Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su da kuma farin cikin gidansa, tun yana Soye halin da yake ciki sai ga shi Matarsa ta soma fuskantar komai, wanda ya ja musu tsiya da faWace-faWace kala-kala, har kuma ya fito fili ya bayyana mata matsayin Madina a wurin sa a can baya da bata sani ba, wanda sanadin hakan yasa tayi yaji tabar gidan ta koma gidan ubanta, kuma ta kwashe Yaran ta tafi dasu, sannan kuma takai ™aranshi wajen mahaifinta,
Wanda shi ya goya mata baya ne sabida ita kenan ´arsa da ya haifa, duk abun da take so shi yake so, yana ganin tamkar cin amana ne Yunus yayi mata tunda har ya iya aure batare da ya faWa mata ba, sannan kuma har da sakamakon Wa, don haka ya kira shi yayi masa zaga-zaga kuma ya ™wace duk wani abu da ya san ya ba shi, hatta da gidan da suke zaune,
Ko kusa a lokacin basu san cewa Yaya Yunus ya siya sabon gidansa ba tunda har wannan lokacin ya ™i komawa bare ya sanar da Sharhabila, shiyasa koda mahaifinta ya ™wace komai kuma ya kore shi a wurin aiki abun bai taSa shi ba, tunda dama yana sana'ar sa ya kafu da kanshi, ko kusa bai ji haushi ba sai dai da gayya ya saki Sharhabilan tunda shima yana ganin ai yana da hanyar da zai rama,
Ya kuma sake ta ya koma sabon gidansa, wanda ya Wauki alwashin sai ya samu hanyar da zai dawo da Madina cikin rayuwarsa, komai zai iya yi domin ta a yanzu, idan ta kama koda dur™usa mata zai yi ya kuma ™as™antar da kansa a wajen su domin su yafe mishi kuskuren da yayi, don ya Wauki Wammaran komawa gidan Umma domin ya sake basu ha™uri

A ranan ya je ya ga gidan a kulle kamar wancan lokacin da ya zauna jiransu, yanzu ma yana nan jingine da motansa yana ta duban hanya; sai ya ga sun fito daga gidan su Mashkur, ita Madinan tana ri™e da coolern abincin su, Umma kuma ta goya Khalifa a bayanta, basu ankare dashi ba sai da suka taho gab dashi sannan ne suka ganshi,
Da sauri Madina tayi baya kamar zata kifa ta Soye a bayan Umma gabanta na wani irin buga wa,
Hakan ne yasa Umma ta kamo hannunta suka yi maza suka nufi bakin gidansu, Umma ta saka mukulli zata buWe

Hakan ne ya samu damar ™arisa wa inda suke cikin sanyin murya yace, "don Allah Umma ku saurare Ni wlh ban zo da nufin cutarwa a gare ku ba, ina son in gyara kuskurena ne kamar yanda nayi a baya, yanzu haka na sanar da dangi cewan Yaron da Madina ta haifa Wana ne, don Allah ku taimaka ku yafe min mu gyara abun da ya faru baya, na yarda zan mayar da Madina Wakinta zan kula da ita."
Tuni Umma ta buWe ™ofan ta shigar da Madina ciki, itama ta shige tana shirin rufe ™ofan,
Amma sai yayi saurin saka hannu ya ri™e ™ofan yana ™ara ro™anta cikin tsantsan nadamar abubuwan da yayi,
Umma sam ta kasa sauraren shi domin a yanda take ganin ba™in shi da tsanar da take mishi; sam ta kasa ba shi wata damar da zasu yi magana, sai ma cewa da tayi, "ai ka makaro wlh har abada Madina ta fi ™arfin ta koma gidanka, ka cire ma wannan tunanin a ranka."
Ta ja ™ofan da ™arfi ta datse,
Ya kasa jirgawa a wurin yana tsaye kamar gunki, kuma ya ci gaba da buga musu ™ofan yana kiran sunan Madina,
Ya jima a wurin yana buga ™ofan, sai da ya ga baza a buWe mishi ba sannan ya juya zuwa bakin motansa ya ci gaba da tsayuwa a wurin

Har su Hussaina suka dawo makaranta suka tarar dashi, suna ta kallonshi duk da basu sanshi ba,
Shima Win ya zuba musu ido yana kallonsu bai dai ce komai ba har suka nufi ba™in ™ofan gidan,
Buga ™ofan suka soma yi amma ba a buWe musu ba, tunda a tunanin Umma har yanzu Yunusan ne a wajen bai tafi ba, shiyasa tayi banza dashi ta ci gaba da aikin ta,
Madina na zaune a cikin daki ta gama shan kukanta tayi shirun dole tana cin abinci

