Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwanto goyon Ihsan ta mi™a mata, yarinyar sai Barci take yi tunda bata da aiki sai barci

Umma bayan ta amshe ta ta Waurata a jikinta tana kallon fuskarta, tare da kai hannu tana cire mata kwantsan da ke idanunta Waya; kana ta kalli Yaya Haula tana cewa, "kina mata amfani da maganin dana ba ki?"

"Eh Umma har ma ya ™are, jikin nata da sau™i yanzu ai." Ta bata amsa tana tura ™osan a bakinta tare da korawa da kokon; tunda dama ba kari mai kyau tayi ba, Mijinta shima be dashi sai ya fita yake nemo wa, kullum a cikin Wame-Wame suke ga shi ita tana shayarwa, shiyasa yanzu Win ta shanye kokan tass tana siWe baki

Sannan Umma ta kalle ta tana cewa, "ina jinki meke faruwa ne? Hankalina ya kasa kwanciya duk yanda aka yi ba lafiya ba?"

Ajiyan zuciya Yaya Haulan ta saki, kana damuwarta ta dawo sabo, a nan ta sanar da Umman duk abun da ke faruwa

Shiru Umma tayi sabida yanda maganar ta bige ta ainun; yayinda idan hankalin ta yayi dubu to ya tashi a wannan lokacin

"Ni Umma ba wai yin kaciyar bane yake damu na, Madina yarinya ce duk su Binta sun girme ta, ita ce ™arama memakon su barta sai wata shekaran amma sun CE da ita za'a yi, Umma ki duba yanda na sha wahala a lokacin da aka yi min; idan har aka yiwa Madina yanzu bamu san wani hali zata shiga ba, don Allah Umma ki je ki ro™e su a dakata ko zuwa nan gaba sai ayi mata, Madina yarinya ce."

Umma tace, "to Haula ya zan yi wannan abun ya fi ™arfi na, amma ban ji daWi ba; ba ki ji yadda zuciyata take zafi ba hankalina duk ya tashi, wannan al'adan kwata-kwata be da tsari, da ace ina da fawan da zan Wauko Wiyata ta dawo hannu na da na jima da yi tunda na san dole zasu yi mata wannan kaciyar, sai dai na san baza su taSa yarda ba, insha Allahu Allah bazai basu dama ba dole ne zan je in Yi musu magana tunda ina da ha™™i a kanta." Sai ta kalli su Hassana da ke zaune suna ta shan kokan su tace, "ku tashi idan kun gama ku je gidan Asabe ku zauna, idan lokacin Islamiyar ku tayi sai ku wuce; Ni zan tafi anguwa."

"To Umma." Suka amsa mata suna mi™ewa tunda sun gama abun da suke yi

Ita kuma sai ta mi™a wa Haula Ihsan Win ta mi™e tana cewa, "bari ta ™arisa aikin ta." Da haka ta fice daga Wakin

Itama Haulan mi™ewa tayi ta shimfiWa Ihsan Win sannan ta fita ta taya ta aikin, dama shara ne kawai da wanke-wanke, suna gamawa Umman ta saka kaya da hijabi suka fito gidan, sai a waya ta sanar da Mijin nata, kuma bae hana ta ba sai fatan alkhairi da yayi mata. Kai tsaye gidan da take aiki suka nufa sabida tana son ta faWa musu, "baza ta samu shigowa yau ba." kar Matar ta ji ta shiru

Suna shiga kuwa suka cid da tsohuwar Matar a katafaren falon ta, duk da ta manyanta sosai amma kana kallon ta zaka san ´ar kwalliya ce, domin har yanzu gayu take yi babu ruwanta da tsufan da tayi, hannayen ta dukka sun sha jan lalli da aka yi mata hannu da ™afa ya Wauki farar fatanta sosai, sai sar™a da awarwaro da ta zuba su na gwal sai walwali suke yi, duk da fuskarta babu kwalliya amma ta sha kwalli da Powder tayi kyau ainun, tana zaune a kan sofa tana kallon labarai a t.v, ta amsa musu sallaman cikin fara'an ta tana cewa, "yanzu nake tunanin lafiya ban ji ki ba? Shiyasa nake tunanin in aika a duba min ke."

