Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kasa yin masa musu."

Nan fa sai aka hau hayaniya sabida jin zantukan Baban sasa, wanda ya hautsina wurin nan take wasu suka cika da mamakin furucin nasa, wasu kuma sosai sun yarda da maganar nasa tunda ai Wan siyasa ne dole zai iya yiwuwa akwai abun da yayi musu, musamman ma in har labarin abun da ya aikata a baya gaskiya ne,
Al™ali ya buga guduma ya bu™aci a yi shiru, sai sannan ne aka soma natsuwa hayaniyar ta lafa

Ansar ya ™ara neman alfarma domin jin ta bakin Madina,
Don haka aka ba shi dama; shi kuma ya taka har inda take tsaye kanta a sunkuye, ya kirayi sunanta tare da faWin, "ta basu labarin abun da ya faru a ranan da Alhaji ya tafi da ita, da kuma dalilin da yasa ta aikata mishi hakan?"

Kasa Wagowa tayi bare ta kalli kowa da ke wajen, sai dai jikinta wani irin rawa yake yi wanda zaka gane cewan a mugun tsorace take, don ma wai Mashkur ya bata ™warin gwiwa a jiya da suka koma wurin ta, sannan shi kuma Ansar ya ja mata kunne sosai ya kuma gargaWe ta a kan, "muddin ya tambaye ta kar tayi shiru ta ba shi amsar tambayar shi, kuma abun da ya tsara mata shi zata faWa dolenta.. if not zata ga mai zai yi mata don bata isa ta kunyata shi ba, already ya baro aikin da yake yi ne ya zo taimaka mata."
Madina gwanar tsoro, bare Allah ya dasa mata tsoronsa da shakkarsa, wannan dalilin ne yasa bata kawo musu gardama ko wani cikas ba a yanzu, har ta iya bada labarin komai tiryan-tiryan, har da ™arin gishiri da Maggi da Ansar yace sai ta faWa,
Tana yi tana kuka domin ta kasa jurewa ga tsoro ga tashin hankali

Smile Ansar yayi lokacin da ya ji ta gama bada labarin daidai yanda yake so, sai ya juya yana duban Al™ali tare da furta, "My judge! Wannan shi ne abun da ya faru a ranan da tayi ™o™arin ™wace kanta, Macen da ta shiga irin mawuyacin halin nan a wancan lokacin, Macen da ta kasa manta u™ubar da ya gana mata a wancan lokacin; yarinyar da bata san komai ba kamar wannan don ta aikata abin da ta aikata, yana nufin tsoro ne da kuma kokarinta na ™watan kanta, ya nemi ya sake amfani da ita wanda yayi mata barazana da nufin kashe ta da wu™a. Sai kuma ga shi Allah ba azzalumin bawansa bane ita tayi nasaran caka mishi, i know wannan ba laifi bane, ™o™arin kare kai ne, zan so katu mai adalci kamar wannan ta yi wa Madina adalci sannan ta ™watan mata ha™™inta a wurin mutumin nan, and we want to file a complaint against laifin raped Winta da yayi da kuma auren dole, muna bu™atar a bi mata ha™™inta then a raba auren, thank you my judge."
Ya risinar da kansa before ya koma ya zauna

Kotun sai ta sake rikice wa da hayaniya kamar jira ake yi ya gama bayaninsa,
Al™ali ya buga guduma yace, "a yi shiru don Allah."
Sai ya dubi lauyan Sangaren gwamnati yace, "ko kana da abun cewa?"

