Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi kuka tace, "Yaya Haula Ni ba na son aure yanzu, ban san me zance mishi ba shiyasa na amince, sabida ya wuce gaban in mishi musu, tamkar Mahaifina haka na Wauke shi, amma wlh Yaya ba na son aure, Ni na fi son zama a haka."

"Kullum haka kike cewa Madina, kuma kin san hakan bazai taba yiwuwa ba, rayuwar Mace bata yiwuwa sai da aure, abun da ya faru dake ba shine hujjar da za ki ri™a fadar haka ba, muna miki zaton alkhairi Madina, insha Allah za ki samu dauwamammen farin ciki daga nan har ™arshen rayuwarki, shiyasa idan ma kina jin haka a ranki ki ri™a addu'a ki bar wa Allah zaSi; shi ya isa da komai, bazai taSa bari ki ™ara shan wahala a rayuwarki ba, ki yi ta addu'a don Allah Madina ki ri™a sallan dare kina neman zaSin Allah, ba wai ki ri™a waWannan maganganun ba sam ba na jin dadin su."
Hawaye Madinan ta share tana cewa, "Wlh Yaya tsakanina da Allah nake faWa miki ba na son aure, Ni ba na so kuma ba na jin ko nayi auren zan yi farin ciki, Yaya na san cewa daga lokacin na rasa sauran farin cikin da nake rayuwa dashi domin ku; ban ga mene ne dalilin aure ba da har za a matsa min..."
Katse ta tayi tace, "shikenan na ji yanzu mubar wannan maganar, amma dai ki dage da addu'a kinji Madina Allah ya zaSa miki abun da ya fi zama alkhairi."

"To Yaya Haula, ina yi ina iya bakin ™o™arina, zan ™ara dagewa insha Allah."
Sai kuma Haulan ta koma bata labarin Yaran gidansu da za a yi wa kaciya wannan karon, su huWu duk ´a´an yayyinsu,
Sai da gaban Madina ya faWi tace, "Yaya Haula don Allah ki dena faWa min irin wannan zancen, wlh na tsani jin kalman kaciyar nan."
Sai kuma tahau sheshshe™an kuka

"To ya za a yi Madina? Ai dole ne in faWa miki tunda ´an uwanki ne, abun da muka san dole ne kuma muma mun WanWana dole mu taya su jimami, ki sanar da Umma don Wazu na manta ban sanar mata ba."