Murmushi Umma tayi tana zama a ™asa tare da cewa, "wlh kuwa Hajiya, ba™uwa nayi ´ata ta zo daga ™auye, shi ne zamu je can saboda wata matsala, abun da yasa ban zo ba kenan kuma kar in tafi ban sanar miki ba shi ne na shigo. Ina kwana Hajiyam?" Ta ™are maganar tana gaishe ta

"Lafiya lau, wlh babu komai, nima fita zan yi ai."

Haula wacce ta zu™una itama a ™asa ta gaishe ta cikin girmamawa

Hajiya Ummee ta amsa mata cike da fara'a tana cewa, "yanzu Asiya wannan yarinyar ´arki ce?"

"Eh wlh Hajiya, ita ce babban ´ata sai ™anwarta."

"Masha Allah sannun ki, ya sunan ki?" Hajiya Ummee ta tambaya cikin fara'a tana kallon Haulan

Itama Murmushi tayi cikin girmamawa tace, "suna na Haula."

"Masha Allah! suna mai daWi." Sai kuma ta kalli Umman tana cewa, "yanzu ki je kichen ki haWo muku Breakfast sai ku ci kafin ku tafi."

"Wlh a'a Hajiya sauri muke yi, kuma mun ci abinci yanzu kafin mu fito."

A lokacin ne Ihsan ta tashi ta soma kuka

Hakan yasa cike da mamaki Hajiyan tace, "wai da goyo ne a bayan ta dama?"

"Eh, Wiyarta ce." Umma ta bata amsa

"Ikon Allah! Šiyarta?" Inji Hajiyan tana sake cika da mamaki yayinda take kallon Haulan, "yanzu Asiya kina nufin yarinyar nan tana da aure ne?"

Murmushi Umma tayi tace, "eh Hajiya, ga ta nan har da ´arta takwarata."

Hajiya Ummee ta cika da al'ajabin da ya kasa Soyuwa a kan kyakykyawar fauskarta, sai ta cewa Haulan, "ta sauko yarinyar ta bata." Hakan yasa ta sauko ta ta mi™a mata, sosai yarinyar ta bata sha'awa tana faWin, "Masha Allah yarinya tubarakalla. Amma taya ya zaku yiwa yarinya kamar wannan aure Asiya? Wannan ai ganganci ne; kamar wannan fa?" Ta sake maganar tana nuna Haula da a yanzu ta koma ta zauna tana kallon Hajiyan cike da burgewa

Ita dai Umma murmushi kawai take yi bata ce komai ba

A lokacin ne wani kyakykyawar farin saurayi yayi sallama ya shigo cikin falon; yana ri™e da farar riga lab coat a hannun sa, yayinda idanuwansa suke sanye a cikin farin medical glass da ya haskaka mishi idanun suka ™ara yin kyau ainun, jikinsa sanye da ™ananan kaya riga da wando sun mishi kyau, kansa kuma babu hula sai kwantaccen gashin kansa me haWe da yalwataccen sajen sa tare da Wan guntun gemun sa, kana kallon sa zaka ga kamalan sa da kwarjinin sa a fuska

Duk amsa mishi sallaman suka yi, inda Hajiya Ummee take cewa, "Ah ah! Mashkur ka dawo ne kuma?"

Sai da ya samu wuri ya zauna kafin ya bata amsa yana cewa, "eh. Already na gama abun da na je yi." Daga nan sai ya mayar da hankalinsa a kan Umma yana gaishe ta

Ta amsa a cikin sakin fuska tana tambayar shi aikin nashi?

Yace, "alhmadulillah."