Mi™ewa yayi yace, "ya mai Shari'a wannan zantukan da suka yi zai iya zamowa shiri ne da suka yi domin ganin sun samu nasara, domin bazai yiwu a ce babu Alhaji a nan yana kwance a asibiti sannan a yarda da zancen su ba, kowa ya sani abun da ya faru a gaban Matarsa ne da kuma sauran security Win sa, idan har gaskiya ne cewan abun da ya aikata mata meyasa suka sake ba shi aurenta? Taya ya zasu ce hankalin su ya gushe ba a son ransu suka sake aura mishi ita ba; har sai daga baya? Ya mai Shari'a wannan abun duba wa ne, domin bata yanda za a yi su shirya zantukansu babu hujjoji sannan su zo su faWa kuma a amince da su, ina fata kotu zata yi mana adalci ta tsaya ta bincika maganar su sannan ta yanke hukunci. Nagode ya mai Shari'a."
Komawa yayi ya zauna yana duban Ansar da suka haWa ido dashi,
Sai dai kowannensu kawar da kansa yayi

Inda al™ali ya sake duba takardun asibitin da aka ba shi, sannan ya Wago yana duban su yace, "wannan kotu baza ta yarda da zantukan mutanen nan ba har sai idan sun kawo shaidun da ya fi wannan ™arfi, sannan sai idan Alh. Badamasi ya samu lafiya ya zo kotun nan mun ji ta bakin sa, sannan wannan takardun na asibiti muna son mu ga likitan da ya duba ta domin tabbatar da gaskiya."

Zumbur Ansar ya mike yana cewa, "Oh judge! give me a chance to introduce the doctor because he is here."

Kansa ya jinjina tare da faWin, "an baka dama."
Bayan ya faWa sunan Mashkur, sai Maga-takarda ya mi™e ya hau sanarwan, "ana bu™atar ganin Doctor Farouk Umar Farouk a nan."

Mashkur mi™e wa yayi ya fito zuwa wurin da ake tsaya wa,
Da kansa al™alin yahau masa tambayoyi a bisa jinyar da tayi,
Kuma ya ba shi amsar duk abun da ya faru,
Aka sake kiran Umma itama ta bada labarin duk abun da ta sani,
Wannan dalilin ne yasa Ansar ya bukaci ganin matar Alh. Badamasi,
Dayake ta zo wajen shiyasa aka kira ta, a nan ya tsare ta da tambayoyin da dole ta amsa gaskiyar abun da ta sani, tunda kasancewar yanda ya rikita ta; ta yanda dole ne ta fito da gaskiyar abun da ta sani batare da ta san ta faWa ba, har auren da aka yi lokacin suna ™auye da kuma wannan auren, iya abun da ta sani ta faWa,
Nan fa mutane suka yi ca ana ta surutu abun ya Waga hankalin mutane,
Shi kansa Al™ali ya gamsu da hujjojin nasu, dalilin da yasa ya bu™aci lauyan Alh. Badamasi yayi magana idan yana da abun cewa,
Amma sai yace, "bai dashi."
Al™ali bayan yayi rubutu sai ya yanke hukuncin, "za a Wage Shari'a nan da sati Uku masu zuwa, har sai idan Alh. Badamasi ya samu sau™in da za a iya kawo shi nan a ji ta bakinsa, sannan kotu ta bada belin Madina Sulaiman Umaru har zuwa ranan da za a sake dawowa zaman karshe."
Sai ya buga guduma yana mi™e wa tsaye

Wannan hukuncin ba ™aramin faranta ran duk wani Wan uwan Madina yayi ba, farin ciki ya cika zukatan su Umma, haka suke kukan murna duk sun nufo inda Madinan take, duk da an hana su ™arisa wa don a lokacin ´an sanda sun tasa ta waje zasu fitar da ita,
Hakan ne yasa su Mashkur suka isa wurin su suna tattaunawa,
Wani police da ya fita zuwa wurin motansu, shi ya je Wauko mukullin da za a kwance hand cuff din hannunta, don haka sai da aka fita da ita waje sannan suka kwance ta,
Wurin ya cika ma™il da mutane don ´an jarida sun yi ca suna son musu tambayoyi, ga su Baban sasa suma duk sun iso wurin,
Ganin jama'a sun yi yawa ne sai Mashkur ya ja hannunta ya saka ta a motansa,
Lokacin Ansar na ciki ya zauna a gaba yana duba wayansa, tunda ya Wago ya dube su ya kau da kansa, yana jin sautin kukan Madina na shiga kunnensa, sai dai bai ce komai ba sabida har a ransa yana jin tausayinta,
Mashkur sai da ya koma ya sanar da su Baban Sasa, "kawai su hau mota su biyo su zuwa gidan Kakansu, sai su ga Madinan a can, don nan jama'a sun yi yawa sosai."
Hakan kuwa suka yi, bayan su Mashkur sun tafi suma motocin su suka bi bayansu suka tafi gidan Uncle Hashim.
[3/2, 9:09 AM] OumŠahira: =ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ
   *RAYUWAR MADINA* =Ĝ§Ü
=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
     _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>ĜŬŬ*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* <Ĝß

