Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Waukar mataki a kan duk wanda yayi mummunar aika-aikan nan, already fa ya Sarka ta yayi mata illar da zai yi wuya bata samu matsala ba."

Jinjina kansa yayi zuciyarsa na zafi sabida takaicin abun nan, sai yace, "Doctor Jamila Let's do our best to save this girl, Insha Allah hakan bazai gagara ba, bamu da ishashshen lokaci yanzu; Please mu ™o™arta."

Don haka cikin azama suka soma ™o™arin daidaita numfashin ta before su fara ba ta taimakon gaggawa,
Daga ™arshe dai dole suka kwance mata Winkin buhun da aka yi mata, wanda shi ya ™ara taSarSara wajen; wurin yayi Wanye hakan yasa sun gagara yin mata wani sabon Winkin, dole sai an bari wurin ya Wan yi ™arfi before su sake mata sabon Winki, gaskiya sun tausaya mata duk da har  wannan lokacin bata farka ba, amma sun samo numfashin ta, kuma sun yi ™o™arin yin mata alluran rage raWaWi wanda zai taimaka mata,
Dole aka sanya mata drip da jini a time Win; don bata da ishashshen jini wanda hakan ne yasa kamar ta shiga coma; har da oxygen aka saka mata,
Gaskiya a halin da take ciki sai du'a'i tunda addu'ar take bu™ata

Sai da suka gama tsab before Mashkur ya fita ya samu su Hajiya Ummee a waje har lokacin,
Kuma har wannan time Win Umma hawaye take yi ta kasa zaune ta kasa tsaye, sai ma Hajiya Ummee ne take bata baki tana mata nasiha tare da nuna mata, "addu'a kawai yarinyar take bu™ata."
Suna ganin fitowar sa sai suka nufe sa hankali a tashe, Hajiya Ummee tayi saurin cewa, "ya jikin nata Mashkur? Ya ake ciki ne?"

˜o™arin Soye damuwar fuskarsa yake yi, sai yace, "Hajiya da sau™i za a ce tunda mun shawo kanta tana numfashi yanzu haka, sai dai dole zamu yi hakuri har zuwa wani lokaci domin samun lafiyarta, sau™i sai a hankali, yanzu haka muna son a yi mata aiki a wurin ne amma sai dai zuwa nan da kwana biyu after ta samu ™warin jikinta."
Bai musu bayanin halin da take ciki gaba Waya ba don kar hankalin su ya sake tashi, musamman mahaifiyarta, tunda yanzu haka ma yabar doctor Jamila tana sake bincike sosai a kan yarinyar; since abun da ya fi Waga musu hankali ™ananun tsutsan da suka ga sun faWo daga jikinta, hankalin su yayi matu™ar tashi sun girgiza ™warai da gaske, shi kansa ya rasa ma abun yi amma yana kyautata zaton duk yanda aka yi akwai abun da ke faruwa da ita, wannan ba haka kawai aka kusance ta ba, dole an gwada mata mugun ™arfi wanda abun ya nuna musu kamar ba mutum daya bane yayi aika-aikan, wannan ya fi ™arfin fyaWe

Cikin kuka Umma tace, "to yanzu zan iya zuwa in ganta?"

Kallonta Mashkur yayi gunun tausayi, cikin natsuwarsa sosai da kamalan sa yake ™ara kwantar da murya tare da furta, "no ba yanzu ba gaskiya, don a halin yanzu duba ta ake yi, sai dai ku ci gaba da mata addu'a don abun da take bu™ata kenan a wurin mu, amma shi wanda yayi mata aika-aikan nan yana ina? Aina za a same shi?"

Murya a raunane Umma take faWa mishi abun da ta sani tunda Haula ta sanar mata guduwan da Alh. Badamasi yayi, yanzu haka ba a san inda ya tafi ba

"Amma wannan mutumin an yi asararre, Allah sai ya saka mata da ikon Allah, iyayenta sun cutar da ita tunda su ne sila, Allah ne gatan ta Insha Allahu zata samu lafiya nan kusa, don Allah Mashkur kayi iya ™o™arin ka wajen samun lafiyar yarinyar nan; domin mu ne gatan su a yanzu, muna da damar taimakon su."

"Insha Allah Hajiya zan yi iya kokarina, zata samu lafiya ta warke kamar kowa, addu'a kawai take bu™ata, kuma na so a samu yanda za a yi a bincika inda mutumin nan yake, domin wannan ba abun bari bane, laifin fyaWe a kansa dole ne a hukunta shi, in har za a ga Mutumin nan dole mu gabatar dashi a kotu."

