa sabida jin ihun nawa ba na hankali bane, Yaransa tuni sun bar Wakin sun nufi inda suke jin kukan nawa, don haka shima ya mike ya fita da sauri don kar a yi kisan kai a gidan sa, don ya ji abun ba na hankali bane,
A lokacin da ya shiga Wakin tuni azaban ciwo da na dukan da take min yasa na sume gau,
Amma ita bata gane hakan ba sai lafta na take yi tana zagina ta uwa da Uba

Da sauri Yaya Yunus ya kama bulalan yana cewa, "wai kanki Waya kuwa Sharhabila? Kina ganin yarinya ta sume ba ta motsi kuma kike ci gaba da dukan ta? Kashe musu a za ki yi?"

"Bar Ni in kashe ta mana ai ba asarana bane, don wlh ban ga ar iskan yarinyar da zata zo ta ci arzikina sannan ta i min biyayya ba, ba a haife ta ba, ar iska shegiya matsiyaciya, dama auyawa basu iya cin arziki ba, to Ni bazan lamunta ba gwara su zo su Wauke ta tunda baza ta ci banza a nan ba, tunda ba wani shege daga can yayi mana wahala ba, dama tun yaushe ake faWa min son banzan mutanen auye amma ban ji ba, ga shi yanzu na soma gani an fara kawo min Waya gida, nan gaba ma sai su zo su tare gaba Waya mu ci da su, ai Ubana ba kuWin banza ne da shi ba."

Gaba Waya ta soma tunzura Yaya Yunus bata sani ba, don bai taSa jin haushin abubuwan da Sharhabila take yi ba irin na yau da take faman zagin masa asali, sai ya ga kamar har da shi take yi ga kuma iyayensa da take haWa wa, ransa ya soma Saci dalilin da yasa ya tsawatar mata kenan yana cewa, "wai me kike son fada ne Sharhabila? A gabana kike zagin asalina ko an ce miki iyayen nawa basu da abun yi ne da kudin Dadyn ki suka dogara? Kin taSa ganin dangina sun zo maula gidan nan ko sun tako afansu haka kawai babu dalili?"

Yatsina fuska tayi tace, "ban taSa gani ba, amma ga shi nan sun turo min Waya ta zo tana cin arziki tunda su basu da arzikin rie ta, suna ganin kamar dukiyar Ubana dukiyar su ne..."

Tsawa ya daka mata yana cewa, "da Ni kike yi kenan ba da ita ba? Yau Ni kike yi wa gori Sharhabila? Ni Yunus kike gaya wa wannan maganar don kawai Mahaifinki ya taimaka min a rayuwa? But duk da taimakon da yayi min yanzu shi yake ciyar da Ni Ko Ni nake ciyar da gidana? Ki faWa min?"

Tsaki ta ja tana sakin bulalan da ya rie, tare da juya wa zata fita tana cewa, "oho dai, koma dai mene ne shine silan arzikin ka, duk wani abun da zaka zama shi ya taimaka maka, don haka baka da bakin da zaka iya Waga min murya don nayi magana a kan waWancan banzayen mutanen."
Tana faWan haka ta saka kai ta ficewarta

Yayinda ran Yaya Yunus sosai ya sake Saci da jin kalamanta, lallai kuwa zai nuna mata kuskuren ta tunda har zata iya gaigaya masa magana irin haka, yau shi Sharhabila take yi wa gori don yana yale ta? Hmm
Numfashi ya ja yana janye Sadam da ya aname sa yana kuka da kiran sunansa a kan, "ya taimaka wa Aunty Madina zata mutu, jini na zuba a jikinta."
Sai lokacin shima ya kula da jinin da yake zuba ta afafuna, sai da gabansa ya faWi sabida ganin jinin, da sauri ya dua a gabana yana mai kware skirt jikina tare da duba wurin, sai kuma ya sanya hannu ya Wage rigana, sai da jikinsa yayi sanyi sabida ganin yanda Sharhabila tayi min ruWu-ruWu da jiki, abun ka da mai farar fata tuni zanen bulalan ya fito yayi jazur ya tara jini,
Janye Sadam ya kuma yi a gabansa sabida anameshin da ya sake yi yana kukan, ya rasa ma abun yi don ganin halin da nake ciki, yana ganin kamar idan ya bar Ni a haka zan iya mutuwan musu a gida, kuma arshe shi Iyayensa zasu tuhuma, a karon farko ya soma jin tausayina yana ganin abun da yayi bai dace ba, idan da ace yana hana Sharhabila dukana baza tayi min irin wannan dukan mutuwan ba,
Haka nan ya sanya hannu ya Wago Ni kamar wata aramar yarinya, don ji yayi tamkar ya Wauki Mubashir sabida rashin nauyi da ananta,
Da sauri ya fitar da Ni daga Wakin ya nufi hanyar waje

Sharhabila na zaune a falon ta ganshi ya Wauko Ni a hannunsa yana shirin fice wa da Ni, sai ta mie da sauri ta nufe sa cike da zallan kishi da bain cikin ganin ya dauko Ni rungume a jikinsa.
[2/10, 10:47 AM] Oumahira: =؎=؎=؎=؎=؎=؎=؎=؎
*RAYUWAR MADINA* =ا
=؎=؎=؎=؎=؎=؎=؎=؎


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
_(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* <

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS=ت)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A
'*





*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga an uwana Mata waWanda suka fuskanci uuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya

Please Login or Register in order to submit comment