Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiyasa Allah ya Waura min ™aunar Madina a raina, yanzu ga abun da yake faruwa babu ko Wigon so na a zuciyarta, babu tausayina a zuciyarta, ai ina ganin ko Allah ana mishi laifi ya yafe wa Bawansa bare mu Wan adam, Madina ta kasa gane inda na sa gaba."
Cike da tausayinsa Doctor Bilal yace, "ba wai ta kasa gane inda ka sa a gaba bane Yunus, Ni ina ga akwai cutan da yake damunta sabida abubuwan da suka faru a baya, a mahanga ta idan ka duba abubuwan da ke faruwa da ita; tunda tace baza tayi aure ba to ba na tunanin akwai sha'awar hakan a tattare da ita, irin wannan abun yana faruwa da ire-iren ta duba da abun da ya faru da ita a baya, Ni a ganina tana bu™atar Likita na musamman domin ya bincika asalin me ke damunta, domin abu na farko da zaka fuskanta bayan kun yi aure Akwai yiwuwar kayi dana-sani, sabida baza ta taSa baka goyon bayan mu'amalar ku ba, because tun farko babu sha'awa da kuma soyayya a tattare da ita; da dai makamantan su. Hakan na faruwa gaskiya musamman kaciyar nan da ka taSa bani labarin an yi mata."

"No, ba na tunanin haka ne, domin ai ba a kanta aka fara ba, sannan yanzu maganar da nake maka akwai wanda ta amince zata aure shi, ko a baya ai soyayya tayi da wani, Ni ne kawai bata so."

"Ban fahimta ba?"
Nan Yaya Yunus ya sanar dashi abun da ke faruwa, da musabbabin tashin ciwon nata tunda yayi ™o™arin tafiya da ita ™auye ne; domin yakaita wurin iyayensa ko zasu lallaSa ta ta amince ta aure shi,
Ko kafin Doctor yayi magana; sai ga Nurse ta shigo tana sanar musu, "yarinyar ta fice a Wakin, bata ganta ba."
Da sauri suka tashi suka fita suna neman ta, duk hankalin Yunus a tashe yake ya rasa inda ke masa dad'i, sun duba kan hanya har waje babu Madina har ta tafi,
Ko sallama Yunus bai yi wa Doctor Bilal ba ya shiga motansa yabar asibitin.
[1/9, 8:18 AM] My Airtel Numb: =ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ
    *RAYUWAR MADINA* =Ĝ§Ü
=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
           _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>ĜŬŬ*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* <Ĝß

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS=ĜŞÜ)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A
'ŝ*




            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ´an uwana Mata waWanda suka fuskanci u™uban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ™arshen wahalar rayuwa._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 270
2gb. 500
3gb. 800
4gb. 1100
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.











______________ *EPISODE 64*
_____Kai tsaye gidan Umma Yaya Yunus ya wuce; sabida yana kyautata zaton gida Madina zata koma,
Ilai kuwa lokacin da ya shiga ya tarar da Umma ta fito daga Waki,
Tayi mamakin ganin ya sake dawowa; ganinsa a firgice yasa ta soma tambayarsa cike da mamakin sa?
Sai yayi saurin Soye halin da yake ciki yana cewa, "Umma, dama na dawo ne in duba ko Madina ta dawo itama? Na je makarantar ba ta can."
Umma tace, "yanzu ta shigo itama, tace bata da lafiya ne shiyasa ta dawo gida, yanzu na gama matsa mata ta sha magani ta kwanta, sai dai kayi hakuri don na ga alamun jikin ya matsa mata na san halinta baza ta iya tashi kuyi magana ba."
Saurin murmusawa yayi yace, "babu komai Umma, ki barta kawai bari in je, zan dawo ko zuwa gobe ne, amma Umma don Allah ki rarrashe ta a kan maganar mu ta amince a mayar da auren mu, shi wanda za a nema mata bata san halin sa ba, bata san wanne hali zata shiga idan ta aure shi ba, ni yakamata ta aura ko domin Wanmu Khalifa, don Allah Umma ki amince ku bani wannan damar."
Umma tace, "to shikenan Yunus, idan ta tashi zamu yi maganar da ita, amma ka sani komai yin Allah ne babu takura a wannan lamarin, mu bi ta a hankali tunda ka ga a halin da take ciki don Allah."
Jinjina kansa yayi yace, "to Umma, Ni bari in je in dawo da Khalifa tunda na ga lokacin tashin su school yayi."
Daga nan sallama suka yi ya fice, but yana shiga cikin mota ya ga Jakar Madina a ciki wanda ta bari, har zai fita ya mayar gida sai ya tuna kuma batare suka zo ba, idan yakai kuma Umma ta tambayi inda ya samu jakar fa? Shiru yayi yana nazarin abun da zai yi, daga karshe kuma sai ya ja motan ya nufi school Win su Khalifa don ya Wauko shi