Itama Haula gaishe shi tayi

Sai ya Wago yana kallonta, kana ya amsa ta a hankali yana Wauke kai a kanta; ya mayar a kan yarinyar da ke hannun Hajiya Ummee, "yarinyar wace ce?" Ya tambaya yana ci gaba da tsira mata idanu

"Yarinyar Haula ce Wiyar Asiya, ga ta nan zaune ai."

Hakan ne yasa ya sake Waga kai yana kallon Haulan; yayinda mamaki kwance a kan kamilalliyar fuskarsa na jin cewa wannan figaggiyar yarinyar; tsamurarriya; ita ce Maman jaririyar nan, ikon Allah! domin abin mamaki ya ba shi, saboda gani yake yi ai baza ta wuce shekaru 14 ba amma har da Wiya? sai dai bai ce komai ba saboda shi ba mai yawan magana bane

Inda ita Hajiyan tace, "Mashkur akwai kuWi a hannun ka; ka bani zan ba wa Asiya ne?"

"Eh akwai." Ya furta yana saka hannu cikin aljihun wandon sa tare da zaro kuWin, bai ma san ko nawa bane ya mi™a mata

Itama sai ta amsa ta mi™awa Umma gaba Waya tana cewa, "to ga shi sai ku rage kuWin mota, sauran sai ki ba wa Haula, Allah ya kiyaye hanya, nima fita zan yi kuma zamu kai yamma kafin mu dawo, sai Allah ya kaimu gobe sai ki zo; yau dai ki huta da aikin nan."

Sosai Umma tayi godiya, daga ita har Haula, sannan Hajiyan ta mi™a mata Ihsan Win ta goya ta, daga nan suka yi musu sallama suka fice.



Kai tsaye keke napep suka yi drop ya nufi da su ™auyen. Bayan sun kai suka wuce babban gidan su, koda suka shiga Yara suna hangen Umma suka soma mata Oyoyo suna cewa, "ga Umman su Madina, ga Umman su Madina."

A lokacin ina cikin Wakin mu naji abun da suke faWa, ai da gudu na fito domin gasgata abun da suke faWa, ilai kuwa Ummata ne tare da Yaya Haula da suka shigo sasan a yanzu, da gudu na nufe ta ina kiran sunan ta, na rungume ta cikin tsantsan murna da farin cikin ganin ta; domin ba ™aramin murna ne ya kama Ni ba sabida rabo na da ita tun bikin Yaya Haula

Murmushi ita kuma take yi tana shafa min kai tare da cewa, "kar ki ka dani mana Madina."

Ni kuwa sai dariya nake yi murna ta kasa Soyuwa a kan fuskata, nace, "Umma sannu da zuwa."

"Yauwa Madina." Umman ta amsa tana kuma mayar da hankalinta a kan Yaran da suke mata sannu, su ma tana amsa musu

A lokacin ne Inna Lami ta fito daga Waki tana Waura Wankwali a kanta; tare da cewa, "wa nake ji kamar Asiya a gidan namu?"

"Ni ce wlh Yaya. Ina wuni?" Umma tafaWa cikin yalwata fuskarta da fara'a sosai

"Lafiya lau, maraba da zuwa, ke Madina Wauko mata tabarma mana kin barta a tsaye."

Da gudu na shiga Wakin Inna Lamin na Wauko tabarma, ta amsa ta shimfiWa mata sannan Umma ta zauna itama ta zauna, a lokacin sauran Matan Baban Sasa suka fito su ma suna cewa, "Ah ah Asiya ce a gidann namu?"

"Wlh Ni ce."

Daga haka aka soma gaisawa cikin mutunta juna tunda an yi zaman lafiya tare, aka kawo wa Umma ruwa ta sha. Sun Wan taSa hira kaWan ana ta raha daga nan ne ta mi™e ta wuce sauran sasan suma aka gaisa, sai ta wuce ita kaWai sashin Baban Sasa, ta same shi yana kwance a falon shi, ya kishingiWa yana fifita kasancewar babu wuta, ta shiga da sallama ya amsa mata yana mi™ewa zaune tare da kallon ta

"Asiya ce?"