Sai can da Umman ta tuna da cewan lokacin tasowan su makaranta yayi shiyasa ta nufi ™ofan tana cewa, "wane ne?"
Da sauri suka amsa mata da faWin, "Umma mu ne."
Jin muryansu yasa ta buWe ™ofan suka shige, ta mayar da ™ofan ta rufe duk da ta ga Yaya Yunus a wurin, tana jin dole ne ta Wauki mataki mummuna a kansa don baza ta bar shi ya ri™a mata sintiri a gida yana tsorata mata yarinya ba,
Don haka Baba na dawowa ta sanar mishi halin da ake ciki, don a lokacin tuni ya gaji da zaman wurin ya shiga motansa ya tafi, shiyasa koda Baba ya dawo bai gansa ba,
Baba Yace, "ki ™yale shi kawai idan ya gaji da sintirin zai dena zuwa, ai sai an kula shi sannan zai samu damar yin abun da ya kawo shi."
Umma tace, "Ni kuma zuwan nasa ne ba na so ko kaWan, kana tunanin bazai aikata wani abun ba? Kullum muna fita yana tsorata min ´ata duk idan ta ganshi sai ta firgice, da haka zai iya Wauke yaronsa ya kama gabansa, abun da ya yi wa Madina wlh sam ko fuskarsa ba na son gani, ya je can ya ji da tsiyansa, amma idan ya ci gaba da takura mana da Mashkur zan haWa shi ko don yayi mana maganin sa."

Hakan kuwa ta faru domin tun ranan sai Yaya Yunus ya zo ™ofar gidan dai-dai lokacin da suke dawowa, tunda shima ya fahimci daga gidan da suke fitowa,
Umma baza ta iya ganin yana firgita mata ´a ba tunda Madinan ta kasa kwantar da hankalinta; a guje take ™arisa wa gida duk idan tayi karo dashi, kuma idan suka koma gidan ta dinga kuka kenan tana ce ma Umman, "ba ta son ganin shi zai cutar da ita ne."
Wannan ne yasa Umma ta sanar da Mashkur don tayi ™o™arin Soye wa bai san da zancen ba, kuma ta hana Madina faWa masa duk da a kwanakin bai zo gidan ba ma, dayake ba ya fita da wuri da safe in sun je suna haWuwa dashi su gaisa, idan ya tafi kuma sai dare,
Hakan ne yasa Umma ta sanar mishi yau da safe da suka je gidan,
Dama a lokacin yana ta tambayar Madinan ne abun da ya same ta? Duk da ya ganta cikin damuwa a kwanakin nan kuma ya tambaye ta amma ta ™i sanar mishi, yau kuma ya ganta kamar idanunta sun kumbura kamar ta kwana tana kuka,
Shi ne Umman take sanar musu da abun da ke faruwa har Hajiya, tunda a jiya ma da daddare ya zo Baba ya buWe gidan bai san cewa shi ne ba,
Sai da Umma tayi masa zaga-zaga tace, "wlh yanzu zata Wauki mataki a kansa tunda bazai dena zuwa musu gida ba."
Hajiya Ummee tace, "yanzu shi Wan uwan nata ne yake ta muku sintiri a gida a nufin yana son mayar da ita?"

"Wlh kuwa Hajiya, abun ba™in cikin ma kullum sai ya zo, Ni damuwata halin da Madina take shiga tunda ta kasa cire sa a ranta ta dena wannan koke-koken, nima sam ba na son yana ganinta tunda bamu san me zai yi mata ba duk kashedin da nayi masa ya ™i dena zuwa, tsorona kar yace zai Wauki Khalifa shiyasa ma na sanar muku ko akwai matakin da za a Wauka, tunda bazai yiwu ya ci gaba da mana sintiri a gida ba, da ina da hali ma wlh bazai sake ganinta ba ko ya zo."