While Madina da ke kwance a Wakin Umma; duk tana jin abun da suke faWi, tayi lamo ta kwanta ne sabida Umma kar ta gane halin da take ciki, idanuwanta sun kaWa sun yi jazur har yanzu zubar da hawaye take yi, jikinta babu ™wari ™irjinta buga wa yake yi zuciyarta na mata zafi, duk da yanzu da sauki sakamakon magungunan da ta sha; amma duk da haka tana jin jiki don ta kasa runtsa wa sabida ciwo,
Sai can daga baya barcin ya fizge ta cikin wani hali wanda alamun jikin nata babu dad'i

A lokacin da su Hussaina suka dawo; tare da Falak suka taho cikin motanta driver ya kawo su,
Saboda tunda Madina ta tafi ta ji ta shiru bata dawo ba, tayi kiran wayanta har ta gaji, dole ta koma class tunda lokacin lecturen su yayi, bayan sun fito ne ta kira Hussaina take tambayarta, "ko sun yi waya da Madina ne? Ta ji shiru bata dawo ba tun sanda wani ya zo ya kira ta, tana tunanin Wan uwansu ne."
Dayake Hussainan ta gane Yaya Yunus ne tunda ita ta kwatanta mishi inda zai sami Madinan; a lokacin da ta kira Falak ta tambaye ta,
Sai tace mata, "eh Yayansu ne, amma bari ta kira wayansa ta ji suna ina."
Koda Hussaina ta kira sai Yaya Yunus yace mata, "Madina ta koma gida bata jindaWi, tana gida yanzu haka."
Har zai kashe wayan sai kuma yace mata, "kar ta sanar da Umman su komai a kan zuwan shi makarantar, don ba ya son ta sani."

"To Yaya."
Ta amsa mishi sannan ta kashe wayan,
Bayan ta kira Falak ta sanar mata, itama kuma tace, "zata biyo ta su je su gaishe ta."

A lokacin da suka isa kofar gidan; daidai shima Yaya Yunus ya dawo da Khalifa, don haka ya samu damar tsayar da Hussaina ya bata Jakar Madina yace, "ta shiga mata dashi gida."
Hannun Khalifa ya sakar mata yana mishi bye-bye yace, "ya bi Hussaina su shiga ciki."

"To Daddy, but baka shiga ciki ba?"
Yaron yayi maganar yana kallon Babansa,
Shi kuma sai ya shafa kansa yace, "sauri nake yi Khalifa, kuma daga gidan nake na shiga Wazu, yanzu ka bi su ku shiga ka ji ko?"