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS=ĜŞÜ)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

          *P.W.A
'ŝ*





         *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ´an uwana Mata waWanda suka fuskanci u™uban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ™arshen wahalar rayuwa._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 270
2gb. 500
3gb. 800
4gb. 1100
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.







*KIRA ZUWA GA MARUBUTA*

_A matsayinka na Wan Nigeria bai kamata kayi murnar Independence ba, bai kuma kamata kabar wani yayi ba!_
  _dalilina kamarhaka_
_a satin daya_ _gabata an sace Walubai a jahar Zamfara, an kashe wasu a sakkoto, An harbe wasu a cikin Jos, a kaduna kuwa an tare jirgin ™asa an kwashe mutanen cikinsa wanda har yau ba'a san inda sukeba!_
    _kai yanzu ko tafiye tafiyen da akeyi da an daina saboda irin wannan matsalolin!_
_Kuma duk haka yana Faruwa ne saboda sakacinmu na mutanan AREWA, ko har kun manta da ´an matan da aka sace a cikin jahar Barno state a shekarar 2014 su Wari biyu da sabai'n da shida?!, ´an matan ´an matan chibok, toh haryanzu ba'a san inda saura suke ba..._
_Idan mukace AREWA muna magana ne da ´a´an cikinta waWanda suka sami Waukaka koya take kama daga ³an social media,  ´an film, mawak'a, masu shirin barkwanci, tare da_ _*Marubutan mu*, mu taso mu buWe baki muke_ _magantuwa,  muyi amfani da wannan damar ta social media,  kuna ganin celebrity Win nan na kudu daya mutu zargi suke akan kashe shi akayi ba tabbatarwa ba, amma ji yadda abun ke yawo a ™asa baki Waya!_
  _mu kuma ´a´a mata ake kwasa ake shiga jeji dasu, banda tsadar rayuwa, da azaba da ™uncin da muke ciki, kidnapping,  kwace,  Haure, ana kashe mana ´an uwan mu Waruruwa batare da munce komaiba!_
   _shin da mukayi shirun gajiya_ _sukayi suka daina ko kuwa abin ta'azzara yayi?_
_a matsayinki/ka na *Marubuciya, Marubuci* ´an AREWA ga dama tasamu, masu novel na kuWi dama free, masu Waukakar cikin mu dama sabbin tasowa, magana ake aji murya iri Waya gabaWaya a social media a yau first October dan already no more Independence, Dan girman Allah kar mu raina abin da zamuyi, koda ba™ya update na novel kiyi koda shot writing akan matsalar dake faruwa!_
  _kar mutsaya sai abi yazo kan ™anwarka ™anina babana ko mamana, Kaduna Zamfara Barno Kano da dukkan arewa muWin duka abu Wayane, dan Allah marubata mufito ™wanmu da ™war™wata mutaya ´an uwanmu ´an_ _social media isar da sa™o,  tunda mu baiwar rubutu_ _ubangiji ya bamu muyi amfani da ita wajan yin g´ara._
_ubangiji yayi mana Jagora ya Allah ka sakawa duk wacce tayi ™o™arin tallafawa da gidan Aljannatul-Firdausi._



















