Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta buga mishi a kafansa a karo na biyu, tana cewa, "dalla tashi Kasa kamar wani mushe, ko dai sake maka wani daren za a yi? Farouk tashi mana, Farouk... Farouk..." Sai da ta kira sunansa kusan sau uku before ya motsa,
Tace, "amma Allah yayi maka nauyin barci wlh, ban taSa ganin mutum irin ka ba."

Idanu ya buWe yana kallonta, sai kuma ya mayar yana mai kwantar da kansa batare da yace mata komai ba yana sauraron surutun nata, ganin ta cika sa da faWan yawan barcin nasa ne, cikin magagin barcin da bai ishe sa ba yake cewa, "Hajiya kin cika ™orafi wlh, kina ganin fa ba na samun isasshen barci ne sai a wannan time Win, kuma yanzu na kwanta but kina min ™orafi."

"To wani yace kar kayi barcin? Ko Ni na hana ka? Mutum kullum agogo baza ka sarara wa kanka ba kana hanyar asibiti koyaushe, ko lokacin kanka baka dashi, a haka zaka yi auren ma baka da lokacin yarinyar mutane, ai dole ka ™i ™aunar aure tunda aiki ka saka a gaba, ga karatu ka hana kanka sukuni."
Sai ta ja yatsun ™afafunsa ganin tunda yayi maganar ya sake kifa kansa a pillow kamar ya koma wani barcin, "da Allah tashi ka bani aron dubu biyar inyaso sai ka koma barcin, ka kwana ma a haka Ni bai dame Ni ba, amma sallame Ni in tafi."

Šago kansa yayi yana bin ta da kallo fuskarsa a dame, da alamun ta takura masa ne shiyasa ya kumbura fuskar yana kallonta ya ™i magana

"Tashi mana ina sauri ne, nabar Asiya tana jira na."

"Mai za ki yi da kuWi kuma Hajiya?"
Yayi maganar yana mai ™o™arin tashi zaune da sanyin jiki, wanda barcin ne ya cire masa karsashin sa

Zama tayi gefen gadon tana ba shi amsa da faWin, "Asiya zan ba, zata yi wa Madinanta siyayya sabida zata je duba ta, shiyasa nima zan bada nawa gudummawar."

Shiru yayi yana kallonta, kamar zai yi magana kuma sai ya mi™e bai ce komai ba, wurin wardrobe Win sa ya nufa tare da buWe wa, sai da ya za™ulo wani farin gajeren wando mai aljihu da zip a jikinsa, sannan ya zuge ya ciro kudi har 10k, ya dawo ya mi™a mata yana cewa, "nima ga nawa nan a haWa a yi mata siyayyar."

Baki Hajiya ta washe cike da jin dadi, tare da furta, "ai kuwa ta gode, ka ga yanzu sai in kai mata duk wani abun bukata na Wiya Mace sai ta siya mata, har kayan girki, Allah yasa dai mu ji alheri don wlh ina tausayin yarinyar nan, Allah yasa ta dace da gidan Miji na gari."

"Amin." ya furta yana mai bin hanyar toilet batare da ya koma barcin ba, don ya rigada ya ji barcin kuma ya gudu

Ita kuma Hajiya Ummee sai ta tashi ta fice ta koma falon, bata tarar da Umma ba don tuni ta wuce kitchen tana wanke-wanke, can ta nufa ta same ta ta mi™a mata kuWin, "ga shi nan har dana Farouk ya bayar a ba ki, sai ki siyan mata duk abun da kika san zata bu™ata."

Hannu biyu Umma ta sanya ta amsa cikin tsananin farin ciki tana yi mata godiya, saboda ta san karamcin Hajiya in har bata amsa ba baza ta ™yale ta ba, shiyasa ta amsa cike da murna tana sake mata godiyar kamar zata du™a mata tana mata addu'o'i

Hajiya Ummee tace, "Ameen Ameen, ai babu godiya a tsakaninmu Asiya, yi wa kai ne, kuma zaman tare ne dole mu taimaka wa juna bamu san amfanin da zamu yi wa juna a nan gaba ba, duk sanda kika je dai ki gaishe ta da kyau da kyau, Allah ya zaunar da su lafiya Allah yasa mu ji alkhairi."

Umma na murmushi ta amsa da Amin tana sake cewa, "insha Allahu zata ji, zan sanar mata."