Hajiya Ummee tace, "nima abun da na gani kenan, tunda Ansar yana nan a Kaduna bai koma ba ka ga zamu samu sau™in samun lauya, shi sai ya tsaya mata."

Mashkur yace, "mu bari dai idan muka koma gida sai muyi zancen, amma yanzu zan sake kiran ´an sandan nan zasu koma can su binciko inda za a same shi, yanzu abun da za a yi ku koma gida please sabida zaman ku a nan babu wani amfani, akwai nurses Win da zasu kula da ita."

Jin hakan yasa dole suka yi masa sallama suka tafi gaba Waya, kai tsaye gidan Hajiya Ummee suka wuce tunda Hajiyan tace, "su je can inyaso ta daukar musu taliya ita da ´a´anta su je su dafa."
Umma tace, "a'a ta bar shi don Allah, suna da abincin su ma, don akwai tuwo ta san zasu Wumama su Hassanan su ci."
But Hajiya tace, "A'a, su je ta Wauka tunda tayi ninyar basu."
Dalilin da yasa suka tafi gidan kenan, bayan ta cika mata leda da kayan abincin sannan tayi mata godiya sosai har da du™a mata a ™asa,
Cikin rashin jin dad'i Hajiya tace, "babu godiya tsakaninmu Asiya, abun da yayi ki shi yayi mu, duk mu tsatson Annabi Adam da Hauwa'u ne, idan bamu taimakawa na kusa damu masu bu™ata ba; to wa zamu taimaka wa? Don haka ki dena godiya ´a´anki tamkar jinina ne, duk abun da zai same su zan yi iya yi na don basu kariya tunda zaman tare muke yi, Allah ne ya haWa mu don haka dole in taimake ki, yanzu ma kinga abun da Mashkur yace, inhar an samu Mutumin nan to Insha Allahu sai mun kaishi ™ara kotu, mu da muke da hanya kala-kala ai abu mai sau™i ne a Waure shi har igiya sai tayi ra-ra, kinga shi ˜anin Mashkur Win; wato Ansar kenan, wanda ya zo gidan nan kwanaki, ai lauya ne shi, kinga bamu da matsalar samun wanda zai tsaya mata a kotu, kuma duk halin da aka shiga ya wuce tunanin mutane babu mai iya ja dashi bare ya ka dashi, in dai an samo mutumin nan to Insha Allahu ina tabbatar miki Ansar zai tsaya mata tunda bai rigada ya koma Riyadh ba, don haka ki je ki kwantar da hankalin ki ko nawa ne zamu kashe don samun lafiyarta, fatan mu dai Allah ya bata lafiya mai amfani, Allah ya tashi kafaWun ta, kar ki sa damuwa kinji ko? a yi ta ha™uri Allah zai yi mana maganin abun."

Sosai Umma ta dinga mata godiya har da kukan ta, sai da™yar ta tashi ta tafi zuciyarta cike da farin ciki da samun natsuwa, da ba don su Hajiya Ummee ba da bata san ya *RAYUWAR MADINA* zata kasance ba? Allah kenan mai yanda ya so kuma ya taimake ka a sanda ya so,
Ba abun da zata yi musu sai fatan alkhairi da fatan gama wa da duniya lafiya, idan za a samu irin su a al'umma ha™i™a ba mai zubar da hawaye, ga shi da iya ™arfin su da aljihun su sun shiga sun fita sun taimaka mata; bayan babu wata ala™a mai ™arfi a tsakanin su, Allah shi ne abun godiya.*****

_____A ranan haka Mashkur ya sake biyan ´an sanda suka koma can ™auyen domin gudanar da bincike a kan Alh. Badamasi,
Sai dai koda suka je babu labari mai daWi tunda duk tuhumar da suka yi wa iyalansa; sun tabbatar musu da cewan, "Alhaji ya gudu, ya kwashe kayansa ya gudu."
Sun yi iya yin su don su gano inda zasu same shi amma babu wani labari, dole suka dawo suka sanar da Mashkur, "mutumin ya rigada ya gudu, kuma ga dukkan alamu baza su iya samo shi ba. Amma zasu ci gaba da bincike."