"Yaya Haula wlh duk ranar da nayi ilmi wata rana sai nayi ya™i da wannan zaluncin, bazan taSa bari kowacce Wiya mace ta ci gaba da karo da wannan ™alubalen ba, wlh sai na hana sai na taimaka musu, domin Ni kaWai na san wahalar da na sha wanda har yanzu ina kan sha; don ina jin ™unan abun matu™a, har yanzu jina nake ban dawo dai-dai ba, ba na jin dai-dai yaya Haula sun rigada sun cutar dani, Allah ya isa."
Kukan da take yi sosai; sai itama Yaya Haulan ta fara zubar da hawaye, yayinda tace, "to ya zamu yi Madina? Cuta dai an rigada an cuce ki don naki ya zo da matsalar da har yanzu ba a samu wacce ta sha wahala kamar ki ba, Allah ya ba ki ikon cimma burinki Madina, wlh ina goyon bayanki domin a yanzu Ni kaina a tsorace nake musamman in na tuna Ihsan itama ta kawo kai, lokaci kaWan za ki ji ana maganar nata, wlh gaba Waya a tsorace nake."
Da sauri Madinan tace, "to ki Wauko ta ki kawo ta nan kawai ta zauna, kin ga ko makaranta sai tayi a nan wurin Umma, don Allah ki tambayi Mijinki ya barta ta zauna a nan."
Murmushin takaici Yaya Haula tayi tace, "ke dai kawai a yi sha'ani Madina, amma wlh baza su taSa yarda ba abun ma bamai yiwuwa bane, an rigada an haife mu a can sai hakuri Allah ya kawo maganin matsalar mu, amma ban san ranan da ™auyen mu zasu waye ba, kwanaki ma wasu sun zo gina makarantar boko wlh ™iri-™iri su Baban Sasa suka hana su, sai da suka shiga suka fita suka yi musu koron kare, Allah mun gode maka ko awanne hali muke shine abun godiya; domin bamu san ya rayuwar wasu yake ba Allah abun godiya ne, don Allah ki dena wannan kukan don ba shi da wani amfani a gare ki, mu taya su addu'a Allah yasa a yi lafiya a gama lafiya, bari in kashe wayana ina da aiki Madina, ki gaishe da su Hassana."
Dakyar Madinan ta amsa mata sannan suka yi sallama ta kashe, sai dai ta kasa tashi a wajen don zuciyarta ta karye da tausayin ´an uwanta, yanzu shikenan zasu WanWani azabar da ta WanWana? Shikenan daga yanzu an gurSata musu rayuwa? Ta yiwu ma su kamu da ciwo makamanciyar nata da ta azabtu a sanadin haka,
Hawaye sosai ta dinga zubar wa ta faWa zuzzurfar tunanin makomarsu da kuma hanyar da zata bi wajen ganin ta taimaki ™auyen su, amma ta san da kamar wuya burinta ya cika, kamar yanda Mashkur ya taSa faWa mata ne insha Allah baza ta kasa ba sai ta nemi ilmin da zai kaita matsayin nan, sai Allah ya cika mata burinta,
Sai da Umma ta kira ta sannan ta tashi a wurin ta fita waje, sai dai tayi ™o™arin share fuskarta saboda kar ta gane halin da take ciki, sai ta je mata da maganar da Yaya Haulan tace ta sanar mata za a yi wa wasu kaciya daga cikin ´an gidansu.
[1/9, 8:18 AM] My Airtel Numb: =ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ
    *RAYUWAR MADINA* =اÜ
=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ=ØÜ


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
           _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>Øİİ*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* <Øß

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS=تÜ)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A
'ş*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ´an uwana Mata waWanda suka fuskanci u™uban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ™arshen wahalar rayuwa._





*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb 270
2gb. 500
3gb. 800
4gb. 1100
5gb 1400
6gb. 1700
Verlid for 30 days.