"To Ni bari in koma Waki, don zan yi sallan walha ne da ban yi ba."

"To Hajiya, amma mai za a dafa ne?"

Šan yatsina fuskar tsufan ta tayi tana cewa, "duk abun da kika dafa Asiya yayi, amma ki yi dai abun da Farouku yake so ne tunda yana gida, da alamu bazai fita da wuri ba sabida yanzu ma haka barci ya tashi."

"To Hajiya."
Ta amsa mata tana ci gaba da ™arisa wanke tukunyar da yanzu ta zo kansa

Ita kuma Hajiya ta fita ta koma Wakinta don yin Sallah.***

Koda Umma ta tashi aikin a gidan, kai tsaye kasuwa ta wuce tayi duk siyayyar da ta san zan iya bu™ata cike da farin ciki; sabida samun kuWin nan da tayi, ta san bani da matsalar kayan saka wa tunda lokacin da su Baffa suka zo tafiya dani sai da suka yi mata bayanin kayan da zan tafi dashi, don haka abubuwan girki ta haWa min duk abun da ta san zan bukata, musamman namu na ™auye wanda ta san na saba da shi, sannan ta siyan min wasu ´an robobi haka da zasu yi min amfani, a takaice dai sai da ta kashe dubu goma cif ta taho da raguwar dubu biyar, a ciki ta yanke zata yi kuWin mota sai ta bani wasu daga ciki in ri™e a hannu zai yi min amfani

Kasancewar ta ga ta samu kuWin mota, shiyasa tana koma wa gida ta sanar da Mijinta zuwa jibi zata je duba Ni, kuma a ranan ta kira Yaya Haula tace mata, "ta je ta samu Baffa ta tambaye shi gidan Yaya Yunus a yi mata kwatance."

Jin hakan yasa Yaya Haula tace mata, "itama zata je, don Allah ta bari idan ta zo sai su tafi tare, tana son ta je ta ga ˜anwarta, itama hankalin ta duk a tashe yake tunda aka tafi dani tana cikin damuwa."

Umma tace, "ai babu damuwa, in har kin tambayi Mijin naki ya bar ki, to zuwa jibin sai ki zo da wuri mu wuce taren."

Cike da farin ciki Yaya Haula tace, "to Umma Nagode, bari in je yanzu in tambaya Baffan; tunda na san yanzu haka yana gida ya dawo aiki."

Daga haka suka yi sallama da nufin in Haula ta tambaya zata yi mata Flash sai ta kira.
*** *** *** ***

_____Sai da na daidaici sun gama sun tashi a wurin sannan na je na kwashe kayan gaba Waya, ina shiga kitchen ban fara ci ba na ji kiran Sharhabila tana kwaWa min kira, jiki na rawa na isa Falon lokacin tana tsaye a bakin ™ofan dakin ta tana bi na da mugun kallon da ta saba koyaushe, da sauri na isa gefen ta ina du™a wa tare da amsa mata ina cewa, "gani Anti."

Wani kallo ta watsa min cikin kakkausar murya take bani umarnin, "in yi maza in shiga in yi wa su Mabashir wanka, saura kuma in daWe in Sata mata lokaci har ita ta shirya ta fito."