Wannan dalilin ne yasa suka ha™ura da neman Alh. Badamasi tunda ba a ganshi ba,
Yayinda aka ci gaba da kula da Madina wacce har lokacin bata farfaWo ba bata san halin da take ciki ba,
Mashkur yayi iya yin sa wajen bata taimako, domin shi da kansa yake kula da ita sabida tsananin tausayin ta da yake ji, yarinya karama Kamar wannan an cutar da rayuwarta an yi mata mummunar illa, ya rasa ma ya zai yi ya fassara wannan bada™alar tunda wurin har yanzu fitar da wasu ™ananun tsutsotsi yake yi,
Hakan yasa dole a washe gari da aka yi ninyar yin mata aikin, sai aka dakatar da yi sabida a samu tsutsotsin su dena fita, shiyasa ake wanke mata wurin ana treating, abun da zai baka tausayi yadda ta kamu da laluran yoyon fitsari; wanda hakan ne yasa aka sanya mata kwararin roba, tunda har kashi da fitsari fita suke yi babu notis,
Wannan dalilin ne yasa ma har lokacin Mashkur bai bari kowa ya ganta ba,
Kullum su Umma sai sun zo da Mijinta da kuma Hajiya duk tare suke zuwa, amma yace musu, "su bari sai an yi aikin zasu iya ganin ta, sai dai su yi hakuri, don a yanzu ma bata farka ba kuma ba sa bu™atar hayaniyar kowa a inda take."

A kullum ranan duniya sai Umma ta sha kuka ta gode wa Allah sabida tunanin ´arta, don gani take yi tamkar Mashkur yana Soye musu halin da take ciki ne maybe ta mutu ma bai sanar musu ba, tunda a ce har yanzu bata farka ba yau kwanan ta uku a kwance

A kwana na huWu ne sai ga Haula da Baffa sun zo Birnin Zarian suma, can gidan Umma suka wuce suka same ta a can,
Da farko Umma ta so ta yi wa Baffa tijara ne, sai dai kasancewar yanda ya zo mata da nufin bata ha™uri sabida halin da suka jefa Madina,
Shi ne dalilin da yasa ta dakata har ta iya sauraron sa

Ita kanta Yaya Haula kukan da take yi a kwanakin da halin da ta shiga duk ta sauya ta rame gaba Waya, kwata-kwata bata da sukuni tun a ranan ta so ta biyo su Umman, amma bata samu dama ba tunda Mijinta ya hana ta, kuma yace mata, "bai da kuWin da zai bata ta je can, tayi ha™uri har ya samu."
Shi ne dalilin da yasa ta ha™ura amma kullum cikin kuka take da tunanin wanne hali take ciki ´ar uwanta? Ga shi wayanta tuni ta sake lalace wa tunda Ihsan ta jefa mata shi a cikin ruwa, har yanzu ba a gyara ba, koda ta kira Umma ma wayan Mijin take ara

Ana haka kuma sai ga Baffa yau ya zo har gida yace, "ta shirya sai ta raka sa birnin tunda ita ta san inda Umman take zaune, su je su duba jikin Madina."
Wannan yasa ta ji dad'i sosai ta shirya nan da nan ta tambayi Mijinta ya barta, daga nan suka taho cikin Zaria,
Wanda shi Baffa ya so su taho da ´an uwansa a duba jikin nata, amma Baban Sasa yace, "babu ruwansu, shi in ya ga zai iya zuwa ya je ya ganta."
Shi kuma Baffa abun da yasa ya damu don ya ga shi ne silan komai, da bai yi mata hanyar auren Alh. Badamasi ba; da duk hakan bata faru ba, duk da bai isa ya sauya ™addara ba, amma bazai taSa sukuni ba har sai ya ga halin da Madina take ciki, shi ne dalilin zuwan su tare

Kuma sai dai sun so su ga Madina amma babu hali, don Umma ta faWa musu, "ko sun je asibitin baza su samu ganinta ba, Likitan ya hana a ganta, addu'ar su kawai take bu™ata."

A wannan lokacin sosai kuka ya dawo wa Haula sabo, sai kuka take yi tana cewa, "ita baza ta koma ba har sai ta ga ´ar uwanta."

Baffa shi da kansa ya rarrashe ta yace mata, "zasu dawo daga baya su ganta, zasu rika zuwa Insha Allahu akai-akai suna duba ta."