______________ *EPISODE 43*
_____A ranan gaba Waya suka taho Zaria, su Baban sasa suka wuce ™auyen su har Yaya Yunus da ya bi bayansu,
Sun so su tafi da Madina, amma Umma furr tace, "basu isa ba, yanda suka sallamata haka ta bar wurin su har abada, Madina babu inda zata jirga a wurinta."
Don haka gida suka wuce da ita a Motan Mashkur da ya tafi dasu,
While Ansar kuwa kai tsaye Kaduna ya wuce tunda zuwa gobe zai koma Riyadh, bazai iya zama har nan da three weeks ba since yana da aikin yi, zai tafi sai lokacin koma wa court before ya dawo

Yaya Haula ma biyo su Umma tayi har gida don ta ™i komawa ™auyensu, tana manne da Madina har suka isa gida dukkansu sai kuka suke yi har lokacin, Hajiya Ummee tayi rarrashin har ta gaji, shi kansa Mashkur ya rarrashe su amma sun gaza yin shiru, haWa kai suka yi inda Madinan ta rungume Wanta tana ta sharSan kuka, dayake an je dashi yana hannun Umma,
Tunda ta kalli Yaron kukanta ke ™aruwa ta gaza yin shiru, wani irin kuka take yi mai tsuma rai, shi kansa Yaron sabida yanda ya sha matsa a jikinta dole ya fashe da kukan kamar ya san mai ke faruwa,
Wannan ne yasa tayi saurin shanye kukan nata tana Wago yaron tana kallonsa, sai dai hawaye na zuba a idanunta kuma ta kasa rarrashinsa, har sai da Yaya Haula ta amshe shi tana jijjiga shi sannan yayi shiru, tana ganin yayi shiru ta sake amsar Wanta ta rungume tana ta zubar da hawaye, babu wanda ya sake cewa komai har suka kai gida,
Dayake dare yayi shiyasa su Hajiya Ummee suka wuce gida bayan sun sauke su,
Baba ya zo ya buWe musu kofa tunda ba dashi aka je ba, dole ya zauna a gida tare da ´an biyu, lokacin ma har sun yi barci don haka basu san da dawowan su Madina ba,
Umma ta amshi Yaron ta goya shi sannan tace, "su shiga Waki su kwanta su huta tunda dare yayi sosai."
A lokacin kusan karfe sha biyu ne, ga Khalifan sai tsala ihu yake yi tunda suka dawo, shiyasa ta amshe shi sannan ta basu umarnin, "su kwanta kuma su dena kukan da suke yi,"
Šakin Umman suka shiga inda su Hassana suke kwance, har lokacin Madina bata dena zubar da hawaye ba, don har yanzu gani take yi abun kamar a mafarki, bata taSa tunanin zata fito ta ™ara ganin ´an uwanta ba, ™arshe sun kasa runtsa wa ita da Yaya Haula don manne wa suka yi Yaya Haulan tana ta rarrashinta, sabida tuna baya da suka yi na rayuwarsu,
Sai gabanin asuba sannan suka samu barci

Da sassafe Umma ta tashe ta ta gasa mata jiki da ruwa mai zafi,
Lokacin har ta gama musu karin kumallo ta zuba musu tace, "su karya."
Su Hassana sai murna suke yi tunda suka ga ´ar uwansu ta dawo, su kansu sun kasa jirgawa a wurinta ko zuwa makarantar sun ™i

Wurin ™arfe tara da rabi sai ga shi an aiko breakfast daga gidan Hajiya, Umma ta amsa tayi godiya sosai sannan ta buWe ta ga mene ne a ciki, ™wai ne da arish cikin cooler, don haka ta zuba wa Madinan tace, "ta cinye."
Madina ta girgiza kanta jiki a sanyaye tace, "Umma na ™oshi."