"To Daddy.. ba-by."
Ya Waga mishi hannu sannan ya juya suka wuce da Hussainan,
While Falak da Hassana su sun shige cikin gidan tuni

Har wannan lokacin Madina bata farka ba don bata san da zuwan Falak ba,
Dayake Umma ta san waye Falak a wajen Madina; duk da bata santa a fuska ba; amma ta amshe ta hannu bibbiyu suka gaisa tana tambayarta nata iyayen da mutanen gida?
Bayan sun gaisa sai ta saka Hassanan ta zubo mata abinci ta kawo mata,
Falak na zaune gefen Madina inda ta kwanta a saman gadon Umma, Hassanan ta fita zuwa dibo mata abincin, itama Umma ta fice tana ci gaba da aikinta,
Khalifa ne ya shigo ya tarar da Falak Win zaune gefen Madina tana kallonta,
Tahowa yayi wurin shima yana kallon Falak sabida ganin bakuwar fuska,
Ita kuma murmushi tayi masa tana kallonsa cike da sha'awa; tsananin kamannin da ta gani na Madina a fuskarsa; sai tayi zaton shima kaninsu ne tunda babu bambancin su da Madina, yaron ya burge ta shiyasa ta janyo hannunsa tana cewa, "Aboki zo mana, ya sunanka?"
Shiru Khalifa yayi yana kallonta bai bata amsa ba,
Sai ta sake mishi murmushi tana cewa, "Ya sunanka baby tell me your name please?"
Cikin muryan yarinta ya amsa mata yana ci gaba da kallota, sai ta Wauko shi ta Waura a jikinta tana cewa, "wow my baby, which class are you?"
Ta tambaye shi sabida ta ganshi da school uniform,
Ya amsa mata yana kallon fuskar Madina, sai kuma ya kwaSe fuska yana kiran sunanta,
"Mama... Mama.. tashi."
Ganin yana dukan fuskarta sai Falak tayi saurin tare shi tana cewa, "Oh oh! Khalifa, dena dukanta barci take yi, kar ka tashe ta bata da lafiya ne."
Narai-narai yayi da fuska zai yi kuka, sai ya kalli Madinan ya sake duban Falak yace, "Mamana... ki ce ta tashi."
Rungume shi tayi a jikinta tana rarrashinsa; duk da ta ji mamakin kiran ta da Mama da yake yi; but bata kawo komai ba don a tunaninta rashin wayau ne,
Hassana ta shigo Wakin da plate a hannu, tare da pure water tana cewa, "ah ah! Kai kuma fa? Kukan me kake yi?"
Falak tace, "yana rigima ne sai ya tashi Madina."
Ajiye abincin tayi sannan ta amshe shi tana cewa, "haba Boy Mamanka bata da lafiya ne ta kwanta, kar ka tashe ta zo mu je in cire maka uniform Win."
Fita tayi dashi zuwa Wakin su,
Tabar Falak zaune tana tunanin maganar Hassanan, fuskar Madina ta kalla tana sake mamakin ganin tsantsan kamansu da Khalifa, kamar an tsaga kara, sai kuma ta tuno fuskar Yaya Yunus wanda shima kamansu Waya, su ukun suna kama da juna amma kwata-kwata bata kawo tunanin da gasken Khalifa zai zama Wan Madina bane, sabida babu ta yanda za a yi Madina ta haifi yaro kamar wannan, infact ta san bata da aure tunda bata yi mata kama da masu aure ba, shiyasa bata sake ma tunanin ba,
Har su Hassanan suka tafi islamiyya tana zaune a gidan bata tafi ba, tare da Khalifa suka wuce amma ta sha mamakin ganin yanda Khalifan yake ta kiran Madina da Mama,
Duk da har lokacin bata tashi ba tana kwance amma Yaron sai zuwa yake yi yana kiran sunanta, ga kuma maganganun da suke fitowa daga bakin yan gidan; sai abun ya tsaya mata a rai, sai dai tabar maganar a zuciya duk da ta so ta tambayi Hassana ko Hussaina,
Sai da suka tafi kuma suka koma hira da Umma, duk da Umman tace mata, "ko in ta gaji ta tafi tunda Madinan bata tashi ba."
Tace, "a'a zata jira ta har ta tashi."