Da haka suka koma gida batare da sun je asibitin ba,
Wanda Baffa ya dawo cike da damuwa yana sanar da su Baban Sasa halin da ake ciki

BuWan bakin Baban Sasa yace, "ai kamar yanda Asiya ta nuna mana rashin kunyarta har ta nemi ta ci zarafin mu, babu mai taka wa zuwa duba yarinyar nan har sai idan ta warke, kuma shima don in nuna mata ikon mu fiye da nata ne, wlh summa tallahi tunda Asiya ta wula™anta mu sai ta ga abun da zai biyo baya, da zaran ta gama iddarta Insha Allahu sai na Waura mata aure."

Baffa cike da damuwa yake cewa, "don Allah Yaya a duba wannan zancen, kar mu sake tafka babban kuskure a kan wanda muka yi, itama Asiya tana da hakki a kan Madina, kamar yanda muka yi mata auren nan a baya abun bai zo da dad'i ba, mu bari a samu tazaran lokaci har ta warke ta manta da wannan abun da ya faru; tukunna sai mu samu damar yin mata wani auren, kuma ka ga dole sai mun yi tunani kafin mu san wanda zamu sake bata, kar mu tafka wani babban kuskuren, ka ga har da laifin mu tunda bamu duba ™an™antar Madina ba muka bata Mutumin da a haife ya girmi Mahaifinta, mu nema mata dai-dai ita."

"To kana so ka nuna min ban isa bane Ali? Ko kuma kana so ka ce abun da muka yi ba dai-dai bane kuskure ne?"

A yanda yayi maganar a fusace shiyasa Baffa yace, "a'a Yaya, ba wai haka bane..."

"Kayi min shiru da Allah in har ba so kake mu fara jayayya da kai ba, abun da ya faru da Madina tsautsayi ne kuma yana kan kowa, Alh. Badamasi shine ya cuce mu ya wulakanta mana ´a ya tozarta ta, kuma yanzu ya mayar da ita Bazawaran ™arfi da yaji; kana ganin zamu barta ta zauna a haka ne bamu nema mata wani Mijin ba? Ko kuma so kake yi mu barta a wurin uwarta ta zama ´ar Mace tamkar bata da mafaWi ko kuma danginta sun ™are a duniya; Ta lalace daga baya ta Sata mana suna a dangi? to hakan baza ta yiwu ba, kowacce Mace gatanta shi ne gidan Mijinta, don wannan tsautsayin ya same ta ba hakan ke nuni da cewan zamu bar Madina haka nan har takai wani munzali babu Miji ba, ka san dai a nan bamu barin yarinya babu Miji balle wacce tayi aure ta fito, ko ma mene ne na gama magana da zaran Madina ta gama iddarta nan da watanni huWu za a Waura mata Aure".
[2/2, 9:35 AM] OumŠahira: =ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ
    *RAYUWAR MADINA* =Ĝ§Ü
=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ=ĜŽÜ


_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA'IL*
           _(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT>ĜŬŬ*



*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* <Ĝß

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS=ĜŞÜ)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

       *P.W.A
'ŝ*





            *SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ´an uwana Mata waWanda suka fuskanci u™uban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ™arshen wahalar rayuwa._







*DATA SHARE*

Call, message or whatsap  07065334256

*MTN*
500MB 150
1gb  280
2gb.  550
3gb.   840
4gb.    1120
5gb      1400
6gb.     1700
Verlid for 30 days.



















______________ *EPISODE 17*
_____A cikin sati Waya da kaini asibitin; sannan na farfaWo, wanda yayi dai-dai da lokacin da za a yi min aikin da aka sanya rana, tunda ganin halin da nake ciki dole sai da aikin a nan kusa, duk da ba a so taSa ni ba sai wurin ya Wan yi ™arfi ta yanda zai Wauki aikin, domin har lokacin basu ga sauyi ba na daga yanayin wurin,
Zafin ciwon da nake ciki bai sa na dawo cikin hayyacina ba, don a lokacin zan baka tausayi sabida kwata-kwata ba na gane komai, kawai a farke nake da kukan kiran UmmanA; baya ga haka ba abun da nake yi

A ranan da aka yi aikin wanda suna saka ran samun dacewar aikin,
Sai dai kuma hakan ya gagara tunda kusan kwanaki biyar ban farfaWo ba, kuma abun da ya basu mamaki yanda har yanzu ina yoyon fitsari ban dena ba, hakan ne yasa Mashkur ya maida mini da roban da aka sanya min, ransa duk babu dad'i wanda sai da suka sake du™ufa a kaina da ya™inin dole a sake min wani sabon aikin,
Amma ganin ban farka ba shine yasa aka dakata don ganin farkawa na da samun lafiyata; sai a sake wani sabon aikin, idan ba haka ba Shikenan na kamu da cutan kenan