"Ki ci nace, Wauka ki ci ban son gardama, ke ma Hussaina kawo naku plate Win in zuba muku."
Amsa tayi ta zuba musu sannan ta tura musu, ta Wibi na Baba ta fita dashi zuwa Wakinsa,
A lokacin dayake Yaya Haula ta tafi yin wanka ne,
Sai da ta dawo sannan Umma tace, "ta zuba in zata ™ara ta ci."
Ta amsa mata da to tana wuce wa wurin kayanta zata mayar a jikinta, tunda bata zo da wani kayan ba, ko Yaranta a gida ta bar su

Tun kafin Madina ta gama cin abincin, Umma ta Wauko Khalifa wanda ya tashi daga barci, ta mi™a mata tace, "ba shi abincin sa."
Hannu ta sanya ta amshe sa tana kallon yaron gunun tausayi, yadda itama ta zama Abar tausayi haka shima ya zama, don duk Wan ™iban nan da aka haife shi dashi a yanzu duk ya zagwanye, sabida rashin Mahaifiyarsa kusa; da kuma sauyin abinci da ya samu, wanda ada ya saba da shan nonon mahaifiyarsa, rana tsaka aka tuge shi, shiyasa a wannan lokacin tunda ya ji wannan garWin wani irin zu™a ya fara yi yana wani ajiyar zuciya kamar zai shiWe yana ta haWama, Madina ta kasa Wago kanta tunda ta kafa mishi ido, kunya da kuma kuka ne ya taho mata, tana jin su Umma da Yaya Haula suna maganar yanda yake shan nonon, amma ta kasa furta komai,
Har sai da shi da kansa ya ture sannan ta ™yale shi,
Da sauri Hussaina ta amshe shi ta goya shi tana jijjiga shi, wanda ita Madinan ta bata ne kawai don baza ta iya hana ta ba, sai ta ja gefe tayi shiru kanta a ™asa tana faman share hawaye

Umma tace, "kibar kukan nan kin ji ko? Godiya yakamata ki yi wa Allah da ya nuna mana wannan ranan har muka ga fitan ki, ba na fatan irin wannan bak'ar ranan ta sake faruwa da ke Madina."
Shiru ta Wan yi sabida wani irin ™unci da ya tokare mata wuyanta, yanda take jin kukan Madinan na shiga cikin zuciyarta yana sukan ta, ji take yi kamar da tana da hali ta sauya mata ™addaranta, komai a kanta yake faruwa, tunda ta haife ta bata huta ba, Madina ta ga rayuwa, har tsoro da fargaban abun da zai faru a gaba take yi, sai yaushe ne yarinyar nan zata samu farin ciki kamar kowa? Ita ce kawai rayuwarta take tafiyan mata ba dai-dai ba.
Guntun hawayen da ya zubo mata ta share tare da sake kallon Madinan da ta haWa kai da gwiwa, tace mata, "addu'a shi ne mafita a gare mu, Insha Allahu Allah zai yaye mana wannan damuwar tamu, ban son in sake ganin kina irin wannan kukan kar ki ja wa kanki wani ciwon. Haula yaushe za ki tafi ne?"
Ta mayar da akalar tambayar ta a kan Yaya Haulan

"Umma ba yau ba, gaskiya bazan iya tafiya in bar Madina a wannan halin ba, zan ™ara kwana sai in tafi gobe."

"A'a bazai yiwu ba, kin baro yara a gida har da ™aramar yarinya kuma ki ce za ki sake kwana? Zuwa anjima za ki tafi tunda komai ya wuce ta samu dawowa, kuma Insha Allahu Allah zai bamu nasara a gaba komai zai zo karshe."
Dayake basu saba mata musu ba shiyasa Haulan ta ha™ura da kwanan kamar yanda ta so yi, duk da ba a son ranta bane

Wurin ™arfe biyu sai ga Hajiya Ummee da Mashkur sun zo gidan,
A lokacin ita Madinan ta samu barci, har Mashkur ya tafi bata farka ba,
Sai dai ta tashi ta ga Hajiya tunda ita ta zauna har yamma sannan ta wuce.***