Da sauri na amsa mata yayinda jikina na rawa na tashi na bar wurin, ba wai tsoro ne kaWai ya sani rawan jiki ba; har da yunwa tunda ko karyawa ban yi ba, ga shi har sha biyun rana tayi, amma bani da ikon yin magana dole abun da ta sanya Ni zan je in yi,
Haka kuwa na shiga nayi musu wankan na shirya su bayan ta zo ta fitar min da kayan da zan saka musu,
Sai da na gama sannan ta kira Ni muka shiga kitchen, ta nuna min abun da zan girka kafin su dawo gidan, "saura kuma in yi mata kuskure sai na lahira ya fi Ni jin daWi."
Ta ja min kunne tana murWe wa wadda har sai da na fitar da ™wallan azaba,
Haka ta ture Ni ta fice batare da ta sake bi ta kaina ba,
Ni kuma na ci gaba da aikin jiki a mace ko abinci na kasa ci, haka na Waura abincin gudun in yi laifi, yadda tace min haka nayi tunda jallop Win taliya Macaroni ta nuna min, a risho nake girkin kasancewar har yanzu bata taSa bari na; na taSa mata kayan wuta ba, sai dai ita ta kunna min, risho Win ne kawai take bani damar kunna wa in har ba ta wurin,
Ni ina kitchen Win ban san sun fita ba duk da na ji kamar ™aran mota, amma ban fita ba sai da na gama girkin tsab, tuni na cinye sauran breakfast Win su tunda yunwa ta dame Ni, ina yi ina ci har na gama girkin sannan na zuba a Kula na kai saman daining, kasancewar na fahimci kamar babu kowa a cikin gidan hakan yasa na Wan saki jikina, duk da a gajiye nake tiSis ga barci da nake jin yana ™o™arin Wauka na, ko sallah ban yi ba na kwanta a tsakar falon sabida jin iska na hura ni, kuma ganin babu kowa shiyasa na ™i zuwa masaukina tunda nan ya fi iska da daWin kwanciya, kun san Wan ™auye bai iya samun wuri ba, kawai na Ware musu kan Kujera nan da nan daddaWan barci ya sure Ni wanda na daWe ban yi irin sa ba,
DaWin barcin ne yasa ban san iya lokutan da na Wauka ina sharan shi ba, ashe har Yaya Yunus ya dawo ya shigo Falon ya tarar da Ni baki a wangale a saman Kujeran su ina sharan barci kamar wata gawa.
[2/10, 10:45 AM] OumŠahira: =ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ
    *RAYUWAR MADINA* =Ĝ§Ü
=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
           _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>ĜŬŬ*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* <Ĝß

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS=ĜŞÜ)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A
'ŝ*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ´an uwana Mata waWanda suka fuskanci u™uban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ™arshen wahalar rayuwa._






*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  550
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.














______________ *EPISODE 23*
_____Yaya Yunus da ya shigo ya hange Ni kwance baki wangale ina sharan barci, mamaki ne ya cika sa sabida ganin yanda na shantake ina barcin kamar na samu gidana, wurina ya nufa ya saka hannu ya buga ™afana da ™arfi,
Wanda a nan take na farka ina zare ido a kansa, muna haWa ido nayi saurin mi™e wa zaune har jikina ya fara rawa cike da tsoron abun da zai yi min, tuni na zamo ™asa kaina a ™asa ina mai ™an™ame jikina sabida tunanin ko duka na zai yi,
Shi kuwa wani kallo ya watsa min yana jan dogon tsaki, murya a kausashe yace, "wato abun da aka bar ki kiyi kenan? Kin zo kin wani saki leSe kina sharan barci hanci cike da majina; idan kika yi mana fitsari uban wa zai wanke iyee?"
Yanda ya ™arisa maganar ne da sauri na girgiza kaina batare da na kalle sa ba, cike da tsoro da rawan baki nake cewa, "kayi hakuri don Allah bazan sake ba."
Tsaki ya kuma ja yana mai koma wa can wani kujeran ya zauna tare da cewa, "tashi dalla ki je ki zubo min abinci, shashashan yarinya, saura in ™ara ganin kin hau mana Kujera kina barci, sai na sabauta ki, ™azamiya."
Ya ™are maganar cike da ™yama yana aika min da mugun kallo mai cike da tsana,
Sai kuma ya kuma jan tsaki yana bin hanyar da na bi da kallo tare da tunanin cutan da iyayensa suka yi masa, wai su rasa wacce zasu aura mishi sai wannan tatsitsiyar yarinyar da komai bata dashi, to ya aure ta ya auri mene kenan? Rainin hankali. Fuska ya sake Waure wa yana mai cira wayansa daga aljihun gaban rigan sa; tare da soma latsa wa, koda ya ji motsina bai Wago ya kalle Ni ba har nabar wajen