A kwana na shida ne hankalin kowa ya kwanta sabida farkawata, sai dai ba na gane komai da kowa a wannan lokacin, tsawon kwanaki uku ina cikin wannan halin, wanda su Umma kullum sai sun zo duba Ni, tunda aka yi aikin ake barin su suna gani na,
Umma tayi kuka har ta godewa Allah, yanzu ma idanun sun soye sai dai addu'a da kullum take min domin Allah ya bani lafiya, amma ha™i™a kowa ya tausaya min, sabida halin da nake ciki, tamkar bazan rayu ba, don duk a tunaninsu mutuwa zan yi,
Sai dai aka ce ciwo ba ya kisa sai idan lokacin ka yayi

Da taimakon Allah da kuma jajircewan Mashkur wurin kula dani da bani duk wata kariya a matsayina na mara lafiyarsa; cikin hukuncin Allah kusan sati biyu da yin aikin na soma gane kowa da komai, domin a lokacin har abinci ana bani ina iya zama kaWan, sai dai yanayin da na tsinci kaina da kullum kuka babu ™a™™auta wa; shi ya fi komai Waga wa su Umma hankali,
Babu abun da suke yi illa rarrashina da ririta ni kamar ™wai, amma kwata-kwata na kasa saba wa bare in dena zubar da hawaye, musamman a halin zafin ciwon da nake ciki, ga kuma tashin hankalin ganin cutan da ta same Ni na yoyon fitsari, shiyasa kullum kukan nawa ke daWuwa tare da firgice wa su Umma; ga shi har hakan ya soma taSa min ™wa™walwata don tamkar mahaukciya haka na koma, bani da maraba da ™aramar yarinya kullum a firgice nake babu natsuwa bare kwanciyar hankali a tattare dani, kai bani kaWai ba har su Umma babu wannan kwanciyar hankalin a tattare dasu, tunda ga shi jikin nawa ya ™i dad'i tsawon wannan lokacin, ga yawan firgitan da nake yi kullum ina manne da ita ba na yarda da kowa sai ita, duk rarrashin da za a yi min ba na yin shiru, sai idan an yi min alluran barci sannan nake huta wa suma su samu sau™i, abun tashin hankalin ma yadda da zaran na ga namiji zai zo wurina sai haukan nawa ta motsa, na dinga ihu da kururuwa ina faWin, "ga shi nan zai zo, zai kashe Ni, ku taimaka min."
Don tsab nake ganin kowanne namiji tamkar Alh. Badamasi ne ya biyo NI, abun da yayi min ya taSa Ni sosai ya saka Ni a halin Wimuwa da firgita

Dalilin da yasa Mashkur ya dena zuwa duba Ni kenan, dole yake bari Dr. Jamila Abokiyar aikin sa take duba Ni, tunda ko ya zo haka shima zan ri™a mishi ihu ina sambatu, sai ya Waga ™afa yana bari Dr. Jamila tana duba Ni, sai Nurses da suke kula dani,
Kuma halin da na shiga dole aka soma duba min ™wa™walwata sabida suna ganin kamar na samu matsala,
Sai dai koda aka duba babu wani abun da ya samu ™wa™walwan tawa normal ne, kawai dai abun da Alh. Badamasi yayi min ne yayi kamar ya zautar dani, har yanzu ban dawo cikin natsuwata sosai ba, wanda suna fatan nan kusa komai ya wuce da ikon Allah

Su Yaya Haula sun sake dawowa ita da Mijinta da kuma Baffa suka zo, sai Yaya Shamsu da Yaya Nasiru, su biyar suka yo tattaki har asibitin tunda Umma ta sanar musu da farkawan nawa; bayan sun yi waya tare da Baffa, wanda ya kira ya tambaye ta sai ta sanar mishi, basu samu damar zuwa ba sai wannan lokacin,
Abun zai baka tausayi a halin da suka ganni, su kansu sai da suka yi kamar zasu zubar min da hawaye, tunda a lokacin ina farke ne basu yi tsammanin farkawa ta ba, lokacin Dr. Mashkur ya shigo yana duba Ni zai saka min wata allura a cikin ruwan da ake ™ara min, kawai sai na farka wanda yayi dai-dai da buWe idanuna na zuba a kansa, take na tsandara uban ihu ina kiran sunan Ummana, take a nan na sume gau