Wurin karfe biyar da rabi sannan Madinan ta farka, ganin Falak a zaune a kusa da ita sai tayi saurin tashi zaune tana kiran sunan ta,
While Falak ta ri™o hannunta tana mata murmushi tare da cewa, "ki yi a hankali mana."

"Yaushe kika zo?"
Ta tambaye ta da muryan marasa lafiya; wadda maganar nata dakyar take fita sabida halin da take ciki,
Falak tace, "ai tun Wazu ina nan, tare muka dawo dasu Hassana na biyo su in ga jikin naki."
Shiru Madinan tayi tana du™ar da kanta,
Falak tace, "ya jikin naki?"

"Da sauki."

"Masha Allah! Bari in kira Umma in sanar mata kin farka."
Mi™e wa tayi ta fita zuwa kiran Umman,
Tare suka dawo itama Umman tana tambayar jikin nata?
Ta amsa mata da sauki tana nuna karfin hali don kar su gane yanayin da take ciki, don har yanzu babu karfi a jikinta, kuma tana jin ciwon a ™irjinta har yanzu,
Ruwan wanka Umma ta juye mata tace, "ta zo tayi."
Bayan ta je tayi ta dawo ne sannan ta zuba mata abinci ta ci kaWan ta sha maganinta,
Sai a nan ne Falak ta san me ke damunta tunda ta duba kwalin maganin ta ga magungunan ciwon zuciya ne, cikin mamaki ta tambayi Umma tace, "wai Umma ciwon zuciya ke damun Madina?"
Umma ta amsa mata da faWin, "wlh kuwa, ai ta kwana biyu tana fama dashi."

"Innalillahi... But wlh bata taSa sanar min ba."
Sai ta kalli Madinan cikin tausaya mata take mata sannu,
Madina murmushi tayi mata bata ce komai ba tana haWiyar maganin da Umma take Sallo mata,
Bayan tA gama sai ta fita ta basu wuri,
Shiru suka yi, sai kuma Falak tace, "amma akwai abun da ya daure min kai Madina, duk da har yanzu ban san wani abu a game da ke ba, since ga shi kina fama da wannan babban ciwon ba ki taSa fada min ba, na san da ni ce wlh bazan taSa Soye miki ba, still dai ba ki dauke ni a matsayin ™awa ba Ni kaWai na dauke ki a matsayin ´ar uwa ™awa."
Kallonta Madina tayi, cikin sanyin murya kuma tace, "ki yi hakuri, amma ba wai ban Wauke ki a matsayin ™awa bane kawai maganar bata haWa mu bane."

"No babu wani nan, ba dai kiyi ninyar sanar min bane, Ni da nake ba ki Labarina ke kika tambaye Ni? Ni na sanar miki don ra'ayin kaina sannan don ki san ko Ni wace ce; maybe ™awancen mu tayi ™ar™o, ai Ni a tunanina haka ake yi duk da ban taSa yin ™awa ba, gayyar danginmu ma sun ishe Ni."
Sai tayi murmushi kuma tana girgiza kanta, hannayen Madinan ta ri™e tare da cewa, "anyway; ga tambayar da nake son yin miki a kan Khalifa, I don't understand na ji yana kiran ki da Mama ne, kuma na ga kuna kama sosai wlh kamar ke ce kika haife shi, shi ne abun ya Waure min kai."
Gaban Madina ne ya faWi; sai dai ta kasa yin magana don bata san me zata ce mata ba; idan tace yaronta ne ta san babban magana ta Sallo yanzu zata sha tambayoyi a wurin ta, duk da har a ranta ba wai tayi haka bane don ta Soye mata ainihin wace ce ita ba; duk tsawon lokacin nan suna tare bata san labarinta ba ta san dole Falak zata yi tunanin ta ™i sanar mata ne don bata dauke ta a bakin komai ba, irin wannan tambaye-tambayen take gudu shiyasa tun farko bata son shiga harkan mutane,
Shirun da tayi shiyasa Falak ta girgiza ta tana cewa, "kin yi shiru ba ki bani amsa ba?"
Sai kuma tayi dariya tace, "maganar ne fa ta tsaya min a rai that's why kika ji ina miki wannan tambayar, ai na san dole ™aninki ne tunda ga shi kuna kama, sai dai ya fi biyo ki wlh kamar an tsaga kara, bai yi kama da su Hassana ba, da mutumin Wazu ma kun yi kama kamar Mahaifinsa."
Murmushin ya™e Madina tayi tace, "wai baza ki je gida bane dare ya soma yi fa?"
Hararanta tayi tace, "kin ™osa in tafi ko?"