"To ai kuwa wannan abun dole ne a Wauki mataki, amma bari Farouk yayi magana mu ji hukuncin da zai yanke ko hukumar ne ma a haWa shi da su, haka kawai ana zaune ™alau ya zo da wani shirmen shi."
Mashkur kuwa kasa yin magana yayi sabida halin da ya tsinci kansa, kasancewar sa mai sanyin hali shiyasa baza ka taSa fahimtar ya zuciyarsa ta shiga da jin wannan zancen ba, amma hankalin sa yayi matu™ar tashi ransa ya Saci sosai, sai dai yayi ™o™arin Soyewa gudun gane halin da yake ciki, shiyasa da ya bude baki yace, "Ni ina ga idan har ya dena ganin Madinan hakan zai fi bazai ci gaba da takura muku ba."
Hajiya tace, "to ina za a kaita ga mahaifiyarta a nan? Kana ganin akwai inda za a kaita ne?"
Kansa ya jinjina yana duban Umma tare da cewa, "Umma idan har kin amince sai a Wauki Madina a kaita gidanmu can Kaduna ta zauna a can, na san hakan ma zai taimaka mata wajen sakin jikinta ta manta da duk abubuwan da suka faru da ita, idan tayi nesa zata fi samun kwanciyar hankali, inyaso sai tayi karatun ta can kinga bazai sake ganinta ba bare ma ya san inda take, babu wani zancen hukuma shi da kansa zai hakura da nemanta."
Da sauri Hajiya tace, "yauwa shawara mai kyau kuwa, domin can ne kawai ya fi dacewa ta zauna tunda Zulaihat bata da wata matsala zata rike ta kamar ´arta, idan har kin amince Asiya sai ku yanke shawara da Mijin naki a tura ta can ta zauna tayi karatun ta a can, kinga abun da Mashkur yace ai."
Cike da sanyin murya Umma tace, "amma anya Hajiya hakan zai yiwu? Baza mu takura a dauke ta a kaimusu ita ba? Ai Wawainiyar sai yayi yawa."

"Kinga Asiya nace miki babu matsala in dai ´ata ce zata rike ta, suka ri™e na wasu ma bare wacce mu muka kai musu, ai yanda Mijinta yake da taimako ko gidan kika je za ki ga a cike yake da jama'a masu cin arziki, wlh in dai kin amince babu wata matsala Asiya a kaita can Win kawai; itama zata samu sauyin rayuwa."
Umma ta yarda da shawaran nasu tunda har a ranta tayi tunanin da tana da inda zata kai Madina baza ta barta a nan ba, amma tunda ta samu hanyar da zata kaita kamar taimakonta aka yi, ta san waWannan Mutanen masu kirki ne da sanin yakamata, ta san cewa Madina zata ji daWin zama a can fiye da tunanin ta. Don haka tayi amanna da hakan har a ranta kuma ta ji dad'i sosai, sai dai kuma bata san yanda ita Madinan zata Wauki zancen ba ko zata amince? Tunda matsalar dama ita ce,
Ga Madinan a zaune tana sauraron komai kanta a saman gwiwowinta ta ™i Wagowa ma bare tayi ™wa™™waran motsi,
Lallai kam in dai Madina ta amince to itama ta amince bata da matsala, Allah yasa hakan shi ya fi alkhairi.
[3/4, 8:55 PM] OumŠahira: =ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ
   *RAYUWAR MADINA* =Ĝ§Ü
=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
          _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>ĜŬŬ*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* <Ĝß

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS=ĜŞÜ)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

              *P.W.A
'ŝ*






         *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ´an uwana Mata waWanda suka fuskanci u™uban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ™arshen wahalar rayuwa._






*DATA SHARE*

Call, message or whatsap 07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 270
2gb. 500
3gb. 800
4gb. 1100
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.


















______________ *EPISODE 47*
_____Ita da kanta Hajiya Ummee ta kirayi sunan Madinan tana cewa, "Madina Wago kai ki kalle mu; kin amince a kaiki gidan su Farouk ki zauna a can ki yi karatun ki? Kinga wannan Wan uwan naki bama zai sake ganinki ba bare ya tayar miki da hankali, kina can hankalin ki kwance babu wanda zai takura miki, Mashkur zai ri™a zuwa yana duba ki duk sanda kike so, itama Umman naki zata rika zuwa tana duba ki kinji ko? Yanzu ki faWi ra'ayin ki idan kina so sai a kaiki can?"
Shiru Madinan tayi sabida ta kasa yin magana domin ta rasa amsar da zata bayar, bata jin cewa zata iya rayuwa a wani wuri idan ba a wurin Ummanta ba, tsoro take ji, tsoron kuma bazai barta ta iya zama a wani wurin ba, dama ga ta kamar farar Kura haka take akwai rashin son jama'a,
Amma kuma ganin yanda Umma ta soma tausanta tana cewa, "ta je can tayi karatun ta zai fi ita kanta zata fi samun farin ciki."
Ta lallaSa ta sosai wanda yasa dole ta amince ba da son ranta ba,
Mashkur ya fi kowa jin daWi duk da ya san zata yi nesa dashi ba kamar a nan ba, yana ta kallonta cikin farin ciki amma har lokacin ta ™i Wago kai bare ta kalli kowa, shi a ransa yana jin idan ya kusanta ta da iyayensa zasu fi sonta, kuma idan ya fito musu da maganar aurenta baza su ™i yarda ba, duk da yana ji a ransa baza su ™i abun da yake so ba, mutane ne masu sau™in kai