Ni kuwa jikina na rawa nake komai kamar ana kaWa Ni sabida tsoro kar in kuskuren da zai dake Ni, duk da har yanzu bai taSa saka hannu ya taSa Ni ba amma ina gudun yin musu laifi, don na san bazan ji da daWi ba,
Kai tsaye Waki na koma sabida na san ban da abun yi a nan kuma,
Ashe har magriba ma ta kusa, sallan da ban yi ba na je nayi sannan na zauna a Waki,
Ina nan zaune na ji ™aran buWe gate, a tunanina ko Aunty Sharhabila ce ta dawo, shiyasa na fita amma babu kowa, fahimtar hakan na gane ™ila Yaya Yunus ne ya sake fita,
Shiyasa na koma Waki tunda na tabbatar babu abun da zan yi,
Sai can bayan isha'i na ji hayaniyar dawowarsu; daga shi har Yaran da Matarsa, ban fita ba tunda na san ba abun da zan yi musu, kuma kasancewar Aunty Sharhabila ba ta son gaisuwana shiyasa na san ko na je zagina zata yi, shiyasa nayi zamana har sanda zata kira Ni,
Ai kuwa babu jima wa sai ga shi ta aiko Mubashir Wakin in zo in cire musu kaya in yi musu wanka,
Hakan ne yasa na fita zuwa Wakin nasu, nayi musu wanka sannan na saka musu kayan barci, daga haka na koma Waki tunda na san ba wani sauran abun da zan yi,
Sai da na bari sun daidaici barin falon; wurin karfe sha Waya sannan na fito saWab-saWab na cinye sauran abincin su, daga nan na koma na kwanta, dayake yau na samu na runtsa nayi barcin rana, shiyasa barcin bai Wauke Ni da wuri ba sai daga baya, asuban fari na tashi na fara aikin da na saba koyaushe wadda na zama musu ´ar aikin gidan bisa tilas; tunda bani da galihu bare in samu sassauci daga mutanen gidan.***

_____Ranan Monday daga Aunty Sharhabila har Yaya Yunus suka shirya zasu tafi wurin aiki,
Ni na yi wa su Sadam wanka na saka musu kayan makarantan su, bayan sun gama karyawa da zasu tafi Aunty Sharhabila ta ja min kunne sosai a kan gidanta da kulan mata da zan yi dashi, sannan ta faWa min abun da zan girka musu, "zuwa ™arfe biyu zasu dawo gidan in tabbatar na gama komai,"
Na amsa mata jiki na rawa har sanda suka tafi sannan na fara aikin, ba ™aramin daWi na ji ba da gane cewan aiki zata fara daga yanzu, ko banza na rage samun tsangwama daga wurin ta, yanzu zan ri™a kasancewa Ni kaWai har sanda zasu dawo, wata™il na samu rahama a wannan lokacin.
Sai da na gama aikin tsab sannan na samu wuri ™asan Kujeran na zauna ina duban wurin Tv, duk da a kashe yake, basu bar min komai ba sai da suka kashe, amma na zauna ne in huta kafin in Waura musu abinci kamar yadda ta umarce Ni, ban Waura da wuri bane kar yayi sanyi sai da na daidaici sha Waya tayi sannan na shiga kitchen Win, kamar yanda a risho ta bani damar yin mata girkin haka na Waura na soma yi, duk da ba komai na iya ba na game daga cikin abincin su, taliya da Macaroni tare da shinkafa kawai na iya girka wa, sai suyan dankali da ta koya min tare da ™wai, duk da dama na saba yin girki a gidanmu shiyasa hakan bai wani bani wahala ba, a cimanmu na ™auye babu abun da ban iya ba kasancewar yadda aka hora Ni da aiki.***

A wannan lokacin ne su Umma suka ™ariso gidan, bayan sun buga ™ofa mai gadi ya fito ya same su, sai da suka gaisa sannan suka nuna mishi gidan suka zo wurin mai gidan, suka faWa sunan shi,
Mai gadi yace musu, "mutanen gidan ba sa nan gaskiya, sai dai mutum Waya ina tunanin ´ar aikin gidan ne."

Hankalin su ya Wan tashi don har fuskokinsu sun nuna alamun damuwa, Umma sai tace mishi, "don Allah ya barsu su shiga su jira su saboda baza su iya tafiya ba."

Mai gadin ya basu hakuri a kan, "bazai barsu su shiga ba," amma ganin yanda suka matsa sosai suna ta ro™on sa, har Umman take faWa masa, "wurin ´arta ta zo kuma Matar mai gidan ne."