______________ *EPISODE 63*
_____Tun haWuwar da Madina tayi da Falak suka zama tamkar ™awaye; duk da ita Madina tana jan baya da ita domin sun Wauki tsawon lokaci bata iya sakin jiki da ita ba, sai dai ita Falak akwai surutu da wasa da dariya, wannan ne yasa ba don tana so ba dole ta sakar mata fuska sabida ko bata so sai falak ta saka ta magana, ga ta bata da Soye-Soye komai nata ta sanar da Madina tamkar wacce suka daWe da ita, kullum bata da labari sai bata labarin Familynta da ´an uwanta da kowa da kowa; hatta sunayen su Madina ta soma ri™e wa sabida yanda ta gundura da jin labarin su,
A ha™i™a sai yanzu Madina ta sake tabbatarwa Falak irin ´a´an masu kuWin nan ne; kuma Allah ya saka mata kyauta abun hannunta ba ya rufe mata ido, sai dai in ita Madinan ta ™i amsa idan tayi mata kyautar wani abu, ita kuma Falak a nan ne zata yi fushi tace, "wlh sai ta amsa dole tunda ita ta bata, ai yanzu sun zama ™awaye, infact ma ita bata taSa yin ™awa ba sai a kanta, kuma ta burge ta ne shiyasa take mata kyautar, sai dai idan bata sonta da ™awar."
Hakan ne ke saka wa Madina jikinta yayi sanyi ta kasa mata musu, domin tana ganin Falak ta fi ™arfinta nesa ba kusa ba bare tace zata iya wulakanta ta, ko a irin labarin su ta gane irin babban Family suke dashi, takan yawan faWa mata, "duk yawancin Familynsu Likitoci ne; iyayenta da yayyinta da kowa nasu, suna da babban Asibiti a Kaduna,  *Al'amin Family hospital,*
wanda Babanta ne babba a yanzu a cikin familynsu da ke kula da shi, sai sauran kawunnansa da yayyinsu; yanzu ne kawai wasu daga jikinsu masu tasowa suke karantar abun da suke so ba doctoring ba, domin a baya babu mai karantar wani course idan ba doctor ba, shiyasa ake kiran Familynsu da *Doctor's Family,* I know na san kin taSa zuwa Kaduna right?"
Saurin girgiza mata kanta Madina tayi; don bata son maganar tayi tsawo,
Sai ita kuma tace, "ok na san da wurin zuwanki ne za ki san Familynmu don ba Soyayyu bane mu, kuma idan ma ba ki taSa zuwa ba domin Ni za ki je."
Ta ™are maganar tana dariya,
Yayinda ita kuma Madina har yanzu mamakin halin Falak Win take yi; domin surutun ta yayi yawa abun da ba a tambaye ta ba sai ta furta; sai ka ce tace tana son sanin waye ita, alamu tana da prouding da ita wace ce; sai dai tana da sau™in kai da yawa kuma bata da wulakanci shiyasa abun ya zo mata da sauki, kuma dama prouding a jininsu yake don ita bata san su waye ahalin likitoci bane shiyasa zata yi mamakin Falak,
Duk ire-iren labarin nan da take bata; ita Madina bata taSa bata labari a kan kanta ba, in fact ma babu abun da Falak ta sani a kanta sai dai sanin tagwaye da tayi ™anninta ne, tunda sau tari suna zuwa wurin Madinan kuma suna haWuwa da Falak, ranan farko ne da suka haWu Falak take tambayarta ´an uwanta ne? Shine tace mata, "™anninta ne."
Ita kuma ta ™i yarda sabida ganin su kansu Waya gaba Waya, babu yadda za a yi kace Madina ne babba a cikinsu domin sun fita girman jiki ko a fuska ma kamar sune babba, kuma ba wai kama suke yi sosai ba tunda ta fi su kyau gaskiya kasancewar ta fi biyo Babanta, sai dai idan ka kalle su tabbas zaka ga jini kuma zaka ga kamanninsu,
Tace, "ita bata yarda ba gaskiya, ba ™anninta bane sai dai in ita ce ™anwa."
Dariya Madina tayi, sai tace, "Allah kuwa ™annina ne, Mamanmu Waya but Different Baba."

"Oh! Sai yanzu zan iya yarda, but I'm sure ba ki girme su ba."

"Na girme su mana, Ni aka fara haifa before su, infact ma na basu 3yrs and Babana Ummanmu ta fara aura ai."
Sai da su Hassana suka bata tabbaci suna mata dariya sannan ta yarda,
Sai ta koma basu labarin, "itama Familynsu akwai tagwaye irin su masu kama da juna da yawa, ´an Wakin Dadynsu ma sun haifi tagwaye, akwai Aunty Yusra autan Wakin su Daddyn ita har sau biyu tayi tagwaye."
Haka ta dinga lissafo musu tagwayen Familynsu, wasu tace sun rasu wasu kuma suna raye,
Sun dai sha labari a ranan har suka rabu da ita,
Yau da gobe kuma ta wuce wasa; tun Madina tana Wari-Wari da sakin jiki da ita; har dai ta saki jikin tunda in dai Falak ne babu yadda zata yi da ita, don ma wani abun tana ™in biye mata ne domin ta sha ce mata zata bi ta gida idan lokacin basu da lectures sai zuwa anjima, sai ita Falak Win sai ta kira driver sai tace mata, "su zo su tafi tare, daga nan sai ta ga ´an uwanta tunda suna jin labarin ta a wajen ta."
But Madina ta ™i sai dai ta kawo excusing,
Dole Falak sai dai ta ha™ura ta sallami drivern su zauna tare,
Daga baya kuma da ta fahimci Madinan bata son zuwa ne, sai ita kuma tace, "to mai zai hana su su je gidan su Madinan?"
Nan ma ta ™i yarda don ita tace, "bata son tana yawo in dai ta shigo school."
Dole Falak ta ha™ura suka ci gaba da tafiya a haka, kuma ta nace ko a weekend ne ta zo tayi mata wuni but ta ™i zuwa; sai dai ta saka mata ran zata zo wata rana,
Ga shi ita ta ™i faWa mata inda take bare itama ta zo tunda tana son zuwa sosai,
Hakan ne yasa Falak ta ha™ura tunda ta ga alamun kamar Madinan ko bata yarda da ita can-can bane sosai, shiyasa ta dena matsa mata wata rana in ta amince suyi zumuncin sai su je gidan juna