"Laa a'a wlh, kar a ji ki shiru ne shiyasa nayi miki magana."
Baki ta taSe tace, "ai na kira Mamy Wazu na sanar mata, but yanzu zan tafi duk da na so in bari su Khalifa su dawo muyi sallama."
Madina murmushi tayi mata tace, "akwai labari idan na zo gobe school, nima zan ba ki labarina tunda na ga kin soma jin haushi a kaina ba na sanar miki da komai."
Dariya Falak tayi tace, "wlh a'a Ni ban ji haushi ba, amma dai zan yi farin ciki in kin sanar min tunda ina bu™ata, ina son mu zama ™awaye aminai; wlh Madina jin ki nake yi kamar ´ar uwata don kina burge Ni ne ina son mu zama Good friends."
Itama dariyan Madina tayi tace, "amma fa bazan iya da surutun nan naki ba don shi yake saka min ciwon kai."
Sosai Falak tayi dariya tace, "wlh haka ´an gidan mu suke faWa; ke ma ga shi kin faWa min, ni kuma in dai ban yi maganar bane ba na jin dadi, ni kadai na fita zakka a gidanmu; wlh rashin maganar ki kamar su Ammeena suka haife ki, duk familynmu basu da magana sai Wai-Wai, ni ce farot number one..."
Shigowar Umma ne ya tsayar da Falak Win daga surutun da ta Wauko,
Umma tace, "Falak baza ki tafi gida ba magriba ta kusa, kar a neme ki kuma?"

"To Umma yanzu dama zan tafi."
Sai ta mi™e tana daukan gyalenta da Jakarta tayi musu sallama zata fice,
Madina ta mi™e ta raka ta har bakin ™ofan gidan,
Sai da ta ga ta shiga mota sannan ta Waga mata hannu ta koma cikin gidan.
*****

_____Washe gari tunda jikin Madina da sauki sai suka wuce makaranta, bayan sun samu interval ne suka zauna da Falak take bata labarinta sabida ta yanke shawarar sanar mata; don bata son su ci gaba da haka tayi tunanin tana Soye mata gaskiyar waye Khalifa a wurin ta, tunda ita ba wai ya dame ta bane don ta sani, babu amfanin boyewar tunda tana bu™atar sani

Falak ri™e baki tayi cike da tsananin mamaki tun kafin ma ta faWa mata sauran labarin, sai tace, "wai kina nufin Khalifa Wanki ne?"
Murmushi Madina tayi tace, "meye abun mamaki a ciki?"

"Don Allah ki faWa min gaskiya Ni ban yarda ba."
Madina kallonta tayi tace, "wlh da gaske nake miki, Ni na haifi Khalifa, kuma shiyasa zan ba ki labarin rayuwata ko don ki yarda Ni na haife shi, sabida tun ina ´ar shekara goma sha Waya aka yi min aure, aurena na fari kenan; kuma ina da shekara 12 aka kaini Wakin Miji."
Sai ta Wan saki murmushi hawaye suna cika mata idanu; ta sake kallon Falak Win tace, "aurena huWu Falak, mazan da na taSa aure su uku ne."