"Eh Yaya." Ta furta tana zama a ™asan tare da gaishe shi cikin girmamawa

Ya amsa ta shima cikin kulawa yana tambayar ta iyalan nata?

"Alhamdulillah suna nan lafiya."

"To Haulatu har ta sanar miki da sa™on namu kenan?"

"Eh yau ta je gidana ta sanar min, shiyasa na taho sabida in ro™i alfarma."

Gyara zamansa yayi yana mayar da idanunsa a kanta tare da cewa, "to fa! Wanne alfarma kenan Asiya?"

Shiru ta Wan yi ita kuma, kana kuma ta buWe baki tare da cewa, "a kan maganar Madina ce da za'a yiwa kaciyar nan Yaya, Madina yarinya ce bata kai shekarun da ake yiwa sauran ba, shiyasa nace idan da hali a barta zuwa wata shekaran kamar yanda lokacin ne ta cika shekarun da za'a yi mata, don Allah a duba maganata Yaya."

Šan jimm. Baban Sasa yayi kana kuma yace, "mu ma mun yi wannan tunanin Asiya tun kafin kiyi, amma abun lura a nan dole ne fa za'a yiwa yarinyar nan al'adan nan tunda babu wanda zai tsallake ta, mu kuma muna ganin sau™in hakan ne shiyasa muka yanke wannan shawaran, ba ki fi mu sanin me muke yi ba babu abun da zai samu Madina don wai bata kai shekarun sauran ba, ko a baya da muke gudanar da al'adar nan daga shekaru 5 ne zuwa 6, amma yanzu ita takai shekaru goma a lissafina, kinga kuwa tayi girman da itama za'a iya mata, duk a gidan nan babu kuma wanıÿÿÿ‚ƒ„…†‡ˆ‰Š‹Œ‘’“”•–—˜™š›œŸ ¡¢£¤¥¦§¨©ª«¬­®¯°±²³´µ¶·¸¹º»¼½¾¿ÀÁÂÃÄÅÆÇÈÉÊËÌÍÎÏĞÑÒÓÔÕÖ×ØÙÚÛÜİŞßàáâãäåæçèéêëìíîïğñòóôõö÷øùúûüışÿi sa'anta da za'a haWa su wata shekaran ayi musu, sauran duk Yara ne, to, a ganin mu da mu sake jira wata shekaran ayi mata da wasu tsirarun ´an ™auyen gwara a haWa su gaba Waya ayi musu yanzu; tunda mun duba duk basu da yawa, Ni abun da yasa nace a sanar miki sabida ki sani ne kar a shiga ha™™in ki a matsayin ki na Uwarta, amma ba shawaran ki muke so ba."

Umma da ke faman share hawaye tun soma maganar sa, kasa Wagowa tayi da kanta sai da yace mata, "zata iya tafiya tunda shi ya gama magana." Sai ta Wago tana ro™on shi cikin magiya tana sake jaddada mishi, "Madina yarinya ce a barta ta sake girma, tana gudun abun da zai biyo baya kar su kashe mata yarinya."

Ran Baban Sasa ya soma Saci, shiyasa ya buWe baki a zafafe yace, "ke Asiya ba ma son maganar banza da hofi a nan, ita kanta farau ne da za ki ce wani abun zai same ta? Tun yaushe ake wannan al'adar babu wani abu da ya taSa samun jama'a sai a kanta? Idan ba'a yi mata ba taya zata cika Mace a martaba ta a duniya? Ba na son zancen banza tun kafin raina ya Saci muyi rabuwar Satacciya ki Sace min a gaba na." Sai ya ja dogon tsaki yana mayar da jiki ya sake kishingiWa tare da kuma mitan cewa, "idan ba shirme ba; Ni ne za ki zo gabana kina gaya min abun da yakamata? ita ´ar uwanta da aka yi mata uban me ya same ta? Al'adan mu ne babu wanda ya isa ya hana ta."