Yau da gobe rayuwa ta ci gaba da tafiya; ga shi har an Wauki tsawon watanni takwas da fara karatun su, yanzu haka saura 3months su zana jarabawar shiga aji biyu, karatun su kuma alhamdulillah gaskiya sun dage dukkan su, bare Madina ta samu Falak a wannan fagen ba ™aramin taimaka mata take yi ba, ko rashin yin turanci da bata yi a baki duk da ta iya, sai ya zamana zamanta da Falak ta soma ™warewa tunda suna communicating sosai; shi dama turanci practicing ne, idan baka yi ko ka iya a banza since zai iya guduwa, amma in ka ™ware da furta wa shikenan kuma ko a gaban waye zaka iya,
Wannan yasa yanzu normal ne a wajen Madina, bata kunyar furta turancinta abun da ta sani, ko a gida ma suna yi da su Hassana domin su ™ware sosai, yanzu ko Khalifa shima babu abun da ba ya ji sabida Madina ta dage tana koya mishi, ga kuma school da yake yi ba a Hausa ma,
Yaron ya taso da haza™a gaskiya kamar ba shi ba; don in yana wani abun ka ji shekarunsa ma sai ka ri™e ba™i, akwai matu™ar wayon; just bai fi 6years da wasu watanni ba yanzu

Umma dai ta kasa sanar da Yaya Yunus zancen ya ha™ura da Madina har yanzu, domin idan ta yunkura zata yi mishi maganar sai ta ga kamar zai tayar da hankalinsa ko kuma wata hatsaniyar ta biyo baya, shiyasa ta dakata tana ganin kamar zai ha™ura ko don irin abubuwan da Madina take mishi; na ™in kula sa da rashin shiga harkansa, ai ya ci ace ya ha™ura amma ji yake yi bazai taba hakura da Madina ba; domin ™aunarta sake shigansa take yi ya kasa janye jikinsa duk irin kasa samun mazu™uni da yayi a wajen ta,
Ita kuma ba wai bata sonshi bane; domin tuni ta yafe mishi tun ba yanzu ba; kawai tausayinsa ne yasa ta kasa Waukan mataki a kansa, idan ta yunkura kamar zata yi masa wulakancin da dole sai ya rabu da ita, sai ta ga meye amfanin hakan? Yaya Yunus babban mutum ne ya wuce gaban wulakanci a gare ta; tana matsayin ™anwar-™anwar bayanshi da ya ci ace ya haifi kamarta, don kawai yana sonta ba shine hujjar da zata wulakanta shi ba,
Sai dai shi a wurin sa shirunta ma tamkar wulakanci ne a gare sa, sabida soyayyarta kawai yake shanye wa yana ci gaba da bibiyanta; da sa ran wata rana zai shawo kanta; shi dai tunda yake bai taSa ganin mai taurin kai irin ta ba, idan har ta yafe mishi ai zata ba shi dama; amma ta ™iya,
Bai san cewa har zuciyar Madina da gasken take ta tsani aure ba shiyasa ya kasa gane kanta, kuma in dai a kan aure ne kaWan ma ya gani wajen banza dashi, da ya biyo ta wata hanyar ce da tuni zumuncin su yayi ™ar™o, tana ganin idan ta sakar mishi fuska tamkar ta amince da auren shi ne, shiyasa sam ta ™i tan™waruwar masa, ko maganarta ba ya ji ko sau dubu zai yi mata magana baza ta kula shi ba, da zaran ya zo gidan ma zata Soye, idan kuma ya cidda ita sai dai tayi harkan gabanta tamkar bata san dashi ba,
A baya ma yana samun gaisuwar ta; amma yanzu sai ta ga dama take gaishe shi, ko kuma idan Umma ta saka ta dole