"Don Allah Madina kar ki mayar dani wawiya mana, ki yi min abun da hankali zai Wauka, don Allah da gaske kike yi ko wasa?"
Kukan da Madina ta fara shiyasa Falak ta ruWe, tayi saurin riko ta tana cewa, "mene ne na kuka kuma Madina? Me ya faru?"
Bakinta ta rufe da bayan hannunta, sai ta shanye kukan tana sakin numfashi duk da hawayen sun kasa tsayuwa, sai ta girgiza kanta idanunta sun kaWa sun yi jazur, tana son buWe baki tayi magana amma ta gaza, sai ta buWe zata yi magana sai ta kasa,
Halin da ta shiga sai ta bata tausayi, dafa ta tayi tace, "I'm so sorry, na yarda da ke don Allah ki bani labarin ina son sani, tabbas akwai abun da ya faru a rayuwarki wanda yake miki ciwo, Please sanar dani don Allah bazan iya jira ba."
Numfashi take ja tana fesarwa, sai da ta samu natsuwa sannan ta soma bata labarin komai da ya faru da ita,
Kafin ka ce me Falak ta fashe da kuka, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...! Abun da take iya furta wa kenan, ta ™an™ame Madinan a jikinta suna kukan a tare, domin labarin ya fama mata ainihin ciwon da ke zuciyarta; musamman idan ta tuna da Mashkur; zuciyarta ta kasa ha™ura dashi, gani take yi kamar komai nata ya ™are idan babu shi a rayuwarta,
Kuka sosai suke yi a tare; wanda ita kanta Falak ta kasa magana illa furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un da take yi,
Sai can da ta ga numfashin Madina na sauya wa tana jan shi dakyar; tayi saurin dakatar da nata tana cewa, "ki yi hakuri na famo miki mugun ciwo Madina, wlh tallahi idan ba ke kika bani labarin nan ba bazan taSa yarda ya faru da ke ba; gaskiya na tausaya miki, kin yi juriya sosai Allah ya ba ki ikon cinye wannan jarabawar, ki yi hakuri."
Sai ta sake rungume ta before ta Wago tana share mata hawaye, "Please Madina ki dena kukan nan duk da ya zama dole ne, amma sabida ciwon da kike fama dashi kinga numfashinki ya soma sauya wa, ki yi hakuri."
Murmushi Madina tayi hawaye na tsiyayan mata daga kuncin ta, sai tace, "ba komai Falak, na yarda da kaddara ni nawa jarabawar kenan, kuma haka Allah ya ™addara min, kinga yanzu kamar ba a yi ba ko? Komai ya wuce."
Wani irin kuka ne ya taho wa Falak; sabida tsananin tausayinta, hannayenta biyu ta ri™e tana kallonta tace, "wlh kina da juriya duk da haka Madina, idan Ni ce zuciyata buga wa zata yi, kin jure wahalhalu da yawa, abu mafi ciwo mutuwar Mashkur, shi kaWai ya fi ™untata min a rai; domin na san da yana raye za ki ji dadi a rayuwarki; za ki samu farin ciki mai Worewa, wlh kin rasa masoyi na ™warai, but Allah zai musanya miki da mafiyin shi albarkan Annabi, na tausaya miki Madina."
Kuka ne ya ci ™arfin ta sai tayi shiru tana rufe bakin ta,
While Madina share nata hawayen tayi tana cewa, "ki dena kukan yanzu to tunda na ba ki labarin komai, kin san ko Ni wace ce yanzu, mu tafi class sabida na san yanzu an fara lectures."

"Ni bazan iya jin wani karatu ba yanzu, wlh labarin ki yasa gaba Waya farin cikina ya tafi, Madina bazan iya jin karatun nan ba; bazan iya ba."
Shiru suka yi dukkansu, while Falak tana sheshshe™an kukan da ya kasa tsaya mata, zuciyarta cike da tsananin tausayin Madina; idan ta tuna da labarin sai gaba Waya gwiwowinta su sacce, ba abun da ke ™ara karya mata zuciya idan ta kalli Madinan a ™an™anin shekarun ta but ta fuskanci u™uban rayuwa, wai har gidan yari ta zauna; ga ™addaran aure-aure; mai ya fi wannan ciwo?
Karshe sai Madinan ne ta koma rarrashin Falak sabida yanda gaba Waya jikinta ya saki har lokacin ta kasa dena kukan; sai tayi shiru kuma sai ta fara matsan hawaye tana ce wa Madinan, "yau baza ta iya barci ba."