Koda Umma ta koma gida ta sanar da Baba, shima bai ce komai ba yace, "duk yanda take so tayi shi bazai ™i goyan bayanta ba."
Shiyasa a weekend Win nan Mashkur ya shirya tafiya da ita, don har an sanar da iyayensa kuma sun amince sun ce, "babu damuwa a kawo ta."
Dama baza a samu matsala a wurin su ba kuma hakan ne,
Har da Khalifa za a tafi tunda Hajiya tace, "baza a raba uwa da Wanta ba, a je dashi idan aka yaye shi sai a dawo dashi nan, amma yanzu a bar mata abun ta."
Bare dama sun lura ba ta son rabuwa dashi,
Kuma hakan ba ™aramin sanyaya ranta yayi ba, har ya cire mata fargaban da take ciki, duk a tunaninta za a iya raba ta da Khalifa amma sai ta ga an bar mata shi, shiyasa har ta ji sanyi da tafiyan,
Ranan asabar suka wuce bayan Mashkur yayi mata duk siyayyan da ya san zata iya bu™ata, Madina ´ar gata ce sosai yanzu don bata rasa komai ba, ko suturun jikinta abun kallo ne sabida kulawan da Mashkur yake basu, shiyasa duk ta sauya kamar ba ita ba, abu Waya ne zaka iya gane ta idan ka santa ada, shine rashin son mutane da nuna kunya, ba ta sakin jiki da kowa sai su Umma, sai kuma su Mashkur yanzu da suka zama tamkar ´an uwa,
A hanyar tafiyan nasu ma sosai ya ja ta da hira don dai ta saki jikinta sosai yanda yakamata, duk da rashin son surutun nata dole sai da ta biye mishi tunda yanzu ta soma rage jin kunyarsa fiye da baya, tana girmama sa matu™a kuma duk abun da yake so tana mishi, don wani lokacin ma idan suna hiran har dariya zaka ga tana yi,
Wannan ya fi komai faranta ran Mashkur, a komai nata ya fi ™aunar ganin farin ciki a kan kyakkyawar fuskar nan nata, shiyasa duk wani abu da ya san tana so ya fara noticing kuma yana ™o™arin yin mata, kawai don dai ya ga farin ciki a fuskarta

Bayan sun isa da yammaci ne, Madina ta ga karrama wa a wurin mutanen gidan, don yanda Mummynsu ta Wauke ta kamar ´arta sai haba-haba take yi da ita, don a cewar ta, "yarinyar ta shiga ranta ainun, ga ta fine girl very innocent."
Khairiyya ma sai jin daWi take yi, don tunda aka faWa musu maganar take murna sabida tun farkon ganinta da Madina ta ji tana sonta, amma mamakinta ya aka yi Madinan zata dawo gidansu da zama bayan da auren ta? Amma a ranta tayi tunanin maybe sun rabu da mijin ne, musamman da ta ganta har da Wanta, lallai sun tausaya mata don Mummy ma abun da Hajiya ta faWa mata kenan, shiyasa suka tausaya mata, a ganin su yarinya kamar ta tana zawarci,
Nabeela dai sam bata yi farin ciki da ganin Madinan ba, domin abu Waya ne ya tsaya mata a rai tun wancan ganin da suka yi mata, ta kula da yanda Mashkur yake bata kulawa komai yace Madina, sannan wannan zuwan da ya kawo ta sai ta ™ara tabbatar da cewan tabbas akwai abu aransa, tunda ga shi kamar ma bai ganta ba hankalin sa gaba Waya yana a kan Madina, abun ya Waure mata kai nan da nan sai ta ji tsanar Madinan a ranta, domin tabbas idan har hasashen ta ya zama gaskiya baza ta taSa raga mata ba, wlh dole ne ta fita a gonanta Mashkur nata ne