Yanzu dai Umma ta ha™ura ta sanar mishi gwara ya ha™ura tunda abun ya zo da haka, ita Madinan da kanta ta amince da Alh. Umar Farouk da ya zaSa mata Miji, ta faWa masa komai kuma tace, "yayi ha™uri kawai ya nemi wata ko don kare mutuncin sa, tunda har yanzu basu sasanta da Madinan ba."
Dama kamar yanda tayi tunanin zai tayar da hankali ne, hakan kuwa ta faru domin har da hawayensa ya du™a ya dinga ro™on Umman,
Umma dai ta rasa abun ce masa, sai tace, "ita bata san me zata ce ba, matsalar daga wajen Madina ne; hakuri kawai zata ba shi yayi hakuri ya fauwala wa Allah komai."

A wannan halin yabar gidan tare da nufan ™auye domin ya sanar da Iyayensa, su zo su nema mishi auren Madina don Gaskiya bazai hakura ba, shi ne Wan uwanta shi yakamata ya aure ta,
Ya so ya wuce kai tsaye can kauyen; but sai ya fasa ya wuce makarantar su Madina,
Bai san inda take karatu ba sabida ya sha cewan zai kaita school; bata taSa bin shi ba, shiyasa sai ya kira Hussaina tayi mishi kwatancen inda zai same ta

Lokacin Madina tana tare da Falak a wani rumfa suna Wan hira a tsakaninsu; tunda sun fito lectures ne sai zuwa can anjima zasu koma,
Sai kawai ganin kiran Yaya Yunus tayi ya shigo wayanta, kasa Wauka tayi sabida ta san halin sa kamar maye in ya dinga kira ba ya bari; tana da numban shi but bata Waukan wayansa sai dai ya tura mata sa™o idan ya matsu; in abun ya shafi harkan Khalifa ne,
Yanzu ma koda ta gani ta ™i Wauka; har sai da Falak tayi mata magana ganin ana ta kiran wayan nata tana kallo ta share,
Wayan ta sanya a silent batare da tace mata komai ba,
Ita kuma Falak sai tayi murmushi tace, "anya ba boyfriend Win ki bane yake kira? Dama ba ki taSa bani labarin shi ba."
Madina tace, "boyfriend kuma?"

"Yes, I know kina dashi ai baza ki yi min karya ba."
Shiru kawai Madinan tayi ta kasa magana,
While ita kuma tace, "ok, let me tell you about my boyfriend, and where we met."
Murmushi Madina tayi sabida ta san yanzu zata fara,
But wayan Falak Win ne ta soma ring, sai ta Wauka tana cewa, "Hussaina ke kira na."
Jin hakan yasa Madina ta dube ta tana sauraron abun da take cewa,
Kwatancen inda suke ta yi wa Hussainan sannan ta kashe wayan