A kwana biyu da dawowan Madina har ta Wan warware, tunda tana samun kulawa daga mutanen gidan, sai dai ta ci ta kwanta ta huta ko tsinke Umma ba ta barinta ta Wauka, duk da soyayyar da take yi wa Wanta da son manna shi a jikinta, amma ba ta samun dama, don yana shan nono Umma take dauke shi ta goya shi, idan akwai su Hassana a gidan kuma ta basu shi su fita dashi yawo,
Shiyasa bata da aikin yi sai cin abinci da kwanciya, ko damar samun yin tunani Umma bata barin ta tayi, takance, "tayi ta addu'a domin yanzu shi ne abun yin su, idan har basu mi™e tsaye wurin yin addu'a ba wata rana makamancin irin hakan zai iya faruwa, tun farko sun yi kuskure da suka bar addu'a har wani mushiriki ya ci galaba a kansu, wanda sun tabbatar da cewa Alh. Badamasi yayi amfani da bin Malamai wajen samun damar su a karo na biyu."
Wannan ne yasa Madinan take ™o™arin kamanta yin addu'a duk idan tana zaune bata yin komai, duk da wasu abubuwan duk ta manta amma tana zama tayi zikiri musamman in tayi sallah, sai yazamana Umma ta saka su Hassana suna koya mata wasu abubuwan tunda su suna zuwa islamiyya karatun su ba Waya ba

Tun ranan da Mashkur ya biyo Hajiya bai sake dawowa ba kasancewar yana da aiki ba ya zama,
Sai Hajiyan ne take zuwa jefi-jefi duba su har wani lokacin takance, "Madinan ta zo gidanta su zauna."
Dayake sau biyu ta taSa zuwa kuma da yamma ne basu taSa cin karo da Mashkur ba, kuma tare da su Hassana suke zuwa tunda Hajiyan da kanta take aiko mai gadinta ya kira ta,
Umma kuma bata hana ta ba tunda Hajiya ta wuce komai a wurin ta,
A sati Waya da dawowansu ma Umma ta koma bakin aikinta, a ranan sai suka fita da safe ita da Madinan

Time Win su Hajiya suna zaune suna breakfast suka shigo,
Hajiya ta ji daWin ganinsu tace, "ah ah Asiya, kin dawo ne kuma?"

"Wlh kuwa Hajiya na gaji da zama nace yau bari in le™o tunda Madinan yanzu ta sake jikinta, zaman babu amfani in bar ki kina aiki da kanki."

Mashkur da ke goge bakinsa da tissue, ya Wago yana dubansu wanda tuni ya sauke idanunsa a kan Madina wacce ta du™ar da kanta kamar yadda ta saba, a kullum haka take tamkar za a sace ta tayi ta ™an™ame jiki kamar mai jin sanyi, shi kuwa hakan yana matu™ar burge shi, tsoronta, sexy eyes Win ta masu ban sha'awa wanda suke nuna ainihin rauninta, idan ya kalli Wan tsukakken face Win ta ba ™aramin shigar da shi wani yanayi yake yi ba, wanda a yanzu ma saurin janye idanunsa yayi a kanta sabida jin muryan Umman tana masa magana, sai ya wayance wurin kau da kansa yana gaishe ta cike da girmamawa, ta amsa shi cikin fara'a tana tambayarsa aikin nasa?

Yace, "alhamdulillah Umma, yanzu ma zan tafi."
Sai ya dubi Madina da har yanzu take a tsaye tana dun™ule da hannayenta, yace, "Madina, kawo Khalifan mu gaisa mana, ko rowansa kike min?"
Saurin Wago kanta tayi ta kallesa, sai tayi saurin girgiza masa kanta tana kuma tahowa inda yake, cikin sanyin murya ta soma gaishe da Hajiya Ummee

Hajiya Ummee ta amsa tana cewa, "zauna mana in kin kwance sa, sai muyi breakfast din tare. Asiya kema ki zo ga karin kumallo."