Hankalin kowa ya tashi ainun, barin ma Dr. Mashkur da nan da nan ya ™ufe wajen ceto numfashin nawa,
A wannan yanayin ne mutanen gidan mu suka zo suka tarar da Ni, babu wanda bai tausaya min ba,
Ita kuwa Yaya Haula kuka ta sanya kawai tsaban kiWima da ganin halin da nake ciki,
Babu wanda zai iya gane Ni a halin da nake ciki, na canja gaba Waya na koma tamkar bani ba, nayi wani irin rama tamkar ´ar ™aramar yarinya haka na koma, sai ™asusuwa da suka fito a saman wuyana da ™irjina tunda babu ko riga da aka sanya min, sai wani gajeren wando da ke jikina wanda aka suturta min al'aurana, shima yana da faWi don kar ya fama min aikin da aka yi min, yadda ka san Aljana haka na koma musamman yanda na sake Washe wa nayi fari tarr kamar babu jini a jikina ko ruwa, bayan kuma duk an ™ara min amma kamar ba a saka min ba, bakina ya bushe yayi ™amas sai fatan da ya Wago ya SaSSare har da jini a laSSan

Yaya Haula ta kasa yin shiru sai da ta ji Baffa yace mata, "yanzu zasu koma in har bata dena kukan nan ba, tunda tana Waga musu hankali."
Hakan ne yasa dole ta shanye kukan nata har suka Wan jima a asibitin sannan suka tafi, ko gidan Umma basu je ba suka wuce don a halin da suke ciki babu wanda zuciyarsa take mishi dad'i, tabbas sun tausaya min ba kaWan ba, sun tafi da jimamin halin da nake ciki, suna ganin kamar bazan kai gobe ba sai wani ikon Allah, kowa yana min fatan samun lafiya a ransa; yayinda zuciyoyinsu a karye cike da sanyin jiki haka suka koma gida

Umma tun ranan da na farka ita take zama dani, tunda a halin da nake ciki dole sai tana kusa dani, don Ni kaina ba na barin ta jirga a jikinta nake kwance, dole sai tahau kan gadon ta ri™e Ni,
Baba ne kaWai yake koma wa gida tunda shima kullum sai ya zo musamman in ya dawo daga sana'arsa, wani lokacin yana tahowa da su Hassana sai su duba Ni tunda su kansu a damuwa suke rayuwa, sai dai kasancewar yadda suke Waga hankalin su sai ya dena zuwa dasu sosai, sai idan an kwana biyu sannan suke zuwa

Ita kuma Hajiya Ummee ita ta Wauki nauyin kawo mana abinci asibitin kullum, ko bata zo ba zata aiko driver dashi a kawo, itama sosai take kula damu don an zama ´an uwa yanzu, tana jin mu tamkar ahalin ta, tana kallona tamkar jikarta, shiyasa ba ta gajiya da mana hidima

Shi kuma Mashkur dolen sa ya dena zuwa duba Ni koda ina barci ne, dole Dr. Jamila ce take min komai har lokacin da komai ya soma lafawa, tamkar komai bazai wuce ba haka rayuwar take tafiya, amma kuma yau da gobe tun ban saba da halin da nake ciki ba har na soma saba wa, musamman kasancewar akwai UmmanA a tattare dani, tunda tayi min alkawarin, "baza ta taSa barina ba, zata zauna dani a koyaushe."
To yawan buWe idanuna ina ganin ta a tare dani; shi ne yasa hankalina ya soma kwanciya har na fara ™o™arin saba wa da halin jinyar da nake ciki, ita take min komai ba ta bari Nurses suyi min, don da ita na fi yarda,
Tunda na ga Yaya Haula ta sake zuwa na ganta ido da ido; sai hankalina ya sake kwanciya ainun,
Sai dai ashe wahalar na gaba sabida har na soma jin sau™i kuma aka sake min wani sabon aikin, gaskiya na sha wahalar da Ni kaina bazan iya misalta shi ba, tamkar an sake famo min asalin kyambon ciwon ne, ciwon ya sake dawowa sabo dal haka na sha jinya kamar bazan rayu ba, na sake sauya wa fiye da baya, na rame nayi ba™i a wannan lokacin ko abinci ba na iya ci sosai sai dai a bani ruwa-ruwa sau Waya a rana, hakan ne yasa na ™ara lalacewa gaba Waya halin jinya yasa na sauya kamanni, komai sai dai a yi min don na fi satikai ba na iya

Please Login or Register in order to submit comment