Kamar wasa sai ganin Yaya Yunus suka yi a wajen; Wago kan da Madina zata yi ta ganshi a gabansu yana kallonta, sai dai ga dukkan alamu babu walwala a kan face Win sa, yana kallonta yace, "ki taso mu je Mota zamu yi magana Madina."
Falak da ke kallonsa itama. Sai tayi saurin gaishe shi sabida ganin kamannin sa da Madinan; ko ba a faWa mata ba ta san Yayanta ne ko Kawunta; sabida ganinsa babba,
A fizge ya kalle ta before ya amsa ta yana sake duban Madinan wacce ta kasa motsi, sai da ya sake kiran sunan ta sannan ta mi™e jiki a sanyaye, ba don ranta na so ba sai dai don kar ta wulakanta shi a gaban mutane, shiyasa ta bi bayanshi bayan ta cewa Falak tana zuwa,
Kai tsaye wurin motansa ya nufa ya shiga ya zauna ya rufe, itama sai ta buWe ta shiga batare da ta kalle sa ba; dakyar ta iya gaishe shi,
Ko amsa wa bai yi ba yace, "wai Madina mai kika Wauki kanki ne kamar ke inta bibiyanki amma ki kasa bani dama, me kike so in miki ban miki ba da kike guduna? Sai yanzu na gane cewa Ni ne ba kya so amma ba aure ba; tunda har kika ba wani dama zai nema miki Miji bayan kin san gani ina jiranki ne, mai zan yi miki ki so Ni a rayuwa ki yafe min abun da nayi miki? Don Allah ki faWa min me zan miki?"
Yadda ka san dutse haka Madina tayi mishi; ta ™i Wago kai ma bare ta ba shi amsa,
Wanda hakan ya fusata Yaya Yunus yace, "wai ke ba magana nake miki ba? Kin mayar da Ni sa'ar wasanki sabida ina sonki ina bibiyanki; duk wannan abubuwan da nake miki ba kya gani, idonki na can gun waWancan mutanen sabida kina tunanin gidansu; Ni ba Wan gwamna bane sannan ban da Waukaka kamar su; amma ai Ni uban Wanki ne, ko ba kya so Khalifa ya haWa mu, ni Yakamata ki aura ba wanina ba, idan kuma har baza ki aure ni ba na rantse da Allah kin dena ganin Khalifa kenan har abada."
Haka ya dinga surfa bala'i domin idanunsa sun rufe da takaicin abun da aka faWa mishi,
Wanda sam bai kula da halin da Madina take ciki ba; kuka take yi ta toshe bakinta da hijab tana ta sheshshe™an kuka,
Sai daga baya ne ya sassauta zuciyarsa ta soma saukowa daga tu™u™in ba™in cikin da yake ji, sai ya soma dana-sanin abun da yayi mata, nan da nan yahau rarrashinta zuciyarsa a karye kamar zai yi kuka, yana sake ro™onta a kan ta amince dashi bazai taSa cutar da ita ba,
Hannu yasa ya riko nata yana ™o™arin Wago ta,
Sai tayi saurin fizge jikinta tana bin shi da kallo, idanunta sun kaWa sun yi ja laSSan bakinta sai rawa suke yi, buWe ™ofan zata yi batare da ta furta komai ba tana ci gaba da kukan,
Saurin ri™o mata hannu yayi da ™arfi ya rufe ™ofan yasa luck,
A nan ta tsorata da ganin abun da yayi; ga shi ya zo ya haWe da ita wajen kulle ™ofan, shiyasa wani irin tsoro ya shige ta, cikin Sarin murya tace, "meye haka ıÿÿÿ‚ƒ„…†‡ˆ‰Š‹Œ‘’“”•–—˜™š›œŸ ¡¢£¤¥¦§¨©ª«¬­®¯°±²³´µ¶·¸¹º»¼½¾¿ÀÁÂÃÄÅÆÇÈÉÊËÌÍÎÏĞÑÒÓÔÕÖ×ØÙÚÛÜİŞßàáâãäåæçèéêëìíîïğñòóôõö÷øùúûüışÿka buWe Ni in fita."