Umma mi™ewa tayi itama ranta a Sace, sai dai ta kasa tsayar da hawayen nata sai kwaranya suke yi, sai da ta fita sannan ta share hawayen gudun kar a gani, amma ana kallonta za'a gane tayi kuka, baza ta iya tsayawa tana kallo a yiwa Wiyarta kaciya ba, kamar Madina, wannan ai zalunci ne, ko a sanda aka yiwa Haula bata da yanda zata yi ne, bata ma san an yi ba sai daga baya, sannan bata manta wahalar da Haula ta sha ba a kan wannan kaciyar, Allah ne ya ta™aita wahala sai da tayi ta zuwar mata da magani tana bata da™yar ta samu sau™i, domin su sun ™i kaita asibiti a duba ta sai ji™e-ji™e da ake bata, kuma sun hana ta ta Wauke ta ta kaita tunda basu yarda da asibiti ba sai magungunan gargajiya, dole ta ri™a zuwa da maganin a Soye na asibiti tana bata har aka samu ta samu sau™i, sai ga shi yanzu za'a kuma a kan Madina wacce bata kai shekarun su ba ma, wannan mugunta har ina? Baza ta iya tsayawa ta gani ba. Shiyasa tana shiga sashin su Inna Lami tace musu, "ita zata tafi."

"Ah ah baza ki bari ayi musu a gaban ki bane? Naji an ce Mutumin ne bai zo ba har yanzu." Cewar Inna Asabe da ta fito tsulum daga Waki jin abun da Umma take cewa

"A'a bazan zauna ba, tunda nayi abun da ya kawo Ni dole zan tafi, su kuma Allah ya basu lafiya Allah yasa ayi a Sa'a."

Tuni hawaye sun soma wanke min fuska saboda jin abun da Umma take faWa, da sauri na mi™e daga kusa da Yaya Haula ina dire mata Wiyarta, sai na nufi wajen da Umma ke tsaye na rungume ta ina me fashewa da kuka, cikin kukan nake cewa, "Umma kar ki tafi ki bar Ni don Allah, ba na so ayi min don Allah ki tafi dani."

Wasu sabbin hawayen ne suka soma sintiri a kan fuskar Umma sabida tsantsan tausayi na, da sauri ta sa hannu ta share tana me kamo fuskata tare da cewa, "kiyi ha™uri Madina Allah shi ne zai kare ki, babu abin da zai faru da ke sai alkhairi, Ni zan tafi gida kinji?"

Kuka sosai nake yi a yanzu, ina cewa, "kar ta tafi." Na ™an™ame ta sosai a jikina ina kuka har da su majinu, kuma na hana ta tafiya

Dole Yaya Haula ce ta taso itama tana kukan ta kama Ni, amma duk yadda ta so ta SanSare Ni ta kasa

Su Inna Lami kuwa sun samu abun yi sai faWa suke yi amma ko jin su ba na yi, Ni kuka na da tashin hankali na ya ishe Ni, ™arshe Yayan mu Shamsu aka kira tunda shi ne a sasan, shi ya zo ya SanSare Ni ya shiga dani Waki, ita kuma Umma tayi musu sallama ta fice ba tare da ta jira cewar su ba, haka Yaya Haula ta bi bayan ta domin suyi sallama sai share hawaye take yi

Mutanen gida kowa taSe baki yayi ya ci gaba da aikin gaban shi domin su a wurin su ba tausayi na basu ba, su ma idan da hali baza su so a yiwa Yaran su ba amma an fi ™arfin su basu da yanda zasu yi, duk yaran su na gidan aure sai da aka yi musu ba yau suka saba shiga ba™in ciki irin wannan ba, dole su danne kayan su tunda ko sun nuna a fili ™arshe a kansu zai ™are

Ni kuwa da™yar Yaya Shamsu ya natsar da Ni sai da ya saka min hannu, tare da daka min tsawa yace, "idan ya sake jin kuka na zan ga abun da zai yi min."