To Madina dai bata san tana yi ba, domin tana can hankalin ta a kwance don yanda aka karSe ta a gidan sai kuma duk ta saki jikinta, tunda suka zo Khairiyya ta amshi Khalifa yana hannunta ta ™i bada shi,
Karshe ma a Wakin su Khairiyyan tace Madina zata zauna,
Nabeela sai haushi take ji amma ko kusa ba wanda ya kula ta,
Don haka mai aiki a can Wakin ta je ta jera mata kayanta,
Khairiyya ta tafi da ita duk ta nuna mata abubuwan da yakamata,
Sai dare sannan suka haWu da Daddy tunda ba ya nan a gidan, shima ya ji daWin ganinta sosai, har amsan Khalifa yayi yana mishi wasa yana cewa, "ya samu Aboki daga yau."
A ranan dai haka suka kasance a tare suka ci abinci har sanda lokacin barci yayi,
Sannan suka tafi Waki, Khairiyya tayi wa Khalifa wanka sannan aka sauya mishi kaya suka kwanta,
Washe gari ma komai Khairiyya ta yiwa Yaron, sai ta zama kamar ita ce uwarsa don ko kusa yaron ba ya zuwa hannun Madina sai idan yana kuka yana neman abincin sa

Mashkur ba ™aramin jin daWi yayi ba da ya ga Madina ta saki jikinta fiye da yadda yake zato, don bai yi tunanin hakan ba, kuma abun da ya fi faranta mishi rai yanda ya ga iyayensa sun amshe ta hannu bibbiyu suna bata kulawa kamar ´arsu ta cikin su, shiyasa ya samu ™warin gwiwan tafiya bayan yayi kwana biyu ranan Monday ya wuce,
Madina sai ta ji sam babu daWi da tafiyan nasa, sabida a yanzu ba ™aramin sha™uwa suka yi ba sai ta ji gidan bai mata daWi ba, har kuka tayi a Soye sabida tunanin sa,
Amma kuma kulawan da ake bata dole yasa ta Soye tunanin gida ta soma sakin jikinta,
A gidan babu abun da suke yi sai dai su ci su sha su huta komai sai dai a yi musu, wannan rayuwar yasa Madina ta ™ara sauya wa fiye da baya, don idan tana kewar gida sai dai Khairiyya ta kira mata su Umma su gaisa, dama tun ranan da Mashkur ya tafi ya soma kiran Khairiyya yace, "ta bata wayan su gaisa."
Wannan yasa kusan kullum idan yana son jin muryanta sai ya kira Khairiyya ta haWa su,
Da Nabeela ta fahimci hakan sai kishin ta ya fito fili sosai, don har ba ta iya Soye tsanar da take yi wa Madina, har ta soma hantaran ta tana gaggaya mata maganganun da ita ta kasa fahimtar inda ta dosa

Wannan yasa Khairiyya ta kira ta gefe tana cewa, "wai don Allah Nabeela mai kike yi haka? Me yarinyar nan ta tare miki da kike son ™untata mata a gidan nan?"
Wani kallo ta watsa mata tana cewa, "Oh ba ki san me tayi min ba? Duk abun da ke faruwa ba kya gani kenan? Wannan yarinyar ficiciya da ita take son shiga gonan da ba nata ba, ko ba ki fahimta bane?"

"Nabeela ba abun da kike zato bane tsakanin su, haba taya Yaya Mashkur zai so ta bayan ga ki a raye? Kar ki yi tunanin da zai hana zuciyarki sukuni, kin san halin Yaya Mashkur akwai son taimako kawai tausayi yasa kike ganin mu'amalar su a haka."
Hannunta ta fizge Nabeelan tana cewa, "wlh ™arya ne Ni na ga alamun so a idanunsa, idan babu rami mai ya kawo maganar rami? Ki tsaya ki yi tunani da kyau kema dole son yarinyar nan yake yi sabida kulawan da yake bata is to much. As for me, I know what I'm doing. I'm not a little girl."
Ta ja tsaki ta wuce tabar Khairiyya da sakakken baki a wajen,
Sai da ta Sace mata sannan ta ja numfashi tana cewa, "Nabeela problem, amma mene ne abun Waga hankali a nan in ban da sanya kai a jaraba, Ni naga Yayan ai bai ce yana sonki ba ke kaWai kike kiWan ki kike rawan ki." Sai ta Wage kafaWu tana komawa ta shige Wakin da suka bar Madina a ciki