"Bazan buWe ba sai kin yi magana, na gaji da wannan shirun naki, wlh idan ba ki yi magana ba sai dai mu kwana a nan."
Sai kuma ya koma mazaunin sa tare da furta, "bari mu wuce ™auye a tare; a can sai ki yi bayani don bazan taSa amince wa ki auri wani bani ba."
Taka motan ya soma yi ya nufi hanyar barin makarantar,
Wani irin kuka mai sauti Madina ta saka mishi tana cewa, "bazan je ba, bazan je ba ka sauke Ni don Allah."
Banza yayi mata ya ci gaba da tafiya,
Sai ta kalle sa a fusace, "wlh tallahi bazan bi ka ba, bazan taSa auren ka ba Yaya Yunus, don Allah ka sauke Ni; Ni babu inda zan je, ka sauke Ni."
Kuka take yi sosai amma ya ™i ya sauke ta, ya durfafi hanya ya tafi ko sauraronta bai yi ba,
Zuciya ta ciyo ta wani abu ya tsaya mata a ™irji; abun ka da mai fama da ciwon zuciyar sai nan da nan ™irjinta ya soma suya ciwonta ya tashi sai tahau tari tana kuka sosai, hannunta dafe da ™irjinta tana kiran sunan Umma,
Hakan ne yasa Yaya Yunus ya daburce ya tsayar da motan yana kiran sunanta, duk ya gama ruWe wa sabida yanda ya ga tana kukan, bai san meye yahau kansa ba ya aikata hakan bayan ya san komai zai iya faruwa, kama ta yayi yana bata hakuri, yace, "ya fasa zuwa zai kaita gida."
Jikinsa sai rawa yake yi saboda ganin duk ta fita hayyacinta sai kuka take yi sosai gunun tausayi tana ta numfarfashi,
Hakan yasa ya juya motansa ya nufi asibitin abokinsa Bilal,
Tun kafin ma ya je ya kira sa a waya, suna shiga ya ciro ta a motan ya ri™o ta zuwa ciki,
Dayake Doctor Bilal Win ya fito tare da Nurse, sai yace, "su taimaka su amshe ta zuwa emergency room."

Bayan sun duba ta; sai da aka siyo magungunan da take sha aka bata, sannan aka yi mata allura saboda samun relief; take jikinta ya mutu komai nata ya dena motsi amma idanunta biyu; illa hawaye da take zubar wa,
Sai daga baya ne Likitan ya ba Yunus damar shigowa Wakin, sai da ya duba ta sannan suka koma office Win sa yana mishi bayanin halin da take ciki,
But sai da Doctor Bilal ya tambaye shi dalilin tashin ciwon nata; tunda result ya nuna mishi dole Sacin rai ne ya haifar da hakan,
Amma Yunus ya Soye komai yace, "babu abunda ya faru, suna hanya ne zata koma gida ta fara kukan ™irjinta na mata ciwo."

"Anya Abokina? Na san halin ka fa a kan yarinyar nan, don Allah kar ka matsa mata ka san yanda wannan ciwon yayi mata illa, wlh kana mamaki koyaushe zata iya rasa ranta, baka san illan zuciya bane abu kaWan ne zai haifar mata da bugawar zuci, domin Ni ina ganin gwara ma a yi mata aiki saboda baza ta iya juran Sacin rai ba, mistake kaWan ne za a samu matsala."
Cikin tsananin damuwa wanda har a muryansa ya nuna yace, "Bilal ya zan yi? Na rasa yanda zan yi da Madina, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...! Wlh ina cikin wani hali."
Hawayen da ya gani a fuskarsa shi ya tabbatar masa tabbas akwai Matsala, Abokinsa na cikin mawuyacin hali, hankalinsa ya tashi yake cewa, "haba don Allah Abokina ka zama mai tawakkali, idan Allah ya ™addara Madina Matarka ce babu makawa za a yi aurenku, ka zama namiji ka dena wannan hawayen wlh kana Waga min hankali."

"Baza ka gane bane Docta, i know alhakin ta ne yake bibiyana;

Please Login or Register in order to submit comment