Da mamaki mai gadin yake duban Umma, duk da bai san wace ce Mahaifiyar Sharhabila ba; amma ya tabbata wannan baza ta zama Ummanta ba, amma haka nan sai yace, "su shigo yayi musu jagora ciki."
Abun da yasa yayi haka kar yayi laifi ne tunda tace ita ce Mahaifiyar Matar gidan, tunda a tunaninsa Sharhabila ce; babu wanda ya san Madina matarsa ce,
Har ciki ya shigar da su, ya buga ™ofan yana jiran a bude musu

Ina kitchen ina aiki lokacin na Waura sanwan abincin kenan, sai na ji bugun ™ofa, dayake na rufe shiyasa sai na fita da sauri ™irjina na buga wa don a tunanina masu gidan ne suka dawo; ga shi ban gama girkin da ta bani ba, hankalina ya soma tashi zuciyata tana buga wa da ™arfi, cike da tsoron da ya zame min jiki yanzu na saka hannu na rawa na bude ™ofan, babu zato babu tsammani nayi arba da su Umma a bakin ™ofan; wani ihu na saka da ban san sanda ya fito daga bakina ba, cike da kerma cikin hanzari na faWa jikin Umman cikin tsananin farin ciki da murnan ganin su

Mai gadi tunda ya ga haka sai ya juya sabida ganin yanda na tabaibaye Umma ina ihun murna, a ransa yayi tunanin ™ila ´an uwana ne kenan, tunda ya ga na nuna na sansu shiyasa yabar wurin kawai

Yayinda Ni kuma tuni na Wafe Umman na ™i sakinta ina kiran sunanta bakina ya ™i rufuwa, faWan murnan da na ji a wannan lokacin bazai iya misaltuwa ba, don ban taSa tunanin ganin su a wannan lokacin ba, musamman da na ™illa ido na ga Yaya Haula tana dariya itama, dariyan farin ciki da ya bayyana a kan ™aramar fuskarta irin nawa,
Take na saki Umma na koma na rungume ta sai na fashe da kuka tsaban farin ciki,
Itama kukan ne ya ciyo ta tana hawaye tana dariya tare da ™an™ame Ni

Umma da ta ga haka sai tace, "kai Madinah! Wannan murna haka har da kuka? Kukan kuma na mene ne tunda gamu mun zo?"

Jikina na janye ina kallon Umman idanuna sharkaf da hawaye, yayinda cikin yanayin raunin da ganinsu ya sanya Ni nake cewa, "Umma ai kin yi min al™awarin zuwa amma kika ™i zuwa sai yanzu, ina ta jiran zuwan ki har na cire rai."

Murmushi tayi ta kama hannuna tare da cewa, "mai zai hana Ni zuwa Madina? Ai ban manta da ke ba, bazan taSa manta wa da ke ba har abada kina raina, mu shiga ciki zamu fi gaisawa sosai, kinga ki share hawayen ko tunda gamu."

Hannuna Waya na sanya a saman fuskata ina mai share hawayen, inda muka shiga ciki gaba Waya muka zauna a saman Kujerun Falon, dukkansu sai kallon falon suke yi suna mamakin kyawun sa da alatun da ke ciki, musamman Yaya Haula wacce bata saba ganin irin sa ba, gwara ma Umma tunda tana aiki gidan Hajiya Ummee bata wani nuna kauyancin ta ba, amma tayi mamakin ganin gidan Yaya Yunus Win, tare da tunanin duk wannan daulan nasa ne kenan? A nan ´arta take rayuwa?
Ita kanta Yaya Haula abun da take tunani Kenan, sai kawai tarin farin cikin ta ya yalwata tana ganin inda ´ar uwanta ta samu ci gaba,
Yayinda dukkansu kallona suke yi cike da burge wa don ba ™aramin sauya musu nayi ba a wannan ™an™anin lokacin, baza ka taSa tunanin Ni bace sabida fatar jikina ta ™ara haske da she™i, ainahin fatata ta sake fitowa sabida samun hutu da jin dadi, ga dai shi ba wani daWi nake ji a gidan ba, amma yanayin sauyin wuri da kuma AC da ke ratsa Ni; shiyasa nan da nan jikina ya sauya, da alamun jikina bai da wuyan sauya wa ne don su mamakin ganin kyawuna suke yi, duk da sun ga ´ar raman da nayi a fuska kasancewar fuskar tawa bata ™ara komai ba, idanuna suna waje har yanzu sun sake fitowa ainun, har da ™ashin wuya, amma gani suke yi kamar na ™ara tsawo da girma kaWan da kyawun fata,
Sun ji daWin ganina a haka matu™a,
Amma duk da haka Umma sai tambayana take yi yanayin zaman nawa tana ce min, "babu wata matsala ko?"