"A'a Hajiya mun yi kari kafin mu fito, bari dai in je in fara miki aikin zai fi."
Sai ta wuce zuwa Wakin Hajiyan batare da ta jira jin ta bakin ta ba

Wanda shi Mashkur tuni ya amsa yaron yana dubansa gunun sha'awa, idan ya kalli Yaron sak fuskar Madina yake gani shiyasa yake matu™ar son yaron, da murmushi a kan fuskarsa yake cewa, "Hajiya, wannan Yaron wlh kullum kamannin sa ™ara fitowa yake yi da Madina, kowa ya kalle sa ya san yaronta ne, amma gaskiya Ni za ki ba Yaron nan don bazan bar ki dashi ba, yana soma tafiya zan amshe shi, Allah yasa za ki bani shi kanwata?"

Murmushi ne ya suSuce mata sai dai tuni ta sake du™ar da kanta ™asa, wani irin girma da ™imansa take gani tamkar mahaifi a gare ta, Mashkur ya wuce komai a gare ta, idan ta tuna irin taimakon da yayi mata sai ta ji hawaye sun soma cika mata idanu zuciyarta na jin wani irin ™aunarsa na musamman, shi tamkar jigo ne a gare ta ya taimaka mata wanda har yau ta kasa samun damar da zata sake mishi godiya,
Tana jin sanda Hajiya take mishi tsiyan, "shima yayi zuciya yayi auren idan ba haka ba wlh sadakan su zata bayar, kuma wannan Yaron ai na riga ka, da zaran ya soma tafiya nan gidan zai dawo don Ni zan amshe shi.
Madina maza ki haWa tean ki sha mana kin zauna kamar wata ba™uwa, ba na jin daWin ganin ki a haka har yanzu kin kasa sakin jikinki damu; bayan mun zama Waya, Ni kike jin kunya ko Yayanki Mashkur iyee? Maza haWa tea ki sha kar muyi faWa. Ni wlh ba na son wannan ™unbiya-™unbiyan naki."

Mashkur kuwa shiru yayi yana kallon yanda Madinan take haWa tean, yana jin wani irin soyayyarta na ™ara shigansa, sai murmushi yake yi a fakaice yana yi wa Khalifa wasa, sai yazamana ma ganinta ne yasa ya kasa tafiya aikin da wuri don ya ji daWin zaman da tayi kusa dashi tare da Hajiya, don ita ta zaunar da ita ta hana ta ko jirgawa, shima sai ya fake da ri™e Khalifa ya kasa tashi suna ta hira da Hajiyan, don ita Madina ba ta cewa komai ko kanta ba ta Wagowa,
Sai daga baya ne ya bata Yaron yana musu sallama ya fice a motarsa zuwa wurin aiki

Bayan Umma ta gama duk aiyukan ta suka wuce gida da abincin a cooler,
Lokacin da suka je bakin ™ofan gidansu suka tarar da wata bak'ar mota a fake sabuwa dal, sai dai ba sa ganin na ciki tunda bak'a™en glasai ne,
Wuce wa suka yi suka rufo ™ofan su,
Jima wa kaWan suka soma jin bugun ™ofa,
Sai Umman tace ma Madinan, "ta je ta duba ta ga ko wane ne?"
Madina ta tashi ta fita bayan ta mayar da hijabin ta jikinta,
Tana buWe ™ofan suka yi ido huWu da Yaya Yunus tsaye a gabanta,
Wani irin buga wa da ™irjinta yayi har sai da ya jiyo sautin da kuma Wagawan ™irjinta,
Take ta sake ™ofan da nufin juyawa ta shige cikin gidan,
Ko kafin tayi taku biyu har ya saka hannu ya cafko nata ya ri™e ta gam yana furta, "ina kuma za ki je? Ko ba ki yi farin cikin ganina bane?".
[3/2, 9:11 AM] OumŠahira: =ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ
    *RAYUWAR MADINA* =Ĝ§Ü
=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
           _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>ĜŬŬ*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* <Ĝß

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS=ĜŞÜ)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A
'ŝ*






            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ´an uwana Mata waWanda suka fuskanci u™uban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace

Please Login or Register in order to submit comment