Dole na gimtse baki har da ri™ewa da hannu ina ta shashshe™a, yayinda hawaye ke gudun tsere a idanu na amma babu halin fitar da kukana waje, idan ma na fitar abun da ya same Ni ni naso domin duk gidan nan babu mugu kamar Yaya Shamsu, shi a wurin shi ya kama yarinya yayi mata shegen duka na fitan hankali abu ne mae sau™i, yawancin ´an gidan namu haka suke sam-sam ba sa wasa Mazan. Ina nan a zaune aka soma kiran mu wai Mutumin da zai mana kaciyar ya iso, nan fa kuka na ya dawo sabo, ™in fita nayi sai da aka zo aka Wauke Ni, haka nake kuka ina bori baza ayi min ba, a lokacin da aka kai Ni zauren gidanmu har an yiwa Fatimah da Fa'iza sai tsandara ihu suke yi, saura su Luba da su ma kukan kawai suke yi, gaba Waya iyalan gidan mu Maza suna wajen, su Baffa da su Yaya Shamsu duk su ne masu kama mu

Nima fa sai na ruWe kuka na ya ™aru, amma sai aka ce a Waure min ™afafu da hannaye tunda bazan tsaya ba sai bori nake yi. Hannayena suka soma Waurewa ta baya sai su ma ™afafuna kamar wata akuya, aka rufe min idanu ya zamana ba na ganin komai sai kukana da na kasa denawa, dole shima aka ™ulle min baki saboda yanda nake yanka kuka kamar raina zai fita, a lokacin ne aka fito da bakin al'aurata da aka cire min skirt Win jiki na. Bayan wasu mintoci, sai na ji raWaWi, na yi kururuwa amma ba mai ji na, na yi ™o™arin fincike ™afata amma sai na ji wani ™arfe ya rirri™e ™afafuna, babu wani abun rage raWaWi sai wani ganye, ina jin sanda aka manna min shi a jiki na, daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba sabida azaban da yayi min yawa, a tunani na raina ya gama ficewa a cikin jikina.
[1/30, 5:51 PM] OumŠahira: =ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ
*RAYUWAR MADINA* =اÜ
=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
_(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>Øİİ*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* <Øß

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS=تÜ)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A
'ş*






*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ´an uwana Mata waWanda suka fuskanci u™uban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ™arshen wahalar rayuwa._

















______________ *EPISODE 3*
_____Ha™i™a ban taSa fuskantar azaba irin makamanciyar wannan da na sha ba, ban yi tunanin a duniya akwai irin wannan u™uban ba, tabbas sun gana min azaba ba kaWan ba, tunda na sume ban sake sanin inda kaina yake ba har aka gamawa kowa kaciyar, yayinda aka Wauke Ni aka kai Ni Waki Ni da sauran ´an uwana waWanda ko wacce Wakin Mahaifiyarta aka kaita domin ta kula da ita, Ni kuwa babu kowa a tare da Ni sai Yaya Haula da take zuwa gida take dawowa, tayi kuka ba kaWan ba, ta shiga tashin hankali matsananciya ganin har yanzu ban farfaWo ba, duk da kuwa zuba min ruwa da akai tayi, amma sai Baban Sasa yace, "a bar Ni zan farfaWo ne, babu abun da zai same Ni." Daga nan ne aka tafi aka bar Ni, Yaya Haula da ta gaji da jiran farkawa na itama sai ta koma gida, tunda tana da aiyuka duk bata yi ba, dole ta koma gida ta soma aikace-aikace tare da Waura girkin dare tunda a lokacin goshin magriba ya gabato, bayan ta gama ne ta sake dawowa gidan amma har a lokacin ban farka ba, da abincin da ta dafa ta ri™o min ta kawo min, sai dai hankalin ta ya sake tashi sabida ganin babu numfashina har yanzu, ga shi kuma jinin da ke fita daga ™asa na bai dena fita ba, dole ta fita tana kuka ta je ta samo ganyen da aka yi mana amfani dashi wajen Inna Lami, ta shigo dashi ta sake duba min ™asana ta ga yanda yake zubar da jini, sai ta cire wancan ganyen ta sanya min sabo, kana ta buga tagumi tana ta hawaye yayinda idanuwanta suna a kaina

A lokacin ne Baban Sasa ya aiko yana tambayar, "har yanzu ban farka ba?"