Sun jima suna tare a wurin basu koma class ba; har aka tashi sannan suka wuce, karshe Falak bin Madinan gida tayi don ta kasa tafiya gida,
Tun daga ranan sai ya zamana sha™uwar su ta ™ara ™arfi sabida ita kanta Madina bata taSa tunanin zata samu ™awa mai hali irin Falak ba, gaskiya tana da tausayi domin tun ranan da ta ji labarin ta kasa sukuni; koyaushe buWan bakinta sai tace mata, "tausayinta take ji, ta kasa manta labarin ta."
Madina kuwa dariya kawai take mata, daga karshe tace mata, "ita dai tana da raki ne, daga bata labari duk ta sauya abu kaWan tace tana bata tausayi."
Falak tace, "baza ki gane bane, wlh duk mai imani dole ya tausaya miki, kin haWu da ™alubale mai yawa Madina, amma kin shanye duk da Allah ya jarabbe ki da wannan ciwon; amma cuta ba mutuwa bane komai zai wuce da sannu, Allah ya ba ki ikon cinye jarabawar ki ya kuma cika miki burinki."

While fannin Yaya Yunus tun ranan da abun nan ya faru shima ya dena takurawa Madina; sabida ko don halin da take ciki, bare tunda Baban sasa ya gargaWe shi a kan maganar ya soma ha™ura; yace mishi, "idan har yayi sanadin mutuwar Madina tabbas zai fuskanci mummunan hukunci a gare sa, tunda ta nuna rashin amincewarta a wurin sa don me bazai bi ta a hankali ba? Kar ya ™ara zuwar musu da maganar muddin ba ita ta nuna tana son auren sa ba."
Wannan ne yasa Yaya Yunus ya janye duk da zuciyarsa ta kasa ha™ura da Madina; sai dai halin da take nuna masa a yanzu yayi muni don ko ganinta ba ya yi yanzu, da zaran ta ji muryansa zata shige Waki baza ta fito ba sai ya tafi, ta sauya mishi gaba Waya ko ya kira wayanta a yanzu ba ya samu tayi blocking Win sa, dama ita ba wai tana Waukan ba™uwar number bane, shiyasa ko ya kira ba ya samun ta; idan kuma ya tura mata text message tana gani zata saka shi a Blacklist since ta gane shi ne

Ana haka suka fara jarabawa; wanda zasu shiga aji na biyu, a sati biyu da farawan su suka gama,
A washe garin ranan da suka gama Falak ta zo tayi mata wuni har dare, duk da ita har wannan lokacin Madina bata taSa taka gidan su Falak Win ba, bata taSa zuwa ba har yanzu, dayake Falak Win tace mata, "zata wuce Kaduna a can zata yi hutun ta."
Shiyasa Madinan duk bata ji dadi ba domin zata yi kewarta; yanzu sun rigada sun saba sosai; musamman halin Falak in dai kana tare da ita sai ka saba da ita sabida shegen shishshigin ta da surutu kala-kala bakinta ba ya shiru

Ana haka kuma Daddy ya taWo da maganar auren Madina da Ansar, a cewarsa za a yi auren nan da sati Uku masu zuwa before hutun su ya ™are, a yanda ya yanke Madinan in ta zo Kaduna sai ta Waura karatun ta a can za a yi mata transfer,
Wanda Ansar ya amince da auren ne sabida shawo kan Daddyn da yayi, ya yi wa Daddyn alkawarin, "zai amince da auren amma don Allah a bar shi ya koma Riyadh da zama, don

Please Login or Register in order to submit comment