Ita kanta Madinan ta soma fahimtar Nabeela ba ta ™aunarta a gidan, don ko magana ba ta mata, idan ma zata yi mata magana sai dai ta ri™a zagin ta da turanci wanda ita sam Madina bata fahimtar mai take cewa, sai dai tana gane tsantsan tsanar da take mata a tattare da ita, musamman wani lokacin tayi ta kushe ta tana hantarar ta,
Amma ita Madina nata ido ne tunda bata da yanda zata yi, arziki ta zo ci sam baza ta iya faWa da ´ar masu gida ba, bare ita ba mai hayaniya bane ko dukanta tayi baza ta iya rama wa ba, ta san Nabeela ko bata girmi Yaya Haula ba zasu iya zuwa sa'an juna, a ganinta amma.*****

A satin da aka kawo Madina aka soma mata lesson kamar yanda Mashkur ya sanar da iyayensa, shiyasa har sun samo mata mai yin mata lesson tun daga begging, kuma ya soma karantar da ita cikin natsuwa da kuma yanda zata fahimta,
Hakan ne yasa idan su Khairiyya suka dawo nasu school Win, sai ta zaunar da ita ta ™ara koya mata abubuwan da bata gane ba tana tisa mata shi sosai,
Wannan yasa Madina ta soma fahimtar inda aka dosa a karatun, ya kuma soma mata sau™i sosai tunda ta samu inda ake koya mata

Yau da gobe kayan Allah sai ga shi Madina har tayi kusan watanni biyu a gidan, sai dai fa tun haihuwar Khalifa bata ™ara yin jini ba har kawo wannan lokacin, kuma babu wanda ya sani don har Umma sam bata fahimta ba, duk da ta ga bata ga alamar hakan ba; amma kuma zaman da tayi a gidan bayan an fito da ita daga kurkuku just one month ne da wasu satikai, so bata fahimci cewar ba ta jinin ba,
Tun wata uku da zuwan ta gidan su Mashkur aka gama mata duk wasu shirye-shiryen fara zuwa school Win ta, a wannan lokacin ta tsinci abubuwa da dama daga wurin Khairiyya da kuma lesson Win da ake mata, shiyasa da aka tashi sai aka saka ta a J.I.S 1 a wata makaranta mai tsananin tsada da kyau, har sun shiga zangon karatu na biyu ma (second time)
Daddy da kansa yace, "shi zai Wauki nauyin karatun nata; da duk wasu abun da zai taso na school Win."
A ranan da zata fara zuwa Mashkur ya zo ya kaita da kansa,
Makarantar gaskiya mai kyau ne koda gani ga tsada, don duk yaran masu hannu da shuni ne a school Win, kuma ana koyarwa sosai wanda dole mutum ya mayar da hankalinsa, wannan dalilin ne yasa tunda Madina ta shiga school Win ta soma fuskantar sabuwar rayuwar da bata taSa tunanin ganinta a ciki ba, sam bata da lokacin ma da zata samu damar yin wasa bare tunanin wani abu can, sai dai tana shan wahala duba da yanda ta taso bata san komai ba a kan harkan ilmin Boko, amma kuma ta dage matu™a tunda sau tari Mashkur shi ke ™arfafa mata gwiwa matu™a, don wani lokacin ma a waya yakan tambaye ta duk abun da bata gane ba, kuma tana faWa mishi shi kuma ya fahimtar da ita, shiyasa zaka ga yakan jefa mata wasu words masu sau™i na turanci yakan mata magana da su don ta koya ta iya,
Sannan tana samun ilmin hakan a wurin su Khairiyya duk da bata san me suke cewa ba, amma yau da gobe tana jin kalmomin kuma ta fara understanding since a school ma shi ake musu,
Alhamdulillah to za a ce don daga gani ™wa™walwan Madina tana ja,
Tun sanda ta shiga makarantar bata taSa zuwa da Khalifa ba, kuma mutane da dama na school Win basu san cewa ta taSa aure ba bare har da Wan ta, duk wanda zai kalle ta ma bazai taSa tunanin hakan ba, dama ga ta da rashin son jama'a, sai ya zamana ta kame kanta a school Win musamman da ta fahimci babu wani sa'anta a ajinsu, yawanci duk ta girme musu gaskiya kuma duk yaran masu kuWi ne

Please Login or Register in order to submit comment