Yayinda Wan aiken ya koma ya sanar mishi da halin da nake ciki. To tun suna Waukar abun da wasa amma har dare ya soma tsalawa ban farka ba, abun ya soma damun su Baffa, haka aka kira mae maganin gargajiya ya sake duba Ni, ga shi na kowa jinin ya tsaya amma ban dani, jinina sai zuba yake yi haka na sake yin fari a lokaci Waya tamkar bani da rai, lokaci Waya na zabge nayi wani irin firiricewa sabida jinina da ke ™arewa, amma su basu san da haka ba, basu kaiNi asibiti ba tunda ba sa kai Yaran su asibiti, kula dani kawai ake yi ana min maganin gargajiya sai toshe min gaba ake yi da wasu abubuwa duk don jinin nawa ya tsaya, da™yar aka samu ya tsaya

A ranan Yaya Haula sai a gidan mu ta kwana domin hankalin ta ya ™i kwanciya, kuka take tayi dole Mijinta yace, "ta je ta kwana dani tunda hankalin ta bae kwanta ba."

Sai goshin asuba na farfaWo, sai dai ba na iya gani sai dishi-dishi, hakan yasa na saki kuka a hankali wadda muryata gaba Waya ta dishe ba a jin kukan nawa sai hawaye da ke zubar min sosai

Ganin na farka da gudu Yaya Haula ta fita ta sanar da jama'ar gidan,
Nan da nan sai ga su sun shigo har da su Baban Sasa sai sannu ake min, nan aka ce, "a Waga Ni a bani maganin da aka ajiye min domin jiran farkawa na."

Sai dai babu inda nawa ke motsi duk yanda aka yi da ni haka nake bi, har yanzu ba na ganin Mutanen da ke cikin Wakin sai maganganun su da ba na ganewa, yayinda bakina sunan Umma kawai yake furtawa sai dai babu mae ji na, da haka ina jin yanda ake ta Wura min maganin a baki sai dai kawai in buWe baki in amsa ana ri™e dani, da™yar nake iya haWiyewa shiyasa duk yake zuba a ™asa, daga ™arshe aka bani abinci sannan aka kwantar da Ni, raWaWin da nake ji a jikina bazai taSa iya misaltuwa ba, ha™i™a nayi tunanin mutuwa zan yi sabida azaban da nake sha, gani da raina amma ba na sanin abun da ke faruwa, ba na iya magana sannan ba na iya gani, sai dai jin murya, a koyaushe ina iya jiyo muryan Yaya Haula da kukanta da yadda take rarrashina, amma ko na buWe baki da ninyar kiran sunan ta in yi magana domin in faWa mata irin tsananin zafin da nake ji a ™asana; ba na iyawa, harshe na ba ya furtawa, sai dai in ta hawaye wanda ke nuni da tsananin azaban da nake sha

Yaya Haula ta kasa jirgawa ko nan da can ne tana nan tare da Ni, lokaci bayan lokaci tana min sannu

Amma Ni idanuna a rufe suke still hawaye suna sauka a kan kuncina, ko na buWe ido ba na iya ganin ta, ko nayi yun™urin yin magana ba a ji na, shiyasa tunda na kwanta a haka ban sake motsawa ba, sai dai azaban da ke ratsa Ni ji nake yi kamar mutuwata ta zo ta same Ni, ko kaWan ba na bu™atar

Please Login or Register in order to submit comment