Ko kusa ban faWa mata halin da nake ciki ba, duk da a lokacin ba wai na dena hawayen nawa bane sabida tsananin kewarsu da nake ji, a tsakiyar su na zauna na ™an™ame su; su dukka kamar za a ™wace min su

Umma da ke kallona ta shafa kaina cike da samun natsuwa kaso bakwai bisa goma na daga damuwar da ke damun ta, take ce min, "to mene ne na kukan wai Madina? Ko dai akwai abun da ke damun ki ne kin Soye min kin ™i ki faWa? Ko kuma Yayan naki yana miki wani abun ne baza ki iya sanar min ba?"

Da sauri na girgiza kaina ina mai cewa, "a'a Umma, babu abun da ake min, ina jin daWin zamana, amma Umma kewarku nake yi, na san zaku tafi ku bar Ni."
Sai kawai wasu hawayen masu zafi suka sake wanke min fuska

Yaya Haula da ke dariya tace, "haba Madina, mene ne kuma na kuka tunda Allah ya kawo ki inda za ki huta? Ai nan ya fi wancan ™auyen namu gwara zamanki a nan wlh, ba ki ga yanda kika sauya bane, kuma a haka za ki saba ai tunda zaman aure ne bamu da yanda zamu yi. Kinji don Allah ki dena kukan nan ba na son ina ganin ki cikin damuwa, Ihsan ma tana gaishe ki, ita ta bani sa™o da kanta da nace wurin ki zan je."

Murmushi nayi kawai na kasa cewa komai ina mai share hawayena, sai kuma na gyaWa kaina ina kuma dariya ina kallon cikin Yaya Haulan da ya Wan tasa alamun ciki take dashi, amma Ni ban fahimci komai ba

Hira muka soma yi duk yawanci tambayoyi ne Umma take ta min cike da kula wa da son gane abun da ke damuna, Ni kuma ina bata amsa cike da Soye halin da nake ciki don kar ta gane, don bazan so ta gane wanne irin zama nake yi a gidan ba, sabida ban shirya zaman aure ba, zamana a haka ya fi min alheri gwara in dauwama ina musu bauta,
Koda ta nemi in kaita Wakina su gani; ban wani ji War ba tuni na ja su zuwa Wakin tunda na manta da tunanin zaman aure nake yi a gidan

Basu ga aibun Wakin ba kuma hakan bai saka musu wani zargi ba, duk da bai da wani girma sosai, kuma babu komai sai kayan gado da sif, Umma dai bata ce komai ba har suka shiga bayin suka yi alwala suka yi sallah ina zaune tare da su, nima tuni nayi alwalan na gabatar da sallan,
Sai lokacin take tamabayana inda mutanen gidan suka je?
Ina bata amsa kuma sai na tuna ai fa girki nake yi,
Jikina na rawa na mi™e ina salati na fita da gudu,
Umma na kirana amma ban tsaya ba,
Hakan ne yasa Yaya Haula ta bi Ni da saurin ta tana sake kiran suna na, inda ta ga na bi nan ta bi muka shiga kitchen Win kusan a tare,
Koda na buWe tukunyar har ruwan da nayi sanwa ya kusa ™are wa,
Ganin yanda na ruWe sosai sai Yaya Haula tace min, "wai mene ne kika ruWe haka? Dama girki kike yi kika bar shi haka nan?"
"To Yaya Haula farin cikin ganin ku ne ya mantar da Ni fa, yau na shiga Ukuna idan Aunty Sharhabila ta dawo ban gama ba, tace min karfe biyu zasu shigo."

Ganin dai kamar hankalina ba ya jikina ne duk na bi na ruWe, abun da ya Wan bata mamaki, amma bata tsaya tamabayana ba sai ta hau taimaka min, tunda dafa-dukan shinkafa zan yi shiyasa nan da nan ta taimaka min muka yi a tare, lokacin ™arfe Waya da ™wata ne kafin biyun har ya kusa tsotse wa,
Muna a kitchen Win na ji ™aran buWe gate, da sauri na Wauki cooler ina cewa, "Yaya Haula wlh ga su nan sun dawo, bari in kwashe haka nan kar tace ban gama da wuri ba."

Ganin yanda jikina ke rawa sai ita ta amsa ta kwashe sabida kar in zubar in ™ona kaina,
Bayan ta kwashe ta bani na fita dashi, ita kuma ta tsaya kashe risho Win

Lokacin da na isa falon har sun shigo Yaran suna ta tsalle-tsalle

Itama Umma jin motsin su ne yasa ta fito daga Wakin da nake kwana zuwa falon don su gaisa;

Please Login or Register in